Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

makaranta me kyau sosai ya saka ta, yayi hiring 'yan aiki saboda kula da gida, baya son mama ta ringa aiki da kanta, amma duk da haka tace a bar mata girki zata ke yi musu da kanta tunda bata saba da zaman banza ba. Ya saka mata DSTV a dakinta saboda in babu kowa ta ringa debe mata kewa. Maimunatu kuwa a part dinsa ya ware mata daki, ya cika mata shi da dukiya duk abinda yasan little girl zata bukata sai da ya saka mata, amma ita duk wannan bai dame ta ba, ita babban burinta shine ta ganshi tare da ita, dan sam kin zama tayi a dakinta sai nashi dakin ta dawo, tare suke kwana ta makalkale shi kamar zai gudu, har ransa yake jin tausayinta, bata san mahaifiyarta ba shi kuma mahaifin nata yayi watsi da ita yana chasing dead dreams dinsa, rannan yana shiryata zai kaita makaranta tace "Daddy please don't take us back to ibadan" ya durkusa a gabanta yana shafa gefen fuskarta yace "I promise you I won't". Dadin gidan yake ji sosai yanzu, amma da har baya so ya dawo gida saboda zaman kadaicin da yake ciki, yanzu kuwa kullum cikin nishadi yake da dariya, bashi da wani sauran problem sai Amina. Sam Amina taki kulashi, tun ranar nan har yau taki daukan wayarsa, yaje gidan yafi sau a kirga amma taku fitowa, direct take cewa a gaya masa ba zata zo ba, yayi messages din ban hakurin har kalamansa sun kare, kullum yana ganinta online a WhatsApp amma maganar duniyar nan in yayi mata ba zata bashi amsa ba, kuma tana karantawa yana gani. Gashi kuma wani irin sabon sonta ne yake kara shigar sa, ita kuma kamar da gayya kullum sai ta chanza DP dinta, sai yayi saving yayi ta kallo, sam yanzu ya daina kanin fuskar moon a fuskarta, har mamaki yake yi ya akayi da yake ganin suna kama, they are totally different, kowacce is special in her own way. Daga baya ya yanke shawarar zai biyo mata ta sama, dan haka yaje gidan ya binciki ranar da zai samu Daddy, ranar kuwa yaje ya aika akayi masa sallama dashi, Daddy ya gane shi dan haka yayi masa iso har palon bakinsa yana tambayarsa ya saukin jiki, Ibrahim kan har ya manta ma da yayi wata jinya, shi yanzu jinyar zuciyarsa ce a gabansa. Nan ya yiwa Daddy bayanin abinda yake tafe dashi, Daddy yayi murna sosai amma kuma sai ya tambashi ko Aminan ce tace masa yazo? Nan fa Ibrahim ya fara shafa kai, daddy yace kar ya damu zai yi magana da Aminar yaji menene amsarta, duk abinda ake ciki zai saka walid ya kira shi a waya ya gaya masa. Ibrahim ya riga yasan amsar da Amina zata bayar dan haka sanda walid ya kira shi ya gaya masa abinda tace bai yi mamaki ba, amma Daddy yace a gaya masa ya cigaba da nemanta, inta chanza ra'ayi shikenan, in bata chanza ba kuma sai dai yayi hakuri dan ba za'a yi mata dole ba. Nan Ibrahim ya kara kaimi gurin rarrashi da ba da hakuri amma shiru kamar an shuka dusa, kuma har a zuciyarsa bai taba tunanin ya hakura ba saboda yana ji a ransa cewa itace matarsa. Ranar wata Friday kawai yana zaune a office sai yaga message, har sai da ya mitstsika idonsa dan yana ganin kamar yaudarar sa idon yake yi, Amina, ya bude ya fara karantawa "if you can, come over tomorrow, someone wants to meet you" da