Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yafaru da ita bayan barinta gida har zuwa auren d'an yayar mahaifinta datayi da mutuwar aurenta.... mamma takarasa maganr tare da yin shiru tana kallonsu daya bayan daya Ammi ta kasa boye farin cikinta ta matso su'ad sosai ta rungumeta tsam ajikinta tana godiya ga Allah gabadaya takasa boye tsantsar farin cikinta "mun yi kewarki mamana mun shiga tashin hankali rashinki ashe kina nan tare da kakarki kin manta damu ko kina nan kina jin dadinkiko ?

"Allah sarki shiyasa Ummanki tace in kwantar da hankalina jikinta nabata kina hannun na gari "ashe gsky ta fad'a Allah mun gode maka daka kawo mana k'arshen wahalarmu ,kalli nan ta nuna mata inda prof Taufeeq ke zaune wannan shine mahaifinki wanda yayi silar zuwanki duniya "Taufeeq ga d'iyar cikinka.

idanunta ta meida kansa tana kare masa kallo Sir mahbub " kenan hasashenta zai zama gskiya?

"Sir mahbub shine mahaifinta , tasha kawar da zuciyar datake karyata hakan gareta ta yaya hkn zata kasance ?
a she kasan cewarsa na nan zuwa ,wani irin kukan farinciki ne ya kufce mata wanda bata san sanda ta mike tsaye da kyar hade da dafe kasan mararta ta isa gabansa ta durkushe har kasa bisa gwiwowinta tana kuka ahankali ya d'aura hannunsa bisa kanta yana jin wani irin sanyi da farin cikin mara misaltuwa na kai kawo a gbdy ilahiri gangar jikinsa.

"yau ga diyar da salimarsa ta haifa masa, diyar daya bari aciki ya tafi kasar spain, itace ta girma haka har tayi aure ..

cikin muryar kuka su'ad tace" zan kiraka da baba ka amsa min ya mahaifina" tsawon rayuwata nayi kwad'ayin wada zan kira da haka narasa sai yau "babana ina sonka bazan ta'ba kinka ba duk da kayi sanadin zuwana duniya bata hanyar dabata dace ba .......

" nima ina tsananin sonki diyata tun kina ciki nake mutuwar sonki da kwad'ayin ganin zuwanki duniya, Allah be kaddaro faruwan hkn ba har sai munyi wasu shekaru kafin muga juna, ta riko hannwansa duka cikin nata tana kallon fuskarsa tabbas shine dai mahaifinta da mahaifiyarta ta nuna mata hotonsa kuma shine dai me gidan Abdulkabir, furta sunan ak da zuciyarta tayi yasa ta runtsa idanunta dan bata son kawowa zuciyarta shi .
mutumin data so kamar rai da ajali amman ya barta akan macen daya ya sha gaya mata baya sonta a can baya..

tacigaba da kallon mahaifinta tana jin tsantsar soyayyarsa na ratsata tana son ubanta bata da kamarsa ,duk da kasancewarta yar gaba da fatiha amman dole za'a kirasa da sunan mahaifinta, wannan farincikin kad'ai ya isa takarasa rayuwar datayi saura cikin jin dade.


" sun dade tana kuka shima prof kukan yake har salima "to yane zasuyi da kaddarar da gifta musu kowani bawa da silar zuwansa duniya sannan babu wanda ya isa ya gujewa kaddararsa.

a tsanake ta mike ta karasa ga kakanta wanda yayi shiru yana kallonsu cike da matsanancin tausayawa "kayi hakuri ka yafewa iyayena abinda suka aikata maka arayuwarsu ,samuwata a duniya ,kadarrasu ce babu tsimi babu dabara dole sai hkn ta faru "amman dan Allah kayi hakuri kabarsu su auri junansu a karo na biyu ina bukatar sucigaba da rayuwa a inuwa d'aya koda ban kasance cikakkiyar d'iya ba ina buk'atarsu atare ina son ganinsu cikin inuwa d'aya ka ..taimakeni dan Allah kabarsu su auri juna.... takarasa fad'ar hk tana me had'e hannunwanta duka tana rokonsa tana kuka ...

