Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

karami" na danyi digesting maganar kadan, wanne karatu ne akeyinsa a shekara daya?. Taci gaba da labarin Sultan tace "daga nan sai kakansa ya dauke shi, ya mayar dashi dakinsa, hatta kayan sakawarsa a can suke, gata da soyayya sosai ya nuna masa, a haka har yaron ya saki jikinsa ya daina kuka, amma kuma duk da kankantarsa bai manta da mahaifinsa ba, dan duk inda ya ganshi zai tafi gurinsa da gudu, amma ko kallon inda yake baya yi, in yazo ya rike kafarsa sai ya ture shi ya fadi yayi tafiyarsa. A gurin sarkin lokacin kuma babu tamkar karamin sarki, dan har bacci akan gado daya suke yi, ko taba shi babu wanda ya isa yayi hatta su Yaya da Nani, abin ya dami yaya kwarai amma duk sanda tayi magana to ranar kuwa zata ga bacin rai. A haka har yaron ya shekara goma, ya sangarce sosai babu mai saka shi babu mai hana shi, ko tafiya zuwa kasashen waje tare yake tafiya dashi, a fada suna tare, in taro zaije tare zasu tafi. Rannan kawai da safe aka ga basu fito sallar asuba ba, aka shiga za'a tashe su amma sai jikan ne kawai ya tashi, kakan Allah ya karbi ransa a cikin bacci. Wannan mutuwar ta tayar da hankalin kowa a masarautar nan amma babban abin tausayi shine karamin sarki, bai saba da kowa ba sai shi bai san kowa ba sai shi, dan haka rasa wanda zai rarrashe shi akayi, kwata kwata ya hana a yi wa gawar sutura, sanda mahaifinsa yazo muka ji dadi cewa an samu mai rarrashinsa amma yana zuwa sai ya dauke shi chak ya tafi dashi wani tsohon store ya daure masa bakin sa, ya daure masa hannayensa da kafafuwansa ya rufe shi a dakin yayi tafiyarsa. Babu wanda bai tausayawa yaron nan ba, kuka biyu muka yi a lokacin, har yanzu ina iya tuno wani irin gunjin kuka daya ringa yi babu baki, kamar ransa zai fita, wallahi ban dauka yaron nan zai yi rai ba, na dauka zuciyarsa zata buga ya mutu, amma zuciyarsa mai karfi ce. Haka ya kwana anan sai da safe sannan ya fito dashi kuma ya gaya masa in ya kuma yin kuka sai ya kuma daure shi. Bayan anyi sarauta su Hajiya suka dawo nan mu kuma muka koma sabon guri tare dasu Yaya, nan Hajiya tace abar mata Karamin Sarki, Yaya sam bata so hakan ba amma sai ta barshi din wai ko hakan zai sa ya saba da mahaifanan. Mu dai daga nan bamu kuma jin labarin da yake ciki ba sai kawai muka ji labarin wai an kai shi Lagos gidan kangararru, Yaya ta tayar da hankalinta sosai, amma ko ta kira Takawa ta yi masa magana sai ya nuna mata kamar zai aika a dawo dashi amma shiru, sai da ya shekara biyu acan sannan Yaya ta aika galadima ya dauko shi, tace masa ya mayar dashi gidansa ya zauna acan, ai kuwa nan rigima ta tashi dan har saida Yaya tayi sharia tsakanin sarki da galadima akan me yasa galadima ya dauko karamin sarki daga Lagos, wannan shi yasa duk 'yan uwa kowa ya dauke hannunsa daga kan maganar karamin sarki har aka turashi kasar waje karatu babu wanda yayi magana, amma ni nice shaida, duk watan duniyar nan sai Yaya ta saka an sauke masa alqur'ani da niyyar ya zama kariya a gare shi a duk inda yake".
