Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

so muyi, be serious please" yace "ina jinki" na dan sassauta murya nace "kana ji, dama wani dan course ne daga makaranta aka tura mu zamuyi a US, to gobe zamu tafi insha Allah, shine dama na ke so in gaya maka tun dazu a school kuma na kasa" shiru bai ce komai ba, na cigaba "Sultan dan Allah kar kayi fushi, ina taso in gaya maka wallahi tun tuni bansan yadda zaka dauki maganar ba, ba wani dadewa za muyi sosai ba, please say something" murya a duskure yace "for how long zaku kasance a can din?" Na yi shiru kalmomin sunyi min nauyi, sai da ya maimaita tambayarsa sannan nace "6-8weeks akace mana" nayi sauri na kara da cewa "amma ba lallai ne mu kai hakan ba, da mun gama zamu dawo" shiru bai ce komai ba amma ina jiyo numfashinsa ta wayar, sai da na gaji na kira sunansa "Sultan?" Yace "yaushe zaku tafi" nan ma amsar tawa ba mai dadi bace "gobe" ya maimaita "gobe?" Na daga kaina kamar yana kallona, "wato kina nufin dazu da muka rabu bye bye kika yi min kenan sai nan da wata biyu?" Na danyi dariyar yake nace "wata biyu ne fa kawai Sultan, kuma ai kullum zamu ke yin waya, kuma dana kammala wata biyun nan na gama project dina sai in rubuta report in yi submitting.... " kawai ji nayi ya katse wayar, na tsaya ina kallon wayar a hannuna, sultan dan rigima, text na rubuta masa da kalamai masu dadi cikin sigar bada hakuri na tura masa, shiru2 babu reply, lallai da gaske fishin yake yi, bamu taba fada da sultan ba, bai taba yin fushi dani ba, sai naji rai na duk babu dadi. Washe gari 12 jirgin mu zai tashi dan haka da wuri na tashi na kaya na da zan tafi dasu, bini2 sai in duba waya ta amma babu missed call babu message from sultan. Kudi sosai daddy ya bani kuma ya kira uncle Ben ya sake tuna masa yau ne fa zuwa na. Mommy har lokacin cewa take yi ita fa sam hankalinta bai kwanta da zancen tafiyar nan tawa ba, nima kuma haka, duk jina nake yi jiki a sanyaye ko dan ban taba yin tafiya mai nisa on my own ba. Gaba dayan su ne suka raka ni airport har mommy, har na shiga jirgi ina ta kiran Sultan amma yaki dagawa, duk sai naji kamar in fito ince na fasa tafiyar dan dai kawai babu yadda zanyi ne. Kira after kira nake ta jera wa Sultan kafin passengers su gama shigowa amma still no answer, na kashe wayar na jefa a jakata, hankali na duk ya tashi, anya kuwa nima zan iya jure wadannan satittikan ba tare da sultan ba? Especially in ya cigaba da kin daukan wayata. Muka sassaka seat belt din mu jirgi ya tashi, wani dan tsohon bature ne a kusa dani dan haka muna gaisawa na gyara kwanciyar kujera ta na saka earpiece ina jin karatu na lumshe ido na ina so inyi bacci ko Allah zai sa zuciya ta tayi sanyi. Nasan dole Sultan zai sakko dan kansa dan haka nayi alkawarin ko mun sauka bazan kira shi ba har sai ya kira ni da kansa. Jiki nane ya bani kamar ana kallona, to shi wannan tsohon menene nashi na kallon mutane kuma? Su turawa fa sam basu da kunya wallahi. Mayafi na naja na rufe fuskata ba tare da na dube ido na ba, ji nayi ansa hannu an bude fuskar tawa, da sauri na bude ido na zanyi bala'i amma se me? Sultan na gani zaune a kusa dani yana kunshe dariya "do you miss me, Love?" Na rasa dariya zanyi ko kuka, mamaki da takaici duk suka rufe ni shi kuwa dariya sosai ya ke yi, na dauki magazine din kusa dani na fara dukansa aka da ita, ya saka hannayensa ya kare yana cigaba da dariya, can dai na lura mutane da yawa a jirgin mu