Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tsaya sororo tana kallonta da gudu su'ad ta karaso ta rungumeta eiman tana kuka "ki taimakeni eiman ta kwace min miji shikenan abdul yazama nata ita kadai?

"aa waye yace miki ta kwance miki miji kina nan fa har yanzu amatsayin matarsa.

girgiza kai su'ad tashigayi tana kuka " abdul ya daina sona eiman abdul bai son ganina yanzu nagansa a waje ko kallo inda nake bai yi ba "ku taimakeni ku taimaki rayuwata kar narasashi idan narasa zaku rasani kuka take Sosai har sanda ammi tashigo dakin takamota suka shiga daki .
ahankali tashiga rarrashinta "kukan ya isa haka "ammi ki taimakeni kar narasa abdul ina son shi bana son narasashi tayi mgnr tana dafe kirjinta .

"haba mamana yanzu fa muka fito daga asibiti ki kwantar da hankaliki idan ma abdul ya daina sonki zaki samu wanda yafishi ..


"aa ammi tashiga girgiza kai karki fadi haka ammi ina son mijina bana son rabuwa dashi bashi da laifi wallahi nasan bashida laifi yana ni yake so ba zeey kawai dai anfi karfin tinaninsa ne, sau nawa yasha gaya min baya son zeey bazai iya rayuwa daita ba" ni dai ammi kisan yadda zaki yi abdul ya dawo gareni idan ba haka ba zaki rasani takarasa mgnr tana sakin wani matsanancin kuka ummanta ce tashigo dakin "malama kiyiwa mutane shiru tayo kanta gadan gadan kmr zata doketa ammi ta tare "aa salema kar naga hannunki ajikinta.


umma tasoma mgn cikin fushi "mutun yace bai sonki dole sai kin kashe kanki akansa, kisa ni kuma nashiga uku ta ina kike son fara tawa rayuwar ?

can kuma tayi kasa da muryarta "kina jina ko, ban ce ki cire son mijinki ba, dan nasan yadda soyayya take dadinta da d'acinta, amman kiyi kokarin ki cire wannan damuwar aranki, idan kuma kinki kikayi sanadin da ciwon zuciya yakamaki kika mutu amatsayina na uwa bazan miki adduar samun rahma ba sbd kece kika kashe kanki.
"aa salema karki ce haka da me kike son taji?

murya cike da matsanancin kuka umma tace "to ni yaya take son nayi , ta duba taga yadda rayuwa tayi dani kowa fa da kaddarasa yakamata kigaya mata wannan itace kaddararta , idan da rabon zai dawo ya fuskacin lamarinta zai dawo har yazamonto kmr ba'ayi ba ,idan babu rabo iya zaman kenan haka zata hakura "ni na wuce kuma bazan sake takowa cikin gidan nan da suna daba lafiyarki ba idan kingadama ki kashe kanki akansa ruwarkice dan shi bai san kina yi ba ta juya a fusace ta bar dakin dama gidan gbdy .

"kingani ko kinsa ran mahaifiyarki ya 'baci mu da muke neman daidaituwar lamarin fushinta zai iya haifar mana da komai, ki daure kicire komai aranki abdul d'ana ne dana haifa da cikina ina tabbatar miki sai ya dawo gareki sai dai idan bana raye ta rungume ammi ajikinta tana kuka itama ammi kukan take.

shi kuwa ak suna gama magana da hjy kaka daga can gidansa ya wuce bai shigo part din ammi va.

tsakar dare ta tashi da kyar taje ta d'auro alwala ta fito ta isa tasoma tashin ammi "ammi ammi ki tashi ammi da baccinta ya d'anyi nisa ta tashi ta zauna akan gadon tana duba agogo jikin gadon karfe 1 ta wuce da wasu y'an mintuna yunkura tayi ta tashi tsaye tashiga bayi ita kuma su'ad ta soma sallah dare ranar haka suka dukufa gurin kaiwa Allah kukansu.

