Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ina jin wani abu yana min yawo a jikina. Na jima banji irin wannan feeling din ba, tun rabo na da Ibrahim. Nayi tsaki na gyara kwanciya ta, ya kamata in nutsu in san me nake yi especially after warning din da yaya Habeeb yayi min cewa sultan is a drunk, but he didn't look or sound drunk to me. Oh dear God, don't let me fall in love with a wrong guy again. Not again. Da kyar na samu bacci ya dauke ni.

Washegari tun safe aka tafi "yalleman daurin aure, mu dai muna abuja muna ta shirye shiryen kai amarya, Zayed ya dage shi lallai babu zancen wani kafi ko gara, su a al'adarsu in kayi aure mata kawai za'a kai maka, shi wai a gurinsa abin kunya ne aga ana shigar da kaya gidansa wai daga gidan surukansa, dan haka daddy ya hada kudin duk da yayi niyyar yiwa Hafsat kayan daki ya saka mata a account dinta yace inta ga dama tayi jari dasu, in bata ga dama ba kuma ta kashe kayanta, kudin kayan gara kuma ya saya wa Zayed dalleliyar mota ya bashi a matsayin wedding gift. Tunda akayo mana waya an daura aure Hafsat take kuka tamkar wacce aka yiwa auren dole, sanda muka zo tafiya airport kuwa cewa tayi ta fasa auren ta shige daki ta rufe kanta, sai da daddy yazo da kansa sannan ta bude kofar. A hanyar zuwa airport na duba waya ta naga 5 missed calls daga sultan da message guda daya "please in kin samu chance call me" sai na samu kaina dayi masa reply cewa yanzu zamu tafi England, in naje zan kira shi da number ta ta can.

Masha Allah, gidan Hafsat ya tsaru iya tsaruwa, tsayawa bayanin gidan bata lokaci ne, likita matar likita, ina kallon gidan ina tunanin cewa some people are so lucky in life, komai yana zuwa musu da sauki. Embassy muka sauka, anan zamu yi kwana biyu sannan mu dawo Nigeria. Ranar da muka baro Hafsat a gidan miji kwana nayi ina juyi, Allah sarki 'yaruwata shi kenan an shiga layin manya. Sai kawai na samu kaina da imagining what will it feel like, ga mamakina kuma a imagination din nawa sai naga Sultan with his muscular body, red lips and shiny brown eyes maimakon Ibrahim da nake gani duk sanda nayi irin wannan tunanin. Nayi sauri na kawar da tunanin daga raina tare da sake sabuwar addu'a amma still babu bacci. Nayi tsaki na jawo wayata na duba time, 12:30am, a Nigeria zai zama around 8:30am kenan. Nayi dialing number dinsa, bugu daya ya dauka kamar mai jira. "Assalamu Alaikum" na amsa masa, sannan yace "God, saura kadan in running mad, ban taba jin haka a rayuwa ta ba, what have you done to me woman?" A raina nace kai zanyi wa wannan tambayar ai, a fili kuma cewa nayi "haba dai, da girman ka?" Yayi dariya yace "nima na dauka am strong, sai yanzu nake ganewa ashe shayi ma ruwa ne" hmm kawai nace, yace "to ya hanya? Ya kuma amarya" nace "lafiya lau, mun kaita mun baro ta, gobe zamu huta jibi mu dawo insha Allah" yace "so, tell me about yourself" nan na bashi labari na in brief, abinda ya shafi family na da karatu na, ko kadan banyi mishi zancen Ibrahim ba, shima ya fara bani labari da cewa "well, as unbelievable as it may sound, babana shine sarkin Abuja, ni ne first born sai Abbas, Saratu sannan fa'iza, nayi primary a Abuja, sec da university duk nayi su a USA. Na karanci architecture first and second degree. I have many friends but Amir shine babban abokina, he is like a brother to me" daga nan yayi shiru, a hankali nace "what about your mother?" Yayi shiru kamar ba zai magana ba, can yace "I don't know who my mother is" duk da ta cikin waya ne sai da na fahimci irin zafin da maganar da ya fada tayi masa a ransa. Ba wai besan babarsa ba, a'a bai ma san wacece babarsa ba.