Jin tayi shiru yasa na gyara zamana nace "to yanzu baba gaji, duk gidan nan babu wanda yasan ina ne garin su mahaifiyar Sultan?" Tayi shiru tana tunani, sannan tace "to mu bayi dai kam bana jin akwai wanda ya sani, amma Yaya ba zata kasa sani ba, amma kuma ranki shi dade bana jin zata gaya miki, dan da zata fada da duk tsahon shekarun nan da ta gayawa karamin sarki". Na koma na kwanta na lumshe ido na ina juya maganganun a raina, na samu wasu amsoshin, amma kuma amsoshin sun kuma tayar da wasu tambayoyin. Menene gaskiya dalilin rabuwar iyayen sultan? Menene dalilin da yasa soyayyar mahaifinsa ta koma kiyayya a lokaci daya? Menene kuma dalilin da yasa ake boye labarin mahaifiyar Sultan ba'a so kowa ya sani? Na tuna da labarin da Sultan ya bani na amsar da Yaya ta bashi sanda yayi mata irin wannan tambayar 'to protect the family name' but what kind of protection?
Follow me on wattpad @maman_Maimoon

Episode Seventy Four : The Cook

Ranar ba'kin gidan mu suka zo yi mun sallama, daga 'yan 'yalleman har 'yan niger duk gobe kowa zai tafi gida. Zuwan su ne ya saka na manta da hirar mu da baba gaji. Nan take 'yammata na suka fara hidima dasu, sun iya aiki sosai dan ba sai bace ayi abu ba zanga kawai anyi, da kyar na samu kebewa da Amina nace mata " Amina kin kira Ibrahim din kuwa?" Ta dauke kanta ta bata rai tace "na kira shi once, bai dauka ba, ni kuma na rabu dashi" sai naji ba dadi a raina, it has been three days, ya kamata ace an san halin da yake ciki. Nace "please Amina ya zaki yi haka, gashi gobe zaki tafi and I don't know who else zan saka" ta daga min hannu tace "relax, ba tare zamu tafi dasu ba, Mommy tace in zauna anan for the time been" nayi ajjiyar zuciya nace "please Amina, kema kinsan ai ranar in kika kira shi ba zai dauka ba amma yanzu at least na san ya dan huce zai saurare ki" ta kara tabe baki tace "I will try amma ban miki alkawari ba, in naga yana daga min kai I won't go around chasing him" na yarda a haka. Sai bayan zuhr Sultan ya dawo, tun daga waje yaga motocin gidan mu dan haka sai ya zagaya ta baya ya shiga direct part dinsa sannan ya kira ni a waya ya ce min ya dawo. Ina shiga palon sa na ganshi a zaune ya kunna kallo da remote a hannunsa, na tsaya daga bakin kofa nace "sannu da zuwa" ya juyo yana kallona sai ya nuna min cinyarsa yace "come here" na makale kafada, yace "to ni ma bana cin mike, bana amsa gaisuwa daga nesa" na karasa shigowa na rufe kofar nace "Sultan baki ne a gidan, inna zo nasan ba bari na zakayi in fita da wuri ba" ya bata rai yace "da ni da bakin waye yafi muhimmanci?" Ban bashi amsa ba nace "amma ai su tafiya zasu yi ko? Sallama suka zo yi mana fa" yana kallona kasa kasa yace "OK, just a kiss, shikenan" na karasa gurin sa na tsaya, ya nuna min lips dinsa yace "here" na matso da fuska ta dai dai tasa, ina kallonsa har da lumshe ido wai shi nan za'a yi masa kiss, na cije shi kadan akan hanci na juya da gudu, ina jinsa yace "ouch, zan kama ki ne" na juyo nayi masa gwalo na fice. Sai bayan la'asar baki na suka tafi, sai a lokacin na