Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

leka palon naga Amira na rike kugu nace " au dama ke ce bakuwar zaki wani zauna a palo? Ki tashi ki cire wannan mayafin ki taho kitchen" tana dariya ta ajiye mayafin ta ta taho, a kitchen din muka gaisa sosai sannan ta gaisa da Asma'u da sauran yarana, na lura tayi sanyi sosai kuma naji ina tausayinta har cikin raina. Sai da muka kusa kammala aikin sannan muka bar su Asma'u muka dawo palo muka zauna, muka fara hira, mostly hirar da yadda kawancen mu yake, da yadda tayi ta bani shawara akan sultan ni kuma na rufe idona naki dauka, wani gurin muyi dariya wani kuma muyi jimami, ina sane na sako mata zancen Ibrahim da labarin yanzu Amina yake nema, ina maganar ina kallon fuskarta inga yadda zata dauki maganar amma sai naga babu wani chanji a fuskarta sai ma alamar tana taya Amina murna. Muna nan zaune muka ji sallama, Amira tayi saurin daukan mayafinta ta yafa, a raina nace 'har yanzu ustazancin yana nan kenan' Abbas ne ya shigo cin abinci, da yake shima yanzu anan yake cin abinci tunda har yanzu bai huce da Hajiya ba. Ina sane nace Amira tayi serving dinsa, ta harare ni na langwabar da kai na nuna mata cikina, ta tashi ta bishi dining tana serving dinsa, ina jiyo maganganun su, dan Abbas akwai surutu kamar fa'iza, saratu ce mai shiru shiru dinsu. Bayan ta gama ta dawo gurina muka cigaba da hirar mu, sam ban bata labarin komai da yake wakana a rayuwar mu da sultan ba saboda ance once biting twice shy, bayan Abbas ya tafi muma muka je muka ci abinci tare sannan ta tafi gida. Bata jima da tafiya ba sai ga Abbas ya dawo, ina ganinsa nace a raina tarko na yayi kamu kenan, yazo ya zauna yana shafa kai yace "babbar yaya wacece dazu tazo gidan nan?" Na hade rai amma cikin wasa nace "ina ruwanka da ita?" Yace "please ki dan shigar dani mana" na wara hannuna nace "a nawa? Kasan ni bana aikin banza" yace "zanyi ta yi miki addu'ah kullum idan nayi sallah. Please" nace "ni ba zan shigar da kai ba, zan dai baka number dinta ka je ka shigar da kanka" yayi godiya ya karbi number din ya fita. Asma'u tana daga kitchen ta leko tace "dama nasan za'a rina, wai an saci zanin mahaukaciya" muka yi dariya tare.
Na kira Hafsat na gaya mata an bar ni zuwa, nace ta gaya wa Ummee cewa zanzo amma ni kadai, anan take gaya min cewa khairat ta hana ta komawa gidan su zayed tun da tasan dangantakata da ita, anan gidan yanzu take sai dai zayed yazo gurinta, tace min itama tana murnar zuwan nawa nan da sati daya. Satin da sauri yazo, tun kwana uku tafiya ta na fara hada kaya, sultan kam sai kumbura yake yi, kullum sai ya tsara min yadda tafiyar zata kasance, yace gurin Hafsat zan sauka, sau daya zanje gurin Ummee, in naga babu fuska kar in sake zuwa, ni dai to kawai nake ce masa amma ni na gama plan dina, ana gobe tafiyata naje gida na wuni gurin Mommy, Daddy dama baya nan lokacin, na gaya wa Mommy komai yadda ake ciki da kuma plan din da nayi, farko ta fahimta kuma ta yarda, sai kuma daga baya ta zama alarmed, "kin ga neman takawa dama suke yi suyi masa hukuncin sace musu 'yarsu da yayi, kar kije kuma su kama ki ke" nayi dariya nace "Mommy ba abinda zasu yi min, shekara talatin fa da yin abin, besides, gurin Hafsat zanje". Sai dare sultan yazo daukana, tun a mota yake cewa shi ya akayi ya bar ni wannan tafiyar ne, a ranar yadda muka ga dare haka muka ga rana, sultan yayi nadamar bari na yafi cikin charbi, sai kara jaddada min yake yi "three days kawai, babu kari, make sure wayarki a kunne take all the time, in kinga zasu daga miki kai ko su Hafsan ne ma ki rabu dasu kije ki kama hotel ki kwana da safe kiyi tahowar ki" ni dai sai to kawai nakr ce masa. Da safe saura kadan ya saka inyi missing plight kuma nasan yana sane, so yake in fasa tafiyar amma naki. Muna zuwa airport yace "ko dai ince na fasa barinki tafiyar nan ne?" Nace "nasan ma ba zaka fadi haka ba" yace "saboda me kika ce haka?" Nace "because you are a man of your words" ya girgiza kai kawai ya fito min da akwatina, har sai da aka fara cewa za'a rufe kofar jirgi sannan sultan ya sake ni na tafi. Ina shiga jirgin ina zama naji na fara missing dinsa, na dauko waya na kira shi nace "already missing you Darling" yace "then come down ki fasa tafiyar nan please" nace "no, na riga nayi niyyar, just pray for me" ya kashe wayar bai ce min komai ba.
