Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Nigeria martabar ta sai ta ragu a idanun sauran kasashe. Dan in dai suka ka.a Sadiq sai sunyi publishing a international papers cewa ga abinda Nigerian Prince yayi. Sarki ya sauke ajjiyar zuciya ya sunkuyo da kansa yana kallon malamin yace "a yi. Ni kuma nayi alkawarin zan zamarwa Sultan uwa kuma zan zamar masa uba. Zan bashi duk kannin wani gata da ya kamata iyaye su bashi. Insha Allah sultan ba zai yi maraici ba. Ina rokon Allah kuma ya dubi uzurina, ya dubi dalilin da yasa nayi haka, ya yafe min".
Kaico, mai martaba sarki babu wanda yasan gawar fari sai Allah.



Episode Eighty Two : The Light
Like I always say and always emphasize, things are not always what they seem. Duk abinda kake zargi, karka yanke hukunci a kansa sai kayi bincike ka tabbatar, duk abinda aka gaya maka akan wani indai har ba kaine da kanka ka gani ba, kar kayi saurin yanke hukunci akai, kayi bincike sosai first. Never and never judge a book by it's cover, in ba haka ba you might spend the rest of your life regretting.
How far will you go to save your family?
Hakan kuwa akayi. Daga nan sarki Abdallah ya saka akaje dakunan da khairat ta zauna aka kwashe duk kanin kayanta aka rufe dakunan. Gari yana waye wa yasa aka tara masa duk mutanen gidan tun daga kan iyalinsa har bayinsa ya ce ya hane su da ko da ambaton sunan khairat ne a gidan ballantana labarin ta ko wata magana data shafeta. A lokacin da Prince Sadiq ya tashi daga bacci jin kansa yayi fresh, babu abinda yake damunsa, kamar bashi da wata matsala a duniya. Ya danganta hakan da bacci mai nauyi daya samu. Yayi wankansa ya shirya ya tafi gurin mahaifinsa, ya tarar dashi yana cin breakfast, ya gaishe shi ya zauna gefe, mahaifin nasa kallonsa kawai yake yana studying dinsa, sannan yace "Sadiq yau baza a fita gurin abokanai ba ne?" Sadiq ya dan shafa kansa yace "Ranka ya dade yau gida zan zauna, sam yau bana son hayaniya" sarki abdallah yaji babu dadi har cikin ransa. Sadiq ne za'a ce masa ya fita gurin abokanai yace shi ya zashi ba? Sadiq din da kullum in yana gari gidan a cike yake da mutane saboda shi? Bayan ya baro mahaifin nasa ne ya tafi cikin gida gurin yaya, yana shiga palon ta yaga wani yaro yana ta kuka a hannun baba gaji, kallo daya ya yiwa yaron yaji wani irin tsanarsa a ransa, ji yake kamar ya hada daga baba gajin har yaron yayi musu duka ya kore su daga palon amma ya daure zuciyar sa ya wuce ciki, tunda ya shiga Yaya take kallonsa da mamaki har ya durkusa ya gaishe ta, ba zai iya jure kallon yaron ba dan haka ya mike ya fice, ga mamakin sa sai yaga yaron yana yunkurin zuwa gurin sa dan haka ya kara sauri ya fita in ba haka ba zai iya kwada wa yaron mari. Babu shiri Yaya ra dau mayafinta ta tafi gurin mai martaba, ta tarar har yanzu abinci yake ji ga Nani a kusa dashi, babu kishi a tsakanin Yaya da Nani dan haka a gabanta tayi magana, "Ranka ya dade me akayi wa yaron nan ne?" Ba tare daya kalle ta ba yace "Abinda yafi alkhairi a tare dashi shine abinda nayi masa" hawaye ya fara zuba a idon Yaya tace "Allah ya taimake ka ko dansa fa bai gane ba ya zakace hakan shi yafi alkhairi a rayuwarsa? Wannan ba Sadiq din mu bane ba, wani ne daban ba dan mu ba" bai ce mata komai ba, nani ta tambaye ta ta fada mata abinda ya faru, itama nanin kukan ta fara yi dan duk sun fahimci abinda mijin nasu ya aikata, nani tace "ayi mana afuwa, amma muna ganin wannan ai ba shine mafita ba, a zaunar da yaron ayi masa nasiha, asaka malamai suyi tayi