Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

"sorry tare da langwabar dakai, ta harare ni ta dauke kai alamar har yanzu fushi takeyi. " is he good? " na tambayeta. Kamar ba zatayi magana ba sai kuma tace "you will find out tomorrow, we have him double period da safe" " oh my God Moon, he is so good, ban taba enjoying mathematics irin na yau ba, I really did enjoy it. Wato dalla-dalla yake bin komai kuma sai ya tabbatar kowa ya gane sannan zai yi gaba. Gaskiya Moon kinyi missing " inji Hasiya wacce ta dawo kusa da desk dina fuskar ta kamar gonar auduga. Na mike tsaye na dubi sauran 'yan class nace "OK people, tomorrow, I will give the Thin Tall Man a chance" "Thin Tall Man?" suka kusan hada baki. Nace "yes" matter of factly, "baku ga yadda yake bane? I think the name fits him perfectly". Dariya ajin ya dauka gaba daya, inda ni kuma na bawa Hafsat hannu muka kashe muna kyalkyala dariya. Amira na hango ta gefen idona fuskarta dauke da bacin rai.


Episode Eight: The New Imam

Muna hostel da daddare Amira tazo dakin mu ta sameni nayi wanka ina shirin yin bacci, ta zauna a bakin gadona. Da yake yanzu mun zama seniors ba bunks ne damu ba. Still dakin mu daya da Hafsat da wadansu Christians su biyu Naomi da Abigail. Mu hudu ne a dakin mai dauke da gado hudu, lockers hudu da kujerun karatu kowacce da table dinta guda hudu, sai fridge guda biyu. Dakin babu tarkace da yawa da yake Hafsat akwai tsafta kuma duk ta fimu girman jiki hakan yasa ta zama kamar Senior din mu. Babu wanda ya isa yayi kazanta. In kaga Hafsat tana bamu order sai ka dauka ba class din mu daya ba. Muna da toilet din mu guda daya a dakin wanda muke sharing mu hudun, kuma kullum twice cleaners suke zuwa su wanke mana shi duk da ba wani datti yake yi ba. Masifar Hafsat ma ba zata barmu muyi kazantar ba.
Ina tsaye ina kallon fuskata a mudubin jikin locker din Abigail Amira ta shigo dakin sanye da dogon hijab har kasa tare da sallama. Ina ganinta nasan har ta kwanta ta taso. Ta cikin mudubin nake kallonta har ta zauna a kan gadona tace "kai Moon wannan bargon naki da laushi yake, wannan inna kwanta a kansa ai ba zan iya tashi daga bacci ba" na juyo ina fuskantar ta nace ' ko kina so in bar miki ne, u can take it if you want. Ina da wani" da sauri tace " a'a wannan ai sai in kasa tashi sallah asuba" muka yi dariya baki daya. Hafsat dake kwance kan gadonta tana karanta novel tace "Amira wai da gaske yasaiyadin mu ya tafi umrah?" Amira tace "eh wallahi Hafsat, shine ma maganar da nazo muyi. Ya tafi umrah, sai nan da at least a month zai dawo. Na taho na zauna kusa da Amira nace " to fa, yanzu me ake ciki kenan Amira? Waye zai ke janmu sallah kuma wa zai ke yi mana dori? Amira a lokacin itace mosque prefect dan haka duk wasu bayanai akan harkar addini a gurinta a ke samu. Tace "senior master dai yace they will find a solution. Maybe da assuba in muka je sallah zamu ga new face" na dafe kai nace "oh God, I don't like these changes da muke samu wallahi" Amira ta gyara zama tace "change is sometimes good Moon. Dama maganar da nazo muyi kenan, karki damu kanki da wadanna changes din har su zo suyi affecting dinki negatively, please Moon, give the change a chance, ki daure, you might even like it. Bana so gobe idan munje masjid kinga new imam ki yi loosing interest akan karatun ki. Kinga kun kusa sauka ke da Hafsat. Kada kizo karatun