You Cannot Download this book untill you login but you can read it .
Login Register
hakan zanyi. But not Amir, sai dai in sami wani, Amir hasn't been himself lately" naji babu dadi nace "why? Me ya faru dashi?" Yace "akan wata yarinya ne da yake nema. Sunanta Aisha, 'yar maiduguri ce, tazo bikin cousin dinta garin nan suka hadu suka fara soyayya, bayan ta koma gida har maiduguri yake zuwa gurinta, wajan shekarar su daya kenan tare. To yanzu sai iyayenta suka ce ta fito da miji ita kuma tace shi take so, aka aiko wa aunty din ta tanan garin akan ta bincika waye shi, the first thing da tayi finding out shine babu wanda yasan iyayensa, a kofar orphanage aka tsince shi ko cibiyarsa ba'a yanke ba. Suna jin haka suka aiko masa cewa kar ya sake zuwa gurin 'yarsu, su ba zasu bada 'yarsu ga wanda bashi da asali ba. And that break him down, bai taba nuna damuwarsa ga rashin iyayensa ba sai yanzu, lokuta da yawa yana mayar da maganar kamar wasa amma yanzu he is devastated, it hurts me that there is nothing I can do for him" naji kamar zanyi kuka, naji tausayin Amir sosai, how can some parents be so cruel, ki haifi da da kanki sannan ki je ki jefar dashi? Shi yaron menene laifinsa? Shi yace ki haife shi? Ana samu kuma har da masu kashewa, wadansu su jefa a toilet, ni dai a ganina wannan shine extreme of cruelty. Allah ya shirya mu baki daya.
Nace "but da na dauka yana son Amira ne ai, har na fara tunanin idan abin yazo zan yiwa Daddy magana ya shigar masa tunda akwai sanayya abin zai zo da sauki" Sultan yace "gaskiya bai taba yi min maganar Amira ba, kullum ina tsokanarsa akanta saboda inji ta bakinsa amma bai taba cewa komai ba, wannan Aishan dai ita ce a gabansa" nace "Allah sarki Amir, Allah ya kawo masa mafita" yace "Ameen".
Tun daga lokacin Sultan ya fara zuwa fada duk ranar Fridays, ranar farko da zai je haka na zauna nayi ta addu'ar Allah ya dora shi akan mahaifinsa kar ya wulakanta shi a cikin mutane, dan nasan zuciyar Sultan, in dai Takawa ya kore shi to kuwa ba zai sake zuwa ba, tunda yanzun ma ba wai a son ransa yaje ba. Cikin ikon Allah kuwa babu abinda ya faru, sai dai kamar kullum da ya gaishe shi bai amsa ba, Sultan bai nuna ya damu ba ya gaishe da sauran mutane ya dan zauna for one hour sannan ya tashi yayi tafiyar sa. Kiri kiri ya hango bacin rai a fuskar Abbas amma bai kula shi ba, sai ya nuna kamar bai san yana yi ba. Ranar ina zaune ina jiran sultan ya dawo daga office sai ga sako daga Abbas, alkyabba da rawani, wai a bawa sultan inji shi a ce masa in dai yana son zaman fada he should dress like dan fada, nasan tsokanar fada ne, dan haka na nuna wa dan aiken kamar Sultan yana dakin sa, na shiga na fito na dawo masa da kayan nace sultan yace a gaya wa Abbas ya gode sosai, amma ya riga yayo order nasa kayan daga saudiyya, idan sun iso ma har shi zai aikowa, tunda dai hakkin yaya ne ya jagoranci gida ya kuma kula da kannensa. Ni nasan na kunna wuta a zuciyar Abbas ranar nan, Sultan yana zuwa na bashi labarin abinda ya faru, muka yi ta dariya tare dashi na kuma cigaba da rokon sa akan dan Allah duk abinda Abbas zai yi masa kar ya kula shi, dariya kawai sultan yayi bai ce komai ba.
