Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Karfe biyar na yamma sultan ya gaji da zama shi kadai ya fita waje, sai kuma gashi ya dawo da sauri yazo ya daga ni tsaye ya fara kokarin cire min riga, na rike hannu sa, "sultan menene haka?" Bai ce min komai ba ya dauko wata rigar mai kauri da dogon hannu da collar ya saka min, ya saka min hula da safa ni dai duk ina kallonsa, nace "ina zamu je kuma" yace "kifi zaki je ki kamo mana ki gasa mana muci da daddare" na dan bata fuska nace "kifi kuma? Ni ban iya kama kifi ba" yayi murmushi yace "yau zaki koya, common, let's go" ya kama hannuna muka fita. A hankali naji na dan fara sakin raina, bawai na daina jin zafin mutuwar bane ba, na dai daina jin haushin sultan. Wani boat muka dauki haya muka shiga, daga ni sai shi, shi ya tuka ya kaimu tsakiyar ruwa sannan ya dauko wani dan kwando ya bude ya dauko wata kugiya ya daura zare a jikinta, sannan ya zagayo ya zauna a baya na, ya saka kafafuwansa a both sides dina, ya kama hannayena da nasa, ya saka fuskarsa a wuyana yace min a cikin kunnena "I am going to teach you how to catch a fish" cikin raunanniyar murya nace "sultan Baffa ne fa ya mutu, how can I just be busy catching fish bayan Baffa ya bar duniya?" Yace "mutuwar Baffa tana nuna mana abubuwa da yawa, daya daga cikinsu shine; there is an ending to life. Duk shekara, duk wata, duk sati, duk yini, duk awa, duk minutes, duk second din daya wuce ba zai dawo ba. What we need to do is to make the best of our time kafin namu lokacin muma yazo. We should live our life because it is a gift from God. Baffa yaji dadi, yayi rayuwa mai tsaho kuma mai kyau, ya tafi ya bar zuri'ah mai albarka. Wani tun kafin yayi aure ma yake mutuwa, wani tun yana yaro ma kafin yasan menene rayuwa yake mutuwa, wani ana haihuwarsa yake mutuwa, wani kuma tun a cikin mahaifiyar sa yake mutuwa, shi ko duniyar ma bai gani ba ballantana yaji dadinta. Wani kuma zai yi rayuwar mai tsahon har yakai kamar shekarun Baffa amma kuma sam babu abinda ya tsinana a cikin ta, babu abinda in ya tafi za'ace ga abinda ya bari na alkhairi sai dai na sharri. Amma baffa kuma fa? Ko mu daya bari ba mun isa mu taya shi gode wa Allah ba? Mu taya shi neman rahamar ubangiji ba?. Mutuwa is a circle of life, wani ya mutu sannan a haifi wani. Jiya da baffa ya mutu hundreds of babies were born all over the world, sannan hundreds of people sun mutu tare dashi" ya dora hannayen mu akan babyn mu da yake ta tsalle tsallensa babu abinda ya dame shi, yace "ranar da za mu haifi babyn mu, ranar hundreds of people zasu mutu. And what favor of our Lord do we deny?" Na lumshe idona ina ina jin dadin iskar gurin, ina jin dadin dumin jikin sultan, ina kuma jin dadin kalamansa, sannan inajin dadin motsin baby na a ciki na, what favor of my lord do I deny? Allah yayi min komai, ya bani komai, why should I be sad dan ya karbi abu guda daya daga cikin dubun daya bani? Na bude ido na ina kallon clear ocean din nace "I thought we are suppose to be fishing? Ya dan yi dariyar jin dadi yace "yes Love". Mun kama kifaye da yawa, dan sai da muka cika dan basket din da muka taho dashi, daga baya sai muka fara zaba, duk wanda muka ga mummuna ne sai mu mayar dashi cikin ruwa, gaba daya hankali naji ya kwanta, babu wani sauran bakin ciki a tare dani, nishadin mu kawai muke muna dariya, in mun kamo kifi yana ta tsalle mai in kankame sultan wai tsoro nake ji kar ya cije ni, in mun mayar dashi ruwa kuma sai muga sun fita a guje, nan ma muyi tayi musu dariya. Bamu ankara ba sai gani mukayi rana zata fadi, nan muka tsaya muna kallon rana tana setting on the ocean, rana tana gama faduwa kuma sai duhu ya fara saukowa, nan take naji tsoro ya kamani, na duba naga we are in the middle of nowhere, babu gida gaba babu gida baya, na zaro ido ina kallon sultan nace "sultan yanzu idan shark yazo ya cinye mu fa" yace "kin san kuwa akwai sharks a ruwan nan ba" da sauri na kankame shi "na shiga uku, shikenan a teku zamu mutu, ko gawar mu ma ba za'a gani ba, wayyo Daddy" dariya sultan yake min sosai sannan yace "am just joking, babu shark anan" ni dai ban yarda ba nace ya mayar damu hotel din mu. Hankali na vai kwanta ba sai da naji kafa ta ta taka kasa tukunna. Muna zuwa sultan ya dau basket din kifin ya kai restaurant din gurin yace su gyaro mana shi su kawo mana tare da kayan barbeque. Da daddare kifin mu muka gasa muka ci a matsayin abincin dare. Da daddare na tashi na gabatar da salloli na roka wa Baffa rahamar ubangiji.