masa adduoin nutsuwa, babu abinda yafi karfin addu'a, a hankali komai zai warware. Amma yanzu ba khairat aka raba shi da ita ba, rayuwarsa aka raba shi da ita gabadaya" sarki Abdallah ya ajiye chokalin hannunsa ya juyo yana kallonsu, a hankali yace "ku tashi ku bani guri" babu musu suka tashi suka bar gurin, ya jingina kansa a jikin kujerar dake bayansa, har yanzu ya kasa tantance cewa abinda yayi dai dai ne ko ba dai dai bane ba, odds din sunyi yawa, Sadiq yana da taurin kai kuma tunda yace sai yaje to sai yaje din ko me za'ayi masa, yes addua tana maganin komai amma tana taking time, sadiq ba zai jira ba. Yanzu addu'ar da zaiyi shine Allah ya karya abin wata rana, bayan komai ya lafa, yadda ko Sadiq yaje Riyadh maganar ta riga ta wuce. A ranar da yamma ya aika aka kira Sadiq, ya mika masa takardu guda uku yace "wata takarda nake so ka rubuta min, kayi copy uku, daya da larabci, daya da turanci daya da hausa" ba musu sadiq ya dauki takardar da biro ya fara rubuta abinda mahaifin nasa yake fada masa kamar haka "Bismillahir rahmanir rahim. Assalamu Alaikum wa rahmatullah. Ni Sadiq Abdallah, na saki matata Khairat Abdallah saki daya, idan ta sami miji tayi aure. Bissalam" yana gamawa yayi sauran copies din ya mika wa baban nasa, sannan yace "takardun menene wannan ranka ya dade?" Sarki Abdallah yace "sample ne na yadda ake rubuta takardar saki, zamu ajiye a fada saboda harkar shari'a" sadiq ya danyi dariya yace "sunana na gani shi yasa nayi tambayar" sarki yayi dariyar shima yace "da kai akayi sample din ai, kuma kai ai baka da mata khairat ko kana da ita?" Sadiq ya girgiza kansa yace "I never heard the name". Sarki ji yayi kamar zai yi hawaye dan tausayi.
Haka Sadiq ya cigaba da rayuwarsa, kullum yana ganin wannan yaron mostly tare da sarki, kuma ga mamakin sa sai yaji ana nuna kamar dan nasa ne, duk sanda yaji maganar sai yaji wani bakin ciki kamar ya kama yaron ya shake shi ya mutu, to ya akayi ya zama nasa? How comes? Duk sanda yayi wannan tunanin sai yaji kansa gaba daya ya to she ya kasa tuna komai, wannan shi yake kara irritating dinsa a duk lokacin da yaron yayi masa magana ballantana kuma idan yaron ya tambaye shi wacece uwarsa, sai yaji gaba daya kansa ya toshe kwakwalwarsa ta daina aiki, wannan shi yasa kullum yake kara nisanta kansa da yaron.
Present days
Sarki Sadiq ya share hawayen fuskarsa yana jin matsanancin hausin kansa, duk wannan ya faru ne sanadiyyar taurin kansa da rashin jin maganarsa da kuma kin yiwa iyayensa biyayya a lokacin da suka hana shi auren khairat, amma kuma da akwai rabon sultan a tsakanin su, duk da haka da ace yayi biyayya ga mahaifinsa da mahaifin ya nemi hanyar maslaha cikin sauki ba tare da anyi masa abin da akayi masa ba. Taurin kansa cost him 30 years of his life. Ya tuna da auren da akayi masa, a take wani daci ya taso masa a bakin sa, wannan yarinyar zuwaira ya tsane ta tun tana yarinya, sannan kuma ga abinda tayi, what kind of a father will do what his father did to him? Gashi yanzu ba shi da rai ballantana ya tambaye shi why, amma ai da akwai wacce take da rai kuma yadan da sanin ta akayi komai. Aka hada shi aure da yarinyar da an san da a cikin hayyacin sa yake ko daura masa ita akayi a kafa ba zai tafi da ita ba, gashi yanzu har 'ya'yansu biyu together. Ya mike tsaye ya wake fuskarsa a sink ya dauki towel ya goge, ya sauke ajjiyar zuciya yana kallon reflection dinsa ta mirror, he is back, shekaru basu chanja original sadiq ba, from now everything will be alright.
