Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

daki na zauna ina sauke ajjiyar Zuciya, ina jin kuma babu dadi a cikin raina, but haka Allah ya tsara mana ni da shi, we are not destined to be together. Ina nan zaune har Hafsat ta shigo, ta jefo min wani complimentary card tace "gashi nan yace a baki, he is so hot headed sai da na kusa loosing temper dina, he believes hada ku aure akayi da Sultan, yace yaji labarin dan sarkin garin nan ne, shi a ganin sa kin yarda da auren ne saboda babu shi. Yayi yayi in bashi number dinki na hana shi shine ya bani card dinsa yace in baki ki kira shi, yace in baki kira shi ba zai sake dawowa gobe" ta zauna a kusa dani tace "Moon, ki kira Sultan ki gaya masa halinda kike ciki, he will know what to do" na girgiza kaina nace "Sultan will definitely hurt Ibrahim in na gaya masa" tace "to ki fada wa David ya hana shi zuwa gidan nan" nan ma na girgiza kai "securities will treat him badly and I don't want that" ta mike a fusace tace "to hada kayan ki ki kirashi yazo ya dauke ki ku gudu tare a fasa auren" ta fice a fusace ta bugu min kofa. Kwalla ce ta taru a idona ina jin zafi a raina. Na sunkuya na dauki card din nasa, kallo daya nayi wa number din na haddace ta na jefa card din a waste bin. Ina bukatar inyi addu'ar sosai in nemi Allah's guidance. Ranar kam da daddare haka na tashi nayi ta jero adduoi akan Allah ya fitar dani daga matsalar da nake ciki, Allah ya saka wa Ibrahim dangana ya fahimci cewa ni ba matar sa bace ba.

Seven days....

Na tashi zucita ta fes kamar babu abinda yake damuna. Muna ta harkikin mu da 'yammata Amir ya aiko kiran Amina zasu je su gano venue din dinner. Muna zaune sai ga kungiya guda nan ta kawayen mu na sec sch, nan fa guri ya kuma hargitse wa, muna ta hira sai ga hasiya nan ta shigo daga baya, tana zuwa tace "guess wa na gani a waje yanzu?" Tun kafin ta fada nasan waye, nan take cikina ya kada tace "uncle Ibrahim" nan da nan suka kuma rude wa "yana ina?" "Moon dama kuna da contact dashi?" "Ko sallama yazo?" Duk ban basu amsa ba, hasiya tace "yana waje wallahi, ina ganin sa na gane shi, kunga yadda ya kara kyau kuwa? Ya goge sosai ya zama dan gayu fiye da yadda kuka san shi a baya" Walida tace "ke Hasiya, kina matar aure kike kallon wani ko? To wannan maganar kamar a kunnen abban Na'im" duk muka yi dariya tacigaba da cewa "da muka gaisa ma bai gane ni ba fa, wai yasan fuskar a cikin kawayen Moon amma ya kasa tuna sunan, sai da na gaya masa tukunna ya tuna. Yace yaji labarin bikin Moon shine yazo yayi mata Allah ya sanya alkhairi amma ya rasa wanda zai aika ya kirawo ta, nace masa in na shigo sai inyi mata magana sai yace kawai ma sauri yake yanzu in bashi number dinta zai kira ta, shine na bashi" hannu biyu na dora aka nace "kin bashi number ta fa kikace?" Ta kalle ni da mamakin yadda na rude tace "eh na bashi, Murna fa zaiyi miki shikenan, kuma ba'a daura ba ballantana kice kin zama matar wani ba zaki yi waya da wani ba" a raina nace "Hasiya had killed me" na tuna dramar da mukayi da Sultan akan musbahu ballantana Ibrahim. Duk abinda muke yi Hafsat tana jin mu baya tanka ba, sai kawai naji tace "'yan 'uwa ku matso in baku wani labari" duk suka juyo suna kallonta, tacigaba "kun tuna rannan a makaranta da Ibrahim yace wata a ajin mu tana sonsa amma shi baya sonta?" Duk suka