Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tsaye ya zarce inda motarsa take nima nasoma kokarin wucewa inda tawa motar take naji ya kira sunana saleemat ...na dawo na tsaya ina jiran naji me zaice min amman naji yayi shiru sai motarsa danaga yashiga ya zauna amazaunin direba tare da yiwa motar key .
ya kalloni ya tsura min kyawawan idanunsa yana kare min kallo wanda bansa meyasa yake yawon kallona hk ba.
yayinda nima km gbdy a tsorace nake dashi dan hk na meida kallona gefe sai dai zuciyata cike take da aika masa kallo na musamman.
" ahankali naji sautin zazzakar muryarsa ta doki cikin kunnuwa zagayo ki shigo .
nace uhmmm nima nazo da motata ,ke.. banson salo nace ki shigo yayi mgnr a dake sannan fuskarsa a daure. wanda yasa har naji zuciyata na kokarin bugawa .
waige waige nasoma ko zanga wanda nasani domin banason wani ido yagan ni nashiga motarsa.
ganin banga wulgawar kowa ba yasa nazagaya dayan bangare wanda oready ya bude min kofar nashiga na zauna.
" jikina ya sake yin sanyi muryarta a matukar sanyaye nace yanzu wazai kai min motata gida?
banza yayi min ya miko tafin hannunsa batare da ya juyo inda nake zaune ba yace bani key din motar.
babu mutsu na mika masa, yaja motar daidai inda motocin dalibai suke ya tsaya ina motartaki ?
na nuna masa sai da juyo ya kalleni ganin irin motar danake hawa ,sbd a wannan lokacin sai wane da wane ke hawanta, sannan ya fige motar muka bar cikin makaranta.
" ina jiran naji ya tmbyeni unguwar da nake ko ya dauki hanyar zuwa cikin gari kawai naga ya dauki hanyar dazata kai mutun zuwa sayme border.
ina ganin hk nayi saurin waigowa inda yake zaune fuskar nan tasa a hade tuki kawai yake yana cin magani.
tsorace nace ina zamuje ne hk?
batare da ya kallo inda nake ba.
kiyi shr kawai kicigaba da zama, na sake tsorata ka gaya min ina zaka kai ni.. ...
dan Allah ka gaya min ina zamu ,ina jin zuciyata na min wani iri shiiiiiiii banason yawon tmby ni dai kagaya min ina zamuje... wani irin wawan burki yaja da karfi sannan ya kalloni ransa a matukar harzuke.
a fusace yace saukar min daga cikin mota muryata na rawa nace wayyohhly me faru? sauka nace meyasa kace na sauka anan alhalin hayar cike take da tsoro?
nace ki sauka na daukeki zuciya pal da gsky sai wani tmby kike ina zan kaiki ina zamuje..ina zamuje kmr zan cinyeki banason irin hk jikina na kirrrm hk na fito daga cikin motar na tsaya na juyar da fuskata gefe titi tare da rungume hannuwana duka akirji.
" ki tsaya anan ....
nan minti 5 ina zuwa yaja motar a guje ya bar gurin ni km ya barni zuciyata cike da matsanancin tsoro fiyye da lokacin danake cikin motarsa. byn motar na juyo nabi da kallo har ya karya kwana, take jikina yasoma rawa rawa tsoron dake boye cikin zuciyata ya bayyana idanuna suka cicciko da ruwan hawaye wannan shine lokaci na farko dana tsinci kaina a irin wuraren nan.
ban taba xuwa ba asalima bana fita koina daga gida sai school ko gidan dangi dan ko islamiyya bana zuwa tun tasowata sai dai malami yazo har gida yakoyar dani .
ahankali na furta wayyo..hhly..
Allah kasa ba barina yayi anan ba ?
idan hk takasance yaya zanyi gashi komai nawa yana cikin motata hatta wayata ban riko ba hawaye ne suka soma sintiri akan kuncina na juya gabas na duba yamma babu kowa sai tsirarrun motoci dake kai kawo .
