Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kuma kwalin fresh milk, ya tashe ni zaune yace sai naci, ina ta shagwabar ni bacci nake ji amma haka ya matsamin sai da muka ci tare, muna gamawa ya dauko min magungunan wajan Hafsat ya bani nasha sannan na koma na kwanta, ban jima da kwanciya ba naji shi ya kashe fitilar dakin ya hawo gadon shima, ya jawo ni jikinsa kamar zai tsaga kirjinsa ya sakani ciki, nayi 'yar kara, yayi dariya yace "ya jikin?" Nace "da sauki" yace "Maimunatu" nayi mamaki saboda yau ne rana ta farko daya kira ni da wannan sunan, nace "Na'am" yace "thank you, I really mean thank you, for yesterday, for everything, bansan me zance miki, bansan sunan da zan kira ki dashi ba, I will continue calling you my love, saboda you are the love of my life, amma ki sani ba wannan ne kadai matsayinki ba, you are my everything, I was nothing kafin in hadu dake kuma I will be nothing without you" bance komai ba amma ina jin dadin maganganunsa har cikin raina, ina kara jin sansa yana shiga har cikin bargo na, he is mine, and I am his, forever and ever.

Ni na sake riga shi tashi wannan karon ma, na farka naga still dakin duhu, wato shi wannan dakin na sultan koda yaushe a dare yake kenan, sai mutum yayi ta bacci bai san me duniya take ciki ba. Na tashi zaune, ga mamaki na sai naji babu ciwon sam, sai dan ciwon jiki kadan, na kunna bedside lamp, na duba agogon wayata, 1:15, oh my God, nasan mutane sunyi ta zuwa suna ganin gidan a rufe, na juya na kalli sultan da yake bacci a gefe na, sai naji na kasa tashin sa, he looks so handsome, hasken lamp din yana reflecting a golden skin dinsa, na koma na kwanta a side dina ina kallonsa, I have never see him this peaceful before, na tuna maganar hausawa da ake cewa wai angwaye suna kwallin goshi, to ko dai da gaske ne? Na kai dubana kan kirjinsa, Ya dan yaye bargon ya bar kirjinsa a waje, gashin da yake kwance a kirjinsa yafi na fuskarsa kyau da sheki kamar yadda fatar gurin tafi da fuskarsa haske, a hankali na gada hannuna, na sake kallon fuskarsa naga baccin yake yi, I couldn't stop myself, a hankali na sauke hannuna akan gashin na fara shafawa ina jin laushinsa a hannuna, I was so consumed in doing what I was doing kawai naji maganarsa "hey woman, you already had me, if you want more all you have to do is ask" nayi sauri na dauke hannuna na rufe fuskata dashi, ya mirgino ya hade fuskarmu guri daya yace murya can kasa "do you want more?" Na girgiza kaina da sauri, yace "but I do want more" nace "ni fa tashinka zanyi, lokacin sallar azahar ya kusa, kuma kaga ko bude kofa bamuyi ba kar mutane su yi ta zuwa gida a rufe" yace "so what? Duk wanda bai zo jiya ba yayi wa kansa, an gama ganin gidan amarya. Let's not open the door forever, let's not get out of this bed forever" nayi dariya na dan dake shi a kafada nayi kokarin tashi ya sake dawo dani baya nace "Sultan, ka bar ni inje dakina in saka kaya, inje in samar mana abinda za muci kuma, we can't stay here forever" ya saka fuskarsa a wuyana yace "sai kace girkin ta iya da gaske. Za'a kawo abinci, za'ake kawo wa daga cikin gida har nan da seven days, kafin nan sai mu nemi cook. Yau bana son ko tashi inga kinyi, I want to treat you like the queen you are, komai kike so ni zan yi miki, duk abinda kike so shi za'ayi".

