Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dayayi musu darasi akai cikin harshen tsadadden turancinsa kai kace baturen America ne kalmomin oral English dayake ta ambatowa yana jerawa layi layi batare da yana duba litafi ba, kai kace shine ya lakaba musu suna dan yadda ya haddacesu tsab.
muna nan tsaye agurin yayinda zazzakar muryarsa take sake shiga kunuwanmu hakan yasa sai dukkanmu muka k'agu mu ganmu cikin ajin mu sanyashi agabanmu domin mu kalli fuskar ma'aboci muryar kasancewar ya juya mana baya
yana cigaba da bada darasi. yasa gbdynmu da muke tsaye a waje muka matsu bamuyi ido 4 dame wannan zazzakar muryar nan.
keyarsa kawai nake iya hangowa daga nesa yayinda take km alokacin gabana yashiga faduwa da karfi wanda bansan dalili ba.
daga yadda nake hangoshi nasan ba bakar fata bane domin a kallo daya zaka tabbaar da hkn fari ne sosai sai dai sumar kanshi ce kawai irin namu ,sai dai gashin agyare yake yana sheki da daukar hankali sannan ya kwanto sosai zuwa byn keyarsa.
na gane hkn ne sbd k'anshi babu hula kmr an ce ya juyo zuwa bakin kofar ajin.
ya sauke kyawawan idanunsa akaina tunda nice daga gaba sosai yana sanye cikin wasu hadaddun bakaken kaya riga da wando sai farar riga me dagon hannu daga ciki .
ya daure wuyansa da jan kyalle wato tie ..ahankali nayi tsuru ina kallon kyakkyawar fuskarsa wace take min kmr nasanta.
lafiyayyen fatar fuskarsa nake cigaba da kallo me dauke da launi me tsananin kyau irin kalar launi da take matukar tsada a wannan lokacin nayi shr ina tsananta kallonsa da tunanin inda nasan fuskar .
ahankali cike sanyin jiki da sanyi tafiya yasoma takowa ya matso kadan kusa dani sai ga fararen idanunsa tar ina kallo take na ji wata mummunar faduwar gaba wanda in ba sa'a akaci ba hatta wayanda ke kusadani zasu iya jiyo yadda kirjina ke bugawa da karfi a lokacin.
tunda nake aduniya ban taba gami irin wannam dara daran idanuwan ba, masu tsananin haske daga ciki tare da bakar kwayar idanu me tsananin baki da tsagwaron kyau wanda aka zagayesu da wasu gashin idon da gashin gira masu tsananin yawa da tsananin baki .
ya gyara sunyi kyau a natse ya sake matsowa take zuciyata tagama gano inda tasan fuskar mutumin dake tsaye nesa dani kadan.
gbdy ya dubemu yana kallonmu, bama ni kadai ba duk wata ya'mace dake gurin sai taji ina ma wannan kadarar dake tsaye agabanmu ta kasance mallakinta ce. yayinda nasan yan uwasa maza ma sai da suka raya hk acikin zuciyarsu ina ma sune da wannan hadadden kyawu nasa.
ga nagarta ga kyau ga ilimi ga iya daukar wanka ashe duk ganin danayi masa shekaranjiya a aiport banga kome ba yanxu ne nake karewa sansar jikinsa kallo.
, kyau me sunan kyau sai ma ka kalleshi gbdynsa daga samansa zuwa kasansa dagon mutun ne sosai me kyawun sura gashi bashi da kiba dayawa hk bashi da rama jikinsa daidai mgn yayi mana cikin zazzakar muryarsa cikin harshen tsadadden turancinsa ya kuka tsaya alhalin ana gabatar da darasi?
jin sautin muryarsa har yafi komai na tsantsar jikinsa ..
fuskarsa a dan daure yacigaba da mgn kamata yayi ku nemi izinin shigowa baku tsaya ba.
domin baku san irin hasarar da hkn zai jawo muku ba sai kun yi kuskuren rasa darasina . dan hk
kuyi hanzarin shigowa wannan km yazama karo na karshe daza'atsaya min akai yayinda naks bada darasi ya karasa mgnr yana nuna muna cikin aji da hannusa .
nice a farko amman bansa yadda akayi gbdy wadanda suke byna suka rigani shiga ba.dan tunda yasoma mgn komai ya nami kwance min na manta inda nake banda tsalle babu abinda zuta take.
sai da kowa yagama shiga sannan nasoma daga k'afafuna na shiga.nasamu guri kusa da aminiyata ramlat na zauna ina sauke naunauyen ajiyar zuciya.
shi km yacigaba da bada darasi xuwa sanda ya kare ya bada Assigment har zai fita ya dawo yayi shr yana kallon gbdynmu sannan ya sauke kyawawan you akaina yace inda munga assignments din na kawo masa.
sannan ya fita.
ai yana fita hayaniya ce ta kaure acikin ajin kowa na fadar albarkacin bakinsa akansa.
barin ma matan ajin sai cewa suke yau sun ga wanda yaci uwar saleema a kyau.
yayinda wata budurwa itama diyar me kudi ne sosai, dake bayana a zaune naji tana cewa tunda ta daura idanunta akanshi taji takamu da matsanancin sonshi km ko ta wani hali sai tabi ta mallakeshi .
take na juyo gabana na faduwa faduwa wanda har lokacin bansa me sajin hk ba, nace subuhanallah ina me hb yar uwa karkiyi hk kirkice ko ta wani hali ne sai kin mallakeshi ba gara kiyi addua ba idan da alkari km rabonki ne sai ki sameshi cikin sauki. Nafisa tace ba wai zan fita daga muslinci bane akansa amman dole nasa malaimaina su min aiki akansa .
km alokacin na fahimci dayawa daga cikin matan ajinmu sun mato akansa.
ni dai naja bakina nayi shr domin bana jin zan iya bata lokacina akanshi ita kanta Ramlat zancesa ta dinga min tunda ya fita.
tun iya tsawon rayuwata banta ganin mutun me kyawunsa ba ko ke kin taba gani?
tayi min tmbyr tana kallona .
na danyi murmushin takaici tare da girgiza mata kai .
wlh shi kansa yasan yayi bala'i haduwa shiyasa sai wani yauki yake gurin bada darasi km daga zaiyi jijji da kai .
nan ne na katseta ta hanyar cewa bazai yi ba km da al'amun zaiyi saukin kai dai duba da yadda ya bari muka shigo.
hk ne km fa zancenki zaiyi saukin kai da ala'mun km darasinsa zai yi sigari mukayi dry. ahankali nake duba littafina ina na sake zarta matan ajin kusan rabinsu sun nuna maitarsu a filli akanshi.