Wajan asr jirgin mu ya sauka a birnin Riyadh. Ina fita reception na hango Hafsat da Zayed suna jirana, na karasa da sauri na rungume Hafsat da naga ta kara kiba da kyau, jin dadi sosai ya bayyana a tare da ita, Zayed ya karbi akwatina yana cewa "welcome to my home town sister In-law, kin zama in-law dina ta two sides" muka yi dariya a tare. Muna shiga mota yace "gidan khaloo (Aunty) zamu je ko?" Nace masa "eh" ni dai duk ina feeling nervous, ban san ya zata karbe ni ba, what if sultan is right? What if ta wulakanta ni?" A hanya Hafsat take ce min wai khairat har fenti ta saka aka sakewa gidan ta na tara ta, wai yau tun safe take kitchen tana girki, ta rasa me zata dafa min, jiya kuma sam bata yi bacci ba saboda anticipation. Wannan maganar ce ta dan kwantar min da hankali.
Tun daga gate din gidan nasan an ajiye dukiya a gidan nan. Ya hadu karshen haduwa, dan bazan iya tsayawa fassara haduwar sa ba. Ni dai kawai bin su Hafsat nake a baya da sakakken baki ina kallo, mun wuce palo sunfi uku sannan muka zo inda suka ce min shine palon ta, zayed ya bude kofar da sallama sai kuma yaja baya ya bani guri yayi min alama da in shiga, na hadiye yawu da kyar sannan na daga labule na shiga da sallama. Tana zaune akan kujerar da take facing din kofa, bakar abaya ce a jikinta da rolling irin na larabawa, gashin kanta ya fito ta kasan mayafinta ya sauka har gadon bayanta, ta saka hannayenta a tsakanin cinyoyinta, ta bude idanuwanta tana kallona, she looks more like sultan in reality than in the picture. Kallo daya nayi mata naga extreme of innocence a fuskarta. Ta mike tsaye tana jujjuya hannunta, idonta ya sauka akan dan karamin cikina, naga kwalla ta fara taruwa a idonta, ta kasa cewa komai, na karasa shiga palon a hankali, kafin inyi magana wayata tayi kara, ina dubawa naga sultan, na dauka da sallama, bai amsa ba yace "kin fasa yin kwana ukun, na duba naga gobe da akwai jirgin safe daga nan Riyadh zai dawo Nigeria, ki biyo shi ki dawo" nace masa "an gama" na katse kiran, na kashe wayar gaba daya na saka ta a jaka ta. A hankali tace "Sultan ne" Nace "eh shine" Tace "he is already regretting letting you come ko?" Nace "yes" take naga fuskarta ta chanja kalar tashin hankali, tace "fushi yake yi dani and I don't blame him, sai dai bansan me zanyi masa ya hakura ba. Cewa yayi ki koma Nigeria ko?" Nace "yes. But if he wants me, he will have to come and get me?" A hankali naga damuwar fuskarta tana washewa, farin ciki yana replacing, ta karaso gurina da sauri ta rungume ni tace "thank you my daughter".