Episode Thirty Nine : The Shadow 2

Jinjina ta musamman ga masoya Ibrahim. Lallai kun chika masoyan gaskiya da kuka rike soyayya har tsahon shekara biyar. Ina kuma baku hakuri dangane da jin shiru akansa, na tsara labarin ne a haka saboda in kara masa armashi yadda zaku fi jin dadinsa, amma insha Allahu nan ba da dadewa ba zamu ji labarin Ibrahim.

Jinjina ta musamman again ga masoya Sultan tunda har kuke son sa duk da kasancewar sa bad boy wannan itace soyayya ta gaskiya, kaso mutum ba dan halinsa ba.

💖 you loads

Nayi shiru maganar tana sinking a raina, sannan nace "bangane ba, how comes?" Shima shirun yayi kamar baiji abinda nace ba, munfi minti biyu a haka, ina jiyo saukar numfashinsa ta cikin wayar, can yace "can we please not talk about this? In fact yanzu nasan dare yayi sosai a England, gwara in barki kiyi bacci haka ko?" Na gane waccan maganar ce baya son yi amma nasan bani da right din da zan matsa masa dan haka nima ba bar maganar "OK, good night then" "fi amanillah" na jima bayan munyi sallama ina lissafin maganar sa, me yake nufi? What is his story?

Washe gari tun safe nake baccin gajiya har zuhur sannan inna ta tashe ni nayi sallah naci abinci na sake komawa wani baccin. Sai la'asar sannan na tashi nayi wanka na shirya dan zamu je gidan Hafsat muyi mata sallama tunda gobe da safe zamu koma Nigeria. A gidan Hafsat ne su inna da gwoggo rabi babar su nuraddeen suka yi ta yiwa Hafsat nasiha akan zaman gidan miji, nima na zauna naji kuma na karu sosai, bayan sun tashi suna kara zagaya gidan ne na saka Hafsat a gaba da tsokana wai sai ta gaya min abinda ya faru jiya bayan mun tafi, harara tayi ta watsa min daga karshe tace "wai ke yaushe na fara wasa dake ne? In auren kike so ki fada yanzu zaki ganku a gidan munir" wata harara nima na watsa mata, dan ni har mantawa nake yi da wani munir a duniya, dariya itama tayi min tunda ta kashe min baki. Sai da muka zo tafiya kuma sannan ta fara kuka, babu kunya Zayed ya kama rarrashinta a gaban su inna, sum2 suka fice ina ta yi musu dariya. Kaya sosai maman Zayed ta bamu muka tafi dashi. Washegari da safe muka dawo Nigeria. Duk 'yan biki kuma kowa ya watse sai fatan Allah ya sanya alkhairi.

Sai da aka gama watsewa sannan na fara missing Hafsat, gashi Amina ma bata nan ta bi mutanen 'yalleman zata karasa hutun ta acan. Duk gidan ya gundire ni sam babu dadi. Sultan kuwa kullum sai ya kirani a waya, yayi2 in barshi yazo gidan mu naki, saboda ina tsoron abinda zaije ya zo. A raina nasan ya kamata in dakatar da Sultan amma zuciya ta taki barina in yi haka, sosai nake jinsa a raina, dan wani lokacin ma ni da kaina nake kiransa a waya. Ranar da mukayi sati daya da dawowa daga England na tambayi mommy cewa ina so inje gidan su Amira in wuni acan sai dare zan dawo tunda na gaji da zama ni kadai, babu musu mommy ta barni tace driver ya kaini da daddaren sai ya koma ya daukoni. Na shirya cikin riga da skirt na jar atamfa mai adon fari da baki, na yafa farin mayafi, da farin takalmi, na debi wayoyina muka tafi. Muna cikin tafiya munbi ta wata siririyar hanya sai muka tarar da go slow, gurin ya chunkushe mutane sai hayaniya suke yi, nayi mamaki saboda normally gurin babu traffic, driver nane ya fita ya tambaya sai ya dawo yace min wai wani ne yayi blocking hanyar yace yau babu mai wucewa ta nan, sai dai mu koma baya sai mubi ta wata hanyar. Nayi shiru ina tunani, sai na dauko waya ta na kira number din sultan, ya dauka nace masa "kana ina?" Dariya yayi yace "na fita unguwa ne kuma sai na tsaya neman rigima" bance komai ba na kashe wayar nace da drivern ya zauna ina zuwa, na fita na kutsa ta cikin mutane har inda problem din yake, katuwar Jeep Dodge na gani anyi crossing dinta akan titin yadda ta rufe titin completely, duk glasses dinta a tinted dan haka bana hango wanda yake cikin motar, mutane sai hayaniya suke, wani naji yana cewa "to tunda ba zai dauke ba ba sai a kira masa 'yan sanda ba, in yafi karfin mu ai baifi karfin hukuma ba" wani kuma yace "to in an kira 'yansandan ma ya za suyi dashi? In sun kama shima ba zai awa daya ba za'a sake shi, su kansu yanzu sun gaji da kama Sultan" a raina nace da gaske shi din ne. Number motar na duba naga "SULTAN 3" na karasa kusa da motar, inajin wani daga bayana yana cewa "'yan mata kiyi a hankali fa, wannan mutumin is very dangerous".

