Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

muka dauko kayan mu muka fito, muna fito wa na fara wara idon ganin motar da zata dauke mu, dan nasan duk sanda muka je Niamey wani cousin din mommy ne yake zuwa daukan mu, babu shi babu alamar sa. Taxi naga daada tana tsayarwa, na karasa gurinta naji suna magana da mai taxi din da yaren da ban sani ba, abinda na fahimta kawaj shine kudin da ya gaya mata, kudi ne masu yawan gaske, ya fito ya fara zuba kayan mu a mota, nace "daada ina zamuje ne?" Tace "zaki gani ne ai" nace "daada ko ma ina zamuje mu fara zuwa gidan su Ahmodou mana mu gaisa, kinga sai mu huta acan" bata kulani ba ta tura keyata cikin mota sannan itama ta shigo. Tun muna tafiya ina gane titunan da muke bi har muka fara shiga inda ban sani ba, daga baya muka dau hanyar barin gari, ni maimunatu na shiga uku, ina zamuje ne? Ni in banda Niamey ban taba zuwa wani gari a Niger ba, na sake cewa "daada ina zamu je ne?" Direct tace min "Tahoua" na kwantar da kaina a jikin window ina kallon jefi jefin bishiyoyi suna wucewa, Tahoua, nasan sunan garin amma a iyakacin sani na bamu da 'yan'uwa acan. Lallai mommy da gaske take, na danyi murmushin takaici nace a raina 'tace bazan dawo ba sai na manta da Sultan. Bata san sai da ya dauke ni shekara biyar ba kafin in chire Ibrahim daga raina ba? Sultan kuwa nasan kuwa nasan zan tafi dashi ne a raina zuwa kabari na' a haka bacci ya dauke ni, can naji daada tana tashina, na dauka munzo ashe tsayawa mukayi sallah, cikin sahara, dan gurin da muka tsaya ko 'yan bishiyoyin babu, ni dai a tsorace nayi sallar na koma mota. Bayan mun kuma daukan hanya daada ta dauko wata food warmer da soyayyun kaji a ciki ta hado min da ruwa da lemo ta miko min, na diba na zubawa drivern na mika masa. Ni lemon kawai nasha dan sam bakina babu taste.

