Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

jimawa ba.

Muna komawa pc tayi taron Muslim students ta sanar mana cewa akwai musabaka da federal government take shiryawa, ance a bada daliba guda daya da zatayi representing din school din mu, dan haka mu zaba a tsakanin mu wa muke ganin zata iya. Nan take muka zabi Amira, kuma tace ta yarda zatayi, muna ta murna sai pc tace zata hada ta da malami guda daya wanda za su ke yin tilawa tare kafin likacin musabakar. Muka tashi daga taron muna ta yiwa amira murna.

Da daddare after islamiyya sai Ibrahim yace da Amira ta tsaya yana son ganinta, inajin haka nasan shi akace yayi coaching dinta. Amira ta ja hannuna muka tsaya tare. Sai da aka gama tafiya sannan yazo yace mata "congratulations Amira, naji abin alkhairi, Allah ya bada sa'a" muka ce amin. Nan suka fara tsara yadda zasuke karatun ni kuma ina jinsu ina dan bada tawa shawarar. A karshe suka yanke shawarar zasu keyi daga magrib zuwa isha. Haka kuwa akayi, kullum in munyi sallar magrib sai Amira ta zauna a masallaci tare da Ibrahim har sai munzo sallah isha tukunna mu tafi ialamiyya tare.

A bangare na kuma lokaci daya girma razo min, ni kaina bansan yaushe ba sai gani nayi kayana duk sunyi min kadan. Kirjina kullum kara chika yake haka hips dina, har saida nakai ga komawa aron kayan Hafsat ina sakawa ita kuma tace sam ba zata yiwu ba sai dai in aika gida akawo min wasu kayan. Ina aika wa kuwa sai ga kaya akwati guda duk size din Hafsat kuma dana saka sai naga duk sunyi min dai dai. Wata ranar sport muka saka sport wears kamar yadda muka saba muka fita. Ni dama basketball nake yi tun jss1 haka Ibrahim ma, duk ranar sport tare muke yi dashi kuma ya iya sosai saboda yana da tsaho. Ina zuwa na tarar dashi already a field da wadansu staff su biyu tare da students wadanda mostly 'yan kallo ne. Ban yi wata wata ba na shiga muka fara bugawa, amma sai na lura Ibrahim hankalinsa sam baya kam ball din, duk ya zama distracted, ya kasa scoring ko kwallo daya, gashi anaso ayi mana game, nan na tafi gurinsa da niyyar in tambayeshi mai yake damunsa sai na lura gaba daya ransa a bace yake. Ina zuwa kusa dashi sai kawai naga ya chire jacket din daya daura a kugunsa ya kama kokawar saka min, na kwace daga hannunsa cikin fada nace "what is wrong with you?" ya dora min jacket din akan kirjina yace "just go and play table tennis or snooker, ai ba sai lallai kinyi basketball din ba" raina naji ya fara baci, nace "saboda me? Kullum ba basketball din nake playing ba? Dan me yau zaka ce wai inje inyi snooker bayan kai ne ma kake bata mana game din" wani kallo da yayi wa kirjina yasa naji kafafuwana duk sun sage, kallon kawai yayi min na gane ma'anar me yake nufi, wata kunya ce naji kamar zan narke a gurin. Bai ce min komai ba ya juya ya bar field din. Daga baya na naji wasu sababbin coppers suna cewa "wannan Ibrahim din dan bakin ciki ne wallahi" wani hawayen takaici naji yana taho min, nayi sauri na mayar dashi. Da sauri sauri na zura jacket din Ibrahim na bar gurin. Ina jin wata tana kwalla min kira na rabu da ita. Can kasan wata bishiya na hango hafsat tana zaune akan kujera da novel a hannunta tana karantawa, ta dora kafa daya kan daya. Itama sport wears din ne a jikin ta amma tayi rolling farin vail har saman kirjinta. Na tsaya a gabanta nace "why didn't you tell me?" Ta kalleni da rashin fahimta tace "tell you what?" Na zauna kusa da ita nace "ba za kiyi min fada kice kayan jikina are showing ba, kika barni na fito mutane suna kallona?" Dariya tayi ni kuma na kara kuluwa, sannan tace "kusan shekaru biyu da suka wuce na taba fada miki magana akan Ibrahim sai kika ce min you are old enough to make decisions for yourself, to dan me yanzu kuma zan yi miki magana, tunda you are not blind. Yanzu ai kin dauki darasi ko?" Na kara bata rai bance mata komai ba. Kamar daga sama naji yana cewa "barka da hutawa big sister" duk muka kalleshi Hafsat tana dariya tace "ni fa bana son big sister dinnan, sai inji duk tsufa ya kamani" suka yi dariyar su su kadai. Ya zauna kusa dani naja kujera ta na matsa yace min "am sorry, bai kamata inyi miki magana a cikin mutane ba, amma bazan iya hakura mutane suna kallonki ba" Hafsat tayi gyaran murya tace "Hello, ina nan fa" ya kalleta yace "in ba zaki tashi ba to ki toshe kunnuwanki" ni dai bance musu komai ba dan duk haushi suke bani. Tun daga ranar na koma saka dogon hijab irin na Hafsat, 'yan sport din mu kuwa tun suna nemana har suka hakura.

