Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

hular rigar jikinta na saukowa bayanta, hkn ya bayyana tarin sumar kanta.
tsaye yake ya harde hannuwansa duka akirjinsa mayatattun idanunsa akansu .yana kallonta. idan dai idanunsa ba getso yake masa ba ita yagani dazu abayansa, sannan yana yawon cin karo daita. to meye kawo nan.?
bai kamata kayi wannan tmbyr yanayinta kadai ya isa ya tabbatar maka da abinda tazoyi nan inji ziciyarsa.
gyara tsayuwarta tayi ahankali fararen idanunta har lokacin suna kansa.
shi din ma kallonta yake fuskar nan tasa babu wani annurin kirki cikin natsuwa batasan sanda take daga kafafunta tana tahowa inda yake tsaye ba.
ore tayi saurin karasowa ta sha gabanta tana girgiza mata kanta kar yi kokarin kaikanki zuwa gareshi ,lokacin yin hk baiyi ba tuku....
lokacin hk yayi ore har yaushe ne zan cigaba da boye burin zuciyata gareshi kinfi kowa sanin irin wahala da gwagwarmayar dana yi facing akanshi arayuwa. nagaji enough is enough ore let me face him ..let me talk to him one's today .
da hanuta tayiwa ore nuni databa hanya . babu musu ore ta kauce .
shi kuwa
juyar da kanshi gefe yayi kmr baisan tanakarasowa gurin ba sai yaji tace you lack manners kalmar yabashi haushi sosai and he don't want any dilemma with her ko bazan baya bukarta mgn da kowa yanzu so ko juyowa baiyi ya kalleta ba .
duk da yadda sihirtaccen kamshin turarenta ke kaiwa zuciyarsa farmaki ,take km kirjinsa yashiga bada wani irin sound kmr ana masa bugun makiya muryarta a matukar sanyaye tace hey mrs man am talking to you ko baka da bakin yin mgn ne? takarasa mgnr zuciyarta na tsalle da bugawa at the same time numfashinta na kokarin barin gangar jikinta ..a sheke ya juyo kirjinsa na pat pat take Zuciyarsa da ilahiri jikinsa suka amsa suna yi masa kuuuuuwa. yayi shiru yana karemata kallon tsab da mayatattun idanunsa masu bugar da zuciya tare da raunata ruhin ma'aboci kauna, sannan muryarsa a harzuke yace mgnr tawa ta tafi koyon sallama ..fuskarta dauke da murmushin takaici sai yaga tashafa sumar kanta dake dunkule guri daya atsakiyar kanta alamun taji kunya kafin ta sake hanzarin yin wata mgn yace look i don't have any issues with you so plz get the hell out of my life ok!! bar nan yanzu kafin na tarwatsa miki rayuwa stupi kawai .
sai yaji tace am very sorry sir dama ina son muyi wata Yar karamar mgn ce da kai ko zaka bani dama takarasa mgnr
muryarta na craking. kallonta yayi a yatsine tare da cewa no sannan yakama hanya yasoma tafiya zuwa gurin daya yi parking din motarsa .
yayi mata key ya Bude murfin yashiga ya zauna amazaunin direba..
yana kallonta tsaye tana kallonsa, hk kawai ya tsinci kanshi cikin matsanancin faduwar gaba me tsanani ,kallonsu yacigaba yi ahankali daga inda yake dukansu shigarsu iri daya babu wata banbanci tsakaninsu sai ta fuska daya fara ce sol Wanda farinta har daukar ido yake .
yayinda dayar takasance black, hatta yana jikinsu na rashin kiba is the same.
tsaki yaja abayane yana takaicinta daganinsu irin matan nan ne marasa kamun kai da tarbiya .
kalli shigarta dan girman allah bazaka taba cewa kalmar hausa fulani,zata fito cikin bakinta ba. motarsa yatayar yayi gaba abinsa sai dai still zuciyarsa na harbawa wanda yarasa dalilin jin hk tunda yake bai taba samun kanshi dajin wannan yanayin faduwar gabar ba.
take suma suka kunna machine dinsu mubishi muga inda zashi .
ki bari muje gida first musan abinyi bibiyarsa bazai bata fishemu ba at least munkai 2 months muna biye dashi ,atsawace su'ad tace mubishi kawai that's what I want from you.

