Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

waje daga bisani gangar jikinsa ya biyo baya ,ya fito gbdy daga cikin motar sanye cikin wasu haddaun riga da wando, rigar dake sanye ajikinsa fara ce sol me ratsin baki ajikita da wando baki kafafunsa sanye cikin canvers baki da da fari kanshi babu hula sai agogon dake daure a tsintsiyar hannunsa duk da dare ne amman farfarjiyar gidan ta wadatu da hasken wutar lantarki hkn ne ya yabawa su'ad damar kare masa kallon tsab daga inda take tsaye shi km yana jikin motarsa tare Kokarin dannan key din dake rike a hannunsa.

ahankali ya juyo da niyyar soma tafiya abinda yagani ne yasa kasa cigaba da daga kafafunsa dan hk ya tsaya cak tare da tsura mata mayatattun idanunsa yana kare mata kallo daga inda yake .

sanye take cikin wasu haddaun wando da rigar body hook me maseefar kyau wace tayi mugun kama mata jiki sai wandon pencin jean shima ya matse Hip's dinta sosai wanda hkn ya fito da shep din halitar jikinta ta rufe kanta da hular sanyi tare da rungume hannuwanta duka akirji wanda hkn yasa ya kasa gane yanayin halin da dukiyar fulaninta suke ciki ,tayi wani irin azababben kyau na daukar hankali .

ganinta tare tsinannun gang dinta yasa yaji ransa yayi mugu mugun baci yji wani irin masifafen kafirarran kishi ya caki kahon zuciyarsa yana neman barazana da rayuwarsa take yashiga antayo musu mugun kallo me hade da harara wanda yasa hantar cikin su'ad kadawa jikinta ya dauki rawa ,gbdy tsoro da firgici suka farmaki zuciyata tana kallonsa yasoma daga kafafunsa ahankali yana tafiya cike jin shi wani ne yayinda ita km bugun zuciyarta ya tsananta .


duk daga kafafunsa daidai yake da bugun zuciyarta amman ta daure ta cije ganin wannan tsoron bai yi tasiri ajikinta ba ,.
yana gama karasowa gurin tasoma hawayen xuci sbd tasan me zai iya faruwa alokacin, yanayin fuskarsa yagama bayana tsantsar rashin mutunci da zaiyi, ita kadai tasan yadda take ji cikin zuciyarta a halin datake tsaye a gurin jiyatayi kmr ta gudu ta barsu ore amman wani bangare na zuciyarta ya karfafa mata gwiwar tsaya wa.

har ya kawo daidai inda suke tsaye cirkocirko cike da matsanancin tsoro kawai taga ya dauke kanshi akansu ya wucerwasa batare daya sake kallon inda suke ba .

hanunta tasa ta goge gumin dataji yashiga tsatsafo mata a fuskarta wanda tsoro da firgici yasa ta kasa gogewa tare da sakin naunauyen ajiyar zuciya tashiga Allah Allah su bar gidan.

basu wuce ba har AK ya fito ya wucesu a inda ya barsu tsaye yashiga motarsa ya figa da gudu bar gidan sai wuraren goma da rabi suka bar gidan.


washegari hk yazo tara dasu sun cika farfajiyar gidan da hayaniyarsu ya wuce still kmr jiya batare da yace musu komai ita kanta su'ad bata bi ta kansa ba.


rana ta uku AK ya sake zuwa gidan ya iske su baba laye da wasu maza su uku tsaye tare da su'ad ,nan fa ya kasa hakurin ganinsu kai tsaye ya nufo gurinta yana mazurai yadda taga yanayinsa yasa gabanta ya fara faduwa da sauri sauru
"har gabanta yakaraso ya tsaya kyam yana kare mata kallo batare daya kalli inda su baba laye suke tsaye cirkocirko ba.

yayi kusa daita sosai numfashinsa ya bugi hancinta wanda yasa tayi saurin ja bada kadan kirjinta na mahaukacin bugawa

"muryarsa a kausashe yasoma mgn.

