Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yake zuwa mind dina shine illiterate mutanen daji masu kiwon shanu" dariya mukayi gaba ki dayan mu sannan nace masa "duk family na babu masu kiwon shanu" muka sake yin dariya sannan yace "now we all know better "

Muna haka alarm yayi beefing a wayarsa, ya duba yace "time for asr prayer" Muka mike a tare muka yi shirin alwala. Bayan munyi sallah a masallaci na riga shi dawowa inda muke zaune, na bude textbook din maths a cikin littattafan da ya dora akan table din na fara karantawa, sai gashi yazo sai ya dauko notebook dinsa ya nuna min note din da yayi forming na abinda zamuyi this week a maths. Nan muka zauna yana ta koya min har magrib sannan mukayi sallah na tafi hostel shi kuma ya tafi staff quaters. Ina shiga hostel dakin su amira na tafi muka zauna tare har lokacin islamiyya yayi, muna ta hira da ita amma ga mamaki na bata tambayeni game da Ibrahim ba, har sai da muka zo tafiya islamiyya sannan nace mata "Amira baki tambayeni yadda muka yi da Thin Tall Man ba? " sai ta ce "nasan ai zaki bani labari ne when you are good and rready" naji dadi har cikin raina. Amira is such a good friend to me, bata damu da sai na gaya mata komai ba, kuma duk sanda nake bukatar shawara she ia there for me. A islamiyya muka hadu da Hafsat amma ko kallo na bata yi ba. Ibrahim ma bai yi min magana ba sai dai duk sanda muka hada ido sai yayi min murmushi kuma nima haka kawai sai na sami kaina da mayar masa.

Da muka tashi nima banbi takan Hafsat ba nayi tafiyata daki nayi wanka na kwanta. Ina jinta ta shigo tana shirin kwanciya su naomi suna yi mata magana tayi banza ta rabu dasu. Ni dai ina kwance amma na kasa bacci ina ta lissafin abubuwan da suka faru a ranar. Alaka ta da Ibrahim tana neman kawo matsala tsakani na da Hafsa kuma bana jin dadin hakan saboda no matter what, blood is thicker than water. Duk duniya bayan iyayena bani da sama da Hafsat. Amma Hafsat tana da matsala, idan na bata dama zata ce zata ke controlling dina ne akan komai, bawai akan Ibrahim kadai ba. Dan haka na yanke shawarar ko menene zai faru bazan bata damar controlling dina ba. A bangaren Ibrahim kuma though yayi admitting cewa he has feelings for me, amma baiyi magana akan soyayyaba dan haka na yanke shawarar zan ci gaba da kulashi kamar yadda ya bukata amma da zarar naga yana kokarin wuce gona da iri zan taka masa burki, and so help me God. A dan fahimtar da nayi masa na fahimci cewa shi mutun ne mai ilimi, dan haka nayi alkawarin zan mori ilmin sa, zan ke koyan karatu a gurin sa, in that way duk kanin mu zamu ke gaining kuma relationship din mu ba zai zama suspicious a makarantar ba. Da wadannan shawarwarin bacci ya dauke ni.


Episode Fourteen : The Limit

Washegari tun kafin assuba na tashi nayi wanka na saka uniform dina, assuba tana yi na tafi masallachi nayi sallah daga nan na wuce islamiyya. Nayi haka ne saboda bana son muyi rigima da Hafsat. Har muka fara karatu Hafsat bata zo ba. Amira ta tambayeni ina Hafsat na daga mata kafada alamar I don't know, har aka tashi daga islamiyya babu Hafsat babu labarinta, sai na ringa jin babu dadi a raina, what if she is sick? Na taho na barta. Ana tashi na kira Amira nace mata please tayi checking on Hafsat, ni class zan wuce bana son komawa hostel, tace min ba problem. Ina yin breakfast na wuce class na zauna ina karatu na har aka fara zuwa class. Karatu nake amma duk hankali na yana kan masu shigowa ina jiran inga shigowarta. Can sai gata ta shigo fuskarnan babu alamar fara'a, tana zama na mike na tafi wajenta nace "Hafsat lafiyar ki kuwa yau ban ganki a islamiyya ba?" Tayi min kallon sama da kasa tace "what is it with you idan banje islamiyya ba? Ko zaki saka shi yayi min bulalar fashi ne?" Nayi murmushi nace "that settled it, dama ina ao insan lafiyar ki, na fahimci kuma lafiyar ki kalau" na koma nayi zama na. Ina zama sai ta mike ta kama jan seat dinta sai da ta kai shi can row din baya sannan tayi zamanta.

