Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

babu wanda yake kina sai kai abdulkabir.. bakasona .......
bakason na rabeka ko rabar duk inda Kake ballantana na rage radadin da nake jin a zuciyata.
pls ...pls ...abdulkabir karka min hk NI masoyiyarka ce kamar yadda na sha gaya maka.
,wayyohhly Allah ya Allah ka dauki rayuwata na huta da wanan bak'ar ukubar akan na ga aurenka da wata ..
Allah ka kasheni kafin zuwan lokacin aurenka, na gwamaci mutuwata da wannan rayuwar... ahankali tasoma yin kasa kasa da jikinta tana risgar kuka har ta tsugunna tare da daura fuskarta akan gwiwowinta tana cigaba da kuka me cin rai da taba zuciyar ma'aboci sauraro.
iskan ruwan na sake dukanta inda take tsugune .
zuciyar AK ce tayi wani irin bugawa da karfin gaske sakamakon jiyo sautin muryarta cikin kuka ,har tagama sambatunta yana jingine yana jinta ,
wani irin sanyi ne ya dinga ratsa gangar jikinta.
take tasoma rawar sanyi da karkarwa har hakoranta na kirma.
ruwa ne aka tsugashi ba wasa ba .
domin kuwa duk wanda ya kwana ya tashi a garin Lagos yasan yadda ake tsuga ruwa barin ma farkon damuna.
km duk tsawon wannan lokaci tana nan a tsugunne ajikin kofar part dinsa tana cigaba da kukanta ahankali wanda ya hadasawa kanta sarawa da karfi.
gashi AK kwata kwata bashi da niyyar bude mata kofar balle tasamu mafaka domin tsira da lfyrta ...
hkn yasa tasoma dago kyakkyawa fuskarta dake zubar da ruwan hawaye ..tun kafin takarasa kai ga dagowa gbdy take jin wani irin azababben kamshin turaren wanda yasaba tsaya mata arai ..
km take ji ajikinta kmr tasan shi .
,tana karasa dago fararen idanunta da suka sauya daga fari zuwa ja ta saukesu akan fuskar wani dattijo dake tsaye can nesa kadan daita, yana dubanta .
hannunta tasa ta dan murza idanunta domin sake tabbarwa kanta mutumin dake tsaye agabanta ba abdulkabir dinta bane kama ce kawai, da dan bancanci tsakaninsu, shi wannan fuskarsa ta dan manyata sabanin ta abdulkabir dinta dake cike da tsantsar annuri da zati tattare da nagartacce kyau da kurciya.
kusan Mintuna talatin ta dauka tana kallonsa , kafin daga karshe ta zabura ta mike tsaye a firgice tana zare idanuwa cike da matsanancin tsoro..
bangaren dady kuwa tsaye yake cike da sarkakiya da mamaki ganin mace a kofar part din ak.
duk yadda yasan dan nasa na mu'amula da mata baiyi tunani zai iya kawo mace har cikin gidan dayake zaune ba, wani irin kallo yake bin yarinyar dashi zuciyarsa na kitsima masa wacece ita da kallon sani dayakewa fuskarta? her face is familiar to him .
sosai ya tsura mata idanu ahankali yashiga tunani Inda yasan fuskar ,gabansa ne yashiga dukan uku tabbas duk inda fuskar take yasanta sani km farin sani sai dai,ta ina hkn zata kasance, fuskar wayanda yake gani a fuskar yarinyar dake tsaye agabansa yanzu bata da halaka da fuskar dayasani, kama ce kawai ba wata halaka ko dangantaka ce ba. ahankali yacigaba da kallonta, kafin daga bisani ya numfasa tare da cewa .
yarinya daga ina hk ko wani kike nema..?
tunda dady yasoma mgn su'ad ta sunkuyar da kanta kasa gabanta na faduwa sbd kwarjinin da dattijon yayi mata, bakinta da jikinta rawa suke gurin cewa uhm ..uhm ina wuni sunana su'ad daman nazo wajen abdulkabir ne.. nazo gurin abdulkabir dady ya maimaita mgnrta cike da mamaki, take km zuciyarsa tasoma bashi haske akanta.
duk da bata gaya masa bayanin komai akanta ba ya gane yarinyar dake da halaka da tilon dansa ce tausayin yarinyar ne ya rufe shi ,ya dinga wani iri acikin ransa.