Muna gab da fara SSCE Amira tace min sun daina karatu da Ibrahim. Na tambayeta dalili tace babu komai kawai tana ganin ta iya duk abinda ya kamata ta iya. Washe gari muna class aka kira ta a staff room, shiru shiru bata dawl ba sai na tashi na bi bayanta. A hanya muka hadu da ita. Abinda na gani a fuskarta ya bani tsoro, na tambayeta "Amira lafiya, ko a gida ne wani abu ya faru?" Wani kallo ta yi min wanda naji tamkar ta doka min guduma aka, cikin sarkewar murya tace "me kika biyo ni kiyi min kuma, nace na fasa karatun dashi ba shikenan ba? To yanzu na fasa musabakar ma gaba daya, kije kiyi na bar miki, besides you are the golden one ai, you are so perfect that you must have everything that you want. You can have him, you can have the musabaka and everything else" ta bangaje ni da kafadar ta ta wuce. Ni sam ban gabe ina maganganun Amira suka dosa ba dan ni a iya sanina banyi mata komai ba. Tana tafiya sai naga Ibrahim ya fito daga office din PC muka hada ido ya girgiza min kai alamar kar inyi magana ya tafi.

Tunda muka shiga class Amira ta kifa kanta a desk take kuka, kowa ya tambayeta sai tace babu komai. Hafsat tace a rabu da ita, dama tun mutuwar babanta she has not being herself maybe mutuwar ta tuna. Ana tashi Ibrahim yazo ya kira ni ya tambayeni ko zan iya yin musabakar? Da mamaki nace masa "Amira fa" yace "tace ta fasa" na tambayeshi dalili yace bai sani ba. Muna zuwa hostel nayi wa Hafsat bayanin duk abinda ya faru. Tayi shiru sannan tace "Are u sure babu wani abun a tsakanin su?" Naji maganar ta kamar kibiya a zuciyata amma sai na maze nace "wani abu kamar me fa?" Ta kalleni da nutsuwa tace "Amira ba haka take ba, in har ta gaya miki wadannan maganganu to da akwai dalili, kuma they have been spending a lot of time together lately, maybe something happened".