*anan ison na janyo hankalimu iyaye mata ba sai abubuwa sun rincebewa rayuwarmu ba tukun zamu kusanta kanmu ga Allah , yana da kyau koda yaushe mu dinga tsananta yiwa kanmu addua ga mazajenmu da yaranmu ta hanyar yin azzakar din safe da yamma*

washegari a dakin dady tara tayiwa ammi bayan sun gaisa tashiga bayi ta hada masa ruwan wanka yashiga.
ya fito ya isketa a inda ya barta zaune ta rafka tagumi , yasoma shirins har yagama bata dago tabi ta kansa ba .
sai da ya zauna zaiyi breakfast yaga har lokacin hankalinta baya garesa sannan ya dago ya dubeta atsanake yana nazarinta kusan minti goma ya d'auka yana kallonta gbdy ta zabge ta saka damuwar yaranta cikin ranta ,ahankali ya kira sunanta "baraka ta dago ahankali ta dubeshi batare da tace masa komai ba "matsalar yaran nan ce ko?

ta furzar da iska ta bakinta still bata ce dashi komai ba ya numfasa sannan yacigaba da mgn "yakamata ki sanyawa zuciyarki hakuri akan lamarin nan bansa meke damun 'kwal'kwar abdul ba ,daga wannan sai wannan abun nasa yasoma bani tsoro yaro kamar me aljanun boye "idan aljanun ne ma ai daga danginka asaka masa, tayi mgnr cikin ranta, amman azahirance cewa tayi "wayasani ko aljanun gareshi ni kaga karabani da zancesa kwata kwata banason ana yi min maganarsa.


" saboda ya juyawa diyarki baya?


ammi tace "kwarai kuwa saboda iskancinsa da wulakansa baya karewa akan kowa sai akanta ni kuma wallahil azim akan su'ad zan iya ciresa acikin ya'yana wanda ma bai haihu ba d'a ne zai binneshi ba ballanatana ni.

"to ni dai a taimaka ayi masa afuwa Inshaallahu zan nemeshi da zance ,.

"da dai kabarshi dan zuwansa bawani amfani zai mana ba a yanxu da kanshi ke hayaki inji cewar ammi .

dady yace "ni dai kiyi hkr ki yafe masa ta hakan kawai abubuwa zasu sausauta gareshi nan yashiga rarrashita daga dokin fushin datayi dashi har ta dawo tana sanya masa albarka.

shikuwa dady ammi na fita ya yashiga neman layin AK wayar tayi ta ring ba daga ba , ak dake kwance akan cinyar zeey yana labarta mata kyautar company'nsa na toyos mother dayake son mallaka mata ta kamkame kanshi akirjinta tana murna kiran ya sake shigowa ya sa hannunsa ya lalubo wayar dake kan center table yana duba screen din wayar ganin sunan dady'nsa ne yasa shi dauka cike da girmanawa ita kuma ta daura hannunta akansa tana shafa sumar kanshi muryasa na yace "an tashi lfy dady?

dady yace "lfy son ya kake da lafiyar da zainab ?

"duk lafiya muke "

dady ya numfasa sannan yace "son daman nakiraka ne akan zance yarinyar zumbur ak ya mike zaune daga cinyar zeey yana shafa sumar kansa da dayan hannunsa dady yacigaba "yakamata ace itama ta tare agidanka kmr yadda zainab take zaune tare da kai ,zamanta anan bashida wani amfani dan haka duk abinda kake ciki nabaka nan da zuwa nest week kav kasamu amminka da zance, dady na dasa aya bai tsaya jin abinda zaice ba ya katse kiran.

. ......ya cire wayar a kunnensa yana duban zeey dake kallonsa tana jiran yayi mata magana akan wayar da yayi muryarsa a sarke yace "da..dady ne yakira akan zance yarinyar nan .


"daya kira sai akayi yaya? ta katseshi tana hade rai .

"wai cewa yayi su'ad ta dawo gidan da zama.

