Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

lafiyar abdulkabir dina tace min duk suna lafiya . hkn ne ke dan kwantar min da hnkli.



lokacina dana cike shekara biyu cif na gahurta acikin prison har nazama shugabansu ganinya gurinn shaye shaye da harakar dabanci babu wanda ke kawo min rainin wayo ,wani irin karfi nake ji ajikina kmr shara'A bana jin tsoro kowa duk girmanka sai natakaka, wanda lokacin har gasar fada muke yi atsakaninmu km nice nake lashewa, ni kaina idan ina yin wasu abubuwan mamaki kaina nakeyi nasha sigari na sha wiwi wanda duk acikin prison muke samu .
"wani lokacin ma ganiya kan bani shawarar me zai hana idan mun fito daga prison nayi join dinsu cikin harakar fashi.

sai dai na kalleta kawai nayi dry ,rayuwa cikin prison agurina babu dadi sabanin gurin su ganiya da gang dinta domin su sun meida gidan tmkr gidansu sbd yawon kawosu cikinsa da ake.
dan wannan zuwan nasu ba shine zuwansu na farko ba sun shasha zaman yari.

muna samun abinci amman ba ishashe ba ,dan wanda ake bamu baya wani isarmu abinci ne gashi nan kmr loma acikin plet gashi always Bean's ne.

sannan ana yawon kawo mana ziyara lokaci zuwa lokacin.
akwai wani malami daya taba zuwa kawo mana ziyara ya gani ina shan tabar wiwi hankalinsa yayu mugu mugun tashi yashiga min wa'azi tare da jamin ayoyin alqurni me girma abinda yabashi mamaki bai wuce yadda duk ayar daya ja ba, zan amshe na karashe ..

ya dade tsaye yana kallona sannan yashiga tmbyata dalilin xuwana gidan yari?
" kai tsaye nace masa kazafin sata akamin batare da nasan yadda ake yinta ba...

nan shima yace zaiyi iyakacin bakin kokarinsa gurin ya fitar dani daga prison .

da zai tafi nace masa "ya taimaka idan zai sake dawowa yaxo mana da kayan abinci sbd dayawa daga cikinmi suna son yin axumi amman rashin wadatacen abinci ke hanasu yi.
nagaya masa hkn ne sbd lokacin watan axumin ya karato km duk lokacin azumi ina ganin yadda suke wahala daga karshe ajiye azumin suke .


ya tabbar min da zai yi bakin kokarinsa da yarda allah .
" zance taimakon abinci kam ya tabbata domin tirala guda akayi na kayan abinci iri iri , ba prison din danake ba hatta na gefenmu sun cin albarkacina .

zance taimaka min da malamin yace zaiyi ne ya sha ruwa domin shi kansa babu irin shige da ficen da baiyi ba dan ganin na fito amman abu ya gagara.
dan hk na dauka shima rashin fitowar wata kaddarar sakamako ce gareni na sabawa umarnin mahalicina danayi..

akwana a tashi babu wuya har ka'idan da kotu tabani tacika na fito tare da su ganiya muna munar wanda ni duk nafisu murna.
akan hanyarmu daga kiriri zuwa oshodi muke bawa juna addrshin gidanjenmu sannan na tabbatar musu matsawar basu bar harkar fashi da makamin ba, kar suyi kuskuren tunkarar inda nake suma mance munsan juna .

ganiya ta tabbatar da sun daina bazasu sake aikata hkn ba , a daidai under bridge din oshodi muka rabu da junanmu nashiga motar me xuwa ikeja su km suka shiga motar me xuwa munshi ol'osha...

ina fitowa daga prison nasoma kokarin haduwa da abdulkabir dina kwasma ore take sanar min ai aure zaiyi abinda yasa bata sanar min ba tun ina prison ba bata son nashiga damuwa akan wanda nake ciki.
to tunda daga wannan ranar da ore tasanar min nasoma nemo hanyar da zanbi ganin ni kadai bazan iya ba, yasa na nemi taimakon ganiya nace ina son tabani goyon baya akwai aikin da zasu tayani .
dukkaninsu daga ita har ore babu wanda nagayawa abinda nayiwa AK ta wajen nemomasa lfyr jikinsa sbd sharadin alhj tapa daya gindaya min.