lokacin da muka tashi makaranta agajeye na isa gida byn na sauke ramlat a gidansu dayake tare muke tafiya gida.
da safe km yayanta idan zashi aiki ya sauketa ,ramlata ba diyar kowa bace amman suna da rufin asiri.
Allah neya hada jinina daita sannan bawata shahararriyar me kyau bace baka ce irin kalar kasar . nagama duk abinda nake a duk sanda na dawo lukul na kan dauko dararrusan da mukayi aranar ina dubawa wanda tun ina primary school, duk sanda na dawo mamma zata sani yin wanka naci abinci the nest thing karatu ne kafin malamin islamiyyarmu yakaraso, to hkn ne yabi jikina. nasoma duddubawa atsanake ina sake fahimarta komai daki daki har sanda nazo kan darasin sabon malamin turancinmu tun dana zurawa litafina ido nakasa daukewa sannan na kasa fahimtar komai fuskarsa kawai ke min gizo da yanayin yadda yake sarrafa harshensa da labbansa .
tsawon lokaci ina zaune narasa meke damun tunani akansa ,hk ina ji ina gani na hakura da karatunsa na rufe littafina batare da na fahimci komai ba.
duka yinin ranar nayi shi cike da tarin tunaninsa maramisaltuwa gbdy na dawo tmkr wata Mara lfy dan har yar kulawar danake bawa hjy babba inda nagama nazarurrukana ta zuwa yi mata massaging din jikinta banje ba ..
a wannan ranar nasoma tsintar kaina cikin damuwa da bugun zuciya.
kokarin na dingayi naganin na kawar dashi da tunaninsa acikin kwalkwaluwata da zuciyata.

