Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

fito daga building din yana nemana. Nayi baya na fita daga packing lot din ina ganin sa ta mirror yana kallon motar, yayi noticing sunan da aka rubuta a gurin number "Sultan 2" .
Sai da nayi nisa da building din sannan na sauka daga kan titi nayi packing, na kifa kaina akan steering na kama kuka, what hurt me the most is the fact that Amira can betray me like that. Sometimes, the person you trust the most will hurt you the most.
Masoyan Maimoon ina gaishe ku baki daya, nima kuma ina sonku irin sosai dinnan. Ina ganin sakonnin ku ta WhatsApp da Facebook, masu bina private da masu turo wa ta group. Ina so ku fahimci abu biyu. Na farko Moon guda daya ce ba za'a raba ta a bawa kowa ba, dan haka dole wani ya samu kuma dole wani ya rasa. Dan haka at the end dole wani zai ga kamar ba'a kyauta masa ba. Abu na biyu kuma shine, tun kafin in fara rubuta labarin Maimoon na riga na tsara yadda zai kasance, yanzu kawai details din nake filling, kada wani yaga kamar labarin ina rubuta shine yadda zan farantawa wani. Idan kuka cigaba da bin Maimoon na tabbatar muku karshrn labarin zaiyi satisfying kowa insha Allah. Duk da dai ance shi dan adam ba'a iya masa.
I so much love you all



Episode Sixty Four : The Past and the Future

Na jima a haka ina kuka mai tsuma zuciya, jikina har rawa yake yi. Why is my life almost so complicated, me yasa komai ni baya zuwa min da sauki. I hate hurting Ibrahim. Ya sha wahala sosai akan soyayyata, he deserves happiness from me now, but I can't give it to him because it is not mine, it belongs to somebody else. Ina jin wayata tana ta ringing, kira na wajan goma kenan, amma ba zan iya dauka ba saboda ba zan iya magana ba. Da zuciya ta da kaina gabaki daya sun toshe kaina sam babu wani abinda yake fahimta, abinda nake tunawa shine naga Ibrahim, kuma soyayyata da na gani a idonsa ta ninka wacce na san yana yi mini a da kafin mu rabu. A hankali na fara abinda na saba yi indai ina so in saisaita tunani na, na fara kiran sunayen Allah daya bayan daya idona a runtse, a hankali nutsuwa ta fara shigomin kuka na ya fara tsayawa. Na bude ido na ina kallon titi, gari ya fara duhu dan tini anyi sallar magrib. Na fara tunani straight. So Ibrahim did came back like he promised he would. Saura kwana goma bikina, bikina da Sultan. Ibrahim har yanzu yana so na, yana sona fiye da yadda ya soni a baya. But ya dawo rayuwata a little bit too late. My heart already belongs to another. I loved him before. Nayi masa son da a lokacin nake tunanin ba zan taba yiwa wani irin sa ba. But it is all gone now. Sultan ya cike dukkanin guraben da suke a zuciyata. Ibrahim Yace Allah ya hada mu ne a yau saboda we have a future together, in haka be kuwa to ba zabi na bane kenan. Even if da akwai sauran son Ibrahim a raina to yana can kasan zuciya ta wanda tono shi sai an dauki lokaci, and time is what we don't have. Even if an tono soyayyar Ibrahim a raina ta yaya zan iya facing iyayena ince musu na fasa auren Sultan wani kuma daban nake so? Komai sanyin Daddy na tabbatar sai naga bacin ransa ballantana Mommy da inajin sai ta kaini psychiatric hospital. I can't even imaging tunkarar Sultan da maganar wai na fasa aurensa saboda wani tsohon saurayina da muka rabu kusan seven years back. Duk wanda yaje ya gaya wa sultan wannan maganar will be committing suicide. I can't even imaging my life without Sultan. Choosing Sultan over Ibrahim is not a choice, it is a necessity. Kamar yadda Ibrahim ya fada hakane, God have reasons for everything He did. Tunda Allah ya hada mu yau to da akwai wani abu daya boye a cikin haduwar tamu, ko da kuwa ba aure bane. I just hope that whatever God has planned for us zai kawo happiness a rayuwar Ibrahim sannan kuma ba zai wargaza rayuwar ta da Sultan ba.