Na karasa dai dai windown driver nayi knocking a hankali, da sauri ya sauke glass din fuskarsa ta bayyana dauke da murmushin mamaki "Hey, me kike yi anan?" Na daura hannayena akan windown nayi tagumi nace "unguwa zanje kuma an tare min hanya" ya kalli dandazon mutanen da suka taru a gefe sannan yace "lallai kice dara taci gida kenan" nayi dariya nace "dama ai hausawa sunce in zaka gina ramin mugunta ka gina shi gajere, yanzu kaga nice na rufta ciki" shima dariyar yayi yace "da fatan baki balla kafa ba" wani daga bayana yace "baiwar Allah dama kin rabu dashi, wannan mutumin bai san magiya ba, gashi nan an kira police zasu zo suyi mana maganin sa" Sultan ya leko da kansa yace "kafin suzo suyi magani na ni bara inzo inyi maganin ka, dan rainin hankali kawai" ya bude kofar motar ya fito da sauri, sai kuma ya kalleni ya ga yadda na hade rai sai ya koma yana cewa "kaci sa'a, amma na gane fuskarka, zamu hadu wata rana" ni kawai kallonsa nake yi da mamaki, shi babu abinda ya dame shi wai dan mutane suna zaginsa, kamar ma wani enjoying kansa yake yi. Yasa hannu ya bude min kofar kusa dashi yace "shigo in kaiki unguwar" na yi jim ina tunani, anya kuwa in shiga motar Sultan? Anya mutunci nane? Besides ba wani sanin halinshi nayi ba, kuma duk a halayensa da ake gaya min babu wani na kirki. Na sake kallonsa naga shima ni yake kallo pleadingly, oh God, kawai sai na zagaya na shiga. Mutumin da suke fada da Sultan ya saki baki yana kallon mu, ina kallon sultan ya mika hannunsa ta window yayi masa alamar fuck you. Daga nan ya daga windown ya tayar da motar muka tafi. Wani daddadan kamshi ne a cikin motar, irin kamshin nan da yake sa mutum ya lumshe idonsa, da gaske sultan dan gayu ne dan cikin motar tsaf yake, kujerun an lullube su da wani tattausan bargo wanda shi kansa kamshin yake yi. Shi kansa Sultan din gani nayi ya kara yi min kyau da kwarjini, yauma kamar kullum rigarsa body hug ce data kama jikinsa sosai amma yau 3 quarter wando ne a jikinsa, gashin kansa a hargize yake kamar kullum. A 20 yake tafiya da motar kuma gaba daya ba titi yake kallo ba ni yake kallo, har sai da naji kunya na rufe fuskata da mayafina. Motoci sai horn suke yi mana daga baya, duk wanda yazo wucewa kuwa sai yayi bala'i amma sultan ko kallonsu baya yi hankalinsa gaba daya yana kaina. Nace "wai wannan kallon na menene kuma" "duk sanda na ganki sai inga kamar kara kyau kike yi" kamar nima ince masa shima haka sai kuma dai nayi shiru nace "thank you" yace "ina zakije ne?" Sai yanzu na tuna na bar driver da mota a baya, da sauri na dauko waya ta na kira shi nace na tafi, ya danje yawo kadan sai ya koma gida yace ya kaini. A muryarsa naji alamar baiji dadin abin ba amma kuma babu yadda zaiyi. Mun danyi tafiya kadan nace "why do you do it?" Yace " me fa?" Nace "why do you block the road?" Kafin ya bani amsa wani ya danne horn a bayanmu sannan ya zo ya wuce mu a guje yana cewa "malam in ba zaka wuce ba ka bawa mutane hanya su wuce" Sultan yayi dariya yace "that's why" nima dariyar nayi nace "to kai me yasa ba zakayi