Yana bude kofar dakin mutanen da suke waiting room duk suka tashi tsaye suna kallonsa da mamaki, da yawa daga cikin su basu gane shi ba saboda ko babbar riga babu a jikinsa ballan tana rawani, ya bisu da kallon daya bayan daya har yaxo kan drivern sa, ya mika masa hannu "baki key" da sauri ya miko masa key din, ya fusga da sauri ya fita su kuma suka bishi da ido. It has been a while daya tuka mota amma bai manta yadda akeyi ba, a hankali ya tuka saboda baya son ya jawo hankalin mutane kansa. Direct sabon waje ya zarce ya yi packing ya tafi da sauri dakin Yaya, tana palo a tare da huda da kuma bayinta biyu suna yi mata tausa. Babu sallama ya daga labulen dakin ya tsaya yana kallonta, hatta huda bata gane shiba amma Yaya ba cire manyan kaya ba, ko menene dan nata zaiyi ba zata kasa gane shiba, a hankali ta mike duk da yanayin jikinta na tsufa, ta mike tsaye tana kallonsa kamar yadda shima yake kallonta, duk da baiyi mata magana ba amma tasan menene ya faru, da hannu ta yiwa mutanen gurin alama da su tashi su fita su basu guri. Suna fita yace mata "why?" Cikin nutsuwa tace "bani bace ba, mahaifinka ne, kuma sanda yayi bai shawarce ni ba" sarki ya hadiye daci a bakinsa yace "amma ya gaya miki dalilin da yasa yayi min haka?" Tace "bai gaya min ba amma na sani, yayi ne dan ya kare ka, yayi ne dan ya kare martabar gidan nan, yayi ne dan ya kare martabar kasar nan baki daya" hawaye ne ya fara taruwa a idonsa yace "to aura min zuwaira fa? Wanne irin uba ne shi? Wanne irin uba ne zai aura wa dansa yarinyar da tayi cikin shege? Wannan ma yayi ne saboda ya kare martaba ta ko saboda ya wulakanta martaba ta? Bai san Yaya tazo kusa dashi ba sai kawai saukar mari yaji a fuskarsa, ya rike kuncin yana jin zagi a ransa, cikin tsawa tace " wannan shine babban dalilin daya janyo yayi maka abinda yayi maka, dan bashi da rai hakan ba yana nufin zaka fada masa duk abinda yazo ranka ba. Komai yayi yayi ne to protect his family, you included".
Ya fara tunanin yadda auren ya kasance, zuwairah cousin dinsa ce, tun tana yarinya baya son ta, jinin su bai hadu ba, tana da rashin kunya sosai ga shegen munafunci, duk a family shi baya son 'yan gidansu saboda sun zama wake daya mai bata gari, tun daga shigar su ma zuwa yadda suke mu'amala da mutane zaka gane cewa ba tarbiyya ce dasu ba. Bayan rabuwarsu da khairat da shekara kawai rannan babansa ya kira shi palonsa na ciki, yana zuwa ya tarar da baba Abdullahi, wanda kani ne a gurin babansa, ya gan su cikin tashin hankali, ya gaishe su suka amsa, nan Sarki Abdallah yake gaya masa cewa Zuwaira ce tayi ciki, saurayinta yayi ya yaudare ta da sunan aure yayi mata ciki ya gudu, basa son zubarwa saboda suna gudun hukuncin ubangiji, kuma basa son magana ta fito saboda kar sunan zuri'ar su ya lalace. Shine suke son su hada shi aure da ita, za'ayi fake aure anan fadar, daga nan sai ace sun tafi kasar waje zatayi karatu, za'a tura ta dangin mahaifiyarta ta gama renon ciki ta haihu, shi kuma sai ya tafi wata kasar ya zauna a can, in ta haihu yaron yayi dan wayo sai a sake daura musu aure na gaskiya kuma amma a boye sannan sai su dawo a matsayin miji da mata da kuma dansu. Yana tuna yadda yaji zuciyarsa tana yi masa zafi kamar zata kona kirjinsa amma bashi da spirit din da zai yi musu, ranar kwana yayi yana kwana yayi yana kukan takaici amma da baban ya kira shi da safe zancen buga IV sai yace "to" yana ji yana kallo aka kakaba masa auren ta, both fake and real din, suka dawo gida kuma ya cigaba da zaman aure da ita ya kuma rike mata danta kamar yadda mahaifinsa yayi umarni da yayi.