ce eh, tace "a lokacin nace muku zan fada muku wacece amma moon ta hana, to yau zan fada muku kuma har ba bonus na labarin duk abinda tayi" da sauri nace "Hafsat no, please don't do this" bata jira abinda nake cewa ba ta kwashe labarin Amira kaf ta gaya musu" ta cigaba da cewa "sai shekaran jiya sannan Allah ya toni asirinta suka hadu a supermarket, kun ga ikon Allah ko? Da Allah ya tashi kamata ita da kanta ta kai Moon har office din Ibrahim" nan take gurin ya hargitse da hayaniya, daga masu dure2n ashar sai masu Allah wadaran halin Amira, Hafsat ta cigaba da cewa "na fada muku wannan ne saboda idan da akwai wacce take da saurayi to tayi musu katanga da Amira, mai miji ma haka, dan bamu san kan wanda zata koma ba kuma" Zulaihat ce dama masifaffiyar ciki ta mike tace "waye zai je gidan su Amira ya koya mata hankali?" Nan take duk suka mike har da Hafsat, dama ita tun shekaran jiya take son zuwa na hanata, na mike na sha gabansu, "dan Allah ku bar maganar nan, na riga na samu mijina wanda yafi Ibrahim a wajena ita kuma ta rasa Ibrahim din bashi kenan ba, shima Allah ya bashi matar data fini" ture ni sukayi gefe suna kumfar baki suka fice, Hafsat ce ta tsaya tana kallona tace "at least this will teach her a lesson tasan cewa tayi ba dai dai ba, amma in dai aka barta zata ga kamar taci riba ne ai, this will serve as a lesson to her da duk masu hali irin nata" ni dai anan na durkushe a bakin kofa ina hawaye, Amira was a good friend to me, she was my best friend for about 13 years, ni in ta nine ma zan so Ibrahim ya aure ta amma nasan ba zai aure ta din ba. Maman ta kuma kawar Mommy ce, naso rigimar mu ta tsaya a tsakanin mu bana so iyaye suji. Waya ta naji tana kara na duba, number din Ibrahim na gani, na san za'a rina dama, na ajiye ban dauka ba, ya cigana da kira kusan missed calls biyar sannan ya hakura, message naji ya shigo, shima ban dauka na karantaba. Sai can bayan la'asar sannan su Hafsat suka dawo suna ta dariya "dan Allah kuyi hakuri, ku bawa Moon hakuri dan Allah" wai haka Amira take cewa, kawai hawaye naji yana taho min, nace "da Amira ta raba mu da Ibrahim da kar ta raba mu, Allah ya riga ya kaddaro ba miji na bane ba" sukace "ke ai sanyin zuciya ne dake, da ace wani zai kashe ki ki sake dawo wa duniya ya baki hakuri cewa zaki yi kin hakura" sai kuma suka koma gulmar Ibrahim, "kin san har yanzu yana waje?" Nace "oho muku ku kuka sani" Hasiya tace "ni wallahi tausayinsa nake ji, Moon yana sonki da yawa wallahi" na harare ta nace "to bara in hada su shida Sultan in aura kawai". Hafsat ta gama tsara musu yadda events din bikin zai kasance sannan suka tafi suka barmu ni da Hafsat da Hamidda. Gab da magrib sai ga Amina ta shigo, fuskarta kamar gonar auduga, tana shigowa tayi tsalle ta fada kan gadon tana birgima. Muka bita da kallo da sakakken baki, sai da ta gama haukanta sannan tace "Albishirin ku" muka ce "goro" tace "at last yau wani yayi noticing cewa ni kyakykyawa ce" tsaki muka ja a tare ni da Hafsat, Hafsat tace "Allah ya shirye ki Amina" ta tashi zaune tace "am serious fa, anan waje muka hadu dashi bayan Amir ya sauke ni, ya taho da sauri yana yi min magana wai ya dauka ke ce" ta fada tana nuna ni, guiwata naji tayi sanyi na zauna akan stool, ta cigaba "ni ban san me yasa mutane suke hada kyakykyawar mace kamar ni da something