Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

husband to be, ko kana da abinda zaka yi akai?" Wata harara Munir ya watsa masa yace "da masu hankali nake magana ba da bugaggu ba" da sauri Sultan ya yunkura zai kai masa duka nayi sauri na rike shi, nasan a yadda sultan yake a yanzu Munir duka zai yi masa dan gaba daya alcohol din ta zuke karfin sultan. A fusace Munir yace "cikashi kizo mu tafi" nace "am not leaving him here" da mamaki kawai ya tsaya yana kallona yama rasa me zai ce min. Wata taxi ce ta tsaya a gaban mu Amir ya fito da sauri ya karaso in da muke, yace "Moon ya akayi kuka fito nan, what if someone sees you?" Sai kuma ya juya ya kalli munir yace "waye wannan kuma?" Takaici bai barni na bashi amsa ba, nace "ina ka tafi? Dare yayi sosai, I needed to go home, ba zan iya tafiya in bar shi ba, babu wanda na sani a ciki ballan tana in nemi taimako, ina ka tafi?" Kamar zaiyi kuka yace "am so sorry Moon, na dauki motar da Sultan yayi accident da ita niyya ta in kaita gida sai in dawo in dauke shi a mota ta, na hadu da police a hanya sunga damage din da motar tayi suka tare ni suna ta yimin tambayoyi, sai da naje station nayi cike cike sannan suka barni na tafi, I thought zaki kira ni a waya ma, dan Allah kiyi hakuri" nace masa "ai babu waya a hannuna, wayar sultan kuma tana hannunka" ya kuma kallon munir da har yanzu yake tsaye yana sauraren mu yace "waye shi?" Da takaici nace "shine wanda akayi alkawarin za'a aura min a gida" Amir ya dora hannunsa aka yace "ya Salam, am so sorry Moon" Munir yace "are you guys done? Saboda na matsu muje gida inji bayanin da zaki yi musu" nace "ni ba zan shiga motar kaba, ai ba tare muka zo ba, kayi tafiyarka kawai" wani murmushin mugunta yayi sannan ya dauko wayarsa ya fara dannawa yace "in ba zaki shiga mota taba, bara in kira wanda dole ki shiga tasa" kafin inyi wani yunkuri naji yana cewa "Hello Walid kana ina? Guess wa na gani yanzu? Moon. Au dama nemanta kume yi? a buge na ganta a hannun wani gardi suna ta marisa a gefen titi. To shikenan in baka yarda ba kazo ka gani da idonka." Daga nan ya fada masa inda muke ya kashe wayar. Har yanzu murmushin nake yace min "mu zuba ni da ke mu gani, lets see idan gobe ba'a daura mana aure ba" Kaina naji yana wani irin juyawa, idona har wani dishi dishi nake gani. Wata zuciyar tace min in kwashi takalma na a hannuna in fita a guje, wata kuma tace min in dauki halin Sultan in rufe Munir da duka. Na juya na kalli Sultan idona cike da kwalla, daga ganin sa kasan zuciyarsa tafasa kawai take yi amma babu karfin yin wani abu akai, a raina nace 'daga yau zaka fara fahimtar illar shan giya'. Amir kam gaba daya hankalinsa ya tashi, da sauri sauri ya wuce ya shiga cikin hotel din can sai gashi ya dawo da motar sa. Ya bude kofa yazo zai kama Sultan amma sultan ya tubure yaki tafiya, nace "Sultan ku tafi gida kafin yaya walid yazo ya same ku" na juya gurin Amir nace "Amir ka kira doctor din palace sai ku hadu dashi a can ayi dressing kafar" Sultan ya rike hannuna yace cikin gaskararriyar murya "I am not leaving you here, gurin nan bashi da kyau, and am not leaving you tare da wannan mutumin" na rike hannunsa nima, a raina ina jin tamkar wannan shine gani na karshe da zan yi masa a rayuwata. Sam babu kwalla a idona nace "Sultan kayi min alkawarin ko ina nan ko bana nan wannan itace rana ta karshe da zaka kuma shan giya, kayi min alkawarin duk sanda ranka ya baci zaka rungumi alqur'ani not alcohol. Sultan please promise me that you will fight for us, bawai fada zaka yi ba, show people your true self wannan shi kadai zai saka a baka ni. Please sultan, ka manta da zancen destroying family name dinka, koda ba za kayi dan kanka ba, do it for me and for our unborn children, tunda in dai na aureka shi family name din naka shi ne dai sunan da zamu yi bearing ni da 'ya'yan mu" ya saki hannuna daya ya jawo ni jikinsa, ina jin yadda zuciyarsa take bugawa da karfi a kirjinsa, a kunne na ya rada min "please don't leave me, let's runaway together, let's go back to America" nayi kokarin kwace jikina ya kara rikeni "please, I can't live without you" na zame jikina ina girgiza kaina nace "no Sultan, guduwa ba shine solution ba, solution shine mu samu albarkar iyayen mu, in muka gudu ba zamu taba ganin dai dai ba a rayuwar mu" duk da irin son da nake wa Sultan, bazan taba iya guduwa daga gurin iyayena ba, duk da nasan irin abinda yake jira na a gida amma nasan abinda zan fuskanta inna gudu sai yafi wannan, ni ina ji a jikina cewa fitowar da nayi ba tare da sanin iyayena ba shi ya zawo komai ya kara chakude min. A ganina worse abu da 'ya zata yiwa iyayenta shine ta gudu ta barsu, duk duniya babu wanda yake son ki ko kuma wanda zai soki sama dasu, in kika gudu kika bar su kullum zasu zamo cikin tashin hankalin rashin sanin halin da kike ciki, wannan tashin hankalin nasu kuma ba karamin bala'i bane a gurin ki.