Maganar Hafsat ta shige ni kuma nayi niyyar zan samu Ibrahim inji daga bakinsa. Dama yanzu mun daina lectures sai dai revisions ko kuma muyi ta tutorial. Dan haka muna zuwa class na tafi staff room na cewa Ibrahim ina son ganin sa. Mu ka fito tare muna tafiya, direct na tambayeshi nace "Me ya hada ka da Amira?" Ya tsaya yana kallona yace " bangane ba, wani abun tace nace mata" nan na fada masa duk maganganun da Amira ta gaya min, yayi shiru bai ce komai ba. Direct na sake tambayar sa "is Amira in love with you?" Yace da sauri "what? Me yasa zaki fadi haka" na sake cewa "are you in love with Amira?" Da karfi yace "hell no!!" Nayi shiru saboda naga yana son yayi min ihu a cikin mutane. Sai da muka jima a tsaye muna kallon kallo sannan ya fara magana "OK, na jima da sanin cewa amira tana so na, tana dannewa saboda she is your friend, ni ma kuma ban taba nuna mata na sani ba, but I know the signs. Yanzu da muka fara karatu da ita sai ya fara zama worst har bata concentrating akan karatun sai dai tayi ta tambata things about me and other stuffs, to sai nayi suggesting cewa mu gayyato ki kizo muke yin karatun tare, shine taji haushi tace ta fasa karatun, na gaya wa pc kuma shine tace ta fasa musabakar gabadaya, sai dai ke kiyi tunda nace dake nake so muyi karatu" tun daya fara maganar nake sauraron shi ina jin wani daci yana taso min a baki na, ji nayi kamar in rufe shi da duka, amma dana kalleshi sai naga iyakacin gaskiyarsa yake fada min. Na juya da sauri zan bar gurin ya kamo hannuna, wani mugun kallo na jefa masa nan da nan ya sake ni nayi gaba. Ina jinsa yace "maimunatu 🙏please "


Episode Twenty Two: Efisowa

Ina zuwa class Hafsat ta taso take tambayata "well, what did he said?" Na kalleta da jajayen ido nace "it's none of your business" ta jima tsaye a kaina sannan ta daga kafada tace "OK, in tayi tsami maji" da ace ana sayar da maganin sa ido da saina sayo na bawa Hafsat. Two days suka wuce, zuciya ta fara sanyi amma har yanzu ban huce ba. Ibrahim duk ya gama rikicewa saboda silent treatment da nake bashi. Amira kuma ta ja baya da komai, ta zama wata irin silent ba ta yiwa kowa magana, musamman ma ni. On the third day muna aji a zaune sai ga Ibrahim nan yazo, ya taho direct gurina ya tsaya a gabana yace da karfi yadda kowa a class din zaiji "nace miki I don't love her, what more do you want from me?" Gabadaya ajin kowa yayi shiru yana kallon mu ballantana su Hafsat sa ido. Nayi kasa da murya nace "what are you doing?" Ya kara daga murya yace "am telling everyone bana son ta ni ke nake so, ke kadai nake so" Wata jamila tace "sir wacece? A ajin nan take? Cewa tayi tana sonka?" Na dan saci kallon amira sai naga ta juya ma class din baya tana kallon waje, sai kawai naji zuciya ta ta karye, na dauki wani katon textbook na fara dukan Ibrahim da shi ina korar sa waje, amma yaki tafiya yace lallai saina fada masa cewa maganar ta wuce sannan zai fita, su kuwa 'yan aji sai kara tambayarsa suke ya basu labari. Da naga dai Ibrahim da gaske yake so yake yayi wa Amira tonon silili sai nace masa na yarda, maganar ta wuce, yace "kinyi alkawarin ba zaki kara tayar da maganar ba?" Nace "I promise" sannan ya juya ya fita. Yana fita Hafsat tace "well3, dama nace in tayi tsami zanji, 'yan class din nan duk mai son yaji wacece yazo in gaya masa" nan da nan duk suka tafi gurin Hafsat, na kalli Amira naga alamar tsoro a fuskarta, nayi sauri naje gurin Hafsat nace "Hafsat dan Allah ki bar maganar nan" tace "sai kinyi min alkawarin daga yau anti Hafsat zaki ke ce min" nace "done, anti Hafsat from today".

