Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sharaf wlh bazaki kwananmu a daki ba yau .
tashi maza ki koma parlour..wlh ni anan zan kwanta ...umma tashiga janta da karfin tsiya ta kaita parlour tare da ingizata tsakiyar parlour. tana kuka nadama tattare da danasani mara misaltuwa suka taru suka mata yawa.
hakika rayuwa na zuwa mata da abubuwa masu tsauri da azabtuwa.
wa zai taimakawa rayuwarta da rayuwar tilon diyarta ?
kuka take sosai har sanda taji ankira sallar magrib ta mike tashiga bayi ta daura alwala
tafito.
ta dan yaye labulan parlour warwass taganta kwance tana kwasar bacci kyakkyawar fuskarta ta sake fitowa sosai ta yi fiyat har yanzu tana nan da kyawunta sai dai farar fatarta data dan soma disashewa.
kallon su'ad umma ke yi tana kallon yadda tayi muguwar rama tare da canzawa ba wasu kayan kirki ne ajikinta ba nan take jikinta yayi wani irin sanyi tausayin ita da diyarta ya mamaye rurinta .
hawaye na sake ciccikowa a idanunta wace irin rayuwa ta sanya kanta ciki ?
kasa rike hawayen idanunta tayi hkn yasa suka samu nasarar saukowa cikin muryar sanyi tace ya Allah ka dubamin lama'rina dana yarinyata .
sannan ahankali ta saki labulen tazo ta shimfida abin sallah .
ta tayar da sallah .
byn ta idar ta dade zaune tana addu'ointa datasaba yi kullun tare da neman gafarar Allah da nemawar tilon diyarta shiriya agurin allah ..

sai wajen karfe dayan dare sannan su'ad ta tashi ta dawo cikin haiyacinta sharkaf da gumi.
gefe daya km ga radadin zafin ciwon jikinta .
hannuta na rawa tasa ta goge gumin daya rufe mata fuska kasancewar nepa basu kawo musu wuta ba ,tare da kallon agogon bangon dake manne da parlour da dan sauran hasken fitilar charge.
wasu zafaffan hawaye ne suka balle mata ta maida kanta jikin kujerar parlour 'n ta jinginar hawayen tausayin kanta na sake zubo mata idan abdulkabir ya auri wata macen baita ba batasan yadda rayuwarta zatakasance ba..
bata tunanin ruhinta da gangar jikinta zasu iya daukar wannan nauyi.
ya salam ta furta muryarta a sanyaye tana me mikewa tsaye ta kakkabe jikinta tare da shafa raunin dataji a goshinta ta koma cikin daki.
ta iske ummanta kwance a kasa tana bacci ,numfashinta na fita da karfi da jin yadda numfashinta ke fita tasan kuka tayi me tsanani .
karasawa tayi kusa daita ta sunbaci goshinta ummana ba nufina na kasance yar iska ba... naso na zamemeki sanyi idanunki ..
amman kiyi hkr ki cigaba da min addua .
im very sure wata rana i will change .
ta dago ta tsallaketa .
ta nufi bayi tayi wanka tare da dauro alwala sosai taji dadin jikinta sannan ta gabatar da sallolinta .
tana idarwa wucewa tayi makwancinta ta zauna tare da takure jikinta guri daya akan gadon ta tuno rayuwarta ada cike da farinciki da soyayyar ummanta, sabanin yanzu da komai na rayuwa ya sauya mata , ta zabi wannan rayuwar ne akan samun farincikinsa ....
amman duk da hk bai tausayawa rayuwarta ba. daita da banza duk daya ya daukesu .
ahankali ta zame ta kwanta tana tunani .....tare da sake takure jikinta guri daya atsakiyar gadon.
hb abdulkabir bai kamata ka wulakanta soyayyata ba sbd mahimmancinta gareka..
na zabi farincikinka akan komai dake cikin duniyar nan ,dan kawai na rayu dakai wa zan gayawa taskon rayuwar dana shiga akanka ya fahimceni?
wasu siraren hawaye ne masu zafi suka tsiyayo mata .
ranar da kyar tasamu ta runtsa wanda har da mafarkinsa tayi tana rokonsa yasota ya yantota daga shigin wasu..
amman furrrr yaki yace mata sam shi baya sonta baya kaunarta km bazai taba kaunarta ba......