Waya ta ta cigaba da ringing, na dauka ina kallon sunan sultan har ta katse, a cikin dictionary din sultan babu wata kalma wai ita giving up, he never gave up, yanzu kiran nan da ya ke yi min zai yi ta yi ne har sai na dauka ko kuma sai charging wayar ya kare. Na duba missed calls naga 23, amma 5 daga Mommy ne, sauran kuma nashi. Na fara tunanin abinda zance musu tunda duk cikin su babu wanda zan iya gayawa gaskiyar abinda ya faru yau. Mommy na fara kira, bugu daya ta dauka tace "ina kika shiga? Sai da nace muku fa kar ku kai magrib gashi har after seven baki dawo gida ba?" A nutse nace "Mommy mun dan samu matsala ne shagon, Amira ce suka dan samu sabani da wata cashier shine abin yayi delaying din mu, kuma nabar wayata a mota shi yasa ban san kuna ta kira na haka ba" ta dan rage fadan da take yi tace "to amma ai da ko wayar ita Amiran sai ki karba ki kira ki fada mana halin da kuke ciki, ni ba sai inzo da kaina ko in turo wani yaji matsalar da aka samu ba? Na kira wancan yaron ma yace shima yana ta kiranki baki dauka ba, duk kin tayar mana da hankali wallahi" na danyi murmushi a raina nace 'I love you too Mommy' nace "gani nan zuwa yanzu, zan kai Amira gida ne kawai in taho" da sauri tace "NO, duhu yayi kuma unguwar su Amira akwai nisa. Ku tsaya a inda kuke ki kira shi sai ya kai ki ya dawo dake gida" nace "yes mother" na kashe. Ina kashewa kiran Sultan yana shigowa, sai da nayi bismillah sannan na dauka, ina dauka yace "damn it, where have you been?" Cikin sanyin murya nace "am sorry Sultan, na manta waya ta ne a cikin mota, muna cikin wani supermarket ne kuma muka samu wata 'yar matsala, duk everything is Ok yanzu na kai Amira gida zan taho gida nima" kamar sun hada baki da Mommy yace "no, ki zauna bara inzo in dauko ki, dare yayi kuma hannunki bai yi kwari ba" nace "yes sir" ya sauke ajjiyar zuciyar da har sai da naji ta ta cikin wayar yace "you almost gave me a heart attack. Gaba na yana ta faduwa, kuma ina ta kiran wayarki tana ta ringing baki dauka ba. Please don't ever do this again in ba so kike zuciya ta ta buga in mutu ba" kalmar mutun da ya fada ce ta saka ni nayi murmushi nace "kar ka zama ragon maza mana, ko three hours fa ba muyi da waya ba" yace "anything can happen ai a cikin three hours din, kin san babu abinda ban aiyana a raina ba? Har sai da na hango ki a kasan tirela" nayi dariya, yanzu shikenan date din na mu ya wargaje? Har nayi musu waya nace suyi mana reserving table " nace "am sorry, in sha Allahu I will make it up to you. Yanzu Mommy tana can tana jirana in muka tafi fada zata yi. Insha Allahu zan lallabata ta sake bari na fita sai muje" ya shagwabe murya yace "baki ga kwalliyar da nayi miki ba fa" nayi murmushi nace "really?, show me, I want to see" yace "how?" Nace "kayi snapping picture ka turo min yanzu" yayi dariya yace "no, it is kind of special, in kina so ki gani sai dai kisan yadda zaki samar mana fita da wuri. Yanzu cirewa zanyi ma in boye" mukayi sallama yace gashi nan tahowa. Na tayar da mota, I have one stop to make, gidan su Amira. A hankali nake tuki sabida hasken fitulu da yake kashe min ido, addu'ah ta Allah ya kaini lafiya kuma Allah yasa kada Sultan ya riga ni zuwa. Cikin sa'a naje na tarar bai zo ba. Na debi kayan ta data siya ta bari a motar na shiga. Mama ce kadai a palo tana cin abinci, na gaishe ta ta amsa cikin kulawa tace "ya akayi kika zo da daddaren nan bayan dazu ta dawo daga