like Moon ba, ni banga wani kama da muke yi ba" nayi dariya nace "shi yasa aka kasa noticing kyan naki ake noticing nawa" Hafsat tace "uhum, me yace miki kuma" ta cigaba "cewa yayi he is a friend of Moon, yaxo yana son ganin tane, daya ganni ya dauka itace shine ta taso. Yace muna kama sosai ko ni 'yar'uwarta ce, sai nace masa ni yayarta ce, shine yace shi Hafsat kadai ya sani yayarta, nace masa aini ba'a nan na taso ba a England na taso. Ya bani number sa yace in na shigo in kira shi sai in baki. Oh my God Moon ya hadu da yawa" na mike na shige toilet na rufe kaina, a fanfon sink na tara fuskata nabar ruwan yana ta zuba. Dai da naji numfashina yana neman daukewa sannan na cire kaina na goge fuskata da towel na koma dakin, ina shiga naga ta danna wayar ta ta miko min tace gashi, na jima ina kallonta sannan na karba, tace bara taje tayi sallah ta fita. Na zauna a bakin gado na saka wayar a kunne na naji already ya dauka, nace "assalamu alaikum" sai da ya sauke ajjiyar zuciya sannan ya amsa. Nayi shiru. Yace haka.u gaisuwa?" Nace "good afternoon" yace "yauwa ko ke fa, at least dai ai nayi deserving gaisuwa daga gare ki. Please Moon why are you doing this to us? Please don't punish me like this. Ba laifi na bane ba. I was led to believe kinyi aure. Kuma ko da hakan ma sonki bai ragu daga zuciyata ba sai ma karuwa da yayi. I know u love me too. I saw it in your eyes a office dina. You just have to tell Daddy cewa wanda kike so is here, a ajiye maganar wannan Sultan of a thing din" a hankali nace "Sultan is not my parents choice, he is mine. In fact daga farko ma parent dina basa sonsa nina matsa cewa shi nake so sannan suka yarda" yayi sauri yace "saboda bana nan ne yasa kika zabe shi Maimunatu. I am back now. Mun sha wahala Maimunatu kar kiyi mana haka. Abinda Hafsat tayi ta cewa kenan wai ke kika zabe shi. Whatever you think you feel for this man, believe me it is not love." Nace "Ibrahim, please don't make this harder than it already is. I know you are hurting and believe me, bana jin dadin haka sam. Amma abinda kake nema daga gare ni is just not possible. Ko da ace Sultan ba zabi na bane ba vazan iya tunkarar iyayena at the dying minute in ce musu na fasa auren nan ba. Ballantana ni na zabe shi. Put your self in his position, ace kana da budurwa kunyi maganar aure da ita, you went through alot together, kun sha wahala kuka yi convincing iyayen ku, an gama komai hatta jere anyi sai kuma few days to daurin auren ku sai tace ta fasa auren ka, how will that feel?" Yayi shiru for some seconds sannan yace "very bad" nace "good, to believe me it will feel more than very bad to Sultan, it will destroy him completely" yace "me yasa nasa zaifi na kowa zafi?" Nace "because he is kind of special" da sauri yace "ouch, that hurts" na danyi dariya nace "sorry" ya dan jima baiyi magana ba, sannan yace "do you think you will be happy with him?" A hankali nace "yes" muryarsa very deep with emotions yace "then I will be happy for you" wasu hawaye masu zafi naji sun taru a idona. Muka sake shiru sannan yace "Can I at least see you one last time?" Na danyi jim ina tunani, nace "not now, sultan zai iya zuwa anytime" yace "OK, I understand. Nagode for at least talking to me. Good night" ya katse wayar. Na ajiye ina jin zuciyata babu dadi.

Six days to....

