Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kadai ke da idanuwa ganin hanya ba .
kana rike da hannuna sama da minti goma amman ka furta min kalmar iskanci byn kai ne shugaban tantiran yan iska duniya.
ahankali ya gyara tsayuwarsa tare da tsare dan karamin bakin rashin kunyarta datake motsawa ido yana kallonta ,karo na farko kenan da wata 'ya mace ta maida masa da martani magana.da zumar rashin kunya. yanzu shi zata kalla takira da dan iska.. dan iska fa yashiga maimaita kalar..
makil yataso kmr guguwa zai dauketa da mari ak yayi saurin rike masa hannu yana girgiza masa kai ,dan girma allah kar ka dakatar dani kabarni na casa shegiyar nan .na nuna mata akwai baban ninta a bangaren rashin kunya kai zata kalla ta gayawa hk sbd ita bariki ce.
aa kaje kawai abunka ni kadai Dina na isheta.
meyasa ka dakatar dashi ya tsinkayi sautin muryarta yadaki dodon kunenshi..
da kabarshi ya taba lafiyar jikina man ..
wlh daya gane ya tafka babban kuskuren arayuwarsa pulishi man me idanun akuya kawai ,duk datayi mugun sake bashi haushi da takaici Amman sai da mgnrta takarshe ta dan so bashi dry amman ya danne yaki yarda dryr ta fito .
sai su musty ne suka kwashe da dry suna tafa hannu da nuna malik .. daya zama tkmr wawa agurin .
zagaye ak tayi gaba abinta tabarsu nan. suna dryr malik me idanun akuya gsky yarinyar nan taci mutuncinka malik idanun akuya fa inji cewar musty.
,wani abu ne ya tsaya masa a rai,ranshi in yayi dubu ya baci matuka yau shi akewa rashin kunya har da zagi ?
,abinda yafi tsana kenan a rayuwarsa tun lokacin kuruciyarsa,lallai zaiyi maganinta,wacece ita da har take jin kanta daidai da shi ?
ita din wacce da har ta isa tayi masa hk?
me tataka datake ganin kanta ita wata abace babu shakka sai ya hukuntata bisa daidai da laifin data aikata masa .juyawa a zuciye ya bar gurin musty na kiransa ya dawo amman ko kulashi bai yi ba.


tunda dayaje gida yakasa zaune yakasa tsaye zariya kawai yake da tunanin yadda zaiyi da yarinyar da ko takamaiman sunanta baisani ba, numfashi kawai yake busarwa wani tunani yazo masa Wanda yasakashi yin murmushi sbd tasamo mafuta.


