Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bayan daya sannan ta zauna tana tambayar daddy menene yake faruwa, shiru yayi bai amsa mata ba sai inna ce ta fada mata brief abinda ya faru. A take mommy ta day zafi, daga ni har Hafsat din ta hada ta wanke mu tas. Dama tasan halin Hafsat amma bata dauka har a school bata kulani ba. "She is your only sister, me yasa ba zaki so ta ba? Me yayi miki a rayuwa?" Ta juyo kaina " and you little mouse, ta yaya zakiyi ki yi asarar shekara guda ta rayuwar ki just saboda kina so ki raba class da 'Yar uwarki, why didn't you tell me or your father about what is happening so that we can do something about it, we can put u in separate schools or something. Mommy fada take yi kamar zata ari baki har sai da daddy ya koma shine mai bata hakuri, ita mommy takaicinta shine wai ace "ya'yanta mata su biyu kadai da Allah ya bata kuma ace wai basa jituwa. If we didn't look after each other, who will look after us?
Sai da kowa yayi shiru sannan daddy ya fara magana:
"tun farko dama nasan basa shiri? Kuma me Hafsat kece fitinanniya. Wannan shine dalilin da yasa na kaiku boarding kuma bace a sakaku a class daya daki daya. Nayi tunanin in sun zauna tare a inda basu da kowa zasu hada kansu, banyi tunanin hakan da nayi zai kara wa Hafsat jin zafin Moon ba. Kuma Ku sani wannan ba zai saka in raba muku school ba. Yanzu abinda za'ayi shine, me Hafsat Ina so ki fada min menene matsalarki da moon?"
Da kamar ba zata yi magana ba sai kuma ta dago kanta ta share hawayenta fara magana a hankali " daddy ni bansan me nayi wa mutane ba, kowa yafi son moon, hatta Ku kai da mommy, daada, inna, baffa, yaya habeeb har faruk kowa moon yake so, komai aka tashi yi moon za'ace kuma bayan nice babba. Daddy ko waya kayo sai kace a baka moon kafin kace a baka ni even though I am the eldest" hawaye ne yake zuba a fuskar ta sosai " a school, teachers dinmu kowa itace tashi haka friends, at school fa ana referring to me as Moon's Sister as if am her shadow or some supporting actress. I am tired of all this dad, I want to get away from her, i want to start shining on my own, not shining in her light. I never know what she plan, I didn't even think she can do something like this for me. I didn't asked her to do it and now u are already blaming me for it. Kuka take yi sodai yanzu, ni kuwa sai na tashi naje na rungume ta muna kukan tare ina kuma rarrashinta. Saboda ni bana so inga mutum tana kuma ballanta ne Hafsat.
Murmushi Daddy yayi yace" duk naji complaints dinki Hafsat, kuma inaso ki sani, daga ni har mom dinku baku da banbanci ke da moon a gurinmu. Abinda baki fahimta ba shine halinku ba daya bane ke da moon, moon ta Fiji son mutane, ke kina da saurin fishi, kullum kina daki to waye zai biki daki ya kulaki. For example, yanzu tunda muka zo garin nan baki fita ba, inajin mom dinku tana yi miki fada dazu, duk kawunnanki da gwaggwanninki babu wanda kika je kika gaisar. Amma moon duk taje, wasu ma twice taje musu. So tell me, why won't they ask of moon first than u? Duk sanda bans kasar nan Moon kullum sai ta kirani a phone din mom dinku amma ke sai in na nemeki. In kina so mutane su so ki to kema dole ne ki so mutane" nan dai daddy ya yi mana fada sosai. Ni kuma daddy yace min as punishment for what I did, bazan sake exams dina ba, tunda yasan in aka hada first, second and third term scores dina aka day average to bazan yi repeating ba. Inna ma yayi mana fada sosai akan zumunci da kaunar juna kuma da alama fadan ya shige mu Dan tun kafin muyi resuming school na fara ganin chanji daga Hafsat.



