Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

acan, anan zai zauna" ta bata rai tace "ni dai Moon Allah ya gani bana son ki da Sultan wallahi, this is a very dangerous game you are playing. Ita behavior is contagious, idan ke baki chanza shi ba shi zai chanza ki tunda ya fiki taurin zuciya plus kina son shi da yawa. He is handsome na sani, but He is as handsome as sin. Duk wani abin zunubi zaki ga kyakykyawa ne, very tempting, dole sai ka kai zuciya nesa zaka hana kanka" nayi shiru ina lissafa maganar ta, but i know what I feel for Sultan is not lust, it is love.

Bayan munje England ma haka ce ta kasance, kullum muna tare da Sultan a makaranta dan komawa yayi kamar shima student din ne. Kullum in muna tare sai nasan yadda nayi nayi masa nasiha ta sigar lumana, ina nuna masa this is right and this is wrong, amma ga mamaki na sai naga in aya na fara janyo masa sai ya karasa min, in hadisi na dauko sai ya gayamin wani irinsa, wato yana sane da duk abinda yake yi kenan. Abinda na kara fahimta a dangane dashi shine yana da zuciya, muguwar zuciya ma, wannan shi ya saka ya ke da fada, dan a makaranta kullum ina cikin rabon fada da Sultan. Allah yaso makarantar tana da girma shi yasa har yanzu siblings dina basu san da zaman sultan ba. Sannan kuma Sultan yana da mugun kishi dan ko kallona wani namiji yayi indai kallon bai gamshe shi ba yanzu zakuji kansa, ni har dariya yake bani dan ni mai mutane ce kowa nawa ne babu mace babu namiji. Haduwar su ta farko da Mahdi nayi introducing dinsu suka gaisa kamar gaske sai bayan mahdi ya tafi sannan Sultan ya bata rai yace "I don't like him" nace "saboda me? He is nice and shine best friend dina a school dinnan" ya tsare ni da ido yace "amma kin san yana sonki" na sunkuyar da kaina nace "yes, but I don't love him, I love you".

Sau da yawa sai in samu kaina da comparing Sultan da Ibrahim. Sam basu da alaka, kamanninsu sun sha ban ban, yayinda Ibrahim yake da sanyi Sultan kuma zafi ne dashi, Ibrahim ustaz ne sultan is the total opposite of ustaz, amma abinda yake bani mamaki shine lokacin da muna tare da ibrahim har rigima mukayi dashi akan taba ni duk da kuwa lokacin ina kwaila amma sultan ko da wasa bai taba kai hannun sa jikina ba. Situation din da muke ciki da Sultan is exactly wanda muka kasance da Ibrahim, yadda yake bina duk inda na tafi, yadda yake sona kamar ya cinye ni, da kuma yadda duk nake boye su daga gurin iyayena. They are totally different but exactly the same.

A hankali ina ganin chanji a halayen Sultan, yana behaving kansa especially if I am around. Kuma har yau ban taba ganin shi a buge ba kuma na kasa tambayar sa saboda bansan yadda zai dauki maganar ba, amma nasan ko da yana shan giya to ba sosai ba saboda shi dan giya ko yayane sai an gane shi. Shakuwa ce sosai take kara shiga tsakanin mu kuma Sultan is an open guy, komai nasa yana gayamin saboda koda yaushe yana gayamin shi baya son secret. Rannan muna zaune a school yace min "tell me Love, akwai wani guy da ya kamata in san da zamansa? Ina nufin akwai wani da kuke tare kafin ni ko akwai wani da yake sonki bayan ni? I want to know" nayi shiru ina auna maganar sa, bana jin zan iya gaya masa labarin Ibrahim, there is no need saboda by now na tabbatar cewa Ibrahim ba zai dawo ba, nace "actually there is one guy, sunanshi munir" nan na gaya masa labarin munir da alkawarin baffa nayi mana aure in na gama makaranta ba tare da miji ba. Sultan ya saka hannu a cikin gashinsa yana hargitsawa, dabi'ar dana lura yana yi duk sanda wani abu ya taba zuciyarsa, shi yasa kullum gashinsa yake a hargitse. Na saka ido na a cikin nasa nace "wannan shi yasa nake son ka nutsu yadda zan kaika gida kafin in gama project dina" ya bata fuska yace "am trying, really trying, but this is me, I can't just change over night" naga maganar tana so ta bata masa rai sai na chanja topic din nace masa "to kai fa? Any girl that I should know of?" Nan take murmushi ya yi replacing damuwar sa yace "No, not Sultan. Ban taba son wata ba sai ke though akwai yarinyar da take sona, Khulsum, kanwar Hajiya ce. Farkon dawowa ta Nigeria na tarar da ita a gida, she is a good cook ni kuma I love food sai take yi min girki kullum then I realized tana da hidden agenda sai nayi ending alakar mu, she might still be in love with me duk da dai mun dade bamu hadu ba" na gyada kaina nace "it's OK" amma cikin raina na dan ji babu dadi especially inda yace ta iya girki, in akwai abinda ban iya ba a rayuwata girki ne, lol.