washegari wani irin matsanancin zazzabi ne ya rufeta sakamakon raunukan jikinta.
gbdy ilahirin jikinta yayi mata tsami da kyar take iya bude kumburarrun idanunta dake like .
ga jikinta dake kirma, umman su'ad wace ta dade da tashi har tasoma aikace aikacenta na yau da kullun tashigo dakin ta duba ko su'ad din tashi ta cire kayan jikinta domin ta wanke. turus tayi sakamakon yadda taga idanunta da goshinta yayi .
kasa hakuri tayi takarasa zuwa kan gadon datake zaune hawaye na fita cikin idanunta ta rungume su'ad da sauri hawayen idanunwanta na saukowa cikin rawar muryar tace su'ad wace irin rayuwa kika zabawa kanki.?
wannan rayuwar sam bata dace dake ba kiyiwa girman Allah ki tausayawa rayuwar ummanki ki dawo ta kwarai .
duk duniya bani da kowa bani da komai sai ke kadai da Allah yabani....yanzu waye wanda bai da imani da tausayi yayi miki hk.?
wani irin sanyi jikin su'ad yayi idanunta suka sake cikowa da ruwan hawaye ita kanta batason takasance cikin wannan rayuwar me cike da sarkakiyar da kaskanci.
hakika wannan yanayin yakasance lokacin bakincikinta ne da rashin kwanciyar hankali gareta.

waye wanda keson kashe min ke..?

kiGaya min dan gidan ubawaye yayi miki wannan dukan?

ahankali su'ad tasanya duka hannuta ta rungume mahaifiyarta dake rungume daita tana kuka.
umma ta zare jikinta tana goge mata hawaye .kigaya min wanda yayi miki illa hk da ala'mun ma kasheki yake son yi...
hannuta takai kan fuskar mahaifiyarta tana goge mata hawaye muryar a raunane cike da sanyi , ummana ko na gaya miki wanda yayi wannan duka babu abinda zaki iya yi akai....
afusace tace Ki gayamin yau me rabani da uwarsa sai Allah sai yagaya min dalilin dayasa zai aikata miki hk ..
, dan gidan tsohon ambasodor kasar nan ne yayi min hk....
nagaya miki nasan babu abinda zaki iya akai..
domin kasancewrmu kaskantattu marasa gata da galihu.
ummana ki sanar dani inda daginki ko na mahaifina suke idan km banida su na hakura. na sanyawa zuciyata salama da dangana narashin dangi..
hakika ina son insan inda yan'uwan mahaifina suke koda kuwa zasu dinga dibar namar jikina ne .
ina kwadayin sakasu cikin idanuwana.
nayi rayuwa tare dasu .tunda su'ad tasoma mgnr kirjin umma ke bugawa babu abinda tafi tsana arayuwarta sama taji wannan kalmar abakin tilon diyarta. domin bata shirya bata amsoshin tmbyoyinta ba. dan hk ta hade rai tmkr baitace yanzu take kuka da nuna kulawa me tattare da tausayawa ba .muryarta a kausashe tace idan kika sake tayar min da wannan zance ban yafe miki ba.. kina da gata tunda kina dani ...
nice uwarki nice ubanki dama danginki gbdy .
na dade da meye miki gurbinsu ..
komawa su'ad tayi ta jingina bayanta da bangon dakin tana jin yadda numfashinta ke fita da zafi kasancewar zazzabi jikinta.
ta runtse idanunta tana kissima abubuwa masu yawa cikin ranta..

wace irin rayuwa ce hk ?

meyasa umma batason nayi mata zance mahaifina ko danginsa danata ?

why why why ummana ki taimakawa rayuwar su'ad dinki ko zata ragejin radadin da nauyin da kirjinta ke mata a duk sanda hkn yataso..?