Episode five: The Strangers

Bayan shekara uku
Haka rayuwa ta cigaba da kasance mana cikin jindadi da gata. Daddy yana ta samun ci gaba, yana ci gaba da harkar ambassadorship dinsa kuma yana visiting lecturer a Oxford. Ya Walid ya kammala sec sch dinsa inda Daddy ya tura shi Oxford yake karatun degree dinsa a fannin engineering. Ya Habeeb yana ss3, Hafsat dani kuma muna ss2.

Yaune second day of resumption kuma kamar yadda al'adar school din take, yaune ake gabatar da speech and prize giving. Mommy, ya Habeeb, daada da Faruk duk sunzo mana, suna zaune a gurinsu na musamman a side din parents. Ni da Hafsat da babbar kawata Amira munyi kwalliyar mu dai dai misali, muka fito gurin taron. Abinda ya bamu mamaki shine ganin wadansu mutane su biyar da kayan NYSC a jikinsu a zaune a bakin hall din taron. Tsayawa nayi ina kallonsu da mamaki saboda tunda muke a school din ba'a taba daukan coppers sunyi service anan ba, ko teachers din ma ba kowa ake turowa ba, sai very qualified teachers wadanda suka san me sukeyi. A hankali na furta " this doesn't look good " amma ga mamaki na sai naga duk sun juyo suna kallon mu alamar sunji abinda na fada. Kunya ce ta kamani, yayinda Hafsat ta tabe baki tace" I guess there is a first time for everything " tana fadin haka tayi gaba tare da fizgar hannuna, babu shiri ni da Amira muka bita a baya.
A yanzu kam Hafsat zan iya cewa ta zama budurwa, dan inka ganta ba zaka ce she is just fifteen years ba, ni kuma lokacin ina fourteen amma still bani da girman jiki sai tsaho shima ba sosai ba. Hafsat kuwa masha Allah, dan koni da nake mace wani lokacin tsayawa nakeyi inyi ta kallonta. Fatarta bata kai tawa haske ba amma fa a murje take tana daukan ido, ga laushi. Hancinta yafi nawa tsaho kamar yadda fuskarta ma tafi tawa tsawo. Idanuwanta dara dara farare tas, bakinta mai dan fadi wanda yake dauke da full lips shi kansa abin kallo ne. Kirjinta a chike yake taf haka hips dinta wanda yasa dole mommy ta dinka mata dogayen hijabs saboda in tana tafiya gaba daya jikin ta rawa yake yi. Hafsat mai class ce sosai, ba kowa take yiwa magana ba ballantana kaga dariyarta, amma in tayi dariya wani one sided dimple ne da ita ga kuma jerarrun hakora farare tas abin sha'awa. Ni kuwa mostly English wears nake Takawa saboda nafi feeling comfortable a cikin su. Kuma babu mai yi min magana saboda bani da komai a jiki na sai kyan fuska, wannan kuwa mutane da yawa sukance nafi Hafsat amma ni kam ban yarda ba, a ganina yawan murmushi na ne yasa ake ganin kyau na. Saboda shi murmushi ado ne musamman a gurin mace.
