Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tare ,tsawon shekarun da mukayi rayuwa da kai na kasance ina maka wani irin so da uwa kad'ai takema d'anta, kullun kuma ina maka fatan samun lafiya domin sanin wani abu daya danganceka da danginka "sanadin yayana kasamu garkuwa cigaba da rayuwa a doro duniya yayana shine silar komai daka zama a yaxxu...

" yayana yayi wahala da kai daga kasar haihuwarka har zuwa wata kasar daban batare da yasan ko kai waye ba." ya inganta rayuwaka alokacin da kai kanka bakasan halin dakake ciki ba ,amman dan yanzu ka dawo haiyacinka shine zaka manta dani...

cikin abinda bai fi second biyu ba gumi ya rufe shi ya dimauce cikin karfin hali irin nashi ya bude baki yana son furta kalma koda guda daya ce gareta amman ya kasa bayaga girgiza kanshi daya dinga yi yana kallonta da Ammi dake tsaye akansu tana kallonsu cike da matsanancin tausayawa dan tasan wani tashin hankalin ke kokarin sake kunowa cikin rayuwar d'an uwata.. ....

shemah takaraso inda Ammi ke tsaye tare da kamo hannuta cikin nata tana zubda hawaye "hakika nasan yayana yayi kuskure arayuwarsa, kuskurensa kuwa shine amincewa da yayi ya aura min d'an uwanki alhalin yasan yana cikin dimuwar, da watan wata rana zai iya dawowa haiyacinsa wanda gashi hakan yakasance , a yau abubuwa masu radadi da ciwo suna kokarin dawowa cikin rayuwata ciki kuwa har da ciwon zuwan wannan ranar da mahbub d'ina zai tabbatar min da bai sani ba kosanin aurensa dake kaina ba.

Ammi ta rike hannunta sosai cikin nata jikinta na kirrrrma "ki daina kuka haka ni kaina na tabbatar da ke din matarsa ce duba ga yanayinku a lokacin da bai dawo hankalinsa ba "dole nayi kuka saboda nasoma hango karshen zamana dashi duk da bazan so rabuwa da abinda na rayu dashi sama da wasu shekaru ba.


"mun rayu tare da mahbub , mahbub mutun ne me fara'a dasanin darajar d'an adam sannan kullun muna tare dashi sai dai idan baya k'asar, komai tare mukeyi matsawar muna guri d'aya bamu tabayin nisa kmr irin yadda muke a yanzu ba,
"yau ace mun haihuwa dashi nasan ko yaranmu ya kalla wannan kawai ya isa ya tabbatar masa da matsayina agurinsa.


A sanyaye Ammi ta katseta "karkice haka ki ma daina wad'an nan zantuttuka yadda kukayi mu'alamarku kad'ai zai sa ya iya kankarewa ba.. amman zance aurenki dake kansa yana nan har yanzu kina nan amatsayin matarsa ..

take yaji zuciyarsa ta tsaya cak gaba d'aya ta daina bugawa na wani lokacin sannan ahankali tacigaba da bugawa da karfi maganganunta ba iya kunnensa kad'ai ya tsaya ba har cikin zuciyarsa yake jin komai yasoma karasowa gareta yana son ta karyata abinda tace yazama karya ne ba gaskiya ba,
"wani irin aure kuma?

tun kafin yakarasa gareta Ammi ta dakatar dashi ta hanyar cewa "ka tsaya ko kasamu guri ka zauna zance aurenka da ita gaskiya ne tabbas babu k'arya takarasa maganar tana maida idanunta kan shema "
zanso naji yadda akayi kuka tsinci d'anuwana da kuma irin taimakon da kukayi masa..

tunda Ammi ta tsai dashi yake aikawa shemah wani irin Kallon me tattare da alajabi yayinda har lokacin hannunsa ke cikin na Umman su'ad wace ke tsaye sai kifkifta idanunwa take da sake zurfafa tunanin rayuwarta da tarin soyayyarsa gareta," bazantar da rayuwata datayi Sanadinsa iyayenta danginta tana wassafa ina ma komai dake faruwa a halin yanzu karya kunnuwanta suke jiyo mata ba gaskiya bane.." Taufeek d'inta bai da auren kowace mace akansa zasuyi rayuwarsu daga ita sai shi.. yadda Salema ke zurfafa tunaninta haka itama shemah ke tunani, sai dai nata tunanin yasha banban da wanda salema take har zuwa sanda ta matso kusa dashi suna fuskantar junansu.