Tun daga nesa na hango motar ya Walid ta shigo layin, Sultan ya kara rikon da yayi wa hannu na, na kalli Amir nace "take care of him please". Yana zuwa yayi packing ya fito yana bin mu da kallo daya bayan daya, idonsa ya sauka akan hannayen mu ni da sultan. Munir ya karasa gurinsa yana cewa "kaga ni ko? Yanzu ka yarda da abinda na gaya maka? A rungume take a jikinsa ma ganin ka ne ya saka ya sake ta" ya Walid bai ce masa komai ba ya karaso in da muke tsaye ni da sultan, kallo daya yayi wa Sultan ya dawo da kallonsa kaina, muna hada ido na sauke kaina kasa amma na kasa cika hannun Sultan. Wani wawan marin da ban taba tsammanin ya Walid zai min ba shi ya sakar min, sai da na dena gani for some seconds, taste din jini naji a bakina, ina dago kaina naga ya sake daga hannu zai kara min wani, na runtse idona ina jiran saukar marin, wannan karon nasan completely zan karasa makancewa. Jin marin bai karaso ba yasa na bude idona dan ganin abinda ya tare shi. Hannun Sultan na gani rike da na yaya Walid, ba zan iya kwatanta expression din fuskar saba, murya can cikin makogwaro yace "don't you dare hit her again" da dayan hannun ya Walid ya wanka wa Sultan shima na shi rabon, daga ganin marin nasan yafi nawa karfi dan sai da sultan yayi baya kamar zai fadi Amir ya rike shi, sannan yaya Walid ya nuna shi da hannunsa yace "an dake ta din, me zakayi akai?" A raina nace 'ayyah ya Walid, dan dai Sultan ba dai dai yake ba da yau sai ka kwanta a asibiti' ban dawo daga tunani na ba naji ya Walid ya damki gashina ta cikin hijab daga baya ya fara jana, wata azaba naji tamkar zan saki fitsari a wando, a haka ya jani har mota, inajin Sultan yana kwalla min kira amma zafin rikon da ya Walid yayi min ya hanani magana, kafin mu karasa mota Munir ya bude kofar baya, ya Walid ya watsa ni ciki tamkar kayan wanki ya mayar da kofa ya rufe, ina jinsa ya tada motar ya ja muka tafi. Sam babu hawaye a idona sai fuskata data kumbura side daya. Muna tafiya wayarsa tayi kara ya dauka yace "Hello mommy gamu nan mun taho, she is OK but sai munzo dai" Ina jinsa yayi horn aka bude mana gate muka shiga gida, yana packing ya zagayo ya bude kofar baya ya ya fito dani, he half drag me zuwa palo, muna shiga ya watsar dani flat a tsakiyar palon. Ban dago kaina ba ballanta na in san suwaye a palon. Muryar mommy naji tana magana a nutse tace "ka gayawa daddyn ku?" Ya Walid yace "a'a, naga yanzu a can cikin dare ne shi yasa na bari sai da safe tukun na" mommy tace "ka barshi, ni zan gaya masa" yace "Ok mommy" yadda take maganar a nutse ne ya bani mamaki sabida nayi zaton kafin muzo zan tarar ta hargitsa gidan gaba daya. Na dago kaina ina kare musu kallo, mommy tana tsaye a tsakiyar palon ta rungume hannayenta, daga can gefe daada a kan kujera tana ta sharbanen majina, Ya walid yana tsaye shima a kusa da mommy, ya Habeeb yana zaune daga bayana. Mommy ta kura min ido tana kallona sannan tace "kai ka dake ta ne?" Ya Walid yace "eh" sannan tace "Habibi kira David kace asa muna bukatar karin securities a gidan nan, kace masa nace munyi receiving threats, duk wanda suka ga zai hauro mana su harbe shi" wata muguwar faduwa gaba na yayi, na mike zaune daga kwancen da nake. Ta cigaba da magana tana zagaya palon, tace "ina da labarai da yawa akan yaron nan, he is capable of doing anything, nasan zai iya yayi attempting shigowa ya dauke ta. Yazo har gida ya dakar min da, sannan ya dawo yayi kidnapping yarinya ta, in ya sake dawowa for the third time ina da right din da zan saka a harbeshi in self defense" cikin rawar murya nace "mommy he did not kidnap me" marin da dazu yaya Walid bai karasa min ba shi yayi min yanzu, wannan karon kunnena ne naji ya dena ji, sanda na dawo hayyacina a kwance na ganni again. Daada ta kara sautin kukanta kamar ita aka mara. Sama sama naji mommy tana yiwa ya Walid fadan kar ya sake dukana, tace "duka is not a solution to kangararrun yara" kalmar kangararruce ta tsaya min a raina, wato nima yanzu na shiga layin kangararru kenan. Na kuma tashi na zauna ina jinsu suna ta plans na security, a raina nace 'indai sultan yayi niyyar shigowa gidan nan sai ya shigo, but I don't think he is coming, not today' Mommy ta kalleni tace "tashi ki tafi daki" na mike sum sum2 nayi hanyar stairs sai kuma tace "ah ah ah, bani wayoyinki" na nuna mata hannayena nace "ban fita dasu ba dama" tace "Habeeb bita ta baka ka kawo min, manyan wayoyinta guda biyu da karamar Nokia, da laptops dinta biyu, ta hado maka da ATM cards dinta guda biyu suma. Kayi locking kofar balcony dinta sannan in ka fito ka rufe kofar dakin daga waje ka taho min da keys din" mommy is surely harder than steel, tun ina yarinya nasan she is thorough a duk al'amuranta. Muna shiga daki na bawa yaya Habeeb duk abinda mommy tace, bai ce min komai ba ya rufe kofar balcony ya zare key din, ko kallo na baiyi ba ya kwashi kayan ya fita sannan yayi locking kofar daga waje.

