Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yake, tana nan kuma har yanzu a ciki, amma kuma a kusa da gurin anyi wa su saratu sababbin dakuna suma, an kawata musu gurin gwanin ban sha'awa. Sultan yana ta tabani wai in tashi mu tafi amma Ummee tana ta zuba min hira, tana tsara min yadda aka tsara bikin Amir wanda za'ayi next week. Ban tambayeta labarin yadda aka mayar da auren su da Takawa ba ita ma kuma bata gayamin ba. Muna ta hira har akayi sallar magrib, sultan ya fita masallaci mu kuma mukayi anan, tare suka dawo da Takawa, ni dai yana shigowa kaina a kasa na gaishe shi, ya amsa min sosai harda tambayata ya karin hakuri, na dago kaina na amsa masa "Alhamdulillah" and he smiled, this is the second time dana taba ganin murmushinsa. He looks different shima, he looks happy, har wani haske naga yayi da wani annurin fuska irin na angwaye. Tare muka ci abincin dare, ni dai duk a takure naji ni. Su kam hirar su suke yi sosai, Ummee sai dariya take yi, she looks so happy, basu da wani problem in the world, komai yayi farko yana da karshe, duk wata wahala da mutum yake sha a rayuwa mai wucewa ce, musamman idan kana kan gaskiyar ka, musamman idan baka zalinci kowa ba, to ka tabbatar cewa ubangiji yana sane da kai, kuma He has a special plan for you. Allah yasa mu dace.
Muna zuwa gidan mu a palon farko na tarar da baba gaji da 'yammatanta, bakunan su har kunne suna murnar dawowa ta, gidan kal kal kamar banyi tafiya ba, ko'ina sai kamshi yake yi. Na zauna duk suka zo suka gaishe ni kuma duk na ambaci sunayensu, suka dauko kayayyaki na suka kai min dakina, zasu kawo min abinci nace musu na koshi. Anan palon na baje dani da cikina muna hutawa, sai da na gama hutawa sannan na tashi na tafi part dina. Ina tura kofar corridor naka duk fitulun gurin a kashe, amma kuma ga haske nan yana fitowa daga kofar da take facing dina, kofar dakin da sultan ya gina a matsayin our baby's room, ni dai a sani na dakin a rufe yake tunda aka kawo ni ba'a taba koda bude shi ba saboda babu komai a cikinsa. Na karasa na tura kofar naji ta a bude, ina shiga naji kida a hankali yana tashi, irin wakokin nan na lullaby. Ido na bude ina kallon dakin, exactly irin dakin da na taba gani a cikin system din Ummee a Riyadh. A zahiri ma sai naga yafi kyau akan hoton. Kadan ne ya rage ban saki kara ba saboda mamaki, hannuna yana rawa na dauko wayata na kira sultan, "sultan baby's room din nan yayi kyau sosai" yace "what baby's room?" Nace "gashi kuwa, an gama an saka komai" da sauri yace "wait a minute, gani nan zuwa" bai fi minti biyu ba sai gashi ya shigo, ina nan tsaye har yanzu a inda nake ina kallon dakin, komai na dakin blue ne, sai shades din ne wani mai duhu wani mai haske, an saka komai tun daga labulaye da capet, baby crib da drawers, da sofa guda daya da breastfeeding pillows a kanta, ga playpen da toys da yawa a ciki, baby swing, baby carrier, trolley, walker, feeders da starilizer, hatta tissues babu abinda babu a dakin, na karasa na bude closet din dakin, nan ma wani mamakin nasha, kayan baby ne fal a ciki, wadansu anyi hanging wadansu an jera su a lockers, kuma abin burgewar shine yadda akayi arranging kayan according to size, from newborn, sai 1-3 months, sai 3-6 months, 6-9 months, haka har 5 years. Diapers da wipes kuwa ina jin sai mun shekara bamu nema ba. Na juya na rungume sultan nace "oh sultan, it is beautiful" yace "I have no idea yaushe aka hada dakin nan" na dan cika shi ina kallonsa nace "nasan waye, Ummee ce" ji nayi kawai babu abinda nake so irin inga na haihu na fara kula da baby na, har