Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

saka ran zan gani a Nigeria yanzu na tabbatar is no longer mine. Da muka je Nigeria sai muka zama abin kallo a gurin mutane saboda yadda muka zama, ni kaina nasan a cikin wadannan shekaru biyun ba karamin chanji na samu ba, fata ta wani mugun laushi da santsi, nayi kyar kiba ta komai ya cika yayi bulbul, ga kuma uwa uba wayewa, dadin mu daya mommyn mu is very strict, bata son shigar banza, dan haka koda English wear mu ka saka to sai mun rufe jikin mu, bama taba fita waje da matsatstsun kaya. Samari kuwa tun a makaranta har a gida haka muke ta fama dasu, daga ni har Hafsat har Amina babu wacce take kula samari, dan ni a England zobe na saya na saka a ring finger dina, duk wanda yazo naga yana kokarin ya fara nuna min soyayya sai in nuna masa zoben in ce "am married" duk da dai wadansu suna fahimtar karya nake yi amma dole su hakura tinda babu yadda zasu yi dani. Muna zuwa Nigeria ma abinda ya faru da mu kenan, dan ma samarin nan suna dan jin tsoron tunkarar mu amma duk da haka da akwai masu courage, in sunzo nakan tsaya in basu hakuri ince anyi mana miji, Hafsat kuwa ko kwallon inda suke bata yi balle ta kulasu. Rannan Amina tace "ni kam Hafsat zan ga saurayin ki a duniyar nan" nace "gaskiya kam, duk wanda Hafsat ta bude baki tace tana so to ya kamata azo kallonsa" bata kulamu ba saboda in miskilancin Hafsat ya tashi mu din ma bamu ishe ta kallo ba.

Satin mu biyu a Abuja muka tafi 'yalleman. Murna a gurin su inna ba'a magana. Tana ganin mu tace "lah, England din ce haka? Anya ba za abar karatun nan ba kuwa? Kar kuzo wata rana mu kasa gane ku saboda kun zama irin 'yan can" na rungume ta nace "we miss you too innarmu, in mun tashi tafiya next time tare zamu tafi dake saboda kullum kike ganin mu dan karki manta mu" ta rungume ni itama tana cewa "na ki wayon, salon mu tafi da baffa ki kwace min shi da wannan kyan ka kike yi kullum bayan ni tsofewa nake yi" Amina tace "kai inna, ai kamar ku daya ke da Moon"

Naji dadin zuwan mu 'yalleman dan ba kara min missing din su nayi ba. Nan da nan fara bin 'yan'uwan mu gida gida ina gaishe su kuma kowa sai na kai masa kayan tsaraba, har kayan da na siyo musu suka kare na fara diban kayan mu ina rabarwa. Nan take samari kuwa su kace dawa Allah ya hada su ba da ni ba, babu shiri na koma daki kusa da Hafsat na zauna na daina fita, amma duk da haka ban tsira ba saboda har gida ake aiko wa wai ana sallama da maimuna, Hafsat tana ta yi min dariya wai wa ya aike ni futa yawo a garinnnan.

Rannan muna zaune a compound din gidan sai daddy ya shigo zai gaishe da mutan gidan kamar yadda ya saba. Inna ta aika ni na dauko masa carpet a cikin gida aka shimfida masa, duk ya gaishe su mu kuma muka gaishe shi. Sai Hajja tace "ni kuwa muhammadu ina son magana da kai, da Adama naso muyi magana da ita amma sai nayi tunanin kar ta ce bakin ciki nake yi wa jikokinta" ina jin haka nasan maganar mu zatayi masa. Daddy yace "to hajja ina jinki" tace "anya muhammadu yaran nan ba za kayi masu aure haka ba? Yanzu ka debi yara mata ka tafi dasu kasar waje wai da sunan karatu? Wanne karatu mace zatayi wanda ya wuce na dakin aure? Ni dai a shawara ta ka dawo dasu nan, ga 'yan'uwansu nan sai a hada su auren zumunci, ga nuraddeen nan shima in karatun ne ai yayi, ya gama degree dinsa a BUK, ga balarabe, ga manniru duk babu abinda suka rasa. Ni tsoro yaran nan suke bani musamman wannan tsagerar" ta fada tana nuna Hafsat, "yanzu ma tana mana kallon wulakanci ballantana nan gaba in tafi haka? Ai cewa zata yi bata taba ganin mu ba" daddy yayi ajiyar zuciya yace "to hajja, ni ban taba tunanin hana su aure ba, ko yau suka fito da miji aure zanyi musu" Hajja tayi sauri tace "yo ai indai wadannan ne ba zasu fito da miji ba, ai indai ana so ayi wa wadannan aure to sai dai a fito musu da miji" daddy ya sake cewa "shikenan Hajja, yanzu abinda za'ayi ki kira su samarin ki ce su zo suyi magana da su Hafsat din, indai sun fahimci juna a tsakanin su to na miki alkawarin baza mu bar garin nan ba sai da auren su aka".