A gaban gado na durkushe fuskata tana min radadin marin da nasha. Na kusa kaina a tsakanin kafafu wana ina neman kuka amma yaki zuwa. Wani zafi nake yi a kirjina. Kamar yadda na saba duk sanda nake jin irin wannan yanayin sai na fara kiran sunayen Allah 99 a fili amma a hankali, kafin in kai karshe naji raina ya danyi sanyi. Hijab din jikina wanda gaba daya warin giya yake na cire na shiga toilet nayo alwala nazo na yi sallar isha sannan na dauko alqurani na na fara karantawa a hankali, wata nutsuwa ce take shigata a hankali, kamar some kind of assurance cewa everything is going to be alright. Sai da naji muryata ta fara dashewa sannan na rufe alqur'anin na kwanta a kusa dashi, na ki barin zuciyata tayi tunanin sultan saboda kaina ba zai iya dauka ba. A hankali bacci ya fara daukana. Ana kiran assuba na tashi na fara kawo nafiloli sannan da akayi assalatu nayi sallar assuba amma da nazo yin addu'ah sai na rasa me zance, what if Sultan ba shine alkhairi a gare ni ba, ko kuma nima ba nice alkhairi a gare shi ba? Dan haka kawai sai na yi addu'ar Allah ya bamu ikon cin dukkanin jarabawar da zai yi mana, ya bamu karfin zuciyar daukan ko menene zai taho mana kuma ya zaba mana mafi alkhairi a duniya da kuma lahira.