"tab gsky ni ban yarda da wannan tsarin ba kagaya masa bata da wani muhali a gidan idan kuma ya matsa ga bosquater can ta zauna acikisa amman ba dai idan nake rayuwa ba ta mike tsaye zata wuce ya kamo hannuta cikin nasa "plz my zeey kiyi hkr naga kmr ranki ya baci "sakeni dan Allah ni dai kaji abinda nace "karki damu nima banason zaman tare dani ta tabe baki tana hararasa tunda tasan maganar ba daga asalin zuciyarsa ta fito ba sharrin tsubu ne ta fixge hannunta da karfi tashege daki ta barshi nan zaune.

*******
zaune take akan sallaya a dakin ammi tunda suka fito daga asibiti take zaman dakin tana kawai Allah kukanta a zaune datake hannuta rike da casbaha tana lazimi gefe daya kuma tunani mijinta ne ya ishi zuciyarta ji take dama Allah ya aiko mata da mutuwa ta mutu ta hutawa ranta sakamakon shirun gidan yayi kasancewar ammi ta fita .

ammi data shirya kai tsaye gidan umman su'ad ta nufa bata hakurin abinda ya faru ranar, sannan ta tasota gaba sukazo tare domin ta sake duba lafiyar su'ad din wanda hakan yabawa su'ad damar baiwa mahaifiyarta hakuri tare da tabbatar mata zata rage damuwar dake damuna amman bazata iya cire son abdulkabir addua tayi mata sosai duk lokacin da irin hakan ta faru daita mamma take tinawa mahaifiya me dadi ta fadi hk aranta tana ji ajikinta lokacin komawarta ga mahaifiyarta yayi kusa , idan iyaye sunyi fushi da ya'ya bai kamata ace ya'ya suyi fushi dashi ta fadvawa kanta haka tana kuka.

sannu ahankali abubuwa suka dinga faruwa suna wucewa ciki har da samun lafiyar su'ad babu laifi jikinta yayi k'wari sai abinda baza'a rasa ba wanda ya danganci mutuwar jiki datake fama dashi da tsirface tsirface gurin cima, yau tace bata cin kaza gobe tace bata cin wannan, yayinda ammi ke biye mata akan duk abinda tace zatace har ta kai tawo sai an tmbyeta abinda za'a dafa mata duk nisan guri kuwa idan tace abincin gurin zata ci haka ammi zata aika a siyo mata ta bangeren doctor saif shima yana kokarin kulawa da lafiyarta kullun yana kan hanyar zuwa duba jikinta kmr yau sai gurin yamma yazo kasancewar weekend ce sanye cikin kanana kaya yashigo parlour'n ammi su'ad na kwance ita kadai tashin ammi kenan tana jin cent turarensa tayi saurin kawar da fuskarta tare da runtsesu abinda batasani ba yarigada ya gan lokacin datayi haka.
cike da sanyin jiki yakaraso har inda take kwance ya leka fuskarta yana kallonta jin inwards bisa kanta yasa ta d'ago a d'an fusace tana watsa masa wani mugun kallo wanda yasa numfashinsa ya nemi tsarkewa sakamakon d'agowar datayi ta kalleshi ya d'anyi gyaran murya kana' "yace sannu ya karfin jikin?

taki bashi amsa ba illa yatsina fuskata datayi ala'mun ya dameta, ita gsky zata gayawa ammi ataka masa birki da wannan zuwansa, idan dan kula da lafiyarka a sallameshi dan ita warke lura yayi kmr ya takura yasa ya mike tsaye sosai yasamu guri ya zauna yana fuskantarta sai ga ammi tashigo "aa docto sannu da zuwa ai na d'auka bazakazo ba tunda naga yamma tayi ashe kana tafe "

yayi murmushi yana jefan su'ad da wani kallo sannan "yace nazo naga jikin patient dina yakarasa mgnr yana sake murmushi.

"aiko muna godiya sosai ga patient dinka taji sauki sai tsirfa iri iri su'ad ta mike tsaye ta nufi dakin ammi tare da yiwa ammi alamar tazo tana shiga dakin ammi tashigo itama "ya'akayi ne mamana?


muryarta a shgwa'be tace " ammi wai meyasa likitan yake zuwa kullun?