tunda wannan sabon malamin turanci yazo wanda ni har lokacin bansa cikakken sunansa ba.
matan makaranta suka haukace tun daga kan nasama damu har zuwa kanmu dana kasa damu. suka shiga binsa masu nuna masa afuska nayi masu nuna masa ajiki nayi hk zalika masu fitowa gaba da gaba su gaya masa nayi .amman shi ko ajikinsa dan ma ko kallo basu isheshi ba,dan babu ruwansa dasu baya shiga harakarsu yana da matukar kamewa da mutunta kanshi .
asali ma baya son abinda zai hadashi da dalibai .
shiyasa yawancin lokuta yake tsayawa tsayin daka ya bata lokacinsa wajen gabatar da darasi ta yadda mutun duk dakikancinsa aji, sai ya fahimcesa .
km sai ya tabbatar da angane yake fita dan bai son ana yi masa layi da yawan zariya a office kmr yadda yaga wasu daliban nayiwa malamai. wannan halin nasa yasa dayawa daga cikin dalibai ke ganin girman kansa .

ahankali nake daga kafafuna zuwa hanyar office dinsa zan kai masa assignment din dayabamu akaro na uku amman bana zuwa kai masa kmr yadda ya bukata ,sai dai na tura masa ramlat .
kmr ma yau ita din na tura da farko ya dawo daita akan ta kawo min dasu na kawo da kaina ,wanda daman kusan duk lokacin da wani malami yabamu assingment ko test mukayi nice ke kaiwa. wanda a farko ilimina ne yasanya hk .
kaina tsaye na tunkari office dinsa dauke da tarin takardu ahannuna sai dai zuciyata cike take da matsananci gabana na faduwa.
office na biyar ne kmr yadda aka kwatantamin daga hannun dama wanda daga saman jikin kofar office kadan naga an rubuta da bakin rubutu km da manya harafai *prof taufeek abubakar tafeeda gulunbe* wannan ne lokacin da nasan completel name dinsa ,kaina tsaye na kwankwasa kofar office din. tsawon minti goma ina tsaye sannan akabani umarnin shigowa .
ina shiga nayi sallama tare da gaishe shi a ladabce amman yaki amsawa sannan yaki dagowa yacigaba da aikin dana iske shi yanayi.
dan hk jikina asanyaye nasake yunkurin gaisheshi muryarta na craking .
numfashi ya sauke kana ya dan motsa bakinsa ya amsa kansa na duke still yana rubuce rubuce. nace sir ga takard... tun bankarasa ba ya katseni da hannusa yayi min nuni dana ajiye a saman wasu takardu dake kan table din tare da niyyar juyawa na fice daga cikin office din. yace dawo nan cak na tsaya tare da kiran wayyo..hhhly Allah cikin harshen faransanci na juyo ahankali zuwa lokacin har ya mike daga inda yake ya nufi fridge idanuna suka sauka akanshi sanye yake cikin shigarsa ta kullun suit sai dai wannan karon me launi ash colour ce da dan siririn medical glass manne a idanunsa.
ruwa ya dauka ya tsiyaya a glass cup ya kai bakinsa ya dan kurba ya ajiye tare da kulle garon ruwan ya mayar ya sake juyowa gareni amadadin ya koma mazauninsa sai naga ya jingina jikinsa da jikin makeken table din office din ya harde hannayensa duka a kirji idanuna akaina yana kare min kallo tsab. kasa tsayuwa nayi agurin sbd yadda kafafuna Suka soma sagewa nayi saurin durkusawa kasa kasamakon rawar da suka somayi muddin banyi hkn ba ina iya zubewa ta karfin tsiya.kyawawan idanunsa har lokacin suna kaina ni din ma dagowa nayi ahankali na daura idanuna akansa fuskar nan babu wani annuri kirki ha'a! ya km kikayi kasa..? nayi saurin sauke idanuna kasa km sai lokacin naji wata matsananciyar kunyarsa takamani .
dan hk banko sake yunkurin dagowa na kallesa ba.
na furta hkn naga yafimin alkhari ne.. ya share mgnta ya wuce siregth to the point dinsa meyasa duk lokacin dana baki umarni kawo min takardunku kike aiko min wata me bakar fuska da ko kyau gani bata dashi ..?
yayi mgnr tsakaninsa da Allah km nasan iya gskyrsa ya fada wanda bansa sand murmushi ya subuce min ba..

