Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tana bubuga kafafunta, tallafa kanshi yayi cikin wani irin yanayi wanda bai san ina tsaye ina kallonsa ba.

ni km alokacin babu abinda ya shagaltar dani kmr yadda tsarinsa yake da km yadda yake mgn yasoma takowa ahankali yarinyar na biye dashi tana masa kukan shagwaba daidai inda nake tsaye yaja birki agabana ya tsaya kamshin turarensa ya bugi hancina take na runtse idanuna zuciyata na tsananta bugawa sautin muryarsa naji "banson wulakanci ni zaki biyo kina wani kukan shagwaba ? jira ranar da zan sake kawo miki ziyara lokacin daya ya juyo da zumar cigaba da tafiya numfashinsa ya bugi fuskata nayi saurin ja da baya, shi km yasoma daga kafafunsa cikin sanyi jiki .
yarinyar na binsa abaya tana bashi hkr na daina yaya "to idan ban maka shagwaba ba wa zanwa?
"ni kadai ce yar'uwar da Allah yabaka , nima kai kadai ne yayana biye take dashi tana masa mgn cikin sigar shagwaba .
ni kuwa banda kallonsu babu abinda nake yayinda mk wanda ya jingina bayansa da bishiya hannuwansa duka rungume akirjinsa ya masefar ka feni da idonsa yana kallona, km duk abinda ke faruwa akan idanunshi ne .
wucewa yayi lokacin da muka hada ido dashi ya hango tsantsar tsanarsa kwance acikin idanuna. yana barin gurin naji sautin muryar yarinyar "yaya na kaina nagode sosai ka gaida mutanen gidan kace nayi missing dinsu duka ni zan koma hostel.
to princess anan zaki barni kenan?
kayi hkr test zamu yi gobe ,ok Allah ya bada sa'a tace ameen tare da juyowa tazo ta wuceni tsaye, shi km yasoma kokarin karasowa inda yayi parking din motarsa.
"ahankali nima nasoma tafiya ina kallon bayansa har sanda naga ya tura hannunsa cikin aljihun wandonsa ya ciro key' din motarsa ya tura jikin motar yana kokarin budewa sai ga yarinyar dazu ta dawo da gudu tana kiran sunansa yaya.. yaya.. ...juyowar nan da zai yi.....



mmn sudais ce

💗💗💗💗💗💗
SAI KA AURENI DOLE
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗



~NA~



*AYSHA A BAGUDO*



~DEDICATED TO~
HAUWA A USMAN

*bissimillahir rahmanir rahim*

*hasbunallahu wa ni'imal wakil*

page 50

juyowan nan da zai sai dimmmmm naga mutumin yayi wata irin faduwa kasa, yasoma shure shure da kafafuwansa jikinsa na wani irin rawa tmkr mazari, kunfa na fita a bakinsa yayinda gbdy idanunsa sun kakkafe ko bakin cikinsu ba'a gani.

yarinyar takaraso da gudu inda yake kwance yana shure shure cikin rawa jiki tasoma furta inna lillahi wa inna ilaihi rajiun.
kafin kace me mutane sun zagayeshi kowa na fadar albarkacin bakinsa akan ciwonsa, yarinyar ta tsunguna gabansa cikin wani irin kuka zata kai hannuwanta duka zuwa jikinsa.
wani matashin saurayi dake tsaye kusa dani yayi hanzarin dakatar daita ta hanyar cewa karki soma kai hannuki jikinsa wannan ai mugun ciwo ne ,ba'a kusantar me irin ciwon ko tsallaka inda ciwon ya tashi.
cike da matsanancin tashin hankali yarinyar "tace yayana ne fa uwarmu daya ubanmu dashi da zakace kar nata ta'bashi ....
kuka take sosai tana kiran "pls yaya ka tashi jama'a ku taimaka min dan Allah "ku kama min shi mushigar dashi cikin mota takarasa mgnr tana kallon mutane dake tsaye makil akanta ita da yayanta dake kwance yana share share da kafafunsa, kumfar na fita daga bakinsa tana gogewa wasu na sake dalalowa .

ni kuwa na tsinci kaina tashin hankali mara misaltuwa, iya firgita iya tsorata na tsorata ,ganin abinda ke fita daga bakinsa ,wannan shine Karo na farko dana taba ganin abu makamanci hk.
yayinda duk tarin mutane da cike makil zagaye dashi babu wanda yasoma kokarin kusantar inda yake, sai surutai suke zubawa tare da mgnr ciwon.

