Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ki gaya mana gskyr abinda ya fito dake a wannan lokacin mu km zamu fitar dake cikin wannan maseefar .
nashiga girgiza musu kai wallahi bazan iya gaya muku abinda ya fitar dani ba, domin sirrri ne wanda bazan iya gayawa kowa shi ba, ok sai kiyi hkr ki dauki kaddara kasancewa tare damu gobe bazaki sake fita a daidai wannan lokacin ba.
" ke ko gaba kika ga wani zai fita daidai wannan lokacin zaki hanashi, wannan ruguntsiin dazamu shiga tare ya isheki ajiye tarihi arayuwarki.
cikin kuka nace allah ya isa tsakanina daku bazan taba yafe muku ba har duniya ta nade kun cuci rayuwata .
"amman ina son ku san wani abu zan tabbata ina kaiwa ubangijina kararku Allah domin yabimin hakikana da kukaci.
kun zalinci ne hk kawai zaku saka rayuwata cikin kunci rayuwa.... ko kallona basu sake yi ba suka soma hira kasa kasa a tsakaninsu, a yadda nake kallonsu banga ala'mun tsoro ko firgice atattare dasu ba ,da ala'mun sun saba kwana cikin cell.

ni kuwa duk inda tashin hankali yake yayi min dirar makiya kuka nake sosai da iyakacin karfina ina kiran nayiwa kaina, meyasa na jefa rayuwata cikin tsaka me wuya ...

washegari da safe
daya byn daya aka dinga fitowa damu zuwa wasu dakuna dabam dabam. domin yi mana tmbayoyi lokacin da akashiga dani tmbyta aka soma yi tun yaushe nake tare da ganga din barayi, zuwa yanxu sata nawa akafita tare dani ?
"nasoma kuka wiwi ina cewa wallahi bansansu ba sharri suka min asalima ban taba sata ba arayuwata ..

"to me ya fitar dake cikin wannan daren har muka ganku tare dasu?
nayi shr na kasa amsawa sai kuka da nake sbd bansa abinda zance musu ba.
ai wannan shr danayi ashe karawa kaina laifi nayi agurunsu.
aiko take sai ji nayi an rufe da wani irin duka ta koina ajikina sai da suka mun lilis sannan suka barni suka cigaba da aiko min da tmbayoyin. tsayawa nayi kan gskyta , "ni ba barauniya bace km bansan yadda ake sata ba.
wani sabon dukan naci kafi kace me hancina da bakina sun balle da jini kamanin fuskata yasoma sauyawa dukana suke da iyakacin karfinsu dan kawai na amsa laifina, ni km naki amsa laifina na tsaya akan ni barauniya bace km bansan barayin ba...
dan hk wani police ya bada umarni a sakani cikin under ground..under ground guri ne wanda ake saka rikakkun yan fashi masu taurin kai, waje ne dake da tsananin zafi da hudu dan ko tafin hanun mutun bazai iya gani ba.
haka suka daukeni babu tausayi balle imani suka turani cikin Under ground kusan awana biyu ciki wanda zuwa wannan lokacin numfashina ya dauke ,dan koda suka fito dani na suma.
da wani dukan suka farfado dani sannan suka cigaba da azabtar dani wanda babu shiri dana ga azaba ta isheni na amsa laifina, akan tare mukeyin harakar fashi da makami, aka tmbyeni inda muke ajiye makaman aikinmu nace gidanmu.
aranar aka nufi unguwarmu dani byn an saka min handcop hannu da kafa .
tunda muka shigo cikin unguwar idanun mutane ya koma kanmu, Jama'a suka cika makil akaina gbdy police suka firfito tare da tsayar dani , nan fa mutane suka soma gane ni dan da farko babu wanda ya. ganenice sbd kunburin da fuskata da kaina yayi kallona mutane suke suna alajabi ganina cikin wannan yanayin me cike da rudani ,duk wanda ka gani cikin yanayin danake, fuskarsa cike take da matsanancin mamaki sbd kasancewata shiru shiru marason mgn da hayani ,ahankali na nuna musu gidanmu da hanuna dan bazan iya mgn ba sbd muryata ta dashe, wani sabon tashin sai da mukashiga compound dinmu da muka hankalina ya sake tashi jikina ya dinga rawa hawaye yasoma bin kuncina ta inna zan soma hada ido da mahaifiyata alokacin babu abinda yazo zuciyata kmr tausayin mahaifiyata da halin dazata tsinci kanta, da bindiga wani police ya ingiza keyata nakarasa bakin part dinmu na tsaya suka shiga buga kofar da karfin tsiya cikin hk wata makociyarmu ta fito ai tana ganin police da ganin halin danake ciki tayi saurin komawa cikin dakinta ta sake danna key, police suka cigaba da bugun kofar ,daga bayana naji sautin muryar ore tana kuka ,a she anje an gaya mata gani can police sun kamani, na juyo ahankali ina kallonta da kumburarrun idanuna jikinta na rawa tashiga tmbyta abinda ya faru nan fa police sukayi caa akanta suna aika mata da tmbyr ko tasani tace eh tasani sosai.
"wani sana'a nake tace ni student ce a unilag tare da tmbyarsu laifin danayi suka ce mata aikin fashi da makami nakeyi .....