koma gurin Sultan na tarar yana lunch din da na kai masa tun dazu, nace "au baka ci abincin ba sai yanzu?" Yace "bayan yau wulakanta ni kike yi dan kinga 'yan gidan ku ko? Tun dazu nake jiranki kizo muci abincin shine kika ki zuwa ko?" Na karbi cokalin a hannunsa nace "am sorry, ban dauka zaka jira ni ba, nasan halinka da abinci" na diba na fara bashi a baki, yaji dadin hakan sosai, na tambaye shi "how are the kids?" Take naga fuskarsa ta haska da murmushi yace "they are fine, suna ta tambayarki, wai suna so su shirya mana surprise party" nayi dariya nace "then it is no longer surprise tunda sun gaya maka" yace "kuma bayan gaya min din da akayi har list aka bani na abubuwan da suke bukata for the party" ya dauko wata takarda muka fara karantawa, tarkace ne nasu balloon da ribbons, har da cake, wai suna so a jikin cake din a rubuta 'happy marriage life mom and dad, we love you' muka yi ta dariya nan na kara abubuwan da basu saka ba. Bayan Sallar magrib sai ga Hafsat da Zayed da little khairat suma sunzo mana sallama zasu koma England. A palon Sultan muka zauna dasu muna ta hira. Hafsat da tsegumi har bedroom din sultan ta shiga, yace "Hey lady, me zaki yi min a daki ne? Baki san cewa bedroom dina sirrin mu bane" ba tare data kalleshi ba tace "koma menene ba sirri ba sai na gani, nasan babu abinda zan tarar sai kazanta" ta shige ciki, ta dade kafin ta fito, knowing halin Hafsat nasan har toilet ta shiga, tana fitowa Sultan yace "kin dau bashi, duk sanda naje gidan ku sai na shiga dakinki" mu dai dariya muke musu ni da zayed. A nan Hafsat take gaya min in sun koma England zayed zai dauki leave zasu je saudiyya, dan 'yan'uwansa da yawa basu santa ba ga kuma khairat itama babu wanda ya santa. Tare muka yi dinner ina ta mamakin yadda sultan yake sakewa da zayed duk sanda suka hadu, dan yadda yake yi masa ko yaya Walid da suka saba sosai baya yi masa haka. Sai very late sannan suka tafi, ji nayi kamar zanyi kukan rabuwa da Hafsat tunda ban san kuma ranar da zamu sake haduwa ba in dai ba wani abun ne ya tashi ba. Sai bayan mun kwanta bacci sannan na fara bitar hirar mu da baba gaji, na kalli Sultan naga idonsa a rufe amma nasan ba bacci yake ba, nace "Sultan" yace "uhmm" nace "will you one day like to see your mother?" Yayi shiru kamar baiji abinda nace ba, na daga kai na kalleshi sai naga idonsa a bude yana kallon ceiling ya jima a haka sannan yace "No" da mamaki nace masa "why?" Da murya mai kaushi yace "I don't need her now. Sanda nake bukatar ta a lokacin ta ajiye ni ta tafi. I wish her happiness a ko ina take a duniya but I don't wish to meet her. Me yasa kika tambaye ni akanta yanzu?" Nayi tunanin in gaya masa labarin ta da na samu sai kuma bayi tunanin bani da wata concrete magana for now, zan gaya masa amma sai na sami more answers, nace "babu komai, kawai dai naji ta fado min a rai ne" ya kara jawo ni jikinsa yana saka fuskarsa a wuyana yace "forget about her kinji, itama yanzu ta manta dani, am sure ta haifi wasu 'ya'yan yanzu. I have you, I don't need anybody else".