Muna shiga hall din gurin su mommy muka je muka gaishesu sannan muka je muka gaida Maman Amira muka tafi seats dinmu muka zazzauna, saboda an kusa fara taron. Kamar yadda aka saba, bayan bude taro da addu'ah sai aka fara gabatar da jawabai. Hafsat ta dauko novel dinta ta dora akan chinyarta ta fara karantawa ni kuma nayi tagumi da hannu bibbiyu ina sauraren speeches din daki daki. Sai da aka gama sannan aka kirawo passing head girl ta gabatar da farewell speech on behalf of the graduands. Lokacin har kuka nayi saboda tunanin shi kenan bazan sake ganin suba. Hafsat kuwa bama tasan me akeyi ba, sai da taji ina sheshahekar kuka sannan ta dago kanta ta kalleni ta kalli stage sai kuma tayi tsaki ta cigaba da karatun ta. Sai da aka fara rabon gifts sannan ta dago kanta ta rufe littafin da take karantawa ta mayar da hankalinta kan stage. A kayi ta kiran mutane ana basu gifts sannan aka zo kan set din mu. Kamar duk shekara, ni aka bawa overall san nan Hafsat second. Sai da aka gama rabon gifts sannan senior master ya hau kan stage ya fara announcement " I know all of u notice some strangers wearing strange clothes here" akayi dariya gaba daya, yaci gaba da cewa" they are NYSC members, they are sent here because the are the best in their various fields. The NYSC board wants this school to start participating in the scheme, that is why they sent this coppers to work with us. I hope you students will give them your maximum cooperation " daga nan sai ya fara kiran su daya bayan daya suna gabatar da kansu tare da fadin subjects din da zasu ke dauka da kuma classes din da zasu dauka. Tunda suka fara naji gabana yana faduwa, haka kawai naji jikina yana bani cewa something not so good is going to happen. Ina cikin haka naji wani daga cikinsu yace" my name is Ibrahim Adeniran Oluwaseun, from Ibadan. I will be taking SS2 mathematics and geography.
Innalillahi wa inna ilaihir rajiun shine abinda nayi ta maimaitawa a zuciyata. Ji nayi tamkar an juya min dukkan plans dina na rayuwa ta. Mathematics is my best subject, maths teacher din mu is my best teacher, yaya za'ayi a chanja min teacher a hada ni da inexperienced copper? Ji nayi tamkar inbi su mommy mu koma gida saboda ji nayi gaba daya makarantar ta fita daga kaina. Ban kuma fahimtar me ake ciki ba saiji nayi ana hayaniya alamar an tashi daga taron. Cikin sanyin jiki na dauki gifts dina na tafi gurin mommy na kai mata, haka ma Hafsat. Mommy tana gani na tasan something is wrong, tana tambaya ta kuwa na fara yi mata bayani. Mommy akwai daukan zafi dan haka nan da nan ta jamu sai office din senior master ta fara yi masa bayani akan cewa tun da muna senior class bai kamata a dauki subject as important as mathematics a bawa copper ba, kamata yayi ace an bar coppers a junior classes. Murmushi yayi tare da cewa " na fahimci complaints dinki Ma, kuma insha Allah in ya fara daukan su in har sunga akwai problem, ina encouraging dinsu su zo su yi complaining. But first they need to give him a chance. We will all need a chance one day in our lives, one way or another". Da haka muka fito daga office din, mommy tana encouraging din mu akan as soon as muka ga bama gane teaching dinsa mu zo muyi complain. In ba'a dau mataki ba in tazo mana visiting mu gaya mata, in yaso sai tayi wa daddy magana yazo da kansa yayi solving issue din.



