Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

rayuwa tare dashi ba babana.... iyayena sun sallamani akanshi idan bazaki duba soyayyar danakewa taufeek dinki ba ki duba darajar cikin dake jikina na gudan jiniki ..ki taimakeni ki taimaki rayuwata da cikin jikina wallahi taufeek sheida ne.. ban taba mu'amula da wani nmj ba byn shi yasani bankasance mazinaciya ba.. bansa yadda ake aikata ita kan zinar ba ,sai taufeek ya shigo cikin rayuwata na juyo inda taufeek yake tsaye ina kiran sunansa kayiwa hjyrka bayani ta gamsu ni bamazinaciya bace.
ka bata hkr ta bari ka amshi cikin jikina koda bazaka aureni ba ni yanxu na sadaukarwa duniya farincikina tunda iyayena suka kasa daukar kaddarata ko me mahaiifiyarka zatace min bazai dameni ba.
" amman zance cikin bazan lamunci rikeshi ba alhalin yana da ubansa ina karasa fadar hk nasoma kokarin karasawa gurin mahaifiyar taufeek ina kuka ina rokonta tabari danta ya aureni ,ni ba mazinaciya ba cikin jikina km na tilon danta ne.
amman matan tayi buruusss dani sai ma sake maimata kalmar data gaya masa a daki take .
muna cikin wannan halin matarsa ta shigo a haukace kmr an korota bansa yadda akayi tasan da zuwanmu ba .
" kawai ta tsura min ido tana kallona babu wani bata lokacin ta sheidani bata manta fuskata ba ina ganinta naji zuciyata ta buga da matsanacin karfi amnan na kudircewa raina, zan jure duk wata azabar rayuwa indai zasu amshi cikin jikina .
zuwan matarsa bai saka hjy fasa mgnrta ba taufeek.... takira sunansa a matukar fusace nace ka dauke min wannan yarinyar kabar min gidana daita wallahi zan iya tsine maka sanadin wannan yarinya wallahi wallahi kaji rantsuwar dan muslimi matsawar kenan ,kaga ka Auri yarinyar nan sai dai bana duniya.
gbdy na daburce narasa yadda zanyi jina ya dauke kwalkwaluwata ta tsaya cak ta Daina aiki Nasoma fige fige ina zare ido tmkr me cutar hauka ina kallon fuskar taufeek so nake ya tabbatar min maganganun mahaifiyarsa duka karya ne ba gaske ba....
na kamo hannunsa na rike gam cikin nawa muryata na rawa nace taufeek gaske ne abinda naji mahaifiyarka na fada wai bazaka aureni ba ..? kafin yace wani abu nasoma jan gwiwona zuwa inda matarsa ke tsaye tmkr andasata nace kiyiwa Allah da manzonsa kisa baki hjy ta amince kiyi hkr nasamu muhalli agidanki mijinki kawai nake da muradi auren zan kai hanuna jikinta tayi saurin ingizani zata daga hannunta ta sauke min mari taufeek ya rike hannun tare da cewa karki soma wannnan ganganci, nace dan Allah kabari ta mareni matukar zata bari na auri mijina bazan taba damuwa ba. gbdy na gigice ina ta basu hakuri sai alokaci nasan ba mahaifina kadai keda ra'ayin rekau ba..
nasake dawowa gurin taufeek na rike hannunsa kace karya ne wai bazaka aureni ba.
ya rike hanuna dake cikin nasa sosai sannan ya bude bakinsa yace min eh hk mahaifiyata tace amman ni ina sonki tare da cikina dake jikinki .
yadda na tabbatar miki a can baya ina sonki bazan gujeki ba har yanxu hakan ne acikin zuciyata.. ina sonki sale..... tsawar hjy ce ta katse shi ya kasa karasa mgnr .
dauketa nace..... ita matarsa kuwa cewa tayi muddin tana raye itama bazamuyi aure ba sannan takara da cewa taufeek ina sake tabbatar maka wannan ba matarka bace daduronka ce .
amman indai aureta ne sai dai kayi sa alahira idan anayi ,amman ba anan duniya ba. amman a duniyarmu sai dai wannan ta zauna matsayin karuwarka a tana gama fadar hk ta juya cikin matsanacin kuka tashige dakin hjy tace yanzu taufeek agaban matarka kake cewa kana son wata da nuna kulawa da tsantsar soyayya..?
ahankali yace hjy yazanyi kece mutun ta farko dazaki fahimceni amman kika juya min baya kamoni yayi zuwa jikinsa ya mikar dani idanun nan nasa sunyi jawur dasu bai taba tsammanin wannan ranar zatazo masa ba .
bai taba tunanin mahaifiyarsa zata kawo masa matsala a soyayyarsa da salema ba. yasan tayi hkn ne sbd farinciki mee'ad if not hjyrsa me matukar son farincikinsa ce .
"lokacin dana mike tsaye yasoma tafiya dani marata ta sake tsargawa ta rike gam nayi saurin dafe gurin sbd radadin azabar dana ji .
sai km ga jini ya shiga biyo fafuna na tsaya cak na kasa tafiya jikina na rawa .
ganin hk yasa taufeek ya daukeni agaban mahaifiyarsa wanda wannan abun dayayi min ya sake jefa zuciyata cikin tafkin kaunarsa ,km hkn ya sanyaya min raina ko babu komai ya nuna mata irin son dayake min.

