Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

atsakaninsa daita agaban iyayensa gbdy tunaninsa ya tafi ne gurin son tuna baya ko ya taba wata mu'amula daita ko wani abu makamanci hk, amman har ya iso kofar tafkeken get din gidansu 'kwalkwaluwarsa bata hango masa komai daya taba shiga tsakaninsa daita ba.
hon yashiga dannawa da iyakacin karfinsa wanda ya firgita securities din bakin get yayinda take jikin baba me gadi yashiga rawa. cikin hanzari suka isa suka bude masa .
yasanya hancin motarsa xuwa cikin farfajiyar gidan yayi parking yasoma fitowa yana gyara zaman rigarsa ko rufe motar bai gamayi ba yace karamar tantiriya sai ki samu fitowa gamu agidanmu , kin fitowa tayi tacigaba da rera kukanta me taba zuciya, ganin zata bata masa lokaci yasa yazagaya ya fixgota daga cikin motar yashiga tafiya daita yana zaginta har zuwa parlour'n ammi inda ya tarar da iman da wasu daga cikin family's dinsu .

yana karasa shigowa parlour'n yayi wurgi daita wanda kadan ya rage kanta bai bugi glass din center table ba, ita km sai kuka take kmr ranta zai fita muryarsa a hargitse yace "sis ina ammi? yaya lfy dai ko? "ina ammi da dady yayi mgnr cikin karaji...? ta zubara ta mike tsaye cikin gigicewa ta nufi kitchen amadadin ta nufi bedroom din ammi. ya bude baki zai sake mgn kenan yaji sautin muryar
ammi.


abdul gani lafiya km na ganka hk duk a hargitse ?ammi ki zauna ina dady da kowa da kowa wannan karamar karuwar tantiryar shugaba yan iskan ce ke son gayamuku wasu banzanr magana wanda ni bansan dasu ba yakarasa mgnr yana nuna inda su'ad ke durkushe tana risgar kuka...fuskar nan nata yayi jawur.
zama ammi tayi a daddafe tana kallon inda su'ad ke durkushe gbdy takasa samun natsuwar zuciya hk kawai taji Gabanta na wani irin bugawa da sauri sauri tayi saurin runtse idanunta gam tana karanto addua acikin zuciyarta .

karasawa yayi har inda su'ad ke durkushe tana rusa kuka ya damki wuyanta ta baya wanda yabawa fuskarta daman bayyana sai daya gama kare mata kallon tsab sannan yashiga janta bisa gwiwowinta yana matso daita zuwa inda ammi ke zaune tana jin kmr ana fixgar rayuwarta .
sannan muryarsa a zafafe yace ammi ki bude idonki ki kalli idanun wannan tantiriyar mara kunyar da zantuttukanta ya kasa tsayawa akaina har sai ta dangana da iyayena.

ahankali ammi tasoma kokarin bude idanunta kirjinta na bugawa daf... daf ...tare da daurasu kan fuskar su'ad dake durkushe bisa gwiwowinta ai da wani irin sauri ammi ta dafe kirjinta sbd yadda taji gabanta yabada rassssssee .....tsoro da matsanancin firgici AK yaga ya bayyana a saman fuskar ammi dake zaune jikinta har rawa rawa yake yayinda shi km zuciyarsa tashiga bugawa da karfi.

ita km su'ad numfashinta ne ya soma barazanar daukewa sbd kukan datake cikin tashin hankali, da km yadda ya damki byn wuyanta.
cikin sanyi jiki Tasoma kokarin raba hannunsa da wuyanta ,amman ta kasa kwatar wunyata daga hannunsa .

zuba mata ido ammi tayi sosai tana karewa fuskar su'ad kallo tsab tare da jin zallar faduwar gaba . take kwalkwaluwarta tashiga caji akan wannan fuskar da take kallo agabanta .
ahankali ammi ta kai hannuwanta duka bisa fuskar su'ad ta kamo tana mata wani irin kallo zuciyarta na tsananta bugawa da karfi..
kafin daga karshe tasoma shafa fuskar su'ad jikinta na sake daukar rawa... shi AK km har lokacin yaki sakar mata wuya sai huci yake kmr wani kumurcin maciji.