Episode six: The Challenge

Nidai har ga Allah wannan hukuncin baiyi min dadi ba, saboda haka kawai naji raina baya son copper dinnan, he is too young to teach us a ganina. Hafsat kuwa sai na lura babu abinda ya dame ta. Da nayi mata magana sai cewa tayi "laa ni ban wani damu bafa, musamman akan geography, wancan teacher din ya fiya bayar da note, kin san ni kuma bana son note" (Yar Hutu). Unlucky for me, washe gari muna da geography. Tun safe naji raina ya baci dan ma bashine first period ba,sai munyi biology sannan zamuyi shi. Tom teacher din biology yana gama yi mana sai ya bamu assignment, yana fita sai na dauko assignment dina na fara sai naji hayaniya a class anata leka window. Na tambayi Amira nace "menene wai ake wannan leken" sai tayi dariya tace " wannan yaron ne ya taho zai koya mana geography" nayi tsaki nace "zai koya musu dai" na ci gaba da zanen da nakeyi na digestive system dan shine assignment din da biology teacher ya bayar. Hafsat naji tace "sabon shiga, ko dan late coming dinnan ma abar mutane su huta baza'ayi ba". Tana gama fada yana shigowa kuma na tabbatar cewa yaji abinda tace, dariya ce ta kubce min ganin yadda Hafsat ta wani maze kamar ba ita ce tayi maganar ba. Ina kallonsa ta gefen ido na. Ya cire uniform din NYSC ya saka personal shirt da wando amma ya dora p-cap din NYSC din a kansa. Ban wani kalleshi sosai ba na maida hankali na akan zanen da nake yi. Ya jima a tsaye yana kallon mu daya bayan daya sannan a hankali yace "don't u guys know how to greet? Duk class din muka mike a tare, tare da cewa " good morning sir" ya jima yana binmu da kallo sannan yace "sit down" inajin Hafsat a hankali tace "finally" Nayi murmushi na zauna tare da ci gaba da zane na. Takowa yayi a hankali yazo gabana ya tsaya yace "why are u laughing?" Na dago kaina na kalle shi ido cikin ido nace " I am not laughing sir, I was smiling". "Hmm" shine abinda yace sannan ya kunna board, da yake smart board muke amfani dashi. Ya saka flash drive dinsa na nemo slides din da zai yi mana ranar ya kunna. Ni kuma ina ganin haka na cigaba da zane na. Inajinsa yace "our topic for today is rocks and their origin". Sannan yayi tambaya "who knows what this is?" Ban dago kaina ba ballantana inga abinda yake tambaya akai saboda ina expecting wani a ajin ya bada amsa, amma ga mamaki na sai naji shiru babu wanda yayi magana. Jikina ne ya bani ana kallona, na daga kai sai na ganshi a tsaye a kaina "miss smiler, we are trying to have a class here" yace min " can you please, out of the goodness of your heart, tell me what this is?". Ya fada yana nuna board, araina nace lallai wannan mutumin ya raina min hankali. Ya dan bude ido yace "the picture is displayed on the board, miss smiler, not here" ya sake fada yana nuna kansa. Dariya najiyo kasa-kasa daga bayana sannan na fahinci cewa kallonsa nake tayi. A hankali na janye idona daga kansa. Kallo daya nayi wa hoton black shiny stone din da yayi displaying a board, na dauke kaina. Na mai da dubana kan assignment dina tare da daukan pencil dina na cigaba da zanen da nake yi. A hankali nayi magana nace " that's obsidian sir". Shi kansa da yake kusa dani baiji abinda nace ba, dan haka ya sunkuyo da kansa yace "can you PLEASE, raise your voice a little bit?" Take naji raina na sake baci. "PLEASE" Ya sake cewa da muryar challenge. Dariya na sake ji saga baya na. Ni kuma har lokacin zane na nakeyi. Har ya juya zai koma gurin board sai na daga murya ta nace " That is Obsidian " Chak naga ya tsaya sannan a hankali ya dawo inda nake zaune ina zane na yace. "Tell me more" murmushi nayi sannnan na fara kwararo masa bayani tun daga kan yadda earth core take da yadda rocks suke melting su zama lava, yadda mantle da crust suke budewa har lava din ta fito earth surface. Daga nan na koma kan bayanin different types of cooling and solidification na lava din yadda yake producing different kinds of rocks. Sannan na dawo kan shi obsidian din, cooling process din da yake forming dinshi, dalilin da yasa yake black and shiny, composition dinsa, life span dinsa da amfanin sa a gurin mutane. Nafi 30minutes ina magana kuma at the same time ina cigaba da drawing dina. Tunda na fara magana ajin yayi tsit babu wanda yayi magana har na gama. Gamawa ta yayi dai dai da gama drawing dina. Sai da na karewa drawing dina kallo na tabbatar na gama sannan na dago kaina na kalle shi ido cikin ido tare da cewa " Is there anything more you want to know, SIR?" Na fadi kalmar sir din nima cikin challenge. Sai da wajen 30sec ta wuce sannan ya iya magana yace "wow, that is very correct. No, there is nothing more. U have said it all".
