Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da Sultan ba. I terrible miss him. Kullum zan budo number dinsa a waya ta inyi ta kallonta. Duk sanda kuwa naji kira ya shigo waya ta sai naji gabana ya fadi ina tunanin ko shine amma shiru makatau. Last seen dinsa a Whatsaap shine a day to barowa ta America. One week ya wuce, two weeks ma haka. Ni kadai nasan yadda nake ji a zuciya ta tunda babu wanda zan gaya wa in ji dadi. Har aka yi mana fixing ranar defence na project din mu. Meaning mun gama karatu kenan. Na zama busy sosai ina tsara yadda zan presenting project dina, neurology zan fara sannan a week later in yi psychology. Duk sanda tunanin Sultan ya dame ni sai in dauko waya ta inyi ta kallon pictures din mu, wani inyi kuka wani dariya. Ko na dauko waya ta zan kira shi sai in tuna abinda ya faru sai in kashe, kunyarsa nake ji sosai. Ana gobe zanyi defense dina daddy ya tara mu a palo yayi min addu'ah sosai ta samun nasara, dan it is not easy kayi facing professors komai ilimin ka kuwa. Alhamdulillah washegari nayi defense dina successfully na gama. Sosai akayi celebrating a gida amma ni sam hankali na ba'a kansu yake ba dan yau kam da gaske nayi missing sultan saboda kusan tare dashi muka rubuta project din. Ranar har Hafsat tazo gida ita da Zayed sun kawo min gifts. Sai da muka kebe ni da Hafsat sannan ta tambayeni "so... Do you call him?" Na girgiza kaina da sauri, sai kuma hawaye suka fara zuba nace "I can't" ta gyada kanta tace "He is stronger than you, he is suppose to call you first in dai har yana so ku dawo tare" na gyada kaina ina goge hawayena, sai kuma ta rungume ni tana dan bubbuga bayana a hankali, tace "be strong little sister, am sure God have something special for you" Ranar da daddare na dauki wayata da niyyar kiran Sultan ina ajiyewa ya kai sau goma, daga karshe dai na kashe wayar na jefa a cikin jaka na rufe. Har na kwanta kuma sai na tashi na dauko camera ta na kunna videos din da nayi mana ana gobe zan taho, wajen horse race da inda ya hau dutse a guje ya fada cikin ruwa. Kuka na zauna sosai nayi.

Washegari muna zaune palo yaya Walid yace "Wai Moon ina saurayin nan naki da kuke yawan waya dashi? Tunda kika dawo daga America naji shi shiru" Mommy tayi sauri tace "kaima dai Walidi ka fada, nima naji shiru, kinsan dai almost karatunki ya kammala, daga miki kafar da baffa zai yi kawai shine idan ba'a gaya masa kin gama ba, shima kuma delay din da za'ayi kawai zuwa sanda result dinku zai fito ne. Gara kisan me kike ciki Moon. Nima kuma office din mu a Abuja sun fara damuna akan lallai ya kamata in koma aiki in ba haka ba sai dai inyi resigning, so nake muyi magana da daddyn ku kawai mu koma gida haka nan. Faruk ne kawai bai gama karatunsa ba shima kuma zai iya zama shi da daddyn ku zuwa sanda zai karasa" ina sauraronta ina lissafin in dai muka koma Nigeria to ni kam na kade har ganyena. Masifar Hajja da jarabar Munir kadai ta ishe ni. Su familyn mu gani suke yi kamar nayi girma da yawa, musamman yanzu dana gama karatun likita, gani suke ya za'ayi ace har na zama doctor babu aure bayan a zahirin gaskiya am just 22 years, 16 years na gama sec sch yanzu kuma after 6 years na gama first degree na. Har dare ina ta lissafin what to do. Na dauko report dina na psychology ina karantawa, it contains everything about Sultan, sai kawai naji ya kamata in dan kara masa armashi, kamar make-up. Na dan yi tunani kadan sai na mike na tafi part din su yaya walid, na debo kayan drawing dinsa na dawo dakina. I am not a good artist but I am going to try my best. Na zauna a nutse na fara zane, sai da na dauki 3 hours sannan na gama, na tafi palo na dauko fresh milk na dawo na zauna ina duba zanen da nayi. Sultan ne a tsaye, da sleeveless riga a jikinsa da three quaters wando. Ya zura hannayensa a aljihunsa ya dan juya kansa yana kallon side daya. Fuskarsa babu fara'a. Yayi kyau sosai kamanninsa sun fito dan duk wanda ya sanshi in yaga zanen zai gane shi. A jikinsa nayi rubuce rubuce akan behaviours din sa da mutane suka san shi dasu. The drunk, arrogant spoilt rotten prince. Daga bayansa sai na sake wani zanen something like his shadow, a jikinta kuma sai na yi rubutu kanana akan dukkan abubuwan da nayi learning na kyawawan halayensa, saboda yawan abubuwan da na rubuta har sai da gurin ya cika na rubuta etc. Kuma wadannan iyakacin abinda na sani ne kawai, dan na tabbatar da akwai wadanda ban sani ba. Na kalli zanen inajin wani dadi har cikin raina, ina ma mutane zasu ga wannan zanen nawa? Tabbas da sun so sultan kamar yadda nake son sa. I wish one day I will be able to show it to the world. Amma bazan yi hakan ba sai da amincewar Sultan. ( naso ace na iya zane dana zana muku. Lol ).