Chapdi, lallai da rabon Hafsat zata saka wa garin wuta gaba daya. Lol.
I love you all. Thanks for following


Episode Thirty Two : Munnir

Daddy yana gama fadin haka ya mike yayi musu sallama ya fita. Gurin kowa yayi shiru banda Hajja dake ta sambatun ta ita kadai. "Yauwa, yanzu na ji magana, amma abar yara suna so sufi karfin mutane? Yanzu kuwa zan kira 'yan samarin nan duk abinda suke yi su bari su taho gida, azo ayi ta ta kare" tsam mommy ta mike ta shige dakin da muke sauka in munzo, Hafsat ta tashi ta bita a baya, nan Hajja ta sake daukan magana "zasu je suyi kulle kullen yadda za'a fasa, ai kuwa wannan maganar kamar anyi ta an gama ne, yo gida bai koshi ba a bawa jeji?" Duk abinda take yi inna bata tanka ta ba, aikin gabanta kawai take yi. Sai da na gama taya inna juye furar da ta dama a jug na kai kitchen na saka a fridge sannan na shiga dakin mu. Dariya naji tana neman kubucemin saboda ganin yadda akayi upside down da dakin, duk su biyun sun dage suna ta loda kayan mu a akwatinan mu, wadansu kayan ma ba'a ninke suke ba haka ake watsa su. Mommy idonta ya kada yayi jawur, Hafsat kuma fuskarta kamar an aiko mata da mutuwa. Bance musu komai ba suma haka, na samu guri na zauna na zuba wa sarautar Allah ido, nan da nan mommy ta bani aikin kwashe kayan kwalliyar mu da underwears din mu. Muna cikin aikin da bansan na menene ba sai ga inna ta shigo, da mamaki take bin mu da kallo "yanzu Bintou shine kika tisa 'ya'ya a gaba kuke hada kaya zaku gudu?" Maganar guduwar da inna tayi shi ya saka dariyar da nake kunshewa ta fito, Hafsat ta bini da uwar harara hamkar idanunta zasu fado. Mommy ta yar da rigar da take ninkewa ta zauna dabas a bakin gado tace "inna yanzu zama zanyi a yiwa yaran nan auren dole, dududu nawa suke? Girman jiki ne fa kawai dasu amma ba wani shekarun kirki ne dasu ba ballantana ace sunyi kwantai za'a raba wa 'yan'uwa, wai Nuraddeen, har da Mannirun da baya ganin kowa da gashi" inna tace "ke waya ce miki za'ayi musu auren dole? Ya kike abu ne kamar ba kisan halin mijin kiba? Ni dai abinda kunne na ya jiye min yace shine 'za'ayi auren in dai har yaran sun amince a junansu' to menene kuma abin tashin hankali a ciki. Ke kinsan waye Muhammadu, kinsan babu yadda za'ayi yayi wa 'ya'yansa auren dole, amma yanzu kina diban su kuka gudu cewa zai yi ba kya son 'yan'uwansa. Ki zauna kiyi musu addu'ar zabin alkhairi shi yafi miki" tana fadin haka ta juya ta fice daga dakin.

In matsala irin wannan ta samu mutun, musamman harkar ta aure, rigima, koke-koke da tuburewa iyaye ba shine zai samar da maslaha ba, abinyi shine ka bisu a yadda suka zo maka sannan daga baya sai ka same su, ko ka samu wani wanda suke jin maganar sa kayi masa bayanin cewa kaifa baka son hadin nan. Sannan abu mafi muhimman ci shine ka yawaita addu'ah, wani baya taba auren matar wani kamar yadda wani baya taba haihuwar dan wani, rayuwar mu gaba daya a rubuce take duk abinda Allah ya rubuta sai ya faru da kai to babu tsimi babu dabara, addu'ah kadai ita ce maganin masifa. In Allah ya rubuta something bad zai faru da kai in kana yawaita addu'ar neman mafi alkhairi sai Allah ya goge ya rubuta maka something better.

