Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gidan hk yakaraci zaman tare da saheebarsa ya wuce gidansa .

daren ranar ma yadda Su'ad taga rana hk taga dare sai dai wannan daren tayi shi tare da kaiwa Allah kukanta byn tayi sallahr asuba ta koma ta kwanta akan gadon ammi, tunaninsa ne stll ya sakata gaba da kokarin tarwatsa zuciyarta "tarasa wani irin makohon so takewa abdulkabir......amman shi agurinsa babu abin wulakantawa da kyamata kmrta ya tsaneta ya tsani ganinta.

"ina ma zai bar rayuwarta?

"ina ma soyayyarsa zata bar tsokar dake makale da kirjinta ta huta da wannan zazzafar soyayyar datake masa ..?

"ina ma soyayyarsa zata bar rayuwarta hakika data hakura da abdulkabir hakuri km na har abada ,Allah sarki ammi tana iya bakin kokarinta akan lamarinta da abdulkabir amman kullun kmr tunxira zuciyarsa akeyi akanta.

ta janyo daya daga cikin pillow dake kan gado ta rungume akirjinta anya kuwa zata iya rabuwa da abdulkabir wani bangare na cikin yake mata wannan tmbyr wasu zafafan hawaye suka shiga tsiyayowa daga cikin idanunta

tabbas takara yarda da mutane ke cewa Son maso wani koshin wahala tarasa wani irin so take wa ak wanda yasanya takasa fitar dashi daga cikin zuciyarta duk da halin ko in kula dayake nuna mata kai ta wani bangaren so kwata kwata bai yi ba arayuwa ta samu tsayin lokaci tana kwance akan gado tana murkususu soyayya babu abinda yake cin zuciyarta kmr soyayar ak
juyi kawai take tana tunani iri iri akansa taja numfashi sauke da kyar tana sake matse pillow dake kirjinta "ammi ce jigon komai arayuwarta ahalin yanzu byn mahaifiyarta, yayinda ita kanta bazata so wahalar data sha akansa yatafi hk batare datacima muradinta akansa ba.

"zatayi hkr da juriya kmr yadda ammi tasha gaya mata ,za ta daurewa zuciyarta, zatayi komai akan yazamo tmkr bawa gareta abaya ma ta sadaukarwa da rayuwarta gareshi lokacin da bai santa ba, bai san ko wacece ita ba ballantana yanzu dayake shirin zama mallakinta, bacci take son komawa amman yaki zuwa mata dan hk ta runtse idanunta gam kozata samu ya fixgeta.

lokacin biki na sake karatowa sosai amman har lokacin AK bai kawo su'ad motarta ba kmr yadda ammi tace sai siya dole.
dan hk ammi ta sake nemanshi da kanta akan mgnr koda tayi masa mgnr cewa yayi ya manta amman zai sa a turo motar cikin satin nan kiyi hkr abubuwa ne suka sha kaina bana samun lokacin kaina ..amman yanzu nasan da zarar nayi mgn za'a turo cikin satin nan ba mamaki ma daita zatayi....

kada ka sake ce min komai abdul ammin ta katseshi ta hanyar ce masa hk sannan banason jin wani excuse daga gareka ko wasu kalaman yaudararka gareni kaje duk kayi duk abinda ka tsarawa ranka ," mota km kana kallo zan siya mata amman wallahi azim bazan sake yi maka mgnrta ba ,kayi duk abinda kaga dama ammi takarasa mgnr tana sallamarsa " dan Allah ammi kiyi hkr wlh ki tmbyi mus... abdulkabir ammi takira sunansa a zafafe" na'am ammi tashi kabar min dakina dan girman allah .....

"ammi... oooooo ya rabbi nace ka bar min dakina kafin raina yafi hk baci akanka, ko dole sai naji wani uzirinka?