tafiya take ita kadai rataye da wata yar karamar jaka sanye cikin wando da riga .
wasu gayu ne su uku suka zo wucewa ta kusa daita. har sun gifta ta sai km suka dawo da baya ,daya daga cikinsu wani murdede ya janyo jakar dake make ajikinta, ji mana yammata.
su'ad tayi saurin fixge jakarta da karfin tsiya, yammata kaniyarku ..
suka kwashe da wata mahaukaciyar dariya me firgitarwa lallai ke cika ce kalata, kai tiger daukota ka kai min ita kangona yau daita zanyi abinci dare. wanda aka kira da tigar yasoma kokarin daukarta.
ai su'ad naganin hk ta kwasa aguje tayi kwanar dazata kaita gidansu ak daman gidansu zata, gudu take kmr zata tashi sama tana fidda numfashi suna biye daita har ogansu.
daidai ak ya fito daga gida shi da musty zai masa rakiya ,aguje takaraso gurinsa tana haki ta boye abayansa tare da lafewa abayansa tana sauke numfashin ka taimakeni dan Allah zasu cutar dani, a daidai wannan lokacin datake boye abayansa taji tmkr shi din runduna ne atare daita.
ahankali ak ya janyota daga bayansa yana kallonta sama da kasa da kallon yanayin shigarta ta kullun zuciyarsa na wani irin mahaukacin bugu yayinda tunin musty ya ja da baya kasancewarsa mugun matsoraci .
cike da hargagi wannan babban cikinsu ya kai hannusa zai janyota kabani kayan marmarina ita din tawa ce yayi mgn yana murmushi.
ak yayi saurin janyota zuwa garesa tmkr zai shigarta da cikin jikinsa yana sake kallonta.
gbdy ma ya manta a wani yanayi yake. kabamu ita tun bamu tarwatsa maka lisafi kwalkwaluwarka ba yanayin yadda yake kallon cikin kwayar idanunta yabata kwarin gwiwar motsa labbanta ina sonka... daidai lokacin da ogansu ya dauko wani itace ya makawa ak atsakiyar kanshi wanda hkn ya dawo dashi cikin hayacinsa .
ak ya firgita matuka da jin furucinta dataka mana kana ganin takware min. kikace me ina sonka bakinta na rawa ta sake maimaita fadar hk sake maimaitawa yayi mgnr idanunsa cikin nata har bai son daukesu. narigada na fada .
sake fada naji yayi mgnr cikin tsawa ina sonka babu yadda zanyi dole na furta maka ina sonka batare da na shiryawa hkn ba kmr ya to? kmr yadda kaji na fada duk macen datasamu saurayi irinka me bata kariya ai ita dacewa soyayya.
meye take mgn akai ne wayasan mata ita sani ita dashi inji cewar mutanen da suka biyota kunga kawai mu wuce. muryar ak a tunzure yace kenan da wayan nan mutane basu biyoki ba bazaki samun karfin halin da kuzarin furta min wannan banzar kalmar ba....?
ta lumshe fararen idanunta wannan ita ce damar dana samu shiyasa nace bari nagaya maka amman na jima da kwarewa cikin tafkin soyayyarka na boye wannan sirrin na sake boye wa.
na karanta litafin sirrinka na sake karantawa na maimaita har ban san adadi ba ma. tausayi ne yasaki sona ya matsota afusace meyye kika sani akaina dama har zakiji kina sona ..?
ilimin nazarin halayan dan adam.. ilimin nazarin halayar kaniyarki wannan mgnr tamu bata nan bace kazo muje kangona mayi mgn a can wani irin kallon tsana yayi mata up and down take km kwalkwaluwarsa ta tabbatar masa wannan shirinta sannan yace ina Allah ya tsareni da jerawa dake.
kasan ko waceceni nice shugaba ga wannan yakin da duk wasu tsageru da tantiran unguwa idan har baka yarda kabini munje kangona ba to kangon da kanshi zaizo har inda kake .
matsowa yayi sosai kusa daita tmkr zai shige cikin jikinta wanda har suna iya jiyo numfashin junansu da bugun zuciyoyinsu ahankali yasa hannuwansa ya kamo habarta bakinsa daidai nata.
idanunsu tsarkafe cikin juna hancinsu na gugan juna suna shakar numfashin junansu muryarsa a raunane yace ki kalli cikin idanuna.
ai hkn ma nakeyi ahalin yanzu ..
bana ra'ayinta ko muradin fadawa soyayya dake kingane ko. meyasa sai daka matso kusa dani hk sannan zaka gaya min abinda bashine acikin ranka ba.
karya ne kace baka da muradina arayuwarka muryarsa kasa kasa yace sbd tasirin hk ki bani latafin sirrina da alamun tausayina ya janyo kike nema jafa kanki kangin wahala dan bazaki taba samun soyayyata ba har abada bai km zama dole ki fuskanci hk ba.
nabani litafin sirrina. matsawar kana bukatar litafin sirrinka ka amincewa soyayyata.
Allah ya tsareni ......
yana karasa fadar ya saki fuskarta tare da juyawa zuwa inda musty ke tsaye yazama dan kallo.tmkr a fillm
da ihunta tace kai tsohon me cutar farfadiya yanzu soyayyar tawa zakawa hk.. cak ya ak ya tsaya ya kasa motsi balle ya cigaba da daga kafafunsa...

