Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

guri guda kamar wata macijiya ta sunkuyar da kanta k'asa,har yakarasa shigowa dakin ya ajiye abinda ke hannunsa ya juya da niyyar ficewa daga dakin bata motsaba,tambayar daya ya cillo mata tasa ta saurin d'agowa tana kallon bayansa jikinta cike da matsanancin shaukinsa,
"Ina iman take...?"
Bata bashi amsa ba haka zalika bata daina kallonsa ba .ta wani gefen fuskarta cike farincikin ganinta hkn dayayi babu kaya sannan zuciyarta cike da tsoron Allah yasa bai kamata ba.
, shirun daya ji tayi kuma ya tabbata da ba wai tambayar nasa ne bata jiba .
yasa shi jin Haushi yayin tsaki had'e da ficewa ya banko kofar da karfi yana jin haushita da takaicinta aranshi yace zan aurarwa kaina matsala yarinya sai gidadanci bansan sanda zata waye ba .
Sulalewa kasa tayi tana lumshe idanunta.tare sauke ajiyar zuciya. Byn ya fita ta mike taje tayiwa kofar key tacigaba da abinda take wanda yanzu kusan ya zamemata jiki..


Ihuce ihunce da umman su'ad taji kenan yasa tayi firgigit ta dawo hayyacinta,waige-waige ta shiga yi da tuna inda take saboda yadda ta tsunduma a wata duniyar ta daban ta fita wajen gidan da sauri tana dube dube.
samarina unguwar cike agurin ana rabon wasu dake dambacewa .
Ta godewa Allah yau bada diyarta akeyi ba amman duk da hk sai dataje taba da hakuri sannan .
Ta dawo cikin gidan tare dashiga cikin dakinta .
hango su'ad can tayi saman stool tana kokari tufke gashin kanta.
Ta sauke wani naunauyen ajiyar zuciya tare da saurin karasowa ta nufota domin hannata fita dan karshe fadan yazama nata.
,hannunta ta rike tare da janyota suka koma can bakin bed suka zauna ,
"Yawwa ummana kinga na kasa taje gashina dan Allah taimakon nan da kika saba zakimin.."
'Dan murmushi Umman su'ad tayi tace
"Dama ai ba abunda kika iya kullum sai maseefa da tashin hankali ko sauti mutane naji daga waje yanzu hankalina zai tashi Amman ke sam babu abinda ya dame Ki rayuwarki kawai kikeyi . haba Umman su'ad meyasa kikeyin hk kullun mgn daya nifa soma gajiya fa . Da zanji dana dade da dainawa . meyasa yarinyata?
dawota cikin natsuwa daidai yake da cikar burina.
kawai Ki min abinda na saki idan zaki min mutanen ai sune suke shiga track dina.