",ba dai ka zabi farinciki zainab akan nawa farincikin ba duniya ce sakayyar yanzu km tun a duniya akeyinta kajira na sake nemanka akan zance wani abu daya danganci ..dan girman allah ammi karki yi yunkurin furta abinda kike son fada yayi mgnr cike da matsanancin tashin hankali ki taimaki rayuwata ammi dan girman allah karki min baki wallahi yanzu zan fita nemo irin mota na kawo mata ,amman dan darajar Allah kiyi hkr ammi karki min baki ki sanya min albarka arayuwata .

tsakanin uwa da sai Allah take km zuciyarta tayi rauni tausayinsa yakamata " amman ta dane tare da hade ranta sosai "bancin wulakanci ka tashi kayiwa zainab kyautar mota ni uwarka bansani ba sannan nace ga abinda nake yazama jidali "ni dai kiyi hkr zan fita neman motar yanzu "kar bashi kawai ni zan saka kudina na siya mata ba dai mota bace kaje ka rike taka wayyyohly..... ammi karki ce hk " tunda bazaka bar dakin ba bari ni na barka, ta yunkura zata mike tsaye yace "no no ammi kiyi zamanki bari na fita yayi mgnr tmkr zaiyi kuka jikinsa a matukar sanyaye ya bar daki xuciyarsa kmr zata buga.

tsawon kwananki uku kenan AK bai saka su'ad cikin idanunsa ba wanda yake jin kmr ana buga kirjinsa da zuciyarsa da guduma ne .yayinda su'ad kuwa duk hanyar datasan zata hadasu dashi ta kulleta , inda tasan yana zaune a parlour bata yunkuein zuwa ,duk lokacin datasan yashigo gidan bata zuwa inda yake zata kebance kanta.

kwance yake a kan gadonsa idanunsa a runtse duk wani tunaninsa sun koma ga su'ad wace kwata kwata yanzu baya gabanta dan ko kallon arziki ma baya samu daga gurinta abin fa yasoma damunsa, da kokarin taba kwalkwaluwarsa yanzu hk dayake kwance akan gadonsa bacci yake son yi amman baccin yaki kawo masa ziyara balle yayi nasarar daukarsa wata zuciyar ke gargadinsa kar fa yayi saken da zai fada tarkon son yarinyar yayinda wata km na kokarin kara tsudumashi cikin duniyarta tunaninta.
wani bangaren na zuciyarsa na sake kokarin hana wannan tunanin tasiri acikin kwalkwaluwarsa .

bude mayatattun idanunsa yayi ahankali yana kallon saman dakinsa sannan muryarsa a sanyaye yace "meyasa tunaninta ke yawon zuwan min alhalin ba sonta nake ba ?

yayiwa kansa tmbyr wace babu me bashi amsarta sannan ya sake meida idanunsa ya runtse gam.

su'ad kuwa duk kwanakin bata samun yin isheshen bacci ko ta kwanta da niyyar bacci sai tagagara yi ,sai dai ta kwanta lamo har asuba fari ko tayi ta nafilfili wanda ammi ta lura da hkn dan hk ammi da kanta ta aika akasiyo mata maganin bacci tabata.

ranar datasha maganin kam tasha baccinta sosai byn sun gama shan hirarsu da eiman wace yanzu ta zama itace abokiyar hirarta .

hatta sallar asuba sai da ammi ta tasheta, tayi sallahr ta sake komawa sai wajen 10:00 da wasu yan mintina ammi ta sake shigowa ta tasheta tayi break.

tunda sanyi safiya AK yakaraso gidansu kasancewar bai samu ishashen bacci ba jiya gbdy zaune suke akan dining har dady suna break amman banda zeey wace tun dawowar su'ad gidan take ware kanta cikinsu matsawar suna tare daita, wanda hkn ke maseefar cin ran ammin amman take dauke kanta akan lamarin sbd daga su'ad din har ita matsayinsu daya agurinta babu wani banbacin .

bakajin motsin komai acikin parlour'n sai na karar TV da karar cokulan dake rike a hannuwansu, yayinda su'ad dake zaune kirjinta ya dinga bugawa daf daf sakamakon idanun AK datake jin yana yawo a ilahiri sansar ajikinta ahankali take tsakuran abinci kmr batason ci tana kaiwa bakinta zuciyarta na wani harbawa da sauri sauri ji tayi gbdy zaman gurin ya isheta yaushe rabon tasanya cikin idanunta ita kanta tana son kallon kyakkyawar fuskarsa amman tsoron abinda kallon nata zai jawo mata yasa ta kasa dagowa .