"ni kuwa zuwa lokacin bana iya hangosa sbd yawon mutane da sukayi dandazo agurin,
cikin maganganinsu ne na tsinci wani dattijo dake tsaye tare da wata yarinya wace muke depertment daya daita, yana cewa ai wannan kafurtaccen ciwo ne wanda baya tashi tozarta mutun sai cikin jama'a ga da tsoratarwa, wanda samun maganinsa ke da wuya a wannan lokaci, amman idan akayi dace akan samun maganinsa a wani kauye dake cikin idiroko .
jikina har lokacin rawa rawa yake tsabar tashin hankali ,lallai wannan ciwo yaci sunansa kafurtaccen ciwo me tozartar da mutun a bayyanan nasi ,tare da tsoratarwa nayi mgnr cikin zuciyata, ni kaina son karasawa inda yake kwance nake son yi amman tsoro da fargaba ciwon nake ji har cikin zuciyata ga km wani tausayin gayen dake ratsa kowani shashi na gangar jikina,wani irin tausayinsa nakeji yana taso min wanda bansa ni kaina dashi ba .

zuciyata da gangar jikina ban rawa babu abinda suke tunda nake banrtaba ganin irin ciwon ba, ciwo makamancinsa ma ban taba gani ba ,duk surutan da mutanen gurin keyi yana shiga cikin kunena daram, ganin duk yawan mutane dake gurin maza da mata babu wanda yayi kokarin taimakawa yarinyar, da ala'mun kowa najin tsoro kamuwa da ciwon ne yasa suka kasa taimaka mata.

cike da sanyi jiki nasoma daga kafafona ina ratsa mutane domin kokarin son isa inda yake, nesa kadan dashi naja na tsaya na kasa nakarasawa, amman ina hango yanayin dayake ciki ,hankalina yayi mugu mugun tashi sbd ni da yarinyar kadai bazamu iya taimaka masa ba.

matsowa nayi sosai kirjina na wani irin harbawa da sauri sauri,
koda na isa nakarasa na tsaya akan gayen, take na tsinci kaina cikin wannan yanayin nadaban tabbas nayi matukar razana dan gane da ciwonsa , dan hk wayata na daga na kira ore aminyata nace dan Allah ta taimaka ta turo min gayun unguwarsu dake zaman banza "nakara da sanar daita abinda ke faruwa nace dan Allah suzo yanzu ko nawane zan biyasu su taimaka min.

bayan zuwan yan jagaliyar unguwarsu ore suka taimaka mana nida yarinyar aka daukeshi zuwa cikin motarsa, aka kwantar dashi abayan motar ,yarinyar tashiga gaban motar ni km na sallami yan jagaliyar, nashiga gidan baya inda yake kwance jikina na rawa na daga kansa na daura bisa cinyoyina, yarinyar taja motar aguje muka bar gurin, ahankali na cire dankwalin kaina nashiga goge masa fuska zuwa bakinsa da kunfa ke dalala har wannan lokacin .
tun cikin mota yarinyar takira iyayensu bansa me suka fada mata ba naga ta dauki hanyar best step promise dake lagos island ....gudu take sosai ni km ina zaune na tsura masa ido ahankali ina jin sabuwar kaunarsa da sonsa na kara shigata,zuciyata na wani irin tsalle da bugawa raina na raya min abubuwa masu tarin yawa akan gayen, muryata kasa kasa cikin wani irin yanayi nace Allah kabawa wannan bawa naka lfy.....yayinda yarinyar ke tuki tana wani irin kuka cike da matsanancin tashin hankali.