Sai bayan magrib muka isa Tahoua. It is worse than I imagine. Gidan da muka je gidan kasa ne rufin azara, cikin wata chakudaddiyar unguwa. Ji nayi gaba daya hankali na ya kuma tashi, yanzu mommy tana nufin anan zan zauna har sai ranar da ta waiwayoni? Muna shiga muka tarar da wata tsohuwa tana kirki a itace, da mamaki ta taso ta tari daada, suka rungume juna suna ta murna, ni dai 'yar kallo ce, ta kaimu wani daki mai dan girma wanda ko siminti babu sai kasa. Ta shimfida mana tabarmar karauni muka zauna na gaisheta tana kallona tace "tubarkallah, daada ina kika samo 'yar kyakykyawar yarinya haka?" Daada tace "diyar bintou ce fa" tace "hidijan, yanzu bintou ke da diya kamar wagga?" Daada tace "laa wagga ita atta hudu" matar tace "alqur'an daada wagga ya kamata a amra mata dan'uwa ta zamna a Niger" ina jika na mike nace "ina ne bandaki zan zagaya?" Matar ta taso ta rakani, shaddar kasa, na kasa tsugunnawa na fito nayi alwala nazo na tayar da Sallah. Ina yin sallar isha na shimfida zanina na kwanta na lulluba da hijab dina, ba bacci nake ba, so nake inji hirar su daada dan insan halin da nake ciki, ga mamakina ko zance na basu yiba, labarurrukan da kawai suke yi suna dariya. A cikin hirar naji daada tace ai akan hanya muke, tsayawa mukayi mu huta, Agadaz zamu je. Zumbur na mike daga kwancen da nake nace "Agadaz daada? Daada Agadaz fa karshen duniya kenan?" Cos haka muke cewa sanda muna yara. Daada ta harare ni tace "dama ba bacci kike ba ko?" Nace "dan Allah daada Agadaz zamu? Wa muke dashi a Agadaz? Mommy ma da kanta tace bata taba zuwa ba saboda nisan garin? Daada me laifi na har ya kai girman haka?" Sai kuma kuka. Ina jin matar tana ta yiwa daada tambayoyi amma bata ce mata komai ba, aka kawomin abinci naki ci, daada ta dauko min magani na ta bani tasa lallai sai da na sha. Ranar sam banyi bacci ba, ga gajiya ga tunani, da zarar baccin ya daukeni kuwa zanyi ta mafarke mafarke, most of them na Sultan ne kuma duk basu da dadi. Daga karshe dai na tashi zaunr na hade kai da gwuiwa nayi ta rera kuka na. Babu abinda ba zan iya bayarwa ba a lokacin dan insan halin da Sultan yake ciki. Ni kaina ina tsoron zuciyarsa. Sai ya hargitsa garin Abuja gaba daya. Sai gab da assuba sannan nayi bacci, cikin baccin naga sultan a cikin gidan mu yana bi daki daki yana nemana, yana bude dakin mommy ta dauko bindiga ta harbe shi. Na farka a tsorace ina ta jero adduoi. Naji ana kiran sallah na tashi nayo alwala nazo na fara nafiloli ina ta jero wa Sultan addua, ni ban damu da kaina ba, duk abinda mommy zatayi min nasan ba zata taba chuta ta ba, amma shi bashi da kowa sai Allah. Mommy lawyer ce, zata iya creating case against him wanda dole alkalin ya dauke kansa daga ganin cewa dan sarki ne ya rufe shi, babansa kuwa ko dan yatsa ba zai daga ba ballantana ya damu. Hope dina kadai shine daddy, shi kadai ne zai taka wa mommy burki. Amma bansan shi kuma yadda zai dauki al'amarin ba, saboda shi daddy baka ta ba gane inda ya sa gaba saboda kwarjinin sa. Ana yin assalatu na tashi daada sannan na tayar da sallar, na idar ina azkar naji tana gayawa matar ta aika a samo mana mota shata. Karfe shida muka shiga motar, kawar daada ta hado mu da kunu da kosai wai ma ci a hanya. Motar hilux ce saboda sahara. Muna baya ni da daada kayan mu kuma suna gaba tare da driver. Tun karfe shida muke tafiya har karfe uku