wannan wani irin so ne hk takewa abdulkabir dinsa ..?

yanzu duk ruwan nan
akanta yakare kome.?

to yanzu ina shi abdulkabir din yake. daya barta anan ruwa yayi mata duka? ajere
yayiwa kansa tmbyr acikin zuciyarsa.
wani irin sanyi yaji yana ratsashi ta koina, ko babu komai wannan abun alfahari ne ace mace tana maka irin wannan tsaftacencen soyayya ta gsky .
wanda duk wani uba na gari zai so ace dansa yasamu mace irin wannan me tsananin sonshi .
ita kanta soyayyar mace wani jigo ne da taimako a bangaren auratayya,rayuwar aure. sannan tunda yake
a rayuwarsa bai taba ji ko gani irin wannan soyayyar ba .
cikin sanyi jiki su'ad tashiga ware bakin mayafinta domin suturta jikinta , tana kokarin barin gurin dan gane kowaye agabanta.
dady yayi hanzarin dakatar daita da hannunsa yana takawo ahankali zuwa bakin kofar part din ak tare da yin noucking .
"ak wanda ke tsaye jikin kofar yayi shiru kirjinsa na bugawa da karfi, yaki motsawa balle yayi yunkurin bude kofar yayinda zuciyarsa tashiga shawagi tare da harbawa, jin bugun kofar yayi yawa ne yasa zuciyarsa dugunzuma tare bude bakinsa cike datakaici yace dan ubanki tsayuwar uwar wa kike da bazaki bar gidan nan ba ..
ko gidan ubanki ne ?
wlh idan kika sake na fito na sameki agurin zan miki dukan mutuwa na balbalki na aikawa ubanki da kasusuwanki stupid girl kawai ...wace bata san ciwon kanta ba .
yana karasa mgnr bai tsaya jin ko me zat'ace ba ya baro jikin kofar ya nufi cikin bedroom dinsa a tunaninsa ko su'ad ce ke yin nouking .
yana shiga ya fada kan gadonsa yana fidda numfashi ahankali ahankali ko mitin biyu baiyi da kwanciya ba kira yashigo wayarsa,
sai da gabansa ya fadi dan jin wayarsa ta dauki karar sauti ,yasa hannunsa ya lalubo wayar ya manna akunneshi batare daya duba screen din wayar ba.
shiru yayi yaki cewa komai, yana jira daga dayan bangaren, kazo ka bude min kofa....gani akofar part dinka.
ai jin muryar dady yasa ak yin wata irin zabura ya Mike zaune yana kallon kofar bedroom dinsa zuciyarsa nacigaba da harbawa oh my God Allah kasa dady bai ga wannan shegiyar yarinyar nan ba?
cikin sauri ya duro daga kan gadon yasoma kokarin sanya kaya ajikinsa.
short niker yasa tare daura riga tsanyi me hulla abayanta bai tsaya zuge zip din gaban rigar ba ya fito ransa a matukar bace.
ya bude kofar idanunsa suka sauka akan fuskar mahaifinsa tsaye, yana kallonsa , matsawa baya kadan yayi domin bawa dady hanya tare da zabgawa su'ad wata uwar harara wace tasa hantar cikinta kadawa, da sauri tayi Kasa da kanta tare da kamo yatsun hannunwata tana wasa dasu..
kokarin kulle kofar AK yake yaji sautin muryar dady cikin kunneshi yana bashi umarni ,kabar yarinyar nan tashigo.barin kofar yayi a bude
,ya juya cikin fushi batare da ya sake kallonta ba, zuciyarsa kmr zata buga, yana kokarin komawa cikin bedroom dinsa.
dady yakirasa sunansa abdulkabir dawo nan sannan kacewa yarinyar nan tashigo ciki yanxu tun ranka bai fi hk baci ba.
dole tasa ya juya ba dan ranshi yaso ba, koda ya isa bakin kofar bai ce daita komai ba dan bai jin zai iya aikata abinda dady yace, dan hk yakarasa ya kai hannunsa kan nata domin fixgota ,wani irin shock yaji ajikinsa tun daga tsintsiyar kafafunsa har zuwa tsakiyar kanshi take an jona masa wutar lantarki. take jikinsa yasoma rawa yadda yaji ajikinsa hkn ce takasance daita dan hk da sauri ya fixgo hannuta da karfi yayi wurgi daita cikin tsakiyar parlour yana sauke naunauyen ajiyar zuciya tare da kallon hannunsa .
muryarsa ahankali yace dady ina zuwa kabani minti biyu yanzu zan fito.?
nakara maka minti uku akai kashiga ka fito ina jiranka.
tsaki yaja akasan ranshi tare da dago mayatattun idanunsa wayanda suka koma ja ya daurasu akan agogon dake daure da tsintsiyar hannunsa. lokaci ya wuce sosai tsaki sake ja yashiga bedroom dinsa hade da shigewa bathroom, bathtub yashiga yayi wanka ya wanke hannunsa daya taba jikinta dashi sosai sannan ya fito ..
ya saka wasu kananan kayan dagon wando baki da riga shirt itama bata ya fashe ilahirin sansar jikinsa da turare , ya sake fitowa zuciyarsa na matukar bugawa da karfin gaske.
ya zauna akan kujerar dake facing din dady, murmushin takaici dady yayi yana dubansa tare da girgiza kai.
yayinda su'ad ke zaune rakube a gefe kanta ta soke akasa tana cigaba da wasa da yatsun hannunta ta dago ahankali sakamakon kamshin turarensa daya kaiwa hancita ziyara, ta daura idanunta akansa yana zaune yana wani cincin magani,idanu ta tsura masa sosai tana kallonsa kmr zata cinyeshi, gbdy ta manta ko a ina take da gaban wanda take zaune ...
har sai da dady yayi gyaran murya sannan ta dawo cikin hankali da natsuwarta ta sake sunkayar da kanta kasa.
dady ya sake duban ak cike da hade rai dan ma kar ya kawo masa rainin sense yace wace wannan yarinyar?
yayi mgnr yana nuna inda su'da ke zaune sunkuye da kanta