cikin minti talatin muka iso hospital tun kafin mu karaso iyayensa har sun isa ,suna cikin hospital din isowarmu keda wuya likitoci suka gaye motar aka shiga kokarin fitar dashi daga motar zuwa kan gadon majinyata, ni km aka barni zaune cikin motar da zance zuci babu wanda ya lura dani .
amadadin na fita daga cikin motar nakama gabana, sai nacigaba da zama ina karewa cikin motar kallo tare da tunanin duk yadda akayi wannan matashin dan babban mutun ne duba ga yanayin motarsa suturar jikinsa da yadda likitoci suka shiga rawar jiki dashi, ina wannan tunanin ne ahankali idanuna ya sauka akan wani dan karamin littafi wanda gbdy jikinsa ja ne sai digon zanen ruwa zinari da akayi ajikinsa.
cike da matsanancin sanyin jiki da fargaba na kai hanuna na kan litaffin ina shafawa kafin daga baya na dauka ina kallo. tsawon minti goma dauna zaune ina kallo littafin batare dana bude ba, sannan na mayar dashi na ajiye inda nagani, na fito daga cikin motar ina dube dube sannan na kama gabana zuwa gida.

daren ranar zaune na kwana sbd tsananin tashin hankali danake ciki ,idan na runtse idanuna da zumar yin bacci sai naga ciwon mutumin yana min gizo da yadda yake shure shure kunfa na fita abakinsa, idan km na bude idanuna wani sabon tashin hankali ne domin wani azabben soyayyarsa ce ke farmakan zuciyata ,hk na raya wannan daren batare dana runtsa ba, sannan babu abinda yazo cikin raina kmr na sanarwa ore abinda ke cikin zuciya sbd ore kawata ce sosai tun secondry school muke tare daita, up to university tare muke sai dai department dinmu daban, ranar da abin ya faru da mutumin batazo school ba sakamakon ciwon kai da take fama dashi.

tun asuba dana tashi ban koma bacci ba nashiga gyara koina agidan tare da yin abinci sbd alokacin ni nakewa mahaifiyata komai duk da kasancewata ni kadai da haifa , hkn bai sa ta sangartani ba.
ita kanta mahaifiyata ta fuskanci ina cikin damuwa amman sam na kasa sanarmata, gashi jiya tana kallona kwana nayi juyi na kasa runtsawa duk juyin datayi sai taga idanuna biyu, ina gama komai na shirya na nufi gidansu ore.

na koro mata halin dana tsinci kaina agame da gayen jiya ,har muka nufi makarata ina bata labari da yadda naji dattijon ya fadi inda za'a samu maganin ciwon.
kai tsaye gurin *dorisimi* muka nufa sbd binciko mutumin jiya dana gansu tare .


batare da wata shan wahala ba muka gano mutumin, byn mun gaidashi a mutunce nace masa naxo ne akan mgnr dana ji yayi jiya akan inda za'a samu maganin ciwon farfadiya.
cike da matsanancin mamaki ya tmbyeni me zanyi dashi ?
"tace nace masa nima ina da ciwon ne shiyasa nake son sanin inda zan samu mgnanin, naunayen ajiyar zuciya mutumin ya sauke cike da tausaya naga yana kallona, sannan yashiga karanto min full address din zanbi nasamu maganin yayinda ore dake gefena zaune ta ciro biro da farar takarda daga cikin jakarta tashiga rubutawa.
"yace daga nan zaki shiga mota xuwa *songo 'ota* idan kin sauka a sango zaki karasa zuwa Under bridge sai ki tsallaka hannuki na dama ki shiga mota me zuwa idiroko ,sai ki sauka a *ow'odi idiriko* bus stop ,kina sauka zaki ga yan machine ,sai kice gidan alhaji tapa zaki kai tsaye za'a kaiki sbd mutumin ba boyayye bane,yana kaiwa nan yayi min fatan alkhairi tare da fatan samun nasara. muka durkusa har kasa mukayi masa sallama muka wuce.