atsanake Alhaji mahmud ya kai hannunsa yakamota ta zauna gefensa yana murmushi irin nasu na manya cike da jin dadi kana yace "raguwar mata kawai dube yadda kike kuka dagani lusarin miji kike aure ,wannan kukan hk kamar zaki had'iyi zuciya cikin muryar kuka tace "please granpa ka ceci rayuwa iyayena suna bukatar junansu ...

murmushi yayi dan yaga ala'mun bata fahimci komai daya faru ba yasa yasoma magana cikin wasa da dry "ai tuni wannan maganar ta dad'e da wucewa acikin zuciyata" ni kaina cike da muradin sake d'aura idanuna akan iyayenki dake kanki nakeyi a kullun ," kaddara kuma mutun bai isa ya kankarewa kansa faruwata ba, zance auren iyayenki kuma tuni iyayenki sun mallaki junansu matsayin ma'aurata .

ta juyo da wani irin sauri zuciyarta na wani irin harbawa tana kallonsu atare suka gyad'a mata kai ala'mun hk ne "Alhamdullahi ta furta a k'asan ranta "Allah na gode maka daka nuna min wannan rana "a she wannan ranar zata zomin nan kusa ban sani ba ?

ta isa ta rugume iyayenta daya bayan daya tana murna Ammi tasa aka kira minsters da Dady dasuke parlour'n bak'i suzo suga ikon Allah, ai kuwa sun sha mamaki ganin su'ad nan dai akayi ta farinciki da murnar faruwar hk daga karshe ammi ta nasarwa su'ad Ak bai saketa ba da aurensa akanta jikinta na rawa tace "Ammi ya sakeni fa alokacin har tambayarsa Zeey tayi yace duka sakin yayi min idan ma duhun daya tsinci kansa ciki ne yasashi manta ai akwai shida tabbacin sakina dayayi barinaje na kawo miki ta mik'e cikin sauri ammi tabi bayanta da kallon cikin jikinta yafito sai dai bakowa zai tabbatar da cike gareta ba, kasamcewar cikin zumbulelen hijab take bata fi minti goma ba ta sake fitowa rike da farar takarda bata bude ba ta mik'awa Ammi.

Ammi ta numfasa kana tasoma bude farar takarda ta duba tana sakin murmushi tare da mikawa Dady shima dubawa yayi sannan ya mik'awa minster haka suka dinga pacing din takarda atsakaninsu har Prof Taufeek sai daya gani sannan Ammi ta janyo hannuta "zo ki zauna diyata da ala'mun tunda aka baki takadar fargaba bai barki kin budeta ba?

"amshi ki duba ki gani mijinki bai sake ki ba har yanzu igiyoyin aurensa na kanki jikinta na kirma ta amsa abinda tagani ya kusan zautar da tunaninta "to me hkn yake nufi Abdul bai saketa ba ....?

farinciki yakamata tayi ko akasin hk? tayiwa kanta tmbyr cike da matsanancin tsoro da tashin hankali wannan wace irin rana ce gareta me cike da tarin fariciki?

sosai ta tsurawa takadar idanu babu komai rubuce illa farar takarda empty , parlour'n ya d'auki shiru zuwa wani lokaci kafin daga baya Alhaji mahmud yayi musu nasiha me ratsa jiki daya danganci rayuwa aure sannan yasanyawa rayuwar auren salima albarka tare da fatan zaman lafiya me dourewa a tsakaninta da mijinta ..

bayan karramawa da mutunta ka da akayi musu ta fanin abinci na ban girma har da zaga dagin sukayi na
kusa ,sannan suka d'auki hanyar komawa gida cike da matsanancin farinciki da zumar wani sati Prof taufeek zai dawo ya d'auke salima tun cikin jirgi ambasodor yace "kar agayawa Ak abarshi tukun har zuwa wani lokaci ..