Mommy ta fasa tafiya amma daga ganinta kasan ranta a bace yake, Hafsat ta kara hade gida, ni kuwa harkar gaba na nake yi saboda na yarda cewa daddy ba zai taba aura min wanda bana so ba, duk wanda yazo yace yana sona all what I have to do is in ce bana son sa, kalas.

Nuraddeen ne ya fara zuwa, very cheerful and nice guy. A falon inna ya same mu, kallo daya Hafsat tayi masa ta tashi ta shige daki, ni kuwa harda durkusawa ta ina gaishe shi, ya amsa min da fara'arsa yana tambayata labarin England da rayuwar makaranta, nan na zauna na tankwashe kafata na ringa kwararo masa labari yana dariya, shima ya fara bani labarin BUK da irin wahalar da suka sha ina ta mamakin banbancin makarantun mu na gida da kuma na waje. Sai da muka gama hirar mu ya tashi ya daga labulen cikin daki yace "Hafsat ke kuwa ko gaisawa ai kya fito muyi, ni ba cewa zanyi ina son ki ba dan kin fi karfina, in ma zaban zanyi sai dai Moon ita ce mutuniyar kirki, to amma ita kuma na dauke ta kamar kanwa ta" ina jiyo inna tana yi mata fada sannan ta fito ta gaishe shi tana kirkiro murmushin karya. Har ya juya zai fita sai yace "kun taba zuwa hadejia kuwa?" Muka girgiza kai a tare, yace "ku shirya to gobe tunda ina gari sai muje yawo ku gano fadar sarkin mu, kuga river hadejia" da murna ta nace "Allah ya kaimu, mungode Allah ya bar zumunci" daga haka ya juya ya fita, Hafsat tabi bayansa da harara. Yana fita ta kama kunnena ta rike "maza ki zauna kiyi ta wangale musu baki, in aka aura miki daya ni ko gidanki bazan ke zuwa ba" . Washegari kuwa mukaje hadejia da yaya Walid, nuraddeen da kuma mu uku har Amina. Munyi yawo sosai a garin, ya nuna mana duk guraren tarihi, hatta Hafsat ta ware muna ta hirar mu ta zumunci, a hanyar dawowa ne yake bamu labarin budurwarsa 'yar kano, tana karatu a BUK, bai kai maganar gurin iyaye ba saboda yana so sai ta kammala tukun. Hafsat tana jin haka ta sake warewa tana yi masa hira. Da zamu dawo gida ya sayo mana balangu mai uban yawa. Har zamu shiga gida sai ya kirani na dawo, seriousness na gani a fuskar sa nima na nutsu, yace "naji Hajja tace ta kira munnir shima, in yazo kar ki yadda ki sakar, masa fuska, bashi da kirki ko kadan kuma bashi da kunya" na gyada masa kai da sauri alamar na fahimta, daga haka na shige gida. Balarabe bai zo ba, sai yayo waya ta wayar inna wai shi ba zai samu damar zuwa 'yalleman ba sai dai a turo masa hotunan mu ta waya ya zaba. Nan inna ta haushi da bala'i "an gaya maka su atamfofi ne da zaka wani ce a turo maka hotuna ka zaba, aikin banza, ai ba neman kai muke yi dasu ba" ta inda take shiga bata nan take fita ba. Mommy tace "good riddance" nima kaina sai da maganar tasa ta bani haushi, lallai ma wannan mutumin, me ya dauke mune? Duk hajja ce ta jawo mana wannan wulakancin.