ta naga ta daura duka hannuwanta bisa kanta tana kuka da kururuwa sharri aka min ita bata san ni da wannan aikin ba.
asalima ni yarinya ce da babu ruwana, sannan bana shiga shirgin mutane , tana kuka take musu bayanin halina nima kuka nake alokacin.

ina kallo police suka balle kofar part dinmu suka shiga sukayi iya bincike da zasuyi amman basu ga komai ba wanda ya danganci aikin fashi. ba dan hk suka tmbyeta inda mahaifiyata taje, ta dago jajayen idanunta ta saukesu akansu "tace tashiga gari nemana dan yanzu ma tabar gidansu.
" ok idan ta dawo sai ki sanar mata da abinda ke faruwa sannan suka tasa keyata zuwa waje inda sukayi parking din motarsu .
"hawaye ne suka shiga gangarowa daga cikin idana bakina ya kasa furta komai sai kallon dandazon jama'ar da suka cika unguwarmu makil nake, ina cigaba da kuka.

jikina a sanyaye nashiga motar police muka bar unguwar.
in takaice muku har school dinmu police suka kaini zuwa ga shugaban makarata amatsayina na rikakkiyar yar fashi da makami ..

kwanamu uku cikin cell ban ci ban sha dan duk abinda aka kawo bana ci yunwar ma bana jinta tashin hankali danake ciki ya girmami abinci. sannan aka fito damu lokacin idan kagani bazaka taba ganeni ba sbd dukan mutuwar da aka min kaina ya sake yin wani irin kumbura ko iya bude idanuna banayi sai da wata police tace daya daga cikin barayin ya riko hannuna tunda shi da dan sauransa .
kai tsaye koto aka wuce damu .

a koto ma babu wata hujja data nuna ni ba yar fashi da makami bace.
" ni kaina banida effidence din da zan kare kaina agaban majisret , tunda wuya tasa na amsa laifina da kaina a tun farko, batare da wani bata lokaci ba koto ta zartar da hukunci bisa ga laifin da wasu suka aikata har dani........


mmn sudais ce

💗💗💗💗💗💗
SAI KA AURENI DOLE
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗



~NA~



*AYSHA A BAGUDO*



~DEDICATED TO~
HAUWA A USMAN
JIDDAR


*Allah messenger saw said:the different between the sarvant of Allah and infidelity is to abandon prayer*

page 51

"ahankali na dinga maimaita abinda naji majestret ta zartar akanmu ,ina wani irin kuka me cin rai da ban tausayi.