Sam bana jin dadin abubuwan da Hafsat take yi amma kuma bana son in bata chance din da zata ke controlling rayuwata. Farko Ibrahim ya fara kulata yana tsokanar ta da big sister amma sai ya lura cewa bata so dan haka ya rabu da ita. Rannan muna karatu ya tambayeni "how is your sister" nayi mamakin tambayar amma na maze nace "she is fine" he snickered kafin yace "she hates me" na ajiye rubutun da nake yi nace "no, she does not hate you, she has always been like that dama, believe me, sometimes I feel like she hates me too" daga nan bai sake yi min maganar Hafsat ba.

Bayan munyi wata daya da fara term din su mommy suka zo mana visiting. Tun da aka kira mu gaba na yake faduwa dan bansan me Hafsat zata kulla min a gurin mommy ba. Muna tafiya zamu je gurinsu na matsa kusa da Hafsat nace mata "what are you planning to tell mommy? " ta kalleni da murmushin mugunta tace " that's my business, me kike ci na baka na zuba? " na hadiye yawun tsoro cikina ya kulle kamar zanyi zawo a wando amma na daure na cigaba da binta a baya kamar munafuka. Muna zuwa visitors room sai muka tarar da daada da faruk, nan da nan na manta da damuwar da nake ciki na fada kan cinyar daada ina murnar ganinta, Hafsat ma tazo ta rungume ta muna ta dariya daada tace da yaren buzanci "kai ni karku ji min ciwo, ku baku san kun zama 'yan mata bane" nace mata "haba daada, ina abin yake? Sai dai ki gaya wa Hafsat bani ba" Hafsat kuma tace "ai komai girman da zanyi bazan daina hawa cinyar kiba daada" muka sake yin dariya. Faruk yana zaune yana kallon mu nace "autan mommy ko magana babu?" Yace "au kuna gani na? Na dauka ai ni invisible ne tunda babu wacce ta kula ni a cikin ku" nan kuma muka tafi da gudu a tare muka rungume shi yana turemu wai yayi fushi. Hafsat ce tace daada wai ina mommy n ne? Daada tace "muna zuwa principal dinku ta kira ta" nan take wani gumi ya karyo min, tunda muka shigo ban ga mommy ba na dauka bata samu damar zuwa ba har hamkali na ya kwanta. Nayi saroro har wani daci nake ji a baki na. Hafsat ta dafa ni tace "yayane moon? Ko bakya murnar ganin mommy ne? " na ture hannunta na koma kusa da daada ina tambayar ta su ya Habeeb. Muna cikin haka sai ga messenger daga principal's office wai ana kiran mu nida Hafsat. Muka tashi muka tafi, nice a gaba Hafsat tana bina. Ina tura kofar office din naga mommy a zaune a kujerar gaban table din pc daga can gefe kuma Ibrahim ne a zaune yayi folding arms dinsa yana kallon mommy. Sandarewa nayi a gurin na kasa motsi, komai nawa ya tsaya hatta bugun zuciya ta. Hafsat naji tana fadin in matsa in bata guri ta shigo tunda ni bazan shiga ba. Sai a sannan lumfashi na ya dawo si kuma zuciyata ta fara bugawa da karfi, dacin da nake ji a baki na ya karu, Hafsat ta karewa office din kallo sannan tazo dai dai kunnena tace min "whatever goes up must come down" tana yi min murmushin mugunta ta shige ciki da sallam. Ba yadda zanyi dole na bita a baya. Ga mamaki na sai naga mommy ta juyo da fara'a sosai a fuskar ta ta mike tsaye ta buda hannayenta tare da cewa "come here my darlings" ban san sanda na manta da komai ba na fada jikin mommy ina murna. Ta rungume mu sosai a jikinta na wani lokaci sannan ta sake mu, muka gaisheta, muka gaida pc sannan na juya na gaida Ibrahim. Hafsat ko kallon inda yake bata yi ba mommy kuma bata lura ba dan suna magana da pc a lokacin. Sun jima suna magana amma ni hankali na ya tafi akan tunanin dalilin wannan kiran da akayi mana kuma gashi an kira Ibrahim shima, lokaci lokaci inna daga ido na sai mu hada ido da Ibrahim sai ya sakar min murmushi amma ni kam ranar bani da damar mayar masa dan gaba daya hankali na a tashe yake.