kai tsaye hospital din wani amininsa ya nufa dani likitoci suka ce masa ina bukatar hutu ne idan ba hk cikin dake jikina zai iya zubewa dan har yafita daga cikin mahaifata ya koma byn mahaifa.
ina kuka wiwi cike da tashin hankali nakira sunansa muryarta a raunane taufeek....ya dago idanunsa da sukayi ja yana kallona tare da son jin abinda zance, kayi hakuri kabari a cire min cikin nan .......
sbd me?

sbd ingantuwar rayuwarmu data cikin domin shine first step daya kawo mana matsala da danginka nasan banci wannan cikin da killa mahaifiyarka zata amince ka aureni amman sanadinsa kiri kiri hjy ta nuna kinta da cikin nan..
karki damu da zance kowa ni danayi cikina ina son abuna.
ba'a alfahari da irin cikin nan amman ina miki rantsuwa da mahalicina ina mugun kaunar cikin jikinki sannan ina bukatar sa araye ya fada min hk. yana tsura min ido yanacigaba da kallona nace pls taufeek.. ya katseni bana son wulakanci salema cikin da muka samu lokacin muna cikin ganiyar cin wahalar rayuwa da tashin hankali iri iri kinsa walahar danasha kafin na dasar kwansa .. matsawar bakya son bacin raina karki sake min zance zubar da ciki.

daren ranar ciwon ciki ciwon mara yasani gaba banda murkususu babu abinda nake tun yana min sannu har ya tafi kiran doctor kafin doctor tazo har jini yasoma tsiyaya tmkr an bude fomfo jini har da kudaji kudaji taufeek naganin yadda jini hankalinsa yayi matukar tashi yakaraso gareni jikinsa na rawa ya rike hannuna lokacin da doctor ta turo kofar tashigo takaraso inda nake dazamar soma dubani tunin cikin ya fita amman naci wahala taufeek na tsaye akaina yana min sannu sai da doctor tace ya fita ya bar dakin .
amman kasa aiwatar da hkn yayi ya dawo gefena ya tsaya agabansa aka gama komai tare da min allurar bacci.
koda na farka da fuskarshi nasoma cin karo yana zaune akan kujera hannushi cikin nawa yana ganin na bude ido y shiga jero min sannu sannan yaje hado min ruwan tea yabani nasha muryata a sanyaye nace cikin ya xube ko ?
ya daga min kai ala'mun eh .nima na lumshe nawa idon sbd ban ji dadin da cikin ya xube ba sbd yadda naga ya kwalafawa ranshi akan son ciki.
adduar nashiga yi acikin zuciyata allah yasa hjyrsa ta hakura ya aureni tunda cikin ya fita.