wata kwallar dadi naji tana bin idona, ya ilahi, bansan ta inda zan fara gode wa Allah ba. Na saka hannu ina shafa lallausan bargon da aka shimfida akan crib din, a lokacin ne ido na ya hango pictures din da aka rataye a both sides din gadon, daga hannu dama hoton wani baby ne, na dauka ina kalla, sultan ne yana baby, with his red lips, ya tabe baki irin yadda babies suke yi in zasu yi kuka, dariya na kama yi, yazo ya karba shima yana dariya, na lakuce masa hanci nace "daga gani dama kai rigimamme ne kana baby" ya dauko picture din barin hagu shima yana kalla, ni ce nima ina baby, nayi murmushi dimples dina duk biyun sun lotsa, ya saka hannu yana shafa fuskata a hoton, nace "see? In dai babyn nan yayi rigima to kai ya dauko" ya ajiye hoton ya juyo yana kallona yace "idan kuma yayi surutu fa? Da shagwaba, da son jiki?" Nace "oho, wannan kuma bansan wa yayo ba" ya jawo ni jikinsa ya rungume ni ta baya yana dan juyi damu yace "kin san lissafi nake yi yau in kin huta gobe zamu fara shiga kasuwa siyayya?" Nace "ai mu yanzu 'yan gata ne, komai yi mana ake yi" ya yi murmushi yace "yeah, you are right. Ni fargaba ta daya, kada a haifi babyn nan su dauke mana shi su hana mu" nayi dariya nace "shikenan sai mu bar musu shi mu haifi wani". Hmmm kawai yace min. Na dauko waya ta nayi dialing number din Ummee, sultan ya gani yace "ke cikin daren nan zaki kira mata tana dakin mijinta" na harare shi, tana dauka nace "oh Ummee, it is beautiful" tayo dariya tace "har kun gani kenan, do you like it?" Sultan ya zuro kansa yace "we love it Ummee and we love you" ina jiyo dariyar Takawa a background, a raina nace 'dama yana dariya?' Ummee tace "we Love you too sweethearts. Yanzu saura abu daya ya rage" nace "Ummee komai komai ya kammala babu abinda yayi saura kuma" tace "akwai. Addu'ah. Addu'ah ita zamu saka yanzu a gaba muyi tayi ba dare babu rana. Allah ya sauke ki lafiya ya kawo mana new little love lafiya" sultan yace "what? Ummee sunana ne fa?" Tace "daga ranar da aka haife shi za'ayi maka retire, amma before then, you are still our little love, so enjoy it while it last" mukayi dariya a tare, tacigaba da cewa "maimunatu daga yanzu ki dage da cin dabino sosai, sannan kike cin abinci sosai kuma mai kyau wanda zai kara miki karfi da lafiya. Sannan abu na karshe ki tabbatar kullum wayarki tana kusa dake kuma ki tabbatar akwai kudi a ciki kuma akwai chaji. Hospital bag din ku tana gurina, na hada miki kayanki dana baby wanda zaku bukata a asibiti. Allah ya sauke ki lafiya." Sultan yace "Ameen" nima na fada amma a raina, ya karbi wayar ya kashe. Ranar a dakina muka kwana, sultan sai da ya karbi dukkan bashin daya ke bina, nima kuma haka, dan nima ina son mijina. Na kwanta a jikinsa ina shakar kamshin sa da nayi missing kwana biyu, ya taba cikina da yake ta mutsu mutsu yace "kai fa na lura kiriniya ce da kai, to ka sani, wannan wasan bana yara bane ba, ga playpen dinka can Ummee ta sayo maka da toys dinka, sune abokan wasan ka ba mu ba, idan Mommy da Daddy suna yin wani abu yara basa zuwa gurin" nayi dariya ina shafa kansa nace "idan bai yi kiriniya ba ai sai Allah ya tambaye shi" ya dan bata rai yace "yarinyar nan naga alama kinga gurin kwana na shi yasa kika raina ni, zanyi maganin ki ne, dan kinka yanzu ina dan daga miki kafa ko? I will be back to my normal self and sai kin raina kanki" kafin muyi bacci na tambayi sultan "wai Ummee ta dade a garin nan ne har ta shirya dakin can?" Yace "watanta daya da sati daya a Nigeria yanzu" sannan ya bani labarin abinda ya faru bayan tafiyar mu daga Riyadh.