Sai da muka je hostel sannan Hafsat tace "ni daga ke har Amira kun bani mamaki wallahi, ni banga abin so a jikin wannan dogon mutumin ba" nayi dariya kawai ba rabu da ita, amma maganar ta ta tsaya min a rai. A lokuta da dama mutum ba shi yake zabar wanda zuciyarsa zata so ba, kawai haka kawai zakaji kana son mutum, wani lokacin kuma daga kaga mutum sai kaji baka son sa, ba tare da yayi maka komai ba. Kamar yadda lokaci daya na ji zuciya ta tana son Ibrahim duk da irin banbancin da yake tsakanin mu, babu wani dalili da zance saboda abu kaza nake sonsa, kawai dai nasan ina son sa. Da nayi considering Amira sai naga itama haka ne a wurinta, kawai taji tana sonsa ne amma saboda kusancina da ita ya saka ta boye a ranta har sai yanzu da suke spending time together sannan ta fara nuna masa, it must be hard on her, especially yanzu da yayi declaring a gaban kowa cewa baya sonta, sannan gashi gandantakar mu ta shekaru kusan shida tana so ta baci saboda kawai ta kasa controlling zuciyar ta. She deserves a break from me. Ina yin wanka na shirya sai na tafi dakinsu Amira, na tarar da ita a kwance idonta a rufe kamar mai bacci amma kana ganinta kasan ba baccin take yi ba. Na daka mata duka a cinya nace "sleepy heads, ki tashi mu tafi karatu" ta bude idonta tana kallona da mamaki. Ita tasan na sani. A hankali tace "bana jin dadi ne" nace "yeah right, in kika fita zaki warke" a haka na takura ta tayi wanka muka fita. Tun daga nan muka cigaba da kawancen mu da Amira, amma duk abinda muke yi da Ibrahim yazo gurin zata tashi, ni ma kuma bana cewa ta tsaya saboda ta ciki na ciki daurewa kawai nake yi.

Soyayya sabowa muke shimfidawa da Ibrahim. Gani nake tunda na shiga SS3 ai I am old enough, shima kuma dama kiris yake jira. Sam Ibrahim baya kunyar nuna min soyayya ko a gaban waye ma kuwa, ni dai duk sai kunya ta rufe ni. Rannan a class ya zo yana cewa wai ya kasa bacci jiya kawai sai yaji muryata yake so yaji, wai saura kadan ya taho hostel, su kuma 'yan ajin sai su biye masa suyi ta tsokana ta, inna ga sun dame ni sai in tashi in bar musu ajin.

Anan nake so inja hankalin iyayen yara musamman 'yan mata akan mu kula da tarbiyyar 'ya'yan mu. Yanzu makarantu sun baci, da yawa malamai suna soyayya da daliban su mata. Kuma da yawa daga cikin su basa nufin alkhairi, musamman a boarding schools. Kuma school management suna basa kula tunda shi kansa principal din ko vice ba zai rasa budurwa ba, musamman a private school inda yaran suke da budaddan ido. Mu tabbatar mun bawa yaran mu tarbiyya sannan kullum muke yi musu addu'ah dan babu abinda yafi addu'ah iyaye kariya a gurin 'ya'yansu. Allah yayi wa zuri'ar mu albarka baki daya.

