Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

idan kin damu kisan abinda tayi kina iya biyo mu office dinmu daga baya sai ki san abinda tayi.

"yanzu dai ta wuce muje su'ad tasoma kokarin zare hannuta cikin na ummanta amman umma ta rike hannuta gam tana kuka wiwi tmkr ranta zai fita tana basu hkr karsu tafi mata da yarinya ...

dayan police din "yace karki damu hjy da zarar mun gaba bincikenmu akanta muka tabbatar da bata da hannu ciki abinda muke zarginta zamu dawo miki daita har gida cikin koshin lfy .

hk umma naji tana gani aka tasa ketar su'ad gaba zuwa byn motar police suka bar gurin sai police station. itama take tabi bayansu.

suna isa umman su'ad na fitowa acikin adaidaita wanda kusan tare suka iso ,akayi upstairs daita police zagaye daita xuwa wani daki ita km umma tasamu guri ta tsaya jugun tana kuka.

ahankali aka soma yiwa su'ad tmbayoyi abinda ya dangaci rayuwarta ita km tana basu amsa daki daki hankalinta akwance tmkr wace bata cikin damuwa, har zuwa kan batan zeey kai tsaye batare da wata fargaba ba ko tsoro ta bayyanawa police zeey na hannuta ,wanda hkn yasa aka nufi office din commissioner daita .
yace kar a kuskura ata lafiyar jikinta suje daita inda ta boye zeey sannan idan sun dauko zeey, su dawo masa da su'ad akwai tmbayoyin da zai mata.

gaba police suka tasa su'da har bariga inda su ore ke tsare da Zeey suna gana mata azaba suna karasawa gurin sukayi sorrounding din gurin suka shiga harbe harbe dan su tashi hankalinsu ore.

******
shi kuwa AK koda yashigo part din dady ya iske hjy mahaifiyar dady'nsa da maman zeey sai ammi dake tsaye goye da hannuwanta duka abaya tana sintiri wanda yake nuna ala'mun tafisu shiga tashin hankali.
"bakinsa dauke da sallama yakarasa shigowa cikin parlour'n sosai zuwa inda dady yake zaune yana shan coffe hankalinsa kwance har abun yaso bashi haushi ,wato ma shi dady bai damu da abinda yake faruwa ba.

"dady ya karba masa sallamarsa fuskarsa a daure yacigaba da kurba coffe dinsa .
ahankali AK ya bude bakinsa ya gaida dady da sauran mutanen dake zaune agurin.

"cikin dakewa dady ya kar'ba masa tare da cewa masa ya ake ciki da zance masu bincike akan 'batan zainab?
sai daya sauke naunauyen ajiyar zuciya sannan "yace police na kan aikinsu yanzu hk nasan sun isa gidan su yarinyar nan....

shr ne ya dan ratsa parlour'n can dady ya ajiye cup din coffe dake hannusa ya waigo tsaitin da AK yake zaune yana dubansa sannan yace ina fatan basawa kayi ayi arest dinta ba?
ya jefa masa tmbyr ransa abace.

tun kafin AK yace wani abu ammi "tayi saurin cewa dan girman allah dady meyasa kake irin hk?

"meyasa kafi son tantiriyar yarinyar nan akan jininka ?

ranta a bace ta maida idanunta kan AK ta tsura masa idanunta "karkayi sanya akan daukar hukunci akan duk me hannu acikin batan zainab .

"hjy tace shine abinda ya dace ita yarinyar da ake zargi wacece ita?

" waye ubanta agarin nan da zaka dinga daure mata gindi ?
"ko dole ne sai jikana ya aureta nace dole ne sai aureta, kai adamu hjy takira sunansa kafi idona tun wuri wlh banason jin ka sake cewa komai akan mgnr nan matsawar ba goyon baya zaka bamu.

"cike da sanyi murya dady yace hjy kiyi hkr amman ni nasan abinda nakeyi , shiyasa nace abi lamarin nan ahankali ita kanta baraka ta kasa fahimtata ne kawai amman zanyi kmr yadda kikace din .