A kwana a tashi na fahimci shigar ciki a jikina, sam babu laulayi dan ko sau daya ban taba amai ba ko zazzabi, lokacin period dina yana zuwa naga bata zo ba dan haka na tabbatar da zargina, Sultan kam da yaga babu period shi murnar sa ta daban yake yi dan kwata kwata banga alamar yayi linking abin da ciki ba. Babu laulayi a ciki na sai dan karen kwadayi, kullum ina kitchen, in soya wancan inci, in gasa wannan inci, in tafasa wannan inci. Tunda sultan baya wuni a gida dan haka sam bai san me nake yi ba, da daddare kuwa yawo nake masa in gudu daga dakinsa in tafi kitchen in ci abinda zanci in dawo. Ina ta tunanin yadda zan yi in gaya masa, duk da bamu taba yin zancen haihuwa dashi ba amma nasan yadda yake son 'ya'yansa na orphanage dan haka nasan Allah ne kadai yasan irin son da zai yiwa nasa dan ko 'yar.
Ranar wata Wednesday tun da safe nake son chocolate, sauran wadda nake da ita a gida na shanye amma kamar tayar min da kwadayi ta kuma yi, sultan yana dawo wa daga office na saka shi a gaba sai ya kaini mall na sayo chocolate, da kyar na barshi yayi wanka ya dan huta, ana yin sallar magrib na dauko bakar after dress na dora akan riga da zanin jikina, nayi rolling viel na dauki key din mota na tsaya ina kallon Sultan, ya langwabe kai yace "please Love, ki bari muci abinci mana" na girgiza kai nace "in mun dawo ma ci, yanzu fa zamu je mu dawo, ko 30 minutes ba za muyi ba. Yayi ajjiyar zuciya ya mike yace " amma ki sani, ina binki bashi, in mun dawo zan karba" a raina nace 'oho dai, ko ka kaini ko baka kaini ba dama nasan sai ka karba din'. Muna fita nace "sahad zamu je" ya dan bata rai yace "why? Kin san bana son zuwa sahad, it is too crowded" nace "naga yafi kusa ne ai, kuma ba wani special abu zan saya ba kawai chocolate ne" ya daga kafada yace "OK, bara muje can din".
Ibrahim
Tun da safe yace da Amina zai zo gurinta da yamma, dan haka yana tashi daga office gida ya tafi yayi wanka ya shirya, yana yin sallar magrib ya fito ya dau hanyar gidan su, yana shan kwanar gidan ya hango ta tana tahowa bakin titi, bakar after dress ce a jikin ta, tayi rolling mayafin rigar, kamar kullum duk sanda ya ganta sai gabansa ya fadi saboda gani yake kamar Moon ce sai ta matso kusa sai yaga ba ita bace. Yayi slowing down ya barta ta karaso inda yake sannan ya sauke glass dinsa yace "ina zuwa ne haka?" Ta dan tsorata kadan, yayi dariya ita kuma ta bata rai "tun dazu kace min zaka zo ina ta jiranka shiru" ya hada hannuwansa biyu yace "am very sorry, ban tashi da wuri bane ba kuma naga it is already late, shine na tsaya na jira bayan magrib sannan na taho. But ina zaki je kuma?" Ta dan kara bata rai tace "Mommy ce ta aike ni sahad, kuma drivers din duk basa nan" yace "to ga wani drivern yazo, common in" ba musu ta zagaya ta shiga suka tafi. A hanya yace mata "but why sahad? Ba zaki zo gurina kiyi siyayyar ba?" Tayi dariya tace "are you jealous?" Yace "of cause I am" tace "let me tell you why. Shi sahad tsohon guri ne, akwai wasu specific abubuwan da ba'a samu a wani gurin, misali sababbin guri irin naka, sai acan. Dan haka Mommy ta fada min exactly abinda take so bata son substitute, dan haka gwara inje can din direct nasan zan samu" yace "OK, zan kaiki sahad ne kawai saboda inyi proving cewa you are wrong, babu abinda suka fi mu dashi, sai abubuwan da muka fi su dashi ma" tace "OK, we will see". Suna shiga cikin sahad motar su Moon tayi packing suma suka fito duka shiga, amma kowa da side din daya nufa. Ya dauko mata basket suka fara zagaye tare tana duna list din Mommy, ya karbi list din ya duba yayi tsaki yace "babu abinda bani dashi anan wallahi" ta karbi basket din tace "ka ga in kasan zaka dame ni da mita yi tafiyar ka wani gurin, in na gama sai in neme ka" da kamar ba zai tafi ba kuma sai ya tuna cewa a matsayinsa na dan kasuwa ya shigo gurin abokin competition dinsa gwara yayi using chance din ya zagaya yaga abinda suke dashi wanda shi bashi dashi, dan haka ya sakar mata basket din yace "OK, call me when you are done". Ya tafi yana zagaya gurin, har ya fama zagayensa bata kira shi ba, yayi tsaki, su dai mata in suka shiga kasuwa sai ka rasa me sukeyi, shi kuma bai ga abinda wannan gurin yafi nasa ba. Ya juya ya koma ya fara neman ta, ko bata gama bama fita zasuyi, ko me take so suje gurin sa ta dauka.