Episode Ninety Six : The New Bride
Riyadh; bayan tafiyar su Moon;
A hankali Ummee ta juya ta koma cikin gida, tana shiga palon kawai taji gaba ki daya ta tsani gidan kuma, ta tsuguna anan bakin kofar tana jin hawaye yana fitowa daga idanunta. Ta jima a haka sannan taji karar wayarta kamar daga sama, da bata yi niyyar tashi ta dauka ba dan she is in no mood for chitchat, sai kuma tayi tunanin ko moon ce zata gaya mata wani abu, dan haka ta tashi da sauri ta karasa gurin yawar ta dauka, number din Nigeria ta gani, bata san number din ba amma jikinta ya bata ko waye, ta ajiye wayar bata dauka ba a ranta tana cewa 'duk laifin ka ne ai, muna zaman mu ka jawo gashi nan sun tafi sun barni ni kadai' ta zauna akan kujera tana lissafin abinda zata yi kuma, sai ta sake jin karar wayarta, wannan number din ce dai, Sadiq ne, tun da suka rabu ranar nan da daddare a abuja shekaru talatin da suka wuce bata kuma jin koda muryarsa ba sai dazu. Da taso shi kamar rai, son da ya saka har ta guji iyayenta ta aikata abinda bata taba tunanin zaya iya aikatawa ba, amma ta aikata saboda shi. A lokacin daya aiko mata da takardar saki kuma ji ta yi a ranta kamar duk duniya babu wanda ta tsana kamarsa, amma duk da haka duk tsahon shekarun nan, babu wani namijin data taba kalla da sunan namiji, ga larabawan nan, kyawawa na ajin karshe, amma duk kallon mata take musu a idonta, bata jin da akwai wanda zata iya sakawa a matsayin data sakashi a da. Sai kuma ga Maimunatu tazo mata da labarin cewa duk abinda ya faru baya cikin hankalinsa, sakin da yayi mata ma bai ma san ya sake tan ba, asali ma, bai ma san da ita ba all these years. Ga kuma labarin wahalar da sultan yasha a hannunsa. Sai ya zama ta kasa tantance taka mai mai me take ji a dangane dashi. Shin haushinsa take ji, ko tsanarsa tayi ko tausayinsa take ji. Wani kiran ya sake shigowa, ta daga wayar a hankali ta amsa, ta saka a kunnenta amma kuma sai ta kasa magana, to me zata ce masa? Shima daga daya barin maganar ya kasa, sun jima a haka suna sauraren numfashin juna, shekara talatin ba kwana talatin bane ba. Ya lumshe idonsa yana picturing dinta a ransa, sannan murya cikin makogwaronsa yace "how are you, Khairat?" Taji kiran sunan ta da yayi har cikin ranta, da akwai wani tone da yake kiran sunan ta dashi wanda shi kadai ne yake kiranta da hakan, all those thirty years melted in her heart. Ta dan gyara muryarta kadan dan kar ya fahimci yana da wani effect a kanta yace "They are gone, sultan and Moon, bansan inda suka tafi ba" yace "Sultan is a big boy, He will take care of them. Am asking how are you" ta goge hawayen idonta tace "am fine. Am a strong woman now. I have been taking care of myself for thirty years, I can take care of my self now, I don't need you" bai damu da abinda tace ba yace "then why are you crying?" Tayi shiru dan bata dauka zai gane kuka take ba, ya sake cewa "why are you crying, Khairat?" Nan take kukan ya taho mata gaba daya, tayi tayin kayanta bai hana ta ba, har da sheshsheka, sai da ta gama kayanta ta goge hawayenta sannan ya sake yin magana, muryarsa tayi masa nauyi sosai, yace "do you want me to come?" tace "I want my son. I want Sultan. I am tired of living alone. Sultan yayi fushi sun tafi sun barni ni kadai. Ban san inda suka tafi ba" kamar baiji abinda ta fada ba ya sake maimaita tambayar da yayi mata "do you want me to come?" A hankali tace "yes, yes I want you to come" yace "then I will come, I will come for you like I promised. Am sorry I kept you waiting" tace "Sultan ban san inda suka tafi ba" ya dan jima yana tunani sannan yace "zan saka a duba su anan airport din, duk inda zasu je dai nasan jirgi zasu hau, in kuma basu hau jirgi ba to suna cikin kasar nan. Daga nan zamu san inda suka tafi sai mu neme su a can" ta gyada kai kamar yana kallonta, yace "shikenan hankalinki zai kwanta ko Ummeen Little Love?" Bata ce komai ba, yace "I will come to Riyadh jibi insha Allah" ji tayi zuciyar ta ta fara bugawa da karfi, ta kashe wayar tana kallon screen din wayar, jibi? Two days kenan? Anya kuwa zata iya ganin sa? Ya yake yanzu? Ta tuna cewa yanzu shi sarki ne, yayi aure bayan rabuwarsu har ya haifi yara biyu, how much has he changed? Is he still the Sadiq she knows ko kuma ya koma total stranger?