Daren ranar da Salima ta kwana gidan su sam ahalinta babu wanda ya runtsa yadda suka ga rana haka suka ga dare suna hiran yaushe gamo.


da suka isa gida ma Dady ya sake jawa Ammi kunne sosai akan karta kuskura ta sanarwa AK inda su'ad take har sai ya kara shiga hankalinsa .

******
ranar kusan kwanan farinciki Prof taufeek yayi duk kulawar da shema ke masa bai masa ba, hankalinsa gbdy na gurin sahebar ransa, gidansa dake banana estate ya yanke shawarar nan salema zata Zauna ita kuma shema zata cigaba a 1 thousand 4 ,cikin satin yayi duk abinda yakamata akan tarewar salima.

ranar lahadi yan'uwan salema suka dira agidan ammi ,an musu tarba ta musamman da mutunraka daga karshe sukaje sukaga inda salema zata zauna, iyayen salema sun nuna mata gata fiyye da tuninata ,duk da prof taufeek yace karsuyi wahalar kawo komai , amman sai da sukayi duk abinda sukasan anawa duk wata diya me kima da daraja agidan aurenta.


umman su'ad ta tare a hadadden gidanta wanda yasha kayan alatun more rayuwar duniya ,ahankali take bin d'akin da kallo tana mamakin irin duniyar prof ya kashe kamar wasu auren saurayi da budurwa ta dade zaune tare da rafka uban tagumi cikin zullumi da rashin sani madafa, yadda take hango rawar kansa akanta kad'ai yake d'aga mata hankali domin abubuwa yake kmr wani sabon matashin ango, abu me mahinmmaci datake hangowa atattare dashi bai wuce tsagwaron kauna dayake mata ba, musamman soyayyarta datake hangowa a yanzu acikin kwayar idanunsa.

yashigo d'akin bayan yayi wanka sanye cikin wata haddiyar jallabiya ruwan coffee colour yana baza kamshi me sanyi dadi ya jingina bynsa da jikin murfin k'ofar shigowa d'akin yana kallonta cikin hadadden shirinta dan sanye take cikin laulausar rigar bacci cike da matsanancin farinciki bakinsa ya kasa rufuwa yacigaba da kallonta "a yau bazei iya kwantata tarin murna da farinciki zuwan wannan ranar ba wannan lokacin, lokacine dayake cike da tsantsar nishadi da farinciki,tsawon lokaci yana tsaye agurin yana kallonta ,sihirtaccen kamshin turarenta na bugar masa da zuciya kafin ahankali yasoma takowa zuwa inda take itama ahankali ta taso suka rungume junansu suna murna kasancen ma'urata "cikin kunneta yayi mata rad'a "kina nan kamar yadda nasanki da wannan kamshi naki dake zautar dani," muje akwai tanadi me mahimmanci danayi mana daga yanzu mun shiga duniyar farinciki babu mu babu bak'inciki arayuwarmu .

yasoma tafiya daita har suka k'arasa atare suka zauna a bakin gado tare da riko tafin hannuta wani irin lumshe idanu yayi domin shi kad'ai yasan irin farincikin daya tsincin kansa saboda zamowarta mallakinsa, kallonsa tayi tare da sakin laulausan murmushi domin tasan tunanin dayake bai wuce kasan cewarsu tare cikin inuwa daya ba.



ta shafi gefen fuskarsa tare da bud'e bakinta tace "abban su'ad ..
ya bude kyakkyawa idanunsa ya zuba mata yana kallonta batare da yace komai ba "muje muyi alwala muyi sallah domin godiya ga mahalinmu daya nuna mana zuwan wannan rana..


yayi murmushi "ranar da muka so ganinta tun ganinyar kurciya ba Allah bai yin ba sai yanzu" tashi muje d'an ala hakikanin gaskiya jina nake tamkar sabon matashi "kai abban su'ad kafa tsufa..