na sake kai dubana ga hanyar daya bi nace idan bai dawo nan da minti biyar Allah Allah kasa motarsa tayi bindiga na fadi mgnr ina kuka komai na tuna alokacin sai km nayi saurin cewa Allah bazai sa motar tayi bindiga ba take km zuciyata tashiga yi masa adduar dawowa lfy sbd a ganin zuciyata taufeek wani bangarnta ce km abar sonta ce bai kamata tayi mata mugun fata ba. sannan shi din alokacin wani bangarene na rayuwata ina tabbatar miki ban taba jin abinda nake so aduniya byn iyayena da sukayi sanadiyar zuwana duniya ba sai taufeek har yanzu sonshi na nan acikin raina.....
tunda na tsurawa hanyar dayabi da mota ido ban dauke idanuna ba sannan ban motsa ba byn kmr minti goma sai gashi ya dawo wanda zuwa lokacin har na soma yunkurin tsaida motoci da hannuna batare da idanuna na kansu ba.
yana karasowa inda nake yashiga zabga min harara me kike kokarin yi?
nayi saurin girgiza masa kai ala'mun babu komai. ai sai ki shiga mu tafi ina shiga yaja motar ahankali batare da yayi mugun gudu ba sannan km bai ce min komai ba hanyar komawa cikin gari ya dauka .
ina ganin hk nayi saurin sauke naunauyen ajiyar zuciya har ya juyo ya dan kalleni kadan ya dauke kanshi .
wata hanyar ya dauka nayi saurin cewa ba nan ne hayar gidanmu ba.
ya min banza ,na rasa yadda zanyi da rayuwa kai tsaye gidan gona naga ya nufa dani nan fa cikina ya sake durar ruwa gbdy atsorace nake dashi duk da irin matsanancin son danake masa .
banason kebancewarmu dashi.
muna isowa ya faka motarsa yace na fito nace barni anan kaje ka dawo . ke.. fito karki batamin lokaci.
na fito naga ya dauki hanyar daji km yace na biyo shi tafiya mukayi sosai ina biye dashi abaya ,amman ilahirin jikina babu inda baya rawa ji nake jikina kmr banawa bane kafufuwana kuwa daga su kawai nake ina isowa wajen wasu korayen bishiyoyi masu shege tsawo wanda yanayinsa yayi kmr bukka naga yasoma waige waige ni kuwa tini ina can nesa kadan dashi sai daya gama waiwaigawa ya sauke kyawawan idanunsa akaina yana karemin kallo sama da kasa sannan yace min tawo mushiga cikin daji muyi wata mgn .
"lokace ne hankali yayi matukar tashi duk inda muka baro bai isa ayi mgn ba sai atsakiyar daji wayyohhly nashiga uku na furta cikin raina nashiga aika masa da kallon tuhuma ni salema meyasa nabiyo shi?
meyasa tun a makaranta ban tsare masa ba koda kuwa ta hanyar guduwa ce?
me ma ya dawo dani makaranta a irin wannan lokacin ?
hk nayita jerawa kaina tmbayoyi muje ko ya sake maimaitawa byn ya tsareni da idanunsa masu firgitarwa tare da juyawa yasoma tafiya muryata cike da matsanancin tsoro nace uhmm ni gsky... yayi saurin juyowa da sauri ya kafe da ido, nayi saurin sunkuyar da kaina kasa sbd yadda yake kallona idanunsa zasu iya karyar min da zuciya.
gsky me.....? ya tbmy ni still idanunsa na kaina nace agida ance min idan samari suka ce mushiga daji muyi mgn kada na sake na yarda inji mama na karasa mgnr ina kamkame jikina da hijabina dake sanye ajikina ..
uhmmmmm to ni mamata tace na dauki budurwa acikin motata ne?
araina nace kai kasa kanka wannan wahalar muje babu abinda zan miki mgnr da zangaya miki me mahimmace ina bukatar natsuwarki sannan irin wuraren na saka natsuwa cikin zuciya da farinciki ki natsu ki saki jikin babu abinda zai faru.