"sosai ammi ke lura da yanayin irin kallon da AK kebin su'ad dashi, tabbas ta tabbatarwa kanta yanzu AK yasoma kamuwa da matsanancin soyayyar su'ad.. amman bazata tace komai ba tukun zata saka ido tasha kallo taga iya gudun ruwansa.

atsanake su'ad ta ajiye cokalin hanunta tare mikewa tsaye da zumar barin gurin "har kinyi me inji cewar ammi?

"na koshi ammi tayi mgnr muryata cike da rauni .

"me kika ci anan koma ki karasa cin abinciki , kai km ka tashi kabawa mutane guri ammi takarasa fadar hk tana duban inda AK ke zaune rike da wayarsa yana daddanawa wanda idan akace kallon su'ad yake zaka karyata.

ahankali ya dago mayattun idanunsa suka hada ido da ammi tare da dage mata girasa daya , yana mata ala'mun tmby batare da yace komai ba ,ta watsa masa wata uwar harara can km "ya bude bakinsa da kyar me km nayi yanzu ?

"ban sani ba, ni dai ka tashi ka wuce dady yayi murmushi tare da cewa "wannan karfin halin fa? dan ya gano dalilin abinda yasa ammi take son korar masa yaro.

"bakaga yadda ya tsare min yarinya da wadan mayun idanun nasa ba kmr zai cinyeta,?
AK ya tabe baki yana sake watsawa su'ad idanunsa sannan yace "ta zauna ta ci abincinta babu ruwana daita dan banga abin kallo agunta ba.

"nidai ka tashi ka wuce kawai ,bakayi kaura daga gidan nan bane me ke yawon kawoka yanzu?

AK yayi murmushin takaici yana sakarwa su'ad harara sannan ya bude bakinsa da kyar "ta ya mutun da gidan ubansa bazai zo ba?
dady kana jin fa abinda ammi take cewa kaima ka yarda kar naxo?

"ina ai hkn ma ba me yiwu bane dole kullun yarona yakawo mana ziyara idan ke bakya so ganinsa ,ni ina kaunar ganinsa kullun .
ganin da su'ad tayi mgnr ta dawo muhawara a tsakaninsu yasa ta sulale ta gudu daki .


byn sun gama cin abinci ammi ta iske su'ad a dakinta zaune ta zabga tagumi dan batama san tashigo dakin ba ,har sai da ammi ta isa gareta ta cire hannunta data tokare habarta daita "banason yawon tunani mamana ....su'ad tayi firgigib ta dawo hayacinta tare da kallon ammi tana murmushin yake wanda yafi kuka ciwo. "banason wayon tunani, yawon tunani na haifar da cututttuka dayawa masu saurin na kasa jikin dan adam "idan wani abu yasameki bansan yadda zanyi ba? ke kadai kika rage min arayuwa ahalin yanzu ganinki ke dabemin kewar mahaifiyata da dan'uwana dana rasa ...murya cike da rauni su'ad tace "kiyi hkr ammi na daina nima hk kawai nake tsintar kaina cikin wannan tunanin. Allah yasa kin daina dan kullun hk kike cewa takarasa mgnr tare da shigewa bayi.


kullun ammi sai ta jaraba kiran number malam me bada maganin farfadiya bata samu kasanceawar yana ghana ,duk da ance mata sai byn sati biyu zai dawo amman ta kasa hakuri kmr kullun data sabawa gwada kiran number bata shiga, hk ce ta faru yau cikin ikon Allah tana gwada kiran wayar taji yashiga cike da matsanancin murna ta zaku bai dauki kiran ba.
kiran ya katse batare da an dauka ba ta sake gwada kiran a karo na biyu aka dauka "assalamu alaikum "
daga dayan bangaren aka amsa mata da "wa'alaikimu salam" muryar malamin ce ta doki dodon kunneta wani irin murna da faricinki ya sake ruf ammi kmr anbata maganin farfajiyar ne.

