Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shagwaba, ya bude min bargo kusa dashi yace "shigo in rarrashe ki" na ajiye jakar hannuna na shige jikinsa, har da kara cusa kaina na zagaye shi da hannayena, a cikin kunnena yace "ana so ana kaiwa kasuwa ko?". Yau nayi baccin da banyi ba a cikin kwana goman da nayi a Riyadh, washe gari ma sai daki aka kawo mana breakfast.
Kwanan sultan biyu a Riyadh su Hafsat suka koma England, naji babu dadi saboda na saba da ganin ta kwana biyu, har airport muka rakasu suka tafi. Sultan yanzu ya saki jikinsa sosai da ummeensa, dan har hira da dariya zan gansu suna yi tare. A ranar ne kuma Ummee tayi deciding zata nuna mu a gurin 'yan'uwanta. A ranar da daddare ummee ta dauke mu ta kai mu gidan su, gurin mahaifiyarta, mahaifinta kam ya rasu last two years. 'Yar dattijuwar tana ganin mu ta gane sultan, sai kuka, ta rungume shi tana ta godiya ga Allah, bata iya turanci ba dan haka da larabci take magana, sai dai abinda bamu gane ba ummee tayi mana bayani, tace " ashe da akwai rabon zan ganka Abubakar? Kakanka har yabar duniya yana nadamar rabaka da mahaifiyar ka da suka yi, muna neman afuwar ka ka yafe mana," mun jima a gurin ta sannan muka tafi, sai da tasaka muka yi mata alkawarin ba zamu bar garin ba sai mun dawo gurinta. Daga nan gidan uncle din Ummee muka tafi, wanda yanzu shine kamar head of the family n su, ni dai gaba na yana ta faduwa ina tunanin yadda zamu kare dashi tunda har dashi aka je aka dauko ummee, ga mamaki na sai na ga sun karbe mu sosai, ya jawo sultan jikinsa yace "Abubakar din mu ya dawo gida" matan gidan ma sosai suka karbe mu, duk sun san da maganar sultan, 'ya'yan gidan ne dai sai kallonsa suke suna cewa dama khairat tana da 'da? Yayi mana nasiha sosai akan cewa ba laifin khairat bane ba, laifin sune su iyayenta, su suka rabata da mijinta da 'dan ta saboda pride dinsu, ya nuna wa sultan kuma cewa nan gidan su ne, kowa anan dan'uwansa ne babu banbanci, da zamu tafi yace "ina sadiq din kuma? Shi yaushe zaizo?" Duk kannin mu bamu da amsar wannan tambayar. Muna mota zamu koma gida na yiwa ummee tambayar da ta dade a raina nace "ummee ni kuwa ina don inji me yasa likacin aurenki kika samu matsala amma lokacin auren zayed shi bai samu matsala ba" tace "da akwai dalilai. Na farko ni mace ce zayed kuma namiji ne, a gurin zaben miji maza sunfi samun freedom akan mata, saboda mu mata muna da weakness, nan da nan za'a yaudare mu shi yasa iyaye suka fi saka idonsu akan spouse din mata akan maza. Dalili na biyu shi zayed kusan rabin rayiwarsa a England yayi ta, dan haka sanda ya tashi aure in banda wadanda suka je nema mishi auren babu wanda zai ce yasan matar sa, bayan anyi auren ma a England din suka zauna bai kawo ta nan ba har sai da ta haihu, zayed is older and stronger than I was, dan haka babu wanda zai kalli matarsa yace wani abu a kanta, dalili na uku kuma the most important shine, tsakanin aure na dana zayed shekara talatin, three full decades, abubuwa da yawa sun chanza, duk yawancin masu akida ta tribalism a family din mu babu su yanzu sai kalilan, suma kuma sunyi sanyi sosai" na fahimci bayanan ta, na kara tambayar ta daya abinda yake zuciya ta, nace "to yanzu ummee idan Takawa ya dawo kina ganin ba zai samu matsala ba kenan?" Tayi shiru kamar bata jini ba, sai naji babu dadi a raina, I shouldn't have asked that, sometimes surutu na yana sakawa in wuce limit dina, nace "am sorry ummee I shouldn't have asked that" tace "Sadiq ba zai zo ba ai, da ace zai zo da tare zasu zo da sultan, tunda kika ga basu zo tare ba to ba zai zo ba". Ban kuma tambayar ta komai ba, sultan