Afuwan jiya kun jini shiru, abubuwa ne suka dan sha kaina amma lafiya lau nake Alhamdulillah, nagode da kulawarku sosai. I feel loved.

MAIMOON
By
Maman Maama
Episode Eighty eight :Khairat
Ta sake ni ta kama hannuna muka karasa kan kujera, ta zaunar dani sannan ta zauna a kusa dani still tana rike da hannuna, tana min murmushi from ear to ear, na dan sunkuyar da kaina saboda kallon da take min, ta saka hannu ta dago habata, tace "masha Allah, you my dear are very beautiful" naji kunyarta na sunkuyar da kaina. Ta dora hannunta akan cikina tana dariya excitedly, tace "wata nawa?" Ni dai duk kunya ta ishe ni, na kasa bata amsa, tace tana karkata kai "please kar ki yi min haka mana, talk to me, ki dauke ni kamar kawar ki kinji?" Na gyada mata kai, ta sake dora hannunta akan cikina tace "wata nawa?" Ina murmushi nace "almost four" ga mamaki na kawai sai naji babyn yayi motsi, itama taji a hannunta, ai kuwa murna kamar me, tace "shima yasan yazo gida, welcome home my little love" ni dai sai taya ta dariyar ta nake yi, sai da ta gama murnarta sannan tace "how is he?" Na san wa take nufi da he din, to amma na kasa sanin ta ina zan fara bawa uwa labarin danta wanda rabonta dashi shekara talatin? Jin bance komai ba yasa tace "ya kamannin sa suke yanzu" na dago kai na kalle ta nace "you just need to look in the mirror, he looks just like you" ta fadada murmushinta tace "but he has his father's built and temper" nace "yes, he do" ta sake juyo wa tana kallona tace "har yanzu yana da hot temper kenan? Sanda yana baby in yana son abu na hana shi sai yayi ta buga kansa a jikin bango, in na bashi abin ma daga baya sai ya karba ya jefar wai yayi zuciya" nayi murmushi, ta sake cewa "tell me menene yafi so duk duniya" na san me yafi so duk duniya amma am not going to tell her that, dan haka nace "food" ta bude baki da mamaki tace "har yanzu bai daina son abinci ba? Sultan har cikin dare yake tashi yaci abinci, sanda ina feeding dinsa sai da na hada masa da madara saboda tsabar cin sa, da ya fara yawo kuma babban abincin da yake so shine nama, daga nan sai fresh milk" nace mata "har yanzu ma, yana son nama sosai" tace "is he still making troubles? He was a trouble maker as a baby, yana da kiriniya sosai dan sanda ya fara crowling duk abinda nake so sai dai in dora a sama, a saman ma in ya samu abin takawa sai ya dauko, yayi ta faduwa yana jin ciwo amma sai ya koma" ina jinta ina ta murmushi a raina ina hango baby sultan yana ta kiriniya da wannan thick gashin kan nasa, tace "please tell me all about him, nuna min pictures dinsa in gani" na dauko waya ta na zare sim card din dan kada sultan ya kira, na kunna na nemo mata wani hoton sultan wanda yake looking very good and decent, na mika mata, tana karba tasa hannu ta rufe bakinta tace "Ya Allah, he is so grown up and handsome" sai kuma hawaye ya fara zuba a idonta "my son, my darling baby" daga hoton dana nuna mata maimakon ta dawo min da waya ta sai ta fara scrolling tana kallon pictures din mu, mostly na sultan ne da ni, sai few na yan gidan mu, in tazo kan wanda bata gane ba sai ta nuna min ta tambaye ni in bata amsa, har yanzu hawaye bai daina zuba a idonta ba, kuka take kuma tana dariya duk ita kadai, ni dai ji nake kamar in karbe waya ta saboda da akwai hotunan da bai kamata ta gani ba, amma ita babu ruwanta, kalli take yi kawai tana dariya, ta dago kai ta kalleni tace "he really loves you, I can already see it in his eyes" na gyda mata kai nace "yes, he does" sai can kuma ta ajiye wayar tace "oh dear, ko ruwa ban baki kin sha ba" nayi dariya kawai bance komai ba, hannuna ta kama ta jani har dakin da na fahimci cewa bedroom dinta ne, ni dai kawai kallonta nake yi, she is really beautiful and amazing, in ka ganta daga nesa ba zaka taba tsammanin babba bace ba, sai in kun zauna da ita ka kalle ta sosai sannan zaka ga shekarunta a fuskarta, jikinta kam babu alamar girma a tare dashi.