Rannan muna a gaban chemistry lab muna duba past questions and answers na WAEC sai muka hango Ibrahim da wasu mata su biyu a gaban staff room, Hasiya ce ta taba ni tace "kinga mutumin ki can, ko suwa ya samu kuma" ina dubawa naga mata ne su biyu da kaya a hannun daya, dayar daga gani babbar macece dayar kuma budurwa, budurwar da hijab matar kuma da babban mayafi, sun jima a tsaye suna magana sai naga ya karbi kayan hannun budurwar ya wuce gaba suna binsa a baya suka tafi staff quarters. Har dare ban kuma ganinsa ba kuma ina ta tunanin ko su waye wadan nan? Washe gari da safe sai gashi yazo yace min inzo, muna fita waje sai yace "there is someone here that wants to see you" gaba na ya fadi nace "who?" Yace "my mother" nan da nan naji wani tashin hankali yazo min, he wants me to meet his mother, this is serious. To ni yanzu da wacce fuskar zan je mata? Kuma me zance mata? Nace masa "Ibrahim am sorry, I can't" ya bata fuska yace "why can't you?" Nace "tsoro nake ji" dariya yayi yace "tsoron me kuma? Bata cin mutane, besides tare zamu je, just ku gaisa shikenan" na kalli kayan jikina, uniform ne a wanke a goge, hijab dina ya rufe har bom2 dina, fuskata babu kwalliya, dama ba kwalliyar nake yi ba. Na sake kallonsa har yanzu da dariya a fuskarsa. Yace "you look great, let's go" yana fadin haka ya shige gaba, na bishi a baya kamar wadda kwai ya fashewa a ciki. Direct visitors room muka je, ya dan tsaya yana kallona yace "are u ready" na girgiza kaina alamar no, yayi dariya kawai ya bude kofar da sallama. Nima nayi sallama na shiga. Su biyu ne kamar jiya da babba da karama. Ina kallon babbar nasan ita ta haifi Ibrahim sai dai bata kaishi tsaho ba, karamar kuma sam basa kama dan ta fishi hasken fata sosai, dan da kadan zan nuna mata fari, sai dai ita fuskarta duk kuraje yayin da tawa take tas. Kana ganin maman su Ibrahim kaga typical yaroba woman. Da daurin zanin ta akan riga, da goggoron akan ta. Ibrahim ya zauna a kusa da ita ni kuma na durkusa daga nesa a kasa na gaisheta da turanci. Ta amsa min amma daga gani turancin na isar ta yayi ba. A raina nace oho dai ni ba iya yarabanci nayi ba sai dai mu tsaya daga gaisuwar. Na gaishe da dayar tunda daga ganinta nasan ta girme ni. Ta amsa tana dariya, na dago kai sai naga Ibrahim ne yake hararar ta, ya wani dora kafa daya akan daya. Maman su kuwa idonta yana kaina. Sai da muka dan jima a haka sannan Ibrahim yace "Maimunatu this is my mother, and that girl over there is my sister" da saurin ta tace "his step sister" na dago kai na kalleta sai naga idonta a kansa, bansan dalili ba sai naji hankali na bai kwanta ba da kallon da take masa. Mamansu naji ta fara magana da gurbataccen turancinta "kullum na kira Ibrahim zancen sa Maimunatu tace kaza maimunatu tayi kaza, inna yi masa complain akan baya zuwa mana weekend sai yace ai muna karatu da Maimunatu sun kusa fara exams, kullum zancen kenan, shine nace bara inzo inga maimunatun nan dai da ido na" naja hijab dina na rufe fuskata, inaji tana masa magana da yarabanci, naji dai tace fulani a ciki, sai naji yace "mu fa yaroba ba'a wani kunyar suruka, in zaki bude ido ki bude, dan duk randa kika haihu ita zata yi miki wanka" na kara dunkule wa a guri daya a raina ina cewa kai Ibrahim mai ya kawo zancen haihuwa kuma? Gaba daya suka yi dariya. 'Yar budurwar ce tayi magana tace "let me introduce myself properly, ni step sister dinsa ce, ma'ana babana ne mijin mamansa, sunana Efisowa amma zaki iya kira na Efi, nazo in taya shi assessing sabida nasan ba iya zabe yayi ba. Dama tunda naji mama tace Fulani nace sai nazo nagani da kaina, gashi kuma naga kinyi kankanta da yawa" Ibrahim yace mata "shut off" sannan yayi mata magana da yarabanci itama ta mayar masa, sai maman tayi musu magana duk sukayi shiru. A hankali maman tace min "ina parents dinki?" Nace mata "suna cikin garin abuja" tace "ku 'yan Abuja ne" nace "'yan jigawa ne mu" kawai sai naji matar tayi min, yadda take magana a hankali irin maganar Ibrahim. Efi ce dai hankali na bai kwanta da ita ba, duk na damu ganin ta kasa dauke idonta daga kan Ibrahim. Ibrahim ne yace zai mayar dani class dan muna karatu, Efi ta sake yin magana da yarabanci shi kuma ya sake ce mata shut off maman tayi tsaki tana kallon efi alamar warning. Tunda muka fito bamu yi magana ba sai da muka dan yi nisa sannan yace "how do you like my mother" nace "she is OK, you look like her but taller" yace "no, she always say da baban mu nake kama" Har nayi tunanin kar in tambayeshi akan efi amma sai zuciya ta ta kasa jurewa, nace "Your sister doesn't like me" yayi dariya yace "yours doesn't like me either" nima nayi dariya sannan nace "but this is different, i feel like there is some tension between you two" yayi shiru bai bani amsa ba, wannan ya tabbatar min da zargina. Nan take naji raina yana kuna. Sai da muka kusa zuwa class sannan yace "koma menene da a tsakanina da efi is over tun tuni, abinda yake tsakanin mu sam bashi da dangantaka da efi. A mincewar mama da baba kawai nake bukata. Please Maimunatu don't screw this thing off. Mama tazo takanas saboda ta ganki, please show her your best behavior yadda in taje zata bawa baba labari shima zai yaba dake, please don't let Efi get in your head, that is exactly what she wants" muna zuwa gaban class din mu nayi shigewa ta ba tare da nace masa komai ba. Har na zauna yana tsaye a gaban class din ya rungume hannayensa fuskarsa da alamar damuwa.