sannu ya dinga min tare da kamo hannuna cikin nasa ya kira sunana salemat cikin sanyi murya zaki tafi ki bar rayuwa sbd cikin ya zube ko? ya fada yana kafeni da kyawawan idanunsa wayanda kallonsu kadai ke haddasawa zuciyata shiga wani yanayi na daban girgiza masa kai nayi hawaye na gangarowa ta gefen idanuna .
karki yaudareni salemat nasan kinbiyoni ne sbd cikin jikinki banci hk da yanzu wani ne zai mallakeki .
" ko babu komai na godewa Allah da kwai na yayi tasiri ajikinki.

nifa ba kin biyoka nayi ba ...to me kikayi? ni dai ka yarda bakin biyoka nayi ba sannan bazan fita rayuwarka ba amman kamin alfamar daya
ina son ka zauna cikin rayuwata idan har kamin hk zan yarda da tarin kaunarka gareni sannan zankasance tare da kai muddin rai naja numfashi na sauke.. ina sonka taufeek har bansan yadda zanyi ba kawai na tsinci kaina da fada masa hk.
" na gode da soyayyarki gareni kin tabbatar min da hakikanin soyayyar gasky kike min.
ki nuna min ni din kike so bawani abu dana mallaka ba ,ina tabbatar miki zan zamemiki sanyi idaniya zan baki kulawa zan zamemeki komai.. kai zanwa godiya taufeek kamin halacci arayuwa ka nuna min ba kowani nmj bane maci amanar soyayya....... yayinda maza dayawa suke butulcewa masoyansu lokacin bakinciki da tashin hankali akan samuwar ciki amman kai baka gujeni ba ka tsaya tsayin daka wannan kawai ya isheni farinciki lokacin da likita ya shigo ya samemu muna makale da juna yayi murmushi tare da cewa laila majnun ya furta hkn kassncewar abakinsa ne km yasan komai dake faruwa yakarso still yana murmushi yace sai kuzo ku wuce gida da alamun lafiya tasamu.
" kwana na uku a hospital aka sallemini sbd naji sauki sosai taufeek ya sanar da hjy cikin jikina ya zube the nest thing hamdala tayi sannan ta daura da cewa ni dai bance ku kashe rai ba sbd cikar burinku domin bashi zai sa na amince da wannan auren ba ...

********
taufeek ya nemi yar'uwarsa da suke uwa daya uba daya daita, akan ta shawo masa kan hjy ta amince da aurenmu abu na farko data gaya masa shine ya gigigiza zuciyata taufeek ni kaina ina son yarinyar kasancewar tana sonka kaima kana sonta .
amman inda matsalarta take mee'ad ce kai kanka ka san yadda mee'ad take agurin hjy.
diyar yayanta ce da suke ciki daya.
km itace ta riketa har zuwa aurenta, sannan aji ance itace kan gaban gurin bayar da gudumuwar ayi mata kishiya da wata.
" kaima kasan hkn ba abu bane me yuwa ba.
yanxu aunty shikenan sbd mee'ad ni za'a tauye nawa hakin... ?
ka dai kayi hakuri... babu wani zance hkr dazanyi kawai kisan yadda zakiyi ki shawo min kan hjy wallahi matsawar ban auri salema ba zaku iya wayar gari kurasan gbdy
ok naji zan sake tuntubarta kaima ka tsananta addua akan lamarin sukayi sallama.
ni dake kwance kan cinyarsa nace ni dai aunty ta taimaikawa rayuwata tasa baki hjy ta amince da aurenmu .
karki damu duk runtsi zamu kasance da juna sannan da yarda Allah hjy zata yarda da mgnr aurenmu na lumshe idona sbd dadin danaji.