na yamma sannan muka tsaya muka yi Sallar azahar da la'asar muka cigaba da tafiya. Lallai Agadaz akwai nisa, nayi baccin har na gaji, nayi tunanin har kaina yana neman bugawa. Ko bishiyoyin ma babu, inka leka ta window yashi kawai zakayi ta gani babu iyaka. Daada tayi tayi dani inci abinci naki ci. Rabona da abinci tun wanda mommy ta takura min naci ranar da zamu taho. Mun daga nesa na hango garin. Babban gari ne babu laifi amma ko irin 'yan kauyukan kan hanya din nan babu kawai sai dai ka ganshi a gabanka a tsakiyar sahara. Muna shiga garin daada ta gaya wa drivern in da zai tsaya, ya tsaya amma maimakon inga mun fito sai naga mun zauna a mota muna jira, can sai ga wata katuwar Jeep ash color ta tsaya a kusa damu, wani saurayi ne ya fito ya kara so windon da nake yace "baki daga Nigeria?" Hausar shi tas kamar dan kano. Na dauke kaina kamar ban ji shi ba dan ni kowa ma haushi yake bani. Daada ce ta amsa masa da murmushinta tace "eh mune, mustapha ne ko musbahu?" Yayi dariya yace mata "Mustapha ne daada" ya kalleni yace "Hafsat ko Moon" ya sake bawa iska ajjiyarsa. Daada ta kama fada ni bama abinda take cewa nake ji ba, ya bude min kofa shima yana magana amma bana gane me yake cewa. Ina fitowa daga motar jiri ya debe ni sai kasa. Da sauri ya zo zai rike ni na daga masa hannu nace "Don't touch me" ni na manta ma 'yan Niger basa turanci, amma ga mamakina sai naga ya ja baya yace "just trying to help" daada ta zagayo da sauri ta rike ni muka tashi tsaye, muna tashi kuwa nayi mata wanka da amai, babu komai a cikin aman nawa sai ruwa. Sama sama nake jinsu suna ta yi min sannu. Daada tana cewa "bata taba yin tafiya me nisa irin wannan ba ne shi yasa, kai wannan gari naku da nisa yake" ni dai aka sakani a mota na kwanta ina jin dadin sanyin ACn motar. Ina jin alamar muna tafiya amma babu damar in dago kai in kalli gari saboda jirin da nake ji. Naji horn kuma naji an bude gate, daganan naji mun tsaya. Daada ta riko ni muka fito tare, inajin saurayin yana yiwa wata yarinya French sai naga tazo ta kamani itama muka shiga cikin gidan. A palo suka kwantar dani akan doguwar kujera. Mustapha ya sake aiken yarinyar sai gata da cup din tea mai zafi ta kawomin, na karba nace "graciers" na ringa kurba a hankali har sai da na sanye. Sai a lokacin na samu idon kallon palon. Yana da girma kuma an cika shi da kayan alatu, daga dukkan alama mutanen gidan basu da matsalar kudi. Daada ta shigo daga alama sallah tayi. Mustapha shima ya shigo daga masallaci. Nan aka nuna min inda zanyi sallah na shiga nayi. Daki ne babba da katon gado da wardrobe a ciki, sai toilet shina babu lefi mai kyau. Kayan mu na gani a dakin, anan kenan zamu zauna. Ina idarwa yarinyar ta dawo tayi min alama da ana kira na. A palon na tarar dasu suna cin abinci, daada da wata mata da maza samari su uku. Na karasa na zauna daga dan nesa dasu. Matar ta dago ta kalleni fuskarta a hade babu murmushi. Na gane ta. Aunty Zaliha. Kawar mommy ce tun muna yara, gurin aikin su daya da mommy. Tana zuwa gidan mu muma kuma muna zuwa gidanta tare da mommy, muna secondary school mommy tace mana sun tashi daga Nigeria amma sam bamu san Niger suka dawo ba ballantana insaka ran ganinta a agadaz. Tana da yara maza uku. Twins, Mustapha da Musbahu, sai kuma gambon su Musaddiq. Musaddiq shine sa'an Hafsat su kuma twins din sa'annin yaya Walid ne.