Daga nan kai tsaye gida ya wuce, su'ad na biye dashi yana sane da shi din suke bi amman ya share har sai da suka tabbatar daya shiga gida, sannan sukayi tafiyarsu.

Wata irin gajiya yake ji da shigarsa gidan, don haka kaya kawai ya ragewa jikinsa ya fada bathroom , yayi wanka sannan ya fito ya sake shiryawa cikin kananun kaya,
Yanajin yunwa, kasancewar ammi bata nan sunyi tafiya zuwa sudia daga nan har dubai zasu hado kayan auren zeey. dan haka fita ya sake yi zuwa wani haddaden restaurant rose star cin abinci, su su'ad na hanyar komawa hotel din dataga ak domin cin kaniyar koce yarinya ce ,taga wucewarsa, ba shiri tace ore ta juyar da machine tabi bayansa

Tana biye dashi har zuwa restaurant din, yayi parking ya shga tabi bayanshi ta bar ore waje zaune akan machine.
, can nesa dashi tasamu gurin ta zauna.
Waiter yazo yana tambayarta mai take buqata,
Ta nuna mishi bayanshi da yatsan hannunta
"ka kawo mun duk abinda aka kaima wancan saurayin"
Ba wai don taci ba, kawai sai dan tana son taga wanne irin abinci zai ci .

Daga nesa take dashi, amma duk wani motsinsa tana gani. tsura mishi fararen idanunta sosai yana cin abincin,
Can yakai loma a baki, yaji ya faraa kwarewa, da sauri ya zuba ruwa a cup yasha,
Hakanan yakejin zaman wurin bai mishi ba, jikinshi na bashi lallai kallonsa ake,
Ya juya a hankali saitin inda take,zaune da sauri ta daga wayarta ta kare fuskarta kaman tana latsa wayar ya mike yakaraso har inda take yasa wayarsa yana kawar da hannuta yana kallonta itace stil ..
shock tayi da ganinsa dan batayi tsammanin zai iya karfin halin yin hk ba .batare da yace mata komai ba ya juya yayi tafiyarsa kawai.


byn kwana biyu

da wuri su'ad ta shirya daidai lokacin datasan yana toffice tayi parking din
dinta a hanyar datasan yana bi .yau kam ydan makara dan hk sosai tana jiransa har ma tasoma tunanin ko dai yarigada ya tafine ta niyar tada machine ta iske shi office .
sai ga motarsa tazo ta wuce ta gabanta da sauri ta tayar da machine dinta tabi bynsa. tana lura dashi bai tsaya koina ba sai wani guri kawai daya tsaya yabada sadaka tacigaba da binsa yana sane da duk wani motsinta yana kallon yadda take dojewa gurin binsa .
murmushin takaici kawai yayi iya lip's dinsa yacigaba da driving dinsa aranshi yace lallai yarinyar nan bata da aikin yi.

sanda ya isa office din ya iske sectary dinsa ya budewa onye office dinsa tana zaune zaman jiransa yana murda kofar yashigo suka hada ido daita ta sakar masa tautausar murshi a dake yakarasa shigowa batare da ya mayar mata ba. ta taso tana karairaya da salon karuwancinta datasaba yimasa ta sakalo hannuwanta duka a wuyansa ta dare jikinsa tana goga masa tudun nonuwanta a fuska kwana biyu honey kaki zuwa inda nake kasan bazan iya daukar lokaci me tsawo ba batare da dana sanyaka acikin idanuna ba i miss you honey ya dauke cak suna musayar murmushi saman makeken table din office dinsa ya daurata ta hade bakinsu guri daya tashiga kising dinsa cikin dabara ta ajje takardun dake hannunsa ta zagayo da hannunta tana shafa kirjinsa .
sai lumshe idanu suke suna fidda numfashi tare da cigaba da romancing juna .