sauri yayi reply, "of cause I can, And I really hope that someone is you". Saturday yana yin sallar la'asar ya cewa mama zai dan fita ya dawo, sai gidan su Amina, suka gaisa da baba habu dan yanzu sun fara sabawa dashi, ya shiga yayi packing ya kira ta a waya, bata dauka ba har ta katse, sai kuma gata ta fito, ta kira wani yaron gidan tayi masa magana sannan ta koma ciki, yaron yazo yayi masa iso zuwa palon su yaya Walid, ya shiga ya zauna yana karewa haduwar gurin kallo, sam yanzu dukiyar gidan bata tsorata shi saboda yasan karamcin jama'ar gidan. Yaji motsi a bakin kofa, yayi sauti ya juya, Amina ce a tsaye da dogon hijab a jikinta tayi sallama ta karaso ciki, murna kamar ta kashe Ibrahim, gani yake kamar bai taba ganin macen da hijab yayi wa kyau irin amina ba. Ya mike yana amsa sallamar ta, sai kuma yaji wata sallamar daban, ya kalli bakin kofar, nan take annurin fuskarsa ya kau, ko a mafarki baya fatan ganin wannan fuskar, me take yi anan, ta karaso palon kamar wadda kwai ya fashewa a ciki, ya kalli Amina da sauri yace "what is she doing here?" Amina ta yamutsa fuska tace "dama ita ce mai son ganin naka bani ba" Amira ta karaso ta durkusa a gaban Ibrahim, da sauri ya matsa yace "tashi daga kusa dani kar kisa inyi amai" Amina taji wani takaici ya kama ta, ta rike kugu zata zazzaga masa masifa kuma sai ta dakata tana so taga yadda zasu kare kafin ta yanke hukunci, Amira ta fara magana muryarta na rawa "Ibrahim dan Allah ka yafe min. Nasan na munanawa rayuwarka, wallahi sharrin shaidan ne da son zuciya suka kaini ga aikata haka, dan Allah ka yafemin, ni yanzu yafiyar ka ita kadai nake bukata, ka yafemin ko na samu Allah ya yafemin ko rayuwata zata yi kyau" ya kalle ta ya dauke kai, sai kuma ya kalli Amina, ba dan abinda Amirar tayi ba da bai hadu da Amina har yayi mata wannan son da yake yi mata yanzu ba, ya tuna da little Maimunatun sa, ba dan abinda Amira tayi ba da ba'a haife ta ba, ya kuma tunawa da cikin dake jikin Moon, dan Sultan, shima badan Amira ta raba shi da Moon ba da ba za'a haifeshi ba. Babu wanda ya isa ya raya ko ya kashe sai Allah, kamar yadda babu wanda ya isa ya wuce kaddarar sa. Ya kalli Amira yaga yadda take kuka daga dukkan alamu va karamar nadama tayi ba, ya dauke kansa yace "na yafe miki, Allah ya yafe mana baki daya" ba Amira kadai ba, hatta Amina sai da tayi mamakin saurin yafiyar da yayi wa Amira, ya kuma kallon Amirar da take durkushe har yanzu a gabansa yace "tashi ki tafi, na yafe miki nace" da sauri ta mike tana kallon Amina sai kuma ta fita, ya dawo da kansa kallon Amina yace "I now have the most precious jewel in the world, why will I be unhappy?" Murmushi taji ya subuce mata, sai kuma ta sake bata rai, ya karaso kusa da ita yace "ko nima sai na durkusa a kasan ne?" Ta juya kamar zata fita sai ta tsaya ta juyo tace masa "ka dawo ku sake magana da Daddy, wannan karon da izini na". Dadi kamar ya kashe Ibrahim, sai kuma wani tsoron Allah ya kama shi. Haka fa Allah yake kallon mu idan munyi masa laifi mun roke shi gafara, sai ta duba yaga cewa mu din masu gafara ne ga 'yan'uwan mu? Kafin ya yafe masa ko akasin haka. Wannan ma wani darasin ne.