Washegari ina palo da baba gaji naji sallamar Amir, baba gaji tace ya shigo, ya shigo muka gaisa nace masa " wato kwana biyu ko leke ko" ya rike baki yace "ni da aka kora ina zan kuma dawowa" muka yi dariya yace "tare da bakuwa muke" na kara fadin murmushina nace "really? Tana ina" ya dan sunkuyar da kansa kasa yana shafa kai yace "Amira ce" take murmushin fuskata ya bace, yace "ta gayamin duk abinda ya faru tsakanin ku, tace ta turo miki message cewa tana so ta zo amma baki ce mata komai ba, shine nace bara in kawo ta in taya ta bada hakuri, she made a mistake na sani amma..." Na dakatar dashi nace "it was not a mistake. Mistake shine abinda zakayi daga baya kayi realising cewa kayi ba dai dai ba sai ka bada hakuri kace kayi mistake, amma ita bata yi realising ba har sai da Allah ya tona asirinta, dan haka va wai nadama tayi ba kawai dai an riga an kama tane babu yadda zata yi" ya gyada kai yace "na fahimce ki, amma ina so ki saurareta, ta baki labarin in her own version, na tabbatar zaki yafe mata" na daga kafada nace "ni ai already na yafe wa Amira, abinda bazan yi ba shine ba zan kuma bata space a rayiwata ba ballantana har ta kuma cin amana ta" yace "OK let me call her in now" ya tashi ya fita sai gasu sun dawo tare, fuskarta tamkar ba Amiran dana sani ba, idanuwanta sunyi circle din baki alamar kuka da rashin bacci, bakinta duk a bushe, bana jin ko mai ta shafa ballan tana kwalliya. Tana shigowa nace da baba gaji ta bamu guri, sai da ta fita ta rufo kofar sannan Amira ta karaso inda nake zaune, nace "sannu da zuwa" bata amsa ba sai ta durkusa a gaba na, hawaye ya fara bin fuskarta tace "Moon dan Allah ki yafe min abinda nayi miki. Dan girman Allah. Wallahi nayi nadama ba tun yanzu ba. Son zuciya ne ya saka ni nayi abinda nayi da kuma sharrin shaidan. Tun da dadewa nake so in gaya miki amma na kasa gaya miki saboda bana son ki yanke friendship din mu" nace "Amira ni na yafe miki already, saboda ni ma ina da laifuffuka na a gurin ubangiji kuma ina son idan na nemu yafiyarsa ya gafarta min. Amma hakan ba yana nufin cewa we are back to friends zone bane ba" ta goge hawayen fuskarta tace "ni hakan ma yayi min. Dama can I never deserve to be your friend. Tun sanda aka kawo ku muna jss 1 naga kin burge ni, 'yar karama dake gaki kyakykyawa, sai daga baya na fahimci how smart you are, duk mun fiki girma da shekaru amma kin fimu kokari. I wanted nothing more than to be your friend. Ban dauka zaki kula ni ba, na dauka zaki zamo mai girman kai amma sai naga ba haka bane ba, naga kina da saukin kai fiye da duk sauran mates din mu. Moon you will never know how much I admire you. Sanda aka yi hutu kika bani address din ku nazo sai naga how rich your parents are, you have everything, you are everything I wanted to be. You were my model, I always wanted to be like you but I couldn't. Lokacin da su Ibrahim suka zo, you guys were laughing at them. I liked him kallon farko da na yi masa. In kuna yi masa dariya har haushin ku nake ji a raina amma ba zan iya fada ba saboda bana so in bata miki rai. I didn't know love then, kuma ko da na sani ma I doubt in zan iya fada masa ina son sa. Ban san ya akayi ba kawai sai na ganku tare a matsayin saurayi da budurwa. I was angry as to how can you have everything I wanted and then still have him? Amma babu abinda zan iya yi akai dole na hakura nake kallon ku, lokacin da ya fara yi min lessons din musabaka lokacin soyayyarsa ta kara karuwa a zuciya ta, I guess na kasa boyewa ne har na nuna masa, abinda yace min shine ya daina yi min lesson din sai dai in zamu ke zuwa tare dake, I was so pissed up nace na fasa musabakar ma gaba daya, yaje ya gaya wa pc ta kira ni nace eh na fasa, maimakon ya lallasheni ya bani hakuri sai cewa yayi da pc ai kema zaki iya, a