"da dai yafiye maka muhawara ce ta barke tsakaninsu ta yadda za'a yi,cikin hk kiran police yashigo wayar ak ,yana dauka suka sanar masa da sun gano inda zeey take yanzu hk suna tare da su'ad din domin ta su shiga inda ta boyeta ,AK ya zabura ya mike tsaye yana cigaba da receive din cal ,yana duban iyayensa dake zaune tsuru tsuru sannan "yace ok idan anga zeey din kuzo min daita gida kai tsaye ita km yarinyar da gang dinta ayi aresting dinsu ok sir.

hmmmm...! dady ya sake naunayen ajiyar zuciya tare da numfasawa sannan ya fara mgn "hakika abdulkabir kana son biyewa son ran mahaifiyarka domin sake aikata babban kuskuren, wanda ita kanta zata iya shiga matsala daga baya.
kuskuren da suka tafka a baya nake gudar mata sake faruwarsa ,amman taki fahimatata ,ke kanki hjy da ke ma, ya nuna maman zeey babu abinda bakusani ba ni kaina bawai ina bawa abdulkabir goyon bayan auren yarinyar bane dole, abinda zai je ya dawo din nake gudun afkuwarsa, amman babu komai tashi kaje.

uhm dady ka daina kokarin hada yarona da maseefun da suka faru abaya da yarda allah babu abinda zai sameshi sai alkhari km muddin ina raye...... datse harshenta tayi da sauri sbd wani irin kallo da dady ya wurgama sannan yace "ki karasa man ai kinsan illar abinda hkn ya jawo wanda daga baya nadama ce zalla mara amfani.
dady naga fadar hk yayi daidai da jiniyar police ya karade unguwar suka karaso gidan.
gbdynsu suka mike tsaye sukayi waje ranga ranga AK yaga an fito da zeey dinsa rai hannun Allah rege regen karasawa gareta suke gbdynsu, yayinda mutane dake cikin part din ammi dana baki suka firfito harabar gidan.

cikin sauri AK ya isa gareta yana fadin "zeey me suka miki, ina ke miki ciwo ?

gbdy AK ya rude sai jera mata tmbayoyin yakeyi ya ma rasa me yakamata ya farayi mata zeey kuwa cikin tamboyinsa babu wanda ta samu damar amsawa illa wani irin nishi da take fiddawa da sallati samakon jin jiki datayi dan bakaramar azaba taci agurinsu ore ba.
ga babu ci babu sha a kwana dayan datayi agurinsu babu irin azabar da basu gana mata ba. gani irin juyi datake tana rike ciki ai ak bai san sanda ya mike cikin gigicwa ya nufi dakinsa a guje dan dauko makulin .

dube dube yake yi cikin dakin nashi yama rasa inda key din yake dan gbdy a rude yake.
can ya hangoshi saman mirrow da sauri ya dauko ya fito dakin ya dawo da gudu inda jama'a ke tsaye cirkocirko suna kuka ita km zeey sai murkususu take ajikin ammi tana rike ciki da sauri yakaraso ya amsheta daidai lokacin da numfashinta ya dauke cak ...
durkursawa yayi kasa yana kiran sunanta zainab... Zainab.... tare taba kumatunta amman ina babu numfashi atare daita dangi suka taru akansa suna kuka tare da tmbyr ta mutuko?
hk ma police din dake tsaye sukayi kansu suna kallonta take suka gane suma tayi ,daman tunda suka dauko a sume take sai da suka yayyafa mata ruwa ta farka sun so wucewa hospital daita amman jin yace suzo masa daita yasa, hada baki police sukayi gurin cewa suma tayi ba mutuwa tayi ba.
ai AK najin hk daukarta yayi da sauri, ammi na masa mgnr yabi ahankali ya tsaya wani ya tukasu amman ina hankalinsa kwata kwata baya jikinsa dan ko jinta bai yi, inda motarsa ke pake ya nufa , yakarsa ya bude kofar baya ya kwantar daita aunty bilkisu kanwar mahaifin zeey da aunty malika suka shiga motar hankalinsu a tashe shima cikin hanzari ya zagaya yashiga mazaunin direba , me gadin na ganin hk yayi saurin wangeme masa get din gidan.
aguje AK ya fige motar kai tsaye asibitinsu ya nufa daita.
likitoci suka amsheta cikin gaugauwa suka nufi imagecy room daita tsawon lokaci suna kanta suna kokarin dawo da numfashinta .