haka taufeek ya dinga yiwa mahaifiyarsa naci da zariya akan ta hakura tabari ya aureni .
tace sam bazata yarda ya auri karuwace ba .
tun yana bin daginsa su sa masa baki har ya kai ga nemo manya mutane su bata baki.
lokacin da sukazo kayita jamata ayoyi da hadesai imani da kaddara da hakuri akan hukunci Allah tace shikenan ta hkr Allah ya sanyawa rayuwar auren albarka.ai mutanen nagama barin gidan tashiga zazzaga masa fada ta inda tashiga bata nan take fita ba.
ta sake rantsuwa tare da tabbatar matsawar tana raye bazai taba aurena ba muddin km ya aureni sai dai ya canza wata uwar sannan ya biyata nononta dayasha.
"hk ya dawo inda yayi min masauki kafin ya sai min wannan gidan da muke ciki, yayi kuka da idanunsa ranar kwanan kunci mukayi daga ni har shi, fuskarsa ta kunbura nima har lokacin kuka nake jinake kmr rabuwarmu tazo ina kukan rashin kaunar da mahaifiyarsa ta nuna min da km abinda babana yayi min .
ni kaina yarasa wani irin son mukewa juna da taufeek.
taufeek yarasa yadda zaiyi dani domin bayason kebecewarsa dani alhalin banza ma halaliyarsa ba.
dan baya son ya sake tafka kuskuren da yayi baya nima nayi kuka kmr raina zai fita amman daga karshe shi na dawo ina rarrashi sbd yafini shiga tashin hankali.

xuciyarsa ta zarta masa da hukinci km yayi aiki daita domin taufeek cire komai yayi aransa ya ajiye agefe yashiga bani kulawa sosai kullun muna tare da juna yana kwantar min da hnkli baya son yaganina cikin damuwa idan kuwa yaga nayi tagumi yanzu ne zai rude ya kasa ya tsare .
ya kasa zaune duk abinda nake so shi nake ci km yake min .
"tun yana zuwa baya kwana a gurina har yazo ya rabama kwana tsakanina da matarsa kwana daya yana gurina kwana biyu yana gurin matarsa.
sannan duk wani tafiye tafiye da zaiyi tare dani yake zuwa .
duk kasar da zai shiga kafata kafarshi ,muje spain tare muje london tare dashi munje india tare chaina dubai in takaice miki bazan iya lisafo miki iya adadin kasashan duniyar da taufeek ya kaini ba.
taufeek yayi min hallaci arayuwa wanda bakowani nmj bane zai iya yin irin abinda yayi.
sanan duk wannan kasashen damuke xuwa dashi mu kwana waje daya mutashi tare muyi komai tare bai km yunkurin yin sex dani ba..

kwatsam wata rana yazo min a hargitsensa wanda bansa me yasamesa ba hankalina ya tashi sosai na karasa inda yake kishingide akan kujera jikina na rawa nasoma tmbyrsa abinda ke damunsa yace babu komai nasoma cire masa kayan jikinsa na hada masa ruwan wanka na kaishi bathroom da kaina nasoma masa wanka daga gurin wanka ne komai ya faru domin kasa juriya yayi ranar sai da yayi sex dani byn yagama na sakar masa kuka ni kuka shi kuka yana rarrashina tare kwantar min da hnkli duk laifin iyayenki dana nawa gashi sunki yarda da aurenmu zasu daukarwa kansu zununbi akaro na biyu tundaga wannan lokacin na dawo tmkr matarsa duk abinda matarsa ke masa shi nima nakeyi masa har ma fiyye dana matarsa hankalina ya kwanta sosai ahankali lokacin period dina yazo ya wuce shiru wani watan ma hk ni kaina alokacin bansan ina da shigar cikinki ba sai da cikin yayi wata hudu sannan mukasan da cikin tunda yasan da zaman cikin ya sake tattara duka wata kulawarsa akaina baya barina cikin kewa ko tunani ya zame min komai din kmr yadda ya fada. byn wansu satitika yake sanar mim matarsa nada shigar ciki banji haushi ba sai kukan taya kaina jaje danayi sbd ni bansa makomar ya'yan dazan haifar masa ba hk yayi ta bani hkr wai duk daya agurinsa babu bambanci.

