Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dan tsorata kadan "is the baby coming?" Na girgiza masa kai, "asibiti zamuje, za suyi min aiki su fitar da babyn" a take naga tashin hankali a rubuce a fuskarsa, na rike hannunsa sosai nace "don't do this sultan please, I need your support and strength. Please don't freak out" ya dan nutsu kadan yace "me yasa kika ce zasu yi miki aiki? Kince kuma ba labor kike ba" nan nayi masa bayanin duk situation dina da risks din da naje facing. Sosai naga hankalinsa ya tashi, ya daki stirring wheel da hannunsa yace "damn it, I hate that Ibrahim" na bata rai nace "Ibrahim bai dora min ciwo ba Allah ne ya dora min. Ba akaina aka fara ba ba kuma akaina za'a gama ba. Tunda na samu ciki lafiya lau nake, ko mugun laulayi banyi ba, wadansu matan daga ranar da suka samu ciki ba zasu samu lafiya ba har sai sun haihu. Wadansu matan talauci ya saka ko abinci mai kyau basa samu a lokacin da suke da ciki, wadansu matan basa samun medical care, wadansu matan zasi hadu da ciwo irin nawa amma basu san menene ba kuma su zo su fara labor a haka, a karshe su samu matsala koma su mutu gaba daya. Amma ni na samu komai, komai da nake bukata na samu, abinda nake bukata a yanzu shine support dinka, together we will get through this" ya dan nutsu ya dakata yana kallona, na mayar da idona na rufe inajin kaina tamkar zai rabe gida biyu, ga wani jiri da nake ji duk da cewa a zaune nake. Naji hannun sultan yana shafa fuskata, na dan bude idona ina kallonsa, na rike hannunsa da yake kan fuskata nace cikin sanyin murya "I need you to be strong" ya hadiye wani abu a makogwaronsa yace "yanzu me zamuyi" nace "asibiti zamuje. Amma please bana son ka kira kowa, Mommy da ummee in suka zo zasu kara min pressure ne. We can do this alone. Everything is going to be alright" da hannu daya ya dauko wayarsa yayi dialing, na fahimci doctor na yake kira, yana dauka ya fara masa bayanin abinda nace masa da kuma symptoms dina, banji mai doctor din yace masa ba yace "alright, we are on our way" ya kashe, hannun na yana cikin nasa ya kunna motar yayi reverse muka dau hanyar hospital, na koma na kwanta na rufe idona. Sama sama naji shigowar mu asibitin, naji sultan yana gayawa doctor a waya cewa gamu mun iso, hannunsa daya a rike da nawa dayan kuma ya saka yana shafa fuskata, na dan bude ido da niyyar in kalleshi amma hasken fitulun cikin asibitin ya saka na mayar da idona na rufe ba tare dana kalle shi din ba, naji zuwan doctor gurin mu, ya kunna fitilar wayarsa ya haska ni, na kara runtse idona saboda bana son hasken, yace da sultan "gwara da Allah yasa kuka taho yanzu baku zauna kunce sai safe ba, she is in critical condition and we will have to take the baby out now" sultan yace "yes, haka tace". Doctor din ya tafi sai ga wasu nurses sun kawo gadon daukan marasa lafiya, sultan ya chika hannuna ya zagayo ya dora ni akan gadon aka tura ni zuwa cikin asibitin. Ko sau daya sultan bai cika hannuna ba har aka kaini dakin da za'a shiryani. Doctor ya kawo wa sultan takardu yayi signing, har zai fita sultan ya tsayar dashi ya fara magana muryarsa kamar wanda zaiyi kuka yace "doctor please, nasan kasan aikinka ba wai koya maka zanyi ba, but please if anything should arise, in kana ganin Moon zata iya samun wata matsala, please doctor just forget about the baby and save my wife. Gwara in rasa shi akan ace wani abu ya same ta" doctor ya dawo ya tsaya a gaban sultan ya dora hannunsa akan kafadar sa, fuskarsa da murmushi yace "Our Prince, insha Allah nayi maka alkawarin zan kawo maka matarka da dan ka lafiya lau, babu abinda zai same su duk