Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kokuwar raba jikina dana shi.
ke ki natsu man bacewa nayi mun rabu ba fa kawai dai for the mean time zamu kauracewa juna har ta tafi ba dan komai yasa nace miki hk ba nasan halin matata tana da maseefar kishi akaina matsawar taganni dake zata iya illata min ke kinga ai ta cuceni pls salemat ki fahimceni na fixge jikina ta karfi tsiya ina kuka nace nasani ai wata rana sai ka min hk amman koma fiyye da hk. sbd matar zatazo shine zaka nesanceni ko?
amman babu komai na barka da alkwarin daka daukarwa kanka alokacin da kake kokarin yin disvirging dina idan ma kana da niyyar cin amanata ne Allah zai gaugauta saka min. karka manta
ban san komai ba kaine kasoma meidani hk ina gama fadar hk na juya na bar office din ya biyoni yana kiran sunana nayi masa banza . har gurin motata yabiyoni haba salema yadda kika dauki mgnr ba hk bane kalli yadda kika janyo hnkli mutane kaina, kai kaso hkn takasance kasan kana da wannan jin kunyar meyasa kasoma soyayya da yar cikinka naja motata na barshi nan.
daren ranar prof taufeek yazo gidanmu sbd yakasa samun natsuwa ina daga bancoly dina na hangoshi nace kar abarshi yashigo .
bai damu ba yaja ya tsaya kofar gidanmu jingine da motarsa yana kallona daga inda yake..ni km ina tsaye sanye da riga da wando na bacci dana gaji da tsayuwa nakoma ciki wajen awa daya na sake lekowa yana nan tsaye tsaitin dakina naja tsaki hk na dinga lekashi yana gurin har asuba inda bacci ya daukeni a bancoy ..daga wannan lokaci na toshe duk wata kofar dazata sadani dashi shima xuwan matarsa yasa yaji dadin yaddda nayi masa banza dan ko koyardamu yashigo yi ,fita nake nabar ajin har sai yagama na dawo har prof shu'ab yakirani ya tmbyeni me ya hadani dashi nace babu komai.
a wani yammaci dana shigo school kasancewar ina da evening lecture.
ina sanyo hancin motata inda zanyi parking idanuna suka sauka akanshi shi da matarsa suna fitowa daga dogon baradan dazata sada mutun da farfajiyar makarata.
tana rungume danta akafada shi km yana rataye da jaka yar saman suit dinsa na makale da kwarin hannunsa gabana ne yashiga faduwa da sauri nakarasa parking din motata na zauna naki fitowa ina kare musu kallo matarsa farace sai dai nafita fari sosai kyakkyawar mace ce sai dai dan abu daya da bata dashi ,hancinta bai da wani tsaye dan duk wanda ya kalleta bazai ce mata me dagon hanci ba .
akwai ta da idanuwa masu kyau gaske sai dai gajeruwa ce amman ba gajeruwa dukus ba sannan tana dan da fadin baki sabani nawa dan karami .
take jikina ya dauki rawa ganin dana masu zuciyata kuwa wani bugu take ahankali na sanya jikina kuzari na fito .
ina fitowa naga ya juyo da sauri nasan kamshim turarena ya jiyo aiko muka hada ido dashi gabana yashiga dokawa.amman hkn bai hanani takowa ba. daburcewa yayi yana kallona daidai na karaso inda suke naji tace my Hrt muje man.
ni km dan sake rage tafiyata nayi lokacin da na hango walid yana sakar min murmushi .
hannu nadaga masa kawai dan na kular da zuciyar taufeek bawai dan naso hkn ba dan bana shiga tsabgar gayun school . walida wani matashin gayene dake maseefar sona amman sbd taufeek naki bashi dama ,
kasa motsawa prof taufeek yayi daga inda yake tsaye har sanda walid yakaraso gareni muka soma mgn kasa kasa muna murmushi. nan fa zuciyar taufeek takasa hakuri sbd maseefar tashin hankali daya tsinci kanshi ciki take kishinsa ya motsa akaina bai san sanda yakaraso garemu ba yace kai tsayuwar uwar me kake daita ..?
sir babu komai kawai muna gaisawa ne. ni km na kalleshi asheki sanan
nace kanajina ko walid daman fa akwai mgnr danake son yi dakai which is very very important muje ko.. nadaga kafafuna kenan naji ya cafki tsintsiyar hanuna ya juya yasoma tafiya dani nace meye hk ne kasar min hannu bai tsaya ba sai gurin dana paka motata ya amshi key'n motar ya bude ya turani ciki ya kulle motar gbdy ya juya ya koma gurin matarsa dake tsaye cike da matsanancin mamaki da shock yace tashiga suje .
tun daga nan masefafen kishinta ya motsa taso zuwa inda nake cikin mota zaune domin naga sanda ta nufo inda nake ya hanata bandai san me yace mata ba ina kallo ya kamo hannuta yasata cikin motar yashiga suka bar gurin tun cikin mota take masa maseefa tare da tmyrsa meye tsakaninsa dani yace nothing tace karya ne akwai ,yace ok nayi karyar.
byn ya kaita gida ya juyo ya dawo school ya bude motar yashigo ya zauna yashiga min ruwan bala'i ina ramawa ok bakinki ya isa yanka ki shiga hknli dani salemat zan shuka miki rashin mutunci.
rashin mutunci km na nawa sai dai kar a sake bani key din motata inada abin yi nakarasa mgnr ina mika masa hanuna idan bazaka bani ba na kama gabana
ya kamo hanuna yasanya min key ki kama kanki salema dani banason mu'amularki da maza ,dan Allah ki tausaya min.
fixgar key nayi na fito dole tasa ya fito daga motar na kulle na juya na barshi nan yana kallon bayana.
yammancin ranar yana komawa gida suka shiga yin tashin hankali zanga zanga da matarsa inda ta hada kayanta tace gobe goben nan zata koma.