yadda jikin ammi ke rawa hk murya take rawa gurin cewa "abdulkabir a ina kasamo wannan fuska?
wannan fuskar duk inda take nasanta, fuska ce wace bazata taba bace min ba har illa yauminl kiyamati..

ammi wannan fa itace mahaukaciyar yarinyar dake bibiyar rayuwata.....
a matukar tsawace ammi katse shi ta hanyar cewa "ubanka wannan fuskar ta wuce ka siffantata da mahaukaciya... ....dan ubanka ka sakar mata wuya.... wani irin yammmmmmm yaji ajikinsa tare da cire hannunsa a wuyar su'ad yana kallon ammi cike da matsanancin mamaki..wani abu yaji yashiga bin jikinsa tunda yatsun kafafunsa har zuwa cikin kwalkwarsa idan wani ya gaya masa ammi zata iya zaginsa akan wannan tantiriyar karuwar zai ce karya ne, sai gashi da kanta km agaban yarinyar datake kirarin bata son ya aureta take zagin ubansa.

cikin rawar jiki ammi ta mike tare da mikar da su'ad dake wani irin kuka yarinyar ya sunanki....? menene sunan mahaifiyarki da mahaifinki? a ina gidanku yake? ajere ammi ta shinga yiwa su'ad tmby wanda ita km kwata kwata takasa bude bakinta balle ta amsa mata.
cikin kuka ammi tace dan girman allah ki gaya min wacece ke da sunan iyayenki?
sill su'ad shiru tayi taki cewa komai.
ammi ta juyo a firgice tana kallon AK afirgice "maza maza kaje gidan minister kuzo tare yanzu yanzu ,yau ranar ce mafi dadi da farinciki arayuwata , byn wasu shrkaru da suka wuce " ammi wai tsaya menene hkn kike yi nifa bangane nufinki ba?
a think yau ne rana ta farko da kika soma ganin wannan yarinyar kin santa ne ko yaya? ya sake tmbyrta.

"kaje kawai ka kira min minister shi dady'nka yanxu yanzu shi dai ak gbdy ya rude ya kasa aiwatar da umarnin ammi ,sai wayarsa ya ciro cikin aljihun wandonsa ya kiran number minister , dana dady'nsa tare da sanar masu da sakon ammi sannan yakara da su hanzarta domin amminsa na cikin wani hali kar su dade.

atare motar commission data dady'n AK suka jero zuwa cikin harabar gidan .sukayi paking sannan suka fito suka nufi cikin part din dady.


zaune suke gbdy'nsu har Minister da bai dade da karasowa ba dady'n AK commission da mahaifiyar su'ad wace tunda tashigo itama taji gabanta na dukan uku uku ta dukar da kanta kasa ,sai maman zeey da hjy kakar AK, sai wasu daga cikin yan'uwan ammi kowa agurin kallon fuskar su'ad yake wanda hkn yasa tun kafin shigowar minister itama ta dukar da kanta kasa kmr yadda ummanta tayi tare da saka bakin mayafinta ta rufe bakinta zuwa hancinta.
amman duk da hk idanun jama'ar dake parlour 'n na kanta dauke da tmbyoyi iri iri .
banda dady'n ak wanda shi tuni ya dade da taba ganin fuskar da sukayiwa wannan kallo..

parlour'n ya dauki shiru sosai kusan na minti talatin babu wanda yayi yunkurin mgn acikinsu kafin daga bisa ahankali commission ya katse shirun da gurin yayi ta hanyar soma bayanin abinda ke tafe dasu da km dalilin zuwansu danshi bai wani hankaltu da yanayin da suka ciki ba ....
kafin commission yacigaba da bayaninsa ammi tayi saurin hanzarin katse shi.
ta fuskanci dady'n AK da minister sosai wanda shi alokacin ya matsu yaji wani abu daga bakin ammi ,dan jin dalilin dayasa akayi masa kiran gaugauwa .