Shi ogan bai zo ba sai ana ya gobe zamu tafi, muna dakin inna Hafsat ta shigo tana bata fuska tace "wannan dan iskan ne yazo, I was hoping ba zai zo ba, ganinsa ma kawai yayi spoiling mood dina ballantana yin magana dashi" mommy tana jin haka tace "wai munnir din ne yazo?" Hafsat tace "eh shi fa, yana dakin hajja" mommy ta watsomin wani kallo tace "behave your self" bata ce da Hafsat komai ba saboda tasan halin abarta. Duk muna bedroom din mu ya shigo palon, tun daga daki muka jiyo kamshin turarensa. Hafsat ta kwanta taja bargo. Ina jinsu suna gaisawa da mommy da inna, yana tsokanar inna wai kullum kara kyau take ko ita zai zaba ne. A raina nace "oh ni 'yar nan, me hajja ta mayar damu ne? Kashin dankali?" Naji inna ta kalla mana kira wai muzo mu gaishe shi. Na dauki mayafi na na yafa na kalli Hafsat naga ta rufe ido. Ina fita palon mommy ta tashi ta shige daki tana harara ta, inna ma tace bara taje kitchen ta duba abinci. Kallo daya nayi masa na fahimci abinda Nuraddeen yake nufi da yace inyi a hankali dashi. Kallo daya nayi masa naji sam bai yi min ba. Tun daga sama yake kallona har kasa. Inna tana rufe kofa yace "damn, wai mafarki nake yi ne ko gaske ne Moon ce ta zama haka? Ni da hajja ta kira ni ina mita za'a hada ni da 'yar tsakuwa ashe kin zama dakwalwar kaza?" Binshi kawai nake da kallo, wannan me yake nufi ne? Sai a lokacin nayi nadamar saka mayafi ba hijab ba. Ya nuna min kan handle din kujerar da yake kai yace "come sit with me" lallai wannan duk inda nake tunanin sa ya wuce nan. Na tafi kujerar da take opposite dinsa na zauna ina gyara lullubi na. Tsam naga ya taso ya dawo handle din kujera ta ya zauna yana cewa "meye kuma na wannan uban lullubin, ni da nazo in ganki kuma in kika rufe me zan gani kenan?" Ya fada yana kokarin sauke min lullubi na. Na mike tsaye ina kallonsa. Kyakykyawa ne ba karya, dan gayu ne na azo a gani, haihuwa da rainon legas. Baban su shine babba a gurin baffa, kuma shi yake kula da business din baffa a lagos. Acan aka haifesu duk, kuma acan suka girma. Bafulatani ne gaba da baya. Ya riko gefen rigata "ina zaki je kuma ko gaisawa ba mu yi ba?" Na kalleshi a raina nace "yau dole in dauki page a cikin littafin Hafsat" na watsa masa wata hararar da bansan na iya taba, nace "don't you dare try to touch me again, in kana so mu gaisa ka koma kujerar da ka taso daga kai, in ba haka ba bazan kara second daya anan ba" ya mike yana wani shagwabe fuska yace "i can't help it wallahi, you are so beautiful" na wuce na zauna tare da hade girar sama da ta kasa irin yadda Hafsat take yi nace "ina wuni" cikin wata irin murya yace min "lafiya lau sweetheart, ya England? Nima nace "lafiya" a ta kaice. Daga nan ya fara min labarin irin kudin da yake samu, sabuwar motar da ya saya, irin yadda yake shanawa a lagos, ni dai duk ina jinsa, sai da na gaji na mike nace "bara in kirawo maka Hafsat", shima ya mike tare da cewa "there is no need, I have already made my choice" daga nan ya ajiye rafar 'yan dubu dubu akan santa table, ya sakar min wani kasalallen murmushi ya fice.


Episode Thirty Two : Mahdi

Na jima a tsaye ina kallon kofar da ya rufe bayan ya fita, me wannan mutumin yake nufi ne? Ni wannan ko a kafa aka daura min shi ai na gwammata in dau wuka in datse kafar in huta. Na zauna akan kujera na dafe kaina da hannayena. Dear Ibrahim, is this our destiny? Sai kuma naji haushin kaina, why am I even thinking of Ibrahim now. Me yasa har yanzu na kasa cire shi daga raina? Shekara biyu kenan rabona dashi, shekara daya kuma da yin aurensa, maybe har sun haihu by now. Jiki ba karfi na tashi na shiga daki na kwanta kusa da Hafsat. Tun muna yara dama ni bana son munnir, sam bai yi mun ba, ballantana yanzu da ya kara habaka, I must be strong, I must pray hard, in nemi zabin Allah kuma nasan Allah ba zai zabar min munnir a matsayin miji na ba. Ina nan kwance inna ta shigo take cewa waye ya ajiye kudi a palo? Nace "mata munnir ne" ta ajiye akan dressing mirror sannan ta fara yi mana fadan mun kwanta da la'asar bayan munsan babu kyau.