"meke kawo wadan nan tantiran ?

yayi mgnr yana nuna bayansa inda su baba laye suke , kasa cewa tayi komai illa kawar da fuskarta datayi gefen tana kallon shuke shuken flows din dake zagaye da gidan ,hk yasa ranshi ya sake maseefar baci matuka"bada ke nake mgn ba kikayi kunnen uwar shegu dani? ya sake tmbyrta yana tsare da mayatattun idanunsa.

"me kake so nace maka ?
after all karigada kasan friends di na ne ,km you have oready know the relationship between us .

yana gama jin abinda tace juyo a matukar fusace ya fara ihu yana masifa " dan ubanku me ya sake kawoku cikin gidan nan ?


" ance muku nan gidan tantirai yan iska ne marasa kamunkai ?

"kafin na rufi idona na bude naga kun bar gidanan yanzu km banason sake ganin fuskokinku cikin gidan.

sannan ya juya ya sake fuskantar su'ad har tana jin saukar hucin numfashinsa a fuskarta.

"idan iskancin ne aranki har yanzu to ki hanzarta barin gidan nan, zaki iya kibisu can inda kuka saba iskancinku amma ba a gidan nan ba, dan nan ba gidan yan iskabane gidan natsassu ne masu hnkali.

"inbanda jahilci da rashin tarbiya da rashin sanin ciwo kai kalli yadda kika fito waje, pls kalli jikinki yayi mgn yana nuna jikinta da hannunsa saboda bakisan ciwon kanki ba baki san darajar da Allah yayiwa mata ba.

" ki gaya musu banason kara ganin fuskokinsu daga rana me kamar ta yau karsu sake shigowa gdanan wallahi idan na sake ganin fuskokinnsu zaki sha mamaki na stupid girl kawai .

"bacen da gani kafin na kararairaya kasusuwan jikinki yanzu ,tayi masa bazan taki motsawa daga inda take .


"ba dake nake mgn ba?
yayi mgnr tare da daga hannunsa zai dauketa da wani gigitaccen mari ta kauce da sauri ta juya tana kun kuni ,sannan ya meida hankalinsa kansu baba laye "idan kuna son tashin hankali da bala'i da da son jefa rayuwarku cikin jafa'i ku sake dawowa gidan nan
yana gama fadar
hk ya juya fuuuuuuuu babale laye ya bi bayan AK da kallo gentile man kabi ahankali fa karka kashe kaina abanza sannan ya kalli sauran yan'uwansa yace mucewa kawai wannan guy din daganinsa bashi da mutunci suka nufi get domin barin gidan .

a matukar fusace AK ya nufi part din ammi yana kiran sunanta Ummi Ummi Ummi cike da matsanancin tashin hankali ammi take kokarin fitowa daga cikin daki kicibis sukayi da su'ad wace ta boye abayanta .

"jikinta na rawa takarsa fitowa parlour inda yake tsaye tace menene abdul?

"wane irin kira ne hk? me yafaru ?
tajero masa tambayoyi ajere.

"haba ammi wannan wani irin rashin tarbiya za'a dinga yi mana acikim gida?

"ya zaki dinga barin yarinyar nan tana fita gurin wayancen yan iskan bayan bai kamata halakarsu tacigaba da wanzuwa ba saboda Allah.


"karka kara ce musu yan iska duk wanda ya kasannce tare da su'ad ba dan iska bane saboda duk yadda suke suna da anfani ba abin yarwa bane suma zasu tuba su daina abinda sukeyi .

" ai ba zai yiwu lokaci daya ace za'arabasu ba Dole saï anbi komai ahankali.

"haba Ummi meyasa zaki fadi hakan gaskiya wannan mu'amula bata kamaci duk macen da zata kasance cikin gidan na .

" yarbawa ne fa ammi ?

"and so what idan yarbawa ne yarbawa ba mutane bane?