tsaki yaja acikin zuciyarsa sannan ya bude bakinsa da kyar muryarsa can kasa kasa wanda idan ba saka kunne mutun yayi ba bazai ji abinda yace ba. yace dady yarinyar nan ce... yana gama fadar hk ya koma ya dan meida bayansa da kujerar dayake zaune kirjinsa na bugawa tare da runtse mayatattun idanunsa .. amman me nace maka akan yarinyar?
dady banzan iya daya daga cikin abinda kace min ba sbd bata cancanci hkn ba.
i can'tmarry her dady coz she's not my type i can't marry her coz she's prostitute.. i can marry her coz.....short up dady ya bugasa tsawa a fusace kai meye ba dan iska ba ai irinta itace daidai da aurenka ba kamilar mace irin zainab ba, wace ta tsare imaninta tare da tsarkake zuciyarta..
kai kasan baka bukatar mace irinta meyasa kake aikata barna.
ina tabbatar maka wannan ita irin matar data dace da kai..
dady yakarasa mgnr yana furzar da iska

i can't marry her coz she's not my type i can't marry her coz she's prostitute shine kawai abinda su'ad ta dinga maimaitawa acikin zuciyarta .yayinda mgnr ta dinga mata yawo a ilahiri gangar jikinta da kwalkwaluwarta ,wai meke shirin faruwa dani ne?
meyasa zuciyata ta kamu da matsanancin son wanda bai kaunata oh my God what wil i do now?
take zuciyarta ta bata amsa da ki tsaya kiji abinda mahaifinsa zaice first, kafin kinsa matakin dauka akaro na karshe. dan hk ta goge hawayen dake ta tsiyayowa daga kwarnin idanunta a tun sanda ak yasoma mgnr bazai aureta ba idanunta ke kansa tana kallonsa tana zubar da hawaye ganin dady yaki sake cewa komai , yasa tasoma jan gwiwowinta zuwa inda AK zaune tana kuka tana rokonsa karka ce bazaka aureni ba...
da ka gujewa aurana gara ka kasheni na huta da bakincikin wannan rayuwar ta juyo tsaitin dady .
dan Allah dady kace abdulkabir ya aureni ....wlh ina matsanancin son shi da gsky .
zanyi duk abinda yake so... zan .. wata uwar razananniyar tsawa ya buga mata ta hanyar katseta da hannunshi daya, wlh idan kika sake furta wannan bazan kalmar zan miki dukan mutuwa..
na yarda ka kasheni abdulkabir......
. wlh ka kasheni matsawar baka raba gangar jikina da numfashi ba bazan daina furta maka wannan kalmar ba... dau taji saukar mari akan kuncinta ....take wasu taurari sun gilma ta cikin idanunta .
tasa hannunta ta dafe daidai inda hannunsa ya sauka tana kallon cikin kwayar idanunsa .
maza maza ki bar nan ya nuna mata hanyar fita wallahilazim na sake ganin kafafunki a kofar gidan sai nasa andaure min ke muddin rai stupid kawai wace batasan ciwon kanta ..
jikinta a sanyaye ta Mike tsaye kirjinta na harbawa da karfi tana jin yadda kirjinta yayi mata nauyi tmkr an daura mata dutse.
take wasu zafafan hawaye suka shiga ambaliya suna zubowa akan kuncinta.
har ta juya da niyyar barin gurin dady yakirata .
ta juyo ahankali idanunta cike da hawaye, tausayinta ne ya sake kamashi muryarsa a matukar sanyaye yace ki kara hakuri, ni din nan da kike gani nine mahaifin abdulkabir .....
ina me tabbatar miki matsawar abdulkabir mijinki ne bazai taba tsarewa aurenki ba ....kiyi tafiyarki Inshaallahu zan nemek...


manage pls ..........



mmn sudais ce

💗💗💗💗💗💗
SAI KA AURENI DOLE
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗



~NA~



*AYSHA A BAGUDO*



~DEDICATED TO~
HAUWA A USMAN
JIDDARH


*qala rasulillahi sallallahu alaihi wa sallam addua'ussalahul mu'amin*

*Allah messenger s a w said supplication is a believer's weapon*


*besty comments for this novel*.
*mrs adam*
*maimuna matar,abdullahi*
*zahra yakub*
*subby*
*mmn twins*
*i really appreciate for the comment's*