Sai da suka gama hirar su sannan mommy tace " I am very proud of you Moon. Tun ina gida aka aika min da report na yadda karatunki yake progressing, naji dadi sosai. PC ta gaya min cewa ashe kun dai daita da sabon copper din da da kike complaining akansa, tace yanzu har extra lessons yake yi miki kuma kina samun cigaba sosai" bani ba hatta Hafsat sakin baki mukayi muna kallon mommy na juya na kalli Ibrahim shima sai naga bakin ya saki yana kallon ta" principal ce tayi dariya tace "au mamaki kukeyi yadda nasan kuna yin extra lessons? This is my school, I know everything going on in it. Ina da security da suke zagayawa koda yaushe, kuma kullum sai sun kawo min report cewa sun ganku kuna karatu a gaban library, sai na fara tambayar teachers din ku akan performance din moon kuma suka tabbatarmin da cewa she is doing much better than before. Dan haka na rubuta report na aika gidan ku" Mommy ta juya tana kallon Ibrahim tace masa " bawan Allah, thank you so much. I really appreciate what you are doing. Kuma ina so in nemi favor a gurin ka akan ka hada da Hafsat please. I know she can be annoying sometimes but please bear with her. Zanyi making arrangements zamuke baka allowance duk wata" Ibrahim ya kalleni, he looks compused. Ya chire glasses dinsa sannan yace "Thank you so much maam for the offer but it is not what you are thinking. Actually I am not giving maimunatu any extra lessons. In fact she teaches me sometimes, kawai muna karatu ne tare. She is very intelligent and always ahead of her class so we are both benefitting. There is no need for any allowance Maam because I am gaining as well. As for Hafsat, it will be my pleasure " ya karasa yana kallon Hafsat da murmushi ita kuma da dauke kanta sai da mommy ta harare ta sannan tace masa " thank you sir". Ya amsa da you are welcome. Mommy ma tayi masa godiya sosai sannan ya fita. Daga nan muma mukayi sallama da pc muka koma gurin su daada Hafsat tana ta zumburar baki reshe ya juye da mujiya. Ita dai bata da wani evidence da zata nuna wa mommy cewa soyayya muke da Ibrahim tunda report ya nuna cewa karatu muke yi. Nan mommy ta saka Hafsat a gaba da fada cewa lallai itama ta ringa fita muna karatun tare da ita, tace min duk sanda bata fita ba in gayawa principal nace mata to, nace mata to sannan na faki idon Hafsat nayi mata gwalo. Bayan su mommy sun tafi muka aika da kayan da suka kawo mana muka koma class.