Anan dakin nayi sallah, ina idarwa sai ga Hafsat tazo kirana in fito muci abinci, sai a lokacin na kalli Hafsat sosai, nace "yanzu Hafsat dama ciki ne dake baki gaya min ba" ta murguda min baki, nace "yanzu khairat din watanta nawa har zaki ji mata sibling" tace "ke watanki nawa aka haifi faruk? Ni wata na nawa aka haife ki? Me ya ragu a jikin mu? Ko wani mugun ciwo babu wanda yake dashi a cikin mu, itama khairat babu abinda zai same ta" na bita muka tafi ina tambayar ta "wai duk wannan gidan ita kadai take zaune?" Tace "sai ma'aikata, sai kuma 'yan'uwa duk wanda yake so zai iya zuwa ya zauna" ni dai har yanzu kallon gidan nake yi, Hafsat ta dan dakeni tace "kar ki bamu kunya mana, ke tsiya ta dake kyauyanci" muna zuwa dining naga an cika shi da kayan abinci, nan take kwadayi na ya tashi, ina zama Ummee ta taso ta fara serving dina, komai sai da ta zuba min tace dan ni ta dafa dan haka komai sai naci, yi take kamar zata bani a baki, ni kuwa na saki jiki nayi ta zurin abinci, sai kuma naji ina missing sultan, ina ma dai yana gurin nan da sai dai a dauke shi saboda yawan abincin da zai ci. Muna gama ci Hafsat tace min ta kai min akwatina dakin da take, nan take Ummee ta bata rai tace zayed yaje ya dauko ya dawo dashi dakinta, tace yau a gado daya zamu kwana babu mai raba ta dani. Bayan mun tattare gurin muka tashi muka zagaya gidan, ita take tayi mana bayanin ko ina na gidan. Kafin mu gama na gaji sosai, dama ga gajiyar hanya, muna shiga mukayi sallama da Hafsat muka tafi dakin ummee, ina zuwa tace min inyi wanka inyi sallah sai in kwanta, ai kuwa hakan nayi dan Sallar da kyar nayi ta dan idona har rufe wa yake yi saboda bacci, amma ina kwanciya sai na tuna sultan, na tabbatar yau ba zai yi bacci ba, bana nan kuma na kashe wayata ballan tana ko murya ta yaji. Nima sosai naji ina missing dinsa, kamar in dauki wayata in kira shi kuma sai na daure zuciya ta, na runtse idona ina addu'ar bacci yazo amma ina, Sultan kawai nake so. Ranar ba karamin yaki nayi ba kafin in samu bacci ya dauke ni. Ban farka ba sai kusan assuba, na tashi zaune naga ummee a kusa dani tana bacci, abinda ya fara fado min a raina shine sultan, ko zai iya tashi sallar asuba yau? Dan nasan ba bacci zai yi ba kar yazo kuma yayi missing masallaci. Na tashi nayo alwala nazo na dauki alqurnin dana gani a gurin sallah na fara karantawa a hankali dan kar in tashi ummee, har sai da naji anyi assalatu sannan na tashe ta ni kuma na tayar da sallah. Da safe duk jikina babu dadi, na dauki waya ta da niyyar kiran sultan yafi a kirga ina ajiyewa, daga karshe dai na bawa Hafsat sim card dina nace to nace ta bani kar ta bani, tana dariya tace "ai kuwa ba zan baki ba ko zakiyi kukan jini". Tare muka shiga kitchen da Ummee, she is an amazing cook, muna aiki muna hira, nan na bata labarin cewa kafin inyi aure ban iya girki ba, sai daga baya na koya, ai kuwa tayi min alkawarin sai ta mayar dani kwararriya a girki. A kitchen din muka zuba abincin a kwano daya muka ci, ban san me yasa ba kawai naji na saki jikina da ita, ji nake yi kamar dama can nasan ta all my life.