To bazanyi ba injicewar umma kullun nake miki,tsifama ta gagare ki bare kuma tajar kai..Ammmm..! Kin san me zan fad'a miki...?" ta raunata muryarta gurin cewa hk sbd tasan halin diyarta. Itama su'ad ganin yanayin da Mahaifiyarta tayi mgn yasa,
Da sauri ta shiga girgiza mata kai alamun bata sani ba, har sai ta sanar da ita
"Yawwa Autar ummanta abinda nake son ki sani yanzun shi ne,kinga dai yanzu girma kike karayi kullun kwanakin shekarunki na dada jayawa ko..?
to abinda nake sonki dashi shine komai zai hadaki da mutane bason ki k'ara tankawa .
Duk Wanda yashiga track dinki kiyi hakuri kibar mutun da Allah.
duk abu da suka danganci mara kyau ne ki barshi Ki rike maraicinki,haka zalika Ki rik'e talaucinki,Allah shi ya k'addara miki yin wannan rayuwar me cike da kaskanci wanda nasan ba hk kika taso ba, fatana shi ne ki yi hak'uri har zuwa lokacin da Allah zai yaye miki .
ya kawo rangwame a cikin al'amuranmu,kin fahimce ni ai ko..?"
kai ta d'aga mata jikinta a sanyaye kmr zance uwar yashigeta. Yayinda kwata kwata bataji nasihar ummanta yashigeta ba,sai ma wani Abu daya darsu cikin zuciyarta,
har umma zata ci gaba da magana su'ad ta dakatar da ita ta hanyar cewa
"pls ummansu'ad kiyi min abinda nasakaki. Kawayena suna jira na .
Sannan Ummansu'ad ina son yi miki wata tmby a karo na karshe me yasa da Abbana ya mutu muka cigaba da zama a wannan gidan ? Kuma da da damuwa da bakinciki suka miki yawa meyasa ba mu tafi danginki ba.kona mahaifina ba? take uwar ta canza fuska ranta yasoma baci..umma tayi mata banza tasoma tsefe mata gashinta batare da tayi yunkurin cewa daita komai ba.
su'ad ta girgiza kai dayake tana kallon yanayin yadda uwar ta sauya fuska ta cikin mirrow.
wai meyasa duk lokacin da nai miki wannan tambayar umma bana samun amsa daga gareki me yasa ummana bara ki fad'amin ba..?
Na sani kowane mutum yana tashi ne a tsakanin dangi biyu,dangin mahaifi da da kuma dangin mahaifiya,to amma umma me yasa ni na kasance mai dangi d'aya duk da suma ba wani saninsu nayi ba.
,ko sau d'aya baki tab'a gwadamin danginki ba,ina danginki suke umma...?
Dan Allah umma ki sanar dani inda suke ko ba a k'asar nan suke ba,wata rana idan Allah ya tacemin damuwata sai mu ziyarce su..!"
Shiru umma tayi,cikin y'an mintuna da yi mata tambayar idanunta sun cika taf da ruwan hawaye,ganin yanayin data shiga yasa su'ad marairaicewa hawaye har sun fara gangarowa ta rik'o hannun umma cikin nata tana sake fad'in
"Ki yafemin Mahaifiyata,ko kad'an bana son ganin abunda zai saki shiga yanayin damuwa,gashi a dalilin tambayata har kina shirin zubar da hawayenki,dan Allah ki yafemin,idan har a dalilin tambayar dana miki ne in sha Allah haka bare sake faruwa ba,daga yau ban k'ara tambayar inda danginki dana mahaifina suke in dai har bakece kika so sanar dani ba .
na hak'ura da jin asalinki dana mahaifina in Allah ya yarda..."na hakura na hakura daga yau zan cigaba da rayuwata batare da tunanin ina da wasu dangi ba...
Tana Gama fadar haka ta mik'e tsaye zata bar kusa da umma.
da sauri ta rik'o hannunta ta dawo da ita tana mayar da kanta bisa cinyarta data ta tashi..
kiyi hkr yarinya ta babu komai acikin sanin asalinki face damuwa da tashin hankali da saka zuciya shiga uku asalinki yana tattare da tsagwaron tashin hankali wanda daga karshe zakiyi da kisanin jinsa... ...duk munisa zan so ji umma ina son sanin asalina ki taimakeni kisanardani.......

wacece su'adullahi ..?

mmn sudais ce

πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—
SAI KA AURENI DOLE
πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–
πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—