aiko ganiya ta tattaro min duk wasu gang din yan'iska dake munshi olosha muka shiga aiki neman yadda zan rabashi da zeey tare da karuwarsa onye.....

gama bada labarinta ke da wuya su'ad ta mike tsaye domin isa inda ummanta ke zaune tmkr an dasata agurin gbdy ta dawo mutun mutumi agurin azaune tana kuka tana al'ajabin abinda su'ad ta aikatawa rayuwarta ,aiko tafiya daya biyu tayi sai luuuuuu ta zube kasa tasoma rawar jiki irina masu cutar farfadiya tare da shure shure kunfa na fita daga cikin bakinta.

umma ta zabura ta mike tayi kanta zata kai hannunta ammi tayi saurin dakatar daita, da sauran mutane dake kokarin kai hannusu jikin su'ad sannan cikin rawar jiki ta nufi dakinta shima dady ya nufi cikin dakinsa.
maganin da suke yiwa abdulkabir amfani dashi suka dauka cikin sauri suka dawo parlour'n suka shiga rige rigen yi mata amfani da maganin lokacin AK ji yayi kmr kasa ya tsage ya nutse ciki ya huta da kunya tare da ganin wannan tashin hankali dake faruwa agabansa, wani irin ya dinga ajikinsa lokacin dayake kallon su'ad cikin yanayin cutar farfadiya.
" yanzu hk yake kasancewa a duk sanda wannan dan iskan ciwon ya tasamarsa? yayiwa kanshi tmbyr yana takaicin ciwon.

sauran mutane da suke gurin tsaye suke kan su'ad suna karanto mata addua ,sai data dauki sama da awa daya tana shure shure sannan ta farfado bakinta dauke da adduar dataji mutane na karanto mata ,sannan ta fashe da wani gigitaccen kuka kafin ummanta takarasa gareta har ammi tarigata tare da kamota zuwa jikinta tana shafa bayanta sannan ta nufi kan kujera ta zauna tare daita ta kwantar da kanta bisa cinyoyinta tana kukan me cike da tausayawa rayuwarta. ahankali ammi ta daura hannuta bisa sumar kanta tana shafawa tana sake zubda hawaye .

tsawon min 15 su'ad tana kwance bisa cinyar ammi tana jin wani farinciki from know where yana bin gangar jikinta kana ta yunkura ta mike jikinta tmkr ba nata ba ta zauna tana duban dukkanin mutane dake parlour 1 byn 1.

lokacin da ta gama farfadowa commission ya dubaita "yace kinyi ganganci akan mutumin da bai ce yana sonki ba ki tashi kije har wata uwa duniya nemammasa magani cutar farfadiya ,sanadiyrsa kika tsinci kanki bursuna har na tsawon shrkaru 3 byn shi yana da ma wace yake so har sun kusan yin aure.
"amman kin san kin tafka babban kuskure arayuwarki ko?

"cikin tashin hankali ta bude bakinta tace ehhh.. "amman dolensa ya aureni .
"na yarda na zamo kota biyu ce...

bangaren ak kuwa shiru yayi tare da zabga uban tagumi yana kallon su'ad domin rasa abinda zai ce mata yayi, shi fa a yadda yake ji ko me za'a yi bazai iya aureta ba sbd baya jin sonta .
ahalin yanzu zuciyarsa zeey kawai take matsanancin so, amman sbd abinda tayi masa bazai iya kallon tsabar idanunta ayanzu yace bai sonta ba .

ahankali muryarsa atsanake ta fito gurin cewa naji dukkanin bayaninki km na gode sosai bisa kasadar tsaida rai da rayuwarki da kikayi akaina .
"amman abinda nake so dake shine kiyi hkr ki ajiye mgnr aure atsakaninmu ,kinga ahalin yanzu ana tsaka da hidimar aurena da wata amman zan baki million goma kije ki fara sabuwar rayuwa.