su'ad tana isowa office din nasa cikin sa'a bata tarar da sectary dinsa ba gashi km bai karasa rufe kofar ba sbd zumudin da sauri takarasa wurin karamar kofar da bai karasa rufewa ba tana hangensu shi da onye tana kallon duk abinda suke aikatawa zuciyarta sai dukan uku uku take ko motsin kirki ta kasa yi agurin gumi ne kawai ke tsatsafo mata ta koina ajikinta tare da hawayen takaici .wayyohhly Allah me yakamata nayi akan wannan banzar matar da sanyi Safiya ban karya da komai ba sai da bakinciki. meyasa ka kasance mane min mata.

jitayi an tabota ta baya ta kasa juyowa sai da aka kara tabota sannan ta dan juyo ganin sectary dinsa ne sai da gabanta ya fadi rassss me kike yi anan?
ni? yace eh ke din gurin oga nazo shine km kike lekensa ta nan?
tacigaba da inda inda ganin yana neman yimata ihu ya janyo hankalin ak zuwa garesu yasa tayi saurin barin gurin ya bi bayanta yana faman balbala mata fada sai kara sauri take kmr zata tashi sama .
jin hayaniya ya sakashi lekowa ta window office dinsa bai ga fuskarta ba sai dai bayanta daya hango tana ta sauri ta bar gurin ya tabe bakinsa. domin ya tabbatar da mayar yarinyar ce.


yau ma kmr kullun sanye take cikin wasu kayatattun kananan kaya wando pencil jeans da rigar long-sleeved wacce ta dan dane hannu rigar tmkr yadda maza kanyi. fitinan ne kamshi turarenta oud moond ne yasoma kaiwa hancinsa tare da zuciyarsa farmaki na wuncin gadi Wanda hkn ya haddasa masa jin mummunar faduwar gaba , da sauri ya dago mayatattun idanunsa zuwa daidai saitin inda zuciyarsa tafi bashi tana gurin.ita din ce kuwa kmr yadda yatsammani...
       Kyawawan mayatattun idanuwanshi wanda suka wadatu da matsakaita gashin ido kamar yadda giran idanunsa yake cike da yalwa gashi masu matukar kama da wanda ke jin bacci.
wanda kusan koda yaushe hk suke a lumshe..
kusan su biyar ne tsaye a farfajiyar sabon ma'aikatar daya bude sai dai ,shi daya ne kawai ya bambanta cikin tarin mutanen dake zagaye dashi yanayin shigar dake jinkinsu.iri daya ce gabadayansu sanye suke cikin shigar suit .
mayatattun idanunsa ya tsurawa kyakkyawar fuskarta me dauke da sihirtaccen kyau da annurin murmushi.
sosai yake kallonta ya kasa dauke idanunsa akanta yayinda zuciyarsa ta cika pam da matsanancin mamaki .

meya kawo nan km... ?

watazo nema anan ?

meyasa duk inda naje take biye dani?