"idan dani yake zuwa gsky ammi kice masa karya sake zuwa, kinga abdul yasamu labari ko yagansa za'a yi tashin hankali...

"meye dalilinki na cewa karya sake zuwa ko yace yana sonki ne?

su'ad tayi saurin girgiza kai "to me zuwan nasa zai tsara miki tunda bai ce yana sonki ba?

"zai fada ne ai ni dai ki gaya masa ina da aure kawai ya daina zuwa haka.

ammi tayi shiru tana kallon yadda take motsi baki tmkr mahaifinta magana ma sai anyi mata yanga ,tana maganar aure, auren da shi me auren bai san darajarsa ba gani irin kallon da ammi ke mata yasa ta jayewarta gado ta kwanta tare da lullube kanta cikin wanda duk sanda tayi haka ji take tmkr suna tare da abdul dinta ne aiko cikakken minti biyu batayi yakawo mata ziyara ta hanyar jin saukar hanunsa ajikinta tasoma mutsutsu ackin bargon bata sanda ammi ta fita ballantana wani doctor .

*byn wata biyu*

su'ad na kwance a gadon ammi ta lullube rabin jikinta suna hira da ammi eiman tashigo dakin sanye cikin riga da siket na atamfar super exclusive ta sha kwalliya sao kamshi take bazawa ta tsaya gaban mirrow ammi tana gyra zaman mayafin jikinta gefe daya kuma tana magana ammi akan musty yazo zata gurinsa ,tunda eiman tashigo dakin taji komai ya tsaya mata cak ... wani abu taji yazo ya tokare mata kirji kmr an d'aura mata dutse take kuma numfashinta yasoma kokarin tsayawa sakamakon kamshin turarenta datake cigaba da shaka da sauri ta kai hannuta ta toshe bakinta da hancinta, lokaci daya taji kanta yayi wani sarawa da karfi.
ammi dake zaune akan bedside ta waigo ta d'an dubeta tare da cewa "mamana lfy?

su'ad tashiga girgiza mata kai kawai tana wa eiman ala'mun ta fita ,ita kuma eima sam bata gane nufinta ba, sai sake matsota take yi, aikuwa tanagama karasowa taji kanta yasoma jujjuyawa daita take tasoma yunkurin kakarin amai ,ammi ta dafa kafard'ata tana kiran sunanta kafin kace me tuni har ta fara kwara amai .

"inna ilaihi wa inna ilaihi rajiun "me zangani kuma ni baraka daman bakida lafiya ne?

da kyar tasamu ta iya bude bakinta tace " am..mi tu.. tura. ren eim kafin takarasa mgnr sai wani aman ya taho tashiga kyalayawa akan gadon "nashiga uku eiman taimaka min na dagata muje bayi .

abayin ma amai ta dingayi wayyohhly Allah ammi cikina mutuwa zanyi eiman tayi kanta zata wanke mata baki tayi saurin dakatar daita kar..ki sai wani aman eiman ta dafe kirjinta" nashiga uku ammi turaren jikina ke sata amai fa bari nayi sauri na cire kayan jikina ta juya da sauri tabar bayi .
su'ad kuwa na faman kelaya amai,gbdy ammi ta rude ta dafa kafard'arta tana mata sannu babu kaukautawa tun tana iya yunkurin amai har tazo bata iya wa gbdy ta galabaita jikinta ya sake ammi ta jingina da kofar bayi tashiga zuba mata ruwa akanta da kyar ta janyo numfashi da ajiyar zuciya ta sauke, numfashi ta dinga saukewa sama sama idanunta gbdy sun canza launi ammi tashiga wanke mata baki tana sannu sannan takamota zuwa kan doguwar kujera ta kwantar daidai eiman ta sake dawowa dakin cikin sauri sanye da wasu kayan tashiga yi mata sannu kusan minti goma tana suna tsaye akanta suna jera mata sannu sannan ta amsa da kyar ta amsa "tace eiman ina kike samo wannan turaren haka me hawa kai tunda na shaka rasa abinda ke min dadi dan Allah karki kara amfani dashi .