A hankali nace "aunty Zaliha?" Tace "eh nice dai, in kin manta ni ma ki tuna ni, kinsan cewa ni ba Fatima bace bana daukan nonsense. Kin bata wayonki wallahi Moon. Kin bani mamaki. Ni ba dan fatima bace ta gaya min ba zan iya rantsewa karya ake miki. Amma babu komai, zaki dawo hankalin ki ne. Ni na bawa Fatiman shawarar ta kawo ki nan gurina har sai komai ya daidaita tukun" kowa yayi shiru ni kam bakin ciki ne ya kamani jin itace ta bada shawarar rabani da Sultan da babana da 'yan'uwana, sai kuma ta cigaba "yarinya kamarki, me kika rasa ke kuwa a rayuwa, mai kika gani a gurin wannan kangararren yaron da bamu tabbatar ma da asalinsa ba? Kina da asalin ki, ilimi, tarbiyya, ga kyau, na tabbatar samari suna nan suna layi wadanda ko yau akace su fito zasu fito din, amma shine kika gwammace ki zibar mana da mutunci a gurin jama'a" fada take tayi da duk karfinta, ni kuma na sunkuyar da kaina kasa amma ta inda fadan nata yake shiga ta nan yake fita. Daada itama ta dauka suka yi tayi. Sai da sukayi mai isarsu sannan sukayi shiru. Wani daga cikin samarin ne ya zubo min abinci ya miko min, na karba tare da yi masa godiya. Aunty Zaliha tayi sauri tace "a'a, no friendliness of any kind. Duk wanda a cikin ku ya sake ya bata wayarsa ko da wasa ne sai na saba masa wallahi. I am dead serious. There is a very bad person a Nigeria da yake son bata rayuwarta, an kawo ta nan ne saboda a raba su. Duk wanda ya taimaka mata to ya sani cutar ta yayi. Did I make myself clear?" Duk suka amsa da yes. Sakani tayi a gaba sai da na chinye abincin da aka zubo min sannan na sha magani na tace inje in kwanta. Gaba daya jikina ciwo yake yi, ina zuwa nayi sallar isha nayi shirin bacci na kwanta. Bacci me nauyi ne ya daukeni, amma daga baya sai mafarkan suka fara dawowa, na farka na kuma kasa komawa. Daada tana gefena tana ta baccin ta, na tashi na shiga toilet nayo alwala nazo na saka goduwar riga ta na dauko al'qurani na na fara karan tawa, ina yi ina zubar da kwalla. Allah ka fini sanin halin da nake ciki, Allah ka fini sanin waye Sultan. Allah ka huci ran mommy da daddy. Allah ka bani dauriya da juriyar daukan duk wani abinda ka kaddara zai sane ni. Allah ka bawa Sultan hakuri na duk abinda ka kaddara masa. Allah ka zaba mana mafi alkhairi a rayuwar mu baki daya.