muna kan hanyar dawowa gida ne ore ke ban shawara me zai hana na raba kaina da wannan wahalar......
nace sbd me zatakira aikin taimaiko da tsigar wahala?
"wannan ba taimako bane son zuciya ne kike son aikatawa "ta yaya bakisan mutun ba bai sanki ba zakiyi risking life dinki akanshi ?takirara mgnr tana kiran sunana kana ta ja ta tsaya ,nima na tsaya ina kallonta batare dana amsa mata ba .
"me zai hana ki hakura da son gayen nan karki saka kanki cikin wahala "akwai maza dayawa a office fa.
"bazan iya ba ore dan baki san yadda nake ji bane, ki tayani da addua kawai, byn ina matsanacin sonshi ,aikin alkhari zanyi ,kamata yayi ki karfafa min gwiwa nakarasa mgr tare da yin gaba na barta ,ta biyo byna da sauri tana min mgn har muka shigo cikin unguwarmu shawarar ore take bani akan nabar zance gayen amman furrrr naki, nace naji nagani idan ma dan karta rakani ne, take bani shawara tayi zamanta ni kadai dina ma zani . daidai office 's qsuters
muka rabu daita na wuce gida.

washegari tunda asubar fari nabar gida da zumar zuwa school ,na nufi *idiroko*, da taimakon address din da'aka bani.


byn dogon layin dana iske nasamu ganin alhj tapa.
zaune nake gaban alhaj tapa byn nagama koro masa abinda abinda yakawoni gurinsa ya dago da idanunsa dake kan kasar dayake duba, ya kalleni "kana yace me matsayin shi wanda zaki amsarwa magani?
bakina na rawa nace saurayina ne wanda zan aura.
"ya sunan mutumin da sunan iyayensa nayi tsuru tsuru ina kallonsa kmr yadda yake dubana, sai daya sake maimaitawa sannan nace bansani ba "amman kika ce sauranyinki ne wanda zaki aura ?na girgiza masa kai ala'mun eh.
"shine km baki san sunansa ba?
nayi shr tare da tsura masa ido kawai alamun rashin gsky .
"idan baki san sunansa ba kina iya barin gurin nan yanzu dan aiki bazai taba yiwuwa ba, dole sai da sunansa dana iyayensa tukun zamuyi aiki sbd mahimmanci aikin, domin aikin akwai hatsari sosai acikinsa dan hk kije ki nemo sunansa sai ki dawo kiji hatsarin dake tattare da aikin ...

jikina na rawa na bar gurin malamin tafiyar awa ukuce ta kawo cikin garin lagos ,kai tsaye hospital din da aka kwantar dashi na nufa cikin matsanancin sauri .

ina isa hospital daidai step muka ci karo da yarinyar jiya zata sauko muka gaisa daita, tana sake min godiya .
"muryata a sanyaye nace mata babu komai ya jikin yaya faisal din?
tayi murmushi tare da cewa da sauki amman ba sunansa faisal ba abdulkabir sunansa .....
ohhhh ai jiya ne naji kmr kina ihun kiran sunan faisal da sunan mahaifiyarku da mahaifinku uhmmm.. me naji kince?
na daga idanuna sama ala'mun son tunawa can nace yauwa asiya da mahruf na fadi hk tare da saurin waskewa.