Moon
Muna shiga direct gurin sweets na tafi, na dauki basket na mika wa sultan ya rike min, na fara chocolate verities iri daban daban ina zubawa a basket din, Sultan kawai kallona yake yi da mamaki yace "wai yaushe kika zama shazumamu ne ban sani ba? Duk wannan chocolate din me zaki yi da ita? A matsayin ki na doctor ai kinsan illar zaki ga lafiyar ki ko?" Na juyo na murguda masa baki na juya na cigaba da abinda nake yi, yace "ni ko? Zaki yi bayani ne in mun koma gida?" Mun jima ina ta diban alawa, in dau wannan in ajiye in koma baya in dauko wata, Sultan ya gaji, kuma ina sane nake kara delaying din mu, a raina ina cewa 'bani kadai zan sha wahalar cikin nan ba kai ma sai kasha' duk kuwa da cewa har yau bai san da cikin ba. Ya ajiye basket din yace "bara in zagaya wajan perfumes, da akwai wani turare da nake ne ma ban sani ba ko zan samu anan" nasan babu wani turare da yake nema, ya gaji ne so yake in ce masa ai na gama mu tafi, na juyo nace masa "OK" ya saki baki da mamaki yana kallona yace "kin yarda in barki anan ke kadai" nace "I am 23 years old, ba zan bata ba" ya juya ya tafi, har yakai karshen lane din ya juyo, nayi masa alamar bye2 ya girgiza kansa ya sha kwana. Na juya ina dariya, a raina ina tunanin maybe tonight in gaya masa labarin cikin nan, I can't wait to see his reaction. Nayi murmushi na cigaba da kwasar sweets dina.
Kamar daga sama naji an kama hannuna an fara jana da sauri, "let's go, babu wani abinda ba zaki samu ba a gurina, menene anan din wanda ni bani dashi?" Duk da banga fuskar wanda ya rike ni ba amma muryar sa ta saka na gane shi, hakan kuma ya saka ni wata irin faduwar gaban da har sai da naji daci a bakina, wani amai naji yana neman taso min, nayi kokarin kwace hannuna amma bai sake ni ba kuma bai kalle ni ba, cikin muryar fada amma kuma cikin rada saboda bana son inyi calling attention din mutane zuwa garemu nace "what are you doing?" Yayi sauri ya sake ni, lokacin har mun kai karshen lane din, a razane yake kallona, hakan ya tabbatar min ba wai yana sane ya aikata abin da yayi ba, murya kasa kasa shima yace "Maimunatu what are you doing here? Am very sorry na dauka Amina ce, tare muka zo da ita kuma itama bakar riga ta saka. Am very sorry" nace "am here with my husband, go away bana son ya gan mu tare" ya dan bata fuska yace "you look scared, why are you scared of your husband, is he mistreating you" by then gaba daya hankali na ya tashi, na juyo da sauri na matsa daga inda yake amma sai ya kuma zagayo wa gaba na, fuskarsa fal da concern, yace "Maimunatu please tell me if you are not OK" numfashi na ne gaba daya naji yana neman daukewa, Sultan na hango a farkon lane din a tsaye, da kwalbar turare a hannun sa, tun daga inda nake na hango jijiyoyi sun fito rado rado a goshinsa, farin idonsa ya kada yayi jajawur light brown din ciki kuma yayi bakikkirin, mara ta ce ta daure kamar zan yi fitsari, a hankali na furta "innalillahi wa inna ilaihir rajiun".