Ya dago jajayen idanuwansa yana kallon Yaya yace "yanzu da kuka saka ni na rike shege me kuke tunanin zai faru idan bana duniya, kuna nufin zai ci gadona ne ko kuma kuna nufin zai karbi masarautar nan be ya mulka?" Yaya ta girgiza kai tace "babu ko daya, babanka ai ba fool bane ba, ya rubuta a rubuce ya saka hannu cewa duk sanda babu ranka, Sultan shine magajin ka, idan kuma babu ran Sultan to wani daga cikin kannenka ne zai karbi mulki, yace bai yarda da duk 'ya'yan da zuwaira zata haifa ba, ya bada copy din takarda ga dukkan king makers na masarautar nan, maganar gado kuma kuma ya rubuta ya bawa alkalin da yake raba wa familyn nan gado cewa bayan ranka Abbas bashi da gadonka, amma abar maganar a secret, idan babu ran alkalin next alkali shi zai karbi takardar" ya jinjina maganar, his father is really something. Ya tuna da irin rikon da yayi wa Abbas, da irin rikon da Hajiya tayi wa Sultan, ya tuna maganar giyar data rika feeding Sultan kuma Yaya ta gaya masa amma yayi burus da maganar. Ya juya ba tare da ya ce da yaya komai ba ya fice, mota ya shiga ya karasa palace, su kansu masu bude gate basu gane shi ba motar kawai suka gane, direct part din hajiya ya wuce mutane sai kallon sa suke yi sai in sun gane shi suyi saurin zubewa a kasa. A bedroom ya same ta ta fito daga wanka tana shiryawa, bayinta suna ganin sa suka watse, ta juyo da sauri itama tana kallonsa da mamaki, baya shigo wa part din ta ita take shiga nasa part din. Ya tsaya yana kare mata kallo, how can he have marry this? Ya tuna da khairat, da rayuwarsu together, da sauri ya kawar da tunanin daga ransa dan gap yake da hawaye. Ya ce "how dare you? How dare you treat my son like this? Duk abinda nayi miki, duk rike miki danki da nayi amma ke shine kika wulakanta min nawa dan" da tsananin mamaki take kallonsa, cikin rawar murya tace "Ranka ya dade ban gane maganar ka ba? Wanne dan naka? Wanne dan nawa?" Ji yayi kamar yaje ya zabga mata mari amma yasan dukan mace ba girmansa bane ba, yace "kinsan maganar da nake yi ai. An hada ni dake tare da shegen danki na hada na rike ku tikon amana amma ke kika wulakanta min nawa dan, magaji na, me kike so kiyi archiving? Wato plan dinki shine ki lalata rayuwar yaro na yadda naki yaron zai gaje ni ko? Is that your plan? Ke kika zuga ni na kai shi Lagos gidan kangararru saboda kina so ya lalace, ke kuma kika zuga ni na kaishi America tun yana da shekara goma sha biyu a duniya, burinki ya zama tantagaryar dan iska yadda babu yadda za'ayi a bashi sarauta, abinda baki sani ba shine Allah ya fiki, Allah ya kare min shi burinki bai cika ba, kuma ki sani plan dinki duk a banza kike yinsa, babana daya hada auren nan dan ya rufa miki asiri ba jahili bane ba, yasan me yake yi, ya rubuta ya bayar cewa danki ba zai gaje ni ba, dukiya ko sarauta" da baya ta tafi ta zauna akan gado tana rike zanin jikinta, ta shiga uku ta lalace yau menene yake faruwa, me ya samu Sadiq yau kuma? Tunda akayi auren nan bai taba furtawa cewa Abbas ba dan sa bane sai yau, kuma bai taba kiran sultan da sunan dansa ba sai yau. Me ya faru? Ko ma menene ya faru