Episode Ninety Two and Three : Maldives 1 and 2
Riyadh;
Three weeks after the gender reveal party. Sosai Takawa ya putting pressure a kan sultan, sultan ya kara saka ni nayi wa Ummee magana amma wannan karon ko kallon kirki ban samu daga gareta ba. Sai ma ce min tayi in gaya wa wanda ya turo ni yazo ya same ta da kansa. Sam yanzu sultan bashi da cikakkiyar nutsuwa, yana son komawa gurin babansa kuma baya son ya bata wa ummeen sa rai. Ina yin iyakacin kokarina gurin kwantar masa da hankali amma nasan sultan is a busy person, zaman banza da rashin aikin yi shi yake irritating dinsa, duk da ya samu Ahmad sun kulla abokantaka, kullum zai zo ya dauke shi su fita amma hakan is not enough for sultan. Yanzu har ya kai matakin in Takawa ya kira sultan sai yaki dauka, he is out of excuses. Rannan ina shiryawa zan shiga gurin Ummee sultan kuma yana kwance akan kujera ya rufe idonsa, nasan ba bacci yake ji ba, sai da na gama shiryawa sannan na durkusa a kusa dashi na hura masa iska a fuskarsa, ya dan bude ido yana kallona, nace "zan shiga gurin Ummee" ya mayar da idonsa ya rufe yace "zan shigo an jima" na tashi na tafi jikina babu dadi, bana son ganin sultan cikin damuwa sam, sai inji duk nima na shiga damuwar. I must do something about this. Ban sha wahalar hada sultan da ummeensa dan in cigaba da ganinsa cikin damuwa ba, amma kuma menene abinyi? A harkar da ta shafi iyaye dole mutum yayi taka tsan tsan. A bedroom na sami Ummee tana zaune a kan gado da system a gabanta, na shiga da sallama, ta amsa min idonta akan screen din system din, sannan tayi min alama da hannunta na inzo in zauna kusa da ita, ina zama ta juyo min da screen din system din, fuskarta dauke da murmushi tace "what do you think of this?" Na kalli abin da take nuna min, model ne na dakin baby, with complete furniture, crib, drawers, night stand da komai, dakin yayi kyau sosai, amma kuma sultan ya gama tsara mana baby room din mu tun sanda yake zana plan din gidan mu a Abuja. Na kasa bawa Ummee answer, ta cigaba da magana "ina tunanin bedroom din tsakiya ba part dinku za'a mayar baby's room, sultan sai yayi mana dan renovating dinsa kadan, yayi closet a ciki, sai mu fara order kayan baby kuma, furnitures first, sai electronics sannan sai mu dawo kan clothings" tayi ajjiyar zuciya, "we have alot to do, list ya kamata mu rubuta..." Sallamar sultan ce ta katse mata maganar ta, muka amsa masa a tare, yana kallon mu yace "yau hirar ta daki ce kenan" ta dan bubbuga kan gadon kusa da ita tace "come Abubakar, sit with us" ya karaso ya zauna yana satar kallona, tace "we were just talking about the baby, baby room muke so mu fara shiryawa, muna bukatar taimakon ka gurin renovating dakin babyn" ya dan dafe kansa kamar mai ciwon kai yace "Ummee babyn nan fa yana da atleast wata uku kafin yazo, besides already yana da room dinsa a Nigeria" take naga murmushin fuskarta ya kau, tace "Nigeria? I tot I made myself clear cewa babu zancan komawa Nigeria ko?" Sultan ya bata rai, he has reached his limit. Ya saka hannu ya dauko wayar sa yana dialing, kawai sai gani nayi ya ajiye ta akan table din gaban gadon, tana kara sai kuma mugaji an dauka, muryar Takawa, yace cikin fada "Sultan wato ina ta kiranka shine kaki dauka ko? Wannan wanne irin aikin vanza kake aikatawa haka? Kawai ka dauki iyalinka ka tafi dasu can wata uwa duniya ku zauna a can? Zaman me kuke yi har yanzu? Aikin da ka bari wa zai yi maka?" Sultan yayi gyaran murya yace "barka da yamma" Takawa yace "bazan amsa ba, me ya hanaka dawowa har yanzu?" Sultan yana kallon Ummee yace "bani na hana kaina tahowa