"tsufa fa kikace ai namiji baya tsufa most especial agurin macen dayake tsantsar so," duk wani kulawa da gatan da kika rasa a shekarun baya zan tabbatar dana baki shi a yau..
"ni dai babu ruwana ni yanzu na girma nabarwa yara ,yayi laulausar murmushinsa bayi suka shiga sukayi alwala suka fito rike da hannun juna kamar zasu hadiye junansu yana gaya mata kalamai masu sanyi bayan sun idar da sallah ta kasa motsi tana zaune akan sallaya tana dubansa dan oredy shi ya rigada ya mik'e tsaye har ya isa kan gado maganganunsa kunya suke bata hannunsa ya yafitota ala'mun tazo sun dad'e suna bawa junansu kulawa daga k'arshe suka sake shiga bayi domin yin wanka tsarki ranar baccin barawo kasa dcaukarsu yayi da zarar sun runtsa idanunsu da zumar yin bacci sai subud'e domin ganinsu suke kamar zasu nemi juna su rasa acikin kwanaki wata irin kulawa Prof taufeek ke bawa Umman su'ad wadan hkn ke sake tabbatar mata da taufeek dinta daban yake acikin mazajen duniya, har take da yakinin bakowani nmj ne ke wulakanta mace ba byn ya amshi budurcinta a waje, su kaddara ce haka kmr yadda nata kaddarar yakasance tare dashi.

shema ta kawo mata ziyara inda ta bar gidan batare da tashiryawa hkn ba saboda ganin yadda taufeeq ke nuna kulawarsa akan umman su'ad.
bayan tafiyar shemah umman su'ad ta hararesa tare da cewa "kai ko ..

"menayi umman su'ad?

"dan Allah meyasa kakeyin hk ?

"Ko bakasan ka girma bane kai fa kaka ne yanzu?

ya janyo hannunta ta fada jikinsa "gsky ne amman yazanyi kurciyata nake son gyarawa a soyayya babu wani zance tsufa yakarasa mgnr yana lumshe mata idanu ta mike ta nufi kitchen "bazan iya da rashin kunyarka ba Allah.

"ya girgiza kai yacigaba da karanta jaridar daily trust yana murmushi wata irin soyayaya suka gudanar atsakaninsu, ji yake kmr yacinyeta duk inda tayi yana biye daita ko wajen aura tayya baya gajiya da ita kafin sati d'ayan da zai yi agurinta ya koma gurin shemah umman su'ad tagaji matuka, a cikon daren na bakwai suna lullube cikin bargo ya manneta ajikinsa gbdy ya hanata saka umman su'ad "tace kai wai menene haka...?

"yanzu fa ka girma amman sai naji kamar karfi kak'ara, "amu'amularmu a lokacin baya baka wuce kayi sau biyu amman yanzu daya kamata karage malam shine kuzarinka ke sake karuwa..?

murmushi yayi yana dubanta sannan yace "da menayi?

"ai yanzu ne nake jina a d'an shila na, gani ga sahibar rayuwata, jina nake kamar matashi d'an 30yrs tayi murmushi ba ita tasamu kanta ba sai daya koma gurin shema wanda komawarsa bai sa ya barta ta huta ba, dan kiran safe daban na rana daban na dare daban shemah duk abinda zaiyi da idanun take binsa, abun ma baya damunta dan bai rageta da komai ba daman kuma a soyayya dole tasirin wata zai fi nawata ita dai burinta su kasance tare muddin rai.

************
har lokacin Ak bai hakura da neman su'ad gbdy yagama haukacewa tuburan ne kawai baiyi ba kowa yagansa sai ya tausaya masa, sanin inda su'ad take ne yasa Ammi da Dady sake janyosa cikin lamarinsu, sukayita rarrashisa da bashi baki tare da bashi shawarar ya koma bakin aikinsa dan ma musty na tsaye akan komai da abubuwan sun sake tabarbarewa.


alokacin haushin kowa yake ji cikin zuciyarsa most especial iyayenta da sukayi buris da lamarinta suka sanyawa zuciyarsu salama babu abinda suke sai cin duniyarsu da tsinke.

hakika idan kaga Ak bazaka ce wannan matashin mutumin bane me ji da kansa da izza tare da nuna iko da isa. yayi wani irin baki ya rame ga kasunba ya tara, yaki yin aski da kyar Dady yasamu ya shawo kansa akan zai koma bakin aikinsa.