"malam nice wace nazo kan zance yarinyata me fama da cutar farfadiya kace lallai sai anxo daita sai km akayi rashin sa'a mun zo baka nan .

"eh wlh tafiyar gaugauwa ce tasani zuwa ghana amman dazu da asuba na dawowa zaku iya xuwa ..

wani sanyin dadi ya sake rufe ammi "nagode sosai malami gamu nan zuwa "Allah yabada iko karasowa inji cewar malamin.

katse kiran ammi tayi tare da duban inda su'ad ke zaune ita da eiman suna hira wace rabin hirar eiman ce ke yi akan yadda aurensu zai kasance .
"ammi tace mamana maza tashi ki shirya zamuje gurin malamin nan ya dawo tun ammi batakarasa mgnr ba su'ad ta mike tsaye tare da kwance mayafi jallabiyar dake sanye ajikinta wanda ta daurashi akanta ,ta warware tare da nade kanta dashi ta dauki daya daga cikin turarukan ammi ta fashe ilahirin jikinta dashi wajen ajiye takalma ta nufa ta dauki takalmi flat tasanyawa kafafunta ta juyo daidai ammi tagama shirinta sukayiwa eiman sallama suka wuce.

*****
zaune suke gaban malami me tsoron Allah da son taimakawa bayin Allah, wannan malamin kowa ya sheidaishi akan cewar malami ne nagari me tsananin tsoron allah duk abinda wannan malamin za'i maka daga cikin alqurni me girma zai duba.
" ko maganin gargajiya wanda alqurni yayi mgn akansu,bai dogara da komai ba sai da ayar Allah ya dagora .

tunda akayi musu iso ga wannan malamin gaban su'ad ke faduwa banda kallonsa babu abinda take, alahakikanin gsky tana ganin kmr tasan fuskar dan fuskar malamin bazata taba bace mata ba a iya tsawon rayuwata.

malamin ya numfasa byn yagama hada wasu magunguna cikin bakar leda ya mikawa wani mutu, kana ya meida hankalinsa sosai kansu ammi, ammi ta sake gaidashi ya amsa cike da sakin fuska "malam wannan itace diyar tawa me dauke da cutar farfadiya .

malam ya sake numfasawa sannan yasoma mgn cikin hausarshi da batagama kwarewa ba "sannu yarinya ,su'ad ta sunkuyar da kanta tana wasa da yatsun hannunta "tace yauwa ina yini ..
" lfy ina son ki bani labarin abinda ya faru dake tun daga farko sbd ji yanayin labarinki yasa nace azo dake ,saboda mahaifiyarki ta min bayanin komai agame da yadda akayi ciwon ya dawo jikinki, amman nafi son naji daga bakinki kasancewar lokacin da mahaifiyarki tazo min da labarin yadda akayi ciwon yasameki yayi min tuni da wani labari wanda yazo daidai da irin naki .

"dan hk bismilla ina sauraronki su'ad ta sauke naunauyen ajiyar zuciya tare da sake sunkuyar da kanta kasa sosai sannan ta fara bawa malamin barinta tunda daga farko har karshe.
lokacin da su'ad ta kai karshen labarin malamin yayi murmushi yana sake fuskantarta da kyau sbd tabbatarwar kansa babanshi ne yabata wannan maganin .

numfasawa malamin yayi sannan "yace kinga wanda yabaki maganin farfadiyar nan da kikawa abdulkabir mahaifina .......

a matukar tsorace ammi ke dubansa wanda ita su'ad bataji wani tsoron komai ba , daman ita tun shigowarsu ta sanya ayar tmby akansa sbd tsantsar makanin dataga yayi mata da alhj tapa.

"malamin yacigaba daman mahaifina yabani labarinki kafin ya rasu yace komai daren dadewa ko ke baki dawo ba wani naki zai dawo gareshi .

