Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya saka ya rike kansa, Mommy naji tana magana cike da fara'a tace "I suspected as much, bana son in saka rai ne ko ba haka bane inzo inji babu dadi shi yasa na dora wa zafin kitchen" doctor din ya gama yi musu congratulations ya fita, Sultan har yanzu kallona kawai yake yi sannan da sauri kamar wanda aka jawo ya taho gurina, kara na saka da duk dan karfin da ya rage min, wannan ya jawo hankalin Mommy da Daddy kaina, Mommy ta taho da sauri kusa dani tace "lafiyar ki kuwa? Ciwon kan ne?" Na nuna Sultan nace "kar ka karaso inda nake, it is over between us" cikin muryar abin tausayi yace "Moon dan Allah kar kice haka, bazan iya rayuwa in babu ke ba mutuwa zanyi please" nace "then so be it" bai hakura ba ya sake taku daya, na dunkule hannuna na daga dai dai kan mara ta nace "kana kara wani takun zan fitar da abinda yake cikina in baka kayanka" a tsorace ya tsaya, he looks scared, I have never see Sultan scared tunda na san shi. Mommy ta rike hannuna da sauri tace "baki da hankali maimunatu? Me ya hada ku haka?" Fuska ta babu alamar wasa kwata kwata, na kwace hannuna daga hannun Mommy na kuma dagawa a saman mara ta, da sauri sultan ya ja baya, yanayin fuskarsa kadai ya isa ya saka mai karamar zuciya ya fashe da kuka. Daddy ya tafi kusa dashi yana cewa "Sultan me ya faru?" Bai amsa ba ya juya da sauri ya fice daga dakin.
Yana fita na kifa kaina akan pillow na fara rera kuka, Allah kai kasan me kake nufi damu, Allah ka shiga lamarin mu. Ko kadan abinda Sultan ya aikata bai chire min ko digo na soyayyarsa daga raina ba. Amma abinda na fahimta shine; Sultan is too hard for me to break, diamond ne shi kafin a narka shi sai anyi amfani da ice da fire, I have used the ice bai yi min amfani ba, now I have to use the fire. Daddy ne yazo ya zauna kusa dani yana shafa kaina yace "Maimunatu talk to me" na dago kaina naga Mommy tana ta sharar kwalla, na runtse idona ina tuna duk abubuwan da suka faru a ranar, na kwalli agogon bangon dakin naga 3:30 na dare, hakan yana nufin an dauki hours da yin abin, hakan yana nufin Ibrahim yayi spending hours a cikin ramin day fada, wani kukan ne ya taso min, na dora kaina a kafadar Daddy nayi mai isa ta sannan na share hawaye na, tiryan tiryan na basu labarin duk abinda ya faru, na karasheda wani kukan "yanzu Daddy sultan ya kashe Ibrahim, ya zanyi? Shima hukuncin kisa ne akansa in aka san maganar nan, idan kuma nayi shiru ban fada ba kuma kamar na daure wa cin zali gindi kenan, ya zanyi Daddy? Mommy ki taimaka min" Mommy ta jawo ni ta rungume ni tana kuka tana salati "mun shiga uku mun lalace ni Fatima" Daddy kuma cike da mamaki yace "waye shi Ibrahim din ne?" Mommy tace "wannan copper din da yake sonta da a makaranta" Daddy yace "That yaroba guy?" Kai kawai na gyada masa, yace "a dai dai ina abin ya faru? Kamata yayi muje first mu dauko shi, maybe yana da rai yana bukatar taimako, in ma bashi da ran kamata yayi ai muje mu dauko shi" nayi musa kwatance ya mike yace "bara in nemi sultan shima inji me yake ciki, I don't want him hurting himself kuma" na girgiza kaina nace "he won't. He would want to see his child".