ina cikin damuwa kwance adakina tunaninsa nake tare da jin haushin fifita matarsa dayayi akaina kiransa yashigo wayata ban daga ba sai dayayi min kira goma sannan na d'aga nace lfy waye..? yace ke banson rainin hankali nizaki cewa waye byn kingama hadamin zafi kin hadani fada da matata a dalilin dagula min lisafi dakikayi .
ta shirya komawa Nigeria tabarni sai ki shirya karbata kmr yadda kika saba nace never in history taufeek...idan ma bacci kake ka farka sannan kasawa ranka wani abu me kama da abinda kake mgn akai bazai sake shiga tsakanina da kai ba... nifa ka nuna min bani kake so ba jikina kake so, soyayyarkar na gurin matarka kaje ka lallaba matarka ta zauna tare da kai so that zaka samu abinda kake so enough. amman ni saleema dawood yusif bazan sake mallaka maka kaina ba tsaki yaja ya kashe wayarsa.

washegari tabi jirgin safe takoma yakirani yace min ta wuce nace allah ya kai lfy tare da katse kiran.
sosai na fita harkarsa na daina hulla dashi na dinga nuna masa ko in kula duk abinda zaiyi baya gabana shima tin yana sharewa har fa abin yasoma barazana dashi
yasoma neman shiri dani zanga zanga ni kuwa na rantse na sake rantsewa tare da alkwarin babu abinda zai sake shiga tsakanina dashi.
dan duk nacin sa gurin mushirya naki yarda da shirin.
dan hk wata rana monday muna zaune a sitiroom ni dashi byn damben bala'i da sukayi da securities din gidanmu gurin sun hanashi shigowa wanda daga karshe sai dana sa baki suka barshi yashigo.
yatasani agaba atsakiyar kafafunsa tare da tsura min idanunsa ya zagaye kuguna da hannuwansa duka yana bani hakuri akan laifin da yayi min .
na zuwan matarsa wata irin razananniyar tsawa mukaji from know where an buga mana na mike a frigice na bar kusa da prof ina zare ido jikina na rawa tsoro suka min duran makiya na dinga kmr na saki fitsari tsabar tashin hankali dana tsinci kaina mahaifina nagani tsaye yana kallonmu a fusace yace waye shiiiiiii? yayi min tmbyr yana kallona take jikina ya sake daukar karkarrawa na kasa mgn.. wani figici da matsacin tsoro ya farmaki zuciyata tare da min diran makiya .
ya juyo yana fuskantar taukeek dake tsaye tare da auna masa wani irin banzan kallo me hargitse kwanya sannan yace waye kai...?
daga ina kazo nan ?