Da gari ya waye ina kwance a gado naji an bude kofar dakin, nayi sauri na mike zaune, mommy ce ta shigo sai mai aiki a bayanta, a ajiye tray da abinci a ciki ta fita, na ce "mommy good morning" ba tare data kalleni ba tace "ki tashi ki ci abinci" daga haka ta fice tare da rufe kofar. Tunda nazo duniya yauce rana ta farko da na gaida mommy bata amsa ba, It feels really bad, wato haka Sultan yake ji kenan tunda yazo duniya. Ban kalli in da abincin yake ba na cigaba da kwanciyata har zuhr tayi. Ina zaune a kan sallaya aka sake bude kafar, wannn karon Asma'u ce, tajiye trayn hannunta ta kalli na safen da ko taba wa banyi ba. Tace "mai sunan daada ki ci abinci mana? Ya za'ayi mutun ya zauna babu abinci?, murmushi kawai nayi mata na cigaba da jan charbi na. Bata dade da fita ba aka sake bude kofar, wannan karon mommy ce ita kadai. Ta zauna akan bedside drower sannan tace "tashi kici abinci" banyi mata musu ba na dauko trayn ba bude na zuba abincin na fara ci, sam ji nake abincin babu taste amma haka nake hadiyewa da kyar, ina gama cin abincin ta dauke trayn ta fita ta rufe kofa. Sai da akayi la'asar sannan ta dawo, yanzu ma ina kan sallaya ta zauna akan bedside tace "zo nan" na mike naje gabanta na tsugunna, tace "tashi ki zauna a kan gado, ba musu na tashi na zauna ina kallon kasa tace "Maimoon ina so ki gaya min gaskiya, in kika yi min karya abinda zanyi miki sai yafi wanda nayi niyya" a hankali nace "to mommy" tace "tun yaushe kuke tare da Sultan?" Nace "tun bikin Hafsat" tace "shekara daya kenan?" Nace "eh" ta gyada kai tace "good, yaushe ne kuma ya fara koya miki shaye shaye?" Da sauri na dago kaina ina kallonta "mommy nice fa, Moon ce fa mommy" ta dauke kanta tace "I don't know you anymore, Moon din dana sani ba zata bi saurayi gidan giya ba, Moon din dana haifa na raina ba ita ce wannan a gaba na ba. Just answer the question" sai yanzu sannan hawaye suka zo idona, na rufe fuskata da hannayena ina kuka, ta sake cewa "just answer the question, tun yaushe yake kaiki bar?" Nace "wallahi mommy ban tana shan komai ba. In baki yarda ba kisa ayi min drug test" tace "OK, ina son ki gaya min komai and I mean everything da ya faru tsakanin ku" nan na fara bata labarin tun haduwar mu dashi a abuja har komawar mu England shima ya bi mu, sannan na bata labarin bina da yayi America da duk abinda ya mu kayi a can amma na cire labarin abinda ya faru ranar da zan dawo, oh no I can never tell her that, sannan na bata labarin dawowar mu Nigeria da plans din mu na kai maganar gaban iyayen mu, na gaya mata kuma abinda ya faru tsakanin su da yaya Habeeb da kuma bin Amir da nayi zuwa gurin sultan. Na kara da cewa "mother, he is not a bad person, he is a good person. Dan Allah ku tsaya ku fahimce shi" ta yi ajjiyar zuciya tace "you are not as smart as we all thought you are, moon he is playing you. Mutane irinsa abinda suke yi kenan, su samu yarinya kamarki su yaudare ta su bata mata rayuwa suyi dumping dinta. Tunanin ki bai taba baki cewa duk wadanda suke zuwa suke baki labari akansa shi ya ke turo su ba?" Na girgiza kaina nace "mother this is for real, wallahi da gaske ne, I trust him" ta mike tsaye tare da ajjiyar zuciya tace "Maimoon, you are no longer allowed to see or talk to Sultan in dai na isa dake" na fado daga kan gadon na rike kafafuwanta, ina kuka nace "Mommy kiyi min rai, mommy wallahi in kika raba ni dashi mutuwa zanyi, purnish me duk yadda kike so dan Allah karki raba mu" ta kwace kafarta taje bakin kofa tace "you really have no idea about your situation. Already munir yayi waya 'yalleman ya gaya musu abinda ya gani jiya, it is just a matter of time kafin baffa ya turo a bincika masa, so you really understand why I want you as far away from sultan as possible? He is who he is and you are who you are" ta bude kofa ta fita ta barni a durkushe a gurin. Innalillahi wa inna ilaihir rajiun. Allahumma ajirni fi musibati wa aklifni khairan min ha. I can only imagine yadda Hajja zatayi ta yawo da maganar nan. Allah ne kadai yasan irin karyar da munir ya kara akan abinda ya gani din. Na dafe kaina daya fara sara min.