"bisa kwakwarar binciken da kotu tayi akan wadan nan yan fashi da makamin, "kotu ta yanke musu hukunci zama a gidan yari na tsawon shrkaru 3 tare da aikin wahala me tsananin. "sannan lokaci zuwa lokaci za'a dinga kawosu koto idan km basu gamsu da shari'ar ba zasu iya daukar lawye domin daukaka kara .

"court ..... me shari'a takarasa fadar hk tana me mikewa tsaye tare da gyara zaman rigar jikinta ,ta juya tabi wata karamar kofa zuwa cikin office dinta.

"ai ganin hk dana yi da km yadda ganduroba's sukayi caaa akanmu tare da zagayemu tmkr za mu gudu ya sake firgitani .

na daura hannuwana duka bisa kaina ina kururuwar kuka da iyakacin karfina "ina furta ni ba yar fashi da makamin bace ,dan Allah me shari'a ki taimakawa rayuwata ni marainiya ce banida kowa sai mahaifiyata .... .

"sannan na juya inda yan fashin ke tsaye kusa dani "nace ku tausaya ku fadawa kotu gskyr lamari bana cikinku "karku yi sanadin shigata gidan yari " idan hkn yakasance "zan tabbata ina muku adduar mugun al, kaba'i a dukkanni shafuffukan rayuwata.

tafiya muke a tsakiyar ganduroba wadanda suka zagayemu, kowanemu hannunsa daure handcop .

duk cikin barayin nan babu wanda yashiga tashin hankali kmr ni, shiyasa mutane dayawa suka dinga tausayamin da jimami ganina cikinsu.
tausayina nake hangowa acikin idanun mutane suna tayani kuka tare gasganta maganganuna yayinda wasu suke ganin tmkr karya nake ni din abokiyar al'kalarsu ce.
har muka sauko zuwa farfajiyar samuel ilori court dake da kusanci da agege local government kuka nake da sambatu iri iri wata mgnr ma bansa lokacin da suke fitowa daga cikin bakina ba . ...

"ai gama isowarmu farfajiyar kotun keda wuya yan jarida sukayi kanmu da tmbayoyi iri iri yayinda lawyer's suka dinga kokarin kawo mana ziyara dan son taimaka mana, idan bamu yarda da hukuncin da me shari'a ta zarmana ba ,muna iya daukaka kara kmr yadda majestret ta fada ...

"ina bukatar daukaka karar amman wazai taimaka min? "wa zai tsaya min?


bayan motar dazata kaimu gidan yari aka bude tare da bamu umarnin shiga cikinta, nan fa hankalina ya sake kololuwar gurin tashi, kukana ya sake tsananta hankalina yayi mugun mugun tashi na zube kasa ina birgima da ihu.

"wayyo Allah nashiga uku ku taimakawa rayuwata .

"ku taimakawa rayuwa marainiyar Allah.
"ku gaya musu gsky bana cikinku, "karku dauki hakina, na zura zan kwasa a guje ganduroba da police sukayi kaina suna Mazurai da ihu kiran he ..he.. dont move to any where ,tare da tsaitani da gindin bindiga.
hankalina a tashe nake kuka me hargitsa 'kwal'kwaluwa wanda gbdy zuwa lokacin nagama fita haiyacina sosai nake kuka ina zunduma ihu ,zaman dirshan nayi agurin ina cigaba da ihu tare da dibar kasa ina watsawa kaina.. .."gasu nan ku tambyesu basu sanni ba ban sansu ba.
" asalima ban taba ganinsu ba a iya tsawon rayuwata.

"me nayi muku kuka min sharri ?

"me nayi muku kuka zabi ku gallazawa rayuwata?

na rarrafa na isa xuwa inda suke tsaye abakin motar black mariya, suna kallona, na durkusa bisa gwiwowina ina kuka ,ina rokonsu, da su gayawa kotu gsky kar su bari a tafi dani .

"cikin wata irin murya da ban taba jin irinta ba naji an buga min razananniyar tsawa wanda yasa hantar cikina kadawa, batare da nacigaba da rokonsu ba na mike zumbur tsaye ina mazurai da idanuna .