wani guri muka shiga me shegen kyau da daukar hnkl zagaye wajen da korayen flowers takoina acikinsa har da kujeru guda biya daya 2 siter daya km 1 siter waje ne me matukar shiga rai da tsayawa mutun a xuciya ina tabbatar miki ko yanzu na koma kasata banida wajen zuwa sai gurin ,domin debe keya da tuna baya.
waje ne da bazan taba mantashi arayuwata ba kullun kwana duniya ina makale da muradin sake kasancewa a wannan gurin .
waje ya nuna min da hanunsa zauna ,na zauna cikin dari dari shi km yana tsaye yana kallona ko tunani abinda zai gaya min yake ni dai bansan tunani dayake ba.
can km cike da sanyin murya naji yakira suna saleemat ....nace na'am ni ba yaro bane domin ina da mata har da "da" daya.
kalmar datasa gabana yaba rasssssssss take km kirjina yashiga dukawa, na dago idanuna ahankali ina kallonsa yasoma kai kawo agurin ki daina mamaki nace ina da mata har da yarona muhmud ,sannan mata dayawa sun sha nuna min kulawa tare da kawo min kansu da nuna min soyayya amman sam babu wace taba shiga cikin zuciyata amman ke km narasa dalilin dayasa kika hana zuciyata tsukune da samun natsuwar danake bukata .
dan daban nake jinki ajikina wanda bansa me hkn yake nufi ba ...
raina yasoma baci sbd cewa da yayi, yayi yan'mata dan hk a hanzarce na katseshi ta hanyar cewa da yan'mata dayawa suka kawo maka kansu kowace kunyi soyayya kenan ya girgiza min kai tare da lumshe min kyawawan idanunsa sannan yace kar tunaninki yaje inda bai dace ba, ya janyo dayar kujerar kusa dani ya zauna muna fuskatar juna tare da kamo hannuna cikin nasa .
batare da bata lokacin ba na zare hanuna shi km ya hade hannuwansa duka ya daura saman fuskarsa ,iya idanunsa kawai nake iya gani wani yanayi me cike da matsanancin shauki na tsinci kaina ciki alokaci danake kallon cikin kwayar idanunsa sbd ganin yadda yanayinsu ya canza.
ya sake kiran sunana saleemat nace uhmmm dan bazan iya amsawa ba ina matukar sonki... .....na zaro ido waje sbd ban tsamaci fitowar wannan kalmar daga bakinsa ba.
abinda na dade ina muradin kasancewar faruwarsa kenan wani irin farinciki ne ya rufeni na sunkuyar da kaina kasa ina wasa da zara zaran yatsun hannuna tare da murza zoben gwal din dake makale da yatsana daya.
ina matsanancin kaunarki siffofunmu na zahiri sun dace gashi km duk muna son karatu tin ina karami nake matukar son karatu sbd hk ne ma yasa na zabi koyarwa bugu da kari mun dace da juna ki bari more rayuwar soyayyarmu kawai.
duk da farincikin dana tsinci kaina ciki amman hkn bai hanani cewa ni ban yarda da wata soyayya ba.
ni ma hk ban yarda daita
ban amince da duk wani shafika na soyayya ba sannan rashin ganin tasirin hkn ne daga gareki yasa tun lokaci haduwata dake naji kin birgeni wanda hkn yake kokarin dakushe farincikina.
kace kana da mata......? uhm ina mata har da "da" sake maimaita abinda ke taba min zuciya da tayar min da hnkl yayi nace kenan ba kai ka kai kanka gareta ba kace kana sonta ba.
wannan sirrin ne tsakanin ma'aurata sai dai zan gaya miki akwai zumunci ne me karfi a tsakanina da *matata*
abinda nasani kina da matukar mahimmanci arayuwata.
zuciyar taufeek ta kamu da mugu mugun matsanancin sonki,sannan tana son kasancewa tare dake kina birgeni dayawa kin shiga raina batare da duba kyawunki ba .
da sauri na kallosa tare da tsare shi da idanuna dan tun sanda yasoma mgnr matarsa na kawar da idanuna akansa nace uhmm kmr ya kenan kana nufin bana da kyau?. yace ummmm ba dai can can ba amman ba wani abu bane yakarasa mgnr yana sakar min tsadadden murmushinsa .
hade raina nayi sosai har da turo baki ina aikin maka masa harara sannan na sake dauke idanuna akansa na juyar da kaina gefe nacigaba da kallon korayen flowers murmushi ya dinga yi wanda daga karshe yasoma dry me dan sauti yana kallona.
shiru nayi na wasu lokuta ina tunani sannan najuyo da sauri inda yake zaune yana kallona na fuskanceshi nima nace amman ko bani da kyau ina da dabi'u masu kyau ba?
uhmm ..ya fada yana sake yin murmushi ya sake matsowa kusa dani sosai ya kamo tafin hanuna cikin nasa wannan karon kasa kwacewa nayi sbd yanayin rikon da yayi min .
nace yaya dabi'ra tawa take.?
yayinda da kike ke kadai uhm ayayinda ke kanki kinsa babu wanda yake kallon yanayinki alokaci duk abinda kika aikata a moment din shine asalin halinki na gaskiya.
ni dai nasan halinki amman bazan iya furta miki su ba, na gyara zama ina cigaba da kallonsa yace nasan yadda kike alokacin hkn yasa nasoma sonki.. ohhh sai km nayi shr nakasa furta abinda nayi niyyar furtawa tare da zabga tagumi can km nace ta ya zanyi na fahimci dabi'unka?