saurin ba, kana tafiya a cikin abuja a 20 bayan kasan kowa a garin nan sauri yake" ya wani kwantar da kujera kashingida yace "sauri va gurin zuwa ba" da sauri nace "dan Allah ka rufa min asiri ka tashi, ya za'ayi mutum yana driving kuma ya kwanta" sai da yayi dariya sosai sannan ya tashi zaune, ni kuwa duk na rude, yana tashi wani ya yi masa dakuwa daga waje, ai kuwa ya sauke glass sukayi ta zage2 sannan muka wuce. Sai a lokacin na gaya masa inda zanje, yace "OK, inda kika tura mu rannan ko?" Muka yi dariya gaba daya. Muna tafiya a hanya ne yake tambayata me yasa nake yawo da driver? Nace masa "ban iya driving ba" yayi ta min dariya yana tsokana ta wai abin kunya kamata ban iya driving ba, yace "in kin yarda sai in koya miki" nace "not now, sai na gama school tukunna" yace "OK, Allah ya kaimu" mun danyi nisa na sake tambayarsa "yanzu dazu da kayi blocking hanya da mai martaba yazo wucewa fa?" Yace "kinsan kuwa hakan ta taba faruwa" na ware ido nace "haba? Ya akayi kuma?" Yace "kamar yadda nayi dazu, na rufe hanya nace ba shiga ba fita, na rufe glasses din mota na kunna AC na kwantar da kujera ta nayi kwanciyata, mutane suna ta hayaniyarsu da zage2n su, kawai sai ga Takawa nan ni ban sani ba, yana zuwa yaga an tsaya ya tambaya lafiya aka ce ai hanya a rufe take, yace aje a gano me ya faru, aka koma akace masa ai nine na rufe hanya da motata" yayi shiru, nace "me yace kuma?" Yace "dogarai ya aiko yace su farfasa motar su fito da ni suyi min duka su jani a kasa su kaini gida" na rufe baki na ina mamaki nace "ya salam, sunyi din kuma?" Wani murmushi ya jefa min yace "sun fasa mota alright, amma none of them will dare to touch me, duk wanda ya taba ni kuwa sai na kwantar dashi a asibiti kuma ya bar aikin sa kenan" nayi shiru ina jimamin maganar, it seems like there is crisis between the father and the son, does it has to do with Sultan not knowing who his mother is? Ina so in sake tambaya kuma bana so yaga kamar ina bi masa kwakwkwafi. Mun danyi gaba kadan sai naga ya sake hanya yabi wata hanyar daban, nayi sauri nace "ba nan ce hanyar ba fa" bai kalleni ba yace "eh na sani, sayar dake zanje inyi" nayi shiru yace "kinga kuwa zakiyi tsada" ni dai bance masa komai ba, sai a lokacin na fara lissafin babu wanda yasan tare da wa na fita, shi kansa driver din da muka fito dashi baiga sanda na shiga motar sultan ba, what if ya sace ni? Ina kallon shi ta gefen ido na yana min dariyar yadda na takure a gefe daya ina rarraba ido. Wata unguwa muka shiga irin unguwar talakawan nan, a raina nace me yake kawo sultan irin wannan unguwar kuma? I really hope he is not doing drugs kuma? Can gefe ya samu yayi packing yace "please two minutes dan Allah zanje in karbo sako" na gyada masa kai amma a raina ina cewa zaka je ka karbo drugs dinka dai. Ina kallonsa ya fita ya saka hannayensa a aljihu yana tafiya ya shige wani loko. Da sauri na dauko waya ta na kira Amira, "Amira gani na taho amma ba'a motar gida ba, ina motar sultan, in case in na bata a gurinshi zaku neme ni" na kashe wayar ina rarraba ido.