ma kuma tunda muka fara maganar baice komai ba. Washegari muka cigaba da zagayawa gida jen 'yan'uwan ummee, kuma Alhamdulillah muna samun karbuwa a gurin su, duk da few of them ne suka san da zaman sultan a duniya. Rannan mukayi waya da Mommy, tace min " Ibrahim fa yazo neman auren Amina a gurin Daddy" da murna ta nace "laaa, amma shine Amina ko ta kirani ta gaya min?" Mommy tace "ai Amina ta tayar da rigima, tace ita yanzu bata son shi" nace "me ya faru?" Tace "wa ya sani ne, taki gaya min komai, shi yasa na kira ki ko zaki tambayar mana ita, kinga yaron nan sai faman zirga zirga yake amma ko fita gurinsa taki yadda tayi ballantana suyi magana, kuma naga daddyn ku sosai yana son hada wannan auren" nace "insha Allah Mommy zanyi mata magana, ko menene ma zamu sani". Ina kiran Amina ce min tayi "babu wani abu da zaki gaya min in chanza mind dina fa" nace "kin san ma maganar da zanyi miki kenan?" Tace "ai kowa maganar da yake min kenan, tunda ni ce mai auren nasa kuma nace na fasa banayi ba shi kenan ba sai a kyale ni" nace "OK munji mun kyale ki kin fasa auren sa, to amma ko zamu iya sanin dalili?" Kamar ba zata yi magana ba sai kuma tace "he doesn't love me. Duk abinda yake fada a baki ne kawai amma vai kai zuci ba" nace "ya zaki ce haka Amina? Wani abin yayi miki daya nuna miki cewa baya sonki?" Ta fara kuka tace "har yanzu Moon ke yake so, yana kulani ne kawai saboda muna kama dake, bana son in aureshi muyi ta samun matsala akan hakan" nan ta bani labarin abinda ya faru tsakanin su kwanan baya, nace "amma Amina tunda kika ga ya dawo ai ina ganin ya kamata ki saurare shi, ballantana kuma da maganar aure ya dawo, meaning he is serious this time around. Bansan menene a zuciyar Ibrahim ba amma nasan yayi nadamar abinda yayi wa matarsa ta farko, kuma yayi mata hakan ne saboda baya sonta, bana jin zai kuma making the same mistake a kanki, idan da baya sonki da gaske da ba zai ce zai aure ki ba" na jima ina bata shawarwari, da gaske Amina tana son Ibrahim dan haka na san zata sauko ne ta sake bashi second chance.
Bayan munyi waya da Amina sai nayi deciding inkira Amira in ji ita ma ya take ciki, na kira ta ta dauka da murnarta, tace "Moon naje gidanki aka ce ba kya kasar ma, ina kuka tafi haka babu ko sallama?" Nace "munje saudi gurin ummeen sultan" tace "dama 'yar can ce?" Nace maka kawai "eh" munjima muna hira sannan tace "kanin ki yazo gurina rannan" da sauri nace "and?" Tace "I don't know Moon, sam banji wani abu a raina akansa ba. Amir ma yazo yana gayamin maganar aurensa, he said if am interested in him, bayan auren nasa we will talk. Moon nayi addu'ah nayi istikhara amma banji komai a raina game da Abbas ba, I tot I had something for amir amma tunda yayi min maganar aurensa naji na hakura" nace "yanzu me zakiyi Amira?" Tace "Moon alhakinku ne yake ta bina har yanzu, shi dama alhaki ai kuikuyo ne, me shi yake bi, happiness dinku dana katse muku shi ya saka zanyi spending the rest of my life in sadness" nace "ba haka bane Amira, shi ubangiji ai mai gafara ne, yana yafiya kuma yana son bayinsa masu nadama da neman gafara, sai dai laifin da kika yi ba ubangiji kika yiwa ba, mu kika yiwa, dan haka ubangiji ba zai yafe miki ba har sai mu mun yafe miki. Ni na yafe miki ba tun yau ba, amma abin tambayar shine, kin nemi gafarar Ibrahim? Shi kika fi cutarwa, shine yafi kowa shan wahala kuma har yanzu bai huta ba, shawara ta gareki shine, ki je ki nemi Ibrahim ki roke shi gafara, na tabbatar zai yafe miki, in kuma ya yafe miki, na tabbatar zaki ga chanji sosai a rayuwar ki, saboda hakkin wani baya taba barin mutum yaci gaba a rayuwa".