eiman tace "ai tuni ma na mikewa kule shi yaje can yakara, jiya ne fa danaje siyayya addal mall din yaya nagansa naji kamshi yayi min dadi shine na d'auka bansa abinda zai jawo ba kenan .
ammi takarasa taje cire zanin gadon ta kai cikin washing machine ta dawo ta gyara inda tayi amain ta shimfid'a sabon zani gado ta dawo da su'ad ta zaunar daita tare da sanya mata pillow abayanta.

ahankali su'ad taji cikinta yana murdawa still zuciyarta na tashi take kuma miyo ya cika mata baki ta yunkura zata sauko daga kan gadon zaraf taji ammi ta meida ita "ina zaki?
tayiwa ammi nuni da bakinta "zauna bari na kawo miki guri ki zuba . eiman naji haka ta juya da sauri "ammi bari naje na d'auko kitchen taje ta d'auko robar ice cream ta dawo ta kawo mata ta zuba miyo ta koma ta kwanta tana sakin numfashin ammi tace "ko asamomiki goro ko wani abu kisa abakinki?
ta daga mata kai ala'mun eh still eiman ce ta sake fita ta aiki hannatu.

dare yayi kowa yayi bacci amman ita takasa runtsawa sai juyi take akan gado, ko sallar daren datake ma gbdy takasa tashi tayi ,ciwon ciki ya sakata gaba sai murkususu take tana kiran wayyohhhly Allah cikina mutuwa zanyi a zabure ammi tashi daga bacci datake tayi kanta tana mata sannu "sannu ciki kuma?

" yanzu yazamuyi ta duba agogo karfe biyu saura minti goma "cikinki ke ciwo? ta sake tmbyrta har ta dauko jakarta datake zuba magunguna ciki ,tasan baza'a rasa na ciwon ciki ko me ta tuna sai kuma ta fasa ta dawo ta rungumeta ajikinta tana shafa kanta zuwa bayanta can kuma tasoma kakarin amai kwana sukayi tana amai da ciwon ciki ,tun cikin daren ammi takira doctor saif aiko karfe biyar a gida tayi masa yakaraso kanta wanda zuwa lokacin tagama galabaita ta fita haiyacinta, ya zuba mata ido sosai kafin daga baya yasoma bata taimakon gaugauwa ya dan jima akanta yana duba lafiyarta sannan yace wa ammi "tana bukatar drip sakamakon aman data kwana tanayi.

cikin wasu mintina da basu wuce 20 da aka aki kule ba sai gashi ya dawo dr saif ya daura mata drip yayi mata allurar bacci cikin drip din sannan ya shiga tmbyr yadda ciwon ya faru ammi tashiga yi masa bayani tunda ga shigowar eiman har zuwa yanzu, inda take kan docto ya kulle shifa daman tun sanda akawo asibinsu wajen scanning yaga wani abu kmr gas a saman mahaifarta anya kuwa ba ciki gareta ba ya fadi haka cikin ransa ya jima tsaye a dakin yana kallonta sannan ya dibi jininta ya fita.
kai tsaye yana barin gidan hospital ya nufa ya jima cikin office dinsa yana dube dube da aune aunensa gabadaya hankalinsa a matukar tashe yake ya tattara natsuwarsa akan gwajin jinita sabani idan irin haka ya taso bashi ne ke yi ba akwai wad'anda keda alhakin haka. hankalisa yayi mugu mugun tashi ganin da gaske dai abinda yake zargi dai shine yagani amman sam yaki amincewa ransa cewar sakamakonta ne dan haka yanke sha'war azo daita.