A ranar da daddare har nayi bacci na fara jin hayaniya sama-sama, na farka sai naji a compound ake yi, na tashi da sauri na fita palo sai naga Hafsat a tsaye a bakin window tana lekawa, na karasa kusa da ita ina tambayar ta "lafiya" ta yi min alama da inyi shiru. Nan muka cigaba da leke tare. Hajja ce take balbalin fada "ai ba haka mukayi dashi ba, ce min yayi ba zasu tafi ba sai an daura aure, kuma yanzu kawai sai ace min wai gobe zasu wuce?" Baffa yace "kai muhammadu mai yasa kayi mata alkawarin da kasan ba zaka iya cikawa ba?" Daddy yace "baffa ni abinda nace shine, in har an samu fahimtar juna a tsakanin yaran to baza mu bar garin nan ba sai an daura aure, kuma ai daga zuwan manniru yau ba za ace har sun fahimci juna shida maimuna ba, abinda nake gani shine kar ayi gaggawar auren nan ya zama an bata zumunci maimakon a gyara shi, a bari idan yaran sun daidaita tsakanin su shikenan" hajja ta katse shi da cewa "yo yaushe zasu daidaita tsakanin su bayan zaka dauke yarinyar ku tafi? Ai in ma so ake su daidaita sai a bar yarinyar anan yadda zasuke ganin juna" kawu Aliyu yace "hajja rayinyar nan fa karatu take yi, ya za'ayi a raba ta da karatun ta? Daga manniru har maimuna 'ya'yan mu ne, ba za mu so mu tauye wa wani hakkinsa ba, tunda yarinyar nan tace bata son shi a rabu da ita, hajja zamani fa ya chanja, yanzu da da ba daya bane, idan da anyiwa yara aure ba tare da son ransu ba suna hakura yaran yanzu zasu zo su bata mana zumuncin mune. Maimuna yarinya ce mai hankali wallahi, Manniru ba shi da kunya sam, kuma ya girme mata nesa ba kusa ba, ni dai baffa ina ganin in akayi wannan hadin an tauyewa yarinyar nan hakkinta kuma zata iya ta kullace mu har abada" a raina nace "God bless uncle Aliyu, Allah ya baka abinda kake so duniya da lahira" na jingina kaina wanda already ya dau zafi a jikin Hafsat ina cigaba da sauraron mahawarar da zata iya chanza rayuwata gabadaya. Baffa naji ya fara magana "kai manniru kana son auren maimuna kace ko?" Nayi sauri na leqa window, munnir na gani a zaune a gefen hajja, murya kasa kasa yace "eh baffa" baffa yace "to shikenan, na baka damar ka cigaba da neman auren ta daga yau har zuwa ranar da zata gama karatun ta, idan kafin nan ta amince tana sonka shikenan" da sauri munnir yace "baffa shekara uku kenan fa nan gaba" tas, naji saukar mari daga hannun uncle Aliyu zuwa fuskar Munnir, inajin Hafsat tana dariya kasa2, nan uncle Aliyu ya rufe shi da fada "baffan kake musawa magana? Rashin kunyar taka takai har haka?" Baffa yace "rabu dashi Ali, idan ba zai jira ba ya nemo wata a aura masa, ni na gama magana" daga nan ya mike yayi hanyar part dinsa. Nan gurin ya hargitse kowa yana fadin albarkacin bakinsa, kuma daga dukkan alama fiye da rabin mutanen gurin basa bayan wannan hadin saboda duk suna yabon halayena tare da kushe da Allah wadaran halayen munnir, inna sam bata cewa komai, hajja kuwa sai kumfar baki take har da cewa duk sanda mukayi kwantai kar a kawo mata. Munnir kuwa tun daga inda nake nake hango yadda ya murtuke fuska yana bin kawunnan mu da mugun kallo.