A cikin kwana biyun da tayi tana jiran zuwansa har sai da ta rame saboda tunani, wani lokacin sai zuciyarta ta gaya mata ta kirashi kawai tace masa kar yazo yayi zaman sa, tunda in yazo ma mai zai yi mata? Babu wani abu a tsakanin su yanzu, ta tabbatar babu sonsa yanzu a zuciyarta, bata jin haushinsa dai irin da amma bata sonsa, duk sanda tayi wannan tunanin kuma sai ta tsaya ta tambayi kanta, anya kuwa? Amma kuma tana da tabbacin cewa shi babu wani abu a ransa a game da ita, zai zo ne dai akan maganar dan su, amma koma menene a tsakanin su is now over. Ya gaya mata yayi tracing su sultan, dan haka yanzu bata da fargaba a kan su, tasan they are safe. Ranar da zai zo ta gyara masa guest room, amma kuma sai ta tsaya tana tunanin bai kamata ta sauke shi a gidan ta ba tunda ita kadai ce a gidan, sai kuma tayi tunanin mai yasa take wannan tunanin a kansa bayan babu komai a tsakanin su. Bai gaya mata karfe nawa zai baro Nigeria ba dan haka bata san karfe nawa zai sauka ba, ita kuma bata tambayeshi ba, so she get ready, sits down on the sofa and waited, with her hands between her thighs. Akayi asahar ta tashi tayi sallah ta dawo ta zauna, akayi la'asar ma haka, magrib tazo itama ta wuce, sai da taji ana kiran sallar isha sannan hawayen da take ta rikewa ya fara gangarowa daga idonta, he is not coming, he is never coming. Ta mike a hankali ta koma bedroom dinta. Tana idar da sallah taji karar wayarta, sai da taji kirjinta ya buga, ta mike ta dauki wayar tana saka ran ganin 'sultan's dad' kamar yadda tayi saving number dinsa, amma sai taga number din mahaifiyarta. Ta zauna a bakin gado ta dauka da sallama. Tace mata "ki zo yanzu ki same mu a gidan babanki Umar" daga nan ta kashe wayar. Ta ajiye wayar ta rike kanta da hannu biyu, ya salam, me ya faru kuma? Kar dai ace sun gano cewa sun shirya da Sadiq zai zo gidanta, tasan halin uncle Umar sosai, abu na farko da zai fara yi shine zai karbe gidanta yace ta koma gidansa da zama. Amma kuma sanda ta kai masa sultan ai bai nuna wani abu ba, nuna wa yayi kamar komai ya wuce. Bata da zabi, duk da shekarunta amma bata kinyin abu in iyayenta sun gaya mata. Dan haka ta tashi ta tafi. Babu kowa a kofar gidan dan haka ta shige cikin gidan direct, tana gaisawa da matan gidan suka gaya mata ta shiga palon uncle din nata ana jiranta, ta gyara lullubin ta ta shiga da sallama. Gabanta ne ya fadi ganin mutane da dan yawa a palon, ba tare data tsaya kallon waye da waye ba ta shiga, ta zauna daga nesa akan carpet ta fara gaishe su. Sai a lokacin ta lura da akwai bakin fuska a dakin, ta tsaya da gaisuwar da take yi tana kallon su, duk da sun dan juya bayansu daga inda take zaune amma ta gane shi ta yana yin zamansa, ya harde kafafuwansa ya zauna a kansu, tun sanda ta san shi haka yake zama duk sanda zai zauna a kasa ba'a kan kujera ba haka yake zama, kuma taga sultan ma haka yake zama, Sadiq ne, he is here. Bata gaishe su ba daga shi har abokin rakiyar tasa , ta karasa gaishe da iyayenta ta zauna kanta a kasa tana jiran taji ta ina za'a fara yi mata ruwan bala'i.