suke kallo, nayi sauri na ajiye magazine din hannauna na maze kamar bani ce nake yi ba. Sai da ya gama dariyarsa sannan ya juyo, "kin dauka fushi nayi ko?" Nayi banza na rabu dashi, ya cigaba da "ni na isa inyi fushi dake? Ai kin wuce wannan gurin. New York is not England. Bazan iya barinki ki tafi ke kadai ba, jiya bayan munyi waya na kira airport na tambayi wanne jirgin ne zai tafi America yau kuma karfe nawa zai tafi, sai kawai nayi booking na shirya kayana" nace masa "ya akayi ka samu visa daga jiya zuwa yau?" "Visa kuma? Legally ni dan America ne acan aka haife ni, i don't need a visa to go there" what a fool i have been, shaf na manta da wannan tsarin, na kasa tantancewa farin ciki nayi da zuwan Sultan ko bakin ciki. Earpiece dina guda daya ya cira ya saka a nasa kunnen shima ya kwantar da kujerar sa a haka muka yi bacci tare. Bamu farka ba sai da aka fara announcing jirgin mu zai sauka sannan muka tashi muka saka seatbelts din mu. Direct asibitin muka tafi, muna zuwa muka hadu da sauran students aka bamu keys din dakunan da zamu zauna sannan aka fara zagayawa damu za'a nuna mana duk inda muke bukatar sani, Sultan yazo ya ce in bashi key dina ba musu na mika masa ya tafi. Ina kallon yadda sauran students din suke kallona da alamar tambaya, a raina nace ina ruwanku? Mahdi ya dawo kusa dani yace "so..... I have seen you found your dark skinned man, Allah ya bar kauna" nasan magana yake gayamin dan haka na dauke kaina nace "amin" sai kuma yace "are you guys like living together kenan?" Na kalle shi ya hade rai nace "what do you mean?" Yace "naga ya biyo ki nan, kuma gashi har da wani karbar key din dakinki ya tafi zai shiga, ni dai a sani na ba'a gayyacemu daurin aure ba ballantana muce ai mijinki ne" na katse shi nace "dakata ya isa haka, kaya na ne da na zo dasu a cikin motar daya dauko mana shata daga airport, shima kuma da kayan sa a ciki, ya karbi key dina ne saboda ya sauke min kaya na ya tafi ya kai nasa masaukinsa. I don't even know me yasa nake maka bayani cos I owe no one an explanation" daga nan nayi gaba na barshi. Sai kuma naji a raina babu dadi saboda gaskiya ya fada min, sultan ba muharramina bane he have no business da shiga dakina. Bayan mun gama duk zagayen mu, a gajiye muka koma lodge din mu, one bedrooms ne a jere kowanne da number a jikinsa. Na duba nawa na tarar da a bude an dan saya kofar, a hankali na tura ne leka kaina ina sallama, babu amsa, na shiga ciki nace "sultan" nan ma shiru babu motsi, na sauke ajiyar zuciya sannan na kare wa dakin kallo, an gyara shi tas sai kamshin freshner yake yi, sabon bedsheet din da nazo dashi ne akan gadon tare da bargo, wato Sultan har kayana ya bincika ya dauko kenan ko? Shi sam baisan ma'anar boundary ba. Ya share dakin tas yayi mopping ya gyara gadon ya jera min kaya na a chest of drawers da suke dakin, ina dubawa naga har underwears ya saka su a drawer daban, kunyar duniya ta isheni yau Sultan yaga panties dina da braziers dina. Na duba toilet naga shima a gyare tas yana ta kamshi, sai a lokacin na lura har da karamin carpet ya siyo ya saka a gaban gadon. Tun ba yau ba nasan Sultan yana da tsafta sosai dan har mamakin tsaftar sa nake inna lura da irin yadda ya taso, koda yake ita tsafta a jinin mutum take, dan wani zakaga gidan su masu tsafta ne amma shi a kansa kazami ne. Komawa nayi nayi locking kofar, kayan jikina na chire na shiga wanka na tarar har kayan wanka na ya jera min