zeey kuwa sai farkawa tayi ta ganta a gadon hospital, ta fahimci hkn ne ta hanyar ganin wata nurse a tsaye akanta ,dan tana bude idonta daita ta fara cin karo.
tana kokarin sanya mata karin ruwa tayi saurin hanzarin mikewa zaune tana rarraba ido tare da tunanin abinda daya haddasa mata zuwa hospital, aunty bilki ce takaraso gareta jikinta a matukar sanyaye sai dai kallo daya tayi mata abinda ya faru yashiga dawowa cikin kwanyarta, idanunta kmr gauta al'amar taci uwar wahalar da kuka ta koshi, km har lokacin kuka take.

ta rike cikinta tana murkususu yunwa ga makoshinta ya bushe, nurse tasoma yunkurin rike hannuta zeey ta fizge hannuta daga rikon da nurse tayi mata ta kamkame jikinta waje daya tana mgn ahankali "wayyohhly Allah mutuwa zanyi yunwa nake ji kubani abinci naci sabatun yunwa take amman babu wanda yaji sbd muryarta a dace take.
sai km tayi luuu! ta zame kan gadon ta sume daga aunty bilki har nurse suka gigice har aka rasa wanda zaiyi wani abu akai .
aunty bilki tayo kanta tana girgizata cike da matsanancin tashin hankali da kiran sunanta cikin karaji, yayinda kukan datake rikewa tun dazu ya kwace mata.
ita kuwa nurse da gudu ta fice daga dakin zuwa kiran doctor atare suka dawo dakin da doctor a wannan karon har da ammi da maman zeey da AK suka biyo bayansu.

da likita da nures suka shiga yayyafa mata ruwa ai kuwa ta bude idaunta tare da sakin wata ajiyar zuciya ahankali danunta ya dauro akan AK dake tsaye kusa daita hannunta cikin nasa ,yayinda fuskarsa take tattare cikin yanayin na rudani. doctor naga dubata ya juya tare da cewa yana son ganin ak zuwa office dinsa.

koda daya shiga office din likinta, kujerar dake facing ta likitan yaja ya zauna suna fuskantar juna yana tmbyrsa meye matsalar zeey ,ahankali doctor yasoma bayani atsanake.

" bata tare da wata matsala byn raunukan dake jikinta sai km yunwa dake dawainiya daita, amman ka kwantar da hankalinka Inshaallahu zata samu sauki zamuyi duk abinda yakamata,amman yanzu a hanzarta kawo mata abinci da ruwan zafi.
AK ya mike tsaye tare da cewa " yanzu kuwa za'a kawo mata yayi sallami da doctor tare da kiran aunty bilki ya damka mata wasu kudi a hannunta koda za'a bukaci wani abu sannan yagayawa ammi abinda ake bukata, tare da ammi da aunty malika suka baro hospital din ya saukesu agida shi km ya wuce xuwa police station.

kai tsaye office din commissionier ya zarce yana cika yana batsewa yana shiga ya iske su'ad tsaye tare da commission suna zantawa a tsakaninsu shi kuwa AK ko kallon inda take tsaye baiyi ba yasamu guri ya zauna yana watsa mata kallon baza, itama abanzace take kallonsa kmr yadda yake aiko mata da nashi kallo zuciyarta na tafasa. rainshi yayi maseefar baci ganin kallon banza da take masa.