"ka daina tantama ko jin mamaki abinda nace ni din nan matarka ce mahbub tacigaba da kallonsa tana zurfafa tunanin gidanta da rayuwar da sukayi ina ma ace wannan abun daya faru tazo ta tafi ne da yanzu duk tsiya suna tare kwance guri daya ko zaune suna hira da mijinta ma'aboci zolaya da kokarin danne fushinsa. take ta fara tariyo rayuwarsu dasukayi a baya da dalilin haduwarsu....


*asalin faruwar lamari*

mu asalin yan kasar Nigeria ne kasancewar mahaifinmu haifafen Nigeria ne, mahaifiyarmu ce haifaffiyar k'asar koria gaba da baya.

karatu ne ya kawo mahaifinmu engening Nura kasar koria har Allah ya had'ashi da mahaifiyarmu me suna polina, polina ita ce d'iya ta uku gurin iyayenta wanda tunda ga kanta iyayenta suka tsaida haihuwa atsarinsu yara uku sun isheshesu rayuwa.

A loakinci polina ce tasoma nunawa mahaifinmu soyayya ta fitar hankali saboda a kallon farkon data soma yi masa taji Allah ya dauki soyayarsa yasaka mata cikin zuciyarta ,ta yadda take jin bazata iya hakura dashi ba , batayi sanya a gwiwa ba gurin sanar masa inda shi kuma yaki amincewa da hakan ,ya nuna mata bazai iya soyayya da itaba saboda addini da aladarsu ba daya ba.

"ta bishi tayi magiyar duniya da salon jan hankali amman yaki yarda saboda hudubar mahaifinsa garesa domin kafin yazo kasar koria karatu da kyar mahaifinsa ya yarda har sai dayayi masa alkwarin bazai saurari kowace yarinya ba abinda ya kai shi zaiyi ya dawo kasar .

wannan rashin amincewarsa yasa tashiga tashin hankali daga karshe ta yanke shawarar gaya masa ta hak'ura da soyayyar su zama Friend kawai nan ma yaki yarda haka ta dinga yi masa naci,
dan wannan alakar abotaka tayi amfani da matantakanta, kafin zuwa wani lokaci soyayya me karfi tashiga tsakaninsu wanda idan d'aya bai ga d'aya ba babu kwanciyar hankali ,bayan wasu lokuta sukayi nasarar yin aure bayan wahalun da suka sha kafin su samu mallakar junansu domin lokacin da mahaifinmu ya zowa iyayensa da batun auren polina kin yarda sukayi daga karshe suka hanashi komawa kasar koria gaba d'aya wanda sanadin haka mahaifiyarmu tabiyosa kasar haihuwarsa inda ta nunawa iyayensa shi take so kuma duk abinda suke so zatayi ko cewa sukayi ta zauna kasar Nigeria matukar zasu amince da aurensu zata muslinta ta zauna da kyar dai da taimakon wasu daga cikin manya a dangi ,da mahaifinmu ya shawo kansu aka muslintar da mahaifiyarmu inda ta amshi sunan muslinci da khadija sukacigaba da rayuwarsu a can a nigeria a wani bangare daga cikin gidan.

bayan wani lokacin khadija tasamu ciki tashi kwance babu wuya agurin Allah har Allah ya sauketa lafiya tasamu haihuwar d'a namiji tunda ta haifi yaron, ta hana kowa daga cikin dangin d'aukarsa har mahaifiyar babamu daga babanmu sai ita ke d'aukar baby, duk me son ganin baby sai dai ya iskoshi cikin dan karamin gadonsa ya gansa daga nesa amman bazai ta'ba baby ba,har ranar suna inda yaro yaci sunan kakanmu wato salis tunda polina ta haihu mahaifinmu ya d'auki son duniya ya daurawa polina da danta ganin haka yasa ta dinga bashi shawarar su gudu su bar kasar batare da sanin kowa ba, bayan suna da wasu watanni aka wayi gari eng Nura sun gudu tare da khadija da baby'nsu .