ahankali cikin jikna ke kara girma dan lokacin har ya dan tasa wani lokacin hk zai tasani gaba yana kuka ina yi wanda kukan damuwa ne da halin maseefar da muke ciki wani lokacin km murmushi da farinciki har ma da labaru kala kala mace yake son na haifa mashi yasa mata sunan hjyrsa idan km nmj ne za saka sunan mahaifina yadda yake bani faricikin ke sa wani sain na manta wai ni dashi ba aure aka daura mana ba zaman hk kawai mukeyi..

wata rana da misalin karfe shida na yammaci ya kirani a waya yace kar na kuskura nayi ganganci fitowa nace meyasa a tsawace yace min ni dai nace karki fito koina nace masa ai bana fita ya katse kiran ranar bashi yashigo ba sai karfe dayan dare yayinda ni kuwa idona biyu tsoro da firgici ya hanani samun natsuwar balle nayi bacci tmbyrsa nashiga yi akan dalilin dayasa yayi dare da km kiran da yayi min ,yace ummun abdul ce ke bibiyata wlh narasa wanda yagayata inda muke nayi shr ina kallonsa yace duk wanda yazo ya buga miki kofa karki bude ni idan nazo zan kiraki nace to cikin sanyi jiki hawaye ya gangaro min da gata da komai na dawo zaman daduro kawai sbd soyaya.

cikina nada wata bakwai tafiya takama shi zuwa spain shida matarsa da yaransa guda biyu sai karamin cikin da matarsa kedashi wanda bai wuce wata biyu ba..
yaxo min sallama kmr kar mu rabu ya dinga shafa cikina yana cewa my loulooooo zan yi missing din keda bbyna dan a lokacin munsan mace zamu haifa sbd muyi scanning har ya juya zai fita ni km ina rike da briefcase dinsa ya juyo rungumoni jikinsa yana kinsing dina ya dan duka yayi kising din cikina tare da cewa momyna zanyi missin dinki amman karki takurawa hasken zuciyata .
"nace gara kagaya mata karki damu me jin mgn ce she well obey the rules .
muna dariya da fariciki kmr kar mu rabu yace min time to time doctor rak zai dinga xuwa duba lfyr jikina sannan akwai wani sako da zai baki idan yazo nace ok muna manne juna sai da matar tayi ta kiransa awaya sannan ya barni ya tafi cike da matsanancin kewata.
lokacin da jirginsu zai tashi sai daya sanar min nayi masu addua gbdynsu.
hk ma da suka sauka ya kirani koda yaushe muna makale dashi a waya ko video call wata irin shakuwace ta musamman atsakaninmu duk yawancin kayan bby a spain yasoma siyowa duk wanda yasiya kuwa sai ya nuna min idan nace yayi ya dauka idan nace baiyi ba zai canza. bakaramin kaya ya tsiya ba amman yace min kayan zasu rigashi isowa nace ni dai nafinson zuwansa akan kaya .
yace a'a shi dai zai turo banyi musu dashi ba sbd nasan sbd matarsa yake son yin hk .
"dan karta gani ta tadda bala'i kmr yadda yace ya turo da kayan wanda doctor rak ne yaje ya amso ya kawo min ban tsaya dubawa ba dan duk nagansu tun inda yayi tsiyayar ..
akalla sai da taufeek yayi wata daya cur a kasar spain sannan yasoma shirye shiryen dawowa Nigeria lokacin dayake sanar min washegari misalin karfe takwas na yammaci jirginsu zai sauka naji dadi sosai tare da yi masa fatan alkhairi na tmbayi yaransa da matarsa da family dinsa na can duk da basu san da zamana ba sbd alokaci tunaninsu mu raba..