ki sanar min idan ni din mara usuli ce nasani na dauki kaddarar ,irin wace ya'ya marasa galihu suka dauka..
da wannan tunanin ta wuni a daki ranar babu inda ta leka tana kwance tana jinyar kanta dan sai datakai umma ta kira mata nurse gida.
tayi mata allura da karin ruwa duk wannan azabar datake ji ajikinta hkn bai sa ta manta ak acikin zuciyarta ba.
tuninsa yaki barinta yana nan makale akirjinta.
yayinda kawayenta maza da mata suka shiga kai kawo acikin gidan dubata sbd ore tasanar musu da batun rashin lfyrta ..aiko umma taga jama'a har dana wasu unguwanni. ita dai ido ne nata..
lokacin dasu babalaye suka zo sun iske an cire mata drip na uku ana shirin saka mata na 4 zama sukayi suna mata sannu da jiki.
yayinda nurse ke kokarin tsira allura cikin robar ruwa. ta motsa labbanta ahankali ina son nayi fitsari.ok kawai nurse din tace.
ore dake zaune abakin gado taja hannuta ta mikar daita tsaye sukayi toile tayi fitsari suka sake dawowa dakin.
ta kwanta kan katifa tana jin jikinta kmr an daura mata dutse ne sbd tsamin da yayi mata. nurse ta meida allurar cikin drip. da zata wuce take nunawa ore yadda zasu cire allurar daga jikinta da zarar ruwan yakare.
byn fitar nurse hira ta barke tsakainsu amman ban da su'ad dake kwance idanunta a runtse tunanin ak take. babalaye ne yayi gyaran murya tare da tmbyr su'ad garin yaya hk ta faru daita .

wai waye banzar dayayi miki wannan illa hk?

sai lokacin ta Dan bude kumburarrun idanunta kadan .
murmushi tayi wanda bai bayyana sosai a saman fuskarta ba, sannan cikin sanyayiyar muryarta tace wannan dukan na cakwakiyar ce wace zazzafar soyayya ta haifar daita..
take ya gano bakin zaren .ya gyara zamansa sosai .
byn mun rabu jiya ne yayi miki wannan dukan ko ya ? motsi tayi da bakinta kawai alamun eh .
akwai shegen dan iskan mutun ,me idanun mage . stop.. babalaye ta katse shi a dan zafafe .
dont acusing my Hrt I love him so much to the extend i can explain.
baki kawai ya tabe tare da cigaba da mgn amman dai bai gane shirinmu ba ko?
da kyar ta sake bude bakinta gsky bazance ya gane ba.
" dan bai nuna min hkn ba. Allah yasa kiyi nasara akanshi dan kina shan wahala .
ameen tace acikin kasan ranta.
me zai hana kibamu dama da tuni wuya tasakashi amincewa da soyayyarki ..
dariya take sonyi amman babu hali .
baku san waye abdulkabir ba that's why ni nasan halin kayana ku barni dashi kawai tayi mgnr cikin ranta.

zaune AK yake shida musty acikin a part dinsa mgn yasoma yi masa cike da natsuwa.
akan lamarin mahaukaciyar yarinyar.musty wace ce wannan yarinyar .....?sbd al'amarinta yana kokarin tauye zuciyata da lamurana... ina son sani wacece ita.......... ?
gsky ni kaina bansan kowacece ba.. jiya shine karo na 2 dana taba sanyata acikin idanuna sai dai ga dukkanin alamun tana mutuwar kaunarka.... zata iya komai akanka ciki har da sadaukar da raywarka me zai hana kasota ka aureta ka hadata da zeey.. shhiiii dakata mlm dan allah ba wannan banzanr shawarar nake bukata daga gareki ba..... who is she kawai na tmbyeka ba surutan iska ba.
da zaka zauna kana karanto min robbishi me zanyi daita kana tunanin ko matan Duniya sun kare zan aureta ne... ?
zaka iya shahada ka aureta ..domin banga illar aurenta ba.
banza stupid kawai ai bazaka tabani ganin illar aurenta ba tunda kaima Dan'wana shashanci ne dan shaye shaye ban ma san dalilin abinda yasa na sakoka cikin lamarina ba ,amman me zai hana kai ka aureta tunda bata da illa..? sbd batace ni take so ba ...kai tace tana so yayi mgnr yana nuna kirkinsa da yatsan hannunsa amman wallahi azim ina tabbatar maka da ni tace tana so.
zan aureta abdulkabir domin tausayawa rayuwarta. tabani tausayin sosai fiyye da tunaninka ..tsaki ak yaja da karfi yana mikewa tsaye tare da zube hannuwansa cikin aljihun wandonsa sai kayi tajin tausayin nata marasanin ciwon kansa kawai ,yayi shigewarsa bed room yabar musty zaune yana kallon bayansa cike da matsancin takaici.