yarinyar data tsinci kaina cikin jin faduwar gaba sakamakon jin sautin muryarta ,tayi zugun tana kallona ,nasan tunani take akan nacika tmby.
"dan hk nayi saurin katse mata tunaninta ta hanyar cewa kiyi hkr na cika tmby ko? murmushi sake yi sannan tace "no babu komai, wato hk na gigice jiya ina ta zuba sambatu gsky rudewa ce kawai amman duk ba hk sunan iyayenmu suke ba, mahaifiyarmu sunanta baraka wace muke kira da ammi ,mahaifinmu km adam sunansa muna kiransa da dady.
"ayya gsky jiya kin gigice dayawa kina fadar abubuwa ni zan wuce ki gaida dady da ammi har da yaya abdulkabir, Allah ya bashi lfy.
"tace ameen cikin hanzari na juya zan wuce naji sautin muryarta bazaki leka kiga yadda jikinsa yayi ba?
na juya ahankali nace "sauri nake wallahi amman zan dawo wani lokaci na duba jikinsa , ok idan badamuwa muje na rage miki hanya .
tare muka jero har zuwa bakin motar jiya da muka kawo shi hospital ta bude motar tashiga ta zauna, nima na bude dayan bangaren nashiga na zauna ,har tayiwa motar key wayarta ta dauki kara, ta dauka tayi mgn "tare da cewa ok gani nan xuwa ,ta dube gefen inda nake zaune zugun tace dan Allah kiyi hkr ana kirana,amman yanzu zan dawo .
"kaiki damu ta fita ta barni cikin motar tare da kunna min AC 'n motar.
fitarta ke da wuya kmr ance na juya bayan motar, idanuna ya sauka akan littafin dana gani shekaran jiya , hanuna na rawa na kai na dauka ina kallonsa kmr ranar farko dana soma ganinsa ahankali na bude cikin littafin wanda naga a shafin farko an rubuta littafin sirri .......
na meida murfin littafin na rufe ina duban ainihin bangon litttafin, rubutun jiki na kurawa ido sosai amman bangane abinda ke rubuce ba kasancewar ba da harshen turanci aka rubuta ba, ba km da French ba, ina tunanin ko da wani irin yare ne wannan akayi rubutun dashi, na hango tahowar yarinyar nayi saurin tura littafin cikin hijabina na boye na sake tattaro natsuwa na sanyawa jikina, dan karta gane wani abu, tana gama karasowa ta bude ta shigo cikin motar "tace yi hakuri dan Allah na barki zaune ke kadai ?
"nayi murmushi tare da cewa babu komai ai ,ta tada motar muka bar harabar hospital .

muna kaiwa *fadeyi* kafin mu karasa *o'nipan* nace anan zan sauka taja burki gefen titi tayi parking na sauka tana sake min godiya, sunanta nake son tmbyrta amman karta ga kmr nacika tmby yasa na share ,na rufe mata murfin motar taja tayi gaba, ni km nakarasa inda zan samu motar me zuwa unguwarmu.

washegari ma haka na shirya da niyyar zuwa school na wuce *idiroko* byn na isa gidan alhj tapa na gaya masa sunansa dana iyayensa sannan yayi duba cikin fara kasar dake gabansa ya tabbatar da sunan ne nagaya masa ,sannan yasoma min bayani kmr hk za'a yi aiki amman me karfi ,cikin biyu ki zabi daya zaki tare anan tsawon wata daya dodon tsafi zai dinga kwana dake, ko km me a miki tsafi sannan wannan ciwon zai bar jikinsa.
byn ya warke sai ya aureki ..
kafin ayi aiki na biyu akwai sharadin me karfi ,matsawar bai aureki ba ciwon zai iya dawowa jikinki .
"sannan ko kin aure wani bazaki taba haihuwa dashi arayuwarki ba matsawar bashi wannan abdulkabir din kika aura ba.