Washe gari da assuba mommy ta shigo da breakfast a hannunta ta saka ni a gaba na ci, sannan tace in tashi inyi wanka, naje naji na fito na tarar ta ajiye min kaya har da underwears akan gado tace in saka, a raina nace ina zamu je kuma da sassafen nan? Ni dai na shirya na zauna ina kallonta, ta kalleni cikin ido tace "you are going on a journey, ke da daada, ba za ku dawo ba har sai kin manta da Sultan" na durkushe a gabanta nan da nan na fara kuka ina rokonta, ko saurare na bata yi ba, tace it's for my own good, a karshe dai nace mata "mommy, ina son magana da daddy" tace "mun riga munyi maganar dashi, shine ma ya bada wannan shawarar" mommy is a bad liar, in dai tayi karya sai an gane, ina kallon fuskarta nasan daddy bai san maganar tafiyar nan ba. Zata tura ni wani gurin da Allah ne kadai yasan inane, ba tare da sanin daddy ba ballantana wani dan haka Allah ne kadai yasan ranar dawowata. Allah gani gare ka.

When everything seems lost, always have hope. Have faith that God is planning something for you. Believe that God's plan is the best.



Episode Fifty Two : The Journey

Munir, ni mai nayi wa Munir a rayuwa? Kawai dan nace bana son sa? Ai ba yaudarar sa nayi ba, tun farko na gaya masa bana sonsa kuma ni ban saka shi lallai sai ya jirani ba shi yaga dama. Na gane mugun nufinsa so yake yayi ruining reputation dina yadda lallai koda na dage bana donsa sai iyayen mu sun tilasta min na aure shi. Ni kam ban masan me zanyi ba in aka aura min Munir. Ina nan a durkushe a gurin ina hawaye har ta dawo, daga bakin kofa ta tsaya tace "let's go" na kuma rike kafarta "mommy dan girman Allah ki bani wayata, wallahi ba sultan zan kira ba, mommy dan Allah ko Hafsat ki barni inyi magana da ita" ta hade rai tace "am not stupid Moon, ni na haife ki ba ke kika haife ni ba, in dai har zan baki waya menene amfanin kaiki wani gurin. Tunda har kika san ki fita daga gidan nan ki tafi gurin saurayi ai zaki iya komai moon. Moon daga bar fa aka dauko min ke kina warin giya. Moon kece fa har da daukar saurayi ku tafi wani kasar. Duk abinda nayi miki har kina da bakin rokona mercy. In dai har ni na haife kiba zaki kara ganin yaron nan ba har abada. Kuma in dai har ni lawyer ce sai na tabbatar yaron nan yayi jail time saboda ya zama darasi a gare shi da sauran masu hali irin nasa" sautin kukana na kara, tashin hankali na shine jin tace sai ta rufe sultan, sanin halin mommy i know she is not bragging. "Mommy kiyi min rai dan Allah karki taba Sultan, dan Allah ni kiyi min komai, laifi nane, ni naje gurinsa bashi yazo gurina ba, he needs help mommy not more suffering. He will loose himself completely idan ya rasa ni kuma aka rufe shi" ta karaso inda nake tana kallona, ni kuma na sunkuyar da idona kasa tace "did