me kakeyi yayinda kake kai kadai ?tsaki yaja tare da dafe goshi da hannunsa daya Dayan km still na rike da hanuna to komai sai na fito na bayyana miki ki cinka man ta yiwu nayita yawona ba sanye da komai ajikina ba ko inta kallon bluefilms wayasani .
nayi saurin runtse idanuna a irin wannan lokacin kwbabbiyar dabi'ar muce take bayyana yayinda muka nazarci wannan dabi'ar shine zamu gane asalin halinmu ,ni dake yanxu dai bagamu tare ba muyi wani abu ba daidai ba?
nace uhmm ai daman nace hk nagaya miki cewar idan mun shigo babu abinda zai faru.
gashi kinga babu abinda na miki.
nayi murmushi har wushiyarta ta bayyana wasu zantuttuka mgnr iska ce kawai wani lokacin idan nmj ya nemi kebewa da mace ba wani abu zai mata ba ta yiwu wata damuwa ce aransa bawani nufi ba.
yanxu dai ki gaya min taufeek yasamu karb'uwa acikin zuciyarki ko kuwa ?
na lumshe idona sannan na budesu ahankali nace sai nayi tunani akai.
wani tunani zakiyi alhalin nasan kina sona....
karkace hk shakuwa dabam soyayya dabam shakuwa ba itace soyayya ba ta yiwu kaji nace bana sonka ta yiwu km zuciyata ta amincewa hkn ,na karasa mgnta ina mikewa tsaye sakamakon duhun danaga gurin yayi na kai idanuna kan agogon fatan dake daure da tsintsiyar hannuna shima lokaci naga yana dubawa bakwai har ta wuce da wasu mintinoni.
muje ko dare yayi fa Allah bansa mezance agida ba.
dan ban taba kai by this time a waje ba hnklin mamana zai tashi da rashin dawowata da wuri .
karki damu yanzu zan kaiki har gida, na girgiza masa kai karka damu muje na dauki motata.
nasoma tafiya naji ya fizgoni na dawo luuuu sai bisa faffadan kirjinsa ya rungumeni tsam meyasa kike son tafiya kibarni alhalin banason rabuwa dake?
,bugu da kari bansan matsayina agurin ba .
zanyi mgn naji ya hade bakinmu waje daya yasoma tsotsa tsawon lokaci muna cikin yanayin shauki sannan ya sakar min baki yace muje amman ki hanzarta yin shawara da wuri kafin kwalkwaluwata tasoma birkicewa nazo ina aikata ba daidai ba.
nace to hannuna ya rike tare da kunna hasken wayarsa muka soma fitowa daga cikin dajin hara zuwa inda motarsa ke fake ya bude min nashiga na zauna ya rufe sannan ya zagaya yashiga shima muka bar guri.