meye kawoka gidana km har cikin nan ?

shafa sumar kanshi yayi sannan ya gaida mahaifina cike da ladabi. dakatar dashi yayi ta hanyar sake cewa waye kai.. na tmby ba gaisuwa ba.
sunana taufeek abubakar tafeeda gulunbe ni malaminta ne sannan ina sonta .
km aurenta nake son yi.... shine ka tasa min "ya" agaba ka kwakume kmr zaka cinye min ita? duk fadin gurin nan bai isheka zama ba sai sanya min ita ajikinka .. kai tun yaushe ma kasoma zuwa gidan nan da banida masaniyar hkn?
prof taufeek wanda yashiga tashin hankali ganin reaction din mahaifina yayi saurin cewa shekara daya da wata takwas kenan inna lillahi wa inna ilaihi rajiun abinda naji mahaifina ke furtawa kenan yana sake maimaitawa sannan yace ina raye acikin gidan .. Kai a garinku aka ake neman aure ?prof taufeek
yayi shiru ya sunkuyar da kanshi kasa abinda nake son sanar da kai yadda kaxo neman auren yarinyata kwata kwata bai yi ba amman na yafe maka sai abu naga da zagaya maka na dade dayiwa yarinyata miji ..
da wani mugun sauri ya dago idanunsa yana duban mahaifina yace eh abinda kaji nace hk ne nayi mata miji dan hk ga hanya ka kama gabanka kabar min gida tun ban sa ma'aikata sun hukunta min kai ba . tunda mahaifina yasoma mgn naji zuciyata ta tsaya cak ta daina aiki na wucin gadi na dawo tmkr wata matacciya atsaye akan kafafuwana kusan minti biyu sannan zuciyata tacigaba da bugawa da karfi tmkr ana bugamin guduma mgnr babana ba iya kunnena kadai suka tsaya ba har cikin tsokar dake makale akirjina nake jin dacinta .
matsowa nayi kusa da mahaifina ina kallonsa ina son ya sake mgn domin so nake nasake jin abinda ya fada din karya ne ba gsky ba .
sbd dacin kalmar danaji ya fada lokacin.