cikin rawar murya ammi tace "minister dad'y abdul wani abun mamaki nagani yau " ehem meye shi wannan ? suka hada baki gurin cewa daita hk. mikewa tayi cikin sanyi jiki takarasa har zuwa inda su'ad take zaune tasa hannunta ta dago fuskarta tare da tsaita fuskar ga minster da dady'n ak wani irin zabura minister yayi tsaye yana nuna fuskar su'ad hannunsa na karrrrrrr gbdy har da jikinsa rawa suke ...... yayinda dady shi kallon fuskar kawai yayi yana sake tuno mamalakinta.. da kyar minister yasamu ya daidaita numfashinsa tare da sanyawa jikinsa natsuwa amman har lokacin jikinsa rawa yake cikin in.. ina... yace " aunty ina kika samo wannan ........?


mmn sudais ce

💗💗💗💗💗💗
SAI KA AURENI DOLE
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗



~NA~



*AYSHA A BAGUDO*



~DEDICATED TO~
HAUWA A USMAN
JIDDARH


*bissimillahir rahmanir rahim*

*hasbunallahu wa ni'imawal wakil*

no edinting


page 49


tun sanda umman su'ad taji sautin muryar mutumin dake tsaye kusa da matar da ita kanta batasan ko wacece ba, taji gabanta yashiga dukan uku uku har sanda matar tasoma mgn.
"yanxu abdulkabir yazo min daita wai itace yarinyar da take bibiyar rayuwarsa kan sai ya aureta dole, amman ni abinda yafi daure min kai da bani mamaki bai wuce fuskar yarinyar ba....

"shine nima abin daya daure min kai, inji cewar minister.
yayi shi kawai tare da tsurawa fuskar su'ad idanunsa yana sake karewa mata kallon tsab.
yadda yake kallon fuskarta hk gabansa ke bugawa abubuwa na zuwan masa daki daki...
kusan minti goma ya dauka tsaye yana kallonta tare da nazarinta sosai. naunauyen ajiyar zuciya ya sauke da karfi sannan ya sake yunkurin bude bakinsa .

" yarinya daga wani kasa kike zo ?

sannan meye sunanki ?

"ina mahaifiyarki take?

yayiwa su'ad tmbyr ajere hankalinsa a matukar tashe.
kallonsu su'ad take kirjinta na wani irin bugawa yayinda zuciyarta ke cike da tmbayoyi iri iri.
" su waye wadan nan mutane?
" sannan km meye hadinta dasu da zasu sakata gaba su dinga jero mata tmbyoyi kmr wasu yan jarida suna kokarin canza mata tuninta?

"ita fa abinda ya kawota daban ba wannan shirmen tambayoyin nasu ba mara ma'ana , dan batasan abinda suke mgn akai ba .
"ina suka san fuskarta? meye damuwarsu da fuskar da take dauke dashi tayiwa kanta tmbyr ?

ganin kmr ana son bata lokacin yasa commission cewa "wai akan me kuke son sani wani abu akanta yarinyar , byn duk abinda kuke son ji zata mana bayani da kanta?

"idan km damuwarku sanin mahaifiyar ne ai ga mahaifiyata zaune anan dan tare mukazo daita .

take idanu jama'ar dake gurin ya koma kan umman su'ad dake zaune kusa da hjy kakar AK. daidai lokacin datake kokarin dago idanunta dan ganin su waye wadan nan mutanen dake tsaye gaban yarinyarta ...
caraf idanun minister ya sauka akan umman su'ad ai sbd tsabar rudewa a tare suka zaro idanu waje daga umman su'ad har minister suna kallon juna cike da matsanancin mamakin sake ganin junansu ....

saurin dauke idanunta umman su'ad tayi tare da waskewa ,tayi tmkr tunda Allah ya halicceta bata taba ganin me irin fuskar ba..

yadda minister yaga ta dauke kanta akansa tmkr bata sanshi ba, ko taba ganin fuskarsa ba ,yasa take zuciyarsa tasoma wasi wasin anya kuwa itace ba kama bace yagani .
"kai kai wannan ya wuce ace kamace kawai...
idan ma me kama saleema yagani, kamanin fuskar yarinyar fa?