ki ya koma baya kuma. Muka kalli juna nida Hafsa wacce yayi her usual side looped smile tare da whispering "she likes you" na tashi daga dan kashingidar da nayi nace "I like you too Amira. Kuma insha Allah babu abinda zai samu karatu na, besides, I have u". Amira tayi sauka tun kafin tazo school din. Shi yasa run muna jss ni da Hafsat muke daukan karatu a gurinta. Tana dariya ta mike tana cewa "ni din bayan in muna karatun wasa kike yi. Da haka ta mike tare da wishing din mu good night, tayi sallama dasu Abigail sannan ta tafi dakinsu
Ajiyar zuciya nayi nayi rigingine ina tunano abubuwan da suka faru a ranar. Na fahimci cewa abinda nayi ban kyauta ba. Ya kamata in bawa Thin Tall Man chance kamar yadda Amira ta fada kafin in ce bana son teaching dinsa. Abinda nayi na kin shiga class dinsa is very wrong, za'a iya furnishing dina akan hakan. Amma duk da haka bai nuna min bacin ransa ba sai ma neman sulhu da yayi dani. Kafin inyi bacci ranar sai da nayi alkawarin insha Allahu gobe zanyi making up for my mistakes.
Washegari kuwa kamar yadda muka yi tsammani hakane ya faru. Mukaji muryar diff liman yana jan sallah. Muka yi joining har aka idar sannan muka tafi class din da ake mana islamiyya. Muna zazzaune muna bitar karatun mu na baya sai gashi ya shigo ajin. Duk da cewa akwai duhun assuba amma class din tar yake da fluorescent light wacce take a kunne. Kallonsa na tsaya yi cikin mamaki. It is the thin tall man. Jallabiya ce a jikin sa ash color sai bakin dogon wando da bakar hula a kansa. Idonsa babu glasses. Ya shigo ya rufe kofar tare da jingina a jikinta, ya ringume hannayensa a kirjisa tamkar mai jin sanyi. Daya bayan daya ya ringa binmu da kallo har idonsa ya kawo kaina, muna hada ido nayi saurin sunkuyar da ido na kasa. Gyaran murya yayi na dago kaina kawai sai naga ya yi min murmushi nima kuma sai na samu kaina da yi masa murmushi. Na sake sunkuyar da kaina kasa a karo na biyu. Ya sake yin gyaran murya tare da cewa "I was asked by the senior master to guide you through your Islamic studies before your mu'allim returns from his pilgrimage" ya tako a hankali ya jingina da jikin board yana facing din mu sannan ya cigaba da cewa "I don't know how you guys do it, do u have a class monitor or something?" Duk muka amsa masa da "yes" sannan ya bukaci da ta tashi tayi masa bayanin yadda tsarin karatun mu yake. Nan Amira ta tashi cikin nutsuwa ta fara yi masa bayani dalla dalla tare da nuna masa time table din mu. Yana sauraronta attentively yana gyada kai alamar fahimta. Sai da ta gama sannan yace " with your permission, I will like to make some changes. Instead of group progression I will like it to be individual so that we will carry everyone along. Because of the time factor, we will add night classes to the early morning ones so that we will have enough time. I will discuss this with your Senior master to see if its OK to have the night classes". Ya zagayo gabana ya dauki alqur'anin da yake bude a gaba na ya duba inda muka tsaya sannan ya mayar ya ajiye yace " I don't think we can start today, the time has already run out, we will insha Allah start tomorrow. Maassalam to u all" duk ajin suka amsa masa da "bissalam" banda ni wacce haka kawai naji na zama uncomportable saboda tsayawar da yayi a kusa da seat dina. Duk iskar da zan shaka sai na shaki kamshin jikinsa da scent din after shave dinsa.