Bayan nayi sallar azahar, ina zaune a dakin ummee ina tunanin ko me sultan yake yi yanzu? Sai ga ummee ta shigo, ta samu guri ta zauna a bakin gado, na dan juyo na kalleta tayi min murmushi. Tace " maimunatu so nake ki bani labarin sultan, tell me all about him, I want to know everything bana son ki boye min komai" na gyara zama na ina tunanin ta ina zan fara ne, she is his mother, she deserves to know everything. Nan na fara daga labarin da Takawa ya bamu na abinda ya faru bayan an dauke ta daga gidan, na gaya mata abinda sarki abdallah yayi, tun anan ta fara sharar hawaye, na dora da bata labarin rayuwar da sultan yayi tare da mahaifinsa, ban boye mata komai ba har zamansa a gidan kangararru da rayuwarsa a America, na gaya mata past drinking habit din sultan amma na tabbatar mata cewa yanzu ya daina, amma ban gaya mata dalilin fara shan giyar tasa na, na gaya mata haduwata dashi da yadda Daddy ya dauko shi ya dawo dashi gidan mu, amma ban gaya mata kiyayyar da Mommy tayi masa faga farko ba, na bata labarin auren mu da kuma sanadin karyewar asirin Takawa zuwa halin da muke ciki a yanzu, na dora da cewa "Sultan is emotionally not stable, shi yasa yaki zuwa, har yanzu kullum yana tunanin cewa mutane basa sonsa, da kyar ya yadda cewa Takawa yana sonsa da gaske, kema kuma yana tunanin ba sonsa kike ba saboda yana ganin kinyi abundaning dinsa tsahon shekaru baki taba neman sa ba, he is just scared to get his heart broken" bata cemin komai va saboda kukan da take yi, ta tashi ta fita daga dakin. She needed to be alone and I understand. Har bayan la'asar ban kuma ganin ta ba. Zayed yazo ya dauke mu ni da Hafsat muka tafi yawo, ya nuna min birnin Riyadh, garin ya hadu fiye da tunani na, lallai larabawa karshe ne gurin dukiya, ga tsari ga doka. Da magrib muka je gidan su Zayed na gaishe su, sun karbe ni sosai a matsayin kanwar Hafsat, Zayed yace mu bar Khairat ta gaya musu da kanta when she is good and ready. Muna komawa gidan Ummee muka same ta ita kadai a zaune a palon ta, akan kujerar dana sameta jiya, idonta akan kofa, na lura ta dan rame kadan akan jiya. Muna shigowa tayi mana murmushi, tace tana kallona "na dauka kin gudu" na karasa da sauri nace mata "I will never" .
Da daddare sai ka wayar sultan a wayar Hafsat, ta nuna min screen din, na daga kafada, ta dauka da sallama, daga ganin yadda Hafsat take yamutsa fuska nasan masifa yake mata, sai da ta barshi ya gama sannan tace "kana magana da Hafsat ne ba da maimuna ba" sun jima suna ta rigima daga alama cewa yake ta bani wayar ita kuma taki, da ta gaji ta kashe wayar tana kallona "he is really pissed off, yana neman ya kashe min dodon kunne" and my heart went out to sultan, yana can nasan ya hargitsa gidan mu gaba daya, poor Amir shi zaifi kowa dandanar zafin sultan. I hate hurting sultan amma shi zuma ne sai da wuta, he will never come to his mother in ba haka nayi masa ba. Duk hirar da muke yi Ummee tana jin mu amma tayi shiru, she seems deeply in thoughts. Sai bayan munyi sallama da Hafsat naje nayi shirin kwanciya na kwanta ina ta tunanin sultan sai gata ta shigo, ta zauna a bakin gado tana kallona tace "yana son yasan abinda ya hanani zuwa wajansa ko? Yana son yasan ko ina sonsa ko bana son sa? To ga labari zan baki ki gaya masa" na tashi zaune na jingina da jikin frame din gadon ina sauraron ta. Tace "bayan an dauko ni daga Nigeria, ban taho da komai ba, babu miji babu da, bani da ko hoton sa, daga ni sai kayan