Winter is really coming
Episode Seventy Nine : The Lightening and The Thunder
Ibrahim ya juya shima da sauri yana kallon inda nake kalla, yace "ya salam" yayi two steps gefe, Sultan ya fara takowa a hankali yana tahowa inda muke, idanuwansa a kaina har ya karaso gabana ya tsaya, ko kallon inda Ibrahim yake tsaye bai yi ba, ga mamaki na sai naga yayi murmushi, amma murmushinsa bai rage min ko kadan daga cikin faduwar da gabana yake yi ba sai ma karuwa da yayi, I know that smile very well. Ya miko min turaren hannunsa yace "see, I got it" ban karba ba kuma bance masa komai ba, kawai kallonsa nake yi ina jiran bomb din ya tashi. Ya sali kwalbar turaren ta fadi kasa ta fashe, har yanzu murmushin yakeyi, jajayen idanunwansa har kwalli suke yi, yace "kin gama sayen chocolate din? Naga kamar basket din bai cika ba. Let me help you fill it up, in ma gaba daya sweets din gurin kike so sai in saya miki" a hankali nace "sultan not here, let's go home" yace "oh let's go home? Kin gama kenan ashe, oh na tuna fa ashe dama ba sayen sweets kika zo yi ba kin zo ne ki ganshi, kuma kin riga kin ganshi, mission accomplished, so let's go home" jin maganganunsa nake tamkar wuta a kirjina, na juya na kalli inda Ibrahim yake tsaye naga bayanan, na dawo da ido na kan sultan, yana kallona yace "baya nan ai, ya gudu, ko baki gaji da ganin sa bane inje in kira wo miki shi? Am sure bai bar building din nan ba by now" mutane sun fara tsayawa suna kallon mu, na ajiye basket din hannuna na juya nayi hanyar fita daga gurin, tafiya kawai nake amma bana ganin gaba na sosai, how can Sultan even think that? Babu komai a hannuna dan ko waya ta ban dauko ba ballan tana in hau taxi. Na tsaya a packing space din na rufe fuskata da hannayena ina kokarin dai dai ta numfashi na, kaina ya chunkushe bana iya tunanin komai. Tsayuwar mota naji a gaba na, na bude ido na naga Sultan ya fito daga seat din driver ya zagayo ya bude seat din gaba, ba tare da yace min komai ba ya chusa ni a ciki ya mayar da kofar ya rufe, ya zagaya seat dinsa ya shiga ya ja motar a guje muka bar gurin. Na hadiye dacin da nake yi a bakina nace "how can you even think that Sultan? How can you hurt me like this?" Ba tare da ya kalle ni ba yace "what do you want me to think ehh? Ke kika matsa lallai sai mun fito yanzu and you also insisted sai munzo sahad, wai zaki sayi chocolate, since when did you start eating chocolate? You also kept delaying us unnecessarily. And I also saw you holding hands and whispering to each other. Tell me what do you want me to think?" Da hannu daya yake driving din kuma a guje yake tafiya yana ta overtaking motoci. Na lumshe idona saboda kaina da naji yana bala'in sara wa nace "ya kamata a ce kasan ni by now, Sultan ya kamata a ce by now kasan me zan aikata da kuma menene bazan aikata ba" yace "I tot I know you, but when it comes to him am not sure where I stand. He is your first love, har hawan jini kika samu sanda ya gudu ya barki saboda irin son da kike masa, you waited for him years after years, sanda ya dawo it is already days to our wedding, ko kince kin fasa aure na ma kinsan it is impossible Daddy ya fasa....." Na katse shi nima cikin daga murya nace "duk wannan tsahon lokacin dama abinda kake tunani kenan?" Shima ya daga tasa muryar "what do you want me to think? Kullum mutane suna gaya min you are too good for me, and I also know you are too good for me, you always kept secrets from me..." Na juyo ina facing dinsa sosai nace "kasan dalilin da yasa nake keeping maka secrets? Kasan babban dalilin da yasa tun farko ban baka labarin Ibrahim ba? Because I know you will act exactly the way you are acting