gurinki itama?" Nace "wani sako na manta bance ta taho min dashi ba, kuma gobe zan yi amfani dashi" tace "da fatan dai ba ke kadai kika taho ba" nace "a'a kawo ni akayi" tace "kin ga yanzu tsayawarki ta shiga daki amma tunda ta dawo tana kwance a palon nan, tace bata jin dadine, ki shiga tana ciki" na mike na shiga dakin. Ina bude kofa ita kuma tana shigewa toilet. Na rufe kofar na karasa bakin toilet din na zauna a kasa. A hankali na fara magana "why? Me yasa kika yi min haka? Me tasa kika kasance me son kanki da yawa? Me nayi miki da nayi deserving wannan cin amanar daga gareki?" Shiru babu amsa. Na cigaba "ban taba koda jin labarin mutum marar imani marar tausayi irin ki ba. Nayi miki soyayya ta hakika amma ke ashe duk duniya babu wanda kika tsana irina. Amira babu abinda baki sani ba na wahalar da nasha akan soyayyar Ibrahim amma ashe ko sau daya baki taba tausaya min ba, maybe ma dariya kike min a bayan idona, Amira kina kallona a kan gadon asibiti amma ashe kina da maganin ciwo na kika boye kika hanani. To ki sani, ni babu abinda zan yi miki, na barki da Allah, kuma na tabbata Allah sai ya sakamin cin amana ta da kika yi. Kuma ki sani, kanki kika yiwa. Shi wanda kike claiming kina so shi yafi kowa wahala a cikin duk abinda ya faru, shine kuma still har yanzu a cikin wahalar bani ba. Kuma ki sani, duk da Allah ya kaddaro babu aure a tsakanina da Ibrahim to kema ba zaki same shi ba, saboda Ibrahim baya sonki kuma bai taba sonki ba, kuma ba zai taba sonki ba, especially yanzu daya gano gaskiyar makircin ki, he hates you and I hate you also. Kuma ina gargadinki da kiyi hankali da dosar inda yake saboda yace in dai ya ganki sai na lahira ya fiki jin dadi. Ina fatan zaki halarci bikina nan da kwana goma, ina so kizo saboda ki gani da idonki irin farin cikin da zan kasance a ciki, ina so ki gani da idonki irin sakayyar da Allah yayi min tun a duniya kafin muje can. Ga kayanki nan da kika bari a motar mijina" na mike tsaye, ina jiyo sheshshekar kukanta a cikin toilet na fice, nayi sallama da maman su na fita. Ina fita ana sauke Sultan a taxi. Da sauri ya fito yana bani hakurin ya dade, ya karbi key muka tafi. Muna daukan hanya, ga mamaki na sai naji yace "what's wrong?" Nace masa "me ka gani?" Yace "you look and sound different, kamar akwai wani abu a ranki" na tattaro dukkan charms dina nace "Hey, I am suppose to be the psychologist ba kai ba" yayi murmushi yace "kin san ance zama da madaukin kanwa" nace "to babu abinda yake damuna, kawai dai na gaji ne, kwana biyu bana fita kuma yau mun dan yi yawo, gashi ni nake driving" yace "sorry, kuma gaki dama da son jiki ko? Wannan duk sanda aka fara bikin nan bansan ya zaki ke yi ba" nayi dariya nace "ai wadansu events din skipping zan ringa yi, na gaya muku bana son big wedding kun dage sai anyi" yace "karki damu after the wedding zaki huta sosai, I will be there to help you rest" na harareshi duk da babi haske, dariyar mugunta yake min ban ce masa komai ba, yace "ya kika yi shiru?" Nace "oho maka, kai ka sani" Muna zuwa gida yace wai shi lallai sai dai mu zauna a mota muyi ta hira ba zan shiga gida ba, ni kuwa nasan dan dai gidan da akwai baki ne yasa har yanzu Mommy bata kuma kirana ba amma tana sane da cewa ban dawo ba. Da kyar na samu da lallabashi na gudu. Ina shiga bayan na gaishe da Mommy na tafi dakin Hafsat, kawai so nake in samu in gaya wa wani abin da yake raina ko na dan ji sanyi.