ahankali naga prof taufeek yayi kasa ashe dukursawa zai yi agaban mahaifina muryasa na rawa yace ba... ba kayi hakuri nasan nayi kuskuren gurin neman maka yarinya batare da ixininka ba amman dan girman allah karka hukuntani bisa wannan kuskuren dana aikata sbd ina son saleema ..so kuwa me karfi na kwadaitu da son aurenta nayi hk ne sbd kada na yanke mata karatunta ko kawo nakasa cikin rayuwarta.
wanda bansa kuskure na tafka ba kayi hakuri dan girman allah karka rabani daita.
rabani daita tmkr barazana ce ga rayuwata .
nima dukursawa nayi jikina na kirrrma kmr yadda jikin prof keyi .
hawaye kuwa kmr fomfo sai ambaliya suke saman fuskata ,bakina na rawa nace karka min hk ya babana... karka rabani da rayuwata ina son taufeek bazan iya rayuwa babu shi ba asanina nasan baka min miji ba kayi hakuri muyi kuskuren..... a fusace ya dagoni ya daukeni da wani gigitaccen mari ki min shr ..
tunda har kinsa ki kawo nmj gidanku batare da sanin mahaifinki ba zaki iya yin feyye da hk ke idan diyar albarka ce ba gurina zaki turo sa ba .
kwata kwata banji zafin marin dayayi min ba na sake cewa kayi hakuri baba tsoron aikata hkn nayi, ahankali naga prof taufeek ya mike tsaye ya tsura min ido tare da alamomin tmby iri iri akan fuskarsa sai ma nake hango zargina cikin idanunsa tsawon lokaci ya dauka yana kallona sannan ya juya yasoma tafiya nabishi na rungumeshi ta baya dole ya tsaya jikinsa kirrma kar ka min taufeek....
karka barni taufeek... karka tafi kayiwa babana mgn ta fahimta nasan zai gane irin son da mukeyiwa juna ... ya juyo dani tare da ware hannunwasa duka zai rungumeni yaga yadda mahaifina ke auno masa kallon tsana ya fasa ya zareni daga jikinsa yasanya kai zai fice na tsugunna a gurin tare da daura hannuna duka saman kai na rusa kuka me cin rai ina kiran sunansa don't go taufeek.. ka tsaya kabawa babana hakuri yana sona nasan zai baka aurena.... amman ya bar gurin batare daya tsaya ba wani irin haushi mahaifina yaji yakamashi agabansa na rungume wani ina kukan soyayya .. yaushe ne yayi wannan sakacin da rayuwata a tunaninsa duk tattalin dayakamata ya min bai ce dani komai ba illa cike da sanyi jiki ya kamo hannuna muka shiga cikin gida inda mamma take tana ganimu ta mike tsaye tana kiran lfy..?
ina fa lfy yarinyar nan she zance take acikin gidan nan banida masaniya.
bata isa yin zance bane ?mamma ta tmbyeshi . sannan shi wannan mutumin nasan yana zuwa gurinta dan tasanar min kafin yasoma zuwa.. ni dai nadakatar dashi sbd nayiwa "yata" miji dadewa.. bangane ba? yadda kikaji din hk nace sannan daga yau nayi cancelling zuwa wata makaranta ya juya yashige dakinsa ya barmu tsaye cikin rudani da tashin hankali sake rushewa nayi da wani sabon kuka nayi dakin da ake jinyar hjy babba na kamo hannuta cikina nawa ina kuka ina kiran hjy ki warke auren dole babana zai me da wanda bansani ba.. ..
ki warke kakata nasan da kina da lfy ke kadaice zaki min gatan tsaida wannan auren.. yadda nake kuka hk naga hawaye na fitowa daga idanunta motsi take da bakinta da alamun son yin mgn amman babu hali sannan a wannan lokacin na fahimci tasoma fahimtar komai ganin wannan durkuson danayi ba shine mafita gareni ba nabar dakin da da gudu zuwa nawa na fada gado ina kuka har da shesheka na dauki waya nakira number taufeek amman yaki daga na sake shiga damuwa ji na dingayi kmr nayi hauka wani irin radadi da zafi zuciyata ke min na dawo tmkr mahaukaciya sabuwar kamu a dakin ina sambatu ina cigaba da neman layinsa .

*****
byn kwana biyu prof taufeek ya sake zuwa na musamman gurin mahaifina,akan yayi hkr ya bashi aurena , amman furrr yaki yace shi yayi min miji.
yace to ya barni na koma school kar ya tsayar min da karatu..
yace bazanyi ba naga ba yarka bace tawa ce ko lokacin danayi ra'ayin tayi karatu har nasata kai ne kasani .
dan hk mlm ka tashi kabar min gida.