ok dry ma nabaki?

nayi saurin gimtsewa am really sorry sir to be your first and last da zaki km turo min wannan me bakar fuskar, nace ok..
oyya tashi ki bar min office muryarta a dake sannan shagwabe nace kai ma ka koma mazaininka sannan kacigaba da abinda kake gimtse harshena nayi da sauri tunawa da nayi da kowaye agabana ni kaina ban san ya'akayi na fada hk ba tsintar kaina kawai nayi da furta masa hkn. ok ki karasa man..kinga sai nayi yadda kika fada .
nace dan Allah kayi hkr subudar harshe ne.
ban rokeki wani hkr ba simple as kitashi kawai nace.
ko bazaki tashi ba sai nayi yadda kika ce?
nayi saurin girgiza masa kaina dan karamin tsaki naji yaja sannan ya bude wani daki dake manne da office din ya shiga .
ai ina ganin ya bar gurin da sauri na mike fito ina sauke naunauyen ajiyar zuciya. koda nako depaertment din idanun yan ajimu caaaa akaina kowa kallona yake tare da son jin ba'asin yadda mukayi da prof taufeek amman na gimtse ba tmbyr da ramlat bata min ba amman naki yarda nace mata komai daga karshe sai cewa tayi halan ma cewa yayi yana sonki duk naga kinyi wani iri?
nayi saurin jan tsaki tare da dubanta muryarta a dan hassale nace shi wannan fa ba kmr sauran malamai da kikasani bane, da kyawuna zai rudesa har ya kai su dacewa suna sona ...wannan kadarar tafi karfina ke har ma da kowa ina gama mgnr na juya mata baya.

tsawon kwanaki uku kenan rabona da sanya prof taufeek a idanuna nashiga damuwa sosai amman ban bari kowa ya gane ba na barwa zuciyata.