cikin wannan shige da ficen da kawayen su'ad keyi gidan .
har tayi sati daya agidan batare da ta leka koina ba .
hkn yasa takarayin kyau ta warke simul tayi fresh bakace itace tasha dukan mutuwa ba.


ammi da Zainab har ma da iman ke kokarin shiga cikin harami kowanensu sanye cikin doguwar riga da hijab har kasa da safa. ahankali suka karasa gurin dawafi byn sun kamala da dawafi kowanensu addua yake cikin ransa .
ammi na tsananta addurta akan tilon danta dan har dawafi tayi masa na musamman akan lamuransa .
itama iman addua take akan lahirarta da samun miji na gari da samun nasara akan fine exam dinta dazata zana bana.
yayinda uwar gayya zeey tarasa me zata roka agurin Allah.
gbdy kunya rokon ubangijinta take sakamakon munanan halaiyenta gata dai gaban qaba amman tarasa me zata roka domin ko ta nemi tuba a halin yanzu ba tuban zatayi ba sanin datayi akwai aiki agabanta, sanan idan ma rokon ubangijinta zatayi akan soyayyarta da ak. gani take baza'a amsa mata ba. gbdy abin duniya ya taru yayi mata yawa,.
dan hk tasanyawa ranta zata sake dawowa tayi aikin haji domin sauke farali da neman tuba .
tunda daga ranar bata sake taka kafarta zuwa haram ba kullun sai dai ammi da iman suke zuwa ita km tana kwance.
tafi maida hankali a bacci akan abinda yakawota .
satinsu biyu sukayi dubai.

zaune yake shida karuwarsa onye a Z&Z CHICKEN SPECIAL dake cikin ijeka in side su'ad dake maseefar sonshi amman shi kwata kwata bata gabansa sbd ji yake duk duniya babu macen daya tsana sama daita .itace tsaye agabansu tana kare musu kallo cike da wani mahaukacin azababben kishi ... nan zuciyarta tasoma dugunzuma nan zuciya ya debeta ..
kirjijta na buguwa ta kai hannunta ta damki wuyanta ta matse hade da rigar jikinta....


mmn sudais ce

💗💗💗💗💗💗
SAI KA AURENI DOLE
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗



~NA~



*AYSHA A BAGUDO*



~DEDICATED TO~
HAUWA A USMAN
JIDDARH


*qala rasulillahi sallallahu alaihi wa sallam, man kala laila a illallah muklisan dakhal janna*