Washegari ma Sultan bai barni na zauna ba ballantana inyi tunani ko kuka. Ya dauke ni muka tafi shopping. Kaya masu yawa ya saya mana ni da shi, bamu dawo dakin mu ba sai azahar, muna zuwa muka hada duk kayan mu da ba zamu bukata ba sultan ya dauka ya tafi shipping station din gurin ya bayar za'a kai mana har gida abuja. Tun da ya dawo yace min yau zai kai ni wani special guri muyi last dinner tunda gobe da safe zamu bar kasar. Muna sallar magrib muka shirya, ni kaina nasan munyi kyau, dama gashi na kara fari, in ka ganni ma ba zakace na taba shiga rana ba, ga kuma kibar ciki data kara min cika da budewa sosai, hips dina kamar wanda aka dauko aka dora min. Na saka riga da skirt bakake masu adon red, nayi rolling red veil wanda ya kara fito da hasken fata ta, kayan kuma tunda masu girma ne sai suka boye girman cikina. Sultan kuma suit ya saka ash, ya saka red shirt a ciki, ya taje kansa ya kwantar da gashinsa sai kyalli yake yi. Na zauna kawai ina kallonsa saboda kyan da yayi min. Golden brown skin dinsa tana reflecting duk fitilar data haska shi. Duk wanda ya kalle mu sai ya kara. Wani restaurant mukaje mai suna Ithaa, a karkashinin ruwa restaurant din yake, lifter zaka shiga tayi kasa da kai sannan sai kadan yi tafiya kadan a cikin wani glass corridor zuwa cikin restaurant din. Dan karami ne kuma shima duk da glass aka yi shi dan haka ji zaka yi kamar a tsakiyar ruwa kake, ni dai ji nayi kamar glass din zai fashe ruwa a shigo ya cinye mu. Gurin mutane 14 kawai yake dauka, amma fa abincinsu number one ne gurin dadi. Muna ci muna zuba soyayyar mu, dan gurin babu wanda ya damu da abinda wani yake yi. Bamu muka dawo dakin mu ba sai after ten. Muna zuwa muka kammala harhada sauran kayanmu mukayi sallah muka kwanta.