yau ma tafiya nake ahankali cike da natsuwa hannuwana duka rungume da takardu akirjina zuwa offince din prof shu'ab sanye cikin wata haddadiyar daguwar riga me igiya ta cikinta wanda ake daurewa tare da sanya dan karamin hijab ne kalar riga ina baza wani kamshi na fitina .
shigowa nayi kaina tsaye office malamin lisafin batare da na tsaya kwankwasawa kasancewar mun saba da me office sosai ai abinda na gani shi ya firgitar dani har shi sai dayagane nayi matukar tsorata da ganinsa prof taufeek abubakar tafeeda gulunbe ne zaune akan kujera da laptop dinsa agabansa yana dane dane amadadin me office din prof shu'ab juyawa nayi da matsanancin sauri zan bar office din naji sautin muryarsa batare daya dago ba "wacece wannan? ya kika koma wa kike nema? yayi min tmbyr ajere yayinda tuni ni har nayi waje daga office din ahankali na maida kofar na rufe batare danayi gangancin sake komawa office din ba jikina na rawa nasoma tafiya damke da tarin takardu wata muryar naji an kirani dashi wanda zuwa lokacin har na kai karshen barandar waje na juyo ahankali security nagani tsaye yace inje ana kirana .
hankali na yayi matukar tashi kan kace me na fara hada uwar gumi tmkr ana hadani da garwashi dan bansan abinda yasa bason kasancewata tare 'da shi ba .
bakina na rawa nace wa kike kirana yace me office din ce .
office prof shu'ab wannan Secutiy din ya sake nuna min gbdy na tsorace ni kaina alokacin bansa yawan ayoyin dana dinga karantawa akasan zuciyata ba.
gani nake kmr ba offince din prof shu'ab nashiga ba.
jiki a sanyaye na tura kofar nashiga ina me jan gefen karamin hijab din na rufe rabin fuskata dashi ina fargaba me zai ce min daya aiko nazo.. muryar a sanyaye gabana na wani irin harbawa nayi sallama nashiga amman na kasa dago idanuna na dubeshi ,yaya kika lek'o kika koma wannan sautin muryar ba irin ta da bace da bancanci sosai na dago idanuna ahankali ina kallon office din prof shu'ab nagani zaune yana dandana system dinsa ba prof taufeek ba .
wani irin mamaki ne ya rufeni alokacin a zahirance ya fahimci hk take na tabbatarwa kaina akwai abinda ke faruwa muryata a sanyaye nace babu komai dana shigo banga kowa bane shiyasa na koma nakaraso sosai cikin office din na mika masa tarin takardu hannuna yasoma dubawa nayi shr ina tunani na tabbar son prof taufeek yasoma min yawa har ya fara min gizo ki zauna man kin wani ja kin tsaya da dukkanin alamu ma kmr atsorace kike.?
nayi murmushi hb dai me zai tsoratar dani kmr yau ne nasoma shigowa office din nan da farko dai na dauka ba office dina nashigo ba shiyasa kaganin hk.
babu wani kullun hk kike kmr za'a cinyeki.
na zauna yana dan jana da hira dayake mun saba dashi sosai nima ina meida masa daina sauraronsa nayi ganin prof taufeek ya fito daga ban daki da alamun alwala yayi dan jikinsa da alamun ruwa ,kallo daya nayi masa na zaro ido take km na tsunkuyar da kaina kasa nasoma wasa da yatsun hannuna take km zuciyata tashiga tsalle nasoma kokuwa da numfashina yayinda zuciyata tashiga oyoyo naganin abincinta ta kasan idanun nake hango irin kallon dayake min kafin daga baya ya dauke idanunsa akaina ina kallo ya tadda sallah ni km nasoma kokarin barin office din prof shu'ab nakirana ina zaki km muna tsaka da hirarmu me dadi naki dawowa.

daren ranar yadda naga dare hk naga rana .
na kasa runtsawa duk inda na juya fuskar prof taufeek nake gani yana min kallon nan nashi me tsayawa arai.
daga karshe na mike zaune atsakiyar gadona jikina sanye da faral singlet da mini siket na tufke gashina atsakiyar kaina tare da zuba tagumi tunda nake banta b'a kuskuren rashin yin bacci ba sai da idanuna suka hadu da prof taufeek .
tashi nayi na sauko daga gadon nashiga zariya a daki tare da tunanin , tabbas ko tantama babu alokacin na fuskanci na kamu da matsanancin sonshi ..
hk na dinga zagaye dakin ina shafar sumar kaina daga karshe na sake fadawa kan gadona nayi ruf da ciki ranar dai da kyar bacci barawo yasamu nasarar daukata.