tmbyr dayasoma aikawa zuciyarsa kenan wanda ya kasa samun amsarta.
fararen idanunta kurrrr ta daura bisa fuskarsa tana jin dadi mara misaltuwa a cikin ranta.
tsawon lokaci suka dauka suna kallon junansu batare da sun janye idanunsu cikin juna ba .
zuciyar kowanensu cike taf da al'amura daban daban .
"bangaren zuciyarsa ak cike take da matsanancin tsoro da mamakin yarinyar. yayinda su'ad zuciyarta Ke cike da matsanancin farinciki .
,kusan atare suka janye idanuwansu. yayinda ,gaban ak ya shiga faduwa da sauri sauri zuciyarsa na harbawa ,kasa tsayuwa yayi agurin .
,hakika duk inda yarinyar nan ta fito babu tarbiya atattare daita tantiriyar mara kunya ce da rashin ciwon kai.
kwata kwata bata da kamun kai..
kalli yadda ta tsareni da mayun idanunta jikinta ko mayafi babu ...
tsaki yaja yana furzar da iska me zafi ta bakinsa, ahankali ya juya jikinsa na tsuma gabansa na tsananta faduwa ya bar wajen, batare da sake cewa mutune dake tsaye tare dashi komai ba. kai tsaye
evalato ya nufa .Sectary dinsa na biye dashi abaya da wasu file rike da hannusa.
yana isa saman da office dinsa yake .
sectary dinsa samsu yayi saurin karasowa ya bude kofar office ak yashiga tare da kullewa shima ya shiga cikin office. yana biye dashi still.
      zama ak yayi akan kujera yashiga jujuyawa ahankali ahankali yana sauke numfashi.
tunani suka soma zuwa masa daki daki akan yarinyar wanda yarasa dalilin shigarsa damuwa a duk sanda ya daura kwayar idanunsa akanta har yau ya kasa fahimtar komai akanta da abinda take nufi dashi.
lallai yana da buqatar nazari da karin bayani akanta ko zai fahimci me take nufi.
, da duk inda yake tana biye dashi .....
maganganunta ya tuno data gaya masa a bich sanda ta reskeshi .
ka taimaka ..........
,ka taimaki rayuwata wajen gyarata ....ka dawo min da farincikina dana rasa arayuwa ....
naunauyen ajiyar zuciya ya sauke da karfi kamar yaya kenan mgnrta yake nufi ? ya taimaka ya taimaki rayuwarta,to take nema daga ggareshi shi da kwata kwata bai ma taba daura idanunsa akanta ba sai a dan lokacin nan tsaki yaja da karfi
da ala'mun wani mummunan abu take aikatawa mara kyau .
wanda takeso .
tsundimashi ciki har da take neman taimakonsa ?
,amma ita a wa? ina ita ina ni mace irinta mara kamun kai da aji sam bata da wanna power dan ko tsayuwa bazan taba iya yi daita ba.
yayi mgnr abayyane.har samsu na iya jiyoshi wanda ya daura file din hannunsa bisa kan makeken table din dake zagaye da kujerar da ak ke zaune akai.
sannan muryarsa na rawa yace boss naga kmr kashiga damuwa akan wancan stupid girl din, karka damu fa irin yan iska yaran nan ne masu neman maza da karancin shekarunsu daganinta ma yar smoking ce sannnan... wata irin razananniyar tsawa ak ya buga masa ta hanyar katseshi you are very stupid samsu.. who the hell you think you are da zaka tsuma baki cikin abinda bai shafeka ba ? waye kai dan ubanka? meye matsayinka bakinsa na rawa yace sectary
wama yace maka na damu daita..? sorry sir am very sorry for the... shot up Pack's ur things and leave before I sac you idiot