mmn sudais ce


💗💗💗💗💗💗
SAI KA AURENI DOLE
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗



~NA~



*AYSHA A BAGUDO*



~DEDICATED TO~
HAUWA A USMAN
JIDDARH

YA WAHAB

THE GIVER OF ALL THING


page 75

.......batare da 'bata lokacin ba aka d'auki su'ad zuwa asibintin dr saif ,koda suka iso daita gbdy batasan inda kanta yake ba Spcial room ya bari aka kwantar daita sannan ya daura mata drip dan har lokacin bacci take bata farfado ba .
kusa daita yakarasa tare da janyo kujera ya zauna ya rungume hannuwansa duka akirji ya zuba mata ido sosai tamkar ranar ya fara ganinta bacci take hankali kwance sai dai kallo daya zaka mata kasan bata cikin natsuwarta, haka ya tasa gaba ya dinga kallonta ya kasa barinta yaje yayi abinda shine makasudin kawota.

kallonta yacigaba dayi saboda su'ad wata irin halitta ce agurinsa da bai ta'ba ganin irinta ba.
ba dan kyawunta ba daman skin dinta dole ya kasancewar hk kodan yanayin gidan data fito .

sabon gwaje gwaje yayi mata ya sake d'iban jininta wannan karon bashi yayi ba dan kar abun ya dinga maza gizo, hatta scaning sai daya sa aka mata.
tsakanin awa daya komai yayi ready a saman mekeken table dinsa.

gabansa ammi ce zaune gefenta kuma eiman ce tsaye umman su'ad kuwa tana waje dan gujewa kunnuwanta abinda zai d'aga mata hankali.


ahankali doctor saif ya dago fuskarsa tare da zare farin glass din dake manne da idanunsa byn yagama duba sakamakonta ya ajiye agefe tare da xuba tagumi da hannunsa daya ya tsurawa ammi ido na tsawon minti goma wanda zuwa lokacin gbdy hankalin ammi yagama tashi.

Tsawon lokaci ya d'auka yana duban ammi itama shi take kallo atsorace, yarasa meke damun zuciyarsa akan yarinyar jikinsa yayi mugu mugun sanyi a inda yake zaune gumi ne ke karyo masa takoina ajikinsa shifa yana sonta koda dama cikin jikinta gbdy zai iya aurenta koda kuwa cikin jikinta zai kasancen shrge ne .

wani irin kirma jikinsa keyi ,a marairaice yasoma magana cikin sanyin murya "ammi meye matsayin su'ad agurinki ?

bakinta na rawa tace "diyata ce halak malak sbd d'anuwana da muke uwa daya uba daya ne mahaifinta "meke damunta doctor idan akwai wani abu dan Allah kasanar min hankalinmu gabadaya a tashe yake.
ya lura su'ad din tamkar rayuwarta ce dama ahlin gidan gbdy .

ya numfasa sannan yace "ki kwantar da hankalinki ammi bawani abu bane sakamakonta ne ya tabbatar mana da tana dauke da ciki har na tsawon wata uku da yan kwanaki yakarasa mgnr yana jin gabansa na tsananta faduwa ya tsaya yaga reaction dinsu amman sai yaga sabanin hk .. .....

"alhamdullahi alhamdullahi !! abinda ammi ke fada kenan tana fafad'a murmushinta tana sake maimaita alhamdullahi, itama eiman farinciki take tare da rungumo ammi suka 'kwakume juna suna murna wanda hakan yasa numfashin dr saif kokarin barin gangar jikinsa ahanakali kuma kirjinsa yasoma bugawa eiman ta Kalli ammi tana murmushin jin dadi "ammi yaya zai yi d'an kansa bari naje nayiwa dady albashir ta nufi kofar fita da sauri.

gyra zamansa yayi tare cewa "yanaga Duk kuna murna ko daman tana da aure ne?

ammi tashiga daga masa kai sannan tace"tana da aure su'ad matar d'ana ce dana haifa.

a zabure yace "kikace me ?

"matar d'ana ce dana haifa "

"to ina shi mijin nata yake da duk wannan doguwar jinyar datayi bangansa ba ko sun rabu ne? ya fadi hk yana adduar Allah yasa sun rabu ne a zuciyarsa.