2 hrs ยท

Episode Ninety One : His Mother's Son 2
Tace "to ni yanzu moon ta ina zan same shi?" Nace "How will I know ni da bana kasar ma" tace "Moon tsoronsa nakeji, tunda ya gane gaskiya bamu hadu ba, bansan wacce irin karba zai yi min ba" na danyi tunani a raina, tabbas Ibrahim yana jin haushin Amira sosai, dan haka ba lallai ne yasaurare ta ba in taje wajansa, Allah ma yasa karya faffalla mata mari. Sai kuma wata shawara ta fado min arai na, nace "abinda za'ayi Amira, kije gidan mu gurin Amina, ni zan kira ta in yi mata bayanin abinda nake so tayi, zata hada ki da Ibrahim kuyi magana, duk abinda ake ciki kuma sai muyi waya" ina gama yawa da amira na sake kiran Amina, ta dauka tace "what again?" Nace "ke dalla can ba maganar shi zanyi miki ba" sai nayi mata bayanin duk yadda mukayi da Amira, nace "yanzu taimako nake nema a gurinki, so nake ki hada su ta roke shi gafara, kema dan Allah sai ki tayata rokonshi" tace "kuma kika ce min ba maganarsa zakiyi min ba" nayi dariya nace "amma ai ba maganarsa dake nayi miki ba, maganar abinda ya faru tsakaninsa da amira nayi miki" ta danyi tsaki tace "ba lallai ne fa ya yafe matan ba, tunda har yanzu bai manta ki ba ba lallai ya yafewa wadda ta raba ku ba" nace "in kika hada su ne zaki tabbatar cewa ya manta dani yanzu, nayi miki alkawarin zaki sha mamaki, bazan miki alkawarin zai manta dani completely ba tunda nima ban manta dashi completely ba amma babu zancan soyayya, an wuce gurin, sai mutunta juna. Duk kanin mu, ni da ke, Ibrahim da Amira, duk mutane ne mu, muna making wrong decisions a rayuwar mu, muna sabawa Allah ma kansa ballantana mutum, amma in muka nemi gafarar Allah sai ya yafe mana, ya sake bamu chance saboda yana son mu chanza mu zama mutanen kirki, ti me yasa mu mutane ba zamu ke yafe wa junan mu ba? Me yasa zamu ke riko a ranmu bayan munsan cewa muma muna so in mun yiwa wani laifi ya yafe mana. Please Amina kiyi kokari kiga Ibrahim ya yafe wa Amira kema sai ki yafe masa ki sake bashi chance" ina kallon sultan ya shigo dakin da takardu a hannunsa ya tsaya yana kallona, Amina tace "shikenan, zanyi magana da Amirar in gani, I will see what I can do" muka ajiyar wayar. Sultan har yanzu yana tsaye yana kallona, am sure yaji ambaton sunan Ibrahim da nayi a waya, na tsaya ina jiran inga reaction dinsa, ya karaso inda nake yace "miss problem solver, kina nan amma kina solving problems din wadanda suke thousands miles away" naji dadi da ya fahimce ni, ya zauna a gefe na ya miko min takardun hannunsa yace "Ummee tayi miki maganar nan?" Na karbi takardun ina dubawa, da sauri na mike zaune sosai ina kara dubawa, na girgiza masa kai nace "bata yi min maganar ba, ta dai ce saboda kai ta fara kasuwancin ta, amma bata gaya min cewa sunan ka ne akan komai ba" dukkan takardun abinda Ummee ta mallaka ne, hatta takardun wannan gidan, da bank account dinta, da takardun dukkan contracts din data karba na shigo da kaya, duk sunan sultan ne a jiki. Na ajiye takardun ina kallonsa, yace "how do I tell her ni bana son kudinta?" Na girgiza kaina nace "mahaifiyar kace sultan, duk abinda ta baka ba faduwa tayi ba kuma kaima in ka karba ba faduwa kayi ba, karbar da zaka yi a ganina shine nuna godiyar ka gareta, inka mayar mata ka nuna mata baka so ba zata ji dadi ba, ka karba amma sai kace mata ka barta a matsayin care taker ta dukiyar taka, ta cigaba da kula da ita kamar yadda takeyi da" yace "to wannan uban cash din kuma da yake banki ya zanyi dashi?" Nace "kudi ne fa, you can do anything with it" ya jawo ni kan cinyarsa yace "ke a shawarar ki me kike ganin ya dace inyi dasu?" Na gyara kwanciyata a kan cinyarsa na danyi tunani kadan sannan nace "why not ka sake gina wata orphanage din, kuma