" hkn yasa bai san sanda yace dan ubanki ni kikewa wannan banza kallo?
dakata mlm ta katseshi tare da daga masa hannu karka sake zagin ubana idan kai baka san ciwon naka uban ba ,ni nasan ciwon nawa takarasa mgnr tana harararsa...
" ance ubanki waye shi uban naki da baza'a zageshi ba ?
"kai ma dan uban...atsawace ya dakatar daita ta hanyar daga hannunsa zai zabga mata Mari ,yaji sautin wata muryar ta doki dodon kunnensa daga bayansa kar ka sake ka fara taba lafiyarta, karkayi kuskuren aikata hk domin ba yarda zanyi da hkn ba ..ahankali ya sauke hannuna yayi saurin waiwayowa ahankali yaga kowaye ya katse masa hanzari .

wata kyakkyawar mata yagani zaune tana kallonsa a wulakance, matsowa yayi sosai ya tsaya agaban umman yana kallonta tsab ,kawai rasa abinyi AK yayi sbd yadda yaga fuskar matar har lokacin tana watsa masa matsiyacin kallo sannan tana cikin wani yanayi daya kasa fassarawa, ko daganin hk sai shima ya xuba mata ido kmr yadda tayi masa yana kallonta sai daya gama kallonta tsab

" muryarsa a fusace yace wace ke....?

"sannan me ruwanki da marin da zan mata da har zaki dakatar dani ?

da ruwana sbd nice nan na kawota duniya tayi mgnr tana nuna kanta kakiye dan ban haifi jaka ba balle ka mayar min da "ya" abin wulakantawa ta bashi amsa da hk.

"ohh kice kece uwar wannan tantiriya shugaban yan jagaliyar data addabi al'umma?
ya juyo inda su'ad ke tsaye yana kallonta atsiyace lallai kin cika uwa aike ba uwa yakama akiraki ba.... dau.. yaji saukar wani gigitaccen mari a fuskarsa wanda yasashi yin shock atsaye tare da zaro idanunsa a matukar tsorace yana kallonta eye's to eye's ita ce maresa ko km wani ne da ban? yayiwa kansa tmbyr acikin zuciyarsa .

"tsaki ta ja tana kallon kwaryar idanunsa kul.. ka iya bakinka kasan me zaka gayawa mahaifiyata ita din ba kmr kowace uwa bace, ina sonta fiyye da komai, ina girmamata km ina son a girmama min ita duk rashin mutuncina bazan kalli tsabar idanun uwarka nace zan zageta dan hk kasan abinda za fada mata....
hannusa ya daga a zafafafe zai zabga mata mari tayi saurin dukawa kasa tare da matsawa baya,aiko ya dauketa da kafafunsa tayi sama ta dawo kasa tim ..yashiga dukanta , umma naganin hk tashiga kururuwa tare matsowa ta rike hannunsa gam tana yiwa commissionier nuni da idan yayi diyarta illa bazata yarda ba... ..


a wulakance AK "yace ki sakar min hannu tun ban hada dake ba yanzu bazan saki hannuka ba sai ka sakar min "ya" tunda ba jakar ubanka bace take office din commissionier ya hargitse da hayaniyarsu har sai da wasu police guda biyu suka shigo suka shiga tsakanin AK da su'ad datake rike a hannunsa ,da kyar commission yasamu ya shawo kansa ya hakura ya zauna yana huci dan cewa yayi sai ya mata illar da har ta mutu ba zata manta dashi ba ...

shi kansa commission ya dade baiga mace me taurin zuciya irin su'ad ba, ya sallemi umma yace ta wuce gida zai nemata .
"bazani koina ba commission duk abinda za'a yi ayishi agaban idona ,yarinyata tayi laifi km ta amsa laifinta har ta bayyana inda yarinyar take an daukota "me zai hana abani beling diyata na wuce gida daita?
"idan km zamu shiga koto ne to?