Tunda Daddy ya fita babu wanda yayi magana ni da Mommy, kowa da abinda yake zuciyarsa. Mun jima sannan naji Mommy ta fara yi min magana, ga mamaki na maimakon inji tana fadan abinda Sultan yayi sai naji tana addi'ar Allah yasa babu abinda ya sami Ibrahim. Muna cikin haka wayar ta tayi kara, ta dauka tace " wannan number ce ma babu suna, waye zai kira ni cikin daren nan kuma" ta daga tare da sallama, take naga yanayin fuskarta ya chanza, tace "Amina slow down kiyi min bayani yadda zan gane. Kina ina?" Ta jima tana sauraron Amina tana kuma kallona, na mike zaune ina jiran inji abinda ake gaya mata, tace "OK, kinyi kokari sosai Amina, ki zauna anan inda kike bara in kira daddyn ku in gaya masa" ta kashe wayar, bata yi min magana ba sai tayi dialing number din Daddy tace "ba sai kunje gurin ba dear, su Amina sun dauko shi sun tafi dashi general hospital. Yes, he is alive, zan yi maka bayani later" ta kashe tana kallona, wata ajjiyar zuciya na saki na koma na kwanta, duk da bansan details din me ya faru ba amma na fahimci cewa Ibrahim is alive, wannan information din kadai ya isa ya kwantar min da hankali. At least Sultan is safe now, amma kuma dole zai fuskanci hukunci daga gurina, sam ba zan yi masa da wasa ba, he must learn to control his temper especially yanzu da zamu fara ajjiye zuri'a. Daga baya Mommy tayi min bayanin cewa ashe duk abinda ya faru a store Amina ta gani, taga fitowa ta da kuma fitowar Sultan, bayan ta fito itama waje sai taga tafiyar mu a guje, sai kuma taga Ibrahim ya biyo bayan mu shima a guje, shine taji tsoron kar wani abin ya faru ta hau taxi tace yabi yaban mu, munyi musu nisa dan haka basu ga sanda abin ya faru ba amma sunga motar mu tana juyowa amma bata ga ta Ibrahim ba, suna zuwa gurin suka ga alamar anyi accident, ita da mai taxi suka fito sannan suka ga inda motar Ibrahim ta fada, mutane masu wucewa ne suka taimaka masu aka fito da Ibrahim, lucky for him shima ya saka seatbelt kuma motar sa akwai airbag dan haka bai wani ji mugun ciwo ba amma still he is unconscious, sun kai shi asibiti an kaishi emergency.
Gari yana wayewa Daddy ya shigo, ya gaya mana cewa har lokacin Ibrahim bai farfado ba amma doctors din sunce he is stable. Sultan daga bakin kofa ya tsaya yana kallona, kallo daya nayi masa na dauke kaina gefe, ya gaji da tsayiwa ya juya ya fita. Da la'asar aka sallame ni, direct gida aka nufa dani, naji dadin haka dan dama ina ta addu'ar Allah yasa kar Daddy yace a mayar dani gidan Sultan. Shima kansa Daddyn naga ya hade wa Sultan rai sosai. Muna zuwa gida Daddy ya saka ni a gaba yace "zaki dan zauna a gida Moon, hakan ba yana nufin zan raba ki da mijinki ba, a'a, so nake mijinki ya gane cewa abinda yayi ba dai dai bane, for him to think cewa zai iya daukan ran mutum koma me mutumin yayi masa is very bad. Zaki koma amma sai na tabbatar da cewa something like this will not happen again" na share hawayen ido na nace "na gode Daddy" yace "yanzu so nake dake ki nuna masa kuskurensa sosai, kar ki raga masa ko kadan. Ke ce abinda yake so fiye da komai a duniya, kuma yana takama ne cewa kina sonsa, show him you can leave him in dai har ba zai iya controlling kansa ba" na gyada kai na sake cewa "na gode Daddy".