ni kuwa iya tashin hankali nashige shi,gbdy duniya ta cakude min waje daya banta taba sani hk tashin hankali zai riske rayuwarta ba ,na dauka irin so da gatan da iyayena suke nuna min ko dabba na kawo ina so zasu amince .
wata irin soyayyar prof taufeek ce kawai take yawo dani ahalin danake ciki.
jin soyyyayyarsa nake tmkr itace madogarata banson kasra kaina domin ina son mallakarsa arayuwata bance hk zan kashe kaina kowa ya huta tunda abun nan ya faru na daina ci na daina sha sai kuka na shiga tashin hankali.
rarrashin duniya mamma ta min akan nayi hkr na cire soyayyar taufeek acikin xuciyata nabi umarnin mahafina.ina kuka na dubi idanun mamma nace bazan iya cire sonshi ba mamma......ina son taufeek rasashi daidai yake da zaki rasani a duniya , yadda nashiga damuwa da tashin hankali hk mahaifiyata tashiga tashi hnklinta.
wanda har sabani yaso shiga tsakaninsu da babana adalilina abinda bai taba faruwa ba kenan tun iya tasowata.
na dauka radadin rashin amincewa zabin babana zai tsaya iya kaina ne amman sai naga yashafi mahaifiyata.
daga parlour indake zaune na tsinci muryar babana yana cewa daman ke kike daure mata gindi sannan kike kokarin bata min tarbiyar yarinya sannan kece kike neman jifa zukatanmu cikin tashin hankali da tun farko zuwansa kin sanar min da nasan matakin dauka da yanzu batayi zurfi cikin soyayyarsa har hk ba nasan dabazataba kin karbar zabina ba....
kuka mamma take da idanunta tace na gode dawood da sakayar cin mutunci amman kasan bazan so lalacewar salemat sbd ni uwa ce kai km uba duk yadda ta lalace sai nafika shiga tashin hankali fiyye da kai amman naji duk bayaninka km na amsa laifina amman waye shi mijin da kayi mata. yaki gayama sai da rigima tayi rigima sannan yagaya mata nan fa jikinta yayi maseefar sanyi takasa cewa komai.
sbd tasan abin yafi karfinta ,ya dawo kusa daita tare da kiran sunanta habiba lamarin ne yafi karfina ..
ni kaina bansa zan iyawa mamana irin wannan auren ba me tattare da bakinciki Amman kiyi hkr tare da yimata addua.
hawaye ne yashiga zubowa daga kwarnin idanun mamma tarasa wani irin aure mijin nata yake hadawa da ahlin hjy harira .
idan auren zumunci yake da bukata ai hjy babba itama tana da tarin jikoki adakinta .
meyasa bazai bawa wani daga cikinsu ba ,sai cikin jikiokin hjy harira.... ?
muryarta cikin kuka tace kayiwa maza auren dole amman bai kamata kayiwa mace auren dole ba domin gudun abinda zaije yazo..
salema kadai Allah yabamu mace yakamata mubata farinciki ba bakinciki ba.
mutumin dake sonta bashi da makusa meyasa bazaka bashi aurenta ba domin kwanciyar hankalinmu ..?
nima bance yanada makusa ba nasa an bincika minshi mutumin kirki ne me nagarta amman idan nabashi auren salima nacewa hjy harira me... ?

tsawon wata uku kenan ina tsare a gida babu inda nake zuwa zancen zuwa makaranta ma andaina mgnrsa.
wanda kafin zuwa wannan dan lokacin nagama sa'insa da dangina da yan gidanmu gbdy akan prof taufeek babu wanda nake ragawa duk wanda bai son aurena dashi bana shayin na ci masa matunci hade da zagin rashin mutunci ,sannan sai alokacin nasan wanda za'a bawa aurena... wato yakub dan gidan goggota
shima bashi da laifi ko makusa ta fanin kyau da halaiya amman zuciyata bashi take muradi aura ba....

wata ranar monday ina kwance adakina ba bacci nake ba amman idanuna a lumshe suke naji saukar hannu a wuyana har ansoma shafamin wuya na zabura na mike zaune ina zare idanuwa wazangani........