Bayan kwana biyu nayi deciding zan kai Sultan gidan Hafsat su gaisa. Tun safe na kira ta na gaya mata zanzo kuma zan kawo bako, sannan na gaya mata cewa I also want him to meet Zayed. Da yake ranar Weekend ce sai na gaya wa mommy zanje gidan Hafsat tace a dawo lafiya, dama mun gama plan din inda zamu hadu da sultan dan haka muna fita da driver na gaya masa inda zai kaini, muna zuwa na tarar already Sultan yana jira na dan haka nayi changin mota. Tare muka shiga palon Hafsat da sallama. Suka amsa a tare ita da Zayed. Idan sunyi mamakin ganin Sultan to sun boye dan sam banga alama a fuskar su ba. Muka zauna mu hudu muka yi ta hira, nayi ta sha'awar Hafsat da Zayed, yadda suke abubuwansu, Arabic din Hafsat ya gyaru sosai dan dashi suke magana da Zayed. Zayed yayi ta yiwa Sultan tambayoyi shi kuma yana amsawa truthfully, saboda gaskiya Sultan ba shi da karya ko kadan, bashi da boye2, duk abinda ka tambayeshi zai gaya maka, either ka karba ko ka bari. Tare mu kaci abincin rana bayan munyi sallar Zuhr, daga nan su Sultan suka fita suka barmu. Na kalli Hafsat nace "so... Fadi abinda yake ranki" tace "he loves you, that's for sure. But he is Sultan, kinsan sunan da yayi a Nigeria babu inda babu labarinsa da labarin takadirancin sa. Kema kanki kinsan cewa kin debo da zafi Moon. Kuma na tabbatar cewa har yanzu a gida ba'a san da maganar sa ba ko an sani?" na girgiza kaina, ta cigaba da cewa "you are making the same mistake as you do with Ibrahim. Bana so ki shiga da yawa kamar yadda kika shiga son Ibrahim kuma abin yazo baiyiwu ba kika zo kika shiga wani hali" nace "so nake inga na chanja shi kafin in kaishi gida, He is a good guy, kawai dai ya riga yayi wa kansa ado ne da bakin fenti, I want to have a chance dazan yi presenting dinsa as the good guy he is" Hafsat ta girgiza kanta tace "you may not have that chance, kawai kisa rana ki kai shi, in yes, yes in no, no, shikenan an wuce gurin" ita Hafsat bata fahimci cewa no dinne zuciya ta ba zata iya dauka ba, bayan heart break din dana samu akan Ibrahim bana jin zan iya daukar wani heart break din na rabuwa da sultan. Ina so inyi ta jan lokaci for as long as possible saboda bana son rabu da shi. A hanyar mu ta komawa gida sultan ya lura da changin yanayi na ya tambayeni "me ya faru?" Na girgiza kaina nace "babu komai" ya saka hannunsa a gashin sa yace "she doesn't like me ko?" Nace "no ba haka bane wallahi, ta nuna min ya kamata in kaika gida gurin daddy ni kuma am not ready yanzu" ya hade rai yace "why not? ni am ready, ke kawai nake jira ki kirawo ni" na kalle shi naga da gaske yake babu wasa, he is strong, very strong, stronger than Ibrahim, dan nasan Sultan ba zai taba guduwa ya barni ba, ba zai taba rabuwa dani ba sai dai ni in rabu dashi, wannan kuma shine abinda nake tsoro, tunda Sultan yazo duniya yake shan wahala mutane suke juya masa baya da nuna masa kiyayya, bansan abinda zai faru dashi ba in nima iyayena suka tilastamin na rabu dashi.