"sannan mahaifina kafin ya rasu sai daya Shiryu yakoma zuwa ga Allah ya koma cikakken malamin addinin muslinci duk ya daina aikin shirka da tsubuce tsubuce sai da yayi tuba sosai tuba km irin wanda Allah yake so. mahaifina sai dayazama mutumin arziki sannan Allah ya dauki rayuwarsa " kafin ya rasu shi yagayamin duk abinda zanyi nayi sbd da Allah mahaifina ya bar mana wasiyyaha sosai domin kuwa sai daya tara duka ya'yansa yayi mana huduba gbdynyamu "yace Duk Wanda yayi shirka byn ransa Allah ya isa bai yafe masa ba .
"yace mu shiga duniya muyita hajahadi mahaifinmu ya raba dukkanin ya'yansa zuwa garuruwa kasashe kasashe muje muyiwa muslinci da alummar annabi hidima sannan ya rasu.

" mahaifina yace duk lokacin kuka dawo yabani sakon cewa makarin maganin tunda kema alokacin yace baki taba sanin da namiji ba wanda bansani ba ko zuwa yanzu kinsani cewar wanda bai taba kusantar ya mace arayuwarsa shi zai kwanta dake ta hanyar sunan ma'aiki saw.
abinda ake nufi zayi auratayya aure dake sau bakwai acikin halin cutar farfadiyar ajikinki ,shine makarin wannan cuta ta farfadiya .
take gaban ammi yashiga dukan tara tara da mgnr mlm sannan km jikinta ya dauki rawa babu abinda tasoma furtawa cikin ranta kmr kalmar inna lillahi wa inna ilaihi rajiun shi kadai take karantawa tana maimaitawa sbd tashin hankali dataji ya shigeta...

ita kuwa su'ad kusan har tafi ammi shiga damuwa da tashin hankali wani abu taji ya gilma ta cikin idanunta jiri ne ko kuwa buguwar zuciya ne ta sameta daga zaune da take ita dai batasani ba sbd ji tayi kanta da gangar jikinta suna juyawa gbdy idanunta sun soma rufewa .

malamin yacigaba km daman mahaifina yace wani mummunar bala'i sai ya fadawa yarinyar sbd tayi shirka tasabawa mahalincinta km duk wanda yayi shirka ya sabawa allah daman arayuwa sai yaga badaidai ba, idan yaci banza a duniya har yagama rayuwarsa ta duniya batare da ya tuba ba km allah baiyi masa komai ba, definitely idan yaje lahira sai ya hadu da mummunar sakamakon abinda ya aikata arayuwarsa ta duniya.

sosai malamin yayi musu nasiha inda yake cewa su'ad wadan nan yan fashin da makamin da kika hadu dasu a wance ranar dazaki kai tukunyar tsafi har suka yi miki sharrin cewar da
ke sukeyi fashi.
bala'i da mahaifina yace zai sameki shine wannan haduwar da kika yi da yan fashin suka miki wannan sharri har kika fada bala'in da har kikaje kikayi gidan yari.
idan zaki hankalta Allah yana sonki da rahma ne a lahira wanda yasa tun aranar farko da kika aikata shirka yasoma hukantaki tun a gidan duniya bisa ga laifinki .

"yanzu abinda za'a yi hjy ki soma da tuntubar yarinyar idan har zuwa wannan lokacin bata taba kusantar "da" namiji ba arayuwarta .
sai a nemo wanda shima bai san ya mace ba a daura musu aure...

hankali ammi a idan yayi dubu to ya kai kololuwar gurin tashi, a matukar tsorace take agaban malam sai dai duk bayaninsa na shiga cikin kunnuwanta ," cike da raunin muryar "tace na saurari dukkanin bayanika na km gode kwarai da gaske malam Allah ya bar girma sai dai wani hanzarin ba gudu ba yanzu hk ita yarinyar jibi ne daurin aurenta sai dai daga ita yarinyar har mijin bani da tabbaci akansu "yanzu dole sai hkn ta faru sannan zata rabu da ciwon?