Kwana daya ya wuce, na biyu ma haka, sati daya ya wuce na biyu ya biyo bayansa, wata daya yazo, haka wata biyu sannan wata na uku yazo shima. Ko bakin gate ban taba zuwa ba ballantana in fita waje. Daga daki sai palo. Kullum da alqurani na a hannuna dan yanzu shine babban abokina, it's the only thing that's keeping me sane. Ko da yaushe daada ko aunty Zaliha suna kallona, ni kam daga gaisuwa babu abinda nake kara cewa kowa. In an bani abinci inci, in an bani magani in sha. Samarin gidan kullum suna son kula ni amma babu hali saboda suna tsoron aunty zaliha sosai. Amma ina ganin tausayina a idon su. Wanda muke magana dashi kawai shine mijin Aunty Zaliha, kullum in ya ganni palo zai ta tsokanata wai bafulatanar daji tazo birni ko yawo bata zuwa saboda kyauyenci. Kullum sai ina jin aunty zaliha ko daada sai sunyi waya da mommy amma bata taba cewa a bani ba, ni kuma ban taba cewa zan karba ba.

Rannan muna palo da aunty zaliha da Musbahu sai mommy ta kira suna magana ta tashi ta shiga daki dan kar inji me suke cewa, dama haka suke yi kullum. Tana shiga musbahu ya matso kusa dani yace "ya sunan sa?" A hankali nace "Sultan" when was the last time I called his name out loud? Yace "am sorry, I know what love feels like" a lokacin muka ji motsin aunty zaliha zata fito, yayi sauri ya matsa. Tana zuwa ta miko min waya "Fatima zata yi magana dake" na karba kawai ina kallon wayar, hannuna har rawa yake yi na saka a kunnena amma na kasa magana, can naji muryarta tace "Moon?" Wasu hawaye masu zafi suka zu bo min, banyi magana ba ta sake cewa " Moon banyi tunanin zaki dade haka ba, banyi tunanin abinda nayi planning zai dau lokaci ba" ta kuma yin shiru. A hankali nace "mommy ina daddy dasu ya Walid? Mommy in Hafsat ta haihu?" Ta jima bata yi magana ba, sanda tayi muryarta tayi alamar kuka, tace "duk lafiya lau suke, Hafsat bata haihu ba" desperately nace "mommy dan Allah ki bar ni ko waya ne inyi dasu" dif naji ta kashe, na saki wayar na rife fuskata da hannuna ina kuka. Jin muryar mommy ya daga min hankali sosai, gida kawai nake son zuwa. Aunty Zaliha ta dauke wayarta ta sake dialing number din mommy ta koma daki. Ina cikin kuka na naji an ajiye min wani abu a kan cinya ta, na dago kaina da sauri naga Musbahu yana min murmushi, na kalli cinya ta naga waya, a hankali yace "call him, but let it be our secret" gaba nane ya fadi sosai, shi kuma ya mike ya fice daga palon. Da sauri na dau wayar na saka a riga ta ina rarraba ido. I got a phone now, what do I do? Kar a kama ni kuma a kaini wani gurin da yake worse than here. Na tashi na shiga daki naga daada a kwance, nima na kwanta a gefenta na rufe idona kamar mai bacci ina ta lissafi a raina, menene yasa mommy kuka? Me ya faru a gidan? Me yasa tace abinda ta shirya is taking time? Ko dai wani abin ta saka aka yiwa Sultan kuma take regretting yanzu. Na shiga uku. Ina nan kwance har naji daada ta tashi ta shiga toilet, ta fito ta jima tana kallona sannan ta fita palo. Tana fita na mike na shiga toilet nayi locking kofar sannan na dauko wayar, babu security a jikin ta ya chire. Na shiga dialer da sauri na saka number din Sultan, na daga hannu zan dialing na kasa, what if something bad has happened to him? My heart can't take it, ya Ilahi. Sai kawai na goge number. Na saka number din daddy, ta gama ringing har ta katse bai dauka ba. Ya Allah. Na sake re-dialing ina lissafo sunayen Allah a ziciyata. Ringing na uku ya dauka "salamu Alaikum" a hankali nace "daddy" ya danyi shiru sai yace "Moon? Is that you?" Sai hawaye na kasa magana, yace "my God, Moon kiyi min magana mana, a ina kike? Ina Fatima ta kai min ke? Are you Ok?" Kuka ne yaci karfina nace "daddy ina Agadaz" yace "what? Agadaz fa kika ce? Yanzu Fatima cikin extreme saharar agadaz ta kai min yarinyar? To uban wa ta sani a agadaz din?" Nace "aunty Zaliha tsohuwar kawarta ta office dinsu" yace "Zaliha? Dama agadaz suka koma? Are they treating you well? Ko tabo na gani a jikin ki sai na dau mataki akai" nace "daddy am OK. Yaron gidan ne ya taimaka min da aron yawarsa. Please daddy kar asan shi ya bani" yace "don't worry about him, I will come and pick you up tomorrow. OK? Kar ki gayawa kowa kin kira ni, OK?" Na gyada kai kamar yana kallona. Har yanzu hawaye bai tsaya a ido na ba. A hankali nace "Daddy how is Sultan?"