Episode Nine: Give Me a Chance

Geography lecture din da muka yi was very interesting. Sai yanzu na fahimci abinda Hasiya take nufi lokacin da tace yana bin komai dalla-dalla. He makes sure He carries everybody along. Yana making references da abubuwan da na fada rannan yana kara buda su dayi mana bayani using simple terms wanda ko the most stupidest person zai gane. Anan na kara fahimtar cewa shi mutum ne mai tsantsar nutsuwa, komai nasa a hankali yake yinsa. He is very gentle, bashi da hayaniya sam.
Toward the end of the class sai ya bamu classwork, kowa ya rubuta abinda ya fahimta a game da topic din yau for 10mins. Kowa ya dauko takarda ya fara rubutu, ni kuma na duba takarduna na rasa fullscap sheet, sai na juyo gurin Hafsat nayi mata alama da hannu akan ta bani paper, take mutuniyar tawa sai ta makale kafada tare da murguda baki. Takaici ya ishe ni gashi time yana tafiya. Sai na juya gurin Amira. Kafin Amira ta fallo min sai naga an ajiye min paper a gaba na, na daga kai na kalleshi na ce "thank you sir" ya amsa da "don't mention, what are friends for" tare da yi min irin kallon nan na 'kin tuna'. Nayi murmushi nima na fara rubutu. Ga mamaki na sai na ganshi ya zauna akan desk dina kusa da takardar da nake rubutu a ciki. Lokaci daya wannan special kamshin nasa ya ziyarci hancina, naji wani iri a jiki na tun daga kaina har zuwa yatsun kafata, nan tubutun ya gagareni dan duk ideas dina guduwa sukayi suka barni na kasa hada koda cikakken sentence ne. Na saba jin masculine scent a wajan su ya Walid but it never have this effect on me, nashi is like special, it tells me that he is very much male. Na zama very uncomportable har absentmindedly na fara fidgeting da kasan hijab dina.
A hankali ya sunkuyo da kansa sai tin kunnena, unexpectedly naji yayi min magana a kunne yace "am I making you uncomportable?" Ya fada in a very low whisper. A firgice na dago kaina sai ga idona tsaf cikin nasa with his face few inches from mine. In that instance da muka hada ido dashi, everything froze, me, him, time, the class and even my heartbeat. Ido na ya rufe bana ganin komai, kunne na ya toshe bana jin komai. A cikin wadannan seconds din (or maybe minutes, I don't know), babu abinda yayi existing a duniya ta sai shi, only him. Fuskarsa kadai nake gani, kamshinsa kadai nake shaka. Apart from him komai ya zama blank. A hankali na fara jin muryar Hafsat tana cewa " sir, sir, sir" sai muryar kuma ta fara karfi sannan ta zama tamkar kara a kunnena. Nayi blinking once, twice sai a sannan common sense dina ya fara dawo wa, sai a sannan na fahimci abinda ya faru. We have been staring at each other for a while (I don't know for how long). Take naji tamkar kasa ta tsage in shige ciki, na dauke fuskata da sauri zuwa daya side din. Sannan na lura cewa kusan duk 'yan class din mu suke kallo. Hafsat naji ta sake cewa "sir" da karfi, daga jin muryar ta nasan cewa she is really angry. Yau na san na shiga uku. What is happening to me? What just happened? Murya can kasa naji yace " yes, what is it?" "I am through sir" " through with what?" Ya tambaya har yanzu muryarsa bata dawo dai dai ba kuma clearly kansa ma bai dawo dai dai ba. "Through with the class work sir, you gave us classwork, remember?" Ta fada tamkar mai shirin tashi zama, "ohhh" shine abinda kawai yace yana shafa kansa. Sai kuma ya mike ya kama hanyar fita yana cewa "keep it with u. I will collect it tomorrow" daga haka ya fice ba tare da ya juyo ba, ba kuma tare da ya dauki glasses din sa, handset da papers dinsa da ya ajiye akan podium ba.