~NA~



*AYSHA A BAGUDO*



~DEDICATED TO~
HAUWA A USMAN
JIDDARH


*qala rasulillahi sallallahu alaihi wa sallam la yadkulul jannata nammaamu*

*Allah messenger s a w said :the tale bearer will not enter jannah*

page 35

sunana saleema dawood yusuf uba na madugu km ni haifaffiyar kasar Cotonou ce .
kakana let Alhaji Yusuf Uba na madugu haifafen zugu ne dake cikin kasar Cotonou amman iyayensa asalin mutane maiduguri ne a k'aramar hukumar baga .
iyayensa da kakaninsa duk anan meduguri aka haifesu.
su din yan kabilar kanuri ne.
kmr yadda kukasani yan kabilar baga sun shahara a sanar saida kifi band'a ,wanda aka fi sani da busashen kifi. sana'a ce takawo iyayensa Cotonou har aka haifeshi.
Alhaji Yusuf uba na madugu shahararran dan kasuwa ne km sanan nan me kudi ne wanda duniya tasan da zamansa. sannan babu wanda zai iya kiyasta tarin dukiyar da Allah yabashi .
yana da mata uku...
hjy babba wace itace uwar gidansa me suna saleema itama iyayenta asali yan meduguri ne amman ita yaren shuwa arab ce wayan nan kwawawan fararen mutane nan da muke samun labarin kyawunsu ya shahara,
wanda a kasar Nigeria ma an tabbatar da tsagwaron kyawusu.
zama ne ya kawo iyayenta kasar Cotonou har Allah ya hadata da Alhaji yusuf alokacin suna cikin ganiyar kuruciyarsu.
tana da 'ya'ya goma shabiyar mata biyar maza goma.
aisha itace babba sai fatima halima khadija hauwa .
amazan km Awwal Sani Salisu Rabi'u Hamisu Abubakar umar usman aliyu dawood.. wanda shine auta a dakin.

sai matarsa ta biyu me suna saratu wace ita asalin yaren Cotonou ce agumawa ce masu tsaida danye kifi.
tana da ya'ya takwas duk mata.. hasana da husaina ummusalma hannatu rukayya shafa'atu maryam zulaiha.
sai matarsa ta uku me suna harira wace ita km mutuniyar kasar ghana ce yar asalin yaren chambawa tana da yara guda goma rasssssss duka mata.... hafsat amina mardiya janat hameda zakiyya hajara bilkisu lateefa kausar.
" alhj yasif uba na madugu ya mutu yabar tarin dukiya da ya'ya da jikoki bil'adadi acikin ya'yansa babu wanda bai mallaki dukiya me tarin yawa ba daga mazan har matan .
sai dai yan dakin hjy babba sunfi kowa samun dukiya da tarin gidaje da companies da gidajen mai kasancewar ita kadai keda zunzurun zama adakinta.
adalilin hk ya hadasawa sauran mata shiga damuwa da bakinciki ganin kusan akashi dari na dukiyar alhj yusif kashi saba'in sun koma dakin hjy babba.
tun daga wannan lokacin suka soma shiga da fita ganin sun sabauta mazan dakin hjy babba ta kowani hali tare da rabasu da dukiyar da suka gada ta kowani hali.
hjy harari tafi hjy saratu daukar zafi akan lamarin dan tuni ita har ta bazama cikin matsafan chambawa yan'uwanta .

duk acikin ya'ya mazan da alhj yasif uba na madugu ya mutu ya bari babu wanda ya dauki sana'ar kasuwancinsa kmr mahaifina wanda kusan shine karami acikinsu, duk sauran ma'aikatan gwanatine masu zaman kansu. tunda alhj yasif uba na madugu ya mutu aka raba gado akabawa kowa hakinsa mahaifina dawood ya dukufa gurin juya dukiyarsa babu kasar da baya shiga akan neman kudi ta hkn ne ma yayiwa sauran yan'uwansa zarra ..
ahalin yanzu dawood yusuf uba na madugu yazama shahararen dan kasuwa wanda da farko shima ma'aikacin gwamnati ne wanda a sanadiyar aiki ne ya koma cikin Cotonou da zama a babban birnin tarayyar kasar.
acikin aikin ne ya dan fara harkokin kasuwancinsa sbd shi bai dogara da arzikin mahaifinsa ba, shi dai acewarsa mutun ya tsaya bisa kafafunsa ya nemi na kasa yafi.
alokacin yana parm sec a ma'aikatar ilimi a kasar tasu ta Cotonou wanda daga baya yasoma bunkasa a harkar kasuwamcinsa har ya kai ga rubuta ritaya da kanshi wanda a zahirin gasky bai isa yin ritaya ba, tun a farkon soma aikinsa yasoma soyayya da mahaifiyata habiba. wanda alokacin ne km yasoma suna da fice akasashen duniya.
itama yar asalin Cotonou ce diyar kanwar hjy babba ce da suke uwa daya uba daya auren zumunci akayi musu daita .
yanzu hk mahaifina yana daya daga cikin manya manya yan kasuwa a kasar Cotonou yanxu hk shine babba dan kwangilar gina gidaje ko manya companies a Cotonou sannan km shine ministy a harkar kasuwamci na jahar Cotonou..
mu mu bakwai mahaifiyarmu ta haifa maza shida sai ni kadai mace da Allah yabasu. yusif Wanda yaci sunan kakanmu da abdullahi Ibrahim nuhu ismal Sulaiman sai ni saleema danaci sunan kakata wato hjy babba .