bacci a jikina sai abaya da hijab, babu wanda zai gane halinda na shiga a lokacin sai uwar da aka raba da mijinta da kuma dan karamin danta, suna farkon duniya ita tana karshe. Nayi kuka kamar raina zai fita, gaba daya family aka taru a kaina telling me cewa na basu mamaki, na zubar musu da mutuncin su a cikin jama'ar, saboda ba karamin abun kunya bane ace 'yarka budurwa ta gudu da saurayi, kowa abinda zai fada daban. Gashi an samu matsala da familyn wanda aka yi niyyar hadamu aure da shi. Aka sake sakani a daki aka rufe. Babu abinda yayi keeping dina alive a lokacin shine maganar sadiq da yace he will come for me, so I waited, not patiently but I waited. Kwana daya sadiq bai zo ba kwana na biyu shiru, a kwana na ukun ina dakina ina aikin dana saba wato kuka sai ga ummina tazo tayi kirana, ina zuwa palo na samu babana da uncle dina a zazzaune, na gaishe su sai suka miko min takarda suka ce daga Nigeria, da sauri na da bude ina so inji labarin Sadiq da Sultan amma me zan gani, wasika ce daga Sadiq cewa ya sake ni, bai yi stating dalili ba kawai dai ya sakeni, in his own handwriting, after all what we went through together, after irin rabuwar da mukayi da kuma irin alkawarin da yayi min cewa he will come for me, amma abinda na samu daga gare shi shine saki. I list everything, the trust of my family, my dignity, my husband and my son. I was totally broken. Na shirya akan lallai sai naje Nigeria na tambayi sadiq dalilin da yasa yayi min abinda yayi min, kuma in karbo dana, amma family na suna ganin yin hakan bashi da amfani, ya wulakanta ni ya yaudare ni ya rabani da iyayena, sannan kuma ya sake ni, to me zanje inyi masa kuma, sunce matsoraci ne shi, nusari wanda ba zai iya fighting for his family ba. Na nuna musu ni ba ta sadiq nake yi ba ta Sultan nake yi, amma still suka hana ni xuwa, abinda ummi na tace min shine inna je ma ba bani shi zasuyi ba, kuma nasan gaskiya ta fada ba zasu bani shiba, ta gaya min cewa inna dauko shi ba taho dashi gurina what kind of life zan bashi a matsayin dan mace babu uba? Duk abinda mutane suke fada akaina cewa yawon banza na tafi sai su tabbatar kenan in suka ganni da 'da babu uba, tace duk tsahon shekaru sultan shi zai neme ni da kansa. Duk na nuna musu kamar na yarda amma suna sakin jiki dani na gudu, unlucky for me wani friend din babana ya ganni a airport ya kira waya ya fada, aka zo aka sake mayar dani gida, nan take magana ta fara fita a cikin mutane, cewa khairat 'yar faisal abdallah ta fara yawon banza, ance na gudu da saurayi shekara uku sannan aka samo ni, fada da nasiha babu irin wadda ba'a yi min ba amma ni hankali na yana Nigeria, na gwada guduwa yafi a kirga, daga baya family na suka hadu suka yanke shawara, aka yi bannin dina daga fita daga kasar saudiyya gaba daya, ko baje airport da zarar anyi thumb printing dina shikenan ba za'a barni in shiga jirgi ba. Tun daga lokacin har yau ban taba taka kafata outside Saudi Arabia ba. I tried everything i can to get to sultan, I wrote him letters but they all turned back. My family made sure sunyi cutting duk wata hanya da zanyi contacting Nigeria. Su a ganinsu gurin sadiq nake son komawa, inna yi musu maganar sultan sai suce min zai neme ni da kansa. Da addu'ar da nasiha na fara hakura da zuwa Nigeria, amma ko dai da rana daya ban taba dauke hankali na daga kan sultan ba. Na yadda da abinda ummi na take gaya min cewa sultan

Please Login or Register in order to submit comment