rabu dani a saka ki kiyi kawai. Ranar ne na fara gaya miki maganganu kuma daga baya sai naji babu dadi, it is not your fault that you get everything I wanted. It was not your fault that he loves you not me. Kuma shima banga laifinsa ba, dan babu wanda zai samu someone like you ya ajiye ya dauki someone like me. It was my fault that I couldn't control my heart. Bayan nan yazo har cikin class ya fada a gaban kowa cewa baya so na, duk da dai 'yan ajin basu san dawa yake ba. Na fahimci cewa ya gaya miki abinda ya faru tsakanin mu, amma ga mamaki na sai naga hakan bai sa kin chanza min komai ba, saboda ke din ta daban ce. Daga lokacin har adduah na ringa yi ina rokon Allah ya cire min shi daga raina. Bayan munyi graduation ne rannan kika gaya min cewa he left you sai nan gaba zai dawo, a raina nayi adduar Allah yasa ba zai dawo ba saboda bana son abinda zai bata kawancen mu dake. I never thought nima zan sake ganinsa. Kawai rannan bayan kun tafi England sai gashi a kofar gidan mu, na dawo daga makaranta kawai na ganshi a tsaye yana jirana. He looks so happy to see me, and my stupid heart thought cewa guri na yazo, it was very stupid of me to even think that. I was so happy. So excited. Sai bayan da na shigar dashi gida muka gaisa sosai sannan ya gaya min cewa ke yake nema. It hurt me so much then. I don't even know ma yaushe na kirkiri karyar cewa kinyi aure na gaya masa. Sai da naga expression din fuskarsa sannan na fahimci me nayi. It was already too late to gi back, maganar ta riga ta fito babu yadda zan yi in mayar da ita" ta fara kuka sosai "nasan cewa abinda nake ba dai dai bane ba amma na kasa dawowa baya in warware karyar da nayi. Na saka akayi min fake IV na kai masa. I kept telling myself cewa it will be better in na raba ku din yadda ba zan ke ganin sa ba ballantana har in bata friendship din mu dake. I kept telling myself cewa you will soon forget about him. Wani lokacin kuma in gayawa kaina cewa ko na bar ku ma ba lallai bane daddy ya yarda ya aura miki shi. Ita karya in ka yi ta sau daya to ka ringa karawa kenan kullum saboda kayi covering waccan da kayi. Haka na ringa yi masa karya akan ki. At first na yi masa karya ne saboda I was angry cewa baya so na, daga baya kuma na cigaba dayi masa karya saboda in boye waccan karyar da nayi dan inye saving friendship din mu. Abinda nake so ki fahimta shine, ban raba ki da Ibrahim saboda ni ina so in same shi ba, a'a na raba ku ne saboda ina gudun in yi asarar kawancen mu" na goge hawayen da yake ido na. Yana daga cikin ginshikin imani mutum ya zama mai yarda da kaddara, mai kyau ko marar kyau. Amira have always been a good friend to me. Ina jinta a raina kamar 'yar'uwata. Na mika mata hannu nace ta tashi ta zauna akan kujera. Ta zauna tana ci gaba da kuka. Nace "it's OK. Komai ya wuce in sha Allah" Amir ya taso ya dawo kusa da ita ya zauna yace "To kuma kukan na menene, ba tace ta yafe miki ba? Sai kinje ki sa wa kanki wani ciwon kuma". Muna nan tare dasu Sultan ya shigo, ya rike kugu yana kallon su "shikenan kuma mutum bashi da damar ya dan fita waje sai an zo an cika masa gida. Dole ma muzo mu bar kasar nan wallahi". Sam sultan bai nuna wa Amira yasan wata magana a tsakanin mu ba, ya zauna ya saka su a gaba ita da Amir da tsokana nima ina tayashi. Muna tare dasu har aka kawo lunch aka kai dining na yi musu bismillah, Sultan ne na farkon tashi wai dama yunwa yake ji, a raina nace 'acici'. Muna shiga na dauko plates da spoons, sultan na fara serving, na duba naga farar shinkafa ce da miyar kaji, sai brown macaroni. Na zuba masa shinkafar ina cikin zuba masa miyar naji yace " khulsum bata tafi ba kenan" na tsaya da abinda nake ina kallonsa naga bani yake kallo ba abincin yake kallo, na bata rai nace "me kace?" Still bai kalleni