"kai yanzu ina ruwanka da mu'amularta dasu kai da kace baka sonta meye abin jin haushi dan ka ganta da wasu mazan. ina tabbatar maka mu'amularta dasu tana daf da katsewa da zarar andaura muku aure.

"haushi fa kikace ammi?
"kwarai kuwa haushi kaji ..

"haushin me zanji ammi akan wannan yar iskar yarinyar zanji haushi aikuwa wallahi danaji kunyar duniya.

"kana daf kuwa da jin kunya sai dai kasan yadda zakayi ranar da kunyar zata riskeka.

muryarsa kausashe "yace wallahi banji haushi ganinta dasu kawai nayi mgn ne sbd martabar gidanmu kar azo a bata mana sunan gida if not koda mazan duka duniyar nan zanganta bazan damu ba balle naji haushi ai abinda kake so shi kake damuwa akansa.

"ke km zaki ci uwarki ne duk randa kika sake kuskuren tara mana dangin oduduwa agida .

ahankali su'ad ta motsa labbanta tace ba dai uwata zakaci ba wlh sai dai kasan uwar da zakaci tayi mgnr tana murguda masa baki..

mayatattu idanunsa ya zaro waje sbd yaji abinda tace sarai " zo nan me kika cewa ?

tayi saurin koma bayan ammi "ni kike zagi?

oh! my God gaskiya an cuceni an cuceni !!!

an cuci rayuwata da aka rasa wace za hadani aure daita sai wanan tantiriyar yarinyar mara kamun kai yakarasa mgnr yana sake duban inda su'ad take tare da zabga mata wata uwar harara .

"karamar jakar yar iska usuless kawai zaki san kin zageni dan sai datsa datsa da namanki sannan naci uw.. .. ..

da sauri ammi ta dakatar dashi ta hanya buga masa tsawa kamin shiru kada in na sake jin kace mata batada kamun kai ko zagin wani nata idan ba hk ba sai maseefar bata maka rai.

"in ma rashin kamun kai ne bata dashi ai kai ne a sanadi komai .

"ko ba a sadiyyarka tasamu kanta cikin wanan rayuwar ba?
"dan haka daga yau kar na sake jin ka sake kirata da mara kamun kai.

banda kuka babu abinda su'ad ke yi tarasa wani irin tsana AK yayi mata wallahi yanzu tana jin kmr tace a fasa aurenta dashi ,kuka take sosai har da shesheka Ummi ta janyo hannunta suka shiga cikin dakinta tana rarrashi "ki daina bata hawayenki akansa shi fa hk yake da zafin rai akan abu idan yaga kina yawon kuka da tada hankalinki akan lamarinsa zai ninka akan wulakacinsa akanki.

"abinda nake so dake ki cire wannan tsoron nasa cikin ranki sannan ki sawa zuciyarki hkr ki cire akidar shareshi da fita lamarinsa .
ammi ta zaunar daita bisa gado itama ta zauna abinda yasa na fada miki hk sbd kasancewar ku 2 zai aura duk yadda zakiyi ki karkato da hankalinsa gareki shi zakiyi.

"duk wannan gurnanin iskar dayakeyi karki kuskura ki kulashi, ba komai yake dawainiyya dashi ba sai zazzafan kishinki.
" nasan halin abdul sosai tunda ya nuna jin haushin ganinki da wasu ya damu yasoma damuwa lamarinki ne dan hk karki sake tarayya da abokanki maza .

"ki yanke halakarki dasu shine zman lfyrki da abdul idan da hali ma har matan ki rabu dasu.
ammi nagama fadar hk ta sauke naunauyen ajiyar zuciya sannan ta mike ta barta zaune tana kuka taydawo parlour inda ta bar AK wayam ta gani babu shi babu alamunsa .

a matukar fusace ya bar part din ammi amadadin ya wuce gidansa ya wuce part din dady dan daman gurinsa yaxo zasu tautauna akan yadda daurin aure zai kasance ya iske abinda ya tada masa hankali da neman tarwatsa masa kwalkwaluwa byn yagama abinda ya kawosa gurin dady ya mike da zumar barin gidan .
ganin yanayinsa yasa dady yakira sunansa abdulkabir ..
AK ya ja ya tsaya wanda lokacin har ya kai bakin kofa ya juyo ahankali ya tsaya yana duban dady dake zaune shiru dady yayi yana kallon cikin idanunsa wanda suka kada sukayii jawur tmkr an zuba musu garwashin wuta sai daya gama nazarinsa tsab sannan "yace ina zaka yanzu ?