su biyun" sultan ya danyi murmushin yake yace "thank you doctor" doctor yace "amma nima ina bukatar wani taimako daga gareka, akwai maganar da zamuyi ka biyo ni office yanzu" sultan ya dan juyo ya kalleni yace da doctor din "bazamu iya maganar anan ba? Cos I don't want to leave her alone" doctor yace "OK, sai muyi anan din" suka zauna akan kujera doctor ya fara magana yace "kaga dai halin da take ciki yanzu, dan haka dole ba zamuyi mata anaesthesia ba, muna bukatar control over her bp, in muka yi mata allurar bacci ba zamu samu wannan control din ba, we need to keep her awake through the entire operation. Da akwai aikin da ake yi na ido biyu, zamu kashe lower part of her body yadda ba zata ji zafin komai ba har mu gama. Taimakon da nake nema a gurinka shine ina so ka shiga operation room din a tare damu ka zauna a kusa da ita kana yi mata magana mai dadi wacce zata kwantar mata da hankali" sultan yayi saurin girgiza kansa yace "I can't watch" doctor yace "you won't. Zamu saka labule a saman cikin ta mu raba ta biyu, her upper part tana gurinka zaku ke maganar ku, her lower part yana gurin mu muna aikin mu, baza kusan ma muna yi ba sai in mun gama muyi muku magana. Just don't let her sleep" sultan ya gyada kai yace "OK. I can do that" doctor ya mike tsaye yace "and we will need blood, just in case" da sauri sultan yace "you can take mine" doctor yayi murmushi yace "in yayi matching da nata ba. Zamu gwada mu gani in yayi dai dai sau mu dauka, in baiyi dai dai ba kuma sai ka samo mana wasu 'yan'uwanka ko nata a gwada a cikinsu ko za'a samu". In less than one hour da zuwan mu asibitin har an shirya ni suma doctors din sun shirya, duk abinda suke ina jinsu amma bana cewa komai saboda magana ma kara min ciwo take, idona kuma a rufe saboda bana son haske. Sai da aka tura gadona cikin theatre room sannan nayi nadamar cewa da nayi kar a kira kowa, ji nayi babu abinda nake son gani irin Mommy na da Daddy na, kuka naji yana taho min, nayi sauri na mayar dashi dan nasan ina fara kuka zan kara wa kaina ciwo kuma sultan zai kara rikicewa, so far dai yayi abin kirki sai dai ko dai dai da second daya bai matsa daga kusa dani ba. Muna shiga suka yi min wata allura a tsakiyar bayana mai dan karen ciwo, amma tana shiga naji kamar an yanke min daga cikina zuwa kafafuwana, kamar ba'a jikina suke ba, na juya ina kallon sultan wanda idonsa ya kada yayi jawur nace "ka kira daddy ka gaya masa. At least they will pray for me" ya dauko wayarsa, na lura hannunsa har rawa yake, bai iya kiran Daddy ba sai text ya tura masa. Aka sauko da labule aka raba jikina biyu. Sai ya zamana kamar ba'a daki daya muke da doctors din ba, jikina ya bani sun fara aikin amma banji komai ba. Na kalli sultan daya kankame hannuna kamar za'a kwace ni, nace "naji kamar cewa akayi kayi min hira" ya danyi murmushi nervously yace "labarin me kike in baki" nace "anything. Kamar the best day of your life" yace "da akwai ranaku da yawa da zan iya kira da best days of my life. Kuma duk days din da akwai ki a ciki. Because you are my life. Rana ta farko ita ranar dana fara ganinki. It was the day that my life begun. Daga nan sai days din da muka yi spending a America, I will never forget those days. Daga nan sai ranar daurin auren mu and then our first night, you took away not only my body but also my soul. Then, ranar da Takawa ya kira ni da his little love and asked for my forgiveness. Sai ranar dana fara ganin Ummee na. Sai kuma ranakun mu a Maldives" yayi murmushi yace "seriously ban so muka dawo ba" nayi murmushi nima, yace "rana ta karshe a yanzu ita ce yau, ranar da zamu ga