byn wasu lokuta mahaifina ya sanar da ya'yyuna duka uku mgnr aurensu da jikokin hjy harira byn dogon bayani da nasiha dayayi musu akan maganar hadin auren da harira tace tana bukata.
sannan ya kara da ce musu matsawar basu yarda da wannan auren ba shi zasu jefa cikin matsala da shiga tashin hankali domin komai zai iya samunsa ciki kuwa har da rasashi aduniya da zasuyi abinda yasa kenan sukayi saurin amincewa.
lokacin da yan'uwan mahaifina sukaji wannan hadin sun sha mamaki amman dayake yace musu zumunci za'a kulla km daman su masu son zumunci ne sukayi addua tare da fatan alkhairi.

zuwa wannan lokaci hankalina akwance yake dan ni mahaifina bai min zance wani auren hadi da suka shirya da hjy harira ba.
km alokaci ne shakuwa me dan karfi tasoma shiga tsakanina da prof taufeek sakamakon ilimin da Allah yabani domin ina cikin brilliant student a wannan lokaci yayinda kowa yasan wannan duk inda dalibi me kwalkwaluwa da hazaka yake malamai na mugun sonshi da kara bashi wata kulawa ta musamman .
shiyasa nake da mugun farinjin agurin malaimai yau aka kawo sabon malami gobe zakaji sunan saleema dawood yusif.
inda hankalinsa yasoma karkata akaina duk lokacin daya bamu assignment ko test nice first person din da zan gama km cikin sauri cikin kankanin lokaci zanyi sumint.
a wannan lokacin gsky ni kaina nasan nayi matukar shiga zuciyar prof taufeek .

abangaren shi kuwa duk lokacin dazai yi mark din scref dina a office dinsa ya dinga mamakin irin kwalkwaluwata kenan kmr yau dayake makin takardun test din dayayi mana.
takardata ce farko kmr koda yaushe ahankali ya tsurawa takardar idanun yana kallo sosai ya jinjinawa lamarin kokarina uwa uba yanayin tsarin rubutuna dake maseefar birgeshi sannan kamun kaina shima yana daya cikin abinda yake sake sawa nashiga ranshi domin a wannan lokaci matan makarata sunyi masa caaaa kowace rana akwai sakowanin isar da sakon soyayyarsu gareshi wanda kusan rabin yan depaertment dinmu sun fi yawa kowanensu kokari yake yaga yasanyashi a ido amman bandani dan duk inda nasan zangashi bana zuwa ko office din prof shu'ab danake yawan zuwa yanzu na daina tin da naga bashi da gurin hira sai can sannan ko darasi yake mana nafi meida hankalina da natsuwata akan karatuna .
shi kansa yasan ban damu dashi ban damu da lamarinsa ba.
ta bangare na bai na daina sonshi ba son shi na nan kawai ina dakewa zuciyata ne sannan ina son mutuncina .
da son kare kaina daga gareshi domin yana da kyau ina dashi ta fanin hali kowannemu da kyawawan hali idan ban yi nisa da shi ba karshe acikin nida wani zai iya furtawa da'uwansa kamal so wanda bazan so hk ta faru dani ba.

yayinda duk sanda yashigo class yayi tmby duk yawan tarin Jamar dake depertment din mu mutane kusan dari uku amman nice mutun ta farko da zan soma bashi amsar tmbyrsa a yadda nake bashi amsar tmbyr da yadda nake fadade masa nake fayace masa komai daki daki sai dai kiga yayi shr kawai yana kallon bakina da yadda nake motsa bakin gurin fitar da kalamai sanka sanka cike da natsuwar zuciya yadda ya dace. muryata ga dadi ga zaki inda yake so ma atsaya abayani ni har na zarta gurin wanda ina tabbatar miki alokacin da za'a gaya masa ina matsanancin sonshi bazai taba yarda ba sbd banyi rauni a karatuna ba ta yadda zai gane sannan ko bai fito ya fada ba nasan ina matsefar birgishi.
kan wannan baiwar ilimin nawa da km duk inda akayi kuskuren haduwata dashi gaisuwa ne na girmamawa ina masa gashi bana dreess din banza kmr yadda sauran daliban makarantar keyi wanda duk abinda nake asali daga gurin mahaifiyata nasamo tarbiyar.
wanda kema akan hk na dauraki .
kafin daga baya ki dawo watsar. so sannu ahankali har ya fara mgn dani tare da dan jana ajikinsa da hira tun ina zame masa tare da nokewa da jin kunyarsa har naxo nasoma sakar masa .