da hanuna na dinga nuna masa hanyar da zaibi muje unguwarmu har muka shigo cikin unguwarmu shin kansa dayaga yanayin tsarin unguwar yasan ta manyan mutane ce koina haske zaka dauka ba dare bane.
ahankali nace idan ka kai bakin wancen bakin get din na karshe ka tsaya nan ne gidanmu...
ai bazan iya gaya miki yanayin da taufeek yashiga ba alokacin da ganin irin tafkeken get din gidanmu ban da shi kanshi ginin gidan.
ahankali naji yace yanayinki da gidanku kun dace .
nace nagode ka tsaya na sauka daga anan..
sbd me bazamu shiga tare ba? ya jeho min tmbyr.
au a she fa taufeek bashida wannan matsayi acikin zuciyarki ko? amman karki damu very soon zan janyo soyayyar tawa ta karfin tsiya.
kafin na an kare har yasoma danna hon..... na kallosa a firgice karka min hk ban tanadin abinda zancewa iyayena da yayyena ba ,idan suka ganka.
kice musu mijinki ne wanda keda muradin aurnki simple instruction.
kinga sai su soma shiri da wuri ke nifa ba da wasa nake ba bil haki da gsky nake sonki tare da muradin aurenki so sai kisan yadda zakiyi dasu indan sungani.
amman wallahi har cikin gidan zan shiga zuwa lokacina securities din bakin get dinmu har sun bude tafkeken get din gidanmu kowanensu rike da bindigarsa ina kallon taufeek yasanya hancin motarsa cikin farfajiyar gidan mu batare da wani tsoro ba ya paka yace fita a tunaninki dawa zamu soma cin karo..? yayi min tmbyr yana murmushin mugunta ni km idanuna cike da hawaye hanzarin fitowa nayi daga motar .
shima ya fito ya rufe motar mushiga ciki naga mama har da baban ma.. nasoma bashi hkr ina kuka .
kayi hakuri ba yanzu ba tukun kabari da kaina zan soma sanar musu ok soyayyar tawa fa meye matsayinta ?
shima zan.. zan.. ce wani abu nan kusa, da kin kyautawa kanki ya rungume hannunsa duka akirji ya jingina da motarsa .
so nake ya wuce alokacin nasamu natsuwar zuciya har nasamu nashiga cikin gida amman yaki sai ma hira dayasoma jana dashi .
cikin hk motar yaya yusif tasanyo kai a firgice na dubi bakin get din nace kagani ko.... ..
me nagani.. ni banga komai ba baya ga mota kuka nasomayi yace cool down dear babu wanda zai ganni dake ya nemi kawo min matsala.
muna tsaye yaya yusif ya fito daga motarsa ya nufo inda muke tsaye dan daman daga makarantarmu yake nemana .
inagani yakaraso nayi saurin yi masa sannu da zuwa Allah sarki yadda nayiwa yaya yusif hk shima prof taufeek yayi masa dan shi har da karasawa yayi ya mika masa hannu suka gaisa cikin harshen tsadadden turancinsa kusan minti goma suna tare bansa me yake ce masa va.
sannan daga baya ya dawo kusa dani ya tsaya mukacigaba da hira sai daya gaji dan kanshi sannan ya tafi ni km nashiga gida.