jikin samsu na rawa ya sake bashi hkr yana kokarin barin cikin office din. sosai tunaninsa da kwalkwaluwarsa ke neman daurewa .
yasa ya ciza lip's dinsa na kasa da karfi har yana jin radadin gurin.
kenan yanayin dayake ciki yanzu ya nuna ya damu daita ne ko me? furzar da iska yayi tare da Mikewa tsaye ahankali cike da sanyi jiki yana sake gyara zaman tear dinsa gurin window ya nufa gabansa ne yaba rasss yashiga dukan uku uku sakamakon ido hudu da yayi daita tana nan tsaye kmr dazu sai dai zuwa yanzu idanunta na kan window office dinsa, wani irin mamakin ne ya sake kamashi, yayi shr yana tunanin abinda yakamata yayi mata dan tafita harkarsa ta daina bibiyishi ....
a matukar fusace ya saki labulen window ya juyo ahankali ya fito daga office din .
yana saukowa kai tsaye gurin datake tsaye hannuwanta duka zube cikin aljihun wandonta ya nufa. tana ganin yanayinsa zuciyarta tashiga beting da tsalle tare da yin addua cikin ranta allah yasa ba wani abu zai yi mata ba.
yana gama karasowa zuwa inda take ya fixgo hannuta da iyakacin karfinsa sai get din ma'aikatantar.
ya turata waje yana huci yasoma mgn yana nunata da yatsansa bana son sake ganin wannan fuskar taki" karki sake ki kara takowa zuwa inda nake"
meye hadinki dani arayuwa kike biye dani? muryarsa a harzuke ya kira securities din bakin get atare suka iso inda yake tsaye suna kamewa guri daya daga yau cikinku duk wanda yayi saken da yarinyar nan ta sake sanyo kafafunta cikin 'ma'aikatar nan abakin aikinsa .ok sir angama boss suka hada baki gurin cewa hk .
su'ad tayi murmushin takaici wanda sake fito da ainihin sihirtaccen kyawunta tana kallonsa tana jin yadda tarin kaunarsa ke sake huda kahon zuciyarta batare da bata lokaci ba securities suka yi kanta suna bata umarnin barin gurin .
wani cikinsu na kokari kai hannusa jikinta ak yayi saurin runtse mayatattun idanunsa tare da dunkule hannusa ya tura cikin aljihun wandonsa yana jin bugun zuciyarsa na tsananta.
karka sake ka bari wannan dirty hands din naka yakai jikina ........ jin hk yasa ak sauke naunaiyen ajiyar zuciya tasoma takowa atsanake kirjinta na bugawa da sauri sauri wannan security din yasha gabanta yana cewa oya live here now before I get off at..... ai bai kai ga karasa mgnrsa ba yaji ta dauke shi da wani gigitaccen mari kabarni nace.... tayi mgnr muryarta na craking kallonta gabadayansu suka shigayi har uban gayya.
bata bari sun gama mamakinsu akanta ba ta isa inda ak yake tsaye kikam kmr andasashi cike da al'ajabinta da karfin halinta tattare da jarumta ,gabansa ta tsaya har suna iya shakar numfashin juna da kamshin turaren da kowanensu yayi amfani dashi take zuciyoyinsu tashiga bugawa atare karka ce baka son ganin wannan fuskar tawa domin mahimmancinta gareka ya wuce hk. karkayi tunanin zaka iya tserewa daga gareni dan ni nakasance inuwarka ce..... daga yau nasan zan hana zuciyarka tsukuni da kake bukata arayuwarka har sai nasamu abinda nake so daga gareka. baka isa kamin iyaka da duk inda nasan zanganka ba...
tana karasa fadar hk ta juya cike da matsanancin tsoro da sanyi jiki dan duk wannan mgnr datayi zuciyarta cike take fal da matsanancin tsoro..