Duk an gama shirye shirye. 'Yammata ana ta rigima da tailors din da basu gama dinkuna ba, ni kam duk kayana sun kammala kuma suna dakin Sultan, nace ya barsu a can saboda cikin gidan duk a hargitse yake kar inzo in rasa wani abun ranar da nake bukatar sa. Wajan 12 na rana aka ce inzo nayi baki a palo, na sauko na ga 'yammata su uku a zaune, already an riga an cika musu gaban su da kayan ciye ciye, ban gane ko daya daga cikin su ba amma daga ganin su kasan 'ya'yan manya ne, biyu bakake daya fara, amma jikina ya bani cewa farin mai ne. Na zauna da murmushi na ce musu "sannun ku da zuwa" kallo kawai suka bini dashi sannan suka kalli juna, sai suka sake kallona, daya daga cikin su tace "Amaryar ta mu ce?" Na sake murmushi nace "sunana maimunatu" suka sake kallon juna sannan dayar tace "eh haka muka gani a jikin IV. Ita din ce kuwa. But you are younger than we expected. An ce mana medical doctor ce" nayi dariya nace "I am a neurologist and also a psychologist. Karatu ai ba shine shekaru ba, in dai ka fara da wuri shikenan" bakaken biyu suka yi dariya, daya tace "sunana Fa'iza, wannan kuma kanwata ce Saratu. Mu kannen ki ne" ban gane ba, tace "if you know you know" sai yanzu na fahimta, kannen sultan ne, he never talk about them kamar basu yi existing ba. Na kara fadin murmushi na nace "sai yau kuka tuna dani? Nayi fushi" saratu tace "sorry big sister, ba laifin mu bane, mu bamu san ma dake ba sai kawai IV aka kawo mana, ko ince sai IV muka gani, dan mu yaya Sultan ko gayyatar mu bai yi ba, maimakon ace mune masu gayyata ma amma sai a gari muke ji" nace "to kusha kurumin ku, har sai kun gayyaci wasu ma" suka yi dariya, nace "and who do we have here?" Na nuna wacce suka zo tare, fa'iza tace "antin mu ce, umma khulsum" ban nuna komai a fuskata ba nace "sannu da zuwa aunty" da alamar tsokana, ta bata rai tace "in kika ce min aunty ai sai ki mayar dani kamar tsohuwa" muka yi dariya. Bayan sun dan motsa bakin su na tafi dasu sama dakina, har bayan azahar suna nan, tare mukayi lunch dasu, kowa sai da na nuna masa kannan Sultan. Ina lura dasu suna ta kallon gidan, ni kuwa nasan ba 'ya'yan sarki ba, ko 'ya'yan waye karya suke su kushe mana gida. Tunda suka zo suke ta yi mini tambayoyi akan sultan, wai yana dariya kuwa? Har da tambayar is he romantic, nace sosai kuwa. Around 3pm aka zo aka dauke su, na hada musu kayan kyalliya masu tsada da turaruka na basu tare da katinan kowanne event na bikin.

Na koma gida nayi wanka na shirya, nayi sallar la'asar aka sake cewa nayi bako kuma, na sako hijab dina na fito ni da Amina, a tsaye muka ganshi a jikin motar sa. Yayi kwalliya kamar babu gobe. Daga ganin sa kasan hutu ya zauna masa. Ina ganin da na gane shi. Abbas ne, muka karasa muka gaishe shi ya amsa yana tsokanar mu "wacce ce yayar tawa ne a ciki?" Na nuna Amina, yace "to tunda kika nuna ta ke ce" muka yi dariya yace "ya shirye shirye?" Amina tace "Alhamdulillah' nayi kokarin a kaishi palon su ya Habeeb amma yace sauri yake, yace karar Sultan ya kawo min, wai bai saka shi a cikin harkar bikin ba kwata kwata, shida ya kamata ace shi yake organizing bikin amma sai dai yake gani ana yin abubuwa babu shi, nayi masa alkawarin zanyi wa sultan magana akan hakan. Ya sake cewa " sai magana ta gaba, ina so in shirya masa hawan angwanci a matsayin wedding gift dina amma yace baya so, ni ban taba ganin inda akayi bikin dan sarki babu hawan angwanci ba" na jinjina maganar, nasan Sultan ba zai yi ba, tunda yake babansa bai taba hawan sallah dashi ba, kuma ko a magana ban taba jin yana maganar yin hawan angwanci ba, da yana so kuwa da zai ce zaiyi. Nace masa "insha Allah zanyi masa maganar shima, amma babu guarantee zai yi, in ba zai yi ba kawai ka rabu dashi", ya daga kafada yace "it's OK, ina son kuma cards saboda friends dina" na tura Amina ta dauko masa da yawa ta kawo masa. Shima muka yi sallama ya tafi.