Ranar da zanyi presenting ita ce kuma final day dina a Oxford. Tun safe na shiga makaranta ina ta practicing abinda zanyi. A ka'idar makarantar malamai kadai ake presenting to, duk sauran guest suna waje. Ana kira na na shiga na kafe zane na a jikin board. Tun daga yadda malaman suke kallon zanen nasan ya samu karbuwa, wannan shi ya kara min confidence. Katardun hannuna na ajiye a gefe, i don't need them, I am going to talk about Sultan and I know him like the back of my hands. Nan na fara kararo bayani akan rayuwarsa, yadda yake rayuwa with two personalities, as a hero and as a villain. Tun da na fara maganar murmushi ne a fuskata. Ina gamawa daya daga cikin lecturers din yace min "who is this man to you?" nace mishi "he is my boyfriend sir" gaba dayan su sai da sukayi murmushi.

Ina fitowa da gudu na karasa gurin su mommy na rungume ta ina murna, nan muka ta daukan pictures dan har daddy yazo gurin duk suna waje. Muna cikin haka na hango motar Sultan, gaba na ne yayi wata irin faduwa, mutun na gani a tsaye a jikin ta yana kallon inda muke, Amir, nayi sauri na dauke kaina kamar ban ganshi ba amma kuma duk hankali na ya tafi gurinsa, ko tare suke da Sultan? Har muka gama yana nan a tsaye a inda yake, an kawo motoci zamu tafi nace musu "ku tafi kawai ni zan taho daga baya, akwai friends dina da nake so muyi sallama dasu" daddy ya kalleni da tsokana yace "friend ko boyfriend" na shagwabe fuska ina bubbuga kafa nace "daddy" yayi dariya yace "is alright, a driver will come back for you". Suna tafiya na juya na tafi gurin Amir. Nayi masa sallama, ya amsa fuskar sa da murmushi. Yana sanye da geans da sweater ya saka hannunsa a aljihun sweater kamar mai jin sanyi. Yace "can I talk to you for a minute?" Ya fada yana nuna cikin motar, Na girgiza kaina dan na fahimci shi kadai ne babu Sultan nace "akwai gurin zama a can, mu karasa sai mu zauna" ya daga kafada dan ya gane bazan shiga motar ba. Muka danyi tafiya kadan sannan muka karasa wata rumfa da akayi dan students, na jawo mana kujeru muka zauna. Sai a lokacin na kare masa kallo, baki ne amma very handsome, yana da manyan ido, fuskarsa irin mai natural murmushin nan ce. Na gaishe shi ya amsa. Sannan ya fara magana "kin ganni a England ko? Na rasa yadda zanyi muyi magana ne shi yasa dole na taho nan" nace da sauri "wait, kana nufin takanas ka taho daga Nigeria saboda kayi magana da ni?" Ya gyada kai yace "Sultan is my only family, I can do anything for him. I guess ya gaya miki labari na ko?" Na gyada kai, yace "you are very special to him you know, Sultan baya magana akan kansa amma daga dukkan alama kinsan komai akansa. Sultan mutum ne na musamman wanda ni kaina bazan iya kwatanta miki shi ba. Tunda ya hadu dake ya soma chanzawa. Ya daina shiga trouble, I was happy for him, very happy. But now...... " ya dago yana kallona, he looks very sad, ya ce "what