ka bunkasa wacce kake da ita already, kace kana son gina musu makaranta da daukan malamai. Kaga idan kayi haka daga kai har ummee zaku samu lada har karshen rayuwar ku", yana murmushi yace "har ke da kika kawo shawarar" na mayar masa da murmushin nace "yes, har ni dana kawo shawarar". Washegari Ummee ta kaini gidan su zayed na wuni a can Umm zayed me kirki sosai gata wayayyiya, da sister dinsa zahra, na sake sosai dasu muna ta hira da zahra ina vata labarin England, wai tana son zuwa tayi karatu amma an hana ta a gida, muma cikin hira tace "amma kinfi sister dinki kirki, ita bata yiwa mutane magana" nayi dariya nace "ba haka bane ba, Hafsat tana da kirki sosai, kawai dai banbancin halayya ne a tsakanin mu, ni ina da surutu da saurin sabo da mutane ita kuma bata kula mutane sosai, amma in kika saba da ita zaki fahimci tana da kirki sosai. Abinda zakiyi ki lallaba a barki ki je England gurinsu ki dan kwana biyu, zakiyi mamakin kirkin Hafsat" sai magrib sultan yazo ya dauke ni muka koma gida. A hanya yake ce min "yaushe zamu koma Nigeria ne, Takawa yana ta waya wai ya kamata in taho haka nan" nima nayi missing gida sosai, amma nace masa "akwai rigima da ummee kenan" yace "sosai kuwa, dan yadda take ta plans dinta tunani take yi munzo garin nan kenan, ta manta ina aiki a can, besides Takawa ba zai taba barina in dawo nan da zama ba" a raina nace wasa kenan, dan nashi namiji guda daya kamar rai, his only heir, sultan yace "abinda za'ayi yanzu in munje gida, naga kunfi shiri da ita, ki tayar mata da maganar komawar mu Nigeria mu gani abinda zata ce, sai muyi mata bayanin ai ana ta nemana a office din mu sannan kema asibitin da kikayi booking zaki yi antenatal suna nemanki, mu ce mata amma zamu ke zuwa from time to time" na yarda da shawarar sultan dan haka muna dinner na fara maganar, dama sai da na gama jero adduoi sannan na fara magana, tunda na fara ta ajiye spoon din hannunta tana kallona, na duburburce na kasa karasawa, na kalli sultan amma sam yaki dago kansa ya kalleni, tace "yaushe kuka hada wannan plan din? A hanya ko kuma dazu a daki? You are not going anywhere. Me zakayi da aikin a can din? In aikin yi kake so sai ka nema anan ai. Ke kuma wanne antenatal zaki yi wanda ba zaki iya yi anan ba? You are a doctor, kinsan duk abinda kike ji kinsan kuma drugs din da zaki sha, ki rubuta masa sai ya siyo miki, sai menene kuma ake yi a antenatal din? Akwai kanin zayed shima doctor ne anan, ki shirya gobe sai muje ayi miki scanning" na kalli sultan na ga har yanzu baya kallona, nace a raina, wato zura ni kayi dama ka barni ni kadai ko? Ai kuwa muna komawa part din mu na fara sauke masa kwandon bala'i, "shine dazu kaki yin magana ko" yace "dama nasan ba zata yarda ba, I just want to confirm" nace "shine kayi using dina kayi confirmation din ko? I tot we are suppose to be a team" yace "we are a team. Yanzu ni bansan me zance wa Takawa ba idan ya sake kira, dazu daya kira cewa yayi da yasan zamu dade da kema ba zai barki ki taho ba ballantana har in biyo ki. Yanzu me zance masa?" Nace "oho, ni dai ba zaka sake yin using dina ba ehe, kawai dan ace ni ce marar kunya" ya jani muka zauna yana langwabar da kai, "hava love, ba using dinki nayi ba, kin san ina jin kunyar ummee ba zan iya yi mata musu ba shi yasa nayi shiru. Ina son komawa Nigeria amma kuma bana son inyi hurting ummee" na danyi tunani sai kuma nayi murmushi nace "then tell Takawa the truth, ka gaya masa ummee tace ba zamu dawo ba anan zamu cigaba da rayuwa har illa masha Allah" ya dan yi shiru sai kuma ya fara dariya, yace "that means war" nace "then let them have the war, mu sai mu zama 'yan kallo" ya manna min kiss yace "that's why I love you more every day".