Nayi nisa sosai a harkar project dina dan kadan ya rage min in kammala, haka zalika project dina na psychology ma, wanda kachokam akan Sultan nake rubuta shi, ina ware light side dinsa wato behaviors dinsa da mutane suka sani da kuma shadow side dinsa wato behavior dinsa da yake buyewa, wadanda sune hakayensa masu kyau, anan na fahimci cewa halayen Sultan masu kyau sun ninka marasa kyau dan kusan rabin halayensa marasa kyau shaci fadi ne, rabin abubuwan da ake cewa yayi bai yi ba, wadansu abubuwan ma shi yake kirkira ya ce yayi saboda ya kara wa kansa tabo, gashi yanzu tabon shi zai iya jawowa a hana shi aure na. Dama hausawa sunce rana goma ta barawo rana daya ta mai kaya, rannan muna tafiya a makaranta ni da sultan wani bature dan ajinmu ya tsayar dani muna magana, Sultan duk ya gama kulewa sai faman taje kansa yake da hannunsa. Can dai ya gaji yazo ya taba Jack ta baya, ya juyo sultan yace masa "ita wannan da ka sakata a gaba kana kallonta kana mata surutu tayi kama da uwarka ne?" Jack ya bishi da kallo bai san me yace ba, Sultan ya sake cewa "Uwarka nace, shege da fuska kamar danyen kosai" ni dai ina ta kunshe dariyar da take neman kwacemin, kawai kamar daga sama sai ganin yaya Habeeb nayi a gurin yana kallona da mamaki, nan take dariyar ta tafi zuciya ta ta fara lugude a kirjina. Na gaishe shi sannan Sultan shima ya lura dashi ya bashi hannu suka gaisa, bai kuma cemin komai ba ya wuce warsa ya tafi. Tun daga lokacin ban kuma samun walwala ba har na koma gida, nasan yaya Habeeb ya taba kora min warning akan sultan kuma a lokacin nace masa babu komai a tsakanin mu to yanzu gashi ya kuma ganin mu tare kuma a England bama a Nigeria ba. Har dare ina ta sake saken amsar da zan bashi in ya tambayeni. Ina shirin kwanciya kuwa sai ga kiransa a waya, na dauka yace "ki same ni a palo" daga nan ya kashe. Na riga na gama shirya abinda zan gaya masa dan haka da confidence dina na fita gurinsa. Wani mugun kallo yake bina dashi har na zauna yace "me yake yi a garin nan kuma a Oxford kuma a tare dake?" Nayi gyaran murya nace "yaya Habibi" ya katseni "don't yaya Habibi me, ki gaya min gaskiya in ba haka ba straight daga nan sai gurin mommy zan kai ki" nace "yaya Habeeb kasan ina yin psychology, to an bani project topic" kaf na bashi labarin project dina da yadda na lura characters din sultan sun dace da project din nawa nace "to abinda yasa nake tare dashi kenan, idan ban jawoshi a jikina ba bazan iya studying dinsa yadda ya kamata ba. Amma da zarar na kammala aiki na a kansa zan yi masa kafa" naga kamar bayani na bai gamshe shiba na tashi na dauko laptop dina ba bude masa aikin da nake yi akan sultan ya karanta, sai a lokacin naga yayi ajjiyar zuciya yace "OK, but you have to be very careful, guy din is very dangerous" daga nan ya tafi ya barni ina tunani. Anya kuwa abinda nayi dai dai ne? Shi kanshi project din da nake rubutawa har yanzu ban gaya wa Sultan ina rubuta shi ba, gashi kuma nayi wa yayana karya akansa, Sultan ya sha gayamin cewa baya son secret. Amma in banyi haka ba menene a binyi. Kullum ina cikin feeling guilty saboda karyar da nake tayi ina boye boye. Dole in nemi mafita.