d'angi sun shiga tashin hankali matuka daga baya suka rakasu da addua ,komawarsu koria babu dadewa Allah yayiwa Salis rasuwa lokacin yana da wata 6 duniya dan har yasoma takawa,babu rashin lafiya babu komai kwana ne dai ya kare mahaifina yaji mutuwar sosai dan ba'a ta'ba masa mutuwa ba arayuwarsa kowa nashi na nan a raye haka khadija har tafishi shiga tashin hankali sai ta dinga tunani ko dan ta haifeshi a nigeria ne yasa tarashi, tundaga lokacin taci alwashin ita da kasar har abada haka ma duk abinda zata haifa masa bazasu taka kasar ba hatta shi kansa mahaifinmu bazata sake kuskuren barinsa zuwa kasar Nigeria ba ,suka cigaba rayuwarsu cikin so da kauna da kulawa.

bayan haihuwar Salis iyayenmu sun dade basu samu haihuwa ba kafin daga baya suka samu haihuwar yayana Habib alokacin mahaifinmu yasamu cigaba sosai akowani bangare na rayuwarsa dan bai tsaya iya aikinsa kadai ba har da harkokin kasuwanci zuwa kasashen duniya yana yi, shekarunsu biyar dasamun haihuwar habib suka sake samu haihuwata kuma har lokacin maihaifiyarmu bata tunanin sake zuwa kasar mahaifinmu sakamakon wannan tsoron d'an kar arabata damu .

shi kansa mahaifinmu da taimakon kasuwancisa yake samun damar zuwa kasar haihuwarsa yaga iyayensa batare da saninta ba ,mun taso cikin gata da kulawa iyaye sosai takowane bangare iyayenmu naji damu duk abinda muke so shi mukeyi mahaifinmu ya shahara sosai a kashen duniya dan bayan gwagwarmayar rayuwa data aikin gwanati har ma da rike mukamai nasiyarsa kasar yayi da taimakon mahaifiyarmu.


" ina matakin jamia Allah yayiwa iyayenmu rasuwa sakamakon hatsarin mota da sukayi ta hanyar dawowarsu daga office din jakadanci "acewar mutane an kwance musu birkin mota ne .

mutuwan ta gigitamu kwarai da gaske muyi kuka kamar me daga karshe muka fawwalawa Allah komai mukacigaba da rayuwarmu.

yayana habib yacigaba da bani kulawa da kuma abinda yashafi fannin kasuwamcin mahaifinmu domin a yanzu shine kan gaba a komai wanda zuwa wannan lokacin arzikin mahaifinmu ya zarta yadda ka tsinci naka arzikin lokacin da kayi lossing momery dinka.

a lokacin Allah Allah na dinga yi na kammala karatuna domin na samun damar taimakawa d'anuwa na wanda kullun yake nuna min bazan iya komai acikin lamarin , ni kuma sai na dinga nuna masa zan iya ai duk abinda namiji yayi mace zata iya yin feyye da haka duk lokacin dana fadi haka sai dai yayi murmushi kawai yace "sai dai nayi aure mu taru dani dashi da mijina mu tallafawa dukiyarmu.. nima nace yayi aure domin yafini bukatar haka yaya Habib kyakkyawa ne ajin farko dan har ya zartani a komai hakan yasa yan'mata ke yawon kawo masa farmaki amman sai yaki ..

haka na dinga yiwa Habib nacin aure shima yana min naci nayi aure mijina ya tallafawa dukiyata sai dai nayi murmushin nace nafi son shi ya fara a haka har Allah yasa nagama karatuna nasoma taimaka masa .

a shekaru uku darasa iyayenmu da mukayi abubuwa dayawa sun faru ciki har da soyayyyar da mukeyi da wani daga cikin ma'aikacin company dinmu wanda hakan yasa muka dan samu matsala da Habib saboda rashin amincewarsa a cewarsa basona yake tsakanin da Allah ba na canza wani nace masa kawai naji .