_ku dinga min hkr dan allah ba wulakanci bane abubuwan ne dayawa ku da samun post sai on Monday ko tuesTuesday_😏👏🏻👏🏻👏🏻

mmn sudais ce

💗💗💗💗💗💗
SAI KA AURENI DOLE
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗



~NA~



*AYSHA A BAGUDO*



~DEDICATED TO~
HAUWA A USMAN
JIDDARH


*qala rasulillahi sallallahu alaihi wa sallam :assaburu nisful iman*

*Allah's messenger (s a.w) said patience is haif the faith*


page 25

wani abu ne me kama da dalma yaji yana masa yawo a dukkanin ilahirin sansar jikinsa.
,tun daga tsintsiyar kafafunsa har zuwa tsakiyar kanshi yake jin wannan radadin .
"mgnrta ba iya sansar jikinsa kadai ta tsaya ba har cikin zuciyarsa yake jin dacin kalmar datayi amfani dashi.
babu wata mace datasamu wannan damar ta cin zarafinsa da tsohon ciwon jikinsa.
yau shine karo na farko da hkn ta faru dashi.
ko lokacin dayake cikin ganiyar ciwonsa bai samu wanda ya zageshi dashi ba sai yanzu daya tabbatarwa kansa babu sauran burbudin wannan ciwon ajikinsa .
hakika zai ganar daita kuskurenta na shigowa cikin rayuwarsa datayi.
ayau ne zai nuna mata shi din wanene da true colour dinsa .
zai wujijjiga rayuwarta tasan shi ba sa'an yinta bane ..
ya juyo a harzuke jikinsa na tsuma yasoma takowa ahankali zuwa inda take tsaye.
fararen idanunta masu kalar madara ta sanyasu akansa tana kallonsa. kirjinta ne yayi wani irin mahaukacin buguwa da karfi .
take km zuciyarta tashiga shawagi da girgiza tare da harbawa. lokacin daya fargaba tattare da matsanancin tsoronsa ya kaiwa zuciyarta bakunta.
daidai ya kusan karasowa gurinta tasoma ja da baya da baya sbd matsanancin firgita datayi da ganin yanayinsa.
wayyohhly Allah ta furta acikin zuciyarta ....
ya Allah ka taimakeni ka taimakeni kar yayi min komai...
matsota yacigaba da yi a matukar fusace tana ja da baya .
jitake tmkr kasa ta tsage tasamu gurin buya acikinta batare daya cimmata ba .
bata ankara ba kawai tajita ta zube jikin saman wata mota wanda kadan ya rage hannunsa bai kai jikinta ba tsabar tsuma da jikinsa ke yi .
tmkr wani mayunwacin zaki yakaraso gareta zuciyarsa na
wani irin mahaukacin bugu me tattare da muguwar tsanarta da takaicinta .
ya rankwafo samanta . kirjinsa na bugawa yana kallon yadda nata kirjin dake sama da kasa ala'mun atsorace take.
sannan km numfashinta nafita sama sama. ahankali numfashinsu yasoma gyaraya guri 1 zuwa wani shauki na daban.
" yayinda nata numshinta tare da kamshin turarenta dake kaiwa hancinsa farmaki suka shiga circulating cikin kwalkwaluwarsa . ganin abunda ke faruwa yasa musty kamewa guri daya yana kallon ikon Allah da abun mamaki tamkar wasu sumammun masoya wayanda suka shahara cikin duniyar shauki juna. mayatattun idanunsa ya tsura mata yana mata kallon da bai san lokacin dayakeyi aikata hkn ba, tayi saurin runtse fararen idanunta, Dan jin wani abu na tsarga mata har cikin kasanta da kirjinta . tsawon lokaci ya dauka yana kallon kyakkyawar fuskarta kafin daga bisani ya tuno abinda yakawoshi gareta .
wanda yake shirin aikata mata .
take ya dawo abdulkabir dinsa sak... tare da murtuke fuskar nan tasa tmkr kumurcin maciji.