happened?" Nace "bai yaga maka ba?" Ya girgiza kai yace "the fact that bai gaya min mai ya faru ba shi yafi daga min hankali. Bai taba boyemin wani abu ba. Amma yanzu all he keeps saying is that he is a monster, and that he is taking himself as far away from you as possible. Ranar da yace min zaku dawo England na kira shi sai yace min yayi missing flight, that something he never did, Sultan mutum ne mai kula da time, sai yace min kuma ke kin taho, daga nan na gane something is wrong saboda ba zai taba barin ki ki taho ke kadai ba, in ma missing flight dinne sai dai kuyi tare. Daga nan duk sanda na kira sai in tarar still yana America. Rannan Steve ya kira ni yace police sun kama sultan ya kwana a station, anan nake tambayar Steve me yake faruwa yace min everything is wrong, bai san me ya faru ba but yana ganin it has to do with you. Bayan an fito dashi daga station na kira nayi2 dashi ya gayamin me yake faruwa yaki. Yace he is never going back to Nigeria and he is also not coming to England. A america zai zauna. Tun daga nan na yi tunanin dole in neme ki, yaki ya bani number dinki and that your ugly faced friend itama taki bani. Things are going very badly for Sultan, dole na taho England gurin ki. I need your help" na runtse idona hawaye yana sauka akan kuncina. Yaci gaba da cewa "he is back on the bottle. Kin san rabonsa da alcohol?" Na girgiza kaina yace "tun ranar da kuka hadu a Hilton. Ranar sunyi rigima da Takawa as usual, he got drunk and I had to go out and leave him a gida, after he sober up shine ya fita kuka hadu. He told me that he got something better than alcohol, he said he got love" kuka nake yanzu sosai, ya cigaba "please Maimunatu dan girman Allah, call him" ya fada shima kaman zaiyi kukan, nace "but why should I be the one to call him? Mai yasa shi ba zai kira ni ba?" Yayi murmushi yace "because you are the light to his darkness"



Episode Forty Eight : Awkward

Ranar duk ban karasa ta da nishadi ba, today is my graduation day, I am suppose to be happy. Da naje gida ma yake kawai na ringa yi daga baya na tafi daki nace na gaji bacci zanyi. Na kwanta amma na kasa bacci. So Sultan thinks he is tough right? He thinks he can just give me up instead of facing me? Lets see how tough he can be. Wato ni nice soft one din shine Amir zai wani zo yace in kira shi ko? Na ga dai baccin ba zai yiwu ba na mike na fara abinda na saba duk sanda wani abu ya dameni ko wani al'amari ya shige min duhu, na tashi na fara gaya wa Allah. Nayi adduoi sosai akai na da kan Sultan ina nema mishi guidance na ubangiji. Sai a lokacin na fara wani tunani, addu'ar iyaye itace addua mafi inganci a gurin 'ya'ya, Sultan baya samun wannan, shi kansa ba lallai ne yana yiwa kansa da kansa addu'ar ba. Duk da dai adan zaman da nai dashi na lura baya barin sallah. Na gama adduoi na na kwanta akan sallayar nayi baccina.