wayyohhly nashiga cikin nasoma jin saukar mari takoina a fuskata mamma ce abinda bai taba faruwa ba kenan wannan shine ranar ta farko da hannu mahaifiyata ya gareni naci duka naci fada gurin mamma wanda kadan ya rage bata illatani ba tana dukana tana nima ina ina bata hkr kuka tayi sosai da kyar yayyena suka dinga bata hakuri sukace nima nabata hakuri ina kuka na durkusa har kasa nabata hakuri tace ta yafe min amman kar na sake kuskaren dadewa a makaranta . wannan yazama shine na farko da karshe dazaki sake dadewa hk wlh daman baki taba aikata hkn bane sai lokacin km akasoma tmbyr yadda akayi na dade a makaranta na ce mun tsaya yin wani aiki ga motata km tasamu matsala ...ba bari mahaifina yasan da zance ba.

ina dakina nayi shr ina tunanin magangun prof taufeek nasoma zagaye dakin naci abinci dare nasanya kayan bacci nayi karatu daga nan km me nayi?
dabi'un nawa ma na kasa ganewa hk na haura saman gadona to shi taya akayi ya gane dabi'una nayi mgnr tare da kwanciya na runtse idanuna ban dade da kwanciya ba bacci yayi awon gaba dani kasancewar nagaji dawaya ga jikina gbdy sun min tsami da kyar ma nake iya juyawa sbd dukan danaci.

su'ad ta dakatar da umma alokacin kina da shekara nawa ummana naga ba'a dukan yan jami'a murmushi umma tayi sai dai idan bai yi abun duka ba, sannan lokacin ina na wuce duka agurin iyayena duka ba wasu shekaru gareni ba dan ban wuce 21 ba.

umma tacigaba

washegari ni dai bansa yadda akayi ba sai ganin motata nayi a harabar gidanmu. cike da natsuwa nasamu mahaifiyata da zance taufeek domin bana boye mata komai duk wata damuwar itama dani take yinta akwai shakuwa me karfi atsakaninmu, tace taji amma ta min addua tare da nasiha akan na rike mutuncin kaina ta dade tana jadaddamin na rike mutuncin kaina.

tun daga wannan lokacin wata irin shakuwa ce me tattare da zunzuruntu kauna ke wanxuwa atsakanina da prof taufeek har ta kai tawo yana zuwa gidanmu km nice da kaina na bawa securities din bakin get dinmu damar duk sanda yazo abarshi yashigo kai tsaye .
duk wannan budurin da muke nida taufeek da zuwansa gidanmu da yanayin yadda muke gudanar da soyayyarmu mahaifina bai da masaniya akan komai km nima har zuwa lokacin bansa da zance auren hadin da za'a min da cousin dina yakub ba.
hankalina kwance yake nayi zurfin cikin kogin sonshi, shima km yana nuna min kulawa takowani bangarensa duk da har lokacin bakina bai furta masa ina sonshi ba ko akasin hk soyayya kawai muke gudanarwa dan idan muna tare dashi bazaka taba gane waye yafin son wani cikin ni dashi ba.
shi kansa kullun cikin cewa yake yafini sona. nima km gani nake kmr nafish sonshi.