ba, Ummee ce tace bazan dawo Nigeria ba a Riyadh zan cigaba da zama, na saka ka a speaker phone yanzu tana jin abinda kake cewa, sai kuyi magana a tsakanin ku" na kalli fuskar Ummee naga wani missed emotions, sama sama take numfashi, ta kasa magana, sultan ma ita yake kallo ita kuma wayar take kallo. An jima a haka sannan Takawa yace "Khairat, kin san dai bai kamata kice zaki hana yaron nan dawowa gidan su ba ko?" Ta hadiye yawu ta kara bata fuska tace "why not? Nan ma ai gidan su ne, kamar yadda yake da iko da gidanka haka yake da iko da nawa. Kamar yadda kake da iko dashi haka nima nake da iko dashi, in fact na ma fika iko dashi, nace ba zai dawo ba and that is final" yace "you can't do that. Aikin sa kuma fa?" Tace "wani zan samar masa anan" yace "'yan uwansa kuma fa da suke ta nemansa anan me kike so in ce musu? Mutanen gari fa da suka dogara dashi me kike so in ce musu? He is a Prince for God's sake khairat, he has a role here, ko anan ma zaki samar masa matsayin Prince din ne?" Tace "bazan mayar dashi Prince anan ba amma zan bashi rayiwa fiye da wacce zaka bashi a matsayin Prince din, zancan me zaka gayawa mutane kuma oho, that's your problem not mine, abinda na sani shine dana yazo gurina kuma babu abinda zai kuma rabani dashi sai mutuwa" ya kwantar da murya Yace "khairat wannan maganar tsakani na dake ce, ki bar sultan ya taho tare da iyalinsa, kin san dai halin da moon take ciki, she needs her family besides her, in yazo sai mu taho tare dani dashi mu zauna muyi maganar sosai" ta danyi dariya tace "am not a kid ballantana kayi min wayo, Maimunatu will remain here ita da abinda yake cikinta, idan family dinta suna son ganinta da kansu zasu taho nan su ganta, ai dama aure babu inda baya kai mutum, aure ne ya kawo ta Riyadh, kuma babu wata care da zaku bata a can wadda bazan bata a nan ba" yace "amma dai kinsan nima ina da right akan su ko? Yanzu abinda za'ayi tunda sunyi wata biyu a gurinki, ki turo su suyi wata biyi ana sannan sai su take dawowa, kinga shikenan kowa will spend sometimes with him babu wanda zaice an cuce shi" tace "wata biyu? Cuta? You must be joking, sai da yayi shekara talatin ban ganshi a idona ba, how can you tell me wata biyu? In so kake a raba sai ka bari in yayi shekara talatin anan sannan ya koma gurinka" da sauri yace "shekara talatin? Do you think zan kara shekara talatin a duniya? Me yasa kike nema ki zamo mai son kanki ne?" Tace "son kai? Ai sai dai inyi maka wannan tambayar, tunda har ka iya bugo waya kace masa ya koma gurinka, saying you will let him come back again, bayan you don't keep your words, you will keep me waiting and waiting till eternity" ya danyi shiru da alama maganar ta shige shi sannan yace yace "am sure sultan ya gaya miki duk abinda ya faru bayan rabuwar mu, so am sure kinsan ba wai a sona na barki zaman jira tsahon shekaru ba" tace "that's your problem" yace "yes, it is my problem amma let me ask you something, ke menene ya hanaki zuwa kiga dan naki har tsahon shekaru talatin, ki kina son kice daure miki kafa akayi duk tsahon shekarun nan, baki damu dashi ba tunda har baki neme shi ba" nan da nan hawaye ya taru a idon Ummee, ni dai ina zaune sai in kalli ummee in kalli wayar, sultan ya mike tsaye yace "wait, all of you, ya ishe ku haka. All of you are forgetting something, am not your little love anymore. Am not a toy da zaku ke playing around with har kuna lissafin zaku ke passing dina around for one one month or one one week. Wannan duk maganar da kuke is between the two of your, dani da iyalina ba zamu kasance in the middle of it ba, ba zamu