result of our love. Zamu raine shi together, mu bashi tarbiya da soyayya da kulawa, we will give him all the things that I missed in my childhood. He is going to grow up to be better than me saboda he have the best mother in the whole world" I was so lost a maganganun sultan har na manta ma aiki ake min, sai kawai kukan baby muka ji, muka yi murmushi a tare, doctor ya dan daga labulen yace da sultan "a miko maka shi ka rike?" Sultan yayi saurim girgiza kai yace "babu hannun da zan rike shi dashi, I won't let go of her hand. Sai dai ku ku rike shi a wajanku" doctor ya saki baki yana kallon sultan, shi kuwa ko a jikinsa, nace "doctor kawo min shi ni in rike shi" doctor yace "ke kina ji da kanki ina ke ina rike baby? Ka rike ta da hannu daya sai ka dau babyn da dayan hannun, shi yasa Allah yayi maka hannu biyu saboda kayi two things at the same time. Kuma idan yaron nan ya girma sai na gaya masa" ya koma sai gashi ya dawo da baby a cikin towel, har yanzu kuka yake ta tsanyara wa, sai kuma naga sultan ya cika ni ya tashi ya karbe shi, fuskarsa cike da farin ciki, na fara lissafin yanzu fa dinke ni akeyi sai kuma nayi sauri na kawar da wannan tunanin daga raina, sultan ya zauna ya juyo min da fuskar babyn yace "look Moon, he is perfect. Dake yake kama" na kalli babyn, ba dani yake kama ba, hancinsa da bakin sa irin na sultan, idonsa da kuma kalar fatarsa irin nawa ne. Na saka hannu na shafa kansa nace "Allah yayi maka albarka".
Sai da aka gama dinke ni tas, suka gwada bp dina suka ga cewa is almost stable sannan sukace zan iya yin bacci yanzu, suka yi min allurar bacci. Tun kafin a gama zare allurar nayi bacci. Sanda na farka a wani dakin daban na ganni, babu ciwon kan kuma gani na ma ya fara dawowa dai dai, sai azaba da naji a gurin da aka bude cikina, na dora hannuna a gurin naji kamar inyi ihu saboda zafi, na hango sultan a zaune akan sallaya, daga alama sallah ya idar, babu kowa a dakin sai shi kadai. A hankali nace "Sultan" ya juyo da sauri ya taso yazo gurina "Moon? Wani abu yana miki ciwo? Me kike so?" Na nuna masa gurin aikina yace "bara in kira doctor" nace "Mommy tazo?" Yace "suna can sun hada kai ita da Ummee suna kuka a waje" na danyi murmushin yake, kafin ya bar gurin wani baccin ya sake dauke ni. Farka wa ta ta biyu Mommy ce a zaune a kusa dani, idanuwanta sun kumbura kamar zasu fado kasa, fuskarta tayi jawur. Na jima ina kallonta bata san ma na farka ba. A hankali nace "Mommy ki daina kuka, ba mutuwa zanyi ba, the worst part is over. Allurar bacci ce kawai take dibana" ai kuwa kamar cewa nayi Mommy yi kuka, nan da nan hawaye ya fara zuba, ta rike hannuna "Moon na shiga uku, ina can ina wurin dinner ke kina asibiti ana bude cikinki. Why didn't you tell me?" Nace "am sorry mother" na kalli agogon dakin naga 4:30, amma kuma ga rana ina kallo ta taga, this means har gari ya waye yamma tayi kenan. Na duba naga drip a hannuna, shi yasa banji yunwa ba. Akwai sauran ciwon kan kadan amma ina gani tas yanzu. Kumburin ma ya ragu. Nace "Mommy ina Daddy?" Tace "dazu ya tafi, ya zo sau biyu yana ganin ki, sun hana shigowa ne saboda kar a tashe ki. Shima wancan rigimammen an fita dashi yana ta tsala kuka, daga ganin sa acici ne. Bara inje in karbo shi sai a gwada feeding disa ko zai sha" har takai bakin kofa sai ta juyo tace "Allah yasa Khairat ta bani, dan ta hana kowa, duk wanda zai ganshi sai dai ya kalle shi a hannunta" nayi murmushi, dama nasan abinda zai faru kenan. Ai kuwa Ummee bata bawa Mommy ba, sai gata da kanta ta taho dashi, ta zauna tana yi min sannu, ina so in sake ganin fuskarsa amma ta kudundune shi a jikinta, tace "kafin ince komai, tell me, idea din waye a cikin ku kuka taho asibiti ba tare da kun gaya wa kowa ba?" Nayi shiru bance komai ba, tace "you almost give us a heart attack. Mun dauka kuna gidan biki, du kuma sun dauka kun dawo gida" nace "we are sorry Ummee" ta shafa kaina tana murmushi tace "ya jikin ki? Menene yake miki ciwo yanzu?" Nace "babu komai" tace "gurin aikin fa?" Nace "yana yi kadan. Nasan zasu zo anjima suyi min allura" sai a lokacin ta miko min babyn, sai kuma naji inajin kunyarta naki karba, Mommy ce tazo ta dan daga ni kadan tasaka min pillows a baya na sannan ta karbi babyn ta dora min a kan kirjina, na saka hannu na tare shi dan kar ya sauka kan ciwo na, ni duk kunyar Ummee nake ji ita kuma taki ta gane ballantana ta fita. Mommy ta fahimci kunya nake ji tace "Khairat ko zaki zo muje mu gano masu gwajin jinin can ko an dace an samu wanda yayi?" Ba tare data kalle taba tace "jeki kawai Fatima, gwara in zauna a gurinta kar mu barta ita kadai" Mommy tayi ajjiyar zuciya ta daga kafada ta fita. Na rasa yadda zanyi gashi shi kuma har ya fara kusur kusur yana tabe baki zaiyi kuka, Ummee tace "what are you waiting for? Feed him gashi nan zaiyi kuka. Tun da yazo duniya baici komai ba sai dan dabino da zam zam da babansa ya bashi" ya na iya da raina, dole na gyara riga na bashi, ai kuwa da sauri ya karba kamar yasan menene, ya nutsu sosai yana sha, na kura masa ido ina kallo, I can't believe wannan perfect halittar daga jikina ta fito, Allahu Akbar shine abinda kawai zan iya fada. Na bashi ring finger dina ya rike da hannunsa, sai kawai naga ya bude ido yana kallona, nayi masa murmushi sai kace yasan me nakeyi. Ummee ta zagayo ta bayana ta lakuce masa hanci tace "like father like son" Sultan ne ya shigo ya tsaya daga bakin kofa yana kallon mu, fuskarsa filled with feelings, Ummee tayi masa alamr ya shigi da hannunta, ya karaso ya ajiye ledar hannunsa yana kallona yace "ya jikin?" Na sunkuyar da kai nace "da sauki" ya matso kusa da gadon yana kallon babyn yace "an samu abinda ake so kenan, za'a bar kunnen mu ya huta" sai da ya gama sha dan kansa ya cika sannan na gyra rigata, Ummee ta karbe shi ta saka shi a kafada yayi gyatsa sannan ta bawa sultan shi tace "zauna in yi muku pictures" ba musu ya zauna a gefen gadon ya jawo ni jikinsa da hannu daya, daya hannun kuma ya rike babyn a jikin mu, Ummee tayi mana pictures da yawa. Ya dauko ledar daya shigo da ita ya fito da fruits, ya dauko ayaba ya bare ya miko min yace "doctor yace zaki iya cin fruits" na karba na fara ci sai muka ji anyi knocking kofa, Ummee ta saka min mayafi aka turo kofar, mutane suka fara shigowa kamar va zasu kare ba. Hafsat tana kan gaba, da sauri tazo ta dauki babyn daga kan cinyata tana cewa "shine ka hanamu karasa bikin mu ko?" Hatta amare da angwayen jiya duk sunzo, a raina nace 'jiya na hana first nights da yawa' Amina tazo tana yimin sannu, Zainab da Fadila, saratu da Faiza, Huda da Aishan Amir duk suka zagaye ni, mazan kuma suka tafi suna gaisawa da Sultan. Ina kallon Ibrahim ya mika wa Sultan hannu amma yaki karba, sai ya wayance da bare min ayaba. Ana ta hayaniya ana daukan hotu a ba baby, Ummee kuwa sai cewa take a daina jagwalgwala shi kar yayi ciwon jiki. Ni kam sai kallon su nake ina jin dadi a raina. Daddy yayi sallama ya shigo, ji nayi kamar in tashi inje in rungume shi, bai kula kowa ba har masu gaishe shi ya taho gurina bakinsa har kunne, ya sunkuyo yayi kissing dina a goshi yace "well done my daughter. Barakallahu fi ki" ya zauna a kujera yace ku kawo min wannan ragon mazan daya kasa jure taron biki" akayi dariya gaba daya.