Luckly muna da period din Ibrahim. Ya shigo muka fara maths to question din da muke yi jiya munyi ta da daddare ni da shi. Muna cikin yi sai muka kakare sai yace min " maimunatu check your jotter and see how we got the answer yesterday " yana fadan haka Hafsat tana daga baya sai ji muka yi taja wani dogon tsaki. Tsit ajin yayi. Ibrahim yayi folding hannunsa a kirjinsa yace " who did that?" Kowa yayi shiru, ni nasan Hafsat ce amma nayi shiru nima. Ya sake cewa "who did that?" Fuskarsa ta nuna tsananin bacin rai wanda ban taba gani a tare da shi ba. Ga mamaki na sai kawai naji Hafsat tace masa"I am" duk ajin aka juya ana kallonta, fuskarta babu alamar tsoro ko fargaba. Kallonsa kawai takeyi ido cikin ido. Yace mata "walk out of my class and never come in in my period " bata ce komai ba babu sorry sir babu komai ta fice" ni kaina abin ya daure min kai, wai Hafsat wacce irin mutum ce ita? Da kansa yazo ya karbi jotter din hannuna muka cigaba da calculation din mu amma ni duk hankali na yana kan Hafsat. Muna nan kawai sai ga senior master nan sun taho tare da Hafsat, ya shigo ya kira Ibrahim suka fita waje. Ni dai gaba na sai faduwa yake yi kamar in bisu inji me suke cewa. Can sai ga su sun shigo har da Hafsat. Ga mamakina sai naji senior master yace mata tayi kneel down a gaban class. Hafsat tayi nan ya fara yi mata fada ta inda yake shiga ba tanan yake fita ba, wai dama staff da yawa suna kawo masa complain akan rashin kunyar Hafsat yana basu hakuri amma yau da kanta taje tayi reporting an kore ta a aji bayan ita tayi masa rashin kunya. Nan yace lallai sai ta bawa Ibrahim hakuri. A ciki ciki ta bashi hakurin yace ta dada da karfi taki. Ya dauko yawarsa ya kira discipline master. Ina jin haka na fara kuka amma Hafsat ko a jikinta. Ibrahim yace its OK shi ba sai ta bashi hakuri ba, amma senior master yace ai badan shiba ne, hakkin makaranta ne ta koya mata tarbiyya. Ni dai na kifa kaina a kan seat dina ina ta kuka na. Ina jinsu suka fara dukanta. Tun tana daurewa har saida ta fara kuka, na manta rabon da inga Hafsat tayi kuka, sannan suka kyaleta, kuma suka cewa da Ibrahim inyaga dama ya barta ta zauna in baiga dama ba kuma ya koreta. Ina jinsa ya tsaya a gabana yana kiran sunana nayi banza na rabu dashi sai ya ajiye min jotter ta ya juya ya fita daga class din, na tashi na tafi gurin Hafsat ina taba ta ta ture ni, nan naga hannunta duk ya farfashe yana jini



Episode fifteen: blood is Thicker than Water.