cikin haka na fuskanci habib na tare da matsala saboda alokacin ya rame tsotsai ga yawon tunani da yawon ciwo wanda wani lokacin idan yana tari har aman jini yake nan fa hankalina yatashi mukaje yaga likintasa doctor bai yi min bayanin komai ba yayi adminting dinsa akacigaba da bashi kulawa da daurashi akan magani wanda duk daren duniya nice ke bashi magani kafin na kwanta gaba d'aya na tattara dukkanin hankalina garesa domin bana son narasa shi.


"lokaci zuwa lokaci ciwon natashi kuma duk lokacin daya tashi ya dinga tari kenan da aman jini, a wata safiya ne Habib ya tashi da rashin lafiya me karfi wanda yafi duk sauran rashin lafiyar dayake dan wannan karon har da gudaji gudajin aman jini yake.

muka isa ga likita dake dubashi akasoma bashi taimako gaugauwa ranar dai na tsare likinta kan lallai sai yayi min bayanin cutar dake damun dan'uwana dayake aman jini cikin bayanan likita dayake min ne naji wai d'an'uwana na dauke da cutar blood cance wanda yanzu cutar takai matakin da sai an zuke jinin jikinsa an sa masa wani sannan zai samu lafiya yacigaba da lallabata rayuwarsa datayi saura dan a halin yanzu bazai wuce shekara daya araye ba zai mutu ....


hankalina yayi mugu mugun tashi nayi kuka awa raina zai fita dan lokacin gani nake shikenan ma na rasa d'an'uwa na dinga zagin likinta ina cewa shine zai mutu kafin shekara daya, haka na dawo masa tamakar mahaukaciya sabuwar kamu da kyar aka samu aka shawo kaina da taimakon likitoci komai ya daidaita aka d'aura shi akan sabon magani da zai dinga rage tasirin ciwon ajikinsa "lokacin na nemi likintan dake kula da lafiyarsa akan kar yasanar masa da yana d'auke da ciwon.
inda likitan ya tabbatar min da ai ya dade da sani yana d'auke da ciwon dan yana taimakawa kansa sosai gurin zuwa duba lafiyarsa yanzu abinda yasa kikasani dan ciwon ya girmama ajikinsa ne dabazaki sani ba... lokacin da doctor ke mini bayanin yadda rayuwarsa zatakasance ni nake kuka amman shi ko dingon hawaye bai zubar ba "Allah ya sanya masa dauriya d'aukar kaddarar datasameshi acikin ganiyar kuruciyarsa. gashi babu uwa babu uba babu dangin mahaifi sai na uwa suma ba wasu masu yawa ba.....
a kullun tsakanina da Habib kar na aure husein nasamu wani ko bayan ransa na aura haka ina jin son husein araina na daina sauraronsa nafi maida hankalina gurin kula da lfyrsa.

tashin farkon abinda yazowa zuciyar Habib bai wuce yadda zamuyi da tarin dukiyar da muke da ba, saboda shi oready yasanyawa rayuwarsa yana daf da kabari , abu na farko da muka soma dashi muraba dukiyar mu gida uku kashi daya muyi taimako dashi zuwa kasashen duniya amman mu fara da kasar haihuwar mahaifinmu duk da bamusan asalin daga wani jahar ya fito ba amman muka zabi somawa da kasar kano.....


alokacin idan ba ance maka Habib na dauke da cutar cance ba bazaka taba yarda ba, dan irin kulawar danake bashi da taimakon likita yasa cutar kin nunawa a jikinsa kamar farkon kamuwa da ciwon sai dai idan ciwon ya tashi ne zaka tausaya masa sammakon fita haiyacinsa dayake zai ta aman jini gudaji gudaji ni kuma haka zan shiga tashin hankali nayi ta kuka ina masa karatun alqurni me girma har zuwa sanda zai samu lafiya..