page 29

saurin mikewa AK yayi tsaye zuciyarsa na bugawa da matsanancin karfi,yana duban inda dady ke zaune yana sake cigaba da maimaita mgnrsa atsanake, matsawar abdulkabir mijin aurenki ne ina me tabbarta miki da zaki aureshi da izinin Allah.
da yarda allah zane miki da zarar mahaifiyarsa ta dawo kasar .
yanayin bugun zuciyarsa bai saisaita ba.. hk yanayin tsoratar da yayi da furuncin dady sai ya baka mamaki.
bakinsa na rawa yasoma mgn cike da in.. inna ,ha..ba haba dady ....dan Allah dan annabi karka min hk dady.
karkayi kokarin hadani da wannan watsartsiyar yarinyar amatsayin matar aurena..
yarinyar da bakasan ko wacece ba balle asalinta.
dady kowani uba nagari burinansa arayuwa bai wuce yasammama ya'yansa uwa ta Gari ba....
idan na aure wannan gantalalliyar yarinyar nacewa ya'yana me...?
mezance dasu dady....?
kwata kwata bata cancanci zama uwa ko zaman aure ba.
, tafi cancanta da watsatsu maza yan'uwanta ko yan zaman wajoko wlh shine abinda yafi dacewa daita .
ya sake raunata muryarsa sosai kmr zai zubda hawaye hb dady'nah .. ka kalleni ka kalleta kasan babu ta inda muka dace da wannan prostitute din me bin.....
ya isa dady ya sake katse masa hanzari a tsawace ta hanyar dakatar dashi, babu shiri yayi shr sbd yadda ya hango tsagwaron bacin rai shimfide akan fuskar dady'nsa .
"karka sake kuskuren furta wannan kalmar gareta banson sake jinta daga bakinka, kaddara tana kan kowa km babu wanda ya wuceta.
furzar da iska yayi daga bakinsa yana lumshe mayatattun idanunsa kusan minti goma ya dauka runtse da idanunsa sannan ya budesu ahankali ya meida kallonsa zuwa inda take tsaye tsuru tsuru tana kallonsa ,
tsoro da matsanancin firgici yaga ya bayyana akan fuskar su'ad yayinda zuciyarta tashiga bugawa da karfi numfashinta yasoma barazanar daukewa tayi saurin dafe kirjinta da hannunwanta duka, duk da wannan fargaban da zuciyarta ke ciki hkn bai hanata tattaro jarumata tasanyawa jikinta ba tare da zuba masa fararen idanunta tana kallon cikin kwayar idanunsa dake cike da matsanancin tashin hankali iri iri .
tana jin ,wani irin bakin ciki me tattare da tsagwaron bacin rai na ratsa kowani sashi na gangar jikinta .
wasu zafafan hawaye ne masu dumi da ciwo suka soma gangarowa bisa kuncinta.
jitake duk duniya babu bil'adam da aka tabayiwa wulakanci da tozarci irin wanda abdulkabir yayi mata ayanzu .. meyye laifinta ....?
bafa ita tasanyawa kanta soyayyarsa ba.
Allah ne ya jarabeta da matsanancin kaunarsa.
wanda a iya rayuwarta bata taba tsammanin zata tsinci kanta cikin wannan halin tashin hankali ba..
yau ita ke bin namji allah da annabi ya sota amman yake wulakantata hade da tozarci iri iri .
gabadaya acikin tozarcinsa dayake mata kalmar karuwanci dayake hadata dashi yafi komai tsaya mata arai da bakanta mata rayuwa. ganin tana tsaye tana kallonsa bata da niyyar tafiya gashi dady yaki cewa ta tafi .
yasashi harzuka yashiga nuna mata kofar fita da dan yatsan hannunsa tsayuwar uwar me kikewa mutane anan yayi mgnr cikin daga murya ki tafi man ko gidan ubanki ne nan ..?
kawai ina zaman zamana
kina son jazamin bala'i da wahalarki.