hannusa dake rawa ya kai ya damki makoshin wuyanta muryarsa na rawa yace ni.. ni kike cewa tsohon me cutar farfadiya....?
take idanunta suka birkice suka soma raina fata sbd yadda ya shakar mata wuya.
tashiga girgiza masa kai .
musty dake tsaye tmkr picture yakaraso gurin da sauri.
ak kabar yarinyar mutane karka mata illa .......
wai meyasa kake daukar komai da zafi ?
wannan abun da zaka aikata kuskure ne .hannusa daya yasa ya hankade musty baya . batare da yace masa komai ba ..
yashiga zuba mata wasu gigitattun maruka masu fitar da mutun cikin haiyacinsa .
wanda yasa take jinta da ganinta yasoma daukewa .
ya mikar daita tsaye bisa kafafunta yasoma janta sai jikin wani bango gida yana kaiwa bai tsaya wata wata ba ya buga kanta da bango..
ta saki wata razananniyar kara tare da fashewa da marayar kuka.....
zaki sake furta min wannan bazanr kalmar taki mara ma'ana .?
tayi saurin giriza masa kai ala'mun aa .
cikin muryarta dake nuna sanyinta tace Dan girman Allah kayi hkr bazan sake ba amman ina son kasan wani abu raba zuciyarta da sonka bakaramin tashin hankali bane, na fada sonka batare da nasan sanda hkn takasance dani ba.
wasu maruka ya sake zuba mata take bakinta ya balle da jini..... matsawar bazaki daina furta wannan banzar kalmar gareni ba .
zan rabaki da numfashinki ...zaki bar duniya batare kinyi nasarar cikar burinki ba. zan la'antaki na la'anta rayuwarki ...yana karasa fadar hk ya sake buga kanta da bago ginin...ta km sakin kara tana furta kalmar pls..
da kyar musty dake washe gefe guda yasamu ya mike tsaye ya tattaro dukkan wani karfi yasanyawa gangar jikinsa tare da shiga tsakaninsu yana kokarin kwatarta .
,da kyar musty yasamu ya kwace su'ad a hannunsa wace ta zube kasa tmkr wata sumammiya kafin daga baya tasoma fidda numfashi sama sama tana kallon cikin idanun ak hawayen tausayin kanta dana tsagwaron kaunar datake masa yashiga ganganrowa daga cikin kwarnin fareren idanunta.
ak yashiga nunata da dan yatsan hannushi wallahi matsawar baki rabudani ba kadan kikaga zan shayar dake guba da zata la'antaki ... hannusa dake rawa ya miko mata bani littafin sirrina..... tashiga girgiza masa kai bazaki bani ba?
ya tmbyeta nan ma sake girgiza masa kai tayi tana kokarin boye jakar hannuta.
motsota yayi sosai tare da saka kafarsa dake saye da takarmi ya take hannunta 1 yana mutsutsukawa.......
ta saki wata azababben kara .
ya fixge jakar ya bude.
idanunsa ne suka sauka akan littafin sirrinsa wanda ya nema yarasa tsawon lokaci.
yaciro yana turawa cikin aljijun wandonsa sannan ya maka mata jakar a fuskarta.
a matukar fusace yashiga janta yana marin fuskarta har sai daya kaita tsakiyar unguwar sannan yayi filinging daita yana tsare zan baki shawarar ki tsaya iyakarki........ kana
ya juya fuuuuuu yasoma takawa cike da izza zuwa gidansu .
rakiyar da baiwa musty ba kenan.
da sauri musty yakaraso gurinta tunaninsa ko ta suma ne amman sai isketa tana fidda numfashi hawaye na ganganrowa daga cikin idanunta .
nan yayita bata hkr da bata baki akan ta hakura ta rabu dashi tunda yace bai sonta .
nasan halin abokina tunda abdulkabir ya furta bai sonki bafa zai taba kaunarki ba har abada ..