Hajiya habiba wacce muke cewa da mamma mace ce me shegen kyan gaske dan ma agurinta muka dauki tsantsar kyau da fari.
ni saleema dawood yusuf uba na madugu nakasance fara ce sol ko tabo daya babu ajikina. sannan nice na tattara dukkanin wani kyawun mahaifiyata da mahaifina har da kakata hjy babba. duk cikin ya'ya da jikokin marigayi Yusuf uba na madugu babu wanda yataka sawun kyawuna da farinjinina, sbd na kasance kwakkawa ce ajin farko.
ga gashin shuwa arab dana dauko har tsakiyar bayana .
nakasance irin matanan masu dirin gske kallo daya zaka min kaji nashiga ranka.a nan cikin garin Cotonou nayi primary school dina da secondry har zuwa matakin university nake.

bangaren hjy saratu kuwa tayi asirin tayi tsafin tabi malaman tsubu da bokaye amman duk babu narasa dan batasamu biyan bukata ba ,dan hjy babba atsaye take akan lamarin ya'yanta bata baccin daren, kullun tana tsaye agaban ubangijinta tana neman gafara tare da nemawa ya'yanta tsari. dan hk ba dan saratu taso ba ta hakura ta watsar da komai .

ita hjy harira kuwa kullun cikin bin bokaye take da malamai tsubu take amman asiri yaki kama ko daya daga cikin yayan hjy babba, shine wata kawarta tayi mata kwatance wani gahurtaccen boka dake aiki akan dutse atsakiyar ruwa.
yanzu hk zaune take a cikin dakinta ta kasa tsaye ta kasa zaune babu abinda take sai kulla mugun kudiri acikin zuciyarta domin ga alamum aikinta bai yi tasiri akan ya'yan hjy babba ba .
dan hk ta sake wani kudirin gobe goben nan zata km komawa gun bokanta tai mishi bayani har yanzu fa da sauran rina akaba.
domin bata ga wani aiki ba dan sai ci gaba suke samu cigaba arayuwarsu duk tsayin daren ranar hk harira tayi shi batare data runtsa koda idanuwanta ba daga ta kulla wancan sai ta kwance wancan .

aiko gari na wayewa ta dauki hanyar barin garin kmr zuwanta na farko dataje gun bokan cike yake makil da mutane yan neman taimako hk yasanya itama tabi layi sannu ahankali kowa yashiga ya fita har akazo kanta durkushe take agaban boka tana masa bayani .
boka wancan aiki dai baiyi bayi ba....... tun kafin tagama fadan hkn bokan ya daka mata tsawa yace kimin shr.. karya kike kice aikina baiyi ba, sai dai idan daga garekine aka samu matsala, shashasha me jan kunnuwa kawai .
harira tayi shiru tana zare masa idanu tmkr mujiya cikin muryar mgn me dauke da inda inda tace Allah ya huci ran boka ai min hkr tuntube harshe nayi.
ta ciro kudi masu yawa gaske daga gefen zaminta tace ga wannan boka so nake a nunka aiki da akayiwa ahlin mazan dakin salema .
burina a duniya bai wuce naga sun koma sun tsiya ce sun talauce sun koma bara akan titi .
boka ya katseta angama bukatarki zata biya kinga wannan kulli yana dauke da gashin matacce wato gawa kenan.
harira ta jinjina kanta alamun tana tare dashi kije ki nemi ruwan dake gudana kmr teku ,ko ki samu shekarariya rijiya wacce ba a budeta kijefa wannan kulli aciki amman fa asirin ba duka zama lallai zai kama ba. harira tace taji tai ma boka godiya ta bar gun..