Washe gari da sassafe jirgin mu ya tashi, na leka ta window ina kallon islands din nace a hankali "AdiĆ³s Maldives, sai mun dawo" sultan yana kusa dani yace "we will come back for sure". Jirgin mu yana gama settling a sama na cire seatbelt dina na tashi na dawo kan cinyar sultan na kwanta, ban jima da kwanciya ba bacci ya dauke ni, sama sama naji sultan yana cewa plight attendant ta kawo mana bargo, ya dan kwantar da kujerar sa ya lullube mu da bargo. Gaba dayan mu bacci mukayi, dan sai da jirgi zai sauka a malam Aminu kano international airport sannan aka tashe mu. Muna fita reception muka tarar da Mahmud abokin sultan na kano wanda sultan ya kira ya gaya masa zamu zo yana jiran mu. Na kalli agogo naga 9:30am. Ikon Allah, banbancin lokuta a tsakanin garuruwa kadai ya ishi mutum abin mamaki. Mun baro Maldives 8:30, munyi tafiyar at least five hours amma kuma munzo Nigeria at 9:30am, to ina four hours din suka tafi?. Sai da muka tsaya muka danyi takeaway din abinci kuma sultan ya chanza kaya zuwa manyan kaya da hula sannan muka dauki hanyar 'yalleman. Sai a lokacin baji mutuwar tana sake dawomin a raina, muna zuwa kofar gidan naga cikar mutane a gurin, dan gabaki daya garin ma kusan a cike yake da mutane tunda yau ne sadakar uku. Kafin muyi packing na kira Amina nace tazo mu shiga tare saboda bana son shiga ni kadai. Ina shiga naga kowa ido shabe shabe da hawaye ai nan take na fara nawa nima, sai kuma kowa ya dora daga inda ya tsaya, naje na fada jikin Inna muna yi tare. Uncle Aliyu ne ya shigo da fadan sa, yace "dama tunda na jiyo sabon kuka nasan sarauniyar kuka ce tazo, menene haka maimunatu? Ana kokarin ayi masa adduoi ke kina kokarin ki tayar mana da sabon kuka ko?" Nan take na hadiye kuka na, na dau charbi ina ja amma ban san me nake cewa ba, hawaye ne kawai yake bin fuskata ina kallon irin jama'ar da Baffa ya bari, ga dakinsa nan kamar zai fito daga ciki. Sai yamma sannan jama'a suka dan ragu, sai a lokacin na samu naga Hafsat wacce itama nata cikin ya fito ba laifi, Daddy kuwa sai da daddare sannan na samu nayi masa gaisuwa. Washegari wajan 12:00 na safe duk kusan jikoki mata muna palon hajja a zazzaune sai ga aike wai inzo dakin inna nayi baki daga abuja sun zo min gaisuwa. A raina nace 'lallai Yaya da kokari, wannan tafiyar aita yi mata nisa da yawa, tunda munyi waya ba shikenan ba?' Na kama hannun Zainab amaryar yaya Walid muka tafi tare. Amma ga mamaki na ina shiga palon sai ganin Ummee nayi a zaune akan kujera tana kallona, na saka hannu na na mitstsike idona wai ko ba dai dai na gani ba amma still ita dince, da nani, da matar galadima da kuma Saratu da Huda. Na karasa gurinta da sauri na fada jikinta, ta rungume nu tana cewa "careful, kar kiji ciwo kuma" na fara kuka tana rarrashina, da hannu ta saka take goge min hawayena, duk mutanen gurin kallin mu suke da sakakken baki, nace "Ummee how comes you are in Nigeria? When did you come? Did Sultan know you are here?" Ta share min hawaye tace "I will tell you all about it later. Now let's pray for the dead" ta ringa jero adduoi muna amsawa. Na aika Zainab ta kira Hafsat, sai gasu tare da Amina, suka zo suka gaishe su. Haka mutane suka ringa shigowa suma gaishe da Ummee, wasu ma tsegumi ne yake kawo su. Hajja ta fara mita "idan nace sayar da yaran nan akayi sai ace min ba haka bane ba, in uta Hafsat ance balarabe ta aura to ita kuma maimuna fa? Ita data auri bahaushe menene hadin ta da larabawa?" Daga Mommy har Inna babu wanda ya tanka mata, ni dai ina nannade a jikin ummee ina lussafin ya akayi ta baro saudiyya ta taho Nigeria har tazo 'yalleman. Sai bayan sun ci abinci sun huta sannan na dauki waya ta na zagaya baya na kira sultan, yana dauka nace "kasan da zuwan Ummee kuwa?" Yace "wacce Ummee kike magana akai" nace "Ummee dai tamu, gata nan a dakin Inna" dariya yayi kadan yace "Moon rasuwa fa akayi, why are you making jokes" na koma na leka dakin ta taga na ganta akan sallaya tana addu'ah nace masa "wallahi va tsokanar ka nake ba Ummee ce suka zo da su Nani daga Abuja" ya kashe wayar, na koma dakin still ina kallonta, tayi min murmushi ta nuna min kusa ta ita alamar inzo in zauna. Da la'asar su Nani suka koma, amma banda Ummee da Huda, Ummee tace "sai gobe daddyn sultan zai zo sai mu tafi tare" ni dai kawai kallonta nake da mamaki. Sai bayan mun raka su mun dawo sannan nace mata "Ummee sultan fa bai san kinzo ba" tace "eh, bai sani ba" nace "dan Allah in kira shi ya ganki?" Ta dan dungure min kai tace "wai ke nan mai miji ko?" Na langwabe kai ina rokonta, tace "Ok, da daddare sai yazo mu gaisa, yana ina?" Nayi mata bayanin yana gidan nuraddeen, a can ya sauka.