Da assuba na tashi nayi sallah, har na koma zan kwanta naji still raina babu dadi, na dauko waya ta a jaka na kunna na nemo number din Sultan nayi dialing, sai da ta kusa katsewa sannan ya dauka, amma bai ce komai ba, naji takaici ya kamani, why did I even called? Na katse kiran kaman zanyi kuka. Ina ajjiye wayar kiransa yana shigowa. I let it ring. Ya sake kira naki dagawa. Message ya shigo. "Answer the call please" nayi reply "why didn't you call me sai da na kira ka?" "Am sorry, please pick up the phone" wani kiran ya shigo, it has been a month rabona da Sultan, rabon da inji muryarsa. Na dauka tare da sallama. Ajjiyar zuciya naji ya sauke. An awkward moment followed. Nace "look, idan ba zaka yi magana ba zan ajjiye wayar" a hankali yace "how are you?" sai da naji muryarsa sannan na fahimci how much I have missed him. cikin rawar murya Nace "I missed you" ya dan jima sannan yace " I have more than missed you, i have no word for what I felt" "amma me yasa baka kira ni ba? It hurt me sosai, how can you just give me up just like that?" A nutse ya fara magana "you have no idea how much I love you, do you? Bawai nayi giving up on you bane, I am a bad person Moon, You are good, more than good, bana son in bata miki rayuwarki. Ina sonki son da zan iya rabuwa dake even if it kills me, in dai har zaki samu kyakykyawar rayuwa" na katse shi da muryar kuka nace "and who says I want a good life? Huhh? All I want is a life with you. Just tell me idan har kai ka daina sona ne kawai ka gayamin ka daina min wani boye2. You keep saying you are a bad boy, you can never be good in dai har kana tunanin you are bad" yadda na rufe shi da fada ne yasa yayi shiru ya kasa magana. Nima dana gama fada na nayi shiru. Sannan nace "when are you going back to Nigeria?" Yace "I have nothing to go back to Nigeria for" nace a hankali "you can come to England, you have me here, right? Besides, ina son kazo ka gaishe da daddy" ya danyi jim sannan yace "are you sure?" Nace "yes, am sure. Kai na zaba a matsayin mijina, whether you are good or bad, kai nake so" sosai magana ta ta taba zuciyar Sultan dan har a muryarsa naji, shi abinda ya cigaba da insisting shine wai am too good for him, baya so ya sake letting dina down. Daga karshe dai na gaya masa cewa nan da about a month zamu koma Nigeria kuma muna zuwa aure za'a yi min da Munir, whom I despise, dan haka zabi ya rage nasa, is either ya zauna a America ya cigaba da playing bad boy role dinsa ni kuma a aura min munir ko kuma ya dawo yayi facing daddy ya karbi aurena. Ina fadin haka na katse wayar, ko minti daya ba'a yi ba ya kira, na katse kiran na kashe wayar gaba daya. Na san na kunna masa wuta. Dole ya dawo cikin sense dinsa yasan abinyi.

Ranar da yamma naje na samu mommy a dakin daddy tana gyara masa kaya. Na zauna a kusa da ita nace "Mommy wannan da kuke zance ke da yaya Walid rannan, sunansa Abbakar, dan garin Abuja ne, he is an architecture, iyayensa manyan mutane ne sosai a garin abuja. Ina son kiyi wa daddy maganar sa dan cikin satin nan na keso zaizo England ya gaishe da ku" mommy ta kalleni fuskarta kamar gonar auduga tace "kai Alhamdulillah, he is your final choice kenan ko?" Na gyada kai tace "Allah ya kawo shi lafiya" nace "Amin" har na mike sai kuma tace "Moon, kash, kinga har naso in manta, daddynku gobe zai yi tafiya, president ne ya tura shi wani summit a South Korea kuma zasu dan jima a can, dan yace ma maybe sai dai mu hadu a Nigeria tunda mu zamu tafi da wuri kinsan maganar bikin Nuraddeen ya tashi" na danyi jim ina jin babu dadi, dan da karfi na nazo so nake ayi wacce za'a yi a cikin satin nan a gama. Nace "OK, shikenan sa hadu da daddy a Nigeria, in yazo kawai sai ya gaishe ki ke" mommy tayi dariya, na tsaya ina kallonta dan ni banga abin dariya a cikin magana ta ba, tace "Moon kenan, ina kika taba ganin saurayi yazo ya gaishe da uwa?" Sai da ta fada sannan nima nayi dariyar abin, tace "kawai kice masa yayi zamansa a Nigeria za muzo mu same shi" nace "ai baya Nigeria yana America, dama munyi dashi ne zai biyo ta England sannan ya karasa Nigeria" mommy tace "babu wani abu ai, yazo kawai ku gaisa, in yaso sa hadu da daddyn ku a Nigeria" daga haka na koma part din mu ina lissafin ba haka naso ba ni kam. Amma Allah yasa jinkirin ya zamar mana alkhairi. Dan nasan ba karamin takaici zan sha ba a wajen bikin nuraddeen, a lokacin kowa zai san na gama makaranta.