" tarin police's da ganduroba's ke tsaye bisa kaina, umarnin shiga cikin motar akabamu tare da sake bagu mana tsawa..


hk ina ji ina gani nashiga motar zuwa kirikiri prison zuciyata tmkr zata tarwatse, muna isa gabduroba's sama da ashirin suka zagayemu suna kallonmu 1 byn 1
nima kallonsu nake da kallon koina agurin , build's ne jere agurin sama da guda goma sha kowane ajikinsa an rubuta number tkmr yadda ake rubuta number ajikin gida.
"akwai prison na kidnappe's ,akwai na masu satar yara ,da cin nama mutun ,419 tare da yan kungiyar haya killi's.

bakin wani tafkeken get aka nufa damu
wanda ake ajiye kananun yan fashi da makamin , ina kallo aka bude dan karamin get din , mu km akasa muka bi layi ana tmbyr sunanmu daya byn daya tare da mikawa kowanenmu dan karamin plet na cin abinci.

"ni kam kin amsa plet din nayi sbd tashin hankali danake ciki ya girmami wani abinci..

"basu wani damu da rashin amsar plet din da banyi ba, sai ma muryar daya daga cikin dan fashi danaji yace "damana kin amshi plet din wata kila zai miki amfani gaba.

" atake anan nasoma amsar sakamakon abinda na shukawa rayuwata, asanadin taimakawa abdulkabir danayi ,domin wata uwar ashariya na lailayo da yaren yarbanci na maka masa ina hargagi tmkr wata zankanya.

ana gama rubuta sunayenmu da kotu tabayar arubuce, naga an rabamu da yan fashi sunbi ta wata haya daban nima wata hanyar daban aka nuna min ashe ba guri daya za'a ajiyemu ba hkn na nufin gurin mata da ban hk ma maza.


a gidan yari kuwa "ihu nake ina kuka "ina cewa sun cuceni sunci amanata ban san su ba suka min sharin fashi da makamin, "sun yi sanadin saka rayuwata cikin ukuba da taskon rayuwa, tare da zama silar rabani da mahaifiyata .

cikin kuka "nace wallahi wallahi koda laifin da kuka aikata min kadai ya rage muku shiga aljanna bazan taba yafemuku ba. zan tabbata ina muku mummunar addua da jafa'i iri iri a iya tsawon rayuwata ..

can km na dawo nadamar abinda na aikatawa rayuwata .
kaina na dinga bugawa a bango dakin ina ihun meyasa na sadaukar da farincikina akan mutumin da bai san da zamana ba?

"meyasa kika aikata hk su'ad ...?

"me yasa baki dauki shawarar ore ba kika biyewa son zuciya kika aikata tsafi?

"tsafi fa kikayi da iliminki da koma byn kinsa yin hk shirka ne me girma.....

"wayyohhly Allah na "meyasa na aikata shirka ?

"hakika Allah (swa) yana cewa acikin idanuna littafinsa me sarki "hak'kin allah akan bayinsa shine, su bauta masa shi kadai kada su hadashi da komai a gurin bauta "to ni meyasa nabiyewa son zuciyata na aikata ?

"gashi nan ai tun yanzu nasoma amsar sakamakon abinda na aikatawa rayuwata ,yau zanyi bacci acikin gidan yari .

"na juya ina kallon mutane dakin ina wani irin ihun na cuci kaina na aikata shirka da ilimina, byn nasan Allah ya haramta, hada waninsa dashi agurin bauta.