washegari tunda natashi na tsinci kaina da jin yawon faduwar gaba dun inda motsa kirjina ya dinga bugawa kenan ahankali nasoma karato addua tare da soma kimtsa gidan duk da nasan bai zama lallai idan ya sauka yasoma zuwa gurina ba .
amman na kyalkyale part dinmu most especial bedroom dinsa koina agidan kamshi turaren airfreshiner yake ni km nayi shirina cikin doguwar riga baka me igiya agabanta tunda sama har kasa da jerin tsone green na tufke gashina atsakiyar kaina tare da feshewa gangar jikina da turare me dadin kamshi.
naxo parlour na zauna na kunna TV ina kallon zeeyword ina jiran kirani naji ya sauka.. yayinda har lokacin gabana bai daina faduwa da jin sanyin jiki ba.
"can kmr an mintsine na dauki remut na canza tasha zuwa nta kmr jirana ake na kunna akasoma wasu labaru da tumi tuminsa...........



mmn sudais ce

💗💗💗💗💗💗
SAI KA AURENI DOLE
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗



~NA~



*AYSHA A BAGUDO*



~DEDICATED TO~
HAUWA A USMAN
JIDDARH

*Allah's messenger saw said fear Allah wherever you are*

page 46


wani tafkeken jirgi naga an soma nunowa me dauke da tarin fasinjoji bil'adadi ,yayinda me gabatar da labarai tasoma gabatar wa kamar haka cikin harshen tsadadden turancinta .

" take ni kuma dake zaune akan kujera na tasa TV gaba da ritsetsen cikina ina kallon abinda ke faruwa in banda faduwar gaba babu abinda gabana keyi.

ahankali na fara karanta rubutun dake rubuce a k'asan TV abinda nagani ne a rubuce yasa naji cikina yayi wani irin azababben Murdawa da karfi, nan da nan jikina naji ya fara kirrrrrrma, gaban TV na isa na koma nayi zaman dirshan cikin matsanancin tashin hankali, tare da kafe TV da idanuna.


jirgin daya taso daga k'asar Spain zai iso Nigeria a yau, sannan zai sauka a jahar Lagos, a murtala international airport dake Lagos .
ya iso cikin garin Lagos amma bai samu damar qarasowa airport ba, a kasamu air Crash, jirgin ya fada wani babban filin kwallo ne dake ablegba.
Life suka shiga nuna yadda abun ke faruwa ga dai jirgin zaune a k'asa ya sauka yayi tsaye, ma'aikatan cikin jirgin suna kai kawo acikinsa domin kokarin ganin murfin kofar jirgin ya bude.
, sunyi sunyi k'ofar jirgi ya bud'u amma ina kofar taki buduwa, ga mutane nan ana hangowa muraransu.
kuma mutanene cikin jirgin bil'adadi hankalinsu a mutuk'ar tashe yake, hannu suke sawa ta jikin window jirgi dayake glass ne sai faman ihu wasu daga cikinnsu sukeyi.
yayinda musliman ciki suke salati suna neman dauki daga gurin Allah. amman fa duk sun rikice wasu ma kana gani sai faman kuka suke.

"Wata mace na hango zaune cikin shigarta na kamala ta d'aga hannunta sama Wanda da gani kasan addu'a takeyi ga yaro a gefenta sai faman tsanyara ihu yake.
" k'ara fiddo idanuna waje nayi domin k'ara tabbatar da abin nake gani aiko kamar gidan TV sunsan me nake son kara tabbatarwa, haskomin fuskar Matar sukayi da kyau aiko take na gane Matar taufeek ce shi km yana zaune a natse agefenta yana motsi da bakinsa bazaka taba cewa cikin maseefa da tashin hankali yake ba. sai dai hannusa rike da waya wanda bansa abinda yake daita ba .
" kalmar innalillahi wa'inna ilaihiraji'un nashiga furtawa ina maimaitawa jikina na sake daukar kirma.

lokacin da naga matar taufeek ta matso gareshi ta rumgumeshi ajikinta tana kuka tare da danta, shima rungumeta yayi sosai tare da cire farin medical glss din dake manne da idonsa yasa hanky yana goge fuskarsa hannunsa daya abayanta yana rarrashinta.