ban da ita zuciyarki tsinanniyar zuciya ce tarasa wanda zataso sai ni abdulkabir... yakarasa mgnr yana furzar da iska da nuna kirjinsa gabadaya yafita cikin hankalinsa da natsuwarsa idanunsa sun gama rufewa burinsa kawai tabar gurin banda sambatu babu abinda yake yana zaginta da tozartata.
" duk wani tsoron dady dayake ji abaya ayau ya kau acikin idanunsa da zuciyarsa .
sam baya jin zai iya abinda dady yake son aikata wa .
dady kace mata ta wuce wlh idan bata bar gidan nan yanzu ba zan mata lahani zan mata dukan mutuwa zan kasheta da hannuna na kashe kaina kowa ya huta haba narasa wace zan aura sai wannan karu...... ..saurin datse harshensa yayi yana cizan lips dinsa da iyakacin karfinsa sbd gargadin dady garesa.
matsowa tayi ahankali kusa dashi tana girgiza masa kai ciki kaduwa .
jikinta na rawa ta sake matsoshi sosai har suna iya jiyo numafashin juna.....
yaja baya da sauri yana tsaida ita da hannunshi karki sake ki karaso gareni ..naji bazan yi kuskuren aikata hkn ba amman dan girman allah
ka daina furta min wannan kalmar kada zuciyata ta buga Allah yasani ni ban kasance cikin wayan nan matan da kake lisafowa ba ....yiwa mutane shr stupid kawai
Allah yasa zuciyarki ta fashe ki mutu na huta da jarabarki ......haba wannan wani irin naci ne sbd Allah nace ban sonki ban sonki ba sai ki rabudani ba tunda ba'a soyayya dole ayi mutun ba zuciya ...
dady dake zaune yayi shiru yana kallonsu cike da matsanancin mamaki da tausayi abu tmkr a film.
ahankali dady yakira sunanta da yarinya dan har lokacin bai san cikakken sunanta ba.
su'ad tajiyo ahankali idanunta cike da ruwan hawaye ta daurasu akan fuskar dady.
sai da dady yayi gyran murya tukun yasoma mgn atsanake cike da natsuwa.
" kiyi hkr kiyi tafiyarki Insha Allahu zan san abinyi da yarda Allah ..
karasowa tayi jikinta na rawa ta dukursa gaban dady har kasa tana masa godiya tana zubda hawaye me taba zuciya na gode na gode dady Allah yabiya maka dukkanin bukatunka na alkhairi yadda kake kokarin tallafawa maraicina Allah ya duba naka bayan....
a fusace ak yakaraso gareta zai damki wuyanta dady yayi saurin dakatar dashi da hannunsa yana yi masa warning kashiga hankalinka abdulkabir ka fita cikin idona na rufe sannan tun raina bai baci ba.
ka dawo cikin natsuwarka ... wlh dady matsawar kana bukatar natsuwata sai wannan jakar yarinyar tabar gidan shine kwanciyar hankalina but as far as ina ganinta anan wlh bani ba wata natsuwa balle kwanciyar hankali dan kwata kwata bana kaunar na bude idanuna na ganta.
bason daura idanuna akanta.
to naji ka zauna zata wuce yanzu wani irin kuka su'ad take na fitar hankali me taba zuciyar ma'aboci sauraro.
sosai zuciyar dady tayi rauni amman shi ak ko akwalar rigarsa sai ma Allah Allah yake tabar gurin ya huta .
jikinta a matukar sanyaye ta mike tsaye hawaye na sake wanke mata fuska ta tsura masa ido tana kare masa kallo sannan ta juya ahankali tasoma daga kafafunta tasoma tafiya cike da sanyi jiki kirjinta na wani irin bugu kmr ana buga mata guduma ta isa bakin kofa kmr ta juyo ta sake kallonsa sai km ta fasa ta daura hannunta akan handle din kofar ta murda ta bude kofar ahankali tare da turawa ta fice daga part din.