Da kyar na samu ya dauko min kayana a dakina na saka, daga nan ya tafi masallachi sallah ni kuma nayi sallah ta anan, miracle maganin Hafsat yayi min amfani sosai dan bama na tuna wa da wani ciwo sai in na yi motsi da sauri. Man sa na shafa na saka tunarensa, banyi kwalliya ba, na zauna akan kujera ina duba messages din wayata, yawanci sakonnin taya murna ne daga mutanen da basu samu damar zuwa bikin ba, anan naga sakon mahdi, yace min ya cigaba da karatunsa bai dawo Nigeria ba, na rufe WhatsApp kenan naga sakon Amira ya shigo, na koma na bude "Moon dan Allah ina so muyi magana, can I come to your house please?" Ban yi mata reply ba Sultan ya shigo, tray din abinci ne a hannunsa amma idonsa yana kaina, na karaso na karba na ajiye, bai ce komai ba ya sake fita ya dawo da still da wani abincin, na kuma karba nace "Sultan wannan abincin ya zamuyi dashi?" Yace "I don't know which one you will like, shi yasa na debo kowanne. Sun kawo abincin yana dining. Da akwai Baba Gaji Yaya ta turo ta gurinki, I told her ba zaki samu ganinta yanzu ba amma ta zauna duk wanda yazo ta raka shi yaga gida amma ta gaya musu amarya is not available" nace "ayyah, da ka barni naje baka san menene sakon Yayan ba" yace "ba zai wuce zancen masu aiki ba" zan kuma yin magana ya jawo nikan cinyarsa yace "me zaki ci?" Mun ci abincin sosai daga ni har shi duk ashe yunwa muke ji, sam ya hanai fita da kayan shi ya dauka ya fita dasu, kafin ya dawo na gyara gurin na kara freshner a dakin, yazo ya jani muka koma gado yace "ya ciwon? In duba in gani? Nayi sauri na hade kafafuwana nace "bai warke ba ai" yace "OK, kin san me za'ayi masa ya warke da wuri? Wani za'a kuma yi, nan da nan zakiga ya warke" na fara matsawa baya ina zaro ido "please Sultan, wallahi mutuwa zanyi, dan Allah karka tabani" dariya yayi sosai yace "harda mutuwa? Am just kidding, amma babu wani mutuwa da zaki yi, an gama mai zafin ai" na sake matsawa baya, ya jawo ni yace "trust me bazan miki wannan ba, I just want to feel your warmth and smell your scent" na dan saki jikina kadan amma kuma ba abinda ya fada kadai yake yi ba, sai da naga yana neman wuce gona da iri sannan na saka masa kuka, ya sakeni ya gyara min rigata sannan ya gyara min kwanciya, har na dauka yayi bacci sai naji yace "tell me about him" duk da bai fada ba nasan wa yake nufi, kuma nasan dama dole zamuyi maganar amma sai naji bakina yayi min nauyi na kasa magana, jin nayi shiru ya sake magana "I just want to know, shi kadai ne ko kuma akwai wani daban da ban sani ba" na girgiza kaina nace "shi kadai ne, sunan sa Ibrahim, he was a copper a sec sch din mu when I was in SS2, I was 14 years then" daga nan na bashi labarin duk rayuwar mu da Ibrahim him, da yadda muka rabu, da irin zaman jiransa dana zauna yi kafin haduwar mu shi (sultan), na bashi labarin har ranar da muka kuma haduwa da Ibrahim da labarin daya bani na rayuwar da yayi bayan rabuwar mu da irin abubuwan da Amira ta kulla mana, ban boye masa komai ba har wayar da mukayi dashi a phone din Amina da duk bayanin dana yi masa ya kuma nuna ya gamsu, na karasa da cewa "bansan me yasa ya aikata abinda ya aikata ranar nan ba. Am sorry na boye maka duk wanan maganar, at first I never thought zamu sake haduwa dan haka nake ganin there is no point in telling you, daga baya kuma bayan mun hadu dashi na kasa gaya maka ne saboda bana son in bata maka rai". Har na gama maganar baice komai ba,har na fara tunanin ko yayi bacci, na kalle shi sai naga yana kallon ceiling, can yace "promise me you will never see or talk to him again, my heart cannot take it" na dago kaina ina kallon cikin idonsa nace "I promise" yayi murmushi yace "thank you" sannan ya jawo fuskata ya hade bakin mu.