" km duk lokacin da kike bukatar wani taimako daga gareni a shirye nake da na miki shi ko wani iri ne... ina rokon Allah ya baki naki mijin wanda yafini amman ni abdulkabir ba wai dan bazan iya aureki ba, sai dan bani da ra'ayin auren mata biyu..

take jinta ya dauke dif ta daina jin komai dayake cewa, zuciyarta ma ta tsaya cak ta daina bugawa na wucin gadi kafin daga baya zuciyarta tacigaba da bugawa da sauri sauri na nan take su'ad tasoma kuka har da shesheka lallai ta tafka babban kuskuren kmr yadda commission ya fada .

ta banzatar da rayuwarta akanshi, tayi zaman gidan yari akanshi ,ta kamu da cutar farfadiya duk akanshi daga karshe zata kasance zero batare da taga gudan jininta duniya ba.. ..
jama'ar dake zaune a parlour'n kuka suke sosai barin ma ammi da umman su'ad wadanda tun sanda su'ad ta dawo haiyacinta basu sake cewa komai ba.


AK ya fuskanci commission sosai sannan "yacigaba dady abu na karshe da zance a gaya mata shine aja mata kunne karta kara zuwa inda nake ko inda mamata take .....taje tayi rayuwarta nima ta barni bayi rayuwata amman zance aure babu shi.

"you see ur life inji cewar commission dake zaune yana duban inda su'ad take ransa a matukar bace dan jin haushin abinda AK ya fada . "yanzu kinga karshen rayuwarki ko?

"yanzu wa gari ya waya?

su'ad naga jin abinda abdulkabir ya fada jikinta ya dauki rawa ahankali ta mike tsaye tana dubansa ido cikin ido sannan tayi murmushin gefen bakin wanda da gani kasan na bakinciki ne.
batace masa komai ba ta isa inda ummanta ke zaune ta hade kanta da gwiwarta tana wani irin kuka.."ummana takira sunanta cikin rauni da sanyi murya "kiyi hakuri nasan na sabawa ubangijina sannan nayi miki ba daidai ba.
"amman gashi tun a duniya allah ya nuna min iyakata ta hanyar jarabtata da maseefu iri iri,.
"na nemi gafarar ubangiji bisa hadasa danayi da waninsa alhalin yace kada a hadasa da komai agurin bauta .

"a yanzu gani agabanki ina rokonki ki yafemi duk da nasan ke din uwace guda har da rabi me yawon yafiya gareni ..

"kece komai nawa umma banida kmr ki duk duniya kece kika kawoni duniya har nasan koni wacece amman naci amanarki da amanar tarbiyar da kika dauki tsawon lokaci kina bani akan "da" nmj, wanda bai dauki abinda nayi masa abakin komai ba, har yana ganin kudi shine sakayyar datafi dacewa dani ...

"kiyi hakuri kice kin yafe min ummana ko zanga daidaita arayuwata...umma kuka su'ad kuka hatta commission da sauran mutane kuka suke sosai .

umma ta dago idanunta da suka gama rikidewa suka koma tmkr garwashi wuta ta daurasu bisa fuskar tilon diyarta hawaye na sake bin kuncinta.. "na yafe miki diyata duniya da lahira da albarcin annabi muhammadu (saw) zakiyi albarka arayuwarki zakiga daidai arayuwarki .
"ina adduar Allah ya rabaki da wannan cutar farfadiya data sameki "ba yau nasaba daukar kaddara ba.

" kaddara acikin jinina take km zan cigaba da karbarta a duk yadda tazo min Allah yabani ikon cinyeta.
tana karasa fadar hk ta mike tsaye tare da rike hannun su'ad cikin nata suka soma tafiya domin kokarin barin parlour
ammi ta mike jikinta na rawa tare da dakatar daita baiwar Allah umman su'ad taja ta tsaya dan jin abinda zatace.


ammi takarasa gaban AK ta tsaya tana masa wani irin duba muryarta na rawa "tace abdulkabir bakada imani balle tausayi "yanzu abinda yakamata ka gaya yarinyar da tallafi rayuwarka kenan?