Ina shiga na tarar tana lallaba little khairat, tayi min alama da inyi shiru, na rufe kofar na jingina da jikin kofar ina kallon su, sai da ta kwantar da ita sannan ta juyo tana kallona da murmushi tace "rigimammiya, wai ita lallai a jikina zata yi bacci ba zata kwanta ba" sai kuma ta kura min ido tace "lafiya na ganki kamar wacce aka koro?" Direct nace mata "I saw Ibrahim today" ta dan tsorata da maganar sai kuma tayi sauri tayi getting composure dinta tace "what? A ina? I really hope baki kula shi ba ko baki tsaya kin saurare shi ba" na karaso dakin na zauna a bakin gado ina kallon fuskar khairat da take ta baccin ta peacefully, nace "na tsaya na saurare shi, ba dan komai ba sai don ina son inji dalilin da yasa yayi abinda yayi" Hafsat ta watso min kallon tuhuma tace "and? I really don't like inda maganar ki take dosa Moon" nayi murmushi nace "inda kike tunani ba nan na dosa ba, I am not going back to Ibrahim, but he will always have a special place in my heart" daga nan na bata labarin duk abinda ya faru tsakanina da Ibrahim da Amira, bata ce komai ba har na kammala, ina gamawa naga ta mike ta na kokarin saka hijab, nace "ina zaki je?" Tace "I am going to kill that conniving bitch" nayi murmushi nace "shi yace zai kasheta ke kince zaki kasheta, a cikin ku bansan waye zai yi nasara ba amma nasan cewa koma me zakuyi mata ta riga ta aikata abinda ta aikata, kuma duk hukuncin da zaku dauka akanta ba zai dawo mana da hannun agogo baya ba, the past doesn't matter, what matters is the future. Ibrahim is my past, I have a great future to look forward to, I have Sultan" Hafsat ta yarda hijab din hannunta tazo ta rungume ni, I needed the hug, nima na rungume ta inajin zuciya ta tana sanyi a hankali. Mun jima a haka sannan ta sake ni tace "now, what are you going to do?" Nace mata "I don't know. Abinda na sani shine Ibrahim yana son in dakatar da bikina in bashi chance, which I told him I can't. Ya sha wahala akaina sosai kuma har yanzu yana sona, bana son inyi abinda zai kara masa bacin rai fiye da wanda yake ciki yanzu, kuma ni ba zan iya abinda yake so in yi ba. I don't know what to do. Na tabbatar kuma tunda har yanzu yasan bani da aure to zai zo gidan nan, it is a wonder ma da bai zo ba already, ina tsoron haduwar su da Sultan, Sultan is as unstable as a person can be, kuma bai san da labarin Ibrahim ba" Hafsat ta saki baki da mamaki tace "kina nufin baki gaya wa Sultan labarin Ibrahim ba?" Na daga kafada nace "ban taba tsammanin zan kuma haduwa da Ibrahim ba, so I thought there is no need in gaya masa, there is no point in tone tonen abinda yake a binne" ta kalleni da mamaki tace "Moon when will you stop keeping secrets? Duk abinda ya faru bakiyi learning lessons dinki ba. Kin boye wa iyayen mu Ibrahim, kin boye wa Ibrahim gaskiyar su waye iyayen mu, wannan shine asalin dalilin rabuwar ku da Ibrahim. Ki kazo kika boyewa iyayen mu Sultan sannan kika boyewa sultan zancen project dinki, akazo ba'a kare ta dadi ba. Yanzu kuma you are keeping Ibrahim a secret from Sultan? Again?" Nayi shiru ina jinjina maganarta a raina, she is right, nace "I guess it has all being my fault, it is because i have always been afraid of loosing those I love" tace "gaya wa Sultan labarim Ibrahim ba zai saka Sultan ya rabu dake ba. Kin gaya masa sai yafi bata masa rai akan gaya masa" nace "amma ba kya ganin yanzu it is late? In na gaya masa zai ga kamar dan mun hadu da Ibrahim dinne , ya dauka kamar dan ina son komawa gurin Ibrahim ne ko wani abu. Baki san halin Sultan ba, he is unpredictable, kullum gani yake kamar zan iya cewa na fasa aurensa, ko ya ya samu wani hint na wani abu ban san me zai aikata ba" Hafsat ta sake shiru sannan tace "what do you want to do?" Nace "so nake inyi iya kacin kokarina inga Sultan basu hadu da Ibrahim ba har bayan daurin aure, sannan sai in gaya masa, at least by then ya san dai na zama tasa already. Shi kuma Ibrahim ina so ya fahimceni ba tare da bacin rai ba"