ta mike da kyar tana shafa wunyata datake jinsa kmr ya dan soma tasawa alamun kunbura. wani irin radadin azabar ciwon gurin take ji sannan tace wannan karon zai yi abinda bai tabayi ba a tsawon rayuwarsa ..
sbd zai soni koda kuwa shine abu na karshe da zai aikata ya bar duniya... amman matsawar ina numfashi sai na mallaki zuciyarsa da gangar jikinsa ........
kallon tababbiya mara hankali musty yake mata tare da jinjinawa karfin halinta.
yarinya bazaki taba gane waye abdulkabir ba sai yayi miki illar da bazaki taba mantawa dashi ba yayi mgnr cikin ranshi.

da hannu musty yayi mata nuni tashiga mota. muje na kaiki hospital a dubaki... bata tsaya yin musu dashi ba sbd ita kanta tasan jikinta na bukatar hk .
duba da yanayin yadda goshinta da bakinta ke fidda jin .
shiga gaban motar tayi suka nufi wani karamin hospital .
byn an yi mata treatiment din gurin ya dauki hanyar gidansu a motarsa da kwatance data masa. tafiyar da suka yita suna tautaunawa. musty na sake sanar daita akan tsautsauran ra'ayin ak da rayuwarsa.
byn ya sauketa yabata kudi masu yawa ta kula da kanta.
" amman furrrr taki amsa sai ma godiya kawai data
masa tare da shigewa cikin gidansu dafe da goshinta.

ak nashiga gida kai tsaye part dinsa ya nufa yasoma balballe boturan gaban rigarsa, gumi ne ke tsatsafo masa takoina a ilahirin jikinsa surutu kawai yake tare da ciro litafin sirrinsa yana dubawa tabbas litafinsa ne..
to a ina tasamesa...? yayiwa kansa tmbyr.
ranar hk ya wuni yana juyi da tunaninta da gaske sonshi take ko tausayin abinda takaranta acikin litafin sirrinsa take.
Amman zai so ya zauna tare da musty domin zantawa dashi akanta akaro na farko.
hakika yana son sani wani abu game daita kafin ya sake daura idanunsa akanta .

wayarsa dake gefensa ne ta dauki karar sauti alamun ana kiransa runtse mayatattun idanunsa yayi sannan ya bude idanunsa ahankali ya kai dubasa ga inda wayar take .
ganin wace ke kiran ne yasa shi sakin dan gajeren tsaki yana furzar da iska kafin ya dauka.. Hello yayi mgnr a kasalance tare da sake runtse mayatattun idanunsa .
abangaren zeey kuwa sanyin dadi ne yakamata daga ina da take zaune akan gado ,ko babu komai taji muryarsa mai sakata jin kasala da samun natsuwa cikin ranta.
tunowa datayi da abinda yasa ta kirasa, yasa tayi saurin janye murmushin dake saman fuskarta.
a sanyaye tace an wuni lfy my life ?

lfy yabata amsa ataikace yana cixan lip's dinsa na kasa kadan, shr tayi cikin rashin jin dadin yadda ya amsa mata.
kusan tunda ta baro kasar Nigeria lamuranta suka sauya suke neman tabarbarewa ta kasa gane kasan.
wanda tasan ba komai bane ya haifar da hk illa aikinta dayayi sanyi yake bukatar tishi ,duk da hkn bai sa tafasa mgnr datayi niyya ba, dan hk muryarta ahankali tace yaya abdulkabir ........daman najika shr baka nemi ne ba tunda muka baro nigeria ,gashi ina son. mgn me mahimanci dakai shiyasa nakiraka yanzu.
"dan dakatawa tayi taji me zaice .
shiru yayi batare da yace komai ba a tunanin zeey ko bayajinta ne ko km layin ne ya tsinke ..
dan hk tasoma fadin hello ..hello.. hello ..my life kanajina.
dan numfashi yaja ya sauke da kyar.... kinga zeey ina wani abu ne yanzu ba km nason takura ko damuwa we will talk later ok.. batare da yajira abinda zatace ba yakashe wayar .
shiru yayi yana sake jin kirjinsa na rawa da bugawa akan tunanin su'ad da tunanin irin dukan da yayi mata .
sosai tunaninta yashiga yamutsa kwalkwaluwarsa.
ya matsu su kasance tare da musty yaji ina ya kaita sanda ya dauketa ,dan yaga lokacin datashiga cikin motarsa. wayarsa da sake daukar sauti ne ya dawo dashi daga duniyar tunanin daya lula amman yaki dauka.. duk da yaga kiran dady ne.

tunda ya katse kiran take rike da wayar a hannuta cike da matsanancin damuwa ta rafka uban tagumi allah yasani tana matukar kaunar abdulkabir so wanda bazata iya misaltashi ba. tun kafin tasan kanta take faman wahala da dako kaunarsa.
" sai gashi a daidai lokacin datafara murnar ya fara sonta da nuna kulawarsa gareta abu na neman tabarbare mata yazama dole da zaran sun dawo Nigeria tasan abinyi .
tana cikin wannan tunanin ne ammi da iman suka shigo dakin da sallamarsu shr bata amsa ba kasancewar tayi nesa cikin tunanin yadda zata mallakeshi dukansa batare da yana canza mata kmr hawainiya ba.