Sai daga baya mutane suka gane Ummee surukata ce, sai kuma aka koma gulmar yadda muke da ita babu alamar sutukuta. Mommy sosai ta karbi Ummee suna ta hirar su, daga dukkan alama tasu tazo daya, ballantana nasan Mommy da son 'ya'yanta, soyayyar da taga Ummee tana nuna min ma kadai ya isa itama ta so ta. Da daddare bayan an watse sai few mutane, na kai Ummee palon waje, na kira sultan. Yana shigowa tsayawa yayi yana kallonta ya kasa magana, ta tashi ta rungume shi da sauri "my little love, how was the honeymoon?" Muka kalli juna ni da sultan, tace "do you guys enjoy Maldives?" Tayi dariya ganin yadda mukayi da fuskokin mu ta zauna muma muka zauna muka saka ta a tsakiya tace "kun dauka wai bamu san inda kuka tafi ba? Maldives kukaje, kuka sauka a hotel din soneva jani, cabin no 12" sultan ya bata rai "saka wa kikayi aka bi mu?" Tayi dariya tace "bani na saka ba, babanka ne, tun sanda kace masa zaku tafi ya aika wani a can Riyadh ya tsaya a airport yaga wanne plight kuka hau ya gaya masa, sannan ya kira Maldives din ma ya saka wani ya jira ku a airport yaga saukar ku kuma ya biku har hotel din da kuka sauka sannan ya gaya masa" sultan ya mike tsaye ya fara zagaye dakin "shikenan yanxu mutum bashi da private life kenan" ina dariya a raina ina cewa "sultan har yanzu America bata barka ba". Ya dawo ya zauna yana kallonta yace "to ya akayi kika taho Nigeria kuma keda akayi banning from leaving Saudi" Tace "They can't stop me from coming to Nigeria if am married to Nigerian".
Lol, we have new amarya in town.

Episode Ninety Five : The Light
Muka kalli juna ni da Sultan sannan muka kalleta, she was blushing, Sultan ya mike tsaye bacin rai a rubuce a fuskarsa yace "wait, what? Aure? Who did you marry? Kawai dan ki zo Nigeria sai kiyi aure?" Duk kallonsa muke yi daga ni har Ummee, ya fara zagaye palon yana magana "koma waye i will have nothing to do with him. Tunda kin aure shi ya kawo ki Nigeria shikenan mission accomplished, ya sake ki kawai ki dawo gidana ki zauna, in ma ba kya son zama a gidana sai in sai miki wani gidan ki zauna, but I don't want to see any man near you" ni kam dariya kamar zata kwace min ganin yadda ya hakikance yake fada, lallai kishi kumallon maza, lol, tabbas da ace Ummee tayi aure da anyi drama da sultan. Ummee tace "sultan you shouldn't judge people before you get to know them, give him a chance, yana da kirki sosai, you will like him" da sauri yace "I won't. Kuma ma nasan tunda da gaggawa akayi auren yanzu haka baki gama sanin halinsa ba, he may even be a 419 guy for all we know, ko kuma ma arm robber, Nigerians are not like Arabs, ba'a saurin trusting mutane anan Ummee" she was calm duk wannan fadan da yake yi, tace "Sultan I know him tun kafin musan zamu haife ka, zan iya cewa I knew him more than anyone a wancan lokacin, kuma har yanzu ma he hasn't change a bit" ya tsaya da zagayen da yake yana kallonta, sai a lokacin dariya ta kwace min, ya juyo yana kallona fuska a daure yace "menene abin dariya kuma?" Na tsaya da dariyar da nake nace "sultan, Ummee is trying to tell you cewa sun mayar da auren su ita da Takawa" ya dan jima yana kallona inayi masa murmushi, sai kuma ya juya ya kalli Ummee, ta gyada masa kai, a hankali kuma kamar kazar da kwai ya fashewa a ciki sai ya dawo ya zauna a kusa da ita, ta saka hannu tana shafa gashin kansa, tace "you look so much kike your father when you are angry" yace "amma Ummee me ya faru? Ji nake fada kuke yi da Takawa" ta danyi dariya tace "dama can kullum fada muke yi dashi, he is so stubborn and hot headed like you" ya kwantar da kansa a kafadar ta yace "I love you, Ummee" na mike a hankali na koma cikin gida, ina jin dadin auren Takawa da Ummee a raina amma deeply kuma ina alhinin rashin Baffa.