Sai da daddare na kunna wayata. Messages ne suka fara rige rigen shigowa waya ta, nace a raina 'waya gaya maka barno gabas take ne da, dan kaga ina wani lallabaka shine zakake daga min kai. Na fara karantawa "shine kika kashe wayar ko?" "Please karki kuma mentioning wani munir or else.... I don't even know what I will do" "OK, i will come, pick me up in the airport tomorrow morning" nayi murmushi a raina nace 'na gano lagonka ai yanzu, kishi.

Amina ce ta shigo tanata kumbure2, nace "ke kuma ke da wa kike bata rai" tace "wai Nigeria zamu tafi bikin Nuraddeen, ni wallahi banson zuwa, ina zuwa gida yanzu zancen aure za'a fara yi min, duk an bi an saka min ido a gida kamar ni nafi kowa girma" dariya nayi sosai nace "that makes the two of us, at least ke ba'ayi miki mijin bama, ni yana nan an ajiye min dan haka bani da bakin cewa ai mijin ne bai zo ba" ta zauna a kusa dani tace "yanzu muyi shawara, ki lallaba mana mommy ta bar mu anan, sai mu zauna a gidan Hafsat su suyi tafiyarsu" na harare ta nace "you are joking, right? Mommy n ce zata tafi ta barmu a gidan Hafsat? Ai in mafarki kike ma yanzu ki farka" ta sake bata rai "to ni yanzu ya zanyi, ni ba samari nake yi ba kema kin sani, kuma ni gaskiya bana son a yi min auren family wallahi, ni nafi son in samu miji na da kaina wanda nake so shima kuma yake sona" murmushi nayi jin ta ambaci kalmar so, tace "this is not a laughing matter oo, ke ma fa ba son munir kike ba na sani" nace mata "wai waye yake maganar wani munir ne dan Allah? Akwai wanda zai zo kasar nan gobe, shine wanda zan aura, zan hada ku ku gaisa" tace "kina nufin baffa zai bari? Duk wannan zaman jiran naki da munir yayi?" Nace "matsalarsa ce kuma wannan, babu wanda ya matsa masa yace lallai sai ya jira, ni dai abinda na sani shine baffa yace in na gama karatu ban sami miji ba za'a hada ni da munir, to na samu, babu sauran maganar munir kuma".

Sai da nazo kwanciya bacci sannan na kira sultan, bugu daya ya dauka nace "na dauka kayi fushi ai" yayi ajjiyar zuciya yace "ni na isa? Bayan kinsa yau na wuni da waya a hannuna saboda ina tsoron kar in ajiye ki kira ban gani ba" daga nan na bashi labarin cewa ba zai samu ganin daddy ba sai nan da kamar 3-4 weeks a Abuja. Muka gama plan din zuwansa gobe, ban ankara ba kawai sai gani nayi har karfe biyun dare tayi muna ta hira ba tare da lura da time ba.