Da kyar na samu na lallaba hafsat ta koma seat dinta ta zauna. Har aka tashi muka koma Hostel bata yiwa kowa magana ba. Tunda taje hostel ta kwanta take kuka har lokacin islamiyya bata fito daga daki ba, ni kuma ban zauna bata hakuri ba amma sam ranar ban fita gurin Ibrahim ba. Da dare yayi saina samu kaina da kin zuwa islamiyya. Nasan ba Ibrahim ne ya daki Hafsat ba amma still ina ganin duk a sanadin alakata da shi ne komai ya faru.
Sai da na gama shiri zan kwanta sannan nazo kan gadon Hafsat na zauna na fara yi mata magana da harshen fulatanci. "Hafsat nasan yadda kike ji a ranki yanzu, kina jin tamkar duniya duka ta juya miki baya amma ina so ki sani ba haka bane. Ita duniya tana zuwa maka ne a yanda ka dauke ta, inka dauke ta da zafi to babu shakka zata zo maka da zafi. Ina so ki san cewa ni bani da komai a raina a game dake sai alkhairi, bana miki fatan komai sai na alkhairi, ban taba rukon ki a raina ba kuma kema ina rokon yafiyar ki idan na taba yi miki wani abu. Please Hafsat tunda muke ban taba neman alfarma a gurinki ba, dan Allah wata alfarma nake nema as a sister, idan kika yi min wannan nayi alkawarin bazan sake rokon wani abu a gurinki ba, please ina so komai ya wuce dan Allah kiyi abinda mommy tace, kizo muke yin karatu tare da Ibrahim, I assure you you will like him. Please sister just give us a chance" duk maganganun da nake bata cemin komai ba amma ni na tabbatar tana jina. Na tashi naje na kwanta nayi adduoi nayi bacci. Washegari ma duk mu biyun bamu je islamiyya ba, nayi wanka ina saka uniform sai ga Hafsat ta fito daga wanka ta bude fridge ta dauko fresh milk tana sha sai ta miko min tace "do you want some?" Nayi murmushi na karba nace mata "thank you" daga nan muka shirya muka fita class tare. Tun daga lokacin muka daidaita da Hafsat, muka koma yin alamuran mu kamar da. Hafsat ta fara zuwa gurin karatun mu da Ibrahim sai dai ba kullum ba, in taje su kan danyi magana kadan ba sosai ba.
Shakuwa ce sosai take shiga tsakanina da Ibrahim. Kullum muna tare tun daga 3pm har magrib. Kofar library ya zama permanent gurin zaman mu. Abin mamaki shine, kusan duk interest din mu daya; a duk subject nafi son maths shima haka, sport din da nake yi shi ne basketball kawai ranar sport shima sai na ganshi a gurin basketball, duk kanin mu muna da fara'a da surutu kuma bamu da fada. Kullum in aka tashi daga class Ibrahim sai ya rakani har bakin hostel, haka zalika in aka tashi daga islamiyya ta dare ko ta assuba sai ya rakoni har sai na shiga hostel sannan zai koma. Tun ana min surutu ina damuwa har na saba. Zan iya cewa kusan komai na Ibrahim na sani, duk wani abu da yayi idan bama tare in muka hadu sai ya bani labari. Rannan muna zaune a gurin zaman mu sai sister dinsa ta kira shi a waya, ya dauka suka fara hira da yarabanci, ni sai abin ya bani dariya saboda ban taba jin yana yarabanci ba dan har manta wa nake yi shi yaroba ne, daga dukkan alama fada yake mata. Sai da suka gama sannan ya miko min yace mu gaisa, na karba tare da yi mata sallama ta amsa min da accent din yaroba. Muka gaisa babu yabo babu fallasa na mika masa wayar sukayi sallama ya kashe. Nace masa "what is her name?" Yace "Maryam" na sake tambaya "how old is she?" Yace "23" sai a lokacin na sake realising age gap din da yake tsakanina da Ibrahim. Nan yake bani labarin cewa maganar auren ta ne ya taso, ta kawo miji step father dinsu baiyi approving ba shine take so shi Ibrahim din ya shiga cikin maganar shi kuma yaki. Anan na fahimci cewa Ibrahim yana mugun yiwa step father dinsa biyayya like shi yake da final say a duk abinda ya shafesu.
Ibrahim sam ba mai yawan abokai bane dan ban taba ganinsa ko jin sa yana waya da wani aboki ba. Rannan mun tashi daga islamiyya. Nace " why aren't you going into town? Yace "I have nothing to do in town, ni ban san kowa a garin nan ba, school din nan ta bani gurin zama a cikin quarters, tana bani abinci kullum" ya tsaya da tafiya ya juyo yana kallona "and you are here also, so mai zai kaini cikin gari?" Nayi murmushi naji dadi har cikin raina nace "amma tunda har kazo Abuja, why not baza kayi using this chance ba ka ga gari, it is a very nice town, besides, u never know wa zaka hadu dashi a cikin garin. Ka sani ko kayi budurwa. Dariya yayi sosai yana kallona da lumsassun idanuwansa, ya langwabe kai gefe kamar mai shirin yin shagwaba yace "ni nayi kankanta da yin budurwa. Baki ganin ni yaro ne" yadda yayi maganar ne ya bani dariya nima nace "yaro a ina? I thought 25years kake? To in bakayi budurwa ba sai ka fara furfura tukunna? Ya kalleni da serious look yace "Allah da gaske nake bani da budurwa, sai later, da nace sai na gama service amma yanzu ina tunanin anya zan iya jira kuwa? In na tsaya wasa zuciya ta zata iya fitowa daga kirjina" yadda yake maganar a hankali da yanayin da yake kallona yasa naji tsigar jikina tana tashi. Banyi aune ba sai ji nayi Amira ta kama hannuna tana jana gefe tare da cewa "to love birds, times up, goodnight sir, sleep tight " da sauri da sauri take jana muna tafiya hostel ni kuwa har yanzu ido na a kansa suke shima kuma ni yake kallo, sai da muka je bakin gate din hostel sannan naga yayi min alamun 😘 nayi sauri na dauke kaina ban kuma kallon inda yake ba. Muna shiga hostel Amira ta jani gefe "what are you doing Moon? Kinga kallon da yake miki kuwa? Shaidan fa is real komai iliminsa kema kuma komai kame kanki da saka hijabin ki ba guarantee bane na cewa shaidan ba zai yi nasara akan ku ba" raina ya baci da accusation din Amira nace mata "Amira mutumin nan fa ba saurayina bane, we are just friends, sannan kuma bama kebewa mu kadai ni dashi, kullum a waje muke inda kowa zai gan mu" tace "ni ban taba ganin inda saurayi da budurwa za'a keyin friendship ba, you are deceiving yourselves, ko makaho ya shafa fuskokin ku yasan cewa something is there" nace "saurayi da budurwa kika ce. He maybe saurayi amma ni ba budurwa bace" tayi min kallon sama da kasa tace "oh ke 'yar jaririyace kenan ko? Ji nake yanzu haka ma period kike yi? Wanne girma kuma zakiyi nan gaba bayan already hormones din adolescent sun fara aiki a jikin ki. You are a woman now whether you are full breasted or not, dole akwai attraction tsakanin ki da shi" nayi sauri nace mata "am not attracted to him" tace "really? " tayi tafiyarta ta barni.