Kamar hadin baki, yana gama fadin haka aka buga bell din break. Books din mu duk muka rufe muka fice daga class din. Sai da mukayi nisa sannan na juyo na kallo class din mu naga yana nan a tsaye a inda muka barshi ya saka hannayensa cikin aljihun wandon sa yana kallon kasa. "He must be feeling like an idiot" na fada ina murmushi. Amira tace " Ai kin wanke mana shi tas, I wonder ta yaya zai yi facing din mu tomorrow morning for maths" Hafsat tace "and they said I am the cruel one". Dariya muka yi muka tafa ni da ita, nace "ai ba cruelty bane, he asked me a question and I answered him. He then asked me to tell him more, so I told him more" wata kawarmu Hasiya tayi joining din mu tace "baki da kirki Moon. You told him more and more. By the way, how do u know so much? Ni dai nasan ba'ayi mana duk wannan a aji ba" Nayi murmushi nace mata a cikin holiday na karanta, nasan za muyi shi a wannan term din. Nayi forming note a kan shi, in kina so kizo ki karba ki copying " tayi min godiya ta wuce. Amira tace "Tabdi ai ni babu abinda zai saka inyi karatu a cikin hutu, hutu fa akace, we are suppose to huta a cikin hutu"


Episode Seven: The Thin Tall Man

Washe gari first period muke da mathematics. Dan haka tunda na shirya nayi breakfast sai na dauki jotterta, calculator, sannan na duba syllabus naga abinda ya kamata muyi yau sannan na fice sai library. Ina zuwa na tarar librarian din ma zuwanta kenan. Ko gama cleaning library din ba'ayi ba. Na samu guri na jira har suka gama sannan na shiga. Miss Martha, librarian din mu ta tambayeni ya akayi banje class ba, na amsa mata da cewa teacher din mu bayanan kuma inada assignment da nake so in karasa. Ina shiga mathematics section na wuce, na debo textbooks din calculus har uku sannan na samu secluded guri na zauna na fara calculations dina hankalina a kwance. Saboda ina ganin a haka sai nafi ganewa akan ace wannan yaron ne zai koya min. Double period ce damu dan haka a lissafina zaiyi one hour 20min. Ina yi ina duba agogon hannuna har naga one hour ta wuce saura 20mins kenan. Hankali na gaba daya yana kan calculations dina saboda sosai nake jin dadin product rule din da nake yi a lokacin. Ji nayi tamkar ana kallona, da sauri na dago kaina tare da cire earpiece din kunnena. Ido muka hada dashi ga mamaki na sai naga ya sakar min murmushi. Daga dukkan alama ya jima yana kallona. Nayi saurin dauke kaina tare da sunkuyar da ido na kasa ina mamakin ganin shi a nan bayan nasan ya kamata ace yana class dinmu yana koya musu maths. "Mind if I join" ya fada cikin muryarsa mai sanyi. Ba tare da na sake kallonsa ba na ce "no". Kujerar kusa dani ya ja ya zauna. Ta ke naji na shaki kamshin sa. Na dan matsar da kujera ta kadan saboda kafadan shi da naji yana taba tawa. A hankali ya fara yi min magana wanda na tabbatar da ace da akwai mutun a kusa dani bazai ji me yake cewa ba. " Why aren't you in class" "am sorry" na fada a takaice. "Sorry for what" ya fada tare da adjusting kujerar sa yadda zai fuskance ni sosai, na kara jan kujerata baya sannan nace "for not attending your class". Murmushi mai sauti yayi sannan yace" it is not my class, it is OUR class, we are all suppose to be participating in it". Yayi shiru sannan ya kara da cewa " by the way, we miss u in class today. The class was exciting though, but I thought it would have been more exciting if u were there. So I asked of u and was told to check the library. And here u are. So, why are u here?" Ya tambaya yana kallon cikin idona. Na