Ranar da zai koma Dady da kanshi ya tasa shi gaba zuwa gurin aski aka masa aski suka dawo gida amman duk da hk Bai jin zai cigaba da zuwa office alhalin bai san inda matarsa take ba.

umman su'ad tayiwa Ammi magana akan yaka mata Abdul yasan inda su'ad take tunda har yanzu matsayin matarsa take "eh nima nayi tunanin haka amman dady'nsa yace "kar a sanar masa yanzu sai zuwa wani lokaci, dan ta haka ne zai sake sani mahimmancita a duk sanda ta dawo hannunsa.
umman su'ad tayi murmushi "nidai dan Allah kuyi hkr kubashi matarsa ya daina jin haushinmu atare sukayi dry sannan umman su'ad ta katse kiran takira mahaifiyarta suka gaisa har su'ad din sun dade suna hira.

tsaye yake a cikin tafkeken office dinsa wanda rabonshi da shigowa cikinsa tunda abin ya faru bai sake waiwaiyar komai nashi ba, yanzu da taimakon Ammi da Dady ne yasamu yazo gashi zuwan nasa bashida wani amfani ,tunda gashi ya kasa aiwatar da komai sai zariya yake acikin office din goye da hannunsa yana tunaninta ahankali ya waiwaiyo ya kalli hotonta da shine ya dauketa a koria "yace kingani ko hrt beat komai na rayuwata ya canza tunda kika tafi kika barni bana son jin dadi komai banason ayi min abinda zaisani naji dadi har nayi dariya saboda banason nayi dariya matukar bakece kika bani shi ba.

" murmushinki fuskarki da komai naki kawai nake son gani duk inda zanje nemanki naje ki taimakawa rayuwar mijinki ki dawo gareshi .. "mijinki na cikin mawuyacin hali na rashinki .
ya zagayo ya zauna tare da tsurawa system dinsa idanun yana cigaba da kallonta wanda hakan ya ke sake hargitsa masa kwakwalwa yashiga nemo sauran hotunanta .
zuciyarsa na dokawa tashiga yi masa gezo tana masa murmushi yana nan zaune yana kallonta har sanda sectary dinsa yashigo ya ajiye masa coffee ya juya ya fita awuni uku suka shud'e yana zaune babu abinda yayi sai aikin tunaninta yaji motsin shigowa office din.

ahankali ya bude mayatattun idanunsa da suke a runtse ya d'aurasu akan fuskar Musty yasoma kokarin k'arasowa inda Ak yake, tashi yayi daga zaune dayake ya dayo yana layi tamkar wani mashayi ya zauna akan doguwar kujerar gefenshi Musty ya zauna tun awa daya data wuce Ak suna tare da Musty ,musty ya kalleshi yace " haba abokina dan girman Allah ka saki ranka kalli yadda ka dawo a dan kwanaki da basu wuce wata daya ba?

"Na san abu da ciwo amman daurewa zakayi wani irin kallo yayi masa me had'e da harara "ka saki jikinka dan Allah kayi lamurar gabanka akwai abubuwa dayawa agabanmu wanda dole sai da taimakonka komai zai tafi daidai dan girman Allah ka daina fito da damuwar ka a gane.

Ak ya kalleshi ya girgiza kai "fito da damuwa yazama dole yanzu zaka had'a damuwata data iyayenta ?

"Musty kalli yadda na damu akanta kalli yadda nabi na k'are akan su'ad banida lokacin kaina wallahi bana runtsawa yadda naga dare hk nake ganin rana.
Musty yayi murmushin takaici sannan yace " kaima kadamu daita ne saboda Allah Allah kakeyi kaga danka dake jikinta "kadamu da su'ad saboda cikin jikinta, zance iyayenta a kullun bazan daina fad'a maka bakafisu damuwa daita ba kai kanka yazakaji idan karasa cikin jikinta?

ya runtse mayatattun idanunsa yana jin zafin kalmar musty "wai meyasa musty bazai fahimce sa ba?

"meyasa bazai gane zahirin damuwarsa akan matarsa ba?