"duk mgnr bai kai ga hk ba amman yanzu zamu so musan sbd me su'ad din ta sace amaryarsa aranar kamunta sannan musan abinda yasa take bibiyar wannan yaron?

"ni nasan halin yarinyata hk kawai babu wani dalili bazata dinga bibiyarsa ba ,kai dai tmbyi shi wannan mara kunyar ko akwai abinda yayi mata..

karki fada hk domin idan kikace hk ya nuna ala'mun kina bin goyon bayan diyarki da daure mata gindin yin duk abinda tagadama which's bad..

"ga ta nan agabanka ka tmbyeta tunda nake da su'ad ban taba cewa ta aikata mugayen ayyuka ba, kullun fada da addua nake mata, duk uwar arxiki bazata so diyarta ta dinga abinda su'ad takeyi ba ,nasan bata da gsky acikin lamarin amman tunda ta amsa laifinta ai ina ganin komai zaizo da sauki tunda ko koto akaje alkali zaiyi saurin zartar mata da hukucin da yadace .

"ok yanzu dai kije gida domin musamu muyi binciken dayakamata akan aikinmu kina kallo tun awa uku nake fama daita amman taki bani hadin kai.

babu inda zani commission zan dai tsaya a kasa najira har lokacin da zaku gama sannan matsawar wannan dake huci kmr maciji ya illata min yarinya zan shigar da kara koto .

"reacting dinsu irin daya banbacin kadan ita uwar batayi kama da yar ba sannan yanayinsu ba daya bane inji commission wanda yayi mgnr cikin ranshi.
"ok kije waje kijiramu ,umma ta nufi kofar fita tare da budewa ta fice.

commissionier ya numfasawa yana kallon AK dake huci kmr kumarcin maciji sannan ya kalli su'ad dake girgiza jikinta ya nuna mata kujera da hannunsa ala'mun ta zauna kusa da AK .

"karka damu ranka ya dade barni a hk kawai AK ya kallota a kaskance yana jan tsaki da karfi dan har ranshi yasoma tafasa akan yadda commission yayi mata .

tsakin daya ja yasa su'ad sakar masa harara tare da cewa kallon km fa?

ak yayi mata banza dan bai ga abin bata bakinsa wajen bawa amsa ba,

shi kuwa commission bai damu da jin abinda tace ba yasoma mgn kmr hk muna son ki sanar mana ko akwai wani abu dake tsakaninki da abdulkabir wanda yasa kike bibiyarsa duk inda yaje, akaro na karshe..

sannan meye hujarki na sato masa amaryarsa aranar kamunta?

murmushi mugunta su'ad tayi tana duban commission a kyakyace sannan tace babu komai ranka ya dade...

"karya kike ina jin ba wannan ne Karo na farko da abdulkabir ke kawoki gurinmu akan matsalar kina takurawa rayuwarsa ba dan hk karki kuskura kice mana babu komai domin wannan karon ina tabbatar miki ko shi bai dauki mataki akanki ba hukuma zata dauki mataki da hannuta ,dan hk tun wuri ina umartarki ki sanar mana da gskyr lamari ,sai mu sakeki salin alin batare da an taba lfyr jikinki ba.

amsar data bashi da farko ita din ta sake gaya masa wato babu komai ,yayi juyin duniya daita akan tasanar masa amman taki ta tsaya akan babu komai har suka shiga exchange word da commission yayinda AK yazama dan kallo agurin cike da mamaki.

commission ya rasa ta ina zai bullo mata yayi nasara akanta shr yayi kawai yana kallonta can km wani idea yazo masa.

yayi saurin gyara zamansa "yace idan baki gaya mana gskyar lamarin abinda yasa kike bibiyar abdulkabir ba zamu tsareki tare da mahaifiyarki har sai mun gama bincikenmu akanki .
"a wani dalili? ta tmbyeshi "naga a dokar kasa babu dokar data bada wannan damar tsare wani akan wani ya aikata laifi ,nice nan nayi laifi ni yakamata ku tsare ba mahaifiyata ba sbd ita bata muku komai ba.