now. You always let your temper get in your head and stop you from thinking clearly. Kawai ganina kayi tare dashi, baka tambayeni nayi maka bayani ba, you just conclude and start making accusations, a cikin mutane a cikin kasuwa Sultan, I don't think koma menene nayi I deserve something like that from you, you make a fool of me and you make a fool of yourself" ban taba jin raina ya baci irin na yau ba, sam na manta da mijina nake magana, na koma na kwanta akan kujerar na dafe kaina da nake ji kamar zai tsage gida biyu, I can feel my blood pressure rising. Can kasan muryarsa naji yace "she now calls me a fool" a hankali nace "am sorry. Ban taba jin raina ya baci irin na yau ba, ban taba zaton a ranka za kayi tunanin ina son wani bayan kai ba. Yazo gurina ya rike hannuna ne saboda ya dauka Amina ce, tare suka zo gurin da ita, ba wai da gan gan yayi haka ba, bayan ya gane ni ce ya bani hakuri, he saw that I got scared and was wondering me yasa zan ji tsoron ka" da sauri ya kalle ni yace "are you afraid of me?" Nace "No sultan am not afraid of you, am afraid of your anger. In ranka ya baci you are not yourself, nasan gani na tare dashi zai sa ranka ya baci, I was afraid of what you will do" na dora hannuna akan mara ta nace "Sultan so kake ka zama mijin da matarsa take jin tsoron sa? So kake ka zama uban da 'ya'yansa suke guduwa idan sunji muryarsa?" Na juya na kalleshi amma sai naga hankalinsa baya kaina, he is busy looking at the central mirror, yace "can you now tell me why he is following us? Idan a store yayi miki magana saboda ya dauka Amina ce yanzu kuma ya biyo mu ne saboda ya dauka Amina na dauko a mota ta?" Na juya da sauri na kalli bayan mu, a las, motar Ibrahim ce a bayan tamu, na dawo da hankali na kan Sultan naga his rage is coming back, jan idon daya fara raguwa ya dawo yanzu, ya kara gudun motar, nace "Sultan please stop the car" ko kallo na baiyi ba, na koma na kwanta a kan kujerar na saka hannu daya na dafe kaina dayan kuma na dafe marata da nake jin kamar zata tsage gida biyu, a cikin zuciyata nace "hang in there baby, everything is going to be alright" na fara jero sunanyen Allah a hankali ina neman ya kawo min agaji, na jima a haka sannan na bude idona na kalli inda muke, mun dau hanyar barin gari, har yanzu gudu sultan yake yi a motar, duhu yayi sosai dan haka few motoci ne akan hanyar na juya na sake kallon bayan mu, motar Ibrahim tana bayan mu still, oh dear God, what is Ibrahim thinking, na kalli Sultan nace cikin dasashshiyar murya, "Sultan ko ma menene kake tunanin yi please don't, annabi ya hane mu da yanke hukunci idan muna cikin fushi, Sultan please don't do something da zakayi regretting for the rest of your life" bai kalle ni ba ya miko hannunsa ya saka min seat belt sannan shima ya saka nasa, danshi na fara ji a kasa na na rintse idona hawaye suna bin kuncina, yanzu titin ya zama babu kowa sai motocin mu guda biyu, suddenly Sultan ya daga handbrake din motar, a take ta fara katantanwa a tsakiyar titin, da karfi ta daki motar Ibrahim da take dab damu, motar tasa tayi adungure sau biyu akan titi sannan ta gangara gefen titin, sultan ya taka burki motar mu ta tsaya chak a tsakiyar titin, na juya ina kallon motar Ibrahim da har yanzu take ta adungure, a karshe ta fada cikin wani katon rami dake gefen titin, na juyo na kalli sultan wanda shima motar yake kallo, fuskarsa babu dariya ko kadan, a hankali yace "die, you bastard". Kara na fara ji kamar daga nesa da murya kamar tawa, amma kuma kamar bani nake karar ba, can nesa naji kamar muryar sultan yana kwalla min kira, a hankali na fara ganin duhu a idona, daga baya na daina ganin komai.