byn wasu satitika da xuwan harira gurin boka al'mura suka soma sauyawa aka dakatar da mutun aku daga cikin ya'yan hjy babba aiki sannan dukiyar wasu daga cikinsu tasoma lallacewa .
mutane masu kima da daraja a idanun mutane amman yanzu suka dawo kmr wasu kananun yara dan abubuwa suke tkmr tababbu .
su kuwa sauran komai ta umarce su suyi yi suke batare da sanin mahaifiyarsu ba .
sannan basa kaucewa umarninta hatta dukiyarsu sun tattatara sun mallakamata wai a cewarsu ta dinga kula musu dashi ,sbd tana da rikon amana tafi mahaifiyarsu.
yayinda ita km babu abinda take da kudin sai bushasha .
abun kam yayi matukar yin yawa ita kanta hjy babba tsauri, yanzu abun ya fara damunta yadda harira take kokarin mallake mata ya'ya ta karfi da yaji tare da nesantata dasu .
bata jin dadin mutun 3 ga mutun 4 sun tare a gindinta suna faman mata bauta tana jin dadinta.
yayinda ita ke tattare da bakinciki .
hankalin hjy babba yayi matukar tashi domin kirikiri wasu daga cikin ya'yanta suka soma talauci zanga zanga gashi alokacin kowanensu nada iyali har da tarin ya'ya ..
cikin hk hjy babba ta sake dagewa da addua babu dare babu rana tare da rabawa manya malamai kudin akan su tayata da addua.

mmn sudais ce

πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—
SAI KA AURENI DOLE
πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–
πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—



~NA~



*AYSHA A BAGUDO*



~DEDICATED TO~
HAUWA A USMAN
JIDDARH

_alhamdullahi zuciyar bagudo hauwa A usman jiddarh ina matukar farinciki tayaki murnar kammala wannan mashahurin kayataccen daddaden labarin naki me suna gadar zare...... gadar zare labari ne zai ilimantar fadakarta ya wazantar da ul'uma sannan ya nishadarta, hakika kinyi namijin kokari sosai acikin wannan labarin naki sannan kin taka wargani domin kin xo da wani salon rubutu wanda ba duk writer ce zata iya kawo abubuwan masu mahimmanci da kika tattara acikin wannan labari me cike da darasi iri iri ,na jin jinamiki zuciyata πŸ‘πŸ»na sake jin jinamiki zuciyar bagudoπŸ‘πŸ»you are besty writer of the year ,Allah ya kara baseera da karfin ido _

_qala rasulillahi sallallahu alaihi wa sallam: la tabagaduw, wala takhasaduw,wala tadabaruw, wala taqatha'u ,wa kunu ibadallahi ikwanan_

_Allah Messenger saw :said do not harbour grudge against one another nor jealousy nor enmity and not show ur backs to one another and become as fellow brothers_