"za'a soma wannan dokar akanki matsawar baki gaya mana gsky ba.
,duk inda ran AK yake yayi matukar baci, da iskancin yarinyar . commission ya dubeshi abdulkabir ko zaka iya tuna ko wani abu ya taba shiga tsakaninka daita ko ta cacar baki ne?

AK ya dago idanunsa dake cike da tsantsar bacin rai ya zubawa commission yana kallonsa, sannan ya bude bakinsa da kyar "me zai shiga tsakanina da wannan yar iskar yarinya wallahi ina tabbatar maka ko hanya ban taba hadawa daita ba idan ba'a dan wannan lokacin ba....
commission ya dauki waya yasoma daddanawa , can aka dauka "yace asp ganiyu,yakira sunan yana jujjuya kujerar dayake kai zaune "bangare asp ganiyu kuwa kamewa yayi sosai tare da cewa yes sir..
" matar data fito daga office dina yanzu ku tsareta ku kaita cell dan... ai su'ad najin hk ta birkice tasoma kuka muryarta na craking tace pls commission kar saka mahaifiyata cikin cell bata cancanci shiga cell ba ,ita din me daraja ce ba kmr sauran iyaye ba.
"tunda baki son asaka mahaifiyarki cikin cell why not ki gaya mana gsky "akwai matsalar ne commission........
" ita gskyr da kake bukatar sani akwai matsala akanta idan na fadeta .
"dan girman allah commission kar ka bari na fadi ita wannan gskyr fadar abinda ke tsakanina da abdulkabir daidai yake da fadawata cikin halaka ...

"kenan dai akwai wata a kasa kenan ?

"AK dake zaune yace ka daina wani lallabata daday dan nasan babu wani abinda na taba yi mata arayuwata.
" kawai dai tsabar iskanci ne irin nata .

"aiko yau zata ga karshen iskancin daya fi nata matsawar bata fadi gsky ba.
yakarasa mgnr tare da cewa kai asp ganiyu ka aiwatar da abinda nasaka kawai, dan har lokacin yana kan layi.

"jikin su'ad na rawa tace zan fada commission.... "zan fada da dai a saka min uwa cikin cell na gwamaci na fadi koma meye tsakanina dashi idan yaso duk abinda zai sameni na yarda yasameni, takarasa mgnr tana kuka wiwi.
ta juyawa musu bayanta ahankali tare da hade hannuwanta duka waje daya ta rufe fuskarta hawaye nabin kuncinta...... commission ya dakatar da asp ganiyu sannan ya fuskance da kyau.

"uhm muna jinki ?

ta juyo ahankali tana kallonsa kawai wasu sabbin hawayen na sake gangaro mata, sannan ta bude bakin da kyar zan tasoma mgn "zangayi komai dake tsakanina da abdulkabir wanda yasa nake ikirarin sai ya aureno dole da bibiyar duk inda yaje amman sai agaban iyayensa da mahaifiyata.........




mmn sudais ce

💗💗💗💗💗💗
SAI KA AURENI DOLE
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗



~NA~



*AYSHA A BAGUDO*



~DEDICATED TO~
HAUWA A USMAN
JIDDARH


*bissimillahir rahmanir rahim*

*hasbunallahu wani'imal wakil*

page 48

yadda suke kallonta cike da matsanancin mamaki sbd da furucin datayi, hk itama take binsu da kallo daya byn daya most especial AK dake zaune wanda gbdy ya tattara hankalinsa kacukan akanta byn ya tsareta da mayatatun idanunsa yana kallonta.
wani birkitaccen yanayi ya shiga kafin daga baya ya dawo cikin haiyacinsa ya sake ware idanunsa sosai akanta bakinsa mgn yake son yi amman ya kasa sarrafa harshensa.... .