Yana fita Hafsat ta zagayo gaba na tare da saka duk hannayenta biyu ta rike kugunta ta na kallona fuskarnan filled with fury ta fara yi min masifa " were u flirting with the thin tall man ko idona ne yake min karya" na bita da kallo ina mamakin mai take nufi, I still don't fully understand what happened, ni ina ganin kamar stroke na samu, for all I know I could be sick or something " answer me" ta sake doka min tsawa. Kafin in bata amsa teacher din mu na physics ya shigo, a dole Hafsat ta zauna tare da zagaya hannun ta a wuyanta alamar I will kill you.
Muka gaishe shi, ya amsa da fara'arsa, ni dai duk jikina a sanyaye. Bayan mun zauna ne ya kalleni yace "Moon, what is wrong with u?" Hafsat nayi sauri tace " help me ask her oo". Da yake teacher din mai barkwanci ne Sai yayi dariya yace " maybe the geography was so boring, worry not my dear, I will cheer you up with physics " akayi dariya gaba daya. Sai a lokacin ya lura da kayan kan podium, yace " clearly, the geography was boring to the teacher also, he forget his his things. Do u guys chase him out? " aka sake dariya gaba daya tare da cewa "no, sir" yace " OK, to brighten up our Moon, let's send her on an errand to return this to the runaway teacher " na sauri nace "I rather not" ina jin Hafsat a bayana tana cewa "good for you" Yace " why not?" Sai kuma na kasa bashi amsa. Amira ta yi sauri tace "let me take it to him, sir" amma sai ya dage akan lallai ni zanje, a cewar sa it will help clear my head.
Ba yadda zanyi dole na karba na fita, ni yanzu bansan ma inda zan same shiba. Na dau hanyar staffroom. Na shiga naga bayanan, sai naga another copper a zaune yana marking some papers, na gaishe shi tare da tambayar whereabout of Mr Ibrahim, ya dago kansa ya kalleni tun daga kasa har sama with devilish smile on his face tare da cewa " hello beauty, why are u looking for him? Na hade raina nace "is he around?" Ganin na bata rai sai ya zama serious yace "he is not around, but I can take message for him. My name is victor, Ibrahim and I share the same room" " OK " nace " please give this to him, he left them in our class "Nace tare da ajiye kayan a gabansa.
Na juya na fita, in my mind ina godiya ga Allah da bayanan. Kaina a kasa ina tafiya naji nayi karo da mutum. Nayi sauri na matsa. Bana bukatar in kalli fuskarsa, kamshin da naji ya gamsr dani cewa shine. Cikin in ina nace "I brought your things" " OK , thanks "ya bani amsa a takaice. Nayi sauri nace" I was asked to do so by our physics teacher " OK ya sake cewa. Nayi gaba inajin haushin kaina, mai yasa nayi masa magana. Sai kuma naji ya kira sunana" Maimunatu" ban amsa ba kuma ban tsaya ba. Ya biyo ni da sauri yasha gaba na. Ga mamakina sai naga ya kama hannuna, nayi sauri nayi dago kaina na kalleshi, fuskarsa babu murmushin da na saba gani a ciki. Na bude baki na zance ya cika ni sai naji ya saka min wani abu a hannuna yace "this is for u" daga haka ya saki hannuna ya juya ya tafi. Na sauke idona a kan abinda yake hannuna sai naga ashe jotter tace da ya karba a library, a front page kusa da inda na rubuta sunana naga ya rubuta PLEASE, GIVE ME A CHANCE


Episode Ten: I Don't Know

Har na karasa class ina tunanin mai wadannan kalaman suke nufi. Give me a chance: a chance to do what? A chance to prove what? A take naji kaina ya fara ciwo. Ina shiga class din mu naga teacher din mu zaune akan teacher's chair ya zabga uban tagumi da hannu bibbiyu sarcastically, na kalli 'yan ajin naga suma duk sunyi mimicking abinda yayi, bansan lokacin da dariya ta kubce min ba. Yana ganina ya mike taye tare da cewa "ahh she is finally back" nan na fahimci tagumin duk na jira na ne. Ya tambayeni ko na same shi? Sai na samu kaina dayi masa karya cewa ban ganshi ba amma na bawa a mr Victor to give to him, which is partly true. Ina zama ya sake tambayata "are u really Ok? You look pale and not as bright as the moon you are. Make sure you go to the clinic during your break " na amsa da yes sir. Da yake shi mutum ne mai barkwanci sai ya zamana kafin a fita break har na manta da duk wani abu da ya faru tsakanina da Ibrahim.