"yanxu meye makomata da makomar abinda na aikata ...?


cikin hk naji an dafa kafadata ta bayana "kiyi hakuri kiyiwa kanki adduar samun mafuta arayuwarki ta yadda zakiyi ramuwar gayya ga wadan da kuka tsunduma rayuwarki cikin matsala.

ban kulata ba sai ma ihun danake tare da yarfa hannuna ina wani irin kuka ban ankara ba naji saukar hannu bisa kuncina ana share min hawaye tare da rungumeni ana dukan bayan.

fige fige nasoma yi ina kokarin raba jikina daita ina sake sakin wani sabon kuka kafin daga baya na tsulale kasa nasoma jan gashin kaina ina zuba sambatun iri iri ina furta "na aikata shirka da ilimi akan mutumin da bai san da zamana ba gashi zan bata shekara 3 agidan yari ....

rawan roba naga yarinyar ta dauko tashiga bulbulamin tundaga kaina har zuwa jikina sannan ta kafa min sauran abakina .
"kisha ko zaki ragewa kanki radadin da kike ji , dole na bude bakina nasoma sha sbd yadda ta rike kaina da hannunta ga robar ruwan abakina.. byn nagama sha na sauke naunauyen ajiyar zuciya batare da na shiryawa hkn ba.sannan nacigaba da kukana me ratsa zuciya..

sautin muryar yarinyar naji ta doki dodon kunnena wace agirme baxata girmeni ba zamu iya yin sa'anni daita "sunana ganiya ke fa?

nayi mata banza hawayen idanuna na sake gangarowa "a maganganunki na tsinci wasu abubuwan game da abinda ya faru dake.

"amman tunda kika tsinci kanki acikin gidan nan hakuri ya zamemeki dole.

"kiyi hkr ki cire wannan damuwar danake gani atattare dake.
"idanuna ne ya sake cikowa da wasu hawaye.

"ni nan da kika ganmu tayi mgnr tana nuna sauran mutanen dake zaune acikin daki "rikakkun yan fashi da makamin ne babu garuruwan da dama zuwa yin fashi...

" satar da mukayi last a murtala international airport last year January kenan itace sanadin zaman mu anan har tsawon shrkaru biyar kotu ta yanke mana yanxu munci 2 sauran 3..

"Kema yar fashi da makamin ce ko? ta jeho min tmbyr tana dubana "na dago da kumburarrun idanuna da kyar na saukesu bisa fuskarta sannan na girgiza mata kai ala'mun a'a.

"me kikayi aka kawo ki bangaren yan fashi "

"sharri aka min nayi mgnr hawaye na gangarowa bisa kuncinta ....duk yadda ganiya taso taji abinda yakawoni prison naki yarda na gaya mata komai , "na tsaya akan sharri akamin.
hk ta hakura ta barni tacigaba da rarrashina tana bani baki,akan na daina kuka na shiryawa daukar fansa ga wadan da suka min sharri.


ranar yadda naga dare hk naga rana na kasa runtsawa duk inda na juya fuskar mahaifiyata dana abdulkabir nake gani.


"zamana a prison zama ne wanda nayi shi cike da matsanancin kunci da bakinciki tare da tausayin mahaifiyata.

" sannan tun washegarin ranar da aka kawoni aka bani aiki byn bulala hamsi da aka mun, wanda kaidar prison din kenan kullun garin Allah ya waye sai an yiwa duk wanda ya kwana ya tashi agidan bulala 50 tare da aikin wahala..

watanmu uku a prison aka sake dibarmu zuwa Samuel illori court, kafin sharia tazo kanmu sai da akayi case yafi guda goma sannan aka kazo kanmu.
ko ranar ma naci kuka tmkr raina zai bar gangar jikina sai zare idanu nake naga ko zanga wanda nasani .

"bayanin case dinmu dai aka sake maimaitawa da sake jadda mana zamanmu gidan yari har na tsawon shrkaru 3.

kmr zuwanmu na farko tsakayar ganduroba muke, muna tafiya ahankali ,wannan karon a yadda nake kallon fuskokin yan fashin nan ya sake tsoratani na fidda rai da tsammanin kubuta daga tarkonsu .