tasan da sa bakin wannan munafukar matar ta sultan, dama tace tana reading minds yanzu haka ma matsafiyace tazo ta tsafe mata miji zata raba su. Cikin rawar murya tace "wacce magana kake yi ne haka yau kuma. Abinda duk akayi a baya baya wuce ba? Ya zaka taso da wannan maganar bayan ga 'ya'ya muna dasu" ya katse ta yace "ta yaya zan tabbatar da cewa su din ma 'ya'ya na ne?" Da sauri tace "wallahi 'ya'yanka ne, wallahi tunda muka yi aure ban kuma kallon wani namiji ba sai kai" ta durkusa a gabansa ta rike kafarsa, zaninta yana neman kwancewa yayi sauri ya dauke kansa, tace "dan Allah baban Abbas ka daina wannan maganar, ka rufa min asiri yadda Allah ya rufa maka naka" yace "ni kuma kika tona min nawa asirin ba? Ki gaya min abinda kika yiwa dana idan ba tonon asiri ba menene?" Ta dago kai tace "to amma dai ai sanda nace a kaishi lagos din baka musa min ba, kai ka fara wulakanta shi ai, me yasa dana ce maka kayi sai kayo ba za ka yi min musu ba? Ko sau daya baka taba nuna wa kana son yaron nan ba to ni menene laifina dan na taya ka kinsa?" Yasan anan kuma ta fishi gaskiya, amma ko kusa da yana cikin haiyacinsa ba zai bi shawarar ta ba. Ta fara share hawaye tana cewa "dan Allah mu bar maganar nan haka, yadda iyayen mu suka rufe ta to kar mu bude ta dan Allah" ya sunkuyo dai dai fuskarta yace "da ace kin rike min dana da mutunci, da babu wanda zai san waye Abbas, da ace kin kula dashi a lokacin da ni na wulakanta shi, da nima yanzu sai in cigaba da kula da naki dan, d'a na kowa ne amma kika nuna nawa ba naki bane ba, dan haka nima yanzu naki ba nawa bane ba" ya mike tsaye yana kallonta cikin ido yace "na sake ki saki biyu, amma in banda ni da waliyan mu babu wanda zai sani in kin ga dama, zaki cigaba da zama a dakunan ki tare da 'ya'yanki. Abbas kuma ki tattara shi ki kaishi gurin ubansa, ki sanar masa bani ne mahaifinsa ba, in ba haka ba ni zan sanar masa da kaina a fada" ya juya ya fice ba tare da ya kuma kallonta ba. Wani relief yake ji a ransa, ya yarda kwallon mangwaro ya huta da kuda. Hajiya kuma mutuwar zaune tayi a gurin, bata taba tsammanin abin yayi zafi haka ba, saki? Ita din? Da girman ta da komai? Yau wacce irin rana ce? Ita yanzu ta ina zata fara fadawa Abbas cewa shi shege ne? Yau ta shiga uku ta lalace.
Ina fatan 'yan'uwana mata mun dauki darasi daga darasin Hajiya. Indai kika bari wani ya lalata ki to shi tafiyarsa zaiyi kamar baiyi komai ba, ke kuwa ke zaki kasance cikin takaicin abin har karshen rayuwarki, dan in kinyi aure ma kullum mijin zargin ki zaike yi. Ballantana ace kinyi cikin shege, in kin zubar alhaki a kanki, in kin barshi kin bar tambari har abada, shi kansa yaron har ya mutu ba zai ji dadin rayuwa ba, gori kullum, sai an tashi aure ma a rasa wanda za'a hada auren dashi tunda kowa yana son auren mai asali. Darasi na biyu kuma shine, d'a na kowa ne, in kika rike dan wata to kuwa tabbas za'a rike miki naki ko kina raye ko kin mutu. Ki sani zaki iya mutuwa a koda yaushe ki bar 'ya'yanki, za kuma ku iya rabuwa da mijinki ki bar 'ya'yan a gurinsa. Mu shuka alkhairi 'yan uwa, in mune yau ba mune gobe ba.