a toilet din, na fito na shirya cikin riga buba na gyara gashina nayi packing a tsakiya kamar yadda nake yawan yi in ina gida, na fesa turaruka na sannan na saka hijab na fara ramuwar sallolin da ake bina. Ina idarwa naji anyi knocking nace "am coming" kafin in karasa kawai naga an bude kofa an shigo, na tsaya ina bin shi da kallon mamaki ganin key a hannunsa, wato spare key din dakin ya zare ya tafi dashi, as if dakin namu ne mu biyu, na hade rai sosai na rike kugu ina kallonsa, shi kuma yana murmushi, Allah yaso ma ban cire hijab din da nayi sallah dashi ba, "wannan bata ran kuma fa? Ni na kasa banbance yaushe kika fi kyau, in kin bata rai ko kuma in kina dariya" na kare daure fuska na ce "me yasa ka daukar min kex din dakina? Kasan hakan ai ba dai dai bane in kazo gurina sai ka kira ni a waya in fita in same ka ba wai ka shigo min daki ba" yi yayi kamar bada shi nake ba ya karaso dakin ya ajiye ledojin abincin da suke hannunsa sannan ya zauna a bakin gadk yana cewa "wash na gaji da yawa" na kara masa wata hararar nace "malam sauko min daga gadona, kuma ma waye ya baka damar ka bude min kaya? Kasan dai kayan mata sirri ne ko?" Ya sake share ni ya sauko yana bude ledar abincin da akayi sealing dinsa a cikin dan babban container, sai lemuka wanda ban taba ganin irin suba masu sanyi ya ajiye a gefe "malama in zaki zo muci abinci kizo, in kika tsaya iyayi kinsan ni bana wasa da abinci zan chinye ne in barki" daga haka yasa cokali ya fara cin abincinsa, ina kallonshi yana wani lankwasar da wuya yana lumshe ido nima naji yawuna ya tsinke kuma dama yunwa nake ji da gaske, a hankali na tafi kamar wadda ake jana da magnet naje na zauna na dauki cokali na fara ci dadin abincin yana ratsani, sai da muka kusa cin rabin abincin babu wanda yace wa kowa komai, can dai naji babu dadi tunda ni ban iya shiru ba nace "thank you for.... " na nuna dakin da hannuna, ya ajiye spoon din hannunsa yace "you are welcome" na ce "a ina zaka sauka ne kai?" Yana murmushi ya nuna kan gadon, na harare shi yayi dariya yace "relax 'yammata, garin mu fa kika zo, i have a house here duk da dai yanzu da akwai wadansu friends dina a ciki amma acan zan sauka" na gyada kaina alamar gamsuwa, a haka muka gama cin abincin mu yana ta yi min hida, nayi mamakin yawan abincin da naci, da zan sja drink din sai da na duba ingredients dinsa, ina kallon sultan yana yi min dariya na harare shi kawai bance komai ba. Yana gama wa "nace to atashi kuma asan nayi, sai da safe" ya mike yace "ba sai kin kore ni ba nima dama baccin nake ji" har ya kai bakin kofa nace "bani spare key dina" ya jiyo yace "na karfi ne, in kina da karfi ki kwata"

I don't know why inna fara typing bana son tsayawa sai daga baya in ga ashe nayi da yawa. Ya kamata mu koma yi kadan kadan ko?



Episode forty four : America 2

Yana gama fadin haka ya ficewarsa ya barni. Naje nayi locking kofar amma a raina ina cewa wannan ai bonono ne rufe kofa da barawo. Na dawo na kyara inda muka ci abinci sannan nayi shirin kwanciya, ranar sam na kasa bacci saboda rashin sabo da sabon gurin, kawai na tashi nayi alwala na yita salloli ina rokon Allah ya bani karfin zuciyar da zan iya controlling Sultan shi kuma Allah ya shirya min shi, na tuno da maganar Amira da tace am too soft and Sultan is too hard, in dai har ina so in gyara masa rayuwarsa dole nima in zama hard amma how? I have been soft tunda nazo duniya how can I be hard kuma yanzu?.