"sannan duk ranar da kika kuskura kika gayawa wani wannan sirri kece silar nemo masa mgn , shima ciwon zai iya dawo kanki .
"akwai tukunyar tsafin da zanbaki wanda zaki dauka akanki idan dare ya raba,sai ki samu hanyar data rabu gida uku ki ajiye wannan tukunyar tsafin, byn kin ambaci sunansa dana iyayensa sai ki saka wannan maganin a tsakiyar bakinki, ki juyawa tukunyar tsafin baya.
" karki kuskura ki juya bayanki idan kin ajiye tukunyar tsafin sannan karki kuskura kiyi kowa magana ,duk wanda yayi miki mgn karki tanka masa domin akwai matsala idan kika amsa kowace irin murya ce zaki sallawantar da rayuwarki.
"sbd amsawarki tana daidai da rugewar rayuwarki gbdy domin zaki dawo wata bake ba zaki dawo rikakkiyar yar daba me shaye shaye duk abinda ya danganci maye sai kin sha shi, banda fashi da makama.

nayi shr kawai ina kallonsa sbd narasa abinda zance masa yayinda tsoro da firgice suka farmami xuciyata da ilahirin jikina, naji araina bazan iya wannan kasadar ba.. mutumin da zanyi wannan aikin sai da rai akansa bai san ni ba bai san koni wacece ba yanzu idan nazo nagama taimakawa rayuwarsa yace bazai aureni ba meye makomar rayuwata?
nayiwa kaina tmbyr take zuciyata tayi rauni magangun ore suka dinga xuwa min 1 byn 1 ahankali hawaye suka cicciko idanuna na sake tsare alhj tapa da idanuna sannan na motsa labbana nasoma mgn cikin sanyi murya, "gsky aikin nan akwai hatsarin bazan iya sai da raina ba .......
"a she kuwa zaki yawo tsirara ai duk wanda yaji yanayin tsarin aikinmu da ka'idarsa dole yayi ko km ya koma tsince tsince a bola... nayi saurin zaro idanuna waje daidai da hawayen idanuna sun samu nasarar gangarowa bisa kuncina .
muryata a matukar tsorace "nace hauka kake nufin zanyi matsawar ban yarda ba?

"tubaran kuwa domin sai kin zama mahaukaciya karfi da yaji me yaga kayan jikinta tana yawo tsirara haihuwar uwarta ..

hankalinsa ya kai kololuwar gurin tashi jikina ya dauki rawa dan hk ina gama jin bayaninsa nacigaba da kukana ina dana sanin shigar da kaina cikin tashin hankali danayi.
ganin bani da wata mafita ko dabara yasa na amince da zabi na biyu wato daukar tukunyar tsafi dan bazan iya bari mutumin yasadu dani ba. ina zauna ya hada min ruwan magani nasoma wanka dashi tun agindansa sannan yabani wata yar karamar tukunya dake cike makil da kayan tsafi an tsiyaya manja acikin tunkuyar.
ahankali ya sake min bayani duk yadda zanyi na amsa na nufo gida.


tun a hanya zuciyata tabani shawarar nayi wa mahaifiya amfani da maganin bacci ta yadda zn samu damar fita cikin dare,take na amince da shawarar da xuciyata ta bani.
na tsaya wani pharmacy na siyi panador night .

ina shiga gidanmu nasamu waje karkashin step na boye tukunyar maganin sannan nashiga part dinmu inda na iske ummana zaune tana kallon TV nayi mata sannu da gida sannan nakarasa uwar daka nayi wanka na kimtsa zuciyata na wani irin bugu.

dadare byn nagama girki na hadawa ummana cucumber just na saka mata maganin baccin ciki na kawo mata abinci da cucumber just din dana hadata mata.
gama cin abincinta ke da wuya bacci yayi gaba daita akan kujerar datake zaune akai.
ni km ganin tayi bacci yasa na tasheta xuwa uwar daka ta kwanta nima kwanciyar nayi zuciyata cike da tunani iri iri da fargaba..

misalin karfe biyun dare na tashi dan dama banyi bacci ba, na sauya kaya zuwa doguwar riga da dan guntun hijabina na dauki takalmina sadaf sadaf zan fita har na kai bakin kofar fita, na tsaya ina jin yadda kirjina ke tsananta bugawa.na dawo da baya ahankali na isa inda ummana ke kwance kmr ta mutu na dan duka nayi kissing dinta sannan na sake juyawa na bar gidan gbdy.