Washe gari muka je scanning. Dani da Sultan da Ummee. Private clinic ne na Ahmad kanin zayed, kusan sa'an sultan ne dan haka muna zuwa suka kama hira, yana da fara'ar sosai da wasa kamar zayed. Tare muka shiga dakin scanning din gaba daya, ya fara min tambayoyi ina amsawa yana tsokana ta, ummee tayi masa bayanin cewa nima doctor ce, yace "shi kenan ma kinga abin yazo da sauki, duk bayanan da zan miki kin sani, sai dai kawai mu duba muga lafiyar babyn shikenan" nace "doctor we don't want to know the sex of the baby" da sauri sultan yace "when did we decide on that?" na harare shi, ummee tayi dariya, nace "kullum yana cewa mace ce ni kuma ina cewa namiji ne, so I tot mu barshi kawai in an haihu magani" sultan yace "no, ban yarda ba, dan kinsan ke zaki yi loosing shi yasa kika ce haka" Ahmad yace "ai ya danganta da kwanciyar babyn, idan babyn ya kwanta yadda zamuga sex din shi kenan in kuma ba haka ba sai mu bari daga baya mu sake dubawa" ni dai na bata rai, dan nasan in aka ga macece sultan in ya saka ni a gaba da tsokana har sai nayi kuka. Ummee taga na bata rai tace "abinda za'a yi, in kaga sex din kar ka fada musu, ni zaka fada wa, ni zanyi deciding me za'ayi dashi" sultan ya fara kunkunin ummee tafi sona a kansa. Doctor Ahmad har da juya screen din dan kar in gani, sam bai daga min riga ta ba, ta cikin rigar ya saka handle din ya kama jujjuya shi akan cikin yana yiwa ummee da sultan bayanin komai, sultan sai washe baki yake yi. Sun fi minti talatin suna kallo, sultan wai bai gaji da gani ba, sai da doctor yace "kai da za'a haifa maka a baka a hannunka ba sai kayi ta kalla ba?" Ya rubuta result ya bamu, ya rubuta wani ya bawa ummee. Alhamdulillah komai normal yake tafiya. Daga nan muka koma gida. Washegari doctor Ahmad ya kira sultan wai yana son muje gidan sa mu wuni a can, yana son ya hada ni da matar sa. Matarsa mai kirki sosai, Firdausi, zamuyi kusan sa'anni ni da ita, sai dai ita har tayi 'ya'ya biyu, Amra da Afra, su sultan suka fita suka barmu tare, tare muka hada lunch tana ta yaba methods of cooking dina, bata san cewa da zero nake ba daga baya na koya, muna gama shirya table su sultan suka dawo muka yi lunch tare, nace da doctor Ahmad, "da fatan dai baka gaya masa ba" yace "ai nayi wa ummee alkawari, duk wanda yake so ya sani sai dai ya tambaye ta" nan muka zauna hira akan banbancin al'adun mu da nasu, da yadda zamani yake chanza both al'adun mu da nasu. Ummee ce ta kira ni a waya tace mu dawo gida haka nan, na duba agogo naga 4:30, nayi mamaki cewa da tayi mu dawo da wuri bayan hira tana dadi, Ahmad yace bara su biyo mu kawai dama sun jima basu je gidan ummee sun gaishe ta ba. Muna yin packing na lura da motoci da yawa a gidan, ni dai ina mamaki na kalli sultan ya daga min kafada alamar shima bai sani ba, a palon farko muka ga al rataye balloons pink and blue, a kofar shiga palo na biyu an yi decoration an rubuta 'Welcome to the Gender Reveal Party' mamaki ne ya kamamu, dama Ummee party ta shirya mana? Muna shiga kuwa aka dau tafi da sowa, da 'yan'uwan sultan nan kusan duk wanda yake gari yazo, na kalli Ahmad