diyata lfy kuwa naganki hk..?

firgigib zeey ta dawo cikin haiyacinta tare da yin murmushin yake .
lfy ammi har kun dawo? um um zainab karki min karya mana tunani fa muka taddake kinayi. iman takarasa shigowa cikin dakin sosai ta ajiye farar laidar siyayar hannuta.
itama ta zauna kusa da zeey tana murmushi .
aunty kigayawa ammi gsky, tunanin yaya kike kawai dan hankalinta ya kwanta...da wannan firgicin datashiga.
ungo nan ammi tayiwa iman dakuwa na tmbyeki aku kuturu me bakin mgn kibarta tayi mgn man ..
ammi takaraso ta janyo wata karamar kujera da gabadaya jikinta kunshin ce ta zauna kusa da zeey tana fuskantarta.
ki fadamin gsky diyata meke faruwa dake ko tunanin biki ne...? ajiyar zuciya ta sauke tana rayawa aranta ina ma tunanin biki ne ai da sauki akan asirin datayiwa abdulkabir yakarye tana wata uwa duniya.
km wlh ko rantsuwa tayi bazatayi kaffara ba, tasan duk ammi ce ke ruguza mata shirin komai akansa.
tunda suka sauka a sakar saudiya bata zauna ta huta ba .
kullun tana harami ....ta km san gabadaya addu'ointa akansa zasu kare .
gashi ita yanzu komai na neman kwabe mata.. iman ma masowa tayi sosai ta kamo hannuta aunty zeey tunanin yaya abdulkabir ne ko ..?kallonta zeey tayi .sannan
tayi shr taki cewa komai hkn datayi ya tabbatarwa ammin da shi din ne sanadin shigarta cikin damuwa, Allah yasa bawani abun yayi mata ba.
ammi ta numfasa tana kallonta kana tace karki damu diyata zan san abin yi akan lamarin zankirasa zuwa anjima na lura tunda muka zo bai wani tsananta nemanki ba .
da sauri zeey ta zare hannuta dake cikin na iman ta meida cikin na ammi ta rike gam tana girgiza mata kai.
um um ammi bashi bane asali ma babu abinda yayi min lfy muke dashi yanzu ma muka gama waya dashi .
ammi ta sake numfasawa tana cigaba da kallonta .
sosai take jinjinawa kaunarta gareshi har tausayi take bata wani lokacin idan taga yadda yake mata wasu abubuwan.
ta dan bata lokaci zaune kafin daga baya ta mike tsaye tashigewarta bayi .

kinga aunty zeey namiji yanzu ko fa aurensa kikayi sai kina hadawa da hakuri da addua balle irin su yaya da mata ke rububibi.
sannan km tun farko kece kika fara nuna kaunarki da zakewarki akansa dan hk dole ki koyi juriya akan komai daga garesa .
nayi miki wannan mgnr ne amatsayinki na yar'uwata km aunty nah sannan nasan hk kawai ba wani abu ne ya haduku dashi ba .bazaki kasance cikin wannan yanayin ba.
aunty zeey ki tuna inda kike kina kasar saudiya kasar me tsarki .
wace ta wadatu da tarin ni'ima da albarka cikinta ki yawaita kaiwa allah kukanki kafin mubar kasar nan .
kai kawai ta iya dagawa iman nagode sosai iman Inshaallahuu zanyi kokarin yin hk.... mikewa zeey tayi ta nufi dakin baccinsu ta barta zuciyarta cike da sarkakiyar jin tsoron rasa abdulkabir dinta...