Washegari muka fara aikin da ya kawo mu tukuru, aikin shine koyon yadda ake raba twins din da aka haifa a hade ta ka, yadda kowanne daga cikin su zai rayu. Kullum wuni muke yi a lab sai yamma likis sannan zamu dawo, kuma kullum muna dawowa zan tarar da abinci Sultan ya ajiye min, wani lokacin ma har da ruwan zafin wanka, sai yanzu na fahimci dalilin da yasa ya dauki spare key dina kuma inajin dadin yadda yake kula dani sosai, saboda badan shiba gaskiya zaman zai yi min wahala sosai, fita siyan abinci kawai sai ya isheni. Wani abin mamakin shine duk da cewa ni kadai nake zaune yanzu amma Sultan har yau bai taba kai hannunsa jikina ba, ko wani abu zai bani baya barin hannayen mu su hadu, na jinjina masa ta nan gurin sosai dan ba ko wanne namiji ne zai iya haka ba, wani lokacin har tunani nake "to ko he is not attracted to me?" Amma kuma in na kalli idonsa ina gani a ciki, wani lokaci har bana son hada ido dashi saboda irin abubuwan da nake karantowa a ciki, abinka da psychologist, lol. Watan mu daya a America wani aiki ya taso wa Sultan wanda ba zai iya yi tanan ba sai lallai yaje Nigeria, ji nayi kamar zanyi kuka har sai da ya gane yace to ya fasa tafiyar sannan na hakura. Kafin ya tafi sai da ya bada order a restaurant din da yake siyo mana abinci cewa kullum zasu ringa kawomin safe, rana, dare babu fashi. Yana tafiya muka dinke a waya, kudin da Sultan ya kashe a saka credit daga tafiyarsa zuwa dawowarsa Allah ne kadai yasan yawan su, koda yaushe muna tare a waya sai dai in zanyi waya da 'yan gida ince masa ya kashe kuma shima ana jimawa zai sake kira. Satinsa biyu acan ya dawo amma ji nayi kamar yayi wata biyu. Yana dawowa ya shiga lodo min siyayya yana ajiye min wai tsarabar da zan kaiwa 'yan gidan mu, nace "Sultan wannan uban kayan ya zanyi in tafi dasu?" Yace "shipping dinsu zanyi miki ai" na sake cewa "to yanzu in naje dasu gida ince da mommy a ina na samu kudin saye?" Na danyi tunani kadan sannan yace "tell her you won the lottery or something" kawai na saki baki ina kallonsa, shi a ganinsa wannan is a total excuse, shi bai saba in yayi abu a tuhume shi ba dan haka bashi da idea yadda za'a yi wa iyaye karya. Haka yayi ta lodo kaya yana jibgewa.