Washe gari da wuri Takawa yazo, da jiniya da hakimai da dogarai da komai yazo, Allah bai yi zasu gaisa da baffa ba. Kofar gidan baffa kuwa ya cika taf da mutane sunxo ganin sarkin abuja. Ya jima a gurin su Daddy sannan ya aiko aka kira ni, muka tafi tare da mata da yawa muka gaishe shi yayi mana gaisuwa sannan muka dawo cikin gida. Bayan azahar aka aiko su Ummee su fito zasu tafi, Ummee dama ta shirya amma muka nemi Huda muka rasa, gashi kuma ta bar handbag dinta da wayarta a ciki ballantana a kira ta, ni da Amina muka fita daki by daki muna nemanta amma shiru, gashi ana ta jiransu a waje, na zagaya bayan dakin hajja inda take 'yan shuke shuken ta kawai sai na hango hijab din huda a bayan katanga, na kara sauri sai na hango tare suke da wani namiji, gaba na ya fadi, na shiga ni maimunatu, kar dai munir ne ya ja 'yar mutane bayan gida zai lalata musu yarinya inzo inji kunya, ga mamaki na ina zuwa sai na ga Faruk, na tsaya ina kallonsu duk basu san ma nazo gurin ba, faruk ya karkace a jikin jini yana ta zuba mata tsari ita kuma ta sunkuyar da kai kasa tana ta murmushi, nayi gyaran murya, suka juyo a tare suna kallona, da sauri ta ja hijab dinta ta rufe fuskarta shi kuma ya juya baya yana shafa keya, nace "ki zo ana jiranki zaku tafi" sumi sumi tazo ta wuce ni, bance masa komai ba na juya zan tafi, ya biyo ni da sauri, "ammm...... dama wai bata san kayan lambu ba shine nake nuna mata" ba tare dana kalleshi ba nace "to" a raina nace 'maida karuwa 'yar iska' wai dan karamin faruk din nan nr har ya girma shima zai fara tsara 'yammata, sai kuma na tuno cewa yanzu fa service yake yi, dan haka ya girma kenan. Duniya kenan.
Muka fita rakasu sultan yana ta bacin ran Takawa yace tare zasu koma, ni kuma sai anyi sadakar bakwai sai mu taho tare da su Mommy. Na san dan dai babu yadda zaiyi ne, gashi ko wata sallamar kirki bamu yi ba. Motar Takawa suka shiga, shi yana gaba kusa da driver, Takawa da Ummee suna baya a tare. Sai kawai na samu kaina da murmushin jin dadi. Suka shiga motocinsu suka tafi mu kuma muka koma gida. Ranar da Baffa yayi kwana biyar da rasuwa Amira tazo yi mana gaisuwa, ita da Mama da wata aunt din ta. Sun jima sosai sannan sukayi shirin tafiya, mun taho rakasu ni da Hafsat da Amina muna dan tafiya a hankali muka bar su mama suka yi gaba, ina ta studying Amira, she looks happy. Nace "how are you?" Tace "actually am great. Yanzu na fahimci family is everything, babu abinda yafi dadi irin ka ganka a cikin 'yan'uwanka, yanzu a kano duk inda na kalla hagu da dama duk 'yan'uwana ne, kuma rashin zama a cikin su tun farko shi ya saka nake ganin kamar basa sona ashe abin ba haka yake ba" nace "ya angon naki kuma yazo?" Nan take naga wani murmushi ya shi kadai ya isa amsar sauran tambayoyin nawa, tace "yazo, bai jima ba ya koma, da yake karatunsa yazo karshe ne abubuwa sundan shige masa gaba" nace "and" tace "he is OK. A bit different though, mamansa shuwa ce, kuma kamar duk ita yayo, so technically za'a iya ce masa shuwa. He is really nice, a doctor, kuma naji dadin yadda ya karbe ni" na tsaya ina kallonta wani tunani yana zuwa min raina, nace "wait, ya sunan