" a'a wannan al'amari ne na ubangaji idan Allah yagadama zai iya warkar daita a duk sanda yaso ni dai abibda mahaifina yace nasanarmuku kenan duk randa yarinyar ta dawo.

"ammi ta sake marairaice murya" allah gafarta mlm
mijin da ita yarinyar zata su biyu zai aura arana "zai iya jinkirtawa har zuwa sanda zai aiwatar da komai akan ita wannan yarinyar ...." shikenan mlm nagode sosai yanzu nawa zamu bada kudin sadaka?

"bana bukatar ko sisin ku ga wannan itacen maganin sassaken dinya ne, kinsa ciwon farfadiya lamarin iska ne , km iska basa kusantar sassaken dinya zata dinga wanka da wannan sassaken dinyar kullun har sai randa ya kare kuje Allah yabata lfy.

"ameen mlm nagode nagode sosai .

"ki godewa Allah domin kuwa shine abin godiya bisa ga dukkan komai zuwa wannan lokacin ammi ta jima da mikewa tsaye ,amman su'ad na nan zaune cikin wata duniyar tunanin me cike da sarkakiya jin bayanan mlm tun mgbrsa ta farko jin ya dauke ta daina jin komai sai bugun zuciyarta daya tsananta.

da taimakon ammi su'ad tasamu ta mike tsaye da kyar jikinta na rawa rawa suka bar gidan mlm suka nufo hanyar dawowarsu gidan tun akan hanya ammi takira layin ak "tace maza maza duk abinda yake ya ajiye shi yazo yanzu tana nemansa.

koda suka iso gidan gbdy hayaniya ce tacika koina a gidan kasancewar sauran dagin wadan da basu samu damar hallatar biki da farko ba wannan karon sun samu damar karasowa.

jikin ammi da su'ad a matukar sanyaye suka dinga rasa jama'a suna gaigaisawa tare da yi musu sannu da zuwa har suka samu suka karasa dakin ammi , a dakin suka tadda AK tsaye jikin window hannusa akan glss din window yayinda dayan hannunsa ke cikin aljihun wandonsa na dan jujjuya jikinsa.

ammi ta dubi inda yake tsaye tana kallonsa cike da matsanancin rauni bata san sanda hawaye suka shiga zubo mata ba, su'ad naganinsa tsaye ya wani hade rai kmr an aiko masa da sakon mutuwa ta juya da sauri ta bar dakin zuwa nasu eiman ,nan ma dakin cike yake makil da kawayen zeey da yan'uwa .

juyawa tayi ahankali ta nufi bayan part din AK na gidan zuciyarta na wani irin mahaukacin bugu da karfi sai lokacin hawayen datake kokarin makalewa acikin kwarnin idanunta yasamu nasarar zubowa ta durkushe agurin tana kuka me cin rai ita kai tasan yadda take jin zuciyarta tare da tasani mara iyaka.

shi kuwa AK ganin yadda ammi ke kallonsa hawayen idanunta na tsiyaya wasu na sake zubowa ,yayi saurin karasawa gareta tare da rikota hankalinsa a matukar tashe "lfy ammi?
"me km ya faru dake waye yayi miki wani abu?

"ni ne ko ammi?

"nasan ma ni ne nayi miki wani abu, ammi dan girman Allah ammi ki daina zubar da hawayenki akaina kukanki bakaramin tashin hankali da maseefa bane gareni..
jikinsa na rawa ya zaunar da ammi akan gado shima ya dan dosana agefen gadon kusa daita ya zauna wanda har lokacin hawaye ammi yaki tsayawa, yasa duka hannuwansa yana goge mata hawayen "kiyi hkr ki daina kuka ki gaya min laifina gareki wanda yasa har kike zubar da hawayenki hk.

sautin muryar ammi yaji ya doki cikin dodon kunnuwansa "baka min komai ba sai dai ina kukan bakinciki ne, ina kuka ne adalilin wani abu da yataso min me mahaminci nan tashiga koro masa abinda mlm yace takarasa mgnr tare da cewa nasan bazaka taba min amfanin ba ta wannan fanin......... .

naunayen ajiyar zuciya ya sauke da karfi yana me dafe goshinsa sbd jin dayayi kansa yayi mugun sarawa "yanzu ammi dan wannan matsalar kawai kike hasarar hawayenki?