Na yanke shawarar zan daina ganin sultan har sai na samu solution, time is running out. Bani da abinyi a school wannan week din dan haka nayi zamana gida naki fita, wayar duniyar nan sultan yayi min amma naki fitowa nace masa bana jin dadi, wani lokacin sai yayi kamar yayi fushi amma ana jimawa zai kara kirana. Ranar Friday sati guda kenan bamu hadu ba, muna palon mu ni da Amina muna kallo har after 12, daga nan na fara jin bacci nayi mata sallama zanjr in kwanta tunda yanzu mun raba daki ita tana spare dakin part din mu. Ina bude kofar dakina naji kamshin Sultan, nayi sauri na mayar da kofar na rufe ina wara ido, aikuwa ga mamakina shi dinne a tsaye a bakin window. Da sauri na na saka lock a jikin kofar na juyo na rasa ma me zance masa "Sultan how do you get in here" ya nuna min taga, nace "amma duk security din gidan nan ta ya akayi ka wuce get na farko dana biyu, ka zagayo baya, taya akayi ma kasan waccece window na" devilish smile yayi kafin yace "baki san waye Sultan ba har yanzu" lallai sultan ya wuce duk inda nake tunani, tsalle yayo daga inda yake ya fada kan gado na kamar wani karamin yaro, sai da katakon gadon ya amsa, ni maimunatu yau na shiga uku katon gardi akan gadona, yanzu idan mommy ta shigo gurina fa? Ko Amina? Ta yaya zan fara yi musu bayani? Na tabbatar in aka zo aka kama Sultan a dakina to babu wani bayani da zanyi wa daddy ya aura min shi kuma. Nace "Sultan dan Allah ka tafi, this is very dangerous wallahi, idan wani ya ganka fa?" Bai bani amsa ba sai jawo bargo na yayi yana shanshanawa yana wani lumshe ido "hmmmmm I so much miss kamshin ki wallahi" ikon Allah sai kallo, anya sultan kansa daya kuwa. Sai a lokacin na kalli kayan jikina, riga da wando ne na bacci, Allah ya soni dogaye ne sai dai linon ne masu bin jiki. Nayi sauri na dauki hijab din sallata dogo har kasa na saka na bata rai nace "Sultan ka fitar min a daki" ya mike shima ya hade rai ya zo sai tin fuskata yace "if not?" Na kara bata fuska nace "zan danna button din alarm mintu biyu yayi yawa security zasu cika dakin nan har daddy da mommy na" ya kawo fuskarsa dai dai tawa yace "then go ahead and do it" mamaki ne ya cika ni na saki baki ina kallonsa shi kuma ya tsare ni da ido, can yace "nasan ba zaki iya ba because you love me too" murmushin mugunta ya sake yi min sannan ya koma ya yi adungure akan gadona. Ya gyara kwaciya tare da bubbuga gadon yace "zo ki kwanta" na watsa masa harara, yayi dariya yace "I will not touch in abinda kike gudu kenan, ni kaina kishin kaina nake yi akan ki, I can't bring myself to touch you. Zuwa nayi in ganki kuma muyi hira. Me yasa kika ce min baki da lafiya bayan kuma lafiyar ki kalau" na tabe baki nace "in kana son muyi magana ka fitar min daga daki gobe sai mu hadu muyi magana" shima tabe bakin yayi yace "OK then, sai da safe" daga haka ya gyara kwanciya yaja bargo ya lulluba, da sauri na karasa bakin gadon "sultan ka tashi ka fita don Allah" rokonsa nake tayi amma kamar ba dashi nake ba dan ko motsi bai yi ba, idansa a rufe amma nasan bai yi bacci ba. Na tsaya kawai ina kallonsa. Ina bin kowanne feature na fuskarsa da kallo, ban taba kare masa kallo irin haka ba, naga yadda akayi trimming sajensa yayi kyau sosai da yadda sajen ya kwalta akan fatar sa daga dukkan alama zai yi laushi, ji nayi a raina kamar in kai hannu in taba, nayi sauri na mike tsaye na bar gurin na koma bakin kofa ina tunanin abinyi, inna ce zan koma palo in kwanta that means kofar dakin zata zama a bude kenan and I can't take that risk, wani zai iya shigowa yaga sultan, and I can't take the risk of sleeping with sultan saboda I don't trust him and I definitely don't trust myself akansa. Muryarsa naji yace "in kin gama lissafin ki kashe fitila saboda bana iya bacci da haske" wato idonsa biyu ma ashe. Kofar ban daki na bude na shiga ina lissafin ko anan zan kwana ne? Kai gaskiya bazan iya kwana a toilet ba, nayo alwala na fito, ina fitowa na tarar har ya kashe fitilar ya koma yayi kwanciyarsa. Na dauki pillow na koma can bakin kofa na ajiye. Windows din dakin na rufe nayi locking ta ciki sannan na karo karfin AC. Na dauko wani bargon naje inda pillow na yake na shimfida rabi sannan na kwanta na kudunduna ba hijab din jikina sannan na sake lulluba da sauran rabin bargon. Oh ni Maimunatu naga ta kaina, yau zan kwana da gardi a dakina.