Har muka tashi ban kuma tunawa da maganar ba, sai da nazo ina hada books dina zamu tafi hostel sannan naga jotter dina da rubutun sa a front page, nayi saurin sakata a locker dina na rufe na jefa keys din a bag dina. Su Hafsat already dama suna jirana mu tafi. Tunda muka bar class Hafsat take min balbalin fada wai saina gaya mata me ya faru a class, nace mata i don't know amma taki rabuwa dani. Har muka chi abinci, mukayi sallah, nayi wanka na shirya zan fita library ta sha gabana tace babu inda zanje sai na tsaya nayi mata bayani. Ita Hafsat bata san cewa nafi ta son sanin mai ya faru din ba. Kuma duk tambayoyin ta bani da amsa din su sam sam. Nan dai na koma na zauna nayi folding hannaye na a cinyata nace mata " what do you want to know ?" Tace "menene tsakaninki da thin tall man?" nace "nothing more than what is between you and him" " amma menene yasa dazu yake kallonki har ina tayi masa magana bai ji ba? Kuma ya akayi yasan sunan ki bayan bai tambayemu sunayen mu ba? "OK nace mata ina daga mata hannu alamar ya isa haka, sannan na bata labarin encounter din mu a library, na kara da cewa "ina tunanin anan yasan sunana, apart from that, babu wani abu a tsakanin mu." Tayi frowning face dinta alamar tunani sannan ta girgiza kanta tace " OK na yarda dake, for now, i just don't want him looking at you like that" nayi murmushi na ce "my dear sister, ke fa kika taba cemin i can do what ever i want, babu uwanki" ta mike tsaye tana kallona tace " i am your sister, and i don't want any relationship between you and him" ta fada with finality.

A ranar da magrib muna zaune a daki na saka Hafsat a gaba da tsokana akan wani neighbor din yazo takanas saboda ya ga Hafsat amma tace ace masa ba zata zo ba. Ina ta tsokanarta tayi min banza sai ga Amira tazo, anan take sanar damu cewa senior master yayi approving night islamic class din mu, zamu fara yau da daddare dan haka mu shirya. Za'a keyi bayan sallar isha'i zuwa 9pm. Sannan ta kalleni da tsokana tace "saura ki sake tsuye mana malami" nayi dariya nace "not a chance, we have made our peace, yanzu ma a matsayin friends muke" Amira tace "so i noticed, friendship dinne ya kawo kallon dazu ko?" Na bata raina nace "don't start there, kema kinsan in da akwai wani abu you will be the first to know " tace "to Allah yasa, Just be careful my dear friend"
Amira ta bawa Hafsat shekara daya, ni kuma ta bani biyu. Kuma duk ta fimu hankali da nutsuwa. Tun ganin ta na farko da mommy tayi, tayi approving friendship din mu har ya zamanto ita da maman Amira sun fara kawance. Amira black beauty ce, bahaushiya ce usul, gentle ce kuma komai nata tanayinsa a tsare.