Jama'ar dake waje a ka shiga nunowa kowa kagani agurin ta kansa yake, sannan a rikice babu mai kokarin kusantar jirgi hatta ma aikatan da sukazo wuri ta kansu suke suna gudun ceton ransu , Sanadiyar ganin tanking jirgin ya bude diesel ya falle kamar an kunna fanfo sai faman tsiyaya yake .

jirgi na nan tsaye kmr tun farko da'aka soma nunowa, yakai tsawun minti talatin diesel na zuba wanda a lokaci hankali mutane cikin jirgin gbdy yayi k'ololuwa tashi.

Bayan diesel din yagama tsiyayewa tas, sannan wani irin kara me sauti ya karade gurin , bammmmmmm kakeji jirgi nan yakama da wuta kanajin ihun jama'a musliman dake cikin jirgin suna ta salati da salallami.
"kafin kace me har gurin ya turnuke da hayaki ga namomin mutane nan muraran kana gani da k'asussuwansu.
gaba daya jama'a dake cikin wannan jirgi babu wanda ya tsira da rayuwarsa, dan ko mutun daya ba'a samu ba, naman su yayi fatsafatsa.

gidajen ko da suke da kusanci da football field din nan babu wanda be kone ba sai ta bangaren dama inda bata nan tankig jirgin yake ba ,gidajen da suka k'one gasu nan bazasu kirgu ba daga bangaren hagu.

Wani irin razananniyar k'ara me sauti na saki lokacin danaga me afkuwa ya gama afkuwa daga nan ban sake sanin meke faruwa dani ba.

umma taja numfashi tare da ajiyar zuciya ta sauke hawaye nabin kuncinta wanda ita kanta su'ad din kuka take wiwi har tafi umma shiga tashin hankali.

"umma tacigaba a she a daidai wannan lokacin da abin ke faruwa doctor rak da ahlin taufeek suma sun ga komai daya faru .
doctor rak bai tsaya gama kallon news din ba ya baro office dinsa hankalisa a tashe sbd yasan da dawowar abokinsa ranar dan shine ma zaije airport ya daukosu .
direct motarsa yashiga aguje yakama hanyar zuwa gidana dan baya son naga abinda ya faru sbd condition din danake ciki.

ya karaso daidai kofar dakina kenan yaji sautin ihuna cikin matsanancin tsoro take yashiga ihun kiran sunana yana murda handle din kofar ,sai dai kofar a rufe take kmr yadda taufeek yabani umarnin na dunga kulleta akoda yaushe .

ta window yazagayo ya hangoni a sume a kasa ya koma ya nemo jama'a aka tayasa balle kofar ,ya daukeni raina hannun Allah sai asibintinsa.. aka shiga bani taimakon gaugauwa sai danayi kwana biyu a sume sannan na farfado bakina dauke da kalmar inna lillahi wa inna ilaihi rajiun ,cikin matsancin kuka ina kiran sunan taufeek ....
sai lokacin nasan inda nake a she hospital din Doctor rak ne.

iya tashin hankali nashigeshi nayi kuka har na galabaita

3 Comments On SAI KA AURENI DOLE
avatar
zainab-ishaq

1 year ago

Reply

Love it ????????

avatar
zainab-ishaq

1 year ago

Reply

Yes and I want to download it

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to zainab-ishaq

In order to download you have to subscribe for our package at https://tnovels.com.ng/subscribe

Please Login or Register in order to submit comment