bangaren su'ad kuwa tana isa cikin compond dinsa ta iske makwabtansu ,su 4 zaune suna tautaunawa akanta da zaginta wanda daman halinsu kenan sai dai idan basu zauna ba.
suna ganinta kowace daga cikinsu tayi shr ta sha jinin jikinta suka shiga kamekame neman abunyi.
tsaki tayi dan tasan halin nasu suke yi na munafurcin da suka saba.
yau kam bata da lokacin kowace daga cikinsu.
damuwarta kadai ta isheta.
kai tsaye part dinsu ta nufa tana shiga ta iske ummanta zaune a parlour tana bare egusi idanunta na kan tv tana kallon tashar galaxy ko kallon inda uwar take zaune su'ad batayi ba.
balle wani abu shi sannu da gida.
tayi shigewarta uwar daka abinta.
uwar tabi bynta da kallo tana girgiza kai kawai dan taga raunin goshinta dana kafafunta.
amman yanzu ne ,tana mgn zata haiyayyako mata da fada.
ahankali ta maida dubanta ga kallon tv sannan tacigaba da abinda take..

tana shiga dakin kwalkwaluwarta tashiga caji domin nemawa kanta mafuta dan dole tasan abunyi kafin wata tazo tayi mata haye da shishigi cikin lamarinta da abdulkabir dinta. zagaye dakin tafara kafin tasoma zance zuci ita kadai .
su'ad dan dole ki tashi ki nemawa kanki mafuta tun lokaci bai kure miki ba .
akalla yanzu sauran watani biyu masu zuwa yarage wata ta mallekeshi bake ba.
me zanyi.... ..?
meye mafuta ni su'ad..tayiwa kanta tmbyr. ?
rashin samun mafuta yasa tayi shr tare da hawa kan dan karamin gadon ummanta ta kwanta lamo akan katifa. numfashi take saukewa ahankali tmkr wace tayi gudun famfalaki kanta dake daure da bandage tashiga jujjuyawa kafin tasoma sakin murmushin mugunta .
alokaci daya km ta sauke naunauyen ajiyar zuciya.
ta mike zumbur ta isa inda take ajiye kayan cajinta.
ta dauko kwalbar giya daga mabuyarta ta balle tare da tsiyayawa cikin glass cup tashiga kwankwadawa cikinta kafin kace me tunin har tasoma fita haiyacinta tana zuba surutai da sambatu iri iri akan soyayyar datakewa ak cike muryar maye i.....i..na sonka ba..ba.zan barwa kowa kai ba duk runtse .
duk wace tace zatashiga tsakaninmu sai na daddatsa shegiya da ada.. (masha o're enitowu meji.... )a hk umanta tashigo dakin ta isketa cikin mayen giya hannuta rike da tabawar wiwi tana zuka.
gbdy dakin ya turnuke da hayakin wiwi da warinta a zabure umman su'ad tayi kanta tare da rufeta da duka me zangani iskancin naki ya wuce kiyi shi waje.
yanzu tsinaniyar yarinyar adaki zaki zauna kina sha min giya da tabar wiwi...sbd lalacewa tasameki allah ya wadaran naka ya lalace allah wadaran wannan tsinan halin naki.
su'ad ta bude fararen idanunta wayanda suka gama canza kala zuwa jajja .
tasa hannuta ta tunkude ummanta gefe daya tare da mikewa tsaye tana tan gadi da nunata da yatsan hannuta ya ..ya isheki umman su'ad.

meye matsalarki da rayuwata ne. ..?


me kika tsamaci gani daga ya'ya iirinmu marasa gata da galihu ....?


na rokeki ki fita cikin rayuwata tun ban hadaki da hukuma ba ko na sassaraki da ada na raba kanki gida 4.....
ni zaki hada da hukuma su'ad ? sbd ke shegiyar yarinya ce ...umma tayi mgnr tana zubewa kasa kan gwiwowinta tana kuka me cin rai .
ni mahaifiyarki zaki hada da hukuma tare sara ? mahaifiyar banza ..... mahaifiyar wofi da iska gbdy tayi mgnr tana zubewa kan katifa

3 Comments On SAI KA AURENI DOLE
avatar
zainab-ishaq

1 year ago

Reply

Love it ????????

avatar
zainab-ishaq

1 year ago

Reply

Yes and I want to download it

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to zainab-ishaq

In order to download you have to subscribe for our package at https://tnovels.com.ng/subscribe

Please Login or Register in order to submit comment