*wannan dai kam har da arias nayi muku, I love you guys so much. Stay blessed



Episode Forty Three: America

Na jima sam babu bacci a idona, yanzu mai zan ce wa daddy idan ya kamani da katoton namiji a dakina? Wato sultan shi bai san bari ba ko? Babu ruwan shi da what is right and what is wrong shi dai kawai in zuciyarsa ta raya masa yayi abu shikenan sai yayi kayansa babu ruwansa da consequences. Kunnuwa na baza ina sauraron ko zanji motsi, ko motsin Sultan ko motsin wani daga waje amma shiru banji komai ba, a haka har bacci barawo ya dauke ni. Dai dai sanda na saba tashi kafin assuba na farka, jikina duk sai ciwo yake yi sakamakon kwana a kasa da kuma takurewar da nayi a guri daya. Nayi mika ina addu'ar tashi daga bacci, Sultan ne ya fado min a raina nayi sauri na mike na kalli gadon. Babu shi babu alamunsa, babu alamun ma mutum ya kwana a gadon saboda gadon a gyare yake tsaf, to ko mafarki nayi ne? Kai ba mafarki bane tabbas Sultan ya shigo dakina jiya da daddare, na karasa gaban gadon sannan naka rose flower a ajjiye a saman wata farar takarda, na dauka na bude na karanta "na dade banyi bacci mai dadi irin na jiya ba, thanks for the night" da sauri na yayyaga takarda gaba na yana faduwa, yanzu idan wani ya karanta wannan ai sai yayi tunanin wani abu, lallai sultan, da ace bangani ba na tafi school mommy ko wani ya shigo ya ga wannan takardar kuma fa? Rose flower din na dauka na kai hancina na shanshana ina lumshe ido, kamshinta har cikin kwakwalwata da zuciya ta, na tafi da baya na fada akan gadon irin yadda yayi jiya, gadon naji gabaki daya kamshin sa yake yi. Sultan is special, he took a special place in my heart.