"me zatayi da kudin din banza da wofi kasani ni mahaifiyarkace wace tayi silar zuwanka duniya a yanzu ina baka umarnin auren yarinyar.... ammi takarasa mgnrta tana nuna inda su'ad take tsaye da hannunta...

umman su'ad ta juyo ahankali tana kallon ammi, take zuciyarta ta kismamata ammi tayi wannan mgnr ne da wata manufa,killa kodan kasancewar fuskar da su'ad din ke dauke dashi ne.... dan hk tasoma karasowa har inda ammi take tsaye .

"hjy karki damu balle ki takura masa kan sai ya auri diyata dole.
"no no karki takura masa , sbd ni kaina bazan taba amincewa yarinyata ta auri mutun irin wannan ba me zanyi da suruki irinsa ........

mmn sudais ce

💗💗💗💗💗💗
SAI KA AURENI DOLE
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗



~NA~



*AYSHA A BAGUDO*



~DEDICATED TO~
HAUWA A USMAN
JIDDARH

*Allah messenger saw said convey of me even only an ayah of the Quran*

page 52


muryar ammi na rawa "tace dan girman allah karki ce hk.
"shi irin wannan al'amarin ahankali ake bin komai domin ba'a san abinda Allah ya boye acikinsa ba.

minister yayiwa AK tatasssss hk ma commission wanda jikinsa yafi na kowa yin sanyi ,hatta maman zainab labarin su'ad yayi mugun taba mata zuciya sannan ta tausayawa rayuwar yarinyar km har cikin ranta take son abdulkabir ya aureta .
gabdy jama'ar dake gurin babu wanda bai sa baki ba akan umman su'ad ta janye lafazinta .

sosai ammi tashiga gayawa umman su'ad Kalamai masu sanyi masu kama da nasiha wanda yasa ta gagara daga kafafunta daga inda take tsaye niyyar barin parlour 'n.

yayinda shi km AK yashiga tunani akan lamarin dake faruwa yanzu dayake zaune a parlour, duk cikin lamarin babu wanda yafi daga masa hankali da neman tarwatsa masa 'kwal'kwaluwa kmr umarnin amminsa garesa .

"gbdy yakasa gane abinda amminsa take nufi dashi.

" tana nufin shine zai aure yarinyar datayi zaman gidan yari na tsawon shekaru 3?

"sannan yar shaye shaye me tada tarzoma acikin gari ,wayasani ma ko tagama rabawa gayun gari jikinta? yayiwa kansa tmbyr can km a fili ya furta sam bazan iya aurenta ba wlh ...

atare ammi da dady suka waigo zuwa inda yake zaune, dady ya zabga masa wata uwar harara "tare da cewa
*sai ka aureta dole dan ubanka* kana nufin duk uwar wahalar data sha akanka zata tafi abazan ne "ko me makake nufi?

AK yayi zumbur ya mike tsaye jikinsa na wani rawa yace. "dady ni zan auri su'ad?

dady yace "kwarai kuwa kai zaka aureta har ma kuyi rayuwa tare .

ak ya fara girgiza kansa yana tafiya da baya da baya a cikin parlour 'n, yace "haba dady wai me yasa kuke son takurawa rayuwata tunda nake ban taba jin koda digon son auren su'ad acikin raina ba amman sai kuce na aureta dole ?