ba yace "khulsum nace bata tafi ba kenan, this is her cooking" na ajiye serving spoon din hannuna na rike kugu ina kallonsa nace "ya akayi ka san cewa this is her cooking?" ya jawo warmer din ya nuna grated carrot din da aka barbada akan shinkafar yace "this is her signature, in dai tayi abinci tana barbada carrot akai as her signature" sai a lokacin ya dago kai yaga yadda na rike kugu na hade rai ina kallonsa yayi dariya yace "common, da ina yawan cin abincinta, she is a chef, the carrot is just her signature kamr yadda mai zane yake signing a kasan zanen sa dan ya nuna cewa shi yayi" na kara hade rai ganin yayi comparing ita as a chef da shi as an architecture, ya gane abinda nake nufi yayi sauri ya gyara yace "ko kuma yadda likita yake signing a kasan prescription dinsa dan asan shi ya rubuta" a zuciye na jawo plate din abincin da na zuba masa na juye a cikin warmer din na kwallawa Hassana, daya daga cikin yarana kira, tana shigowa nace duk ta kwashe abincin ta tafi dashi gurin su su cinye. Na juya na kalli Amir da Amira da suka saki baki suna kallona kowa da cokali a hannu, sultan mamaki ne ya hana shi magana, sai daga baya yace "common Love, yunwa fa muke ji, yanzu kin bayar da abincin me zamu ci kenan?" Nayi hanyar kitchen ina cewa "I will cook you something" ya taso ya biyo ni, yace "yaushe kika iya girkin?" Nace "I will learn today" ina shiga kitchen na jawo apron na saka na kunna gas na dora tukunya da ruwa. Sultan ya karaso kitchen din ya rungume ni ta baya yace "relax, am sorry, dan nace na gane girkin ta doesn't mean anything, nasan ta iya girkin amma ban taba son taba, nasan baki iya girkin ba amma am head over heal in love with you. Ki bari Amir ya fita ya sami mana abinda zamu ci" Amira ce ta shigo kitchen din ya dan sake ni kadan ta karaso tace min "me za'a dafa?" Sultan yace "no ku bar shi kawai bara mu fita mu siyo" tace "ai kafin ku fita ku dawo ma yaci ace mun gama koma menene, yadda gidan nan yake da nisa zuwa gate ma aiki ne" ya dan tsaya yana kallona, na daga kafada yace "OK, cook us something simple" yana fita Amira ta bude freezer, ina kallonta tana fitowa da abubuwan da take bukata, ta miko min nama tace "wanke wannan" ina tabawa naji shi duk kankara nace "yayi sanyi da yawa ba zan iya tabawa ba" ta tsaya tana kallona kawai, sannan ta dauki naman ta zuba masa ruwa ta koma tana gyara kayan miya. Na dauko waya ta na kira Mommy, tana dauka na shagwabe murya kamar zanyi kuka nace "Mommy ban iya girki ba" tace "au ke da baki san baki iya girkin ba sai yanzu? Babu yadda banyi dake ba akan koyon girki ki ka ki, dama nasan wannan ranar tana nan zuwa. Yanzu me kike so inyi miki?" Nace cikin sanyin murya kamar abin tausayi "Mommy Asma'u zaki bani" tace "ita ma'un an gaya miki toy ce da zance kawai na baki ita? Besides nima ina bukatar ta tunda office aiki yayi mana yawa ba zama nake a gida sosai ba. Cooking classes zaki shiga ki koya ki ringa yi da kanki. Su yaran da aka baki duk basu iya girkin ba suma?" Nace "Mommy ni ba zan iya cin abincin su ba, Sultan ma haka. Professional cook muke nema. Kuma Mommy wallahi sultan ba zai barni in shiga cooking class ba" tace "to ai kuwa kwa kare da siyan abinci" nace "Mommy please" ta dan jima sannan tace "zan tambayi ma'un inji ko zata zo, amma da sharadi, in tazo zama zaki ke yi kuna girkin tare da ita kina koya, yaran naki suma duk su ringa koya, duk lokacin dana bukace ta zan aiko ta dawo gida in baki koya ba kafin nan matsalarku ce" cikin murna na fara yi mata godiya, bata saurareni ba ta kashe wayar. Zuciya ta naji tayi min fari tas, duk wani takaicin khulsum da girkin ta na manta dashi. Nima zan koyi abincin nan dai in huta.


Episode Seventy Five : The Emir

Bara mu

Please Login or Register in order to submit comment