page 26


mikewa ak yayi cikin matsanancin bacin rai da niyyar dakatar daita ta hanyar cin mutuncinta amman tun kafin ya aiwatar da nufisa akanta tuni yaji tasoma yaryarfawa onye wasu mahaukatan maruka masu zautar da kwalkwaluwa.
tana shirin sake bawa onye wani marin kenan yayi saurin rike hannunta ya wanketa da mari gudu 3 ajere masu kyau .. in ur dirty life don't don't ever ...i said don't ever see me wit a girl and re-act like a fool.
banza shasha kawai this girl you seeing here tafi min ke sau dubu.
kina jina ko dakikiya mara kamun kai... Allah sarki su'ad dai bude baki tayi tana kallon shi, sannan ya meida mayatattun idanunsa kan onye dake tsaye dafe da kunci sorry baby kiyi hkr it's me i caused all this let just make takeaway......
wani irin tuttukin bakinciki ne ya tsaya atsakiyar kirjin su'ad wanda ya janyo numfashinta neman tsayawa ,hawayen datake kokarin boye ne suka shiga zubowa ahankali bisa kuncinta ..still idanununta na kanshi tana cigaba da kallonsa kirjinta na bugawa da sauri sauri, gbdy wani irin duhu taga ya gilma cikin kwarnin idanunta, marina yayi akan prostitute,...karuwar ma me zaman kanta.....

tana tsaye kikam hk ak yasa aka hadawa onye komai naci da sha ban dashi, danshi ji yayi bazai iya sanyawa cikinsa komai ba, wannan kazamar banzar yarinyar ta bata masa moon dinsa daya fito dashi daga gida.
tare suka jero yana sake bawa onye hkr.
a zuciyar onye kuwa cewa tayi daman hk ak yake sonta woww lallai ta cire tuta a zuciyarsa wani matsefaffen dadi
taji.
wani sabon shaukin kaunarsa ke sake gudana a zuciyarta ,Dama ilahiri sansar jikinta dan hk suna shiga mota tayi hunging dinsa tana shakar daddaden kamshin turaren jikinsa, shima rungumeta yayi tare da kai hannusa ya gyara mata gashin attachment din daya zubo gaban goshinta dake kokarin rufe mata fuskarta.
muryarta cike da salon karuwanci tace honey muje guest hause sbd kaci abinci muyi hira sannan nayi maka abinda kafi mutuwar so daga gareni before you go home kaji .
tayi mgnr tana kokarin hade bakinsu gurin daya.. yayi saurin janyewa yasoma zareta daga sansar jikinsa wanda bai san abinda yasa shi yin hkn ba.
muryarsa a matukar kasalance ta fito gurin cewa bana jin wannan moon din ahalin danake ciki yanzu .
zan ajiyeki a ojoelagba sai ki wuce hotel na sameki later, yana karasa mgnr yayiwa motar key suka bar harabar gurin.
ahankali ta kamo laulausar tafin hannusa daya cikin nata, tana murzawa ahankali domin son kashe masa jiki.
abinda kayi a yanzu ya tabbatar min da irin tarin soyayyarka gareni ,honey ina sonka dayawa tare da dago hannunsa tayi kissing dinsa tana lumshe ido, bai ce mata komai ba .
sbd shi yasan ba dan wata soyayyarta ko wani abu yasashi aikata abinda yayi ba.
kawai haushin yarinyar da tsantsar tsanarta ne musababbin komai. driving yacigaba yayi kawai zuciyarsa na kissima mashi abubuwa dayawa akan yarinyar. suna isa ojuelegba ya tsaya tare da ciro bandir din yan dubu day day ya mike mata, wajen amsar kudin ma sai data riko hannunsa sosai cikin nata tana kallon cikin kwayar idanunsa .
ta shagwabe murya honey naso kasancewa tare da kai yau ,gbdy ilahirin jikina a bukace suke da kai honey ko sau daya kabari mu dandani juna...
karki damu zamu sake haduwa amman bada niyyar manufarki zamu sake haduwa ba.
yanzu dai ki sakar min hannu akwai inda nake son zuwa.
ta zaro karuwan idanunta waje tana sake narkar dasu cikin nasa tare da damke hannush sosai, hope ba gurin wajen wacen mad girl din zaka koma ba. tsaki yaja yana aiko mata da wani banzan kallo me firgita zuciya duk wanda akawa shi.
sakar min hannu.......abinda ya iya furtawa kenan.
da sauri ta zare hannunta cikin nashi, tare da hade hannuwanta guri daya am sorry honey .. sorry for your self common get out from my car ,jikinta na rawa ta bude kofar motar ta fita tana sake bashi hkr ko sake kallonta bai yi ba yaja motarsa a fusace.