Dakina aka gyara min, na shiga ina karewa dakin kallon, I never thought zan kuma dawowa dakin in kwana a ciki. Dare yana yi nayo alwala nazo na fara jero salloli ina godewa Allah daya ta kaita abin, sannan kuma ina sake neman guidance dinsa akan abin da na saka a gaba na. Na duba agogo naga karfe daya da rabi na dare, na kashe fitila na zauna akan gado ina kallon kofar balcony, I know he is coming, and I pray for God to give me the strength to do what I plan to do. Ban jima a zaune ba naji ana taba kofar, sannan aka bude ta, duk da cewa dakin da duhu bai hana ni gane shi ba, ya jima a tsaye yana kallona amma ya kasa cewa komai, nace "me kazo yi nan?" A hankali ya karasa shigowa dakin yace "Maimunatu dan Allah ki tsaya kiji abinda zan gaya miki" nace "me zaka gaya min, a gaba na kayi kokarin kashe mutum, you almost make me miscarry our child" da sauri yace "how can you say that, ke ma kinsan bansan dashi ba" nace "how can you say naje store ne dan in hadu da Ibrahim bayan bansan yana gurin ba" yace "am so sorry" nace "don't be. Rayuwa ta da taka ba iri daya bace ba. Ka tafi, ni bazan iya zama da mutumin da yake ganin cewa it is OK yayi kisan kai ba, bazan iya haifar 'ya'ya da kai ba, wannan ma da yake cikina in naga baka chanza ba I will make sure cewa bai san kaine babansa ba" da gaske magana ta ta shige shi dan fuskarsa koma wa tayi kamar an chire masa spirit din jikinsa, na mike tsaye nace "now get out of my room" ko motsi bai yi ba, na kunna fitilar dakin, yanayin da naga fuskarsa yasa nayi saurin dauke idona daga kansa tun kafin zuciyata ta karaya, na sake cewa "ka fita ko in kira security su fitar min da kai" a hankali yace "you won't" ban kuma ce masa komai ba naje na danna security button, ba'a jima ba sai ga David da wasu guda biyu sun shigo dakin, David da bindiga a hannunsa. Na nuna Sultan nace "ku fitar mun dashi daga nan" David yace "with pleasure ma'am" dama har yanzu David yana da grudges for sultan saboda dukan daya yi masa rannan ya kunyata shi a gaban yaransa. Ga mamakina ko motsi sultan baiyi ba ballantana yace zai yi fada dasu, suka kama shi suka fita dashi ta gabana, na dauke kaina ban kalle suba, amma suna fita na bi bayansu na tsaya a kofar dakina ina kallon yadda suke jansa akan stairs, ji nake tamkar zuciyata suka fito da ita waje suke ja a kasa, ina kallon su har suka bude kofar palo suka fita dashi waje. Na hango Daddy a kofar dakinsa shima yana kallon su. Na koma dakina da sauri na bude kofar balcony na shiga na cigaba da kallonsu suna jansa a kasa kamar babu rai a jikinsa, har suka bude gate suka fita dashi waje, a gaban gida na biyu bayan namu na hango motar sa, nan suka nufa dashi suka jefar dashi a gaban motar suka juyo, na tsaya ina kallon duhun inda yake a kwance a kasa, a raina ina cewa 'get up sultan' amma shiru bai tashi ba, bayan kamar 20 minutes na koma dakina na dauko waya na dawo balcony din, na kira wayar Amir, yana dauka nace "Kazo gidan mu yanzu, your friend needs you" na kashe wayar, ban bar gurin ba har sai da naga shigowar Amir unguwar mu, har ya wuce inda Sultan yake sai kuma yayi reverse, ya fita da sauri yana taba sultan, sannan ya daga shi, naji wani dadi a rauna ganin sultan din yana kokarin tafiya da kansa, a bayan mota Amir ya saka shi sannan ya koma ya rurrufe motar sultan din sannan suka tafi. Na rufe fuskata da hannayena ina kuka, I really hope cewa abinda nayi is the right thing to do. Waya tace ta fara kara, duk a tunani na Amir ne amma sai naga sunan Hafsat. Nace a raina 'har ta samu labari kenan' na dauka nayi mata sallama cikin sarkakkiyar murya, excitedly ta fara magana "Moon am sorry na kira ki yanzu nasan dare yayi sosai a Nigeria, what ever you are doing ki ajiye ki hau WhatsApp na turo miki hoton wata auntyn zayed, she looks exactly like Sultan, her name is Khairat, Moon I think she is his mother".