"shi yasan yana Allah Allah ya mallaki cikin jikinta amman wallahi yafi bukatarta akan duk abinda zata haifar masa, ita ya fara samu kafin yasamu cikin jikinta saboda idan tana kusa dashi shi kadai yasan irin farinciki dayake," yanzu bai san yadda zai misalta yadda yake ji ba sannan yace masa saboda cikin jikinta ya damu daita cikin da bai sani ba rayayye ne ko akasin hk?

ahankali ya furta "musty ansani nayi hasarar sosai ,ina matukar son matata aka gurbata min tunani akantan" ina son su'ad ina sonta sosai ina kaunarta har bansan yadda zan misalta maka ba ina jinta acikin nama jikina ban san haka so yake ba sai a yanzu dana rasa abinda nake so da muradi .
"kullun na tuna abubuwa da zeey tayi min alokacin baya sai naji wani iri daci ya tsaya min amakoshi ,tundaga lokacin dana waye gari banganta tare dani ba ban sake jin test din komai abakina ba why zaka dinga ganin ban damu daita "ka duba kaga yadda iyayenta ke rayuwarsu daya ne da yadda nike a rayuwata ayanzu?

" musty bazan ce kwata kwata basu damu daita ba, amman wallahi basu kaini damuwa daita ba babu abinda su'ad tasani wanda ya danganci rayuwar duniya batasan komai ba saini dana koyar daita bata da exprence din komai sai wanda na koyar daita ,kai kanka sheidani akan irin rayuwar damuka gudanar a koria daita ,komai a natse take yin sa ga hakuri dayanayina koda kuwa bata so ,ya runtse mayatattun idanunsa sosai hkn ne yasa musty jin kwalla ya kawo a idanunsa yayi saurin meidawa dan kar ak ya lura da hakan.

yayinda shi ak bai lura dashi ba yacigaba da magana " musty yaya zanyi da rayuwata?
" nasan damuwar rashinta shi zai yi sanadin mutu...

musty yayi saurin toshe masa baki "karkace haka dan Allah idan ka mutu ita kanta bazataji dadin rayuwar da babu kai acikinta, dan Allah kayi hakuri har na dawo daga tafiyar nan da zanyi kwana uku kacal zanyi na dawo duk yadda zaayi yi mu gano inda take zan bada gudumuwa ,"wannan tafiyar kai ya cancata kayita amman saboda yanayinka yasa na ajiye angoncina domin cigabanmu yakarasa mgnr cike da zolaya yana murmushi.

"kai kasani da wani banzar angonci ,duk abinda zakuyi , bazai taba kai wanda nayi da matata ba, zuwan musty ya dan kwantar masa da hankali har yasamu karfin gwiwa aiwatar da wasu ayyukan dake zube agabansa..



*********

bayan kwana biyu yana zaune a cikin office dinsa, aiki yake yi but lokaci zuwa lokacin zai waigo ya kalli hotonta sannan yacigaba da abinda yake ,bayasamu kuzarin yin komai sai wani abu daya danganceta na kusa dashi ,itace karfin ikonsa a wannan lokacin.
"a duk lokacin dazai d'aura kwayar idanunsa akan hotonta jinsayake tamkar rudanar taimako ce agaresa.
ya tsayar da aikin dayake tare da shagala gurin kallon hotonta wanda wani lokacin suke birkita masa tunani ya dawo tamkar mahaukaci ahankali yacigaba da kallon hotonta yana tunani baya ,tare da abubuwan da zuka faru kafin ya mallaketa matsayin mata sai dai kalma daya ce tafi kowace irin kalma mahimmanci da tsaya masa cikin kwalkwarsa har yayi mata babban ma'ajiyi a k'asan zuciyarsa.
bazai ta'ba manta wanda ba zai taba wannan kalmar ba "ina sonka abdulkabir .. ba yadda na iya dole na furta maka ina sonka batare da na shiryawa hkn ba, dan Allah kasoni ka aureni zan zamemaka tamkar baiwa agareka duk inda kaajiyeni zan zauna zan bi umarninka ,ka aureni kar narasa raina akanka ...
ya runtse mayatattun idanunsa "ashe sha'war dayake daita ma karfin ikontace ,damar samuwarta ta gahurta ajikinsa tunda ya rasa matarsa ya nemi duk wata sha'awarsa ya rasa amman tun asafiyar yau daya farka daga mafarkinta ya tsinci kanshi cikin wani irin yanayi jikinsa yake bashi komai ya kusan zuwa karshe garesa, domin kuwa yasawa ransa bazai iya aikata komai da wata mace ba byn ita hawaye suka gangaro masa "su'ad na hakura zancigaba da rayuwata haka babu komai....