mmn sudais ce

💗💗💗💗💗💗
SAI KA AURENI DOLE
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗



~NA~



*AYSHA A BAGUDO*



~DEDICATED TO~
HAUWA A USMAN
JIDDARH


*qala rasulillahi sallallahu alaihi wa sallam: ittakil laha haisu makunta*

*Allah's messenger saw said fear Allah wherever you are*

page 43

prof taufeek nagani zaune ya tsura min kyawawan idanunsa yana kallon kayan dake sanye da jikina wando da riga bacci ne masu matukar kyau da taushi wanda basu wuce iya cinyata ba.
gashin kaina wanda suka dade a hargitse sun baje a bayana, idanunsa ya tsura min sosai sbd wani irin kyau na mishi wanda hkn yakasa boyuwa acikin kwayar idanunsa.
"ahankali ya matsoni kadan yana cigaba da auno min kallon dake kashe min jiki aduk sanda yayi min.
yayinda ni km na dinga jin wani irin yanayi na daban ajikina na tsinci kaina ciki farincikin ganinsa .
wani irin dadi ne yamakani har bansan sanda hawayen farincikin ganinsa yashiga gangarowa bisa kuncina ba.
zuciyata tasoma beating da sauri sauri tare da jin dadi tana oyoyo wa abinci ruhinta.
yaushe rabon data sanyasa acikin idanunta.. da sanyi jiki yake karasowa zuwa inda nake zaune .
ahankali har yakarasa isowa gareni ya ciro hanky agaban aljihun rigarsa ya kai hanunsa yasoma goge min hawaye dake tsiyaya daga ciki kwarnin idanuna , wanda narasa dalilinsu farincikin ganinsa ne ko km kaurace min da yayi ne na tsawon kwananki nan ..
my laulooooo ya furta ahankali yana dan murmushin nan nasa me tafiya da ruhina.
" ke saurauniya ce ,baki cancanci wannan kukan ba .
idan kina kuka ni km nayi yaya?
na dago idanuna ina kallonsa still hawayen idanuna sunki tsayawa .
ki daina kuka nan pls idan baso kike nima na miki kuka ba, nasan ina da nasaba da wannan kukan naki amman kiyi hkr wallah ni kaina ina cikin damuwa da tashin hankali akan matsalarmu Ina matukar kaunarki salemat bazan iya bariki ba .
karki yi tunanin zan juya miki baya arayuwa.
ayau zan sake tabbatar miki da ke kadai zuciyar taufeek ta taba kamuwa da matsanancin soyayya, soyayyar km me tsayawa arai da taba zuciya tare da wuyar bari. " tunda yasoma mgnrsa na kafe shi da idanuwana dake cike da matukar bacin rai .
ji yadda yake mgn kmr ya damu da rashin ganina nayi mgnr a kasar zuciyata sannan tsam na mike tsaye nasoma tafiya ina mgn cikin bacin rai baka da abinda zakace min taufeek tsawon kwanaki ka shareni baka damu dasanin ko awani hali nake ciki ba .
yayinda ni duk kwanan duniya sai nayi kukan rashinka amman babu komai kawai ka tafi abinka zan sakawa zuciyata hakurin rashinka na karbi zabin da mahaifina yayi min.
" daman nashiga damuwa ne sbd na dauka kaima kana cikin damuwa kmr yadda na tsinci kaina.
bansa cewar wahalar da zuciyata kawai nake yi ba akanka.
nakarasa mgnr tare da juya masa baya cikin wani irin shauki naji ya fixgoni na juyo a amatukar tsorace nayi luuuuuu sai saman fadadden kirjinsa me cike da yalwa gashi hancina ya sauka daidai inda yafi jin kamshin turarensa oud toch. lumshe idanuna nayi sbd dadin kashim turarensa mai tsayawa azuciya ,da tada sha'awa ya kaiwa hancina xiyara .
ahankali yashiga yawo da hannunsa a sansar jikina tare da tausasan lafazinsa me narkar min zuciya .