bynta ak yabi da kallo har zuwa sanda ta dane kan lefan dinta tabashi wuta ta bar gurin jama'ar gurin na aikin kallonta.

maimakon yaci gaba da tunanin iskancin yarinyar sai kawai ya zarce da daukan wayarsa da'ake ta kiransa tun mintinan da suka gabata.yana juyowa kowa dake gurin ya waske suka kama gabansu .
ahankali yasoma tafiya cikin takunsa me cike da natsuwa tare da haiba yana amsa wayar. gefe daya km bugn zuciyarsa na sake nunkuwa. musty ne yakirasa.... aboki kwana dayawa gabadaya ka sake halaye ace yanzu sai muyi wata da watanni bamu hadu ba.. ak ya shafa kwantaccen sumar kanshi zuwa fuskarsa. kai dai Bari friend al'muran ne babu sausauci ga km yanayin aiki, yanzu how many weeks ya saura bakin? ak ya runtse mayatattun idanunsa yana sakin ajiyar zuciya da dan saura at least yanzu sauran 2months ok Allah yanuna mana. ameen. ka fito zuwa anjima mu hadu a spankys man ..
kai da wuya zuwan nan nawa .
gurin onye jikar iyamurai zaka tafi dan nasan baka da gurin dakafi dokin zuwa kmr gurinta.
a matukar zuciye ak yace gun uwarta zani me ka daukeni ? bani da abinyi sai na zuwa gurinta? ai kai din ne sai a slow dakata mlm ak ya katseshi karka dameni tunda nace banzuwa ka barni man ko dole ne? babu dole amman ka tausayawa yarinyar mutane da zaka aura dan gsky ni ina mugun jin tausayin zeey da har ta nacewa aureta.
idan yarka ce sai ka hanani aurenta yakarasa fadar hk tare da hangin din kiran .
ya koma mazauninsa ya zanyo files files da wasu document wanda suke bukarta sanya hannunsa . yasoma sing dinsu 1 byn 1 .
duk wannan aikin dayake ziciyarsa makale take da tunanin yarinyar da magangunta gareshi . zuciyarsa tashiga rawa rawa anya yarinyar nan ba aljana bace?
kokarin kawar da tunaninta yake amman hkn ya cutura cike da matsanancin damuwa yakasa aiwatar da aikin gabansa sakamakon tunanin yarinyar dake zuwa masa.