naga yana mana dariya, wato dashi aka hada baki shi yasa ya gayyace mu gidan sa. Ni dai ba zan iya cewa ga abinda ya faru ba, they are all talking at the same time kuma mostly larabci suke yi, ni dai naga an jamu ni da sultan gefe, aka hada hannayen mu aka daure da pink and blue ribbons, sai kuma naga an turo wani table da katon cake akai, fari tas cake din kamar snow, aka kawo gabanmu aka ajiye, aka kawo mana 'yar karamar wuka fara aka saka mana a hannayen da aka daure, ina kallon zahra tana recording da wayarta, suka fara chanting 'cut the cake, cut the cake' sultan ya kalleni yace "are you ready?" Na juya na kalli ummee, ta gyada min kai, na kalli sultan nace "yes" nan aka dauki tafi da sowa, suna chanting "pink means girl, blue means boy" wato in muka yanka cikin cake din muka ga pink to girl ce, in kuma muka ga blue to boy ne, na kalli sultan naga sai zuba murmushi yake, dadi ya ishe shi, gani ga ummeensa ga 'yan uwansa duka kuma muna sonsa, ga kuma cikin jikina, dan haka bai damu ba ko mace ce ko namiji ba, nima sai naji ban damu ba, fatana Allah ya bani mai albarka. Muka dauki wukar a tare muka yanka cake din, tun kafin mu karasa yanka wa na ga blue, muna gama yankawa kuma aka dauki ihun "it is a boy" ni dai dariya kawai nake yi, na kalli sultan naga shima dariyar yake yi, ya kalle ni yace "Congratulations My Love, you won" yayi kissing dina a cheeks sannan yayi min a goshi, sai kuma ya rungume ni a jikinsa ya rada min "I Love You" a cikin kunne na, nima nace masa "I love you more".
Nigeria
Ibrahim;
Satinsa biyu a Ibadan ya dawo abuja, a zaman da yayi a ibadan ya kuma kulla dangantakarsa da ubangiji kuma ya kara kulla wa da mama da sauran 'yan uwansa, dan takanas ya fita yawon zumunci, kusan duk 'yan uwansa da suke ibadan, barim mama da baba da kuma babansa mahaifi babu gurin wadanda baije ba, kuma duk inda yaje sai ya kai musu goma ta arziki. Yana dawowa Abuja kuwa ya karawa employees dinsa albashi, wadanda ya kora ya kira su suka dawo bakin aikin su. Shi kansa yaji chanji a jikinsa, dan yanzu fresh yake jin kansa, zuciyarsa da take a kuntace a da yanzu tas yake jinta. Ya nemi masu aikin construction suka zo sukayi masa renovating gidansa aka kara dakuna, aka fitar wa da mama part dinta, da nashi part din shi da Amina, daga baya kuma akayi dan karamin BQ saboda kannensa maza. Har furnitures sai da ya zuba da komai sannan ya koma ibadan, nan fa mama ta saka rigima ita ba zata koma gidan sa ba, sai da ya hada da gaya wa 'yan'uwanta da yasan tana jin maganar su sannan ta yarda ta biyo shi, ita da maimunatu da kannen Ibrahim maza su biyo, matan dama duk sunyi aure suna gidajen mazajen su, mazan kuma an gama secondary school amma babu halin shiga jami'a, 'yar collage din ma ta gagare su. Ai kuwa suna ganin gidan da zasu zauna yanzu sai murna, wahala ta kare dadi yazo kuma, suna zuwa ya nema musu admission a university of Abuja, Allah ya so lokacin sabon dauka ne kuma yana da hanya tunda yana da kudi, dan haka basu samu matsala ba suka samu, maimunatu kuma ya nema mata

Please Login or Register in order to submit comment