Episode Seventy Three : His Father's Son

Washe gari bamuyi missing sallar assuba ba kaman jiya, Sultan ne ya fara tashi, sai da yayi alwala sannan ya tashe ni shi kuma ya fita masjid, ya jima bai dawo ba har nayi sallah na dan taba karatun al'qurani sannan nayi morning azkar dina, ji nayi duk na gaji da kwanciya, I want to do some work, na tashi na gyara dakin na wanke toilet, na dawo palo ina cikin gyarawa ya shigo, ya tsaya yana kallona "wato matar nan kin warke ko? Shine zaki kama aikin da assubar nan ko?" Nace "na gaji da kwanciya ne kawai, I want to do something" ya fara tahowa yana min murmushin mugunta yace "You want to do something? I have got something for you" na ajiye duster din hannuna na fara ja da baya ina jin tsoro har cikin raina dan na warke amma ban manta azabar da nasha ba. Nace "Sultan Allah ban gama warkewa ba, dan Allah kayi hakuri wallahi na daina aikin zan koma in kwanta" ya karaso in da nake yace "really baki warke ba? Can I see?" Nayi saurin girgiza kaina nace "you are not a doctor how will you know if a wound is healed or not?" Yace "am not a doctor but ni mijin doctor ne, dan haka believe me I will know" idonsa kawai na kalla nasan kona roke shi it will be to no avail, jikina har karkarwa yake yi saboda tsoro, me yasa nayi aure ne wai? A kunne na ya rada min "believe me, it will not hurt". And it didn't, at least not as I expected. Yana cikin bacci na zare jikina na tashi, a hankali na lallaba na saka kayana na fice, da sauri na karasa dakina ina shiga nayi locking kofar, finally nazo dakina after two days, da sauri sauri na gyara dakin duk da ba wani datti yayi ba, na shiga toilet na shiga shower ina wanka, at last zanyi wanka without sultan standing and watching. Na fito na zauna na shirya a tsanake cikin atamfa ruwan hoda, nayi 'yar kwalliya kadan na fesa turare na fito. Ina fita palo na tarar da wata tsohuwa a zaune a kan carpet da wadansu 'yammata su biyar daga can bakin kofa, ina fitowa duk suka mike tsaye kansu a kasa, 'yammatan kamar harda tsoro a fuskarsu, sai da na zauna sannan suka durkusa suka fara gaisheni daya bayan daya, na saki fuskata sosai na amsa musu. Babbar matar ce ta matso tace "ranki ya dade, Allah ya taya miki, Allah ya dora ki akan makiyanki duniya da lahira, Allah yaji kan magabata, Allah kuma yasa albarka a zuriya" nace "Ameen" ta cigaba da magana "ranki ya dade ai jiya ma munzo, muna nan har magriba bamu samu ganin ki ba. Dama mai babban daki (yaya) ce ta turo mu, tace tana gaishe ki sosai, kuma tace duk mu shidan nan mu dawo nan gurinki mu zauna muke yi miki hidima. Ni sunana Gaji, tun asalin kakanni na bayi ne a wannan gidan, anan aka haifeni anan na girma nayi aure na hayayyafa, 'ya'yana ma suka yi aure suka haihu duk acikin gidan nan, guda biyu daga cikin 'yammatan nan jikokina ne. Kamar yadda aka kawo 'yammatan nan gurinki yanzu haka aka kaini gurin mai babban daki sanda tana amarya, wannan shi yasa nake daga cikin amintattun bayinta, kuma wannan shi yasa ta zabe ni akan in zo in zauna a gurinki, saboda tasan zan rike mata amana. Suma wadannan duka yaran da kika gani zababbu ne dan ni ta saka in zabo mata masu tarbiyya da rikon amana kuma na zabo su. Insha Allah zamu rike ki da amana Allah kema ya baki ikon rike mu da amana." Kawai naji matar ta kwanta min araina, na tambayi yaran duk sunayensu suka fada min, naga duk sunki sakin jikinsu sai na fara yi musu wasa, ba'a jima ba suka fara dariya. Da kaina na tashi na kaisu har bq din mata na nuna musu komai sannan muka dawo tare. Nace "Ku dauke ni a matsayin yayar ku kunji, dama ni bani da kanne mata kunga shikenan na samu, duk abinda kuke so kuyi min magana in dai ina dashi zan baku, abinda bana so shine kazanta, ku kula da tsaftar gidan nan ku kuma kula da tsaftar jikin ku, ku kame kanku banda shiririta. Allah ya bamu ikon zama lafiya". Sunji dadin yadda na karbe su, kuma daga dukkan alamu sunji dadin bq din dai sai murna suke sunzo gurin 'yan gayu. Nan take baba Gaji ta raba mudu kowa aikinsa, jikokinta guda biyu su ta bawa part dina, sauran kuma sauran parts din gidan. Banda part din