sa?" Tana kallona da mamaki tace "Mahdi" sai kuma ta rufe baki tace "oh my God, kin san shi ashe, Oxford yake yi kuma medicine" nace excitedly "Mahdi was my best friend a Oxford. Congratulations Amira. Mahdi is the best husband that you can ever wish for" nan muka rabu da alkawarin next time idan muka hadu zan bata labarin rayuwar makarantar mu da mahdi. Bayan sun tafi na zauna ina tunanin hukuncin ubangiji. Tayi ba dai dai ba a rayuwa amma kuma tayi nadama, mun yafe mata mu da ta bata wa, Allah ma sai ya yafe mata, sannan kuma tazo ta farantawa mahaifiyarta rai ta hanyar bata zabin mijin da zata aura, sai ubangiji yayi mata zabin alkairi ya bata Mahdi, wanda ni a ganina yafi Amir din da da na dauka zasuyi aure, ya kuma fi Abbas din da naso hada ta dashi. Allah kenan.
Ranar sadakar bakwai Ibrahim yazo yi mana gaisuwa, dama Amina tace min yazo dashi akayi jana'iza. Muka fita gaba daya dasu Hafsat yayi mana gaisuwa, sam babu wani special treatment daya bani, idonsa suna kan Aminan sa. A ranar muka taho gaba daya har Daddy, Amina kadai muka bari acan saboda 'yan shirye shirye da zata yi saboda bikin su yanzu saura sati uku. Su inna sun so a daga bukukuwan amma mazan gidan suka ce babu wani abu, sai dai an yanke shawarar Abuja za'a tafi ayi bikin gaba daya a can. Muna zuwa Abuja gida muka wuce, Sultan yayi ta nacin in taho gida amma naki, saboda ba karamin gajiya nayi ba kuma nasan ina komawa gida sai ya karamin wata gajiyar. Da kyar na samu na lallabashi ya hakura ya barni na kwana a gida. Tunda muka sauka a gida daga ni har Hafsat muka baje cikkuna a gado muka yi ta bacci. Washegari bayan sultan ya taso daga office ya biyo muka tafi. Naga duk ya chanja a kwana biyar din da ban ganshi ba, he looks so calm and happy, loneliness din da nake gani kullum a idonsa is now totally gone, a raina nace lallai duk duniya babu abinda yafi iyaye dadi, komai girman mutum, komai arzikinsa, komai yawan matansa da 'ya'yansa, soyayyar iyaye daban ce, ballantana ga sultan wanda da bai san taba, dan haka yanzu kara'i ake masa. Ina shiga motar ya matso ya jawo fuskata ya fara kissing dina, na barshi yayi dan kansa ya hakura, yace "damn it baby girl, I missed you" nace "ina kayi missing dina bayan nasan kana can Ummee tana goya ka da zani" yayi dariya yace "da ace zan tsaya da sai ta goya nin ai" na taya shi dariyar nace "how is she?" Yace "tana can tana shan amarci" na dungure masa kai nace "Ummeen kake gaya wa tana amarci ko?" Yace "in munje zaki gane wa idonki ai".
Muna shiga naga gidan gaba ki daya ya chanza min, gaba daya an chanza masa traditional setting din sa an mayar da shi modern. Part din Takawa in ka shiga ba zaka dauka a Nigeria kake ba saboda haduwarsa, anan kuma ummee take, basu wani raba dakuna ba. Komai wayewar ka in ka shiga gurin sai kayi kallo. Da sauri Ummee tazo ta rungume ni tana min sannu da zuwa, ta sunkuya kusa da cikina tace " Hello dear, welcome back home" daki daki sai da ta shiga dani ta nuna min, master bedroom ne naki shiga, ina suruka ina ganin makwancin surukai?, lol. Part din Hajiya yana nan yadda

Please Login or Register in order to submit comment