"gidana ya bashi amsa atakaice.

"kar tafi koina shiga ciki ka kwanta har zuwa gobe idan Allah yasa muna rayayyu ,dady yayi mgnr tare da nuna masa dayan dakinsa, bai yi musu ba yaja kafafunsa zuwa cikin dakin ya kwanta sai dai ya kasa runtsawa sai juyi yake akan gado .

bangaren su'ad itama kasa runtsawa tayi, dan hk ta mike ta nufi bathroom taje ta dauro alwala ta fito ta shimfida pray mate tasoma jero nafilfili tana kaiwa Allah kukanta ,byn ta idar da sallahr bata mike daga inda take ba, ta zauna tana istigafari tana zubda hawaye, ta dade zaune tana istigafari sannan daga bisani ta daga hannuwanta duka sama"tayiwa Allah kirari da kyawawan sunayensa dari ba daya tana zubda hawaye ta me kaskantar da kanta zuwa ga ubangijinta "ya Allah ka jin kaina Allah kamin rahma da rahma ya Allah ka gafarta min tarin zunaibai dana aikata arayuwata, Allah na tuba Allah tuba bisa kuskuren dana aikata ,ya Allah ka jibanci lamari ka tausayamin idan aurena da abdulkabir alkhari ne arayuwata da addinina da ni kaina ya Allah kasa ayi auren tare sanya masa matsanancin soyayyata cinki zuciyarsa .

"Allah idan aurena da abdulkabir ba alkhari bane a rayuwata da addinina ni kaina Allah ka cire min soyayyarsa cikina raina kasamin hakuri da juriyar acikin zuciyata.sosai take kuka har da shesheka wanda shi ya tabba ammi daga naunauyen baccin data lula ta mike idanunta cike bacci ta nufi bayi alwala ta dauro itama taxo ta tada sallah.

Washegari ammi da da zeey suna kitchen gbdy tare da hannutu me aiki banda eiman wace ta tsani shiga kitchen .su'ad tashigo kitchen sanye da doguwar riga pupy colour har kasa wace gbdy ilahirin jikinta stone tayi musu sannu da aiki cikin iiririyar muryarta me cike da sanyin dadi, ammi da hannutu suka amsa da yauwa amman banda zeey wacce ko kallon arziki batayiwa su'ad ba baya ga harara.

su'ad bata da damu da rashin amsawar zeey ba kasancewar bata sanyata cikin wadanda tayiwa sannu da aiki ba. zeey nagani su'ad ta tsaya kusa ammi tana kokarin amsar wukar dake hannun hannatu ta cire hannuta cikin aikin gyara kayan hadin coslow ta koma parlour inda eiman take zaune tana kallon zeey word.

ita dai ammi batace mata komai ba ta meida hankalinta kan aikin da hannutu keyi dan ita Allah yayita da son shiga kitchen da kanta koda bazatayi komai ba.
tanaso taga yadda ake gudanar da aikin cike da tsafta da kula, ba kullun mutun ya zauna sai dai adafa a miko masa yaci ba .

yakamata mata mugane wani abu ba wai daukar masu aiki yana nufi zamu zauna mubarraje ne batare da mun sanya idanumu akan yadda suke aiwatar da aikinsu ba.