Washegari ya kira ni ya gaya min sun taso. Sai a lokacin naji gaba na yana faduwa, can I really face sultan? A wayar ma da yaya ballantana ido da ido. This is going to be very awkward. Nayi wa kaina alkawarin na daina munafuntar iyayena dan haka na tafi gurin mommy nace mata "Mommy Abdallah yau zai zo, kuma yace yana so inje in dauko shi a airport" tace "to shikenan ai babu wani abu, sai ki dauki driver ya kaiki. Allah ya sa albarka a ciki" nace "Ameen, nagode mommy" wannan shine abinda muka yi lacking da a relationship din mu, albarkar iyaye, ko da yaushe in iyayenka suna saka maka albarka to ba zaka taba tabewa ba. Na rasa inyi kwalliya ne ko kar inyi? Wanne kayan zan saka? Karshe dai na gayawa Amina nace dan Allah tazo ta rakani, ina ganin kamar in tare muke kunya ta sata yi sauki. Amina ce ta matsamin wai lallai sai nayi kwalliya, wai ai ba haka ake zuwa taryan saurayi ba, ita ta dauka wani sabon saurayi ne, bata san Sultan babu abinda bai sani nawa ba. 😂. Sai da na nemi Hijab din da yafi kowanne girma a cikin hijabai na sannan na saka. Tsaki Amina tayi tace "wallahi baki isa ba, koni da na girma a 'yalleman ba zan saka wannan hijab din inje gurin saurayi ba" ta dauko min gyale nima nace bata isa ba, a karshe dai wani hijab din na dauko wanda bai kai wancan girma ba na saka. Muka yiwa mommy sallama muka tafi. Karfe 12 jirgin su ya sauka. Ni dai tunda naji announcement na sunkuyar da kaina kasa. Can naji Amina tace "gashi nan ya taho" ban dago kaina ba nace mata "ya akayi kika san shine?" Tace "ko yadda yake kallonki ma ai dole a gane. Kai amma fa ya hadu, a ina kika samo shi? Dan Allah ki samo min irinsa nima". Sallamarsa ce ta hana ni karasa kai mata dukan da nayi niyya, ai babu shiri na juya baya na, ga mamaki na sai naji yana dariya, Amina ma ta biye masa suka yi tayi, yace "chafdi, kice akwai rigima kenan" Amina tace "ba karama ba kuwa, kaga kuma yadda ta zauna take ta koda min kai? Wai kyakykyawa, ga ilimi da hankali, shine ta dauko ni wai lallai sai nazo na ganka" dukan da nayi niyar yi mata dazu shina karasa yi mata yanzu, ta matsa daga kusa dani tana dariya, shi kuma ya matso har sai da naji dumin numfashinsa a jikina "please ki juyo mana in ga fuskarki, you have no idea how much I have missed you" ya ga bani da niyyar juyowa sai ya zagayo, ai muna hada ido nayi sauri na rufe fuskata da hannayena, nima kuma zuciya ta tana son ganin tasa fuskar daurewa kawai nake yi. Wayyo ni kam naga ta kaina. Dariya suke yi min sosai shida Amina. Lallai namiji bashi da kunya, wato shi ko a jikinsa ko? Da sauri nayi gaba na tafi gurin motoci, ina zuwa na shiga na zauna. Anan na samu damar kallonsa kafin su karaso, ya rame, ya tara gashi a fuskarsa but he still looks more handsome to me than duk mutanen da suke gurin. Suna tafiya shida Amina tana ta zuba masa zance, Allah ne kadai yasan yawan karerayin da take shirga masa. Suna karasowa ga mamaki na sai naga ya bude wa Amina gaba shi kuma ya shigo baya kusa dani. Ai kuwa na dunkule a guri daya kamar zan shige cikin kujerar, yana shigowa ya kalleni ya kyalkyale da dariya yace "Amina juyo kiga 'yar kauyen 'yalleman" tana juyowa tace "a'a wannan ai kauyancin ta ya wuce nan, maybe daga wata rugar da bamu sani ba ta taho" ni dai ina jin su bance komai ba. Can Sultan yace "kinsan Allah, ko

Please Login or Register in order to submit comment