Sultan. A take suka tashi suka fara aikin su. Ina zaune sai ga abinci daga cikin gida, suka je suka ajiye a dining room sannan suka zo suka gaishe ni, wai hajiya tace ayi min sannu da jiki, na amsa musu, naga suna ta kallon 'yammatana da Baba Gaji da naga ta hade rai. Na tashi na koma part din Sultan na tarar ya tashi yana wanka, na zauna na jira shi ya fito, yana kallona yace "shine kika gudu ko?" Bance komai ba, ya tsaya yana goge jikinsa, ya juyo ya kalleni muka hada ido nayi sauri ya sunkuyar da kaina, yayi dariya yace "ana so ana kaiwa kasuwa. You are welcome to watch" nace "an kawo abinci, nan za'a kawo ko kuma zaka fito dining?" Yana kokarin shiga closet yace "bara kawai in fito, dama zan dan fita" har ya kai bakin kofa kuma ya tsaya ya juyo "bazaki zo ki tayani shiryawa ba?" Na rufe fuskata da hannuna, yayi dariya "wannan kunyar naga har yanzu da akwai saura, zanyi maganin ta ne" ina nan zaune inda ya bar ni har ya sake fitowa, kananan kaya ne a jikinsa yayi stocking rigar ya saka belt, da comb a hannunsa yana taje kansa, na tashi na karasa inda yake na karbi comb din na cigaba da taje masa, nace "ina zaka je?" Yace "orphanage. Yanzu zan dawo. Tunda aka fara bikin nan banje na gansu ba" na gama gyara masa gashin nace "let's go eat then".
Sai bayan ya tafi sannan na dawo palo gurin baba gaji, ina zama tazo ta fara yi min tausa a kafa ta, naji dadin tausar saboda dama kafar ba dadin ta nake ji ba, cikin girmamawa ta fara yi min magana "ranki ya dade ni kam wadannan masu kawo abincin nan ina ma za'a ce musu su daina kawowa? Mu sai mu ringa yi anan" ban amsa mata ba na lumshe ido na inajin dadin tausar. Ta cigaba da magana "Ranki ya dade sai kinyi a hankali sosai da Hajiya. Mutanen da suke waje kullum suna maganar irin yadda take nuna wa karamin sarki soyayya amma mu da muke cikin gidan nan mun san ba haka abin yake ba" na bude ido na nace "waye karamin sarki?" Tace "maigidanki ranki ya dade, haka mai babban daki take ce masa muma kuma duk haka muke ce masa" na koma na kwanta na sake rufe idona, ta cigaba "bata sonsa ko kadan, kema kuma dole nasan kiyayyarsa zata shafe ki. Kar ki yarda da duk wata magana da zata gaya miki musamman akansa, mu mun san komai" maganar ta ta karshe ce ta saka na bude ido na, 'mu munsan komai' na tashi zaune ina kallonta nace "Baba Gaji, kin san mahaifiyar Sultan?" A hankali naga yanayin fuskarta yana komawa alamar tsoro, ta sunkuyar da kanta kasa, na sake magana "baba gaji kince anan gidan aka haife ki, kince kuma kina tare da Yaya tun tana amarya, haka yana nuffin kinsan mai martaba sarki tun haihuwarsa har girman sa har auren sa, hakan yana nufin kinsan haihuwar Sultan, abinda na tambayeki shine; kin san mahaifiyar sultan?" Gani nayi jikinta ya fara rawa, kanta har yanzu yana kasa ta kasa kallona, tace "ki yi min afuwa ranki ya dade, an hana mu yin magana akan ta, an hana mu ko da ambatar sunan tane" cikin mamaki nace "waye ya hanaku maganar ta? Kuma saboda me?" Ta dago ta kalleni tace "mai martaba sarki, marigayi, mahaifin wannan sarkin" wani mamakin na sake yi nace "kina nufin ba wannan sarkin ba, wancan" ta gyada kai, nace "to saboda me?" Ta girgiza kanta tace "Allah masani" nayi shiru ina tunani, Sultan ya taba ce min "no body talk about her, it is as if she didn't exist" na gyara zamana nace "amma baba gaji shi wanda kike magana akansa shekarar sa ashirin da rasuwa, in kin gaya min taya za'a yi yasan kin gaya min?" Ta girgiza kai, tace "ranki ya dade mu bayi ne, muna biyayya ga iyayen gidan mu koda kuwa bayan mutuwar su ne, bama cin amanarsu, bama ha'intarsu" na mike tsaye na fara zagaye a palon sannan na dawo na zauna nace "sanda wancan sarkin yana nan kina a matsayin baiwar sa, bayan ya mutu kika zama baiwar Yaya, yanzu kuma yaya ta bani ke, in dai har zaki yi masa biyayya har bayan ransa to hakan yana nufin zaki yi min biyayya nima. Ina umartarki daki bani labarin duk da kika sani dangane da mahaifin sultan da kuma mahaifiyarsa" ina kallon yadda duk ta rude, na dan dafa kafadarta nace "nayi miki alkawarin duk maganar da mukayi zata tsaya a tsakanin mu".