wayarsa ce ta katseshi daga tunanin daya lula k'ara uku yana ji sai daga can ak yasa hannu ya lalubo wayar ya d'auka ya kara a kunnen daga dayan bangaren musty dake saukowa daga matattakalar jirgi yace "ak kana ina?

jin murya musty cikin yanayin farinciki shima ya tsinci kanshi ciki farinciki maramisaltuwa "ya'akayi ne musty ina office yanzu.

"gobe ne yakama dawowata amman murna ya hanani zama bazan iya jin wannan abun farincikin na kasa gaya makaba ..

"menene musty kasamo min inda su'ad take ne domin shi kadai abinda zanji yasanyani cikin farinciki?

"tabbass nasan wanda yasan inda take yanzu hk ina airport kazo kasameni yanzu "gaya min wace kasa taje ko garin dataje tabarni ina tangaliliyar rayuwa?

"kai dai kasameni yanxu a she an dade dasanin indatake akace aboye kar asanar ma ..ai baigama jin mezai fada ba ya mike a zabure yana kiran sunan musty, musty kuwa tuni ya katse kiran da gudun bala'i ak ya fito mataimakinsa ya biyosa abaya yana tambayarsa kafin kace me tuni escort dinsa da securities dinsa sun zagayeshi bai tsaya sauraronsu ba yashige mota yajata a guje suma suka biyo bayansa .

A airport din ma hk ya dinga gudu gudu sauri sauri zuwa lokacin har musty ya siya musu tiket din shiga conotoun yana tsaye yana jiran karasowarsa ak na arba da musty kuwa ya kankameshi ajikisa " aboki banida kamarka , ka nuna min kai masoyi ne na hakika tun da ake wannan tashin hankali sai yanzu ak yaji hawayen farincikin sun zubo masa .
musty rungumeshi a jikinsa saboda yana goge masa hawayen dayake dan baya son mutane su fuskancisu ..



mmn sudais ce

💗💗💗💗💗💗
SAI KA AURENI DOLE
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗



~NA~



*AYSHA A BAGUDO*



Dedicated To
Hauwa A Usman
Jiddar

YA HAKAM

THE MAKER OF IMMUTABLE
JUDGEMENTS

page 85

........Ahankali Musty ya zaresa ajikinsa yana dubansa, yayi matukar mamakin irin ramar dayaga Ak din ya sakeyi koma yace ya k'ara lalacewa kamar wanda yayi jinya a d'an kwanakin dayayi bai sanyashi acikin idanunsa ba.

" wani irin dad'in farin ciki ke d'awainiya da ruhinsa ya dinga jin kamar ya narke agurin saboda yadda yake ji ajikinsa,
wasu hawayen murna yacigaba da zubarwa "me zaicewa Musty arayuwa?

"Musty ya gama masa komai arayuwarsa tunda yasamo masa labarin inda bugun zuciyarsa take.

ya dinga kallon fuskar Musty yana tsantsar murna a hankali kuma ya dinga murmushi yana hawaye duk atare Musty ya kalleshi yana murmushi, shima

3 Comments On SAI KA AURENI DOLE
avatar
zainab-ishaq

1 year ago

Reply

Love it ????????

avatar
zainab-ishaq

1 year ago

Reply

Yes and I want to download it

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to zainab-ishaq

In order to download you have to subscribe for our package at https://tnovels.com.ng/subscribe

Please Login or Register in order to submit comment