Episode Sixteen : The Letter

Har na karasa dakin mu ina tunanin maganganun Amira. Tabbas duk abinda ta fada gaskiyane. I know my biology and I know I am in adolescent stage. But am I really attracted to Ibrahim? It is not as if we are in love or anything amma kuma do i even know what love is? Am I ready for this? Har na kwanta ina ta lissafi a raina. Soyayya da Ibrahim ba abu ne me yiwuwa ba. Wata tafiya ce mai tsaho. Family na, family n shi, everyone will be against us. Hatta Hafsat ta saurara masa ne yanzu saboda nace mata ba soyayya tsakani na dashi. But i know what I am feeling. Ba zance ina son shi ba saboda ban san menene son ba. Amma nasan ina son kasancewa tare dashi, yana sani dariya, kuma duk sanda bana tare dashi inajin kamar ina missing wani abu. Is this love 💟? Ni na san ba zan iya yiwa Hafsat wannan tambayar ba in ba so nake in tsokano tsuliyar dodo ba. Tambayar da nake yiwa kaina itace: if abinda nake ji shine love din, am I willing to take the chance for him? And more important, is he willing to take the chance for me?
Tun daga lokacin sai na samu kaina da yin baya baya da Ibrahim. Bana barin mu hada ido dashi sam, in ya taho zai rako ni kuma nakan jawo Amira mu tafi tare, ita ma kuma Amiran ba ta ki saboda ta fahimci maganar da tayi min rannan ne ta saka nake gyarawa. Kullum in muna tafiya kuma maganar mu bata wuce ta karatu ko labari gida.
Muna haka har muka fara exams komai ya koma serious, Amira ma tayi joining karatun mu, kullum tare muke karatu mu uku shi kuma Ibrahim in mun gama sai ya dunga yi mana questions muna amsawa. Ana gobe zamu yi hutu mun fito daga Exam sai Ibrahim yayi kirana, muka tafi ni da Amira. Muna zuwa muka tarar dashi yana waya gida da yarabanci. Amira da sunkuyo dai dai kunnena tana dariya, kawai sai na samu kaina da jin haushin ta. Sai da ya gama wayar sannan ya kallemu yace "so u guys are going home tomorrow, right?" Amira tace "yessir" yayi dariya yace "oh su Amira harda saurin amsawa ko? Wato kin gaji da

Please Login or Register in order to submit comment