Episode Eighty Three : The News
Moon
Na jima da wayar a kunnena ina lissafa maganar ta amma na kasa bata amsa saboda wani irin shock da naji, har saida tace "Moon kina jina kuwa" nayi sauri nace "ina jinki Hafsat vara in duba picture din" na katse kiran na shiga WhatsApp, hannuna har rawa yake yi "oh dear God, let it be" na fara downloading picture din amma gani nake yi kamar ba zai gama budewa ba, sau biyu yana failing ina sake trying. Finally ya bude, sai da na dauke numfashi na saboda mamaki abinda na gani, hoton balarabiyyar na gani, amma kuma kamar sultan da siffar mata, the eyes, the nose, the lips, the eye brow, the eye lashes duk irin na sultan ne, hatta murmushin da tayi irin na sultan ne, farin fata kawai ta fishi sai kuma kasancewar ta macece, amma kuma anya wannan ce ta haifi sultan? She is too young to be his mother, amma kuma har sunan iri daya. Na kira Hafsat, tana dauka tace "kin ganta ko Moon?" Nace "na ganta Hafsat. A ina kuka hadu?" Ta fara min bayani "Aunt din Zayed ce, kanwar babansa, to irin bata shiga mutane sosai shi yasa tun da muka zo bamu ganta ba, sai dazu baban Zayed yace masa lallai yau ya kaimu gidanta mu gaishe ta. She live alone a gidan nata ma. Wato Moon kudi ne da ita kamar banza, 'yar kasuwa ce sosai, babu da babu jika, babu kuma miji, ina ganinta gabana ya fadi, nayi ta kallonta ina tunanin dawa take yin kama? Kawai sai da tayi murmushi na gane sultan ne, kuma na tuna cewa mamansa balarabiya ce, amma ban tambaye ki sunan ta ba" na sauke ajjiyar zuciya nace "Sunan ta khairat" da sauri Hafsat tace "Allah da gaske? Moon ita ce mamansa kenan?" Nace "I don't know Hafsat, amma baki ganin tayi yarinta da yawa?" Tace "ke dalla can hutu ne fa, kinga sisters dinta data girma kuwa?" Nace "amma me zayed yace miki a dangane ta ita? Ta taba aure a nan ko kuma ya labarinta yake?" Hafsat tace "it is all mysterious Moon, zayed bai san komai a kanta ba, da yake shi kinsan ba'a Riyadh ya tashi ba kawai abinda ya sani shine rayuwar ta take yi ita kadai bata shiga mutane, kuma tunda ya santa bata da aure" na danyi shiru ina tunani nace "please Hafsat can you get her to talk to you?" Hafsat tace "I think so, kinsan hali na da bin kwakwkwafi, kuma daga gani na ta fara sona bansan dalili ba, ga kuma khairat mai sunan ta" sai kuma tayi shiru sannan tace "wai dama sunan ta kika sakawa khairat" na danyi dariya nace "eh sunan ta ne" Hafsat tace "Munafuka, shine kika saka wa yarinya ta sunan surukarki ko?" Nayi dariya nace "to ai gashi nan kema maybe surukar taki ce" Tace "show sultan the picture ki ji abinda zai ce, ni kuma zan fara tambaya inji labarin ta, ko a gurin ummeen zayed ne, daga nan sai mu gane ko ita ce ko ba ita bace ba" na danyi shiru sannan nace "Hafsat bama tare da Sultan yanzu" kamar bata ji sosai ba tace "what?" Na ce ina jin hawaye yana taruwa a gefen idona "ina gida yanzu" tace "subhanallah Moon wannan wanne irin muguwar magana kike fada min hakan? Sultan din tafiya yayi kika zo gida?" Nan hawaye ya balle min nayi tayi, tana jina bata ce min komai ba, sai da na gama dan kaina sannan na fara bata labarin abinda ya faru gaba daya, na kara da cewa "Hafsat ban san ya zanyi ba, Sultan zafin zuciyarsa yayi masa yawa Hafsat, shima Ibrahim ban san me yake so inyi masa ba, nayi aure kuma ina ruwansa dani?" Hafsat tace "to ai ni sultan yayi min dai dai, cin ubansa ya kamata yayi yadda gobe in ya hango ki a guri da gudu zai fita. Yanzu kina nufin akan Ibrahim din kika baro gidan mijinki?" Nace "Hafsat ba'a kan Ibrahim bane ba, akan Sultan ne, akan bakar zuciyarsa, Hafsat kisan kai fa yayi niyyar yi, da Ibrahim ya mutu me kike ganin zai faru da shi? Me kike ganin zai faru dani? Sannan zargin da yayi min shi yafi komai kona min rai, he should have trusted me" Hafsat tace "tayaya kike tunanin zaiyi trusting dinki bayan ko cikin da kike dashi baki gaya masa ba? Idan da ace yasan da cikin da duk haka ba zata faru ba, idan kakar chocolate kike so zai fita ya sayo miki, in ma ya ganki da Ibrahim din yasan ba purposely kika hadu dashi ba. Idan kika yi la'akari da rayuwar sultan dole yana da trust issues, he is scared of

Please Login or Register in order to submit comment