Da daddare Sultan bai samu zuwa gida da wuri ba saboda friends dinsa na America da suka zo, yana can nema musu masauki da entertaining dinsu, dan haka bamu hadu ba sai waya mukayi. Na gaya masa bakin da nayi yau da yadda muka yi dasu duk, yace "what? Munafukan yaran nan karya suke yi, babu abinda ban basu ba, su dai kawai tsegumi suka zo yi" nayi murmushi nace "it is OK ai. Tom Abbas kuma yace ka ki sakashi a organisers" yace "Abbas ba zai iya organising komai ba, bai san ni ba bai san me nake so da wanda bana so ba, role din Amir yake so in bashi kuma bazan bashi ba" nace "but at least involve him in something, tunda ya nuna yana so karka sace masa guiwa" yace "moon baki san halin yaron nan bane ba. But whatever, zan gaya wa Amir in da akwai wani abu ya bashi. Zancen hawan angwanci kuma bazan yi ba, I already told him bazanyi ba, he is trying me" jin ya fara daukan zafi nayi shiru, sai da naji ya huce nace "tell me something nice" daga muryar sa kadai nasan ya ware yace "what's nice without you. Sai yanxu nake nadama big wedding din nan, da na sani kawai daurin aure akayi aka kaimin amaryata" nace "tukunna ma, sai jibi in an fara ido zai raina fata" yace "ohh jibi za'a fara ko? Gaskiya ya kamata gobe ki san yadda zakiyi maganar date din nan. I really want to see you wallahi" nace "insha Allah tomorrow zamu fita. Kar ka manta da kwalliyar da ka yi min alkawari, I want to see it" yace "baki da problem. Thanks , Love"

Episode Sixty Six : The Wedding

So...... The long awaited episode is here.
Monday
Washegari tun Mommy tana dakinta kafin ta fito naje na sameta, na gaisheta ta amsa. Sai kuma nayi shiru, ta kalleni tace "akwai abinda kike so ne?" Na danyi shiru ina tsoron kar ta hanani, tace "in ba zaki yi magana ba I have so many things to do" nace "Mommy dama zamu dan fita ne in an jima da Sultan" tace "in an jima kamar yaushe kenan?" Nace "kamar bayan magrib" tace "duk tsahon ranar nan bata ishe ku ku fita ba sai da daddare?" Nayi shiru a raina ina cewa 'shikenan, baza ta barni ba' tace "kun san dai gidan nan a cike yake da 'yan sa'ido da tsegumi bana don ku jawo mana wata maganar kuma" nace "to Mommy" tace "Allah ya kaimu, kuje, amma duk inda kukaje kar ku kai karfe goma" na ji wani dadi a raina, da sauri nace "thank you mother" ta harare ni, ni dai na tashi na fita tun kafin ta chanza ra'ayi. Bayan munyi break muka tafi saloon akayi mana gyaran gashi, kusan duk 'yammatan tare muka tafi har Hafsat, acan akayi mana manicure da pedicure, bamu dawo ba sai la'asar. Tun la'asar Sultan ya kira ni yace mu hadu acan. Naji haushin me ya saka ba zaizo ya dauke ni ba. Ina yin sallar magrib nayi wanka na dauko wani bakin material dina da aka dinka min a cikin kayan fitar biki na saka, riga da skirt ne anyi masa ado da golden, na gyara fuskata da light make up, ni kaina nayi mamakin irin kyan da nayi, na dauko golden mayafi karami nayi rolling, mayafin ya sauko ya rufe kirjina, na fesa turare na fita, dakin Mommy na fara shiga na ce mata na tafi, ta kalle ni sama da kasa tace "wannan mayafin yayi karami, ki daura dankwalin kayan sai ki saka babban mayafi, nace "yes mother" na koma dakina na dauko dan kwalin ina kallonsa, ni ban iya daurin dankwali ba shi yasa da wahala kagan ni da dankwali sai dai inyi rolling mayafi. Dole na nemo Amina, nan ta sakani a gaba wai sai ta kara min kwalliya wai wacce nayi tayi kadan, ta zauna ta tsara min kwalliya sannan tayi min daurin dankwalin shima, ina kallon kaina naga kamar ba ni ba, na juyo nace mata "Amina ba'a fara bikin ba fa, wannan kalliyar ai sai mutane suyi ta kallona" tace "to zauna kar mutane su kalle ki, ke da ba'a yi miki abin arziki" nace "thank you" ta kofar baya na fita, motar Mommy na gani a farko dan haka ita na shiga. Wajan 7:30 na isa Hilton, na kira sultan a waya yace "am sorry love, ki shiga nayi mana reserving table, gani nan zuwa, ki bani five minutes" na sake jin haushi nace "yanzu ni da nake mace ni zan je in jira ka? Maimakon ace already kana jira na acan?" Ji nayi bai wani damu da bacin raina ba yace "Sorry, yanzu ba zaki gane ba sai nazo tukunna" na kashe wayar ina tsaki a raina, na shiga ciki.