Aka mika masa shi ya karba yayi masa addu'ah sannan yace "Sultan wannan ai kayi wa Moon yawo" Sultan ya karasa kusa dashi ya leka fuskar babyn yace "wannan idon ba nawa bane Daddy, kuma daga dukkan alama sai yafi ni haske" duk akayi dariya, ya Habeeb yace "Sultan in surukai suna magana aka akan dan mutum baya amsawa" Sultan yace "Daddy ai ba suruki na bane" a raina nace 'koma waye yayi magana amsa zaka bashi'.
Doctor ya bude kofa ya shigo. Yana kallona yace "Maman baby an tashi kenan, at last" nayi murmushi na gaishe shi, ya zo dudduba ni ya bani magungunan da zansha, yayi min allura a hannu, yace "zamu sake miki allurar bacci in an jima, saboda kamata yayi ace kinyi 24hours kina hutawa" sannan ya dauko takarda yana kallon mazan gurin yace "ga result din tests din da akayi muku na jini. Abbakar Sadiq Abdallah, jininka bai yi dai dai ba" su ya walid har da yiwa sultan dariya ganin yadda ya bata rai. Doctor yace "Lawan Muhammad Dikko kaima naka baiyi ba, Habeeb muhammad dikko naka kaima baiyi ba, Faruk Muhammad dikko kaima zero" akayi musu dariya suma gaba daya "Abbas sadiq abdallah kaima baiyi ba, Abdullahi Abdallah kaima zero, Adeniran Ibrahim, congratulations, kai kayi winning, naka yayi matching, mun gwada kuma munga it's free of all blood transmitted diseases, in ka shirya sai muje mu diba" gaba daya aka juya ana kallon Ibrahim, shi kuma ya kalli sultan, sultan kuma ya kalleni, ni kuma na sunkuyar da kaina.

Episode Ninety Nine : New Little Love
Sorry for the delay guys. Na ga sakon ku akan sunan baby, naji dadin yadda kukayi responding. Mutane sun zabi sunaye kamar haka : Muhammad, Abdullahi, Ibrahim, Abubakar, Lawan da sauransu. A lissafina wadanda suka ce Muhammad sunfi yawa dan haka zamu saka Muhammad din. Masu cewa Ibrahim, I salute your loyalty to Ibrahim amma bansan ta yadda zan yi convincing Sultan ya sakawa dansa sunan tsohon saurayin matarsa ba. Lol. Love you all.