Sai da ta nutsu ta daidaita numfashinta sannan ta fara magana " ina nan aka haifi mai martaba sarki na yanzu, ina nan kuma aka haifi dukkannin kannensa. Duk a cikin su shine yafi dauko halin mahaifinsa; zafin zuciya, taurin rai da kuma tausayi. Yadda kika ga karamin sarki haka yake, kuma shima kakansa haka yake. An gaya mana cewa wannan shine abinda yasa suke zama sarakuna, dan shi mulki sai mutum yana da karfin jiki dana zuciya, sai mutum yana da zafi kuma yana da sanyi. Sanda ya girma ya zama saurayi mu dai munsan yana kasar waje karatu, duk sanda yayi hutu yazo gidan nan haka zai cika gidan nan da abokanan sa har sai ya koma tukunna, wadansu abokan ma daga makarantar suke biyo shi su zo nan suyi hutun tare su koma. Rannan ya dawo gida tare da abokanan sa da yawa, aka shirya musu party ana ta murna, aka gaya mana cewa ai murnar kammala karatunsa akeyi, muma mukayi ta murna muna taya shi farinciki. Bai dade da dawowa ba sai suka samu sabani da mahaifinsa, rana daya muka neme shi muka rasa a gidan nan, ba karamin tayar da hankali mahaifinsa yayi ba saboda kowa ya san duk cikin 'ya'yansa babu wanda yake so kamarsa. Yaya ta tada hankalinta, kullum ana cikin tara malamai da addu'ar Allah ya bayyana shi. Rannan muna zaune da daddare tare da Yaya kawai sai gashi ya shigo palon, hannunsa rike da hannun wata yarinya, balarabiya. Muka tashi da murna amma sai muka ga yaya sam bata murna sai ma tashin hankali da muka gani a tare da ita, aka aika aka gayawa sarki sai gashi ya taho da kansa, mu dai duk muka fita muka basu guri, basu fi awa daya ba sai gashi ya fito rike da hannunta ya bude motarsa ya shiga ya fice daga gidan. Sai daga baya muka samu labarin ainahin abin da ya faru, yarinya ce yake so balarabiya, ya nemi babansa ya nema masa auren ta amma baban yaki, wannan shine dalilin da yasa ya tsallake yayi tafiyarsa yaje ya nemi auren nata da kansa, aka bashi ita aka daura musu aure sannan ya dauko ta ya taho da ita, a tunaninsa tunda ya riga ya aure ta ai dole uban ya karba. Amma da suka zo maimakon uban ya karba sai ya kara tunzura yana ganin kamar ya nuna masa bai isa dashi ba tunda yayi aure ba da sanin sa ba. Hakan ne yasa shi kuma ya dauki matarsa suka yi tafiyarsu. Ba'a kuma jin labarin sa ba sai bayan shekara daya. Shima wannan karon muna zaune sai gashi ya shigo gidan, hannunsa daya rike da wannan balarabiyar, daya hannun kuma yana rungume da dan jariri. Wato tunda ya kawo musu suruka sunki karba shine yanzu ya kawo musu jika. Ai kuwa wannan karon yaci nasara, dan kallo daya kakan yayi wa jikan ya tattara son duniya ya dora masa. Tun daga nan Khairat ta tare a gidan nan. Yarinya ce nutsatstsiya sosai, tana da hankali da girmama mutane. Farkon zuwanta sam bata iya hausa ba, amma a hankali ta fara koya. Duk gidan nan, 'ya'yan gida da mu bayi, dama wadanda suke shigowa su fita, babu wanda baya son khairat, babu kuma wanda bai san irin son da