"nifa bazan taba iya hada soyayyar zeey da wata ya mace ba..

ammi ta fusata dan jin wadan nan miyagun kalaman da suke fitowa daga bakin AK "

"kai min shiru shashashan banza wanda bai san inda yake masa ciwo ba km ka rike aranka aure tsakaninka da su'ad kmr anyi angama muddin ina raye.

ak yatako ahankali har zuwa inda hjy kakarsa ke zaune ya zube gabanta ya rike kafar hjy.
"pls hjy ki ceci rayuwata, zeey tana da matukar kishi a kaina.

kafin hjy tace wani abu dady ya mayar da numfashi yace "taje tayi duk abinda zatayi, ai kai mijin mace hudu ne, domin ko addininmu ya halasta maka yin hk..

eiman ta amshe zance wallahi wallahi yaya ka bani mamaki, kasani jin kunya a yanzu danake tsaye acikin parlour 'n nan a iya tsawon rayuwata baka taba yin abinda naji na tsanake ba kmr yau.. "ka zauna kayi tunani da kyau idan mafarki kake yakamata ace zuwa yanzu ka farka kasan abinda kake.
" wannan yarinyar ta cancaci komai agurinka wallahi ko rayuwarka tace tana so yaci ace ka cire kabata ...

"yazakaji aranka yaya ace nice nake cikin halin data tsinci kanta a sanadiyarka? takarasa mgnr tana rushewa da wani kuka, wanda mgnrta bakaramin tsayawa yayi a zukatan mutanen dake gurin yayi ba.

"yanzu shikenan hk rayuwarta zata kare babu sausauci kenan?
"ita baga lafiyar jikinta bada samun aurenka ba.

"ko alokacin da abun ya faru tafini shiga damuwa da tashin hankali ban mance komai daya faru ba alokacin wallahi su'ad masoyiyace ta hakika wanda samun irinsu zai yi matukar wuya a wannan zamani .

"bari tabbatar maka da wani abu ni yar uwarkace uwa daya uba daya amman wallahi yaya bazan iya kasadar datayi akanka ba ...

"pls yaya ka taimaki rayuwarta ka aureta shine kawai abinda zakayi kasaka mata da kasadar saida rayuwarta datayi.

jikin ak yayi mugun sanyi da jin kalaman kanwarsa.
sam ya kasa gane inda kalaman dukkaninsu ya dosa shi fa abinda ke bashi hsushi da hassalashi kenan asa shi yin abinda zuciyarsa bataso dan hk a matukar fusata AK ya bar parlour 'n zuwa part dinsa.

lokacin da AK ya bar parlour, muhawara ce tashiga tsakanin yan'uwa yayinda ammi taki yarda umman su'ad ta wuce ta kasa ta tsare sai gumi ne ke tsatsafo mata agabadaya ilahirin sansar jikinta.

adaidai wannan lokacin AK ya dawo parlour 'n hannunsa rike da takadar cheek ahankali yakaraso har inda su'ad ke tsaye wace tasa hakorinta tana cinzan lips dinta ahankali hawaye na gangarowa bisa kuncinta, hannunsa yasa ya kamo tafin hannuta yasanya takadar cheek din yana share mata hawayen dake bin kuncinta alokacin dayake tsaye gabanta ji yayi kmr ya rungumeta ajikinsa amman bazai iya aikata hkn ba.

sautin zazzakar muryarsa ce ta doki dodon kunnenta
"ahalin yanzu bana jin haushinki ko tsanarki cikin zuciyata sbd karamcinki gareni .
"na yarda na amince ke din masoyiyace ta hakika kmr yadda kowa ke fada zan iya sadaukar miki da komsi nawa ban aurenki sbd shi kadai ne bazan iya yi ba ,amman ga wannan cheek din ki rike na ninka miki abinda nace zanbaki pls &pls ki bar rayuwata kije kiyi sabuwar rayuwa.
ya karasa fadar hk yana me tsura mata mayattun idanunsa yana kallonta wadan da kallon cikinsu kadai ke haddasawa mutun shiga wani yanayi mara misaltuwa.

cike da sanyin jiki ta dago fararen idanunta tana kallon cikin kwayar idanunsa masu bugar mata da zuciya a duk sanda ta kalli cikinsu gabanta na bada wani irin sauti na tashin hankali ,shima mayatattun idanunsa ya tsura mata yana kallon cikin fararen idanunta wanda zuwa yanxu sun sake canzawa sbd tsabar hawayen dake tsiyaya acikinsu ,sunyi luhu luhu dasu.
yana kallonta har sanda ta dauke idanunta acikin nasa ta meida shi kan check din dake rike da hannunta.