you have sex with him?" Na dora hannayena aka na rusa wani sabon kukan tace "answer me, did you? How many times?" Kuka kawai nake na kasa bata amsa, mommy ta riga tayi nisa duk abinda zance mata ba zata saurare ni ba. Tace "ba zaki amsamin ba sai na kira Walid ya nakasa min ke tukunna? Did you?" Na girgiza kaina da sauri "no mommy, never" ta jima tana kallona kafin tayi deciding gaskiya nake fada, tace "tashi mu tafi" nace "ban dau kaya ba ai" tace "no need, na hada miki already" na juyo na kare wa dakina kallo, sannan na fita ta biyo ni a baya. Babu kowa a palo, haka ta tisa keyata muka fita waje, daada na gani a tsaye gaban motar mommy, baya mommy ta saka na ta rufe kofar ta zagaya zata shiga drivers seat. Yaya Habeeb na hango ya fito daga part dinsu da gajeran wando da singlet, daga dukkan alama jogging zai fita, tsayawa yayi da sakakken baki yana kallon mu muna shiga mota, wannan shi ya tabbatar min da cewa suma basu san da wannan tafiyar ba, da sauri ya karaso "Moon ina zaku je" bani da amsar da zan bashi sai kawai na daga masa hannu alamar 'oho' ya karasa gurin mommy tun kafin ya karasa ta watsa masa harara, ya juyo ya sake kallo na sai kuma ya juya da sairi yana kwalla wa ya Walid kira, tun kafin ya shiga part din nasu mommy ta ja motar dan haka ya tsaya kawai yana kallon mu, munje gate na juyo naga ya Walid ya fito shima ya tsaya yana kallon mu fuskarsa dauke da mamaki.

Titi babu kowa dan haka mommy ta ke kwarara gudu san ranta, ta gaban palace muka wuce, na kalli gate din ina lissafin ko Sultan yana ciki? Na lumshe idona knowing this is the closest I can get to him. Airport muka je, a raina nace kasar zamu bari kenan gaba daya. Muna zuwa muka fito muka shiga waiting room muka zauna, ni dai bance musu komai ba, sai da aka fara kiran flight naji an kira Niamey sai naga sun mike, zuciyata naji tayi min fari kal, dan dai Niamey ai bani da problem, wato mommy gidan su zata kaini kenan, ina zuwa zan karbi waya a gurin cousins dina na can in kira daddy in kira Sultan. Na mike da kwarin jikina, amma ban saku fuskata ba dan kar ta gane ban damu da zuwa Niamey ba. Wata jaka ta miko min tace "ga magungunan ki nan kullum zaki rinka shan dai dai" na duba naga magungunan hawan jini nane, watk mommy tasan sai jini na ya hau shine ta dauki precautions. Na rungume ta ina hawaye nace "am sorry I failed you mother" ta dan shafi bayana kadan sannan tace "it's ok, Allah ya kiyaye hanya" daganan ko fuskata bata kalla ba ta juya ta fice daga gurin. A jirgi hankali na a kwance muke tafiya, ni ce har da bacci, dan nasan 'yan Niamey sosai dan haka bani da matsala. I will come back to Nigeria in less than a week. Hmm

11 na safe a Niamey tayi mana,

Please Login or Register in order to submit comment