Ta mirror na hango wani mutum yana tahowa wajen motar daga opposite direction din inda Sultan ya tafi, magidanci ne zaikai kamar 45 years, ta side din driver yazo yayi knocking, ina sauke glass din ya fara kokarin durkusawa zai yi gaisuwa sai kuma yaga babu kowa a gurin. Na gaishe shi ya leko ya amsa cikin sakin fuska sannan yace "yallaban baya ciki ashe" nace "ya fita, wai zai karbi sako" ya girgiza kai yace "zai kawo sako dai, tun dazu mukayi waya yace gashi nan zuwa da naji shiru shine na dan fita" sai kawai naji ina son in san sakon menene zai kawo. Nace "sakon menene zai kawo?" Yace "kudin makarantar yara ne, kinsan an kusa komawa sabon session, to nayi masa list na school fees, kudin books da uniform tunda akwai sababbin dauka to shine yace zai kawo min yau" kaina naji ya toshe nace "yara? Wadanna yaran kuma" yace "yaran unguwannin nan mana, ai duk shi yake musu komai na makaranta, mu kam ba abinda zamu ce masa sai sam barka dan da yawa mutanen da suke zaune a unguwannin nan shi yake ciyar dasu, ya ciyar damu ya biya wa yaran mu kudin makaranta ya samarwa matasan mu aikin yi. Kinga wannan sabuwar orphanage din daya gina duk nan unguwar yazo ya dauki ma'aikata maza da mata" cikin cushewar kai nace "orphanage? Sultan din ne ya gina orphanage?" Yayi alamar rufe bakinsa yace "ai na dauka tunda kuna tare kin sani, ai baya so a sani, da nasan vaki sani ba da bazan gaya miki ba" nayi sauri nace "dan Allah baba gayamin, wallahi bazan ce kai ka gayamin ba" ya gyara tsayuwa da alama yana da surutu, ya ce "ai wannan ta biyu ce, waccan babbar ma ta cikin gari ai shi ya gina ta sai mutane suke cewa dan majalissa ne shi kuma sai ya samu dan majalissar yace yace shine yayi. Ai duk unguwannin nan na marasa karfi yana da representative da yake gaya masa duk bukatun mutane kuma in dai an fada to zai bayar, in dai har maganar kudi ce to mukam sai godiya" nayi shiru ina jinjina maganar a cikin raina. Nayi wa mutumin godiya ya tafi hanyar da naga sultan yayi, har Sultan ya dawo ina jinjina maganar mutumin nan a raina. Yana zuwa ya shiga muka tafi yace "sorry na barki kina jira" kai kawai na gyada masa, yace "are you OK? Naga kin chanza?" Nan na kirkiri murmushi nace masa ba komai, bai yarda ba dai yace "bayan na tafi wani yazo nemana?" Na girgiza kai nace "babu wanda yazo nemanka" ina ganin fuskarsa ta chanza alamar yaji dadi. Dole na ware nima dan kar ya fahimci wani abu har muka je gidan su Amira. Tun 10:30 na baro gida amma banje gidan su Amira ba sai 1:30, kamar wacce na tafi kano. Muna yin packing Amira ta fito da sauri kamar dama a bakin gate take. Sultan ya tsatstsare ni da ido wai lallai sai na yarda yazo a maida ni gida. Amira tana bude kofar ta finciki hannuna "fito daga motar nan" Sultan yana dariya yace "check her from head to toe, ban ciri komai ba" ita dai bata kula shi ba sai jana take ni kuma naki fitowa. Sultan yace "please yaushe zan zo in dauke ki" Nace "after magrib" yayi murmushi yace "thank you" na juya zan fita muka hada ido da Amira wacce ta saki baki da hanci tana kallona.