zama ball ba balle wannan ya buga ya bawa wannan ya buga. We will go away. Duk ranar da kuka yi settling kanku just give us a call sai mu dawo, amma ku tabbatar a cikin settlement din babu zancan muje gurin wannan sannan mu sake komawa gurin wannan, we are not toys, we are our own people" ya mika min hannu na kama ya daga ni tsaye, babu wanda yayi magana a cikin su sai Ummee data fara ruwan hawaye, yace "daddy wannan waya tace kuke fada a cikin ta, kana iya kiran wayarta sai ku cigaba a fadan acan" Takawa yace "sultan listen to me, kar ka dauki yarinyar mutane da ciki kana yawo da ita gari gari, zanzo Riyadh din, we will talk thi gs out" sultan yace "in kun gama talking things out din just give us a call" ya kashe wayar yana kallon Ummee, ita din ma shi take kallo, ba tare daya ce mata komai ba ya ja hannuna da sauri muka fita. Muna shiga part din mu ya zarce bedroom ya fara fito da kayan mu yana zubawa a kan gado, sannan ya jawo akwatina yana jerawa a ciki, hada wa kawai yake yi da nawa da nasa baya ware wa. Ni dai kawai ina tsaye ina kallon sa, nace "are we really going?" Yace "yes, and don't try to talk me out of it" nace "i won't. Amma ina zamuje?" Bai kalle ni ba yace "am not stupid, so kike in gaya miki ki gaya mata ko? But know one thing, ba America zamu je ba saboda can ne inda Takawa zai fara neman mu. In sun gama fadan zamu dawo. Zamu bar wayoyin mu a bude yadda zamuke magana dasu" nace "idan haihuwa ta kama ni a can kuma fa, mu kadai ya zamuyi?" Yace "a haka suka haife ni su kadai. And believe me, ba zasu kai har lokacin haihuwarki basu shirya ba, duk kansu kowa yana so ya zauna a waiting room ranar da zaki haihu" nayi murmushi dan nasan irin lissafin da Ummee take yi kullum, wani lokaci har tunani nake yi anya kuwa zata ke bani babyn ina dauka?.
Tare muka zauna muka shirya kayan mu. Basics kawai muka dauka yace ma sayi kayan sawa sosai a can, dan haka kananan jakankuna kawai muka dauka guda biyu, lokacin an kusa sallar magrib, muna fitowa daga part dinmu na nuna masa part din Ummee ya makale kafada "I don't want to see her crying" na tafi ni kadai, na tura kofar na shiga, tana zaune akan kujerar data zauna ranar da na fara zuwa gidan, idonta akan kofa, ta saka hannayenta a tsakanin cinyoyinta. Na tsaya a bakin kofa ina jin tausayinta har raina, Takawa zai iya tafiya neman sultan amma ita she is tied to saudiyya, dan haka dole sai dai azo gurinta ita ba zata iya zuwa wani gurin ba. Ta mike tsaye tana jujjuya hannunta tace "bai gaya miki ina zaku je ba ko?" Nace "yes" tace "yana ina?" Na nuna mata waje, na karasa kusa da ita na rike hannunta nace "I will call you daga duk inda muka je" tace "magrib tayi yanzu, kice masa ya bari sai da safe sai ku tafi" nayi shiru dan nasan ba zai yarda ba, sultan is soo headstrong in ya saka kansa abu babu mai hana shi, ta dora hannun ta akan cikina taji yadda dan cikin yake motsi sai ta danyi murmushi tace "be safe, ki kula dashi kamar yadda kika saba" nace "insha Allah" na juya na fita ina goge hawayen fuskata. Ina fita na tarar sultan har ya dauko daya daga cikin motocin gidan ya shiga yana jirana, na shiga ina cigaba da kuka na, yace "cry cry baby, dake da ita bansan wanda yafi wani ruwan hawaye ba" sai kuma naga ya juya yana kallon kofar shiga gidan, nima na kalli gurin, Ummee ce a tsaye, tayi folding hannayenta a kirjinta, mayafinta ya sauko kan kafadarta, iskar da ake yi a gurin tana ta yawo da gashinta, she looks so lonely and depressed. Sultan yayi sauri ya dauke kansa ya ja motar da gudu muka bar gurin, ni kuma har muka fita gate idona yana kanta.