munyi exam na zango karshe wanda daga shine zan shiga level 2 prof taufeek ya gayaceni xuwa office dinsa na tayashi mark .
ina tsaka da yin mark shi km yana zaune akan kujera me zagaye da makeken table yana fuskantata muryarsa a raunace ya kira sunana saleemat dan hk yake kirana dashi .
na dago idanuna na zube cikin nasa tare da cewa na'am wai ina kike samo wadan nan amsoshin naki?
gbdy class dinku kece overoll komai akayi kece gaba hatta zaman aji kinki bari su zartaki yakarasa mgnr yana sakar min murmushin me narkar da zuciya.
nima bance dashi komai sai murmushi danayi wanda ya bayyana wushiriyata sannan na meida kaina kan aikin daya sani.

duk wanna qualities din nawa yana cikin abinda yasa shakuwa me karfi da kusanci yashiga tsakanina dashi, ta yadda ko bai nan ina da extral key din office dinsa .
idan baya office zai kirani yace naje office dinsa na dauki abu kaza aguri kaza nabawa wane kaza so a hk a hk wata rana an tashi daga school nazo office na same shi cikin matsanancin damuwa tare da lulawa cikin duniyar tunanin wanda ni bansa abinda yajanyo shigarsa cikin damuwar har hk ba.
yayi shr tare da daga kyawawan idanunsa sama yana kallon celling office dinsa ya afka cikin duniyar tunani sosai .
wanda alokacin ba tunanin kowa yake ba sai na matarsa duk da baya daukar lokaci baije ya ganta ba.
amman this time around ya dan jima bai kai mata ziyara ba wannan distance din da aka dauka tsakaninsu shine silar jefa shi cikin wannan damuwar.
sakamakon tarin sha'awar datadameshi har tayi masa yawa dan duk kwanakin nan da tunanin matarsa yake kwana yake tashi dan ma wani lokaci suna kwana suna video call .
har sanda ya bar tunaninta yashiga nawa yana jina acikin zuciyarsa da gangar jikinsa ta yadda bazai iya misaltawa ba .
na mugu mugun tsaya masa a rai . har
na karasa shigowa bai sani ba sannan bashi da alamun dawowa cikin haiyacinsa.
ganin yadda muka saba dashi yasa na kai hannuna na ja mishi kunne shi still bai ji ba dan hk sai na Kai bakina ahankali dai_dai cikin ramin kunnensa na busa masa iska cikin kunneshi firgib ya firgita ya dawo cikin natsuwarsa tare da dawowa cikin natsuwarsa .
sai yaga na kwashe masa da matsananci dry muryata a sanyaye nace wallah na tsorataka.. natsorataka ...na tsorataka a she kaima kana jin tsoro.
muryarsa a kasalance yace Allah baki tsorata ni ba dan nima bazan yarda ba sai na rama ya Mike tsam zai biyoni inaganin hk nasoma dry ina zagaye office din Allah bazaka rama ba wallah sai na rama muka soma zagaye office din nidashi har dai yasamu nasarar cafko ni na fada cikin faffadan krijinsa ya koma ya zauna dani makale ajikinsa akan kujerar

3 Comments On SAI KA AURENI DOLE
avatar
zainab-ishaq

1 year ago

Reply

Love it ????????

avatar
zainab-ishaq

1 year ago

Reply

Yes and I want to download it

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to zainab-ishaq

In order to download you have to subscribe for our package at https://tnovels.com.ng/subscribe

Please Login or Register in order to submit comment