bakinsa na rawa yakira complete name dinta saleeemat dawood yusif .........domin tabbatar itace ko watace daban, jin yadda yakira sunanta dana mahaifinta gbdy yasa gabanta yacigaba faduwa..
ba ita ba hatta su'ad taji wannan faduwar gaba .
tunani su'ad tashiga yi zuciyarta na wani irin harbawa da sauri, to a ina wannan mutumin yasan cikakken sunan mahaifiyarta ..
"anya kuwa babu ayar tmby akan wannan mutumin da mahaifiyar AK?


"saleemat... minister ya sake maimaita sunan cike da kwarin gwiwa yana tsareta da idanunsa, lokacin har ammi ta isa gabanta tana kare mata kallo tundaga sama har kasa tare da son tabbatarwa kanta ,itace saleemar da suka dade suna nema ko kuwa dai watace daban.

umman su'ad dake zaune ko gezo batayi ba balle ta nuna ala'mun sunanta aka kira ba sai ma daura karfata daya tayi akan daya tana fuskantar su'ad dake zaune tsuru.

"aunty wannan ai saleema ce...... sai lokacin umman su'ad ta waigo inda yake tsaye ahankali tana tsare gira fuskarta babu tsoro balle wata fargaba "tace wannan ba saleemar da kake nufi bace, sannan ta meida idanunta da hankalinta kacukan akan commission dake zaune yana sauraronsu "ranka ya dade yakamata ace zuwa yanzu muyi abinda ya kawomu .... in samu na wuce da yarinyata .

ammi ta gigice ta kalli minister ta kalli su'ad ta juya ta kalli umman su'ad hankalinta idan yayi dubu a matukar tashe yake, banda gumi babu abinda ke tsatsafo mata, ta sake juyowa ta kalli minister fuskarta dauketa alamar tmby, muryarta na rawa tace minister kana nufi wannan itace salemar da muka dade muna nema ? minister ya kasa mgn balle kwakwarar motsi jin saleema ta karya tashi tare da nuna bata sanshi ba. atsawace ammi tasoma mgn cikin zafin rai kabani amsa man kamin shiru kana jina, ka tabbatar min da itace wace muke nema ko kuwa watace daban?
"muryar minister a matukar kasalance yace
"a fuska dai itace saleemar danasani amman abinda ya daga min hankali bai wuce yadda naji tace baita bace yakarasa mgnr yana cewa
may be ko kamace kawai aunty ..

" idan ita uwarta kamace yar fa? ammi ta jeho masa tmbyr data kusan tarwatsa zuciyarsa, tana sake hada uwar gumi .
shima minister gumi ne ke karyomasa takoina ajikinsa ,AK kuwa dawowa yayi tmkr mutun mutumi azaune yana kallon yadda amminsa ta rude ta gigice tasoma fita haiyacinta .
ahankali ammi takarasa gaban dady wanda yayi shiru yana kallonta yana jin wani irin dadi cikin ranshi.
dady'n abdul ka dubi yarinyar nan da kyau dawa fuskarta take maka kama ?
sai daya nufasa sannan yace ai na dade da ganin fuskar ,alokaci dana ga fuskar nashiga rudani sosai amman na barshi amatsayin kamace kawai dan hk kema ki dauka ka mace tunda mahaifiyar yarinyar tace ba ita bace wace kuke nema.
"kama km tana dayawa a duniya nima na taba haduwa da wanda muke kama dashi.. ..dan hk kubar mgnr muyi abinda ke gabanmu.