Muna fita naga ya dauko wayarsa yana kiran Ahmad, tambayarsa yake hotel me kyau inda zamu iya kwana, Ahmad yana tambayarsa lafiya amma bai gaya masa komai ba, daga karshe dai gidan Ahmad din muka fara tafiya muka dauko shi sannan ya rakamu hotel din, yana ta mitar me yasa to ba zamu kwana a gidan saba amma sultan yaki yarda, kuma sai da ya saka shi yayi masa alkawarin ba zai ce da kowa komai ba, ya gaya masa zamu dawo wata rana amma ba yanzu ba. Wani lafiyayyen hotel ya kaimu, sultan ya biya kudin kwana daya, ya tambayesu in da akwai motar da take zuwa airport da safe suka ce masa eh, kawai sai ya bawa Ahmad key din motar da muka taho da ita yace ya ajiye motar a gurinsa, Ahmad ya tambaye ni ina zamu je na ce masa nima ban sani ba. Dan karamin daki ne single room mai hade da toilet, amma kuma ya hadu sosai. Sultan yayi mana order abinci sannan ya dawo ya zauna a kusa dani yace "Moon, do you think what am doing is right?" Bance masa komai ba saboda bansan abinda zance masa ba, yace "I don't know what to do shi yasa nayi haka, ina son komawa Nigeria dan acan rayuwata take ba nan ba, amma kuma bana son inyi hurting Ummee, ba zata iya bina ba saboda shi is tied to saudiyya, I don't know what to do, we will just let them figure out me zasuyi sannan sai mu dawo" na ce "ina zamuje?" Ya danyi murmushi yace "do you promise not to tell any one?" Nace "can I at least tell Mommy?" Yace "yes, only Mommy" nace "OK" yace "am taking you to the Maldives. Dama nayi miki alkawari tun tuni amma ban samu na cika miki ba" yana murmushi yace "we are going to have our honeymoon" nayi dariya na nuna masa cikina, yayi kissing cikin yace "he is welcome to join us". Ranar sultan bai kwanta da wuri ba, yana ta making phone calls, ya saya mana ticket, ya kama mana hotel a can Maldives din, sai daya tabbatar komai is settled sannan ya kwanta.
Washegari daga nan Riyadh muka shiga wani dan karamin jirgi zuwa Maldives. Tun a jirgi nasan lallai da gaske sultan honeymoon din yake so, nima na biye masa. Kusan duk wadanda suke cikin jirgin couples ne, tunda shi Maldives guri ne da ake zuwa mostly fir vacations and honeymoons. Maldives kasa ce amma ba kamar sauran kasashe ba, tana consisting thousands of islands a indian ocean, saboda yawan islands din wadansu islands din ma babu mutane a ciki. Capital dinsu shine Malee, wanda shine babban island din da yafi kowanne girma, kuma anan ne mutanen kasar suke zaune, sauran islands din duk an barwa tourist, wadansu islands din ma saboda kankantarsu hotel daya ne kawai a gurin, wadansu ma babu hotel din sai dai ayi 'yar bukka ayi decorating gurin mutane suna zuwa su wuni ko su kwana. A Velana international airport muka sauka, which is an island on it's own, daga nan kuma kowa sai ya fadi inda zaije sai yayi hiring speedboat a kaishi. Malee sultan ya fara cewa zamuje, nan mukayi ta zagaya garin muna kallon haduwarsa, muka shiga mall dinsu mukayi siyayyar kayan da zamu bukata a hotel din da zamu sauka. Ni kam maternity gowns nayi ta siya, sexy maternity gowns, sultan kam kananan kaya yayi ta diba, ya siya min wadansu nima amma ni nasan cikina ba zai barni ni saka ba, na dai samu wadanda nasan zasu saku na dauka, bama bukatar abinci ko toiletries duk hotel din mu zasuyi providing. Daga na muka tafi port din su muka hau motor speedboat dinsu zuwa Island din Soneva Jani, wanda shine hotel din da sultan ya zabar mana. Tun a cikin boat din sultan ya fara karbar amarcinsa, dan sanda muka zo hotel din ma bamu sani ba sai da me boat din yazo yayi mana knocking yace munzo. Muna sauko wa na saki baki ina kallon gurin, ni in ana cewa hotel abinda yake zuwa kaina shine dogon gini da manyan glass Windows da balconies, sam ba haka gurin yake ba, cabins ne separate from each other, gaba dayansu a cikin ocean suke, sai hanyar da tayi linking from one cabin

Please Login or Register in order to submit comment