zuciyarta ke wani irin harbawa yayinda tsoro da firgice sukayiwa kirjinta dirar makiya jitake kmr ta daura hannuwanta duka bisa kanta ta kurma ihu kozata ragewa zuciyarta radadin datake ji ayanzu datake tsaye agabansa. wani irin dukan tara tara kirjinta kemata, duk wata gaba dake cikin halitar jikinta rawa takeyi, yayinda kallo daya zaka mata kagane hankalinta a matukar tashe yake hannuta 1 dake karkarwa tasa ta rike cheek din hanunta sosai tana sake duba check din daya bata amadadin 10 million din dayace zai bata a farko 20m tagani arubuce, cike da matsanancin takaicin da tashin hankali ta dago idanunta dake tsiyayar hawaye tana kallonsa kana tasoma yaga check din hannuta still tana kallon cikin kwayar idanunsa sai datayiwa check din kuci kuci sannan ta daga hannunta saman kansa tasoma tsiyaya masa piece's check din tundaga kansa yashiga bin gangar jikinsa.

"ka taba zuciyata abdulkabir kaji yadda take bugawa akanka .
"a duk lokacin dana yi tunanin cewa kana guduna, bugun zuciyata yana sake karuwa da karfi da karfi sai naji kmr kirjina zai tsage zuciyata ya fado kasa.
"a yanzu danake gabanka tsaye zuciyata tafi ko yaushe hautsinewa da shiga tashin hankali mara iyaka.

"hakika nasani nasan hk zuciyata zata kasance tunda zan rasaka a rayuwata.
nasan numfashina yana daf da katsewa .

abdulkabir tsawon rayuwata nayita ne cikin tunaninka da damuwa da yadda zanbi naga na malakeka hatta da gangar jikina yana tausaya min akanka, ni kaina nasan a yanzu narasaka har abada.. nan take hawayen idanunta yashiga gangarowa tashga kuka babu kaukautawa .
tare da sa hannunta ta dafe daidai inda zuciyarta take bugawa.

" daga yau daga rana me kmr ta yau, yau uku ga watan tara ka rubuta ka'ajiye a inda bazai goge ba su'ad tabar cikin rayuwarka bari km na har abada.

"abdulkabir koda dagani sai kai zamu rage cikin duniyar nan na hakura da aurenka km a yau zan daina sonka har duniya ta nade.
"ga tsiyar ka nan banaso domin 20m dinka babu abinda zasu min.

" ni kaina inada kadarar data zarta 100m so mezanyi da 20m dinka?
"zan tafi kmr yadda kace na fita rayuwarka naje nayi sabuwar rayuwa har sanda mutuwata zata riskeni naje na iske mahaifina.. tana gama fadar ta hk juya ahankali zuwa gurin ummanta.

"muje ummana daga yau baki sake kukan bakin ciki ba domin zan dawo miki su'ad dinki ta da har abada bazan sake komawa rayuwar danayi ada ba tunda komai yarigada yazo karshe cutar farfadiya km zan roki Allah ya yaye min ita. umma najin hk ta rike hannunta gam cikin nata suka soma tafiya.
da wani irin sauri ammi da minister suka sha gabansu atare "kibar min su'ad na inganta rayuwarta tare da nemo mata maganin ciwon jikinta inji cewar ammi.

shi kuwa minister cewa yayi "saleema ki tsaya asan yadda za'a yi karki sake tafiya ki barmu dan girman allah karki ce zaki tafi baki san wahalar da muka akanki ba.
wani irin duba umman su'ad tayi masa sanan muryarta a hassale tace "wace salema nace maka ni ba saleema bace ni rafiya sunana..
"nafa san kece saleema domin babu ta yadda za'a yi ki bace min .