*when everything seems lost, have hope and trust in Allah, He will always find a way out for you. Remember, there is always darkness before dawn.*

Episode Eighty : The Skeleton in The Closet
A lokacin da su David suka ajiye shi a kusa da motar sa, kasa tashi yayi daga gurin, jira yake mutuwa ta karaso ta dauke shi, dan shi a ganinsa bashi kuma da sauran rayuwa a gaba. To menene sauran rayuwa in babu Moon? Dama itace farin watan data haskakae rayuwar ta sa da hasken ta, to yanzu tunda babu ita kuma menene yayi saura in banda duhu, a cikin duhun zai yi ta lalube har yaje ya afka ga halaka, he is sure that he will be lost without her. Yana kwance yaji tsayuwar mota a kusa dashi, a tunanin sa ma robbers ne kuma he didn't care. Sama sama yaji muryar Amir yana yi masa magana, ya dan bude idonsa ya kalle shi ya mayar da idon ya rufe. What is this man doing here? Me ya kawo shi? Yana jin Amir ya fara kokarin tashin sa, ya kwace, Amir yace masa "Sultan menene hakan kake yi wai? Moon ta kira ni tace inzo gurin ka, me ya faru? I really hope you are not drunk kuma? Sultan ya bude ido ya kalle shi sosai sannan yace cikin murya kamar ba tasa ba "Moon ce tace kazo nan?" Amir yace "eh, me ya faru haka" Sultan ya fara kokarin tashi Amir ya taimaka masa ya bude masa mota ya shiga suka tafi. Me yasa Moon ta kira Amir? Shin hakan yana nufin she still care about him ko kuma just tana so a dauke mata shi daga kofar gida saboda bata son ganin sa?. Ya lumshe idonsa yana tunanin abubuwan dasu ka faru tsakanin su, she even said zata tabbatar da cewa dan da yake cikin ta bai san cewa shine mahaifinsa ba, she hates him that much kuma bai ga laifin ta ba, koma menene ya faru laifinsa ne. Na farko ta ya akayi ma zuciyarsa ta raya masa cewa Moon sun hada plan da Ibrahim zasu hadu? How can he even think that? Kishinsa ya rufe masa ido kawai ya fadi magana without thinking kuma wannan maganar ita ce tafi komai bata wa Moon rai. Shi shine mai bad past, amma ita ko yaushe tana kyautata masa tsammani, ya tuna case din khulsum, tun kafin ma moon ta tuntubeshi da maganar har ta yanke hukuncin karya suke masa, amma shi bai showing mata the same courtesy ba. Wannan shine babbar nadamar sa ba wai ture Ibrahim ba, that bastard, he deserve that, uban wa yace ya biyo su? Har cikin gidansa ya shiga gurin matarsa and he let him go, sannan kirikiri ya ganshi ya rike hannun matar sa a cikin store and he still ignore him, duk da cewa da kyar ya danne zuciyar tasa ya yi ignoring din nasa, dan a lokacin babu abinda zai bashi satisfaction irin ya ga ya zubar masa da hakoran da yake using yake smiling at his wife, amma ya danne zuciyar sa saboda a lokacin yana ganin laifin moon ne kamar ita ce ta bada hanya, bayan sun fita kuma ya biyo su, why will he follow them in ba rainin hankali ba, waye suna tafiya da matarsa zai ga tsohon saurayinta yana binsu a baya kuma ace ransa ba zai baci ba? Laifin sa daya a lokacin, bai kamata yayi playing with rayuwar moon ba, kamata yayi yayi packing motar ya fito da Ibrahim da ga tasa motar ya babballashi ya zubar a gurin sannan suyi tafiyarsu.