"a'a suna tare ya tafi wani aiki ne zuwa koria amman zuwa nest week muke sa ran dawowarsa ta fada masa haka ne dan rufa sirrin gidan d'anta .

sam bai yarda da zance ammi ba amman Bai san me zai sake cewa daita ba ,dan hk yayi shr tare da komawa ya jingina bayansa da jikin kujera dayake zaune ,ya runtse idanunsa yana jujjuyawa shi kad'ai yasan halin daya tsinci kanshi lokacin da ammi tace masa matar aure ce.

ahankali ammi takira sunansa "d'ana saifullahi meye damuwarka naga kashiga damuwa da jin su'ad na da aure ?

Bude idanunsa yayi ya saukesu akan fuskar ammi sai dataji tsoro sbd ganin yadda idanunsa suka dawo tmkr garwashin wuta muryarsa a raunane yace "bazan boye miki ba ammi sbd ina jinki tmkr uwa agarene ,"ammi na kamu da mutuwar son su'ad acikin kankanin lokaci wanda bansa dalilin dayasa Allah ya d'aura min soyayyarta haka ba ,amman babu komai zan bawa xuciyata hakuri yakarasa maganar yana goge idanunsa da yatsu biyu.

jikin ammi yayi mugun sanyi sbd yabata tausayi muryata a sanyaye tace "almarin Allah kenan sannan kayi tinani dakace zaka sanyawa zuciyarka hakuri ,ina maka fatan Allah yabaka mace wace tafita zama alkhari agareka "ameen nagode sosai .

ammi tacigaba da mgn "ala hakikanin gsky da kace su'ad sun rabu da mijinta wallahi zan iya tsaya maka ka aureta ba dan komai ba sai dan kaima kana da nagartar daza'a baka aure duk da bansan tushenka ba.
,"da kuma ba'ayiwa eiman miji ba dana tsaya anbaka ita dr saif yayi murmushin karfin hali wanda yafi kuka ciwo kana yace "na gode kwarai da kaunarki gareni allah yabar girma .

Ammi ta amsa da "Ameen Allah yayi muku albarka yasa kayita samun nasara asha'anin aikin ka, sannan ta yunkura ta mike cike da tausaya masa gefe daya kuma tana cike da murna samun jikan dazatayi ta bar office din.

ta barshi zaune tamkar wanda ya mutu alhalin yana raye , fitarsu ke wuya ya zabura ya mike yashiga buga table din gabansa yana zagaye office yana jin kamar ya d'aura hannunsa duk a bisa kai ya rusa ihu ne, yanzu shi yaya zaiyi da tarin soyayyarta? Hakuri. Zuciyarsa tabashi amsa da haka .

bashi yasamu natsuwar zuciya ba har sai daya dangana da gida addua yayi tayi a game da lamarin soyayyarsa da su'ad, ya dawo asibiti guraren 4 lokacin har ta tashi ammi ta taimakamata tayi wanka tana kwanciya yashigo ya jima tsaye jikin kofar dakin yana kallonta gbdy hankalinsa kacukan ya daurasa ne akanta bai taganin halitar data tafi da zuciyarsa da hankalinsa kmr ta ba, har yagama tsayuwarsa bata juyo ba duk da taji ajikinta shine yashigo dakin.

Kwananta daya a hospital aka sallamota suka dawo gida ,kmr kar labarin cikin ya bayyana shikenan laulayi ya tashi zangazanga komai taci sai ta amayar dashi ga xubar da miyo gbdy lokaci daya ta sake ramewa ,dan haka kusan duk

3 Comments On SAI KA AURENI DOLE
avatar
zainab-ishaq

1 year ago

Reply

Love it ????????

avatar
zainab-ishaq

1 year ago

Reply

Yes and I want to download it

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to zainab-ishaq

In order to download you have to subscribe for our package at https://tnovels.com.ng/subscribe

Please Login or Register in order to submit comment