gyaran murya commission yayi shima yace "gsky kam kubari muyi abinda ya kawomu al'bashi daga baya kwa daura daga inda kuka tsaya .
ke.... commission ya dube su'ad " ki soma gaya musu meke tsakaninki da. abdulkabir .
"dady yace kowa ya samu guri ya zauna, hkn ce takasance kmr yadda dady yace, kowa ya zauna ,amman ammi ta kasa komawa mazauninta , jikinta banda rawa rawa babu abinda yake, sai lokacin idanuwanta suka soma fitar da ruwan hawaye... take tasoma ganin juwa dan hk ta dukar da kanta kasa tana me dafe goshinta, tunanin abubuwan da suka faru baya take ,wanda baza taba mancesu ba, gbdy idanunta suka soma rufewa tayi luuuuu ......zata fadi cikin zafin nama AK da dady suka tarota ,ta fada jikinsu iman takaraso da wani irin sauri ta rike hannun ammi cikin nata tana kuka tana kiran sunanta.. . ammi ammi wayyo ammi.. wai me ke faruwa ne hk? kunsamu a duhu, dan Allah kugayamana abinda ke faruwa ,ku dubi yadda mahaifiyarmu ta dawo.
"yaya kayi wani abu man ,dady dan girman kataimaika kar murasa ammi kuka take sosai tana rike da hannu ammi. wace batasan ko a wani hali take ciki ba.

gbdy yan cikin parlour 'n sun rude sai rige rigen zuwa gurin ammi suke suna sallami da kiran sunanta ,banda ummun su'ad dake zaune kmr batasan abinda ke faruwa ba.
wannan tashin hankali da suke ciki yabawa umman su'ad damar yiwa su'ad rada cikin kunnenta, karki sake ki tabo abinda ya danganci asalin tarihin mahaifinki..

ahankali minister yashiga dubata yaga suma ammi tayi dan hk ahankali yayi mgn cikin mutuwar jiki akawo ruwa suma tayi, iman ce ta kwasa da gudu taje ta kawo ruwa acikin cup minister ya amsa ya watsamata a fuska.

wata naunauyen ajiyar zuciya ammi tasaki hade da dafe kanta ta ware manyan idanunta bisa celling dakin zuwa can ta fara kallon dakin da mutane dake zagaye daita ,dady da AK sukayi mata kuri da ido kowane fuskarsa tattare da matsanancin tashin hankali, mikewa zaune tasoma kokarin yi, sukayi saurin taimaka mata. juyowa tayi ahankali jikinta a sanyaye caraf sukayi 4eyes da su'ad..... ahankali komai ya sake birkice mata yanzu duk wannan fuskar datake gani tsantsar kama ce.... da azama ta janye jikinta daga jikin dady.
a zuciyarta tace wannan fuskar ba kama bace,wannan fuskar ta wuce ace kamace kawai , wallahi wallahi wannan fuskar duk inda ta fito jinina ce takarasa mgnr zuci hawaye na gangarowa bisa kuncinta.
saurin matsowa tayi kusa da salema ahankali tace saleema....... umman su'ad tace ba ita bace ,ni suna rafiya... .. "dan girman Allah karki ce min ba kece salema ba.....
ki taimakawa rayuwarmu karki boye mana wallahi jikina yabani kece salema ....., idan km har ba ke bace salemar ta yaya diyarki take kama damu?
wallahi ko makaho ya dubi wannan fuskar yasan jininmu ce..... ..

"gsky kiyi hakuri hjy bani bace ... girman hukunci da kudirar ubangiji ta wuce hk ,ana iya samun mutane masu kama dayawa a duniya amman ita wannan salemar da kuke mgn akanta bani bace ita ni sunana rafiya takarasa mgnr tana dauke kanta ...

jikin su'ad yasoma rawa jin maganganunsu take tashiga zare ido tana kallon mutane dake zaune agurin, bata taba ganin hoton mahaifinta ba, balle ta kwantata wadan nan mutane amatsayin danginta ,da jin km yadda suke mgn da yadda ummanta tayi mata rada akunne tabbas tasan suna da alaka me karfi da mahaifinta, bakinta tashiga motsawa ahankali sbd tana son yin mgn amman tuno da gargadin ummanta yasa ta kasa furta komai.
ta dukar da kanta kasa tare da hade yatsun hannuna cikin juna ta matse , hawaye yashiga zubo mata tmkr an bude fomfo.