page 36

adduar ake takoina sbd yadda abubuwan suke sake tabarbarewa. amman babu wani sausauci acikin lamarin. kullun abun sai gaba yake.
yana sake tabarbarewa duk abinda suka taba matsawar da hannusu ne take zai narke ya lallace. idan business suka soma yanzu ne kudin zai narke a nema komai arasa .
a wani zuwa ne da mahaifina yayi garin yaga yadda suka koma abin tausayi, yasa aka budewa abbakar katanfarin commpines wanda za'a dinga yin kayan masarufi shi km aliyu companies cement shi da sani,.
duk wani abinda dayakamata a aiwatar dangin mayan injina an zubashi a ma'aikatun duka ,har an soma neman work's.
acikin sati biyu da kammala komai na company .
aka samu matsala domin atsakar daren ranar talata wacce tayi daidai da sati uku da bude companies din .
wata iska tazagaye kanfanunnunka daga baya sai gobara ta kama da duk wani kayan da'aka xuba ciki .
dun sun kone kumarsu. wani irin ci wutan take ta ban mamaki kmr ba wutan duniya ba duk yawan mutane dake kokarin ganin wutar ta mutu amman hkn yaki yiwuwa hatta masu kashe wuta kasa kasheta suka dole hk aka zubawa gurin idanu. sannan hk wutar ta dinga ci har byn kwana biyu sannan ta mutu dan kanta.
idan kudi ne ma hk zai tsiyace ya lalace ya tanbade ahannunsu batare da sunyi abun arziki ba har sai sun dawo suna karya murya tmkr yadda masu ma'ula kanyi ko mabarata. abinda ke ciwa hjy babba tuwa akwarya kenan.
na wannan iftila'in daya samun ya'yanta ,wani lokacin hk zata zauna da tsufanta ta tasa ya'yan agaba tana kuka tana rokon Allah yakawo mata saukin lamarin .
tunda yanzu har takai takawo abinda za'a ci ma agidajensu babu. tallafawarsu gabadaya ta koma kan dawood da sauran matan wanda wani lokacin idan hjy babba na kuka suke rarrashinta da kwantar mata da hknli.wanda dole tasa kullun suna kan hanyar gidan domin kwantar mata da hnkl.

yayinda duk wannan bakin asirin da harira ke bankawa bai shafi mahaifina ba dan shi kmr ma kara bunkasa dikiyarsa ake dan hk koda yaushe acikin taimawa yan'uwansa yake tun kafin su tmbayeshi zai basu hk kawan abinci yadda ake ajiyewa agidansa hk yake aika musu ,wannan abun ke sa hjy babba dan rage damuwar dake damunta tayi sanya masa albarka.

byn shekara uku

asarin da harira tayiwa yan dakin hjy babba yasoma karyewa yana komawa kanta .
domin dukiyar datayi asirin akansu duk sunkare tasss babu abinda ya saura .
sai yakasancewa an soma taba nata dukiyar data ya'yanta dake gidan miji .
nan fa hknlinta yayi mugun tashi.
domin sauran yaranta ma data aurar byn mutuwar marigayi haka dinga sakosu acewar mazajensu masu kafar tsiya ne dan tunda suka auresu suke asarar dukiya kasancewar guda uku daga cikin ya'yan data aurar duk masu mata suka aura nan jama'a suka soma rade radin a gari ai dukiyar da akabar musu ce take konewa killa ma alhj yasif uba na madugu ba kudin Allah da annabi bane kudinsa dan yawan dukiyarsa ace ace abin didiginta, hk dai maganganu mutane sukayita yawo acikin gari.
kowa da abinda yake cewa akan lamarin. wasu suce ba hk bane ba kudin jini bane jarabawa ce yayinda wasu marasa fahimata da imani suce sam kudin jini ne .
rayuwa fa tasoma sauyawa hjy harira duk abinda ta shuka daki daki suka dinga dawowa kanta da ya'yanta ,tashiga cikin matsanancin maseefa fiyye wanda hjy babba tashiga abaya .
tayi bakinciki wannan maseefar data sameta .. tayi kuka tayi juyi da ihu duk ita kadai adakinta babu wanda zata zauna dashi ta tautauna damuwarta dan ko ya'yanta tasanawar da abinda tayi yasa suka tsinci kansu cikin wannan hali tsine mata zasuyi.
dan gbdy ya'yan hjy yusif uba na madugu kansu ahade yake kowane bai son laifin dan uwansa .

rayuwa kenan wani sakamakon tun aduniya akeyinsa duk dukiyar da take bin bokaye akansu babu hk kazalika nata ma babu sai dai dan abunda bazarasa ba rayuwa tayiwa harira tsananin ga km halin damuwar da yaranta mata ke ciki tarasa mafuta abun yana matukar damunta fiyye da tunanin duk wani mahaluki.

tana daga kwance akan kujera tunani barkatai sai zuwa mata suke cikin zuciyarta ta rasa lalubo mafuta.