mijinta yake mata ba dan baya boyewa ko a gaban waye kuwa. Shi kuwa wannan dan jaririn wanda daga baya muka fahimci babansa ya saka masa sunan sa saboda tsananin son da yake masa, sai ya zama an kasa ban bance waye yafi sonsa tsakanin iyayensa da kuma kakansa. Tun yana jariri muka fahimci cewa ba sunan babansa kadai yaci ba harda halayensa, duk duk kiriniyar da babansa yayi yana jariri shima ita yake yi, kamar copy dinsa ne aka ajiye, sai dai yafi kama da mahaifiyarsa. Karamin Sarki yana da shekara biyu a duniya rannan kawai muka tashi babu khairat babu alamunta, babu abinda ta dauka a kayanta, ko danta bata dauka ba, kuma babu wanda yace yaga sanda ta fita. Abinda kuma ya fi bamu mamaki a tafiyar tata shine, babu wanda ya neme ta" nayi sauri na katse ta nace "ban gane me kike nufi babu wanda ya neme taba, mijinta fa wanda kika ce yana yi mata soyayya kamar rai?" Tace "shine abin mamakin Allah ya taimakeki, duk zafin ransa, duk, duk taurin zuciyarsa. Mun dauka zai bita amma ko kofar gida bai je ba. Komawa yayi tamkar wanda aka chanza shi da wani, tamkar ba shi ba gaba daya yayi sanyi duk karfin sa babu. Kamar an zare masa ruhinsa an bar gangar jikin. A rana daya aka saka aka kwashe duk kayanta aka rufe dakinta. A ranar aka taramu aka umarcemu da ko sunan ta kada wanda ya sake ambata a gidan. Bamu tambayi dalili ba kawai dai munyi biyayya. Kwana biyu da tafiyar ta karamin sarki ya galabaita da kukan neman ummin sa da daddyn sa, har zazzabi yayi, ranar da safe ina gurin yaya ina ta faman rarrashin karamin sarki sai ga babansa ya shigo, yana shigowa yaron ya fara zamewa daga hannuna yana kokarin tafiya gurinsa amma abin mamaki ko kallon inda yake bai yi ba, tamkar bai san shi ba, ya shiga ya gaishe da mahaifiyarsa ya juya ya fice, yaron yana ta kiran daddy daddy yana kuka. Tun daga ranar abinda ya cigaba da faruwa kenan, kamar yadda aka goge duk wani abu daya shafi mahaifiyar karamin sarki a gidan nan haka ya zamo tamkar an goge duk wani digo na soyayya tsakanin karamin sarki da mahaifinsa" tasa mayafinta tana goge hawayen idonta, nace "amma hajiya fa, an auro ta lokacin?" Ta girgiza kai tace "ai Hajiya sam basu zauna da mahaifiyar karamin sarki ba, sai bayan da suka rabu da shekara biyu ma sannan aka yi aurenta" ji nayi kaina ya daure, saboda all this while abinda nake tunani shine Hajiya ce ta raba maman sultan da babansa, ita ce kuma ta raba tsakanin su ta saka kiyayya a tsakanin su, things are not always what they seem, na sake tambaya "to daga baya kenan Takawa ya hadu davita har suka fara soyayya suka yi aure?" Tace "Ranki ya dade ai babu soyayya, auren hadi ne, 'yar 'uwarsa ce ai, kakansu daya. Kawai kiransa akayi akace masa an hada shi aure da wance yace to, daga nan akayi auren, anayin auren suka tafi kasar waje tare wai itama zata yi karatu, shekarar su daya suka dawo da yarima Abbas yana

Please Login or Register in order to submit comment