Suna zuwa gida a part din Amir suka tsaya. Amir ya fito ya zagayo ya fito da sultan sannan suka shiga ciki, shi Amir duk a tunanin sa Sultan a buge yake, yana zuwa ya kwantar dashi a kan gado sannan ya debo ruwa mai sanyi ya kawo masa, yana fara sha yaji ruwan kamar madaci, ya furzar ya ajiye cup din a gefe. Amir ya zauba a gefensa yace "Sultan why do you do it? Ka samu good life with Moon why will you throw it all away saboda giya?" Wani takaici sultan yaji ya kama shi yace "fuck off amir" ya juya masa baya yayi kwanciyarsa. Amma babu bacci babu alamarsa sam, yadda jiya baiyi bacci ba haka yau ma da alama va zai yi baccin ba. Wata biyar kenan da aurensu da moon amma bai taba kwanciya ba tare da ita ba sai yau, bai taba tunanin kuma zai kwanta ba tare da ita dinba, amma yau gashi basa tare kuma duk suna raye, suna kuma gari daya. She even call the security on him tasa suka fita dashi ko kallon sa kuma bata yi ba, wannan ya tabbatar masa da cewa she means what she said, rabuwa zatayi dashi kamar yadda wadda ta haife shi ta rabu dashi, kamar yadda wanda ya haife shi ya rabu dashi, bai damu ba ko ya mutu ko yayi rai. Daddy daya ke kallo a matsayin sabon uba ma ya hade masa rai, daya gaishe shi kin amsawa yayi kamar yadda in ya gaishe da takawa baya amsawa. It is all over. He was a fool to even think it will work. Moon was right, rayuwarsu ba daya bace, they care about everyone hatta wanda ya bata musu, shi kuma va haka yake ba, they expect him to do the same, instead sai gashi ya kusa aikata kisan kai. He is a monster, shi ya riga ya dade da sanin hakan, idan zuciyarsa ta debe shi shi kansa abinda yake aikatawa sai daga baya yayi mamaki. Amma kuma yanzu har acikin zuciyarsa bai ji yayi nadamar abinda yayi wa Ibrahim ba, the bastard. Yanzu haka ma da zai ganshi da sai ya karasa shi, tunda shine yayi sanadin duk wannan abinda ya faru.
Shi kam yasan rayuwarsa ta kare, a kan gadon nan zaiyi ta kwanciya har sai mala'ikan mutuwa ya tuno dashi yazo ya dauke shi. Sai kuma ya tuno da halittar da take cikin marar Moon, wani nauyi yaji zuciyar sa tayi masa, his baby, yaci burin ya haifi 'ya'ya ya nuna musu soyayyar shi da ba'a nuna masa ba. Amma kuma Moon ta gaya masa cewa idan bai chanza zafin zuciyarsa ba 'ya'yansa ma gudunsa zasu ringa yi. Yaji wani irin daci a zuciyarsa, just the thought of his children resenting him ya saukar masa da wani mugun zazzabi. Ya jawo bargo ya kudunduna, maybe the baby will be better off without him.
Tun da assuba Amir ya taba shi yaji irin zafin da jikinsa yayi, da kyar ya tashi yayi sallah ya koma ya kwanta. Gaba daya hankalin Amir ya tashi, ya manta rabon da yaka Sultan a kwance babu lafiya, tun wata rashin lafiya da yayi suna America, sultan has always been healthy and energetic. Zuwa karfe goman safe yaga zagin jikin karuwa yake yi, duk uban bargunan daya loda masa amma karkarwa kawai yake yi hakoransa suna haduwa guri daya, a hankali yaji yana magana kasa kasa, ya sunkuyo da kansa dai dai fuskarsa yaji yana cewa "Moon am sorry, moon am sorry, dan Allah kiyi hakuri ba zan sake ba" wani irin tausayin abokin nasa yaji yana ratsa shi. Menene kuwa zai hada shi da Moon har haka? Shi yasan a rayuwarsa bai taba ganin soyayya irin ta Sultan da Moon ba, to menene kuwa zai saka su bata?. Ya dauko wayarsa yayi dialing number din Moon amma wayar a rufe, ya kuma kira har five times amma bai samu ba, yayi mata text "Sultan babu lafiya, kuma ke yake nema" ya tura mata. Daga nan ya kira number din doctor din gidan ya gaya masa halin da sultan yake ciki. Ba'ayi awa daya ba doctor din yazo ya duba sultan, shi kansa yayi mamakin zafin jikin sultan a take ya saka Amir ya taya shi suka cire masa bargonan daya