dady yakarasa ya kamo hannun ammi ya zaunar daita kusa dashi cikin sanyi murya yasoma mgn "abinda nake son ki gane km ki fahimta shine ki natsu baraka ki dawo cikin haiyacinki ita wannan yarinyar matsawar jinimu ce ina tabbatar miki zata dawo garemu, idan km kamace sai mu dauki hakuri muyi kokarin kulla alaka me karfi da ita. amman yanzu ki natsu kibari suyi abinda ya kawo su .
girgiza kai kawai tayi tare da dukar da kanta tana tsitayar hawaye ..
ahankali dady ya fuskanci su'ad dake zaune yace muna sauraronki yarinya, su'ad ta tsinci kanta da jin faduwar gaba sakamakon jin muryarsa......

cike da faduwar gaba yayinda idanunta suka sake cicikowa da wasu ruwan hawaye ta fara bada labari abinda ya faru abaya .

Lagos state university (unilag)


"wata rana ina tsaye a ajikin bishiyoyin cikin makarantarmu tare da wani abokin karatuna me suna mk, wanda yake matukar mugun naci akan yana sona.
kullun idan mun hadu da mk zancesa bai wuce su'ad ina sonki kiyi min alkwari zaki aureni da zarar mun gama karatu. bana kulashi sbd daukar maganarsa danakeyi amatsayin shirme.

"a wannan lokacin da muke tsaye tare dashi ma zance yake sake min na aureshi da zaran mun gama karatu ko idan karatunmu yayi tsakiya muyi aure so that sai mucigaba da karatu .
murmushi nayi masa me narkar da zuciya tare da girgiza masa kai ala'mun bazan iya wannan alkwarin ba.
" nifa kona gama karatun ba auren wuri zanyi ba, sbd banida lokacin wani soyayya arayuwata , zan cigaba da neman ilimi ne muddin rai sbd karatun shine abincin ruhina .
"na fada masa hk ne sbd tun haduwata dashi ban taba jin digon sonshi cikin zuciyata balle har naji zan iya aurensa, sai dai ina kulashi tare da tsananin girmamashi amatsayinsa na abokin karatuna kasancewar yana da tarin ilimi km yana meida hankalinsa sosai akan studies dinsa, kmr yadda nima nake meida hankalina akan karatu fiyye da komai .
a duk sanda zakaga mk karatu yake hk nima.
,duk da wannan son karatun nasa, ak kasance me taba shashanci, dan Allah yayisa da maseefaffen son yan'mata most especial mace fara me kyau, shiyasa a duk sanda yake gaya min irin son dayake min bana jin maganganunsa suna tasiri acikin zuciyata .
km idan ba text ko exam zamuyi ba baka taba ganina tare dashi ba.

wannan lokacin ma da muke tsaye littafi ne rike a hannuwamu muna tautaunawa akan karatu sbd washegari da safe zamuyi text . cikin hk ne ya katse karatun da muke, ya sako zance aure amsar dana saba bashi ita nabashi wanda yasa ya bata rai har jan tsaki .

cikin bakinciki yace ni dai duk ma me zakiyi arayuwa karatu daga nan har birnin sin muna tare km soyayarmu ba zata shafi lamarin karatunmu ba, tunda nima ina matukar son karatu, ni dai karki juya min baya dan duk ranar da kika juya min baya mutuwa zanyi shiyasa nake son kimin alkawari ...