A hankali na fara dawowa haiyacina, sanyin AC naji yana ratsani. Nayi kokarin bude idona naji yayi min nauyi sosai, na motsa hannayena kadan ina son in dawo da karfin jikina, muryar Mommy naji tace " Maimoon? Maimunatu kina ji na?" Na dan bude ido na kadan na kalleta, da sauri ta taho ta rike hannuna fuskarta tayi ja alamar tayi kuka, na danyi kokarin yi mata murmushi amma ciwon da kai na yake min yasa murmushin ya zama kamar gyatsine. Na fara duba dakin da nake, asibiti ne, ga drip a hannuna, Mommy tana zaune gefena, Daddy yana tsaye a gefenta, Sultan yana daga can baya ya jingina da jikin bango, tsantsar tashin hankali ne a rubuce a fuskarsa. Motar Ibrahim na tuno yadda tayi ta adungure kafin ta fada cikin ramin. A take hawaye ya fara kwaranyowa daga idona, innalillahi wa inna ilaihirrajiun, Allah kasa mafarki nake yi yanzu za'a ce min ba gaske bane ba, amma yanayin fuskar sultan ka dai ya tabbatar min da cewa ba mafarki nake yi ba, Sultan yayi kisan kai a gaba na, Sultan ya kashe Ibrahim. Allah sarki Ibrahim why? Menene kake tunani me yasa ka biyo mu? Nasan bacin ran daya gani a fuskar sultan da yadda sultan ya fara acting a cikin store din shi ya saka ya biyo mu, he was looking out for me, amma banda abin Ibrahim koma me Sultan zaiyi min ai munfi kusa ni da shi, ballantana ma Sultan babu abinda zai iya yi min. Yanzu shikenan Ibrahim ya bar duniya, because of me, Sultan yayi kisan kai, because of me, na tuna da little Moon, na tuno fuskarta a hotonta dana gani a office din Ibrahim, she looks so happy, yanzu ta zama marainiya babu uwa babu uba because of me, sultan da yake ta faman kula da marayu kullum maganar shi bata wuce ta marayu yau muguwar zuciyarsa da bakin kishinsa ya nawo yayi making marainiya da kansa. Kuka nake yi sosai inajin ciwon kaina yana karuwa. Muryar Mommy naji tana cewa "Haba Moon, kukan menene kuma wannan? Daga rashin lafiya sai kuka? BP dinki ne fa ya hau idan baki daina kuka ba kuma tayaya zai sauka?" Daddy ya kalli sultan yace "kace a kitchen ta fadi ko?" Sultan ya dan kalleni kadan sannan ya gyada kansa ba tare da yayi magana ba, Daddy yace"amma menene zai sa BP dinta yayi wannan hawan haka? Bai taba hawa kamar haka ba" Sultan ya sunkuyar da kansa fuskarsa kamar zai yi kuka amma sultan never cries, Mommy tace "may be zafin kitchen ne dear, dama masu hawan jini ba'a so su ringa kusa da wuta sosai" Daddy ya karaso ya rike hannuna yace "maimunatu kukan me kike yi?" Kafin inyi magana sai ga doctor ya shigo, yana murmushi yace "finally ta farka ashe, ya jikin?" A hankali nace "da sauki" yace "menene kuma na kuka? The pregnancy is intact ai, munyi nasarar tsayar dashi bai fita ba" a tare Mommy da Daddy suka ce "pregnancy?" Na juyo na kalli sultan naga gaba daya fuskarsa tayi fari tas kamar babu jini, ya juyo da sauri ya kalle ni, na kalli su mommy naga gaba daya hankalinsu yana kan doctor yana musu bayani, na gyada masa kai nace "shi yasa nace ina son chocolate din" hannu biyu
Book Chapters
Chapter 49
Chapter 50Chapter 51Chapter 52Chapter 53Chapter 54Chapter 55Chapter 56Chapter 57Chapter 58Chapter 59Chapter 60Chapter 61Chapter 62Chapter 63Chapter 64Chapter 65Chapter 66