wata rana ina zaune adakina byn nagama duk abinda yazame jiki sanye nake cikin kayan bacci wando da dogon riga . waya na dauko nakirashi dayake kullun sai byn nagama zararrukana zan kirashi ahankali muka soma hira irin ta masoya cikin hirar ne nace nayi my hope dayake yanzu hk nake ce masa nayi kewarka..
yace Allah dear nace eh yau fa ina jin ko bacci bazan iya yi ba matsawar banganka ba, karki damu zakiyi bacci idan har da gaske rashin ganina ne matsalar.
sai dai a nemi wata matsalar bawannan.
zan kau da wannan yanxu yana gama fadar hk naji ya katse kiran abun yayi matukar bani mamaki .
sake neman layinsa nayi byn wasu lokuta kira daya biyu ya dauka hello ...hello ..ya ka katse kiran?
wani aikin gaugauwa ne ya taso ok yanxu nasan kai kadai ne a inda kake?
kwarai kuwa me kakeyi ahalin yanzu kofa nke kokarin budewa ayya a ina kenan..? agidanku man....
dago idanuna nayi da sauri tare da zaro su waje lokacin da suka sauka akansa waya manne da kunenshi yana kokarin bude glass din kofar shigowa dakina ta cikin glass din ya dago min hanunsa take hantar cikina ya kada wani matsanancin tsoro yakamani mikewa nayi da sauri na doro daga kan gadon ina binsa da wani irin kallo wani irin mutun ne shi....?
daga cewa nayi kewarsa shine zai kwaso jiki yazo yama akayi yasan dakina?
ban gama tunani ba yakarasa bude kofar yashigo ya rufe tare da jingina bayansa da kofar yana sauke naunauyen ajiyar zuciya jikinsa sanye cikin riga yellow me dogon hannu da yar samanta baki da wando jeans sai wani kyale daya zaye wuyansa dashi ahankali yasoma takowa zuwa inda nake jikina da bakina babu abinda suke sai kirma zuciyata kuwa kadan ya saura batayi bunduga ba. bakina na rawa nace a... a taufeek meye hk?
meye kawoka acikin irin wannan lokacin ?
kawai naga yasoma zare yar saman rigasa xuwa kaurin hannunsa sai ga asalin yellow rigar dake sanye ajikinsa me gajeren hannu ta bayyana .
agigice nace a'a meyasa km kake kokarin cire kaya ?
kawai naga yakarasa cire rigar gabadaya ya nufo inda nake cike da izza yana kare min kallo bangane meyasa kake kallona hk ba? ahhhh
daman haka kake bansani ba ?
a'a ya girgiza kai ba hk nake ba kece dai kike kokarin meidani hk uhmm ni km?
yace min nace dan girman allah karka karaso gareni da wannan yanayi naka duk nmj da kagansa hk akwai wani abu cikin zuciyarsa..... auuu daman hk kika damu da lamarin maza kmr wani shine komai.dole nadamu sbd gudun abinda zaije ya dawo ne nayi mgnr ina sunkuyar da kaina kasa tare da wasa da yatsun hannuna abinda zaije ya dawo din menene shi? yayi mgnr tare da kwaikwayar muryata yakaraso gareni ya cafki yatsun hannuna na zabura nayi baya ya matsoni.. saleemat.... uhmm... na ansa atsorace ina sonki taufeek dan Allah kada kamin komai a'a ya ambata sannan yabini da wani irin kallon mamakin abinda nace still hannuna nacikin nasa ya rike gam.
amman jin abinda nace yasa ya saki hanuna da sauri yana cigaba da kallona ke me nace me kike mgn akai cewa fa nayi ina sonki ba wai wani abu zan miki ba.
illa ki furta min kina sona kmr yadda nasha gaya miki.. to idan nace ina sonka bazaka min komai ba zaka tafi abunka batare da kamin wani abu ba?
murmushi yayi ya sake riko yatsun hannuna naga alama dai idan ban miki wani abu ba bazaki ji dadi ba

3 Comments On SAI KA AURENI DOLE
avatar
zainab-ishaq

1 year ago

Reply

Love it ????????

avatar
zainab-ishaq

1 year ago

Reply

Yes and I want to download it

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to zainab-ishaq

In order to download you have to subscribe for our package at https://tnovels.com.ng/subscribe

Please Login or Register in order to submit comment