tuki yake ahankali cike da rashin natsuwa. zuciyarsa na matsanancin bugawa akan al'amarin yarinyar amman sai me zai faru hango yarinyar dazu yayi ita da abokiyar shashancinta, ta cikin madubin mota, suna biye dashi abaya akan machine wannan karon itace ke tuka machine din kawarta abaya .
take mamakinta yacika zuciyarsa.
ahankali ya furta meyasa take sake bina km byn wulakacin dana gama yi mata yanzu? yayi mgnr ahankali tare da dukan sitiyarin motar ,ahankali ya gangara bakin titi yayi parking motarsa .
yaga suma sun dan tsaya nesa kadan dashi suna dubansa .
take zuciyarsa tasoma harbawa cike da matsanancin tsoro yana nan gurin sukazo suka wuceshi aguje batare da ko kallon inda yake ba. hkn yabashi damar cilla hancin motarsa kan titi kai tsaye brige din ojuelegba ya hau yana shara gudu cikin minti 30 sai gashi a green hill estate inda yake tamfatsa wani tamfatsetsen gidansa, na zamani gida ne wanda yakashewa makudan kudi bila'adadi akalla ya dauki sama da shekaru masu dan yawa yana narkawa ginin kudin wanda har zuwa yanzu yana kan kashewa gurin kudi .
"babu abinda ba'azuba ba acikin gida .
komai na amfani an zubashi ,a wannan kerarren ginin nasa amman still kullu sake narka kudi yake ,yayinda duk wanda yaga yanayin tsarin ginin gidan yasan an kashe kudi ba ne da kudi ba.
sannan zai dauka ko gidan wasu kusoshin gwanati ne ko gidan shugaban kasa.
a daidai bakin get din wannan tafkeken gidan yayi parking tare da ciro dan karamin remut ya danna, batare da yabude mota ba .
get din gidan yashiga Budewa ahankali har ya budewa gabadaya, yasanya hancin motarsa ciki .
kai tsaye parking space ya nufa ,ya faka motarsa kiran felari spaider .
ya kashe motar tare da fitowa yana gyara zaman rigar jikinsa.
me gadin gida wanda tuni ya iso inda yake yana ronkwafowa domin kwasar gaisuwa ga uban gidansa.
,welcome sir. Williams how are you doing ?
am fine sir ak yacigaba tafiya yana sake karewa yanayin gidan kallo tsab so yake ya gano abinda bai yi ba a farfajiyar gidan, williams... ak yakirasa ,yes sir.
work's din nan basu zo bane yau .bakin williams na rawa yace sunzo boos basu dade da tafiya ba. wayarsa ce ta katseshi ta hanyar dauka karar sauti me dadi.
ya zaro wayar yana duba screen din wayar.
sunan musty yagani kmr ba zai dauki kiran ba sai km yayi pik, friend kana ina ne ganin a gida, dady yace baka dade da fita ba.
uhm ya bashi amsa ataikace dan har yanzu haushinsa yake ji , kayi nisa ne ? ko yanzu zaka dawo na jiraka?
na danyi nisa kadan ina green hill estate, ok har yanzu ba'akarasa aikin bane i thought komai ya kammmala.
sauran kadan aikin ya saura, akwai order mayan kujerun danayi wanda za'a sa " a part dina , sai zuwa nest week km zasu karaso.
that's good friend ai gaskiya bakaramin kudi ka kashe agidan nan ba sai fatan allah yasanya alkhairi ,ameen ak yace a dakile, suka dan daba hira sama sama sannan sukayi sallama ,suka cigaba da zagaye gidan tare da Williams suna zantawa ahankali cikin hk sukaji ana nocking din karamin get din gidan da karfi atare ak da williams suka juyo suna duban get din da mamaki .
barin ma williams wanda yafi ak mamaki this is the first time dayaji wani abu wai shi nocking a get din gidan. dan kwata kwata babu masu zuwa daga ak sai da dady'nsa, da wark's din da suke kan aikin gidan .
su km bata kofar get suke shigowa ba.
ta jet suke zuwa kasancewa turawa ne, daga kasar Spain ya daukosu .
batare da ak yayi yunkurin yin wata mgn ba ,williams ya juya da dan saurinsa zuwa jikin get ya bude hujin dake jikin karamin get yana dubawa.
wasu yan'mata yagani su biyu ,suna tsaye.
cike da mamaki saman fuskarsa ya bude karamin get din yana kare musu kallo, kafin daga baya ya kai ga tbmyrsu gurin wa suka zo, dayar tace nan abdulkabir yashigo...?