ita kuwa wani bakinciki ne ya tokare mata kahon zuciyarta wanda yasa hawayen idanunta tsananta gangarowa bisa kuncinta .
"batason bayyana wannan sirri dake tsakaninta da abdulkabir, wanda yake daidai da tarwatsa rayuwarta a karo na biyu matsawar tayi kuskuren fadarsa . amman babu yadda zatayi da rayuwarta ya zamemata dole ta bayyana wannan sirri kodan martabar mahaifiyarta .

tayi hkr ta jurewa kaddararta data samar daita balle wannan damuwar......tayi imani duk abinda ke tafe da shafukan rayuwarta daga Allah ne.
tayi mgbr imani da hukuncisa gareta tare da yarda da kaddararta me kyau ko akasin hk .
abubuwan dake faruwa daita kaddara ce wace bata isa ta canzawa kanta ba.
commission dake zaune ya sake gyara zamansa lokacin dayake jin wani irin tausayin yarinyar yana bin Jinin jikinsa.
ya tabbatarwa kanshi tabbas akwai wani sirrin boye dake tsakaninta da abdulkabir.......adduarsa Allah yasa ba abinda yake tunani bane ya taba shiga tsakaninsu....

muryarsa ahankali ta fito gurin cewa "ki natsu ki dawo cikin haiyacinki nima tmkr mahaifin abdulkabir ne duk abinda kika san yana tsakaninki dashi ki sanar min dan ina tabbatar miki tmkr yaje kunen mahaifinsa ne.
dan hk karkiji komai zaki iya sanar dani komai .
girgiza kanta tashigayi tana kuka wiwi tare da daura hannuwanta duka bisa kanta alamun tana cikin tashin hankali sannan muryarta cike da kuka tace "kmr mmahaifi kace ,kmr mahaifi kuwa bazai taba zama mahaifi ba, dan hk ka kirasu zuwa nan kawai, ko muje gidansu tunda na rigada na amince zan fadi komai ......takarasa mgnr tana sake sakin wani Sabon kuka me taba zuciya sbd tuna makomarta da zarar ta bayana komai dake tsakaninsu.

juyin duniya commission yayi daita akan tasanar masa amman fafur taki tace zatayi mgn amman sai agaban iyayensa ,dan hk ran ak yayi matukar baci ya zabura ya mike tsaye ilahirin jikinsa na kirrma ya damki hannunta cikin nasa cikin matsanancin fushi yasoma janta commmission na masa mgn ,yayi banza dashi ya nufi kofar fita daita, kafin commission ya ankare tuni har ya fice daga office din.
janta yake tana biye dashi abaya tana kuka kmr ranta zai fita har ya iso farfajiyar police station , kai tsaye inda yayi parking din motarsa ya nufa daita ya bude mata gaban mota ya watsata ciki ya Rufe murfin motar da Karfi ya zagaya yashiga mazaunin direba ya tayar a fusace.

tun daga nesa umman su'ad ta hango yadda AK ya sauko daga saman commmission janye da hannun su'ad yana janta har ya sata cikin motarsa.
cike da matsanancin tashin hankali tasoma kokarin cima masa amman ina har ya tada motarsa, dan hk ta kurma ihu da kururuwa neman dauki tare da daura hannuta saman kanta tana kuka daidai lokacin da commission yakarasa saukowa yace ta bar kuka tabiyo bayansa suje.

tunda ya fita daga harabar police station din ya figi motar a guje duk wanda yaga irin gudun dayake dole ya bishi da kallo, wani irin gudu yake falfalawa akan titi na fitar hankali har suka iso unguwarsu bai ce mata komai ba itama hk batayi yunkurin cewa wani abu ba bayan sheshekar kukanta daya tsananta karfi ,yayinda AK yashiga tunani yadda zata kasance

3 Comments On SAI KA AURENI DOLE
avatar
zainab-ishaq

1 year ago

Reply

Love it ????????

avatar
zainab-ishaq

1 year ago

Reply

Yes and I want to download it

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to zainab-ishaq

In order to download you have to subscribe for our package at https://tnovels.com.ng/subscribe

Please Login or Register in order to submit comment