Bayan na zauna sai nayi tunanin ban kyauta wa Ibrahim ba, kuma gaskiya ya fada cewa this is our chance, ya kamata inyi kokari inyi probing to his mother cewa I am good enough, inna bari kishin Efi ya shiga raina tun yanzu to ina da problem.

Anan zan tsaya inja hankalin 'yammata har ma da matan auren, idan mace ta nuna tana son mijin ki, musamman idan shi mijin ko saurayin baya son ta, don't make an enemy out of her, ki jata a jikin ki kiyi mata kirki sosai, make sure duk sanda saurayin ko mijin yake around kun nuna mata irin soyayyar da kuke yiwa junan ku, ita da kanta zata ji kunya ta ja baya, amma idan kika kama fishi da fada kamar kina tura shi gurinta ne. Ke kuma budurwa da kike neman miji, kar kiga wata da nata kiyi sha'awa kice lallai sai kin raba. In dai har soyayyar tsakani da Allah yake yi mata to ba zasu rabu bafa.

Washe gari da yamma muna kofar library da Amira da wasu kawayen mu sai ga Ibrahim sun taho gurin mu shida Efi, tun daga nesa nake kallon yadda take ta shishshige masa, gaba daya kowa ya tsaya yana kallon su har suka kara so. Kallo daya nayi masa nasan ransa a bace yake. Suna zuwa yayi introducing dinta generally, sannan yace "she said she wants to look around the school" nayi sauri nace "she is welcome" tare da miko mata hannu, ta kalle ni sannan ta kalli Ibrahim kamar me neman izni shi kuma ya dauke kansa ya juya ya tafi, tayi masa magana da yarabanci bai amsa mata ba, ya saka hannayensa a aljihun wandon sa yayi tafiyarsa. Yana tafiya na fara yi mata hira, nayi mata introducing duk friends dina da suke gurin. Amira ko kallon ta bata yi ba. Daga nan nace tazo in showing her around, tun daga classes, labs, kitchen, dining hall duk sai da na kaita, sannan na kaita hostel.
Hafsat tana kwance muka shiga, ta bimu da kallo, sannan tace min da fulatanci "wannan kuma a ina kika samota?" Na amsa mata da turanci "she is Ibrahim's step sister" sannan na kalli Efi nace "this is my Sister, Hafsat" Efi tace "oh my God she is so beautiful, nice to meet you" ta mika wa Hafsat hannu, kirikiri Hafsat ta ki bata hannu tace da fulatanci "ni bazan taba hannunki ba, kurwata kur" nayi dariya, Efi tace "what did she said?" Nace mata cewa tayi "ai kin fita kyau ma" nan da nan ta washe baki tace "thank u" Hafsat ta harare ni. Nan da nan Efi ta fara santin dakin mu, wai wannan ai ko a gida sai haka, ita in tana nan ai ba zata so ayi hutu bama. Nan da nan na chika mata gabanta da kayan chiye2 muka zauna muka yi ta hira, tana bani labarin gidan su. Amma ni bance mata komai ba akan namu gidan. Har akayi sallar magrib muna tare can sai Ibrahim ya kira ta yace ta fito su koma gida, haka kawai sai na samu kaina da jin babu dadi saboda ya kira ta a waya. Na dauko wani set din toiletries na mu na dove na saka mata a keda na bata. Tayi ta mamaki wai ina student har nake kyautar kaya?

Washe gari Ibrahim yace min zasu tafi, na hado sweets da biscuits madu yawa a leda na boye a hijab dina saboda 'yan sa ido, yazo ya kira ni muyi sallama da mama. Ina shiga na

Please Login or Register in order to submit comment