Episode Sixty Four : The Visitors

Ina mika ta'aziyya a madadi na da sauran fans din Maimoon zuwa ga 'yar'uwar mu Nafisa Saleh, admin ta WhatsApp group din mu na mata, a bisa rashin yayanta da tayi sanadiyyar hatsarin mota, Allah yaji kansa ya gafartamasa, Allah ya yafeasa zunuban sa da namu baki daya. Allahumma Ameen.

Nine Days to the D-Day
Ban tashi da wuri ba saboda ban samu isheshshen bacci ba, kuma na tashi da ciwon kai. Amina da sauran cousins din mu na 'yalleman ne suka takura min da sututu a dakina dan haka na fito kan balcony na rufe kofar daga waje na zauna akan kujera ina jin dadin fresh air din gurin. Na jawo waya na kira Sultan, yana dagawa nace "hey busy body, ya kamata ka dauki leave ka samu ka huta, kar azo ana taro ka fadi ka hada mu da aikin dauko ka" yayi dariya yace "sai kace ke? An gaya miki kowa ma rago ne irin ki?" Nace "am serious, ya kamata ka huta" yace "alright amarya, yadda duk kika ce haka za'ayi. Besides, I need my energy for what is about to come" nayi kaman ban gane inda maganar sa ta dosa ba, nace "ina Amir?" Yace "baki bani amsa ta ba ai" nace "baka da amsa. Ina Amir?" Yace "OK, one day zaki buda baki sosai ki bani amsa. Amir ya dan fita, kina neman sa ne?" Nace "No, ka gaya masa kawai Amira bata jin dadi, so ya nemi Amina su cigaba da shirye shiryen da ita" ya dan yi shiru sannan yace "me ya sameta? I thought you guys were together jiya" nace "tun jiyan dama bata jin dadi, yau ta kira ni tace ba zata samu zuwa ba" muka yi sallama na kashe wayar, I feel bad duk sanda nayi wa Sultan karya, saboda shi baya min, baya taba boye min wani abu daya shafe shi. Amma ina jin tsoron gaya masa labarin Ibrahim. A ranar da yamma mai mun gyaran jiki ta zo mukayi, bayan mun gama tace min baza ta kuma dawowa ba sai ranar Saturday, wanda ita ce ranar daurin aure da kai amarya. Ta saka a ka fito mata da duk kayana da daddy ya dinka min wanda zan tafi dasu gidan sultan, dan babu abinda aka taba a lefe na duk already an kai su can ance in naje na dinka a can. Wani katon kasko ta hada turaren wuta take turare kayan nawa dashi, tace duk wankin da zan yi musu kamshin ba zai fita ba, ita shine nata gudunmawar bikin. Nayi mata godiya sosai. Ranar Tuesday za'a fara bikin, za'a fara ne da kunshi sannan da daddare a yi bridal shower, Wednesday za'a kamu da walima, Tuesday mother's eve da dinner, friday luncheon da daddary su sultan suyi bachelor's night dinsu, Saturday 12 na rana za'a daura aure da la'asar akai amarya, da daddare kuma za'ayi bridal welcome party wanda Amir ya shirya mana. Shikenan.