dauke kaina ina inda inda cike da jin kunyar abinda nayi. Ya saka hannunsa ya juyo da fuskata gare shi muke kallon juna, cikin muryar rada ya ce min "you think I am not good enough to teach you, right?" Kunya ce ta kamani, nayi sauri na kwace fuska ta daga hannunsa, nasa hannaye na na rufe idona cikin kunya nace masa "no" da dan karfi. Ga mamakina sai kawai naji ya kama dariya nima bansan sanda na fara dariyar ba. Sai da muka dena dariyar sannan ya dauki jotter din da take gabana tare da cewa " let's see what you have been doing for the past one hour" ban ce masa komai ba. Sai da ya gama studying abubuwan da nayi sannan yace " wow, we were in class tying to solve some few problems while you are here already done with the term. Na zaro ido nace "am not done with the term sir, am not even close" ya rungume hannayensa a kirjinsa, abinda na lura cewa dabi'ar sa ce. Yace " you are special, do you know that? Nayi sauri nace " no sir, am not. Kawai dai ina da son karatu ne" na fada ina kokarin kare kaina. Kallona kawai ya tsaya yana yi chike da rashin fahimta. Sai a lokacin na kalleshi sosai. Ba bahaushe bane. Na sunkuyar da kaina. "What tribe are you?" Ya tambaye ni cikin sanyin murya wadda itama by now na fahimci hakan yanayinsa ne. "Fulani" nace ina wasa da 'yan yatsuna. Yace " but what you just spoke is Hausa, right?". Nace "yes" yace " so u are Hausa Fulani " na girgiza kaina alamar a'a. Bai sake min wata tambayar ba. Can ya ce " I am yaroba. I am from Ibadan, Oyo state. My name is Ibrahim Adeniran Oluwaseun. Will you do me the honor of been my friend? " ya miko min hannunsa alamar shaking. Na gado kaina na sake kallonsa. Fatarsa ba mai haske nace kamar tawa ba kuma baka bace ( wankan tarwada). Dogo ne sosai sannan siriri ne dan bashi da kiba sam amma kuma straight bayansa yake tsahonsa bai sa ya rankwafa ba. Yana da doguwar fuska da dogon hanci da yalwataccen gashin gira. Bakinsa mai dan fadi ne mai dauke da siraren lips wadanda a yanzu suke dauke da murmushi. Fuskarsa tana zagaye da siririn saje da dan karamin gemu a habarsa. Fararen glasses be sanye a idonsa wadanda suke lumsassu kamar na maijin bacci. A hankali na sauke ajiyar zuciya tare da cewa " I am Fulani from Jigawa State. My name is Maimoon Muhammad Dikko. Yes, I will like to be your friend and I am sorry for missing OUR class today" " it is OK friend" ya fada yana sauke hannunsa ganin bani da niyyar shaking dinsa. Agogo hannuna na kalla, ga mamakina sai naga next period har tayi nisa. Da sauri na mike ina harhada takarduna hankalina duk ya tashi. Shima ya mike tare da daukan jotter da nayi calculations yace 'I will look this calculations over if you don't mind" "no problem" nace ina sauri duk hankalina yayi class. A bakin kofa ya sameni ina signing out. Ina fita ya biyo baya na, sai a lokacin na sake lura da tsahonsa, dan gabaki daya na a kirjinsa na tsaya. "See u tomorrow" na fada bayan mun fita daga libraryn. "See u in CLASS tomorrow" yace yana jaddada Kalmar class din. Da sauri nayi gaba dan bana so ya cigaba da bata min lokaci tunda already nayi latti a class din English. Ina shiga Aunty grace ta fara tuhumata akan daga ina nake, inda ni kuma na bata amsa da cewa ina library ina assignment ban san cewa har lokaci ya wuce da yawa ba.
Saida aka fita break sannan na tambayi Hafsat ya akayi a lokacin maths. Ta be baki tayi tace "ina ruwanki, ke da kikayi tafiyarki kika barmu da wannan dogon mutumin" nace

Please Login or Register in order to submit comment