kiyi hkr babu ta yadda zan nemeki ne. nakira number's din ki sau ba adadi basashiga nima ina cikin damuwa bazan iya barinki ba .
bazan iya rayuwa babu ke ba, ki tausaya min ki duba yadda nake risking din life dina akanki.
ya kai bakinsa daidai saitin kunena yasoma mgn ahankali cikin rada kibini mukoma kasata muyi aurenmu acan.
zan rikeki amana bazan taba cutar dake ba, zan zame miki komai arayuwa ,bazan bari kiyi maraici ba .
lamo nayi ajikinsa ina sauraron kalamansa dake ratsani batare da nayi yukunri cewa wani abu ko dakatar dashi ba sbd zuwa wannan lokacin magangunsa nashigata sosai fiyye da tunaninki gashi yadda yake yawo da hannunsa a sansar ajikina yana sake kashe min jiki.
km ina matukar son salon dayake min ,
nasan wasu zasuga laifina akan yadda nake sakarwa taufeek jikina shi din daban yake acikin maza.
" hk acikin zuciyata babu na biyunsa fuskata ya hade danashi idanunshi cikin nawa hancinsa kan nawa bakinsa daf da nawa muna fuskantar juna sosai tare da musayar numtashi juna, sannan muryasa a sanyaye yace zaki bini kasata..?
numfashi da ajiyar zuciya naja da kyar na sauke ahankali yacigaba da yawo da hannunsa ajikina yayinda yasoma wasa da lip's dinsa kan lip's dina kafin daga baya ya hade bakinmu waje daya yana tsotsa sai da dauki minti goma sannan ya sakar min baki yana fesa min numfashinsa .
zaki bini kasata muyi rayuwarmu acan jikina a mace na girgiza masa kai ala'mun bazanbisa ba.
bazaki bini ba ...? na sake girgiza masa kai .
ya tsura min ido yayi shr killa yayi hkn ne sbd rasa abinda zai sake ce min ni dai bansani ba.
" ahankali naji ya sakar min jiki ya juya da niyyar barin dakin nayi saurin riko hannunsa cikin nawa na rike gam ina fidda numfashi ...
" ya tsaya batare da juyo ba, karka tafi ka barnin cikin tashin hankali da rudanin rayuwa.. kayi wani abu akan lamarinmu amman badan tafiya dani kasarka..
bazan iya barin iyayena ba suna da matukar mahimmanci gareni ,ya juyo ahankali hannuna rike cikin nashi yasoma murzawa ahankali tare da juyar dani ya manna bayana a kirjinsa yasoma tafiya dani ajikinsa zuwa gefen gadona ya zauna tare da zaunar dani bisa cinyarsa still idanunsa na kaina .
ahankali yakira sunana salemat ....na dago ina kallonsa mahaifinki bai sona saleemat ..ke kadai kike sona nike mahaukacin sonki.. zance da nike miki yanzu hk nakira yayata da muke ciki daya daita na sanar mata da komai dake tsakaninmu dake.
abinda nake so dake kibini mutafi Nigeria idan mukayi aure muka haihu zaki sake dawowa ga iyayenki nima zan biyoki na bawa baba hakuri abinda muka aikata alokacin nasan zasu hakura su yafe mana .
gsky taufeek bazan iya bin ka wata kasa duniya na bar iyayena ba .
"idan nabarsu ciwo xuciya ne zai yi nasarar kamasu su mutu wa gari ya waya ..?
meye amfanin rayuwar da babu

3 Comments On SAI KA AURENI DOLE
avatar
zainab-ishaq

1 year ago

Reply

Love it ????????

avatar
zainab-ishaq

1 year ago

Reply

Yes and I want to download it

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to zainab-ishaq

In order to download you have to subscribe for our package at https://tnovels.com.ng/subscribe

Please Login or Register in order to submit comment