Alokacin da mukaje islamiyya ne nasha mamakin jin irin karatun Ibrahim. Ban taba jin kira'ar da ta yimin dadi irin tasa ba. Cikin sassanyar muryarsa yake kwararo mana karatu wanda nake jin shigarsa tun daga kunnuwana har 'yan yatsun kafata, naso ace ya cigaba da karatun forever. Yana zuwa inda yake son tsayawa sai ya tsaya. Inajin wata a class din tana furta "masha Allah". Nima masha Allah din na furta amma a zuciya ta, saboda wannan ba karamar baiwa bace ba daga Allah. Muka biya tare dashi sannan muka fara biya wa kow individually. Ga mamakina da akazo kaina bai nuna wani cewa ya sanni ba koya kira sunana ba. Da aka tashi shi ya fara fita sannan muka hada littattafan mu muka fito. Ni na fara fita a students saboda baccin da nake ji, na saba da baccin wuri. Ina tsaye a bakin kofa ina jiran su Hafsat ina ta faman zabga hamma naji scent din sa a gurin, na juyo amma banga kowa ba duk da jikina ya bani ana kallona. Gyaran murya naji yayi, nayi sauri na kalli side din da sound din ya fito anan naga silhouette n sa a jikin katanga. Gurin da duhu bana ganin fuskarsa amma na gane shine, ya rungume hannayensa a kirjinsa. Na juya kamar zan koma ajin sai yace "are you afraid of me? Do u think i might steal you? " Na juyo ina kallon gurin da yake amma ban ce komai ba har ya sake cewa " i just want to say good night to you. I will see you tomorrow morning " ya juya da niyyar tafiya, nayi sauri nace "Why? " ya dakata da tafiyar da yake yi ya juyo yana kallona, har yanzu amma yana cikin duhun bai fito cikin haske ba. Yace "why what? " "why do u feel the need to stay in the shadows, get me alone and say goodnight to me?" Nayi maganar da dan karfi fiye da yadda nayi niyya. A hankali yace min "your friend is here " nayi sauri na juya sai naga Amira a tsaye a verandah class din mu tana kallona da mamaki a fuskarta tace "moon ke da wa kike fada cikin daren nan" na juya na kalli inda yake, babu shi babu alamar sa, ya gudu. Idan har da gaske friendship yake nema mai yasa zai tsaya a cikin duhu yayi min magana, ya fito cikin haske mana kowa ya ganshi or better still yayi min magana mana a class a gaban kowa.
Muka kama hanyar hostel raina a bace. This guy is trying to play a game with me and i will teach him a lesson. To add peppe to my wound, muna cikin tafiya mukaji wadansu 'yan ss3 suna hira a gaban mu. Hafsat da son gulma ta rike hannayen mu muke binsu a baya muna jin hirar su. "Gaskiya gayen nan ya hadu" "kema kin gani ashe? Ga kyau ga nutsuwa ga kamala, ga kuma ilmin addini dana boko" "ni muryarsa tafi komai burgeni, kuma daga ganinsa gentleman ne, komai nasa a nutse yake yi" "ke kinga idanunsa kuwa? Wayyo raina. Ai da naje biya karatu wani kallo da yayi min sai naji na manta a wacce surar muke gaba daya" suka kwashe da dariya suka tafa. "To ko dai ya yaba ne? In kuwa hakane mukam sai dai muce sambarka"
I heard enough, na cire hannuna a cikin na Hafsat nakara sauri na wuce su. Ina zuwa daki na cire kayana na shiga wanka. Sai da na fito naga Hafsat ta zage tana bawa su Abigail labarin abinda ya faru suna ta dariya. Wai ashe har plan suka shirya na yadda zasuyi masa magana akan yake yi musu extra lessons ta yadda zasu ja hankalin sa. Ina fitowa Hafsat ta nemi tayi involving dina a conversation din amma naki magana. Nayi adduoi na na kwanta. Bazan iya fasalta me nakeji a raina ba danni kaina bansan menene ba.
Washegari Thursday sam bamu hadu da Ibrahim ba tunda bamu da class dashi kuma ranar babu islamiyya. Ranar Friday na ganshi a assembly hall amma ban yarda mun hada ido ba. Ya saka complete NYSC kakin sa, ina kallonsa naji gabana ya fadi nayi saurin dauke kaina. Ranar ma bamu da class dinsa

Please Login or Register in order to submit comment