"haba saleema meyasa bazaki kasance me tausayi da ya fiya ba?
"nace maka ba sunana saleema ba meyasa kake son kara min damuwa akan wace nake ciki?
tanakarasa fadar hk tasanya kanta tare da su'ad suka fice daga gidan suna fita ammi ta sulale kasa tana wani irin kuka minister kar kabari ta wuce dan Allah minister nifa jikina yagama bani wallahi itace salimar taufeek dina... ka.. kace ta. .. take mgnr data keson yi ta makale tasoma wani irin tari idanunta na kakkafewa wanda zuwa lokacin tuni su'ad da ummanta sun bar gidan.

gbdy su dady sukayo kanta suna kiran sunanta amman ina numfashinta ya dauke ashe zaune bata kare ba hankali ya sake tashi byn basu gama da wata matsalar ba ga wata ta kunno kai.
da sauri minister ya nufi waje inda escort dinsa ke zaune zaman jiransa ya nufa tare da bawa daya daga cikinsu umarnin bin bayansu umman su'ad sannan ya sake dawowa parlour .

kusan awa biyu ammi bata farfado ba dan har sun fara tunanin ko ta mutu ne domin babu wani gurin a jikinta dayake aiki hankalinsu ya tashi sosai dan babu wanda yayi tunanin wani hospital acikinsu maman Zainab ce ta daura kanta akirjinta sam ta rude hkn yasanya bata ji numfashinta dake sauka kadan kadan ba. basu kansu ba hatta dady da mninster da suke maza wadanda akasani da dauriya sai da suka fara kuka, shi ak janta yayi ya rukunkumi ajikinsa yana ihun kiran sunanta yana zuba sambatu wallahi bata mutu dogon suma tayi ammi ki tashi karki mutu ki barni wallahi zanyi abinda kike so, zan aureta ki tashi zan aureta duk wanda ya kalleshi zai gane matsawar aka rasa ammi shima tabbas za'a iya rasashi jini ne yasoma fitowa daga bakin ammi da sauri AK mike jikinsa na wani rawa ya dauketa sai mota sanin bazai iya tuki ba yasa minister yasa direbansa yaja motar, motocin .
biyar ne suka rufa musu baya, da mata da maza likitoci sunyi iya kokarinsu don suga sun ceto ranta amman ina abin ya gagara sun samata oxygen da na'urorin dan ganin tana raye amman ina har yanzu babu wani abu da zai nuna maka wato tabbas da rayuwarta .
minister ya gigice dan yashiga mugun tashin hankali cikin firgici ya dubi tarin likitocin dake zagaye dashi "yace idan aka rasa aunty sam bazan iya dosar wadan nan family da zance mutuwarta ba.
daya daga cikin likitocin yace" to yanzu yaya za'a yi kenan ?

"wannan ikon Allah ne duk yadda Allah yaso da bawansa hk ce zata kasance dashi ,rayuwa da mutuwa km duk na Allah ne minister ya jinjina kai kawowar wata danja dake jikin na'urar da suka sanya ajikinta shi ya tsayar dasu daga tautaunawar da suke a tsakaninsu, nan minister ya hau hamdala acikin ransa dan ko na'uarar yayi nuni da tana raye bata mutu ba, take ransa yayi masa dadi suka hau nazarin yadda zasuyi ko Allah zai taimakesu .
cikin ikon Allah numfashinta yacigaba da harbawa akai akai ,ransu yayi musu dadi nan fa suka shiga godiya ga allah da yayi musu wannan taimako, sun dau lokaci me tsawo akanta suna bata taimako har numfashinta ya dawo daidai dan har ta bude idanunta tayiwa minister mgn daga nan suka fito suka tarar da jama'a cikin zullumi da jiran tsammani.

alokacin da minister ya bayyana musu cewar bata mutu ba tana raye hkn yayi musu dadi sosai dan hk tace tana bukatar ganin dady.

abdulkabir har ya suma

3 Comments On SAI KA AURENI DOLE
avatar
zainab-ishaq

1 year ago

Reply

Love it ????????

avatar
zainab-ishaq

1 year ago

Reply

Yes and I want to download it

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to zainab-ishaq

In order to download you have to subscribe for our package at https://tnovels.com.ng/subscribe

Please Login or Register in order to submit comment