fitarta ke da wuya AK ya sauke naunauyen ajiyar zuciya tmkr wanda yayi gudun tsare, batare da ya sake yunkurin cewa komai ba ya koma ya zauna akan kujera zuciyarsa na wani irin harbawa da sauri sauri dady ya tsura masa ido kawai yana girgiza kai sannan ya yakira sunansa abdulkabir...da kyar ya iya bude bakinsa ya amsa da na'am dady . abdulkabir banason abinda kakewa yarinyar nan ,yana taba min zuciya wlh ita ma mutun ce kmr kai. akwai tarin mutane dayawa mara iyaka acikin wannan garin da km unguwar datake rayuwa ammam ta zabi takasance tare da kai.
meyasa bazaka amsa tayinta ba?
abinda nake so dakai da zarar anyi bikinka da zainab kayi kokari ka auri yarinya nan kodan yanto rayuwarta.
"lamarin yarinyar akwai tausayi ciki,nasan bata cikin natsuwarta amman shi son datake maka abin a duba ne .
ni kaina hk kawai tun sanda kabani labarin yarinyar na tsinci kaina da son ka aureta wanda bansa dalilin jin hk ba.
a kallon farko danayi mata dazu naji tashiga raina .
hakazalika tausayinta ke dawainiyya dani.
bance zan tursasa maka akan lamarin yarinyar ba amman kayiwa Allah kayi tunani akan yarinyar nan ...
tunda dady yasoma mgn ya runtse mayatattun idanunsa yana sauraronsa har sanda ya dasa aya baice komai ba ya numfasa tare da bude idanunsa wanda suka soma canzawa zuwa ja ya saukesu akan dady dake zaune yana kallonsa muryarsa a kasalance yasoma motsa labbansa dady ba bujirewa mgnrka nake kokarin yi ba .
amman kayiwa Allah da manzonsa dady kabar zance yarinyar nan .
wannan yarinyar da kake gani ba abar tausayin bace wlh azim bata da tarbiya balle kamun kai , duk wani abinda kasan nmj na sha na dangin maye babu wanda bata sha ..
gang ne daita na musamman masu tadda tarzoma acikin gari. nasan bakasan da wannan halin nata ba dady ,dabaza ka taba cewa na aureta ba.
ni dai dady dan girman Allah kayi hakuri kayi hkr da zance yarinyar nan dan bazan iya aureta ba, ya karasa fadar mgnr muryarsa na rawa kmr zaiyi kuka.. dady yayi murmushi irin nasu na manya sbd hango wasu abubuwa da yayi tattare da tilon "dan" nasa.
kana yace yarinyar tana matukar kaunarka abdulkabir sannan bakasan abinda Allah yake nufi da hkn ba . bakasan me gobe zata haifar ba atsakaninka da yarinyar .
a yadda yarinyar take mutuwar sonka zata maka biyayya zaka juyata yadda ranka ke so, sai yadda kayi daita matsawar baka aureta ba km kai kanka bazaka zauna lfy ba, bazata barka ka huta ba . farinciki dakake nema arayuwar auranka bazaka taba samunshi ba...
aurenta kawai shine mafuta agareka damu gbdy ,nima ubane yadda bazan so ganin nawa ahlin cikin halin damuwar da yarinyar take ciki ba.
hk zalika bazanso ganinta cikin tashin hankali ba, amman kayi nazari da tunani da kyau kafin dawowar amminka a thing this week zasu dawo abinda ka yanke ka sanar min ,dady nakarasa fadar hk ya Mike tsam yasoma kokarin barin part din..
yayinda AK dake zaune agurin kmr an dasashi yashiga damuwa mara misaltuwa , babu wani abun da zanyanke akai dady byn taje gaba ta nemi nata mijin yayi mgnr cikin zuciyarsa.