Sati daya ya rage mana mu dawo England, duk ayyuka sun yi mana sauki dan kusan zan iya cewa mun kammala, ana koya mana ne yadda za'a kula da twins din ana monitoring dinsu har su warware. Sai lokacin sultan ya samu damar fita dani yawon ganin gari, ai kuwa nasha gararamba lungu da sako na New York sai da ya shiga dani. A lokacin ne ya kaini gidan sa ya nuna min. Tun sanda yace min can zamu je na kudurta a raina cewa bazan shiga ba, muna zuwa yayi packing ya zagayo ya bude min kofa naki fitowa, ya tsaya yana kallona "ko sai na fito dake ne?" Nace "no kawai dai bazan shiga bane" in yayi mamaki ma ya boye bai nuna min ba yace "ohh really? Duk zirga2 da nake yi gurinki ke ko shiga ki saka min albarka a gida na baza kiyi ba? Thanks a lot" wani barin na zuciyata yace min, he is trying to control you, don't give in, na daga kafada nace "sorry, kawai dai naga kamar shiga gidan ka is way ahead of limit" shima kafadar ya daga yace "if you think so, amma matsalata guda daya ce, what I plan is in munzo nan zan barki anan zanje wani guri in karbo sako a gurin wani wanda gobe zai bar gari gobe kuma gurin da zamu hadu is no place for a lady especially lady din da ba zata iya shiga gidan fiancé dinta ba" na daga masa hannu nace "technically kai ba fiancé na bane yet" yayi murmushi tare da jingina da jikin motar yace "OK, yanzu ya kike so ayi?" Na kalleshi ya langwabar da kai side daya, na dauke kai a zuciyata ina cewa, don't fall for that, ya sake zagayo wa ta side din dana mayar da fuskata yace "na rasa me yasa har yanzu kin ki trusting dina, if I want something da tuni na karba, you are too precious for that, I just want you to see my house, nan shine inda na zauna for thirteen years, tun ina twelve years nake rayuwa a gidannan har na kai twenty five years" ba fito daga motar ina karewa gidan kallo, madaidaici ne, sama da kasa, da veranda a kofar gidan, gaba daya gidan a kewaye yake da flowers masu kyau. A hankali na tambayeshi "amma kai kadai ka zauna a gidan tun farkon zuwanka? Ina nufin girki da kula da gida" ya daga kafada yace "farkon zuwan mu akwai house help da driver da suke zuwa kullum, daga baya muka kore su muke kayan mu da kanmu, fifteen years na fara driving, Amir ya iya girku sosai, so we managed" na runtse ido na ina jin zafi a raina, sultan tun yana karamin yaro yake zaman kansa kuma a lalatacciyar kasa kamar America. Sultan ne ya dawo dani daga tunani na yace "look in baki yarda dani ba ga key ki bude ki shiga ki rufe kanki, just look around in na dawo sai mu tafi" ba kalleshi da tuhuma nace "how do I know baka da spare key?" Dariya yayi sosai yace "Wallahi bani da spare key, kinji na rantse miki dai" na karbi key din ina kunkuni na matsa baya, ya rufe kofar ya zagaya seat din driver ya shiga ya kunna motar yace "in kin shiga sama zaki hau, kasan anan friend dina yake zama, amma nace masa zamuzo dan haka ya fita" na gyada masa kai sai kuma ya tsaya yana kallona, na daga masa kafada alamar what? Yace "this is New York not Abuja, ki shiga ciki kiyi locking kofar sannan sai in tafi" Na turo baki na juya ina kallonsa yana yi min dariya har na shige cikin gidan na rufe kofa sannan ya tayar da motar ya tafi. Kallo daya na yiwa palon kasa na hau sama. Ina shiga wani katon hoton Sultan ba gani hannunsa rike da guitar fuskarsa da murmushi, akwai yarinta sosai a fuskarsa, na karasa gaban hoton ina kallonsa, na daga hannu a hankali na shafa fuskarsa ina jin wani sabon sonsa a raina, na shiga uku ni Maimunatu ya zanyi duk sanda aka raba ni da Sultan? Ba wani tarkace a palon amma kamar yadda nayi tsammani tas yake ko digon datti babu a ciki, na cigaba da kallon pictures din jikin bango, duk yawancin su shi da Amir ne, wani suna yara wani sun dan girma, gaskiya Allah ne kadai yasan shakuwar da take tsakanin Sultan da Amir. Wanj hoto ne ya dauki hankali na, Sultan ne da school uniform ana bashi gift a makaranta, gashin kansa a hargitse kamar wanda ya dawo daga filin dambe. So you are brilliant also. Na shiga bedroom dinsa naga gado ne kawai sai sif din kayan sa, na bude sif din a raina ina cewa kaima ai bude min kayana kake yi. Anan na saku baki ina kallo, sets din kaya ne sunfi karfin a kirgasu, a jere neatly, takalma, undies, p-caps abin ba'a magana. A raina nace dan gayu. Na koma kitchen naga babu kayan abinci amma akwai kayan electronics iri iri. Gaba na ne ya fadi da naga fridge, ko zan ga giya a ciki, a hankali na bude fridge din kamar mai taba wuta, na duba kaf banga alcoholic drink ba, na sauke ajjiyar zuciya na dauko orange juice na dawo palo na zauna ina sha.