Ina shiga naga wata waitress tazo ta tare ni ta tayi min jagora zuwa wani table a can corner din gurin, ga mamaki na sai naga the same table ne da muka zauna ranar da muka hadu. Na zauna akan the same seat din da na zauna ina kallon bakin kofa. A take na fahimci abinda sultan yake nufi, so yake abin yayi looking exactly kamar ranar da muka hadu, nayi murmushi, wannan shine dalilin da yasa yayi insisting in taho ni kadai kuma yace in shigo in jira shi, na kalli wajan naga babu abinda ya chanza. Ina zaune kawai naga waitress ta kawo min tea ta ajiye, na sake murmushi, wato ya tuno da tean da nake sha san da ya shigo. Na dauki tea din na fara kurba ina tina ranar, ranar bridal shower din Hafsat, Munir ya takura min, kawayen mu ma sun takura min da tambayar ina Ibrahim, I was so pissed up a lokacin na fito kawai na taho nan saboda ina son inji ni ni kadai, ashe destiny ne yake kirana. Na kai cup din tea din bakina zan kurba kenan na hangoshi ya shigo, kasa shan tean nayi na ajiye cup din tare da sakin baki ina kallonsa. Dark blue wandone a jikin sa three quarter da kuma light brown body hug short sleeved shirt, rigar tayi squeezing. Exactly kayan da suke jikin sa ranar da na fara ganin sa, gashin kansa a hargitse. Ya dan tsaya a bakin kofar yana karewa gurin kallo hannunsa a cikin aljihunsa. Tsayuwar da yayi exactly yadda na zana shi a project dina, except for murmushin da yake yi. Ya juyo ya kalli side din da nake zaune. Idon mu suka hadu, bansan sanda na mike tsaye daga zaman da nake ba. A hankali ya fara tahowa inda nake tsaye fuskarsa da murmushi, yace "Assalamu Alaikum" ban iya na amsa masa ba, yace "Mind if I join?" Sai a lokacin na rufe bakina na gyada masa kai ina dariya kasa kasa, maimakon ya zauna sai ya zagayo bayana ya rike min kujerata na zauna first sannan ya zagaya ya zauna a exact kujerar da ya zauna almost two years ago. Yana kallona yace "kinyi more than kyau, bama zan iya fassara yadda kike looking ba, kawai dai kinyi kyau" nayi dariya tare da dan shagwabe fuska nace "ba kai bane kace zakayi min special kwalliya shine nima kasa ni nayi kwalliya ashe kai abinda kake planning da ban" yayi dariya yace "kar dai kice kwalliya ta bata burge ki ba, da ita fa nazo na siye zuciyar ki" nace "waye yace maka a lokacin ka sayi zuciyata?" Yace "to yaushe na saya?" Na danyi tunani sannan Nace "nima ban sani ba. Kawai dai naga ta zama taka ce, ban masan sanda aka yi ciniki ba ballantana in san sanda na sayar maka" yace "hummm, ni kuma kinsan sanda kika sayi tawa? The first moment dana dora idona a kanki nasan cewa I am hooked for life, tun daga

Please Login or Register in order to submit comment