Eight Days to....
Gidan kam a cike yake yanzu da mutane, daga maza har mata, munir bai zo ba kuma naji dadi, dan bana son yazo ya kara min wani tension din. Mamansa dai da sisters dinsa sunzo, suna zuwa suka ishe ni da iyayin suna so suga angon, nasan abinda suke nufi, so suke suga waye ya kasa yayansu, babu bata lokaci kuwa na hada su dashi, tunda suka ganshi suka yi kus, babu wacce ta sake magana a cikin su.

Da yamma na fita balcony, nan ne gurin zama na yanzu indai ina son in jini ni kadai ko in ina son muyi waya da sultan. Na dafa railer na dauko wayata ina kokarin kiran sultan kawai ina daga ido na na hango shi, duk da cewa da akwai distance a tsakanin mu kuma gari ya fara duhu amma na gane shi, yayi packing dan nesa da gidan mu kadan yana tsaye ya jingina da jikin mota ya rungume hannayensa a kirjinsa. Wata irin muguwar faduwa gaba na yayi, Allah kenan, babu yadda baya juya lamarin sa, da akwai lokacin da kullum nake tsayawa a balcony din nan ina kallon waje hoping zan ganshi amma yau gashi ina kallonsa amma maimakon inji dadi sai faduwar gaba da ji. Allah ne kadai yasan dadewarsa a gurin, Allah ne kuma kadai yasan dawa yayi magana. Nasan Sultan dai bai dawo gida ba, baya zuwa yanzu sai dare yayi sosai saboda mutane. Kamar ance ya dago ido sai ga idonsa a cikin nawa, da sauri yayi kamar me shirin tahowa ni kuma nayi sauri naja da baya yanda zai daina ganina. Saboda faduwar gaba har daci nake ji a bakina, na shiga uku, na leka a hankali naga har yanzu balcony din yake kallo. Na koma daki da sauri na shiga toilet, sai da nayi calming down sannan na kira sultan. Yace "Hello love" nace "hey kana ina ne?" Yace "naje karbo mana sauran dinkunan mune. What's up?" Nace "babu komai. Kawai da ina so inji ya kake ne" yayi dariya yace "thanks love, ko in taho ne?" Nace "I would appreciate that amma kasan gidan yanda yake yanzu, ballantana yanzu da yamma" yace "right, nima daga nan zanje wajan Daniel ne yazo gari, so sai dare zan shigo gidan, hope ba za kiyi bacci ba kafin inzo" nace "yeah, bazan yi ba sai kazo, bye" muna gama wayar na koma na leka balcony naga har yanzu Ibrahim yana tsaye. Da sauri na sauka kasa dakin Hafsat na same tana shirya kayan khairat, tace "lafiya? Waye ya koro ki?" Nace "Hafsat Ibrahim ne yazo yana waje" tace "and? Kina nufin fita zakiyi gurin sa?" Nace "no, ke nake so kije" ta yatsina fuska tace "ni? Allah ya tsari gatari da saran shuka" nace "Dan Allah Hafsat kije kiyi masa magana, make him understand abinda yake so ba zai yiwu ba" tace "in baki shawara? Ki kira David ki hada shi da shi, nayi miki alkawarin ba zaki kara ganin sa ba" na girgiza kai da sauri, Hafsat ba zata fahimci abinda nake nufi ba, babu wanda zai fahimci situation dina sai wanda ya taba shiga irinsa. Ma zauna a bakin gadon ta nace "I don't want to hurt him, I don't want to hurt Sultan. Please help me" ta dan jima tana kallona sai kuma ta dauki hijab ta saka tace "amma kin san dama can ni ba shiri muke yi da shi ba, dan haka ba lallai ne yanzu ma mu fahimci juna ba" tana fita na koma sama da sauri na kuma shiga balcony, ya baro jikin motar ya dawo dai dai opposite din gidan mu, ina kallon Hafsat ta bude gate ta fita. Yana ganin ta yayi saurin karaso wa wajanta, bana hango su sosai yanzu, sun jima suna magana sannan daga baya naga ya juya ya tafi wajan motarsa, kafin ya bude motar ya sake juyowa ya kallo balcony din sannan ya shiga ya tafi. Na dawo

Please Login or Register in order to submit comment