yakamata mu dinga saka idanu sosai akan yadda masu aikinmu ke gudanar da lamarin aikinsu ta fanin abinci da komai sbd tsaro, domin kuwa dayawa daga cikin masu aiki suna amfani da magani gurin mallakar iyayen gidansu har me gidan da yaran gida, ta yadda duk yadda mutun ya kai da son rabuwa da me aikin bazai iya rabuwa daita ba as ending ma wata ta aure maka miji.

a fakaice ammi take sake nunawa su'ad abubuwa masu mahimmanci wadanda suka danganci kitchen da aninda tasan AK na maseefar so tana yabawa su'ad din sosai gurin dan tana kokari babu abinda zeey zata nuna mata ta bangaren girki dan hk ma take sake jinjinawa mahaifiyarta .

lafiyayyen hadin coslow tayi wanda ammi ta umarce data hadawa Ak kasancewarsa mayen son coslow ne tare da cucumber just.
a tsanake tagama hada komai akan dan karamin tiri amman tsoro da fargaba sun hanata dauka ta kai masa har sai da ammi tayi mata mgn "ki dauka ki kai masa man.

"muryarta a matukar sanyaye tace "tsoro nake ji ammi kar yagane ni nayi yaki ci.

"bazai ki ci ba masoyinsa coslow da cucumber just ne ki kai masa zaici. jikinta a matukar sanyaye ta gyara zaman hular kanta ta nade hannun doguwar rigarta ta dauki tirin zuciyarta na wani irin tsalle da harbawa ta nufi parlour 'inda yake zaune yayi balace yana daddana wayarsa , tazo ta durkusa ta ajiye agabansa ta tsiyaya masa just acikin glas cup muryrta na rawa" tace ga co...slow ......batare da ya dago ya dubeta ba yace ki dauke bana ci "meyasa ....?kawai taji hawaye sun cika a idanunta ta tsura masa fararen idanunta tana kallonsa daidai lokacin daya dago nashi idon idanunsu suka tsarke cikin juna.
ido cikin ido suke kallon junansu batare da kowanensu yayi la'akari da mutane dake zaune a parlour 'n ba muryarta raunace "tace inje in hada maka fruit yacigaba da kallon cikin kwayar idanunta itama shi take kallo zuciyar na wani irin mahaukacin bugu da karfi .
bata dauke idanunta ba har sanda hawayen idanunta suka sauka akan kuncinta sautin muryar eiman taji ya sauka cikin dodon kunnena ya katsenta aunty kiyi masa frut din muma zamu sha ya juyo a matukar fusace yana zabgawa eiman harara sannan meida idanunsa kan su'ad "ke tashi ki bar wajen yanxu tun tunani bai canza ba . ta kasa mikewa tsaye kmr yadda yabata umarni bata ankara ba taji ya fixge glass cup din hannunta da karfi ya watsa mata ruwan just din Cocumber tundaga fuskarta har jikin kayanta ta jikinta da kallo ......shi km ya tsareta da idanunsa
yana sauke ajiyar zuciya sannan ya dauke idanunsa daga kallona ya meida kallonsa ga zeey wace tacika fammmm ta batse jira kawai take ata'bota ta saukewa mutun kwandon jaraba.

sweet baby yakirata.. zeey tayi masa banza tayi kmr bada ita yake ba, sai daya sake kiranta sannan ta juyo afusace kmr zata cinyeshi "tashi ki hado min wani coslow "wannan dake gabanka ubanwaye zai ci?

inji cewar ammi dake tsaye bakin kofar kitchen tana zabga masa uwar harara cike da matsanancin takaicinsa yayinda har lokacin su'ad na tsugune gabansa tana kallon jikinta hawaye na bin kuncinta "ki bude masa coslow yasoma ci yanzu .....

jikinta rawa ta kai hannuwanta duka ta bude masa sannan ta yunkura da kyar ta mike tsaye tasoma kokarin barin gurin zuciyarta tmkr zata tarwatse tsabar backinciki.

ammi ta koma kitchen aunty su'ad ni ki hada min frut din tunda kin tayar min da kwadayi inji cewar eima.