"a hankali muke daga kafafunmu domin sauka kasa inda motar black mariya ke zaman jiranmu kawai naga daya daga cikin yan fashin nan
ya arta da matsayacin gudu yana sauka akan step, ai take ihu da kururuwa ya cika koina a koto yan'sanda dake kai kawo a sorrounding gurin suka mimike tsaye tare da rufe kowace hanya dake cikin kotu ,ai barawon nagama saukowa kasa yaga an kulle koina na sorronding gurin, bai tsaya wata wata ba kai tsaye ya nufi katangar company din guineas dake manne da katangar kotu ya haura. ai nan police suka bishi aguje wasu suka zagaya suka shiga cikin campany ...

cikin minti goma sai gashi sun kamoshi sai dai yaci uwar duka har bai iya daga kafafunsa ga jini daya rufe kanshi yana tsiyaya ...

cell din dake cikin koto aka wuce dasu ni km aka hadani da police sbd sai yamma zamu koma prison, anan zamu yini tun abinci daren jiya ne acikina gashi idan baka nan bakada abinci km ko ansan kana kotu baza'a ajiye maka ba, sannan a kotun ma ba abincin zakaci ba..

"akalla duk byn wata uku sai mun ziyarci kotu gashi har na kai tsawon shekara daya cikin ta biyu mahaifiyata batasan inda nake ba.

ana gobe zamu kotu muke zantawa atsakani yan dakinmu da makotan dakinmu inda akwai wadan da gobe inda munje kotu bazasu dawo cikinmu ba, kasancewar wa'adinsu yacika.

nan duk wani me sako tsakaninmu yabasu zuwa ga danginsa , ciki kuwa har dani danabawa bukky sakona zuwa ga ore aminiyata.

daren ranar kam nayi kuka sosai ina ji ina ma nice zanbar gidan yarin, su kuwa tsabar rashin jin mgn irin tasu da taurin kai "cewa sukayi dama an barsu sun cigaba da zamansu "menene babu acikin gidan yari"duk fa abinda muke so shi mukeyi babu matsi babu takura "muna waya muna shaye shayenmu yadda ranmu keso "to meye km yayi saura?

"ni kam cewa nayi har duniya ta nade bazan taba zabar zama cikin gidan yari ba ,kai ko abinda zai sa na sake dawowa gidan yari bazan aikata ba.

dry suka kwashe min dashi suna nuna da hannunsu, daren ranar kasa runtsawa nayi inaji kmr nice zan bar gidan.

munje kotu wannan karon har da su ganiya wanda shari'ar mu tazo daidai datasu ,byn angama gabatar da shari'arsu aka shiga tamu wace babu wani ci gaba acikin shari'a tamu , sai bakinciki tare da bada kwanan wata da zuwa kotu bisa gaida .

me shari'a ta mike byn tagama watsa mana tsadaddun turancinta muka fito daga cikin kotu zuwa harabarta kotu inda dandazon mutane suke .
"wasu a zaune wasu a tsaye kowa kagani agurin sha'ani gabansa yake ,yayinda wasu kana kallonsu kasan cikin tashin hankali suke dan zakaga har kuka suke sbd masefar tashin hankali dake cikin kotu .


muna zaune inda aka saba barinmu a duk sanda mukazo kotu. zaman dana saka masa suna da jiran tsammani ,muna kallon yan'uwansu bukky suka karaso garesu suka rungumesu suna murnar an sakosu ,.

"alokacin babu abinda yaxo raina kmr ummana ita kadai nake so da kwadayin sanyawa acikin kwayar idanuna dan gbdy tashin hankali danake ciki yasa na tattara soyayyar abdulkabir na ajiyeta agefe nafi jin tausayin mahaifiyata , domin nasan tana can cikin tashin hankali rashina har na tsawon lokaci.

ba'a cike wata biyu ba da tafiyar su bukky ina zaune naji ganduroba na kirana na mike cike da mamaki, domin lokacin shine karo na farko dana ji an anabi sunana da sunan anzo nemana .

ahankali jikina a sanyaye nabi bayansa har zuwa cikin wani office.
ore nagani zaune tana ganina ta mike tsaye jikinta na kirrma ni km sai hawaye sharrrrrr ta karaso gareni ta rungumeni ajikinta tana kuka "a she da gaske ne su'ad kina prison?