yaje kasashen duniya da dama da lalurar ciwon jikinsa sannan
ya shirya tafiya Nigeria inda kwarai naso binsa kasar haihuwar mahaifinmu amman ya hanani dole tasa na hakura domin alokacin bana kuskuren sa'bawa umarninsa duk abinda yace haka za'a yi tashin farko daya isa Nigeria a jahar kano jirginsa ya sauka dan haka yasoma abinda ya kaishi ta fanni taimakawa marasa lafiya da marasa galihu da marayu.

yaje state ya kai ashirin a yadda yasanar min daga karshe ya zo jahar lagos inda nan ya iskeka rai hannun Allah bakasan inda kanka yake ba ganin farko da Habib yayi maka yaji kashiga ransa ya dade sosai akanka yana kare maka kallo cike da tausayawa alokacin yace bai san sanda ya dinga zubar maka da hawaye ba gashi daganinka an ga mutun me kima da dattako sannan siffarka batayi kama da mutumin daya fito daga gidan banza ba, yasamu likinta kwakwalwar dake kula da kai domin son jin dalilin shigarka wannan halin anan likitan yake gaya masa "kasamu matsalar kwakwalwa momery dinka ce ta ta'bu wanda dole sai an fitar da kai kasar waje sannan zaka iya dawowa daidai idan anyi dace.
gashi basu san kowa naka ba tunda aka kawoka babu wani wanda yazo naka take Habib yaji zai d'auki nauyinka amman yasa a sanar a kafafan yad'a labarai domin son binciko danginka.

kusan kwanaki goma ana yad'a labarai da hotonka a halin dakake ciki amman ba asamu wanda yasan wani naka ba.

"dan haka habib yasanya hannu da taimakon likita ya taho koria da kai inda kai tsaye hospital aka nufa da kai akashiga baka taimakon gaugauwa anan likitoci suka tabbatar mana da kayi lossing memory dinka wanda har ya wuce fahimtarsu amman may be idan ka hadu da abinda zuciyarka tafi bukatar arayuwa ko fuskar wanda zuciyarka take matsananci so zaka iya dawowa tunaninka..



mmn sudais ce

💗💗💗💗💗💗
SAI KA AURENI DOLE
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗



~NA~



*AYSHA A BAGUDO*



Dedicated To
Hauwa A Usman
Jiddar

YA MUDHILL

THE GIVER OF DISGRACE

page 83

.........."duk da likitoci na iyakar kokarinsu akanka amman Habib yagaza hak'uri, gani yake kamar basu baka kulawa data dace , sati biyu tsakani ya shirya mana tafiya da kai zuwa wani hospital 'kwa'kwalwa dake k'asar india .

ranar monday mukabar koria zuwa india inda kasoma karbar treatment daga k'wararrun likitici 'kwakwalwa,
cikin wata uku ka warke garas.

"Sai dai lokacin da kasamu lafiya sai ka dawo tamkar me 'kwakwalwa yara komai sai anyi maka gaba d'aya kulawarka ta dawo hannuna alokacin, haka Habib zai tasaka gaba yayita kuka ya dinga furta kalmar Alhamdullahi wato kowani bawa danasa kaddarar, gashi shi d'auke da cutar dake daf da kai shi kabari, kai kuma ga taka kaddarar ta juwewar 'kwakwalwa,ina son na dinga kiran ka da suna amman narasa da wani suna zan kiraka.
dan haka na" cewa Habib mu samu sunan dazamu dinga kiranka dashi, dan shine farkon abinda zai saka ka dawowa aikata halayyan irinta cikakkun mutane.

da fari Habib yaso mu dinga kiranka da sunansa acewarsa shi ba mazauni duniya bane,
"watan wata rana zai tafi ya barni da kai, sunansa zai dinga d'ibe min kewarsa, nan take na tubure na nuna masa sam ban yarda ba wannan tsari ba ,ya canza maka wani suna babu abinda zai rabamu ciwo ai ba mutuwa bane sai ni nazo na mutu nabarshi a duniya ,shine da kansa ya zaba maka sunan Mahbub, a wani daren jumma'a muna zaune da habib byn na bashi ganinsa ya ya kira sunana" Shemah ...na d'ago ina dubansa alokacin kai idanunka na kanmu "ki rike Mahbub amana da gaskiya ina jinsa ajikina sosai ina jinsa tamkar wani jigo ne gareki ko ina raye da bayan raina ,idan mutun yayi wani alkhairi kansa yayiwa hakazalika akasin hk, sai kayi alkhairi ka manta agaba ka tsinci ribarsa, "ki dinga kallonsa amatsayin mutun me mahimmanci ga rayuwarki, irin irin zantuttuka Habib kenan gareni wad'an da suke maseefar kashe min jiki da narka min da zuciya har yasani zubda hawaye tausayinmu .