Shiru dakin babu wanda yayi magana. Ummee ce ta fara katse shirun tace "me ake jira ne wai? Ka bishi mana kuje ya dauka asaka mata" babu wanda yayi magana still. Doctor ya fahimci akwai tension a gurin sai yace "bara inje office, Ibrahim in zaka bayar din ka same ni a office amma da sauri saboda ina son in saka mata sai inyi mata allura tayi bacci, kafin ta tashi an gama saka mata" ya juya har zai fita Daddy yace "doctor bara inzo ka dauki nawa, blood group din mu daya da ita, ban san ana bukatar jini ba da tuni na bayar. Ita da Hafsat group din mu daya su kuma boys din suka dauko Mommyn su" doctor yace "that's OK" ya fita. Ummee ta mike tsaye, "NO daddyn Moon, da shekarunka zaka bada jini bayan ga matashi yayi matching?" Ta kalli Ibrahim "ko kaine bakason ka bayar?" Still idonsa akan sultan yace "it would be my honor to give my blood to her. But I think it is better a dauki na daddyn kawai" Ummee ta sake cewa "why? Ji nake kai mijin sister dinta ne? Doctor yace blood din is clean, so why?" A hankali sultan yace "I don't want his blood in her" Ummee ta juyo tace "me kace?" ya maimaita da dan karfi "I don't want his blood in her" na rintse idona ina gode Allah daya kasance babu bare a gurin duk 'yan'uwa ne, ya Walid yace "Sultan, it is just blood. Babu abinda ake transferring a cikin jini in ba ciwo ba, kuma doctors sunce the blood is clean, don't make a case out of it please" sultan ya mike tsaye idonsa akan Ibrahim yace "it is not just blood, it is HIS blood, and that's what makes it different. I am her husband and I said ba za'a saka mata jininsa ba. I would rather buy it from a total stranger than take HIS. I don't even know what the FUCK he is doing here" idanuna a rufe naji karar mari, na saka hannu na na rufe fuskata, ba sai na kalla ba nasan wa aka mara kuma nasan wa yayi marin. Ummee ce ta mari sultan. Shi aka mara amma ni naji zafin. Ummee ta fara fada muryarta har rawa take yi, na tabbata da zan iya kallon idonta da zan ga hawaye a ciki, tace "Sultan a gaba na? A gaban Daddy? I know you are spoilt but didn't knew you are this spoilt. Mijin kanwar matarka, yazo har asibiti ya dubata kuma yayi offering zai bata jininsa a saka mata amma ka zage shi? Wanne irin mutum ne kai?" Daddy yayi magana "Khairat, Ibrahim is Moon's ex boyfriend, wannna shi yasa sultan yake reacting this way" Ummee tace "dan yana tsohon saurayinta hakan bai kamata ace ya saka yayi treating dinsa this way ba. Karewar aure ji nake 'da ta haifa masa ma yanzu. Shi kuma sister dinta ya aura. Menene kuma saura a ciki? Yanzu shi baiji kunyar ganin idonka ba? Baiji kunyar Amina ba? Ko da baya so ai da akwai hanyar da zai bi yace baya so ba sai yaci mana mutunci ba. Wannan ai mu ya wulakanta ba Ibrahim ba. Ina lura da Ibrahim din tunda ya shigo bai kalli inda Maimunatu take ba har ina tunanin me yasa haka ashe shi wulakanci yake gudu" fada Ummee take kamar zata ari baki. Sai da tayi shiru Ibrahim yace "am sorry. Ban zo da nufin creating trouble ba, na kawo Amina, muna tare da su Habeeb aka kira su gurin daukan jini, at first nace banda ni doctor din yana min wasa yace ina rowar jini ne, I didn't know it will match, I didn't want to create a scene shi yasa na bari aka dauka" Daddy yace masa "it is OK Ibrahim duk mun fahimta. It was just a misunderstanding. A bar maganar haka ta wuce" Ummee tace "ya kusa wucewa dai" ta kalli sultan tace "tashi ka bashi hakuri, kuma ka raka shi da kanka gurin doctor a dau jinin sannan ka kawo a saka mata, that's your punishment for been arrogant" da sauri Ibrahim yace "No ma'am, that's not necessary. Na fahimci sultan sosai kuma banji haushin sa ba. Idan nine nasan I might do something worse than what he did. Bana son a kuma samun wata matsala akaina." Ummee tace "ba akan ka bane Ibrahim, akan sa ne, ina son yasan cewa idan yayi ba dai dai ba dole ayi punishing dinsa. So nake inga in an saka mata jinin ya zaiyi" ta juya tana kallon sultan tace "tashi ka bashi hakuri nace" Sultan ya mike kamar mai ciwon cinya, ya tsara a gaban Ibrahim kamar ba zaiyi magana ba, amma nasan sultan baya taba yiwa Ummee musu duk da kuma nasan zuciyarsa yanzu kamar zata fashe yake jinta, ya dan jima a tsaye sannan yace "am sorry. And thanks for offering your blood" ya mika wa Ibrahim hannu, Ibrahim yayi murmushi yayi shaking hannun sultan yace "it is OK. You are welcome" daga nan suka juya suka fita tare. Suna fita Mommy tana shigowa, ta kalle mu daya bayan daya tace "what did I missed? Me ya faru?" Daddy yace "tsegumi. Kin riga

Please Login or Register in order to submit comment