a matukar firgice nake tafiya cikin wannan daren sbd rashin sabo domin ban taba tsintar rayuwata acikin wannan yanayin ba, byn school da islamiyya bana zuwa koina da zarar na dawo gida bana sake fita sai wata goben .
sannu ahankali na kawo hanyar data rabu gida uku na ajiye tukunyar tsafin ,na tsuguna gaban tukunyar tsafin nayi kirarin sunan abdulkabir dana iyayensa sosai kmr yadda alhj tapa ya koyar dani ,sannan na juyo nasoma tafiya zuwa hanyar komawata gida cikin rashin sa'a har naci rabin tafiya nasoma jin sautin muryar mutane ana ihu tare da sautin gudu ,a she police ne suka biyo barayi wani irin mahaukacin tsoro da firgice ne ya mamaye ilahirin jikina.
take km jikina yasoma rawa naki juyawa nacigaba da tafiya cike da dauriyar xuciya, cikin hk naga barayin sun kwaso aguje sai gashi munci karo dasu gbdy na rude na gigice sbd jin yadda suke harbi ,police na meida musu da martani .
"a matukar tsorace nasoma neman hanyar tsira batare dana juya ba amman hkn yaki samuwa sbd jin sautin police danayi ta bayana suna futar you are under'arest ,all of you drop your gun nan fa na sake gigicewa da shiga matsanancin tashin hankali ,jikina ya sake daukar rawa nayi saurin fita ciki barayin zuwa gefe guda na tsaya jikina nacigaba da kirrma.

inna lillahi wa inna ilaihi rajiun shi nashiga furtawa ina sake maimaitawa ,da bindiga naga wani police yana min nuni na koma cikinsu .
"bakina na rawa nace ai batare muke dasu ba, ban ma sansu ba yau shine rana ta farko dana taba ganinsu ni nazo kawo... short up police ya buga min tsawa nan fa na sake rudewa na daura hannuna bisa kaina ina kuka ina cewa wallahi batare muke dasu ba.
ganin hk yasa daya daga cikin barayin kwashewa da wata uwar dry sannan yacewa police din yasani tare muke fitar dare dasu.
aiko ina jin hk nan na zube kasa bisa gwiwowina na kara sautin kukana ina rantsuwa akan bana cikinsu ,amman hk police suka hadeni dasu muka koma zuwa hanyar dana ajiye tukunyar tsafin, wanda sai lokacin na tuna da sharadin da alhj tapa yace min .
kuka nake sosai har sanda muka isa (area g) police station aka watsa mu cikin cell .

idanuna kuri akan yan'ta'adda nan da suka min sharri, banji ba ban gani ba gashi sun kullamin kullaiya , kallonsu nake daya byn daya hawaye nabin kuncina meyasa kuka min sharri alhalin kunsa tafiyarmu ba daya ba?
meyasa kuka gwamaci ku tsomani cikin rayuwarku me cike da kalubali da tashin hankali?
bancanci wannan rayuwar ba, ni ban kasance me irin halinku ba ,dan girman allah na rokeku ki fitar dani cikin wannan tashin hankali mamana na can na barota kwance tana bacci idan ta farka bata gani ba zata iya rasa ranta .
dan Allah kuyi hkr idan wani laifi nayi muku kuka zabi ku hukuntani ta hk.

daya daga cikinsu "yace ke meya fitar dake a daidai wannan lokacin ?
"wannan lokacin da aka ganmu tare dake, ba lokacin mutanen arziki bane ,lokaci ne na irinmu masu hawan dare.. sauran biyu din suka hada baki.
"

3 Comments On SAI KA AURENI DOLE
avatar
zainab-ishaq

1 year ago

Reply

Love it ????????

avatar
zainab-ishaq

1 year ago

Reply

Yes and I want to download it

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to zainab-ishaq

In order to download you have to subscribe for our package at https://tnovels.com.ng/subscribe

Please Login or Register in order to submit comment