Godiya marar adadi ga duk masoyana masu bibiyar lafiyata, Alhamdulillah lafiyata kalau, biki ne dai muke yi shi yasa akaji shiru. Nagode Allah ya bar zumunci.

Na samu labarin wadansu masoyan moon a whatsaap suna shirya riot dan kwato mata 'yancinta, haha, to sai ku shirya zuwa Agadaz, amma sai dai kuje ku kadai dan ni ban shirya zuwa sahara da zafin nan ba. Lol

I love you all 💖



Episode Fifty Three : Daddy

Yace "Don't worry about Sultan. Kar ki bari zaliha tasan kin kirani har sai na nemi contact da mijin ta, dashi zamuyi magana. Badan jirgi baya zuwa agadaz ba Moon da yau zanzo in dauke ki. Amma highest jibi. Ki kwantar da hankaliki kinji?" Na gyada kaina kamar yana kallona sannan nace "I miss you daddy" ya danyi shiru sannan yace "I miss you too, sunshine" daga haka ya kashe wayar. Nayi tunanin in kira Hafsat amma kuma sai na fasa kar ta gayawa mommy na kira ta. Na mayar da wayar cikin jaka ta na fito daga toilet din ina kalle kalle. Babu kowa a dakin. Na dan tsaya ina tunani, a raina nasan kiran daddy da nayi dai dai ne amma kuma duk da haka sai nake jin feeling kamar nayi ba dai dai ba. Na tsaya a gaban mirror, when was the last time dana kalli fuskata? Tunda muka zo na saka wani towel na rufe mirron dakin saboda bana son kallon fuskata. A hankali na bude, ni kaina sai da na tsorata, babu komai a fuskar sai katon hanci da idanuwa kamar na mujiya, dama haka idona yake? Lallai kiba ma rahama ce. Na kalli wuyana naga wani katon kashin da bansan ina dashi a gurin ba, amma kuma kirjina yana nan dam dam, ramar da nayi ma sai ta karawa girman su fitowa, a raina nace 'su basa ramewa ne?' Na mayar da mirror din na rufe na koma na kwanta. Ina kwance daada ta dawo tayo alwala tazo tayi sallah sannan ta tashe ni, har da dan magagi na kamar me baccin gaskiya sannan na mike na shiga toilet nayo alwala nazo nayi sallah ni ma, muka fita falo tare. Musbahu ne kadai a zaune yana kallo, daada ta zauna kusa dashi ya fara labarin film din da yake kalla, hankalinta gaba daya yana kam kallon na zaro wayar na ajiye a kusa dashi na koma gefe na zauna. Ina kallonsa ya dauka ya saka a aljihunsa ba tare daya kalleni ba. Muna zaune a palon har akayi magrib, anan muka yi sallah aka fara kawo abinci. Mun fara zubawa kenan mukaji shigowar abban su Mustapha, gaba na ne ya fadi saboda nasan ba yanzu yake dawowa ba, tun daga compound yake kwalla wa aunty zaliha kira, ta mike tsaye fuskarta da alamar tsorata, yana shigowa ya fara balbalin fada "Zaliha yanzu dama abinda kuke aikatawa kenan ke da Fatima? Kika ce min yarinyar nan hutu tazo yi gidan nan, dama ni ina mamakin tunda tazo ban taba ganin ta fita waje ba, ashe ita nan zaman prison take yi a gidana. Saboda tsabar rashin hankali ku raba yarinya da ubanta da 'yan'uwanta kawai dan saurayin da take so bai yi muku ba?" Kamar zatayi kuka tace "abban musaddiq dan giya ne fa" yace "to amma baku yi tunanin cewa baban ta shima yana da right na zaba mata miji ba? Ko ita Fatima tana ganin cewa tafi ambassador son ta ne? Yanzu kinga ni kinsa naji kunyar mutumin nan, mutumin kirki wallahi, sai da nayi tayi masa rantsuwa cewa babu hannuna a cikin maganar nan. Yanzu da wani ne da sai dai kawai inga 'yan sanda a gidana" ya zo gaba na ya sunkuya yace "Maimunatu kiyi hakuri kinji? Dana san halin da kike ciki da tuni na dau mataki a kai, babanki ya taho already, a daren yau zai sauka a Niamey dan da private jet dinsa ma ya taho, ni kuma ni zan kai ki Niamey da kaina. Ki tashi kije ki shirya" aunty zaliha ta ce da sauri "wai a yanzu zaku tafi?" Ya tashi yayi hanyar dakinsa yana harararta yace "in bamu tafi yanzu ba yaushe zamu isa can?" Yana shiga daki kowa yayi shiru a palon, na mike sum sum zan shiga daki aunty Zaliha ta danko hannuna fuskarta babu rahama tace "uban waye ya baki waya kika kirashi?" Nan da nan hawaye ya kawo idona saboda zafin rikon da tayi min, nace "ni bani na kirashi ba, bansan yadda akayi yasan ina nan ba" ta juya tana kallon 'ya'yanta har yanzu bata cika ni ba tace "cikin ku waye ya bata wayarsa?" Duk sukayi shiru, cikin tsawa tace "ba za'a bani amsa ba?" Nan suka kama rantse rantse banda musbahu da yake ta game dinsa kamar bai san me akeyi ba, tace "Mustapha kai ne ko? Dan na lura da yawan shishshige mata da kake yi?" Mustapha ya kama rantsuwar bashi bane, ko ta kan musbahu bata bi ba dan sam tunda nazo gidan baya kulani, shi dama ko a cikin 'yanuwansa bashi da harka sosai. Ta sake ni tana girgiza kai fuskarta kamar zatayi kuka "poor you, you have no idea what you have done. Sai kije ai, shi baban naki ya aura miki wanda yake so din. Duk abinda fatima tayi, she did it to protect you amma ke gani kike ta takura miki ne saboda bata son ki" ban gane mai take nufi da babana ya aura min wanda yake so ba, ni dai nasan daddy bai zaba min miji ba kuma shi da kansa ya fada cewa baya son Munir. Ta juya ta shigewarta daki, ina shiga daki daada ta biyo bayana, tana ta maganganun ta akan ban kyauta ba ni ko ko kulata banyi ba na dauki iya abinda zan iya dauka na ziba mana a akwatinan mu, sauran na barwa 'yan gidan. Ban bi ta kan daada ba na jayo akwatinan mu na kawo palo, lokacin already gari yayi duhu, abban su mustapha na gani yana cin abinci a palon, yace min "ina daada? Ku zo kuci abinci mu tafi dan kwana zamu yi a hanya" ba musu na zauna na zuba abinci na fara ci, sosai naci na koshi dan nasan wahalar da nasha sanda muka zo. Har muka gama babu aunty zaliha babu labarin ta, muna gamawa abba ya kira musaddiq ya saka mana kayan mu a mota sannan daada ta shiga dakin aunty zaliha nima na bita a baya, tana kwance a kan gado, suka yi sallama da daada nima na matsa kusa nace mata "zamu tafi" ko kallona bata yi ba,

Please Login or Register in order to submit comment