can I help you ?


just answer my question i finishi you..... uhm nan yashigo ok matsa min nashiga ina son ganinsa.
akan wani dalili zan bari ki shiga byn ba'abani izinin yin hk ba?
dauuu yaji ta dauke shi da wani gigitaccen mari kabani hanya nace na shige banza stupid jaki kawai dakiki me fuskar alade.....,zaiyi mgn yaji dayar tajawo kwalar rigarsa tare da fincikosa waje gabadaya tace su'ad kishiga kawai ni zanjiraki anan zanji dashi . ok tasa kai tashige cikin gidan tana wage wage da kallon yadda ginin gidan ya tsaru matuka tmkr a kasar waje...
tundaga inda yake tsaye ya hangota gabansa yashiga faduwa zuciyarsa tashiga rawa jikinsa ya dinga mutuwa kallonta yake tana karasowa gareshi cike da jarumta wanda bakowace mace za'asamu da irinta ba .
takarasowa tayi tsaya cak a gabansa tana kallon cikin kwayar idanunshi wanda shima ita din yake kallo kyakkyawa ce ajin farko very beautiful and amazing lady fara ce sol babu alamun tabo komai ajikinta, farinta har wani sheki yake da daukar hankali .
ta matso kusa dashi sosai har suna jiyo bugun zuciyoyinsu tare da shakar numfashin juna .
lumshe mayatattun idanunsa yayi na some minti sannan ya budesu fessss cikin fararen idanunta masu launi dana mage.
, kallonsa take har bata son kifta fararen idanunta tana jin kmr ta janyoshi zuwa gareta ita kanta batasan irin tarin kaunar da take masa ba.
a yanzu datake tsaye gabansa ji take tafi kowa sonshi da kaunarsa fiyye da kowa dake cikin duniyar nan ciki kuwa har da iyayen da sukayi sanadiyar zuwansa duniya.
, ganin yadda tayi tsuru tana binsa da mayataccen kallo yasa ranshi yasoma baci, zuciyarsa ta harzuka ta kawo iya wuya ..
a matukar hassale ya dan ja baya kadan ganin tana kokarin shige masa jiki kana yace. me ya kawoki nan....?
me kike nema atare dani ne for God sake .?
yau shine karo na sau ba adade da nake sanya idanuna akanki , wanda bana kaunar hkn .
ke bana ma son sake cin karo da wannan fuskartaki me dauke da rashin gsky.
da alamun ma mayya ce ke ko yar mafiya?
tayi saurin girgiza kau batare da tace komai ba karya kike munafuka, idan bakya daga cikinsu meyasa kike bibiyar rayuwata da duk inda nake sanya kafafuna.
ni ban yarda wata banzar manufarki gareni ba .... for the last time kigaya min.

Meyasa kike bibiyata duk inda naje?

ki bani amsa amman banda wannan kazamar kallarki gareni.tayi shiru still tana cigaba da kallon kyakkyawar fuskarsa me cike da tsagwaron kyau da haiba wanda kallo daya zaka masa kaji ya sace zuciyarka.

3 Comments On SAI KA AURENI DOLE
avatar
zainab-ishaq

1 year ago

Reply

Love it ????????

avatar
zainab-ishaq

1 year ago

Reply

Yes and I want to download it

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to zainab-ishaq

In order to download you have to subscribe for our package at https://tnovels.com.ng/subscribe

Please Login or Register in order to submit comment