"Aka sallamomu daga hospital muka dawo koria cike da tsantsar murna kasancewar kashiga ranmu sosai bayan kyakkyawar surar da Allah ya halicceka dashi, kai din wani hazikin mutun ne me kwarjini da kuzari hade da nutsuwar zuciya, alokacin na d'auki soyayyar duniya na d'aura maka tare da rike amanar da yayana yabani na kulawa da kai gaba d'aya na nemi son da na kewa Husein na rasa adalilin kasancewata tare da kai.

"Anan koria ma lokaci zuwa lokaci kana zuwa ganin likita dan lokacin bama bacci sai kayita juye juye kana rike kanka kana ihu ,sannu ahankali ka dawo normal tamkar baka ta'ba samun matsala a kwakwalwar ka ba,
in da muka cigaba da rayuwarmu har kasoma bin Habib office daga k'arshe ya d'auraka akan matsayinsa alokacin komai tare mukeyi duk inda kake muna tare wata irin shakuwa ce me k'arfi tashiga tsakaninmu wanda hakan yayi wa Habib mugun dadi dan jinka yake tamkar d'an'uwansa na jini karamcika da fara'arka da rik'on amanarka yasa Habib yi min sha'awar aurenka lokacin daya zo min da zance naso k'in amincewa lamarin, amman soyayyar danake maka taki barina kin amincewa .

lokacin da mukayi aure Habib ya tattara duk wata kadarata ya damka maka ,har ma da wasu kadarori daga cikin nasa, ya d'aukaka acikin kasashen duniya duk wani abu da za'a yi da matsayinsa kai ke gudanar dashi duk wasu takardunsa dana wa ya canza suna zuwa sunanka.


" alokacin da mukayi shekara d'aya da aure likita ya sake tabbatar mana Habib bazai wuce shekaru d'aya a duniya ba zai mutu hakan ya sake d'aga min hankali"nace idan rayuwarsa a hannunsa yake sai ya kasheshi " haka kace shekara daya data wuce bazai wuce shekara daya ba, yazo har ya dara hkn yanzu ma kazo da magana mutuwa duk maganarka bata wuce zance mutuwa, "kasani ma ko zaka rigashi mutuwa na dinga zakin doctor duk da lokacin gbdy a firgice nake daganin yanayinsa gaba d'aya komai masa ya sauya hatta tufafin sawarsa sun dawo farare bashi da abin yi sai neman istigifari da salatin annabi .
"a lokacin da kai mukeyin komai gurin tattalin lafiyarsa koma nace kazama jigon komai domin duk abinda yaka mata nayi mishi ka maye gurbina,
"gaba d'aya muka tattara al'amarinmu zuwa ga ubangaji wanda ba'a hanashi shine mai bayar da lafiya ga wanda yaso.


"Allah bai rabani da d'an'wana ba har sai da muka rayu dashi na tsawon shekaru biyar sab'anin yadda likitoci suka sha gaya min.


"mutuwar Habib ta girgiza zukatan mu ni da kai da sauran masoyanmu wanda gaba d'aya kusan rasa gane kaina kayi domin nima a sanadiyar haka na kamu da ciwon zuciya.