karfe hudu daidai ya komai gida gabadaya yaji damuwa tayi masa yawa kasancewar su ammin basu dawo ba km zamansa gida zai iya saka tunanin wacen banzar yarinyar ya dameshi .
    ganin shida tayi ga gidan shr babu kowa sai shi kadai da me aikin ammi dake part dinsu sai masu gadi ya sanyashi yanke shawarar yasamu su musty a spankys . wanka yayi ya shirya kanshi cikin haddadu wando thrre quarter baki iya gwiwarsa da white t shirt yasanya facing cap idanunsa manne da bakin glass ,sai kamshi turaren ameer al aud ne ke tashi a ilahirin jikinsa. ya fito wajen .
inda motocinsa suke ya nufa yashiga daya daga ciki yabar gida. direving yake ahankali yana jin music a hk har ya iso
a bear parlour .
spankys cike take makil da mutane iri iri ak tun daga nesa ya hango musty da Malik da wasu abokan holewarsu ahankali yaso takowa zuwa inda suke.

su'ad wace aka sanarwa da zuwan ak spankys tazo tare da ore amman waje tabarta ta shiga ciki sai dai duk inda ta sauke fararen idanunta domin ganinsa bata gansa ba sai wasu mutane dabam take gani
suna kai kawo agurin wasu a zaune wasu atsaye rike da kwalaban bear suna kurba suna rawa sakamakon sautin kidin dake tashi agurin.
duk da kasancewarta tantiriyar kanta taji wani yanayi na dabam a sansar jikinta kmr zata tattaka mutanen dake gurin haka ta dinga ji.
mutane ta dinga ratsawa ahankali tana wucewa hannuta rike da tabar wiwi tana zuka ahankali har sanda ore takirata take gaya mata taga shigowar ak yanzu cikin gurin .
take tayi cilli da sauran tabar wiwin hannuta tana kore warin hayakin tabar ajikinta tare da ciro sweet lemon plus ta bare ta jefa cikin bakinta . dube duben inda zata ganshi take ko ina harabar gurin cike yake makil da abokan shashanci ana kai kawo.
,kowa ka ganshi cikin maye yake.
daga gefe guda ta hango tarin abokan ak ciki har da wani dan ungwarsu ,suma sun ganta ganin bataga wanda tazo gurin dan shi ba yasa ta juyo da sauri domin juyowa tabar gurin
       Batayi aune ba sukaci karo da shi dai dai lokacin daya kusan karasowa garesu kanta ya daki daidai saitin kirjinsa ,tayi luuuuuuuu zata fadi ta koma ta fada saman lafiyayen kirjinsa, me cike da tarin yalwan gashi .
zuciyarsa kamar zata fito waje gane kowacece kwance a saman fadadden kirjinsa .
wani irin shock zuciyarsa tayi .ahankali ya furta you again...
wani abu ya dinga ji yana mamaye masa ilahiri gangar jikinsa abinda bai taba jinsa ba kenan atsakaninsa da wani bil'adama. a iya tsawon rayuwarsa.
yunqurin janyewa,tasoma yi daga faffadan kirjinsa amman ta kasa samu nasara yin hk sbd hannunsu dake makale cikin juna .
wani irin firgitaccen bakon al'amarine yabakunci ruhinsa a sanda yake duban cikin kwayar idanuwanta,masu matukar haske da kassara ilahirin jikin duk wanda yayi nasarar kallon cikinsu. kamshin turarenta da kamshin tabar wiwin datasha ke kaiwa hancinsa farmaki hkn yasa take yasoma jin ransa yasoma baci zuciyarsa tashiga dagulewa gabadaya yanayinsa ya sauya wannan kamshin nata ya buwayi hancinsa da zuciyarsa.
       So yake ta sakar masa hannu ko don idanuwan mutane da ggbdy ya raja'a akansu ,uwa uba tsabar tsanar da yayi mata .bazai taba barin tararyarsu tayi tsawo ahalin yanzu .
cike da natsuwa
yayi yunqurin zame hannunsa cikin nata amma abu yaci tura tana tsaye kyam rike da hannushi tana murzawa ahankali tare da kallon cikin mayatattun idanunsa Wanda zuwa yanzu cike suke da bacin rai da rudaani iri iri babu abinda take hangowa acikinsu Illa tsagwaron tsanarta da kiyayyarta tare da tsansar kyamarta. dubanta,yake kmr yaddda take kallonsa batare da nuna wata fargaba ko tsoro ba zuciyarta dake harbawa tacigaba da akinta datasaba, sbd wani irin kwarjinisa daya cika wajen ,idannu mutane gbdy ya koma kansu gashi ita kwata kwata babu alamun kunya atattare daita koda zasu cigaba da tsayuwa a hk bazata damu ba. bakinciki takaici haushinta da matsananciyar tsanarta suka taru suka dugunzuma zuciyarsa har yasanyashi cewa
"mayya ki sakar min hannu" cikin izza da kamewa ya motsa bakinsa..
Dago fararen idanunta tayi ta sake watsasu cikin nasa ,duk da yadda kirjinta ke mahaukacin bugawa,lumshe mayatattun idanunsa yayi ya budesu fesss akanta yana janye nashi idanun daga kallonta.
,bata taba ganin nmj me lumtsatsun kwayar idanu ba kamar nashi .
ta raya hk cikin zuciyarta .
kana taja ,tsaki a fili sannan ta soma sakin hannunsa ahankali har ta zare hannuta cikin nasa .
tsakin data ja masa yayi mugun hassalashi bai san sanda yasoma yaryarfa mata mari ba sannan yasoma mgn cikin zafin rai
polish girl ban daukar iskancin da rainin hnkl ni zaki jawa tsaki akan shirmen banzanki " ya fada yana duban cikin idanunta..
idan kina haukane ki dawo cikin sense dinki.
daga yau karki kara kuskuren barin dirty body dinki ya rabi jikina.
ta kalli jikinta up and down sannan ta sake meida idununta kanshi ta tsuru masa fararen idanunta ,ita ke iskanci da shirmen da hauka ga maruka ?,abun yayi matukar bata haushi,kmr ta rama marukan dayayi mata ,amman sai ta fasa kawai ta tsinci kanta da zabga masa wata uwar harara.
duk da yadda kirjinta ke bugawa hkn bai hanata yin masa mgn cikin tsiwa ba.
"Kai..kaine babban dan iska shirmamme mara hankali da tunani sai ka dinga lura tunda ba ni

3 Comments On SAI KA AURENI DOLE
avatar
zainab-ishaq

1 year ago

Reply

Love it ????????

avatar
zainab-ishaq

1 year ago

Reply

Yes and I want to download it

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to zainab-ishaq

In order to download you have to subscribe for our package at https://tnovels.com.ng/subscribe

Please Login or Register in order to submit comment