Episode Forty :TheShadow 3

Tunda muka shiga gida Amira take min bala'i. Ni dai kawai dariya nake mata. "Yanzu kinsan kuwa duk wanda ya ganki a motar sultan irin kallon da zaiyi miki? Kin san ma kuwa waye Sultan? Mutumin nan ko magana bai kamata ace ta hada ku dashi ba ballantana har ki shiga motar sa. Yanzu ma tukunna, ina kukaje da kuka dade haka baku karaso ba?" Na harare ta nace "gidan sa ya kaini. Ina ruwanki da inda muka je?" Muka shiga dakin mamanta muka gaisheta sannan muka koma dakin ta. Nan fa ta saka ni a gaba da nasiha, ita lallai gani take shiga motar Sultan din da nayi tamkar wani katon zunubi na aikata. Tace "Yanzu Allah ne kadai yasan irin maganganun da ya gaya miki, duk sai yaje ya hure miki kunne anzo an kasa gane kanki. Ki rufa mana asiri Moon ki rabu da Sultan dinnan" Nace "Saboda me?" Tace "saboda me? Yanzu har tambaya kike yi saboda me? Just look at him zaki gane saboda me. He is a criminal for God's sake. He is spoilt rotten. A gangster. A rogue. A drunk. Duk wadannan dalilan basu ishe ki ba?" Murmushi kawai nake yi ina kallon yadda ta dage tana ta bayani. Nace "yanzu in tambayeki, ya akayi kika san Sultan is a drunk?" Tace "duk garinnan waye bai san dan shaye2 bane? sau nawa ana ganinsa yana yawo a gari a buge" nace "yanzu ke kin taba ganinsa yana shan giya?" Tace "ni ban taba ganin sa ba amma.. " na daga mata hannu nace "amma me? Annabi da kansa ya hana yada jita jita, abinda baka tabbatar ba kar ka fada musamman akan alfasha" Amira ta saki baki tana kallona kamar zata yi kuka tace "are you truly depending him?" Nace "ba wai goyon bayan Sultan nake yi ba, ina goyon bayan gaskiya ne" ta sake matsowa kusa dani desperately tace "yanzu ki duba kiga irin abokansa, ki kalli wannan shegen Amir din ki gani. Kin san kuwa sunan gang dinsu? Gang Bang they call themselves. Gang din 'ya'yan manya ne wadanda suka fi karfin karfin iyayensu. Abuja, kano, kaduna, legos da duk sauran manyan states na Nigeria an sansu, Sultan da Amir sune 'yan Abuja. Moon duk wanda yake cikin gang dinnan is a known criminal kawai dai dan babu yadda za'ayi dasu ne shi yasa. Kinsan kuwa kwanan baya suka yi gang raping wata yarinya a Nassarawa state?" Ji nayi tamkar ta chaka min mashi a kirjina, amma na daure nace "ke a ina kikaji wannan labarin?" Ta daga kafada tace "a radio, a television, a social media, a newspaper ko ina zancen akeyi" nace "ita yarinyarce tace su su kayi raping dinta" tace "eh mana, anyi hira da ita har a gidan radio" na sake cewa "ita yarinyar ce tace da wane da wane da Sultan suka yi raping dinta?" Tace "just because his name wasn't mentioned doesn't mean he didn't do it" na girgiza kai na kawai ina kallonta, tace "Moon kar ki bari son da kike masa ya rufe miki ido ki kasa ganin gaskiya. Dududu yaushe kika sanshi da har zaki tunanin kinsan shi fiye da sauran jama'a? Duk abinda nake gaya miki kamar yana shiga ta wannan kunnen ne yana fita ta wancan. Already har ya riga ya hure miki kunne" ta mike a fusace ta dauko laptop dinta ta ajiye min agaba na tace "in baki yarda dani ba check for yourself, ki duba internet zaki fahimci waye Sultan" daga nan ta fice ta barni a dakin. Na jima ina kallon laptop din ina jimamin abinda bincike na zai gano min. Can na dauka na kunna direct na shiga goggle, nayi typing sultan sai naga amsoshi da yawa wadanda ba sa dangantaka da abinda nake nema. Na goge nayi typing sultan Abuja prince. Nan da nan kuwa naga an watso min hotunan Sultan, wadansu a kasarnan wasu a kasar waje. Duk hotunan babu ko guda daya da yake da manyan kaya a jikin sa, babu kuma ko guda daya da yake tare da babansa. Nayi typing criminal record dinsa, nan ma naga rubutu da hotuna da yawa, can ya daki wancan, nan yayi trashing wancan shagon, yayi causing traffic jam, duk dai labarin daya ne. Nayi shiru ina karanta labaran daya bayan daya, sai wani tunani yazo min, duk cikin labaran banji ance yayi sata ba,

Please Login or Register in order to submit comment