Ina gama shiryawa na fita palo muka yi breakfast da duk family din. Ana yi ana hira amma ni kam hankali na har yanzu ba'a kwance yake ba ina tsoron ko wani yaga sanda Sultan ya hau window na ko kuma anga fitarsa, har muka gama breakfast shiru babu wata magana mai kama da wannan, sai a lokacin na fara sakewa ina dariya. Daddy yace "Moon supervisor din ki ya aiko min da takarda akan project dinki. Yace da akwai wani experiment da zaki yi amma sai kinje John Hopkins hospital ko?" Ni fargabar Sultan ma ta saka na manta da wannan maganar nace "eh daddy, dama ina son inyi maka maganar bansan ya za'ayi ba" mommy ta ajiye spoon din hannunta tace "john Hopkins? Wai kuna nufin America?" Nace "yes mommy" nan da nan mommy ta fara daukar zafi tana girgiza kanta "wanne irin experiment ne ba za kiyi shi a duk girman UK ba sai kinje USA? Wa kika sani a america ma tukunna? Gaskiya dear kayi magana a chanza mata wani experiment din, ai a ko ina ana substitute, gaskiya ni ban yarda kije America ba" daddy kawai kallonta yake yana murmushi ita kuma murmushin nasa ne yake kara kular da ita. Yace "babu abinda zai same ta in taje america, it will be an experience to her, kuma abinda na fahimta shine ba ita kadai bace suna da dan yawan su za'a tura daga makaranta, dan haka in sunje tare zasu yi komai su dawo tare. Shi asibitin John Hopkins shine number one a duniya a harkar neurology dan haka zuwanta can din yana da muhimmanci sosai" mommy dai har yanzu kai take girgizawa alamar bata gamsu ba, daddy ya kuma cewa "look, shi kansa director na pediatric neurology department na assibitin is a friend of mine, Benjamin Carson, kafin su tafi zanyi masa waya, in hada shi da ita, mutumin kirki ne sosai, shi da matarsa Candy, idan ba kya son ta zauna a cikin students sai taje gidansu ta zauna acan, na tabbatar zai kula da ita sosai. Mutum ne mai dimbin ilmi dan yana daga cikin top knowledgeable mutane na America"

Ina bada shawarar duk wanda ya samu dama ya sayi littattafan Ben Carson, Gifted Hands da Think Big, akwai tarin ilmi sosai a cikin su.

Nan dai daddy ya dauko wayarsa yayi wa Ben waya yayi masa bayanin zuwana da irin aikin da zamu yi ya kuma roki dan Allah ya sa idonsa a kaina. Da yake weekend ne shima Ben din yana gida sai bawa matarsa suka gaisa da mommy. Har suka gama wayar dai mommy bata saki fuskarta ba. Daddy yana fita ta saka ni a gaba da tambaya, tare da su wa zamuje? Kwana nawa zamuyi? Nace mata "6-8 weeks" nan ta kara tayar da hankalinta, nace mata "mommy ba gashi nan daddy yace a gidan uncle Ben zan zauna ba? Tunda shine shugaban gurin nan kinga tare zamu ke zuwa asibitin in mun gama abinda zamuyi mu dawo gida tare" mommy tace "Moon mutanen nan fa ba musulmai bane ba, in fact they are very devoted christians, bana son kije gidansu suna kira miki jesus da yesu, kuma duk gidan nasan sun rarrataya cross, malaikum rahama ba zasu shiga ba gashi kema kuma kina ciki" nace "to mommy in hankalinki bai kwanta ba ki barni kawai in zauna a lodge din da za'a bamu, a cikin quaters din asibitin ne, kuma kowa nashi daban ne, mom trust me" ta dan saki fuskar ta kadan sannan tayi tsaki tace "ni dai da zaku fasa tafiyar nan da sai hankali na yafi kwanciya" nayi ajjiyar zuciya a raina nace "nima da zamu fasa tafiyar da sai hankali na yafi kwanciya" tun sanda aka yi mana maganar tafiyar nake tunanin yadda zata kasance, akai na bani da matsala, problem dina Sultan ne, dole in gaya masa zancen tafiyar kuma I am 90% sure sai ya bini, and that's my problem, bana son ya bini, especially after ziyarar da ya kawo min jiya a cikin gidan mu ma kenan wanda yake cike da security ballantana in na tafi wata duniyar ba daddy ba mommy.

Ban gaya wa sultan zancen tafiyar ba sai ana gobe zamu tafi, a tunanina ai in lokaci ya kure ba zai samu chance din bina ba, bawai inason rabuwa dashi bane a'a sam bana jin dadin yadda nake wa iyayena karya akansa sannan kuma har yanzu na kasa samun courage din zuwar musu da maganarsa. Tun da naje school muna tare dashi har aka zo daukana amma na kasa yi mishi maganar, sai bayan nazo gida nayi shirin kwanciya sannan na kira shi a waya, ya dauka da sallama kamar yadda ya saba, na amsa masa sannan yace "are you already missing me, love" nadan yi dariya sannan nace "magana nake

Please Login or Register in order to submit comment