lulluba suka cire masa riga da wandonsa suka barshi da singlet da gajeren wando sannan suka yi ta goge masa jikin sa da jikakken towel, amma suna dora towel din sai suga ya bushe saboda zafin jikin, a haka dai uka samu da kyar jikin ya danyi sanyi kadan, idan sultan gaba daya ya juye kamar ba nasa ba, doctor din da sauri yace a saka shi a mota su tafi dashi asibiti, suna zuwa aka tafi dashi private room likitoci suka hau kansa, Amir ya zauna anan shi kadai a waiting room, kawai ji yayi hawaye yana zubo masa, a ce mutum mai gata irin sultan, a Prince, da uwarsa da ubansa da matarsa a duniya amma an kawo shi asibiti babu kowa a gurin sai shi? Yana nan yana ta kukansa har doctor ya fito yana kallonsa yace "Haba Amir, kar ka badani mana, kana namiji kana kuka?" Amir bai kula da tsokanar da yake masa ba yace "doctor how is Sultan?" Yace "da sauki zamu ce. Fear dina shine brain dinsa, zazzabinsa yayi zafi da yawa in tsoron kar ya taba kwakwalwarsa, kuma yana tunani da yawa, wannan shi ya saka muka kasa stabilizing bp dinsa, amma for now mun yi masa allurar bacci, za mu jira kuma muga sanda zai farka. But please do your best ka ga ka kawo masa abinda zai faranta masa idan ya tashi daga baccin" Amir yayi masa godiya sannan ya shiga da sauri inda sultan yake kwance, tun kafin ya karasa kusa dashi ya hango irin ramewar da yayi da kuma farin da yayi, fatar bakinsa tayi purple alamar babu isashshen jini a jikinsa, kuma zazzabin ne ya kona jinin. Ya karasa ya rike hannunsa da yaji yayi sanyi kalau yanzu alamar zazzabin ya sauka, a hankali ya fara magana "Sultan ya zanyi? Me zanyi maka ka samu lafiya sultan?" Sai kuma ya mike kamar wanda aka tsikare shi yayi kissing hannun sultan ya fita da sauri, direct gidan su Moon ya dosa, tun daga bakin gate David ya tsayar dashi fuskar nan babu rahama a cikin ta ga bindiga a kugunsa yace "you are no longer welcome here" Amir yace "ba shiga zanyi ba ai, Moon nake son gani" David yace "bata son ganin ka ita" wata zuciya ta debi amir amma ya danne yace "ya akayi kasan bata son ganina, ka shiga ka gaya mata nine nazo zata fito" David yace "itace tace in kazo kar a barka ka ganta" Amir ya sake cewa "can you at least tell her that her husband is sick kuma yana bukatar ganin ta? Am sure in ka gaya mata haka zata ganni" ko kula shi David baiyi ba ya koma kofar gidan kawai ya tsaya yana kallonsa hannunsa a rike da bindigar sa. Amir yayi wishing ina ma yana da karfi irin na sultan da sai ya farfasawa david baki ya shiga gidan ya dauko moon aka ya kaiwa sultan ita. Amma babu damar yin hakan dan yasan tunkarar David will be like a suicide, kuma yasan bashi kadai bane akwai sauran a ciki. Dole ya koma yaja motarsa ya tafi, yanzu ya zaiyi kenan? Ya zaiyi da Sultan idan ya tashi? Wani tunani ne yazo masa, ya juya kan motar sai palace, yana shiga fada ya tafi direct, mutanen gurin sai kallonsa suke yi, sun san shi amma kuma basu taba ganin shi a fadar ba, ya tsaya yana facing Takawa da yake harde akan karaga, ga Abbas a zaune a hannun daman sa, ga sauran hakimai duk kowa ya juyo yana kallon Amir, da karfi amir yace "Your son is dying, yana asibiti kuma yana nemanka" kafin ya rufe bakinsa fadawa sukayi kansa, suka jashi suka fitar dashi waje, amma ko babu komai Amir ya isar da sakon sa. Ana fita da Amir Hakiman gurin suka fara magana, 'dama Sultan bashi da lafiya?' 'Me ya same shi?' 'Allah sarki yaron ya nutsu sosai wallahi' 'ni kam kwanan nan kullum na ganshi sai yayi ta bani sha'awa' da sarkin bai da makama, da madaki, wadanda sune ake kira da king makers, suka kalli juna suka mike a tare suka durkusa a gaban sarki "Allah ya taimaki sarki ai ya kamata muje

Please Login or Register in order to submit comment