rausayar da idanuna nayi wanda suke sake birgeshi, amman kwata kwata mgnrsa batayi wani tasiri ajikina ba cike da zolaya nace "ba yanzu zaka mutu ba ,sai dai mgnr gsky bazan iya maka alkwari aurenka ba ,amman idan Allah ya kaddaro kai mijina ne babu makawa sai mun auri juna ,na karasa mgnta ina juya bayana ahankali.
karaf idanuna suka sauka akan wata hadaddiyar mota kiran reng robe,ahankali me motar ya daidaita tsayuwar motarsa yasoma zuro zara zaran yatsun kafafunsa zuwa waje, kafin daga baya gangar jikinsa ya bayyana ,wani matashin gayen ne majiyin karfi mai tsananin kyau hade da kwarjini ,duk da cewar yana dan nesa damu kadan hkn bai hanani gane tsantsar kyawun dayake dashi ba,ina kallonsa yayi key'din motar yasoma takowa zuwa inda muke wanda ni km hkn yasake bani damar gane irin kyawun halitar da Allah yayi masa sanye yake cikin farin yadi wando da riga fari sol , kanshi babu hula gbdy kamshin turarensa ya game karasowa zuwa inda muke tun kafin yakaraso. fuskarsa kunshe da annurin fara'a , kadan ya rage bai karaso inda muke ba yasamu guri ya tsaya yana karewa yanayin makaranta kallo yayinda idanun dalibai sukayi masa caaa kowa kallonsa yake .
byn kmr minti goma naga wata yarinya kyakkyawa takaraso zuwa inda ya ke tsaye tana sakar masa tsadadden murmushi tare da kamo hannunsa cikin nata tana sake bayyana faricikin ganinsa . take ni km zuciyata tashiga tsalle tare da bugawa hk kawai na tsinci kaina da adduar allah yasa ba budurwasa bace .

mgn suke ahankali wanda bazan iya cewa ga abinda suke tautauwa akai ba,sanye take cikin doguwar riga baka har kasa me ratsin ja ajikinta .
ahankali na juyo da gangar jikina gbdy na jingina bayana da bishiya dake kusa dani na tsura musu ido ina kallonsu cike da faduwar gaba a yanayin yadda suke matukar kama da junsnsu yasa zuciyata tasoma zargin ko yaya da kanwa ne ..

mgn mk yake min amman ina gbdy hankalina da natsuwata basa tare dashi suna gurin matashin gayen dake gabana , har ya gaji da surutu ya kai hannunsa ya kamo hannuna,wanda sai lokacin nayi firgigib na dawo cikin natsuwata tare da buge masa hannu raina abace "nace meye hk mk?
"nifa banson wannan iskanci meye na wani kai hannunka jikina ?

"dole na kai hanuna jikinki mgn nake miki tun dazu amman hnklinki bai gurina ,amman kiyi hkr bazan sake ba tsaki naja tare da cewa "babu wani hkr da zaka bani "ni dai dan Allah karka sake yunkurin tabani dan banaso hkn, yace naji.
ni km ya juya nacigaba da matashin saurayin kayataccen murmushi yake sakar buduwar kmr yadda itama budurwa take masa, nima hk kawai na tsinci kaina ciki farinciki har da murmushi , sannan ahankali nasoma daga kafufuna zuwa inda suke nasamu guri nesa kadan dasu na tsaya ina sauraron hirarsu ahankali ahankali murmushi naga yayi tare da cewa yakamata nazo na koma gida hk sbd yamma tayi yakarasa mgnr yana duban agogon dake daure da tsintsiyar hannunsa.
"hb yaya tun yanxu zaka wani tafi yaushe ma kaxo, kabari nagama abinda nake mu wuce tare kasan tunda naganka bazan makaranta .

tunda naji yarinyar ta ambaci sunan yaya naji wani iri farinciki ya lullube kenan tunanina yazomo gsky ahankali na furta Allah na gode maka da kasa wannan matashin yakasance yayanta ne.

"dan Allah yaya karka tafi yanxu bangama ganinka wucewa zanyi baki ma gode ba danazo jiya fa na dawo ina bukatar hutu km ko ba hk ba kinsa bana son yin nesa da ammina kasancewar ni dan fari ne zatafi bukatata akoda yaushe ba kmr ke ba da kowa bai damu dake ba....
turo masa baki tayi cikin shagwaba

3 Comments On SAI KA AURENI DOLE
avatar
zainab-ishaq

1 year ago

Reply

Love it ????????

avatar
zainab-ishaq

1 year ago

Reply

Yes and I want to download it

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to zainab-ishaq

In order to download you have to subscribe for our package at https://tnovels.com.ng/subscribe

Please Login or Register in order to submit comment