Kamar daga sama naji ance "hello" a tsorace na juya saboda nasan nayi lucking kofa, wani black American na gani kansa ya sha kitso kamar wata budurwa a tsaye a bakin kofar palon. Na mike tsaye a tsorace ina kallonsa. Sosai naga shima ya tsorata yace da American English "Sorry, na dauka kun tafi shi yasa na dawo kuma banga mota ba sai kuma naga sama a bude, na dauka ya manta bai yi locking bane. Am so sorry, please karki fada masa" ajjiyar zuciya na sauke nace masa "babu komai" har ya juya zai tafi sai kawai wani tunani ya fado min a raina, this is my chance to know more about sultan. Da sauri nace masa "wait, at least tun da ka shigo ai ya kamata mu gaisa ko?" Da fara'ar sa ya dawo amma yana dan rarraba ido, daga dukkan alama Sultan ya kora masa warning akan zuwana. Na nuna masa kujera ya zauna nace "my name is Maimoon" yace "I know, sultan talk about nothing else" ya miko min hannunsa yace "I am Steve " nayi ignoring hannun daya miko min nace "so how long do you know Sultan?" Yace "as long as I can remember" na gyada kai nace "to yanzu misali in aka tambaye ka is he good, bad or in between me zaka ce " mamaki ne ya bayyana a fuskarsa yace "Sultan is more than good, he is the best person dana sani a rayuwata, duk wanda ya gaya miki wani abu bayan wannan karya yake yi. Ba dan Sultan va da yanzu ina cikin hoods ina trading drugs, he saw me through sec sch and college, bani kadai ba muna da yawa wadanda sultan ne uban mu a garin nan, cinmu, shan mu, suturar mu duk Sultan ne. Da akwai sanda za'a aiko masa da kudin makaranta daga gida sai ya dauka ya biya mana kudin makarantar mu sai ya aika gida yace kudin sun bata ko sun kare, muna kallo daddynsa zai aiko har gida azo a kama shi a rufe a cell, wani lokacin sai yayi sati sannan a fito dashi. Saboda Sultan ya ciyar damu ya koyi playing guitar, zai dauka ya tafi market square yayi playing ana bashi kudi in ya tara yazo ya siyo mana kayan abinci. Daga baya ya koyi art, sai yaje ya zana mutum ya biya shi kudi yazo ya raba wa mabukata. He once told me saboda orphans yake karatu, duk kudin da zai samu akansu zai karar, in dai yana da rai babu dan da zai yi kukan rashin gata" hawaye naji yana kokarin tahomin nayi sauri na mayar dashi, nace "naji ance kuma yana yin drugs da alcohol" ya bata rai sosai yace "drugs? No, not Sultan, he hates drugs, ko bashi da lafiya sai anyi da gaske yake shan kwaya ballantana haka kawai" na gyada kaina nace "alcohol?" Ya dauke idon sa daga nawa ya kalli gefe, he then shifted from one leg to another, as a psychologist, tin kafin yayi magana nasan amsar da zai bayar, a hankali yace "sometimes, but only when he is frustrated" nayi shiru na kasa yi masa wata tambayar kuma, ya cigaba da magana "he has a bad temper you know, yana da zuciya sosai, wani lokacin in ransa ya baci gaba dayan mu sai jikin mu ya gaya mana, it is his way of releasing his temper, baya harkar mata sam dan babu wanda zai ce ya taba ganin budurwar Sultan duk kuwa da 'yammatan da suke binsa kamar jela cos he is handsome you know and girl fall for his kind but baya kula su" ni dai kawai sauraronsa nake yi ina saving duk maganganunsa a kaina. Nan ya zauna yake ta zuba min labarai na rayuwar Sultan a America, wani inyi dariya wani kuma inji kamar zanyi hawaye. Muna haka mukaji tsayuwar mota, ya tsorata sosai ya mike yana leka window, dariya sosai abin ya bani, wato they respect and fear him

Please Login or Register in order to submit comment