idanunsa ya tsura coslow yadda aka tsara komai atsanake ba a hargitse ba,ta fanin gabaje daban carrot egg Heinz Bean's yankaken nama bama .
yadda ta shirya dole yabawa mutun sha'awa ci ko bai so ci ba.

atsanake yasoma cin coslow wanda yajisa da wani dandano na daban wanda bai taba cin irinsa ba sbd sabon salon datayi amfani dashi ta hanyar saka tafashen nama cikinsa yana cin
coslow su'ad ta sake dowawa falon byn ta canza kaya xuwa wasu shegun kananan kaya wando da riga hamles, ta daura rigar sanyi me hula a saman rigar azababben kamshin turarenta ne ya ankarar dashi dawowarta ahankali ya dago da mayatattun idanunsa ya sauke su akanta yana kare mata kallo ganin zata juyo ne yayi saurin dauke idanunsa .
bangaren su'ad kuwa ko kallon inda yake zaune bata sake yunkurin yi ba balle tasan irin kallon dayake mata .

ta mikawa eiman frut eiman ta amsa tana murmushi tare da cewa "na gode auntynah sauran na yaya ki kawo masa shima yana so sosai.
batace daita komai ba ta sake komawa kitchen byn kmr minti 5 ta sake fitowa hannuta rike da jug ta tsuguna har kasa ta'ajiye agabansa tsuru yayi mata da ido yana kallonta ya kasa cin coslow dake gabansa har tabar gurin bai daina binta da kallo ba.

hakan yasa kafirin kishin zeey motsawa taja tsaki wanda ya ankarar da AK kafin yayi wani yunkuri dakatar tuni ta bar parlour.

"eiman tace very good gara ma hk, hkn yayi maka dade ko yaya?

ya watsa mata harara yana jan tsaki..

duk inda su'ad tayi daga parlour zuwa kitchen mayatattun idanunsa na kanta har zuwa sanda ta samu gurin can nesa dashi kusa da eiman ta zauna tare da daura kafarda daya kan daya ta hade ranta sosai sannan tasoma shan frut ahankali sai dai gbdy zuciyarta da natsuwar tana tare da AK dake zaune a yadda ta hade rai bazaka taba tabbatar da hkn ba.

haka kawai ya tsinci Kansa da son sake kallonta ya tsura mata mayatattun idanunsa jikinta ne yaba yana kallonta sbd yadda taji bugun zuciyarta na sake karuwa .

"eiman .."na'am ammi eiman ta mike ta nufi kitchen ganin eiman tabar gurin duk sai ta takura dan hk ta mike tsam tasoma bada wani irin step na tafiya me azabben daukar hankali da tsuma zuciya, wanda tunda yake iya rayuwarsa baita ganin irin step din ba kara balace yayi yana kallon each and every step dinta yana mamakin yadda take tafiya kmr a tsamata cikin ruwan sanyi, kawai ya tsinci kanshi da kallon tsukaken west dinta wanda wanda yaaawa bombom dinta damar baje kadan ga Hip's dinta daidai da jikinta, hot step ya fada cikin ranshi yana shafa kwantaccen sumar kanshi, yadda yayi mgnr cikin ranshi hk joystick dinsa tashiga harbawa acikin wandonsa yayi saurin dafe joystick dinsa da hannunsa duka yana kamo lip's na kasa ya datse da hakorinsa yana me runtse idanunsa.addua yake kar ammi ko eiman su riskeshi cikin wannan halin bai gama cin coslow ba ya mike ya falon.

abu fa kmr wasa ak ya tsinci kanshi da matsanancin tunanin su'ad duk idan ya zaune sai ya rinka jin yawon faduwar GABA akanta har takai takawo duk sanda yaxo gidan kai tsaye a part din yake wucewa dan kawai ya dinga ganin movement din su'ad .