"cikin kuka nace gaske ne ore gani kuwa agabanki acikinsa.

"ya ummun su'ad take? nayi mata tmbyr ina kokarin barin gangar jikinta domin son sanin halin da mahaifiya take.

"tana lfy ko yanzu kafin nazo sai dana biya gurinta km na sanar mata da gurinki zanzo har tayi adduar Allah yasa bake din bace a prison kmr yadda sako yazo mana.
wasu zafafan hawaye suka sake zubo min.

na runtse idanuna domin rasa abinda zan ce "garin yaya su'ad ?

"garin yaya kika tsincin kanki cikin halin robboling?

"kaddara ore "kaddara ce silar meidani hk km kin gaya min gsky nakiji .
"a she shafuffukan rayuwata suna tattare da kaddarori bansani ba.

"danasan hk zan tsinci rayuwata dana dauki shawarki kingan ni nan cikin prison da sunan robbiling akan soyayyar abdulkabir.

minti 15 akabamu mu gana daita gasu har sun cika batare da hirarmu tayi tsawo ba domin har ganduroba yakaraso bisa kanmu ya tsaya yana bani umarnin komawa ciki ,itama yana bata umarnin wucewa.

ina kallonta taciro kudi akalla zasu kai dubu biyar ta miko min na girgiza mata kai "ki bar kudin ore basu da wani amfani gareni hannuna ta janyo ta tura kudin ciki ta rufe ki amsa zasu miki amfani, ta juya tana kuka kafin nayi hanzari har tabar gurin nan nima na fashe da wani gigitaccen kuka, ganduroba ya matso inda nake tsaye tare da miko min tafin hanunsa ala'mun na bashi kudin, take babu musu na mika masa nasoma daga kafufuna zuwa cikin dakunanmu.

tunda ore ta tabbarwa ummana Hali danake ciki ta tashi hankalinta, tayi kuka sosai har kukan ya janyo mata ciwo me tsananin a yadda ore tasanar min a wani zuwa datayi gurina .

zanga zanga ummana tashiga neman yadda zata fitar dani daga prinson, duk kudaden gidan hayar gadona wanda mahaifina ya barmin babu wanda bata amsa ba domin kubutar dani amman babu biyan bukata lawyer's sai dai su amshe mata kudi su dinga mata yawo da hankali tare da saka mata rana, ahaka a wani zuwa da ore tayi gurina take gayamin yadda abubuwa ke tafiya.

"nace tagaya mata tabar hasarar kudinta ta'ajiye watakila gaba suyi mana amfani ta min addua kawai domin shi nafi bukata daga gareta ahalin danake ciki.

"na kara dace mata ta duba jakar school dina akwai wani diary ciki duk randa zata sake zuwa tazo min dashi duk .

sati daya bata cika ba ta sake kawomin ziyara tazo min da littafin sirrin abdulkabir, cikin na duba naga cikakken address dinsa nataba nace ta binciko min komai akansa da halin dayake ciki .


kullun da tunanin mutun biyu nake kwana nake tashi arayuwta mahaifiyata da abdulkabir burin raina yayinda kullun kwanan duniya zazzafar kaunarsa ke sake wanzuwa acikin zuciyata.


duk sanda ore takawo min ziyara sai na tmbyeta lafiyar mutun 2 mahaifiytata da

3 Comments On SAI KA AURENI DOLE
avatar
zainab-ishaq

1 year ago

Reply

Love it ????????

avatar
zainab-ishaq

1 year ago

Reply

Yes and I want to download it

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to zainab-ishaq

In order to download you have to subscribe for our package at https://tnovels.com.ng/subscribe

Please Login or Register in order to submit comment