tafe take bisa kafafunta tana zance zaci tmkr wata tababbiya sabon kamu, yayinda zuciyarta take cike fal... da matsanancin tsoro da fargaba rashin amincewar ak akan batun aurenta . zuciyarta ce tashiga bata karfin gwiwar bisa ga maganganun mahaifinsa gareta dattijon arziki da sanin yakamata ...
ahankali tayi kokarin kau da damuwarta ta hanyar sanyawa zuciyarta da fuskarta walwala tare da natsauwa samun auren abdulkabir cikin sauki a dan wannan lokacin,
kai tsaye gidansu ta nufa .
"cike da matsanancin farinciki ta shiga part dinsu , ummanta wace ke zaune ta kalleta tace me faru ne su'ad naga kina cikin farinciki hk wanda yaushe rabon dana ganki cikin farinciki irin hk?zama su'ad tayi akan bakin kujerar da umma take zaune tana sake murmushi tace ummana ina cikin farinciki yau ... burina ya kusan cika.. farincikinki dakika rasa ata sanadiyyata ya kusan dawowa zamu cigaba da rayuwarmu kmr yadda mukeyi ada.
, su'ad dinki zata sake dawowa mutun sak, murmushi umma tayi tana shafa kanta Allah yasa, Allah ya nuna min wannan rana me cike da tarihi Allah yayi miki albarka ya shirya min ke shirin na addinin muslinci su'ad tace ameen ummana bari nashiga ciki takarasa mgnr tana mikewa tsaye ta nufi uwar dakinsu. da kallon umma tabita dashi fuskarta dauke da murmushin tausayi tana kara godiya ga Allah da shiriya tasoma wanzuwa arayuwar tilon diyarta ada can kafin tazama haka ta zamemata tamakar ya'ya goma Allah ya bata.
a kullun tana alfahari da kasancewar su'ad diyarta banda yanzu data bata kanta da shaye shaye..
daren ranar da kyar ak ya runtsa tunani iri iri ya sakoshi gaba yarasa meyasa dady'sa keson

3 Comments On SAI KA AURENI DOLE
avatar
zainab-ishaq

1 year ago

Reply

Love it ????????

avatar
zainab-ishaq

1 year ago

Reply

Yes and I want to download it

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to zainab-ishaq

In order to download you have to subscribe for our package at https://tnovels.com.ng/subscribe

Please Login or Register in order to submit comment