"da taimakon Allah da taimakon ka naci gaba da rayuwa a duniya abu d'aya ke kwantar min da hankali a duk sanda na tuna Habib ya koma ga Allah yana me karatun alqurni me girma ana zarar ranshi amman sunan Allah yake ambato wannan abu shiyafi komai yi min dad'i arayuwata,
har nasawa zuciyata danganar rashinsa atare dani.

jinka tare dani ke d'ibe min kewar d'an'uwana danarasa sakamakon kulawar dakake bani, mutuwar Habib ta sake saka shakuwa mai k'arfi a tsakaninmu muka sake yarda da junanmu da zuciyoyimu cewar muna son juna da amana kuma zamu rayu k'ark'ashin inuwa d'aya muddin rai.

" bayan wani lokaci kaima kayi suna ta kowani b'angare cikin k'asashen duniya ka gahurta har ma kaso kafin lokacin da Habib ke raye,
"muyi zama na amana da soyayya a tsakanin mu wanda idan akace min wata rana zamu rabu zan k'aryata hakan sai dai duk wannan tsawon shekarun muna tare batare da wata matsala ba in ma har muna da matsalar arayuwar mu alokacin to bata wuce matsalar rashin haihuwa ba ......

"munyi zariyar asibiti munyi na gargajiya shiru dan haka muka sake rungumar junamu muka d'auki komai muka mikawa Allah. wanda ba'a sa shi kuma ba'a hanashi shine me bayarwa da hanawa ga wanda yaso
d'an likitoci sun tabbatar muna da kowannen mu lafiyarsa lau, lokaci ne Allah bai kawo ba,
shemah ta sauke naunauyen ajiyar zuciya lokacin datazo k'arshen labarin tare da tsura masa ido tana kuka me ta'ba zuciyan me sauraro,sannan tace "wannan shine tarihin rayuwata da kuma silar haduwarmu da kai.

"kayi hak'uri koda baka sona kacigaba da rayuwa dani takarasa maganar tana me had'e hannunwan ta duka ..

Ammi ta rungumeta ajikinta tana rarrashinta "kukan ya isa haka Shemah In sha Allahu ina me tabbatar miki zaki tabbata mallakinsa cikin inuwarsa har yanzu mijinki ne Taufeek da igiyar aurensa akanki.

" Nasani Aunty ina jin tsoron karya ce bazai cigaba da zama dani ba "sannan meye matsayin wannan matar dayake ikirarin zai sake zuwa gurin mahaifinta akaro na biyu neman aurenta..... ?

" ya tab'a aurenta ne
suka rabu har yake tambayar ta cikin daya barta dashi..?

"ni dai koma menene tsakaninsu Aunty ki taimaka yacigaba da rayuwa dani,
Ammi tace "karkiji komai zai rayu tare daku "ita wannan da kika gani tsaye sunanta Salima itace asalin muradin ransa ,a duniya idan akwai abinda Taufeek yafi kauna da so bai wuce wannan bawar Allah dake tsaye a gabanki ba.
soyayyarsu ta wuce na tsaya misalta miki, nan Ammi tashiga bawa shemah labarin Salema tundaga farko haduwarsu da Taufeeq har karshe da haihuwar d'iya macen datayi masa da yadda d'an cikinta ya aureta abu d'aya ne bata sanar mata ba shine batan su'ad shima dan kar kara masa dumuwa ne.

wani irin kuka Shemah ta fashe dashi me tsuma zuciya "lallai ta cancanta yasota fiyye da komai a arayuwarsa "amman dan Allah ni dai sumin alfarmar cigaba da rayuwa dasu, na kasance a cikin inuwarsu, bazan shiga rayuwarsu ba burina nakasance tare da Taufeek araye, saboda bani da kowa a yanzu daya ragemin sai shi....... kuka take sosai har tabawa Salema tausayi ta isa gareta ta rungumeta suka rungume juna suna kuka.

"ki bar kuka shemah zaki rayu da Taufeeq oredy ma taufeek naki ne" daman ni tuni na cire rai da rayuwa dashi ,zuciyata ta dade

3 Comments On SAI KA AURENI DOLE
avatar
zainab-ishaq

1 year ago

Reply

Love it ????????

avatar
zainab-ishaq

1 year ago

Reply

Yes and I want to download it

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to zainab-ishaq

In order to download you have to subscribe for our package at https://tnovels.com.ng/subscribe

Please Login or Register in order to submit comment