idan ykasance shi kadai kuwa babu abinda ke zuwa cikin zuciyarsa illa tunanita da yanayin tsarin halittarta jikinta fuskarta kugunta tafiyar every part of her.
duk yadda yake son yakice tunaninta cikin kwalkwaluwarsa hkn ya gagara yayinda abin yasoma taba masa zuciya da kwalkwaluwarsa "shikansa yana mamakin meyasa yake yawon tunanita bayan a dacen baya bata gabansa.

a office yake itace ke zuwa masa ta hana zuciyarsa sakat , idan ya runtse idanunsa da niyyar bacci ,sai baccin yaki zuwa masa sai dai surar su'ad ne zai dinga kawo masa farmaki.

yanzu ma da yake kwance akan three siter a falon ammi tunaninta yaki bari ya huta a hankalce yake da duk wani motsinta.

" meyasa zan dinga tunaninta alhalin ba sonta nake yi ba ?
yawa kansa tmbyr yana sake gyara kwanciyarsa yana cikin wannan tunanin ne har zeey tashigo falon takaraso zuwa inda yake ta zauna kusa dashi..




mmn sudais ce

💗💗💗💗💗💗
SAI KA AURENI DOLE
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗



~NA~



*AYSHA A BAGUDO*



~DEDICATED TO~
HAUWA A USMAN
JIDDARH


*Allah messenger saw said fasting is a shield against sin's*

page 55

"my life me kake tunani hk ?

ahankali ak ya bude mayatattun idanunsa batare da ya kalli inda zeey take zaune ba muryarsa a matukar raunane yace "nothing sweet baby "

"yaza kace nothing alhalin tun dazu nake zaune anan amman gbdy hankalinka yana wani guri daban ,kodai kasoma tunani wacen stupid girl din ne ?

"hb swet bby ki daina fadar hk ,"me zai hadani da wani tunaninta idan ma tunani zanyi ai sai dai nayi naki dan kece kan gaba acikin rayuwata.

yanzu hk tunanin yadda zamuyi sabuwar rayuwarmu nake tare da tunanin yadda zan nuna miki so fiyye da komai arayuwata yakarasa mgnr yana mikewa zaune ,tare da tsura mata mayatattun idanunsa wanda suke kashe mata jikin a sanda duk yayi mata irin kallon , numfashi yaja ya sauke yana sake tsareta da idanunsa.

" Allah yasani zainab ina matukar ganin kima da darajarki sbd kamewarki da jin tsoron Allah ki.... "bakiji yadda zuciyata ta kwadaitu da matsananci son aurenki ba na matsu na matsu na mallakeki gbdy sweet bby ..

shiru ....tayi tare da zabga uwar tagumi tana kallonsa batare da tace masa komai "ya kika yi shiru?

"babu komai my life kawai tsoro da fargaba ne suka taru suka min yawa, sbd yadda naga kana zumudin nan nasan bazaka taba daga min kafa ba, fatana idan muyi aure duk abinda zaka gani daga gareni zaka min uziri akan sa .

"karki damu zan miki fiyye da uzuri sbd nasanki nasan halinki bazaki taba aikata wani abu wanda ba daidaita ba.

"mgnr tsoro da fargaba km ki ajiye shi agefe zan biki ahankali bazanyi hurting dinki ba ... tasa hannuwanta duka ta rufe idanunta ala'mun jin kunya wadan nan daddan kalamai masu tsuma zuciya ya dinga gaya mata wanda alokacin har taso manta inda take .
hirar soyaya suke atsakaninsu sosai, tsawon lokaci ya dauka yana zaune agurin sallah kadai ke tadashi yayinda zuciyarsa gbdy babu abinda take kwadayin son ganin kmr su'ad amman ko motsin wulgawarta bai gani ba wanda alamu ma sun nuna masa kmr bata cikin

3 Comments On SAI KA AURENI DOLE
avatar
zainab-ishaq

1 year ago

Reply

Love it ????????

avatar
zainab-ishaq

1 year ago

Reply

Yes and I want to download it

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to zainab-ishaq

In order to download you have to subscribe for our package at https://tnovels.com.ng/subscribe

Please Login or Register in order to submit comment