bata ankara ba sai taji saukar hawaye daga cikin gurbin idanuwanta, tabbas wannan shine kaikayi koma kam mashekiya, tayi abu yaxo yasha mata kai .
da tasani keya ce inji hausawa.

byn hannuta ta sanya tana goge hawayenta dake fitowa daga cikin kwarnin idanunta. faruwan hk yayi daidai da shigowar daya daga cikin yaranta cikin parlour tana hango hawayen dake fita daga cikin idanun mahaifiyarsu tayi wani tsalle takaraso gun datake kwance akan kujera tayi durkuso agabanta ta kamo hannayenta a rude take mata mgn hjy hjy meke faruwa dake hk duk kwanakin nan hk nake ganin cikin damuwa da tashin hankali idan ma wani abu ne yakamata ki sanarmana ba wai ki zauna kina asarar hawayenki ba .
tayi mata mgnr da harshen yaren Cotonou wato agumanci ,hjy harira ta kalli diyarta dake zaune agida yanzu tana zawarci ga yaron ciki, tace babu komai jannat .
jannat tayi saurin girgiza kai tare da cewa ban yarda ba wlh akwai dai abinda kike boye mana. babu yadda za'ayi ki dinga zama kina kuka kullun idan ma wannan maseefar data afko mana ce ai ba mu kadai bane kina kallo su yaya tsawon shekaru uku sukayi suna cikin wannan jarabawar me sukayi baya ga hkr . har gashi sannu ahankali sun soma dawowa daidai .
hjy harira tai shiru tana zance zuci duk lokacin data kallesu suna bala'i bata tausayin... jannat ta katse uwar ta hanyar cewa ko bakijin dadi ne a sanarwa yaya dawood ? hjy harira tayi shiru still taki cewa komai jannat ta bala'i rudewa sakamakon rashin yi mata mgn datayi ..bata ankara ba sai ga hawaye suna fita daga cikin idanunta .
da sauri hjy harira ta tmbyeta kukan me kike yi ?
ya zama dole nayi kuka sakamakon halin danaga kin tsinci kanki acikin kinki fada mana abinda ke damunki muna matukar kaunarki a raye bama son rasaki.
hjy harira ta dan yi murmushin karfin hali tare da girgiza kai tace kada wannan abun ya dameki bana jin dadin zuciyata ne .
amman yanzu komai ya wuce diyarta.
jannat tayi murmushi tare da cewa wai har naji dadi ta km yi mata murmshi tace kije ki dauki abinciki gaya can kici yana kitchen .
tana fita daga dakin harira ta mike ta fara zariya acikin dakin ta kai gwaro ta kai mari.
tasanya hannuta na hagu tana dan dukan goshinta dashi ,tabbas na tafka babban kuskuren ni ko me janyo min nayi yayan mijina asiri hk ?
ya zama dole na koma gun boka domin akarya min wannan asirin.
gashi nazo nayi abinda ya daneni inda asirin zai tsaya iya kansu ne ai da sauki .
take anan tayi niyyar komawa gurin boka gobe goben nan domin akarya asirin dataiwa ya'yan mijinta dan ko ya'yanta bata son suji abinda tayi wallahi tasan a yadda suke ji da yan'uwansu sai sun gujeta .
da wannan shawarar da zuciyarta tabata washegari da misalin karfe goma na safiya tayi shiri bata zame koina ba sai kauyen da boka yake amman abin tashin hankali koda ta isa ta iske boka ya mutu harira najin abinda wata tsohuwa ke sanar mata cewar boka ya mutu ai bata san sanda ta salale akan gwiwowinta ba ta daura hannuta duka a saman kanta ta rusa wani giggitaccen kuka.
wayyohhly ni

3 Comments On SAI KA AURENI DOLE
avatar
zainab-ishaq

1 year ago

Reply

Love it ????????

avatar
zainab-ishaq

1 year ago

Reply

Yes and I want to download it

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to zainab-ishaq

In order to download you have to subscribe for our package at https://tnovels.com.ng/subscribe

Please Login or Register in order to submit comment