Washe gari tun assuba muka fara wanka muna fitar da akwatinan mu, inna ta zo ta saka mu a gaba da nasiha "ku kyautata addinin ku, ku bi iyayenku, ku tsarkake zuciyar ku daga mugun nufi akan kowa, in kuka yi haka Allah ba zai munana rayuwar ku ba, kullum in za kuyi addu"a ku nemi zabin Allah, kar kuce 'Allah ka bani kaza ko Allah ka yi min kaza' gwara kuce 'Allah ka zaba min mafi alkhairi a duk al'amurana'. Ku yawaita karatun alqur'ani dan shi kariya ne, musamman ayatulkursiyu, ku mayar da ita tamkar babbar kawarku kullum ta kasance a bakin ku, in zaku kwanta bacci kuyi alwala, na tabbatar muku in kuka rike wannan duk wani mugun nufi na mutun, aljani ko shaidani ba zai same ku ba".

Kiri2 sanda mukaje yiwa Hajja sallama taki kulamu, haka muka taso muka fito, Hafsat tace a hankali "kinyi wa kanki" muna fita waje naga nuraddeen tare dasu ya Walid, muka gaishe su muka wuce. Na shiga gaba Hafsat ta zauna a baya tunda tare zasu zauna da mommy, ba tare da Amina zamu tafi ba, saita karasa hutunta anan zata same mu a Abuja, ya Walid ne zai tuka mu. Ina zama sai ga nuraddeen yazo yana tsokana ta "amaryar yayan mu" sai na samu kaina da daure fuskata, yayi dariya yace "congratulations though, naji yadda aka kare maganar jiya" nayi masa murmushi nace na gode, ya juya yace "gashi nan yazo sallama bara insan inda dare yayi min" sai da ya matsa sannan na hango munnir yana tahowa inda motar mu take, sai a lokacin nayi nadamar fito war mu da wuri, da munsani mun jira mommy dan nasan duk rashin kunyarsa ba zai yi a gaban mommy ba dan zata iya kwakkwada masa mari. Na yi sauri na dauko wani katon bakin glass na saka wanda ya kusa rufe rabin fuskata, yana karaso wa na daga glass din motar, ga mamakina sai naga ya zagayo ta side din driver, ya shigo ya rufe kofar, daga dukkan alama bai san da Hafsat a motar ba, na dauke kaina tamkar ban san ya shigo ba, murya can kasa yace "ba gaisuwa" nayi banza na rabu dashi, ya sake cewa "shine kika ce da kawu ambassador ba kya so na ko?" A zahirin gaskiya ni daddy bai tambayeni ba, asali ma bamu taba maganar dashi ba, nasan ya fadi haka ne saboda shima baya son wannan hadin. Ji yayi bani da niyyar cewa komai ya sake cewa "ina so ki sani, yanzu na fara sonki, kuma zan cigaba da bin wannan tsohon har sai ya amince da maganar nan dan ni yadda nake jinki bazan iya jiran 3 years ba" still no reply from me, na juya kaina ma ina kallon daya side din, kawai sai jin hannunsa nayi a fuskata yana kokarin juyo dani in kalle shi, Hafsat tana daga baya tace "hey, don't" a tsorace ya juya ya kalleta, duk da ban juya ba na tabbatar harararsa take yi, yace "hey, yaushe kika shigo?" Tace "tun kafin ka shigo, naji komai" yace "sa'ido fa babu kyau, musamman a harkar miji da mata" Hafsat tace "not even in your dreams". Suna cikin haka mommy ta fito, da sauri ya juyo gurina yana min blowing kiss tare da cewa "sai munyi waya" ya fice, a tare mukayi tsaki ni da Hafsat. Yana fita gurin mommy ya tafi ya durkusa yana gaisheta, Hafsat tace "chusa kai ba kwarjini" mommy ta amsa masa fuskarta a sake sannan ta karaso mota. Su daddy ma duk suka shiga motar su shida ya Habeeb da faruk, sai motar security a gaba, muka tafi.

Tun daga ranar har muka koma England kullum sai munnir ya kira ni a waya, na rasa a gurin wanda ya samu numberta, muna komawa England muka koma school.

Shakara daya tazo ta wuce muna ta karatu, har shekarar ta wuce babu Ibrahim babu labarinsa, munnir kuwa har yau yaki hakura duk da maimaita masa da nake yi kullum cewa bana son sa. Amira ma muna da contact da ita tana ci gaba da karatun ta a abuja. An tura mu clinicals, daddy

Please Login or Register in order to submit comment