"dole nayi kuka abdul wannan matsalar ba kawai bace sbd nasan bazaka taba kasancewa virgin ba .

sake sauke wani naunauyen ajiyar zuciya yayi tare da kiran sunanta a sanyaye..... ammi ta dago idanunta tana kallonsa batare da tace masa komai ba "ammi ya sake kiran sunanta a karo na biyu wallahi tallahi Bil'lahilazi kinji rantsuwar dan muslimi kenan ban taba kusantar wata "ya" mace ba arayuwata da suna zina byn romacing, duk iskancina a iya romacing kadai na tsaya.

a mutukar firgice ammi ke kallonsa cike da matsanancin mamaki jin abinda ya fada "hk ne ammi matsawar kin amince da rantsuwar dana miki ,, ko alqurni aka bani zan rantse dashi akan bantaba taka diyar kowa ba,.
"sai dai ita su'ad din da kike mgnr akanta kina Da tabbacin babu wanda ya taba kusantatarta?
bakaramin dade ammi taji ba duk da har lokacin zuciyarta na cikin damuwa," karka min karya abdul Allah iya gskyta na gaya miki ammi" ammin da kike zargina ita su'ad din fa?

babu ruwanka da mgnr su'ad "babu ruwana kam tunda kowa yasan yar jagaliya bazata taba samun wannan martaba ni yanzu bakincikina daya ta yaddda ita zan fara kusanta ba zainab ba shi yasa ni gaky sai dai muje ayi mata gwajin HIV ammi ta zaro ido waje, da wa kenan za'a yi gwajin HIV?

"da su'ad man idan na dauki kasadar aurenta ai bazan dauki kasadar daukar cuta ba, take ammi ta birkice masa wallahi babu inda zata wani gwanjin HIV idan km ka matsa sai anje zan bata maka rai .

"shikenan ammi nabar mgnr sbd banida ja da mgnrki Duk abinda kika ce shi zanyi banida mafita , bana son su'ad bana son aurenta amman kika tirsasani kisawa ranki matsawar na auri su'ad ,ki tabbatar da zaki dauki kasadar rasamu wata rana yana gama fadar hk ya mike a matukar fusace ya nufi kofar fita daga dakin tare da nadamar xuwansa.

zaune su'ad take gaban ammi tayi shr tana kallonta itama ammi kallonta take tare da nazarin yanayin da ta shiga tun lokacin da suke gaban mlm , sai data gama nazarinta tsab sannan ta soma mgn cikin sanyi murya "mamana nasan kin rasa budurcinki ko?
su'ad dake zaune taji zance daga sama yayiwa kirjinta darar makiya saurin kallon ammi tayi zuciyarta na wani irin tsalle ki sanar min gsky idan kin rasa budurcinki a gurin wahalallun rayuwar da kika shiga .
cikin matsanancin tsoro su'ad tashiga girgizawa ammi kai sannan bakinta na rawa tace "Allah ammi banta aika wani abu makamanci hk ba take ammi ta saki fuska cike da farinciki mara misaltuwa kafin tacigaba mgn "mamana da gaske kike kina tare da budurcinki har yanzu ko km dai kina son yi min wasa da tunani ne?
tsuru su'ad tayi mata ido tana kallon ammi tare da jinjina mata kai rikota ammi tayi da sauri ta mannata da kirjinta sbd tsabar farinciki "kai kai Allah dai yayi miki albarka Allah jikan mahaifinki Allah yayi miki albarka Allah yasa ki

3 Comments On SAI KA AURENI DOLE
avatar
zainab-ishaq

1 year ago

Reply

Love it ????????

avatar
zainab-ishaq

1 year ago

Reply

Yes and I want to download it

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to zainab-ishaq

In order to download you have to subscribe for our package at https://tnovels.com.ng/subscribe

Please Login or Register in order to submit comment