Abokin tafiyar Takawa ne ya bude taron da addu'ah, ya nemi zabin ubangiji akan duk maganganun da za'ayi a gurin sannan kuma ya nemi tsarin ubangiji daga shaidan da mukarrabansa. Yana gamawa Takawa ya fara magana cikin larabci da jefi jefin turanci, yace "sunana Sadiq Abdallah. Ni bakar fata ne mutumin kasar Nigeria. Ni tsohon mijin 'yarku ne Khairat kuma ni ubane a gurin tilon danta, Abubakar. Nazo ne gabanku yau ina neman afuwar ku akan abinda na aikata na rashin kyautawa a gare ku shekaru talatin da uku da suka wuce, sannan ina neman alfarmar a mayar mana da auren mu ni da matata idan kun amince" ya juya ya kalle ta cikin ido, yace "idan itama ta amince" shiru dakin yayi na tsahon lokaci. Khairat kam gaba daya kanta ya toshe , what is he doing? An jima bayan ya gama uncle Umar ya fara magana wacce take cikin larabci mai chakude da turanci "assalamu alaikum. Babu abinda zan iya cewa yau sai Alhamdulillah. A lokacin da Sadiq yazo neman auren khairat a gurina yazo ya nema, amma a lokacin na shafa wa idona toka ba tare da na bashi dama ba nace bazan bashi ba, saboda ina ganin zai zama abin kunya mu aurar da 'yar mu ga wanda ba balarabe ba, ban duba cewa a cikin abubuwan da ubangiji yace a duba kafin a bayar da aure babu kabila ko kalar fata ba, na tauye hakkin sji Sadiq din sannan kuma na tauye hakkin ita khairat din, dan haka zan iya cewa duk abinda ya faru nine sila, saboda na tsallake tsarin addini nabi son raina, wannan shine ya jawo 'yar mu ta bijirewa umarnin mu tabi saurayi ta gudu daga kasar a wancan lokacin, tun a lokacin nasan cewa laifi nane amma pride ya hanani inyi admitting, sai muka tattara laifin duk muka dorawa shi yaron da yazo ya dauke mana yarinya, muka sha alwashin sai munga bayansa. Abin kunyar da nake gudu kar ace mun aura wa 'yar mu wanda ba balarabe ba sai ya zamanto gwara shima akan abin kunyar da muka fuskanta, cewa 'yar mu ta gudu ana gobe daurin aurenta ta shiga duniya. Wannan yasa muka kara kaimi gurin nemansu dan muga mun goge mugun suna a gurin mutane, kuma amma bamu same suba sai bayan shekara uku, sai a lokacin muka fahimci shima yaron dan babban gida ne, jinin sarauta ne, amma duk da haka maimakon mu zauna ayi maslaha sai muka dauki damarar sai mun nuna masa kuskurensa, muka je har gidan aurenta a gaban surukanta da mijinta muka dauko ta, muka raba ta da mijinta muka kuma rabata da dan jaririn danta. Amma Allah shine shaidar mu, bamu taba tsammanin raba sun da mukayi zai tabbata ba, mun raba su ne saboda mu hukuntasu a bisa abinda suka aikata, tunda har 'da ya shiga tsakanin munyi niyyar zamu hakura mu barsu. Amma sai yazo ya same mu ya bamu hakuri kuma ya nemi aurenta properly yadda kowa zai tabbatar cewa aurar da 'yar mu mukayi ba wai duniya ta shiga ba. Munce zamu hukunta shi idan yazo, amma mun san duk wanda yake da courage din shiga gidan mutane ya dauki 'yarsu ya gudu da ita to tabbas yana da courage din fuskantar hukunci a kanta. Amma kuma sai muka tarar da sabanin hakan, maimakon yazo din kamar yadda muka saka rai sai ya aiko mana da takardar sakin ta. Wannan shine abinda yafi komai kona mana rai, mu ana babban cin mutunci shine a auri 'yarka sannan kuma a sake ta. Ga kuma tashin hankalin da yarinyar ta shiga a dalilin sakin da akayi mata, da raba ta da danta da akayi. Tayi ta kokarin komawa amma muka hana ta saboda mu a gurin mu zubar da darajarta ne ace ta koma gurinsa duk kuwa da sakin ta da yayi, pride din mu ya saka muke ganin cewa shi ya kamata ya neme ta ba ita ba. Shi ya kamata yazo ya bata hakuri, ya bamu hakuri gaba daya. To Alhamdulillah yanzu gashi yazo, kuma ya bamu hakurin, kuma mun hakura, sauran magana kuma ta rage tsakanin sa da ita, in ta amince shi kenan ko a gobe sai a mayar musu da auren su".
Tunda aka fara maganganun, khairat kanta yana kasa, tana wasa da 'yan yatsunta, ji take tamkar mafarki take yi amma kuma gashi kamar gaske. Bata dawo daga tunanin taba taji ana ta fita daga palon, zata tashi auntyn ta tace "ki zauna kuyi magana tukunna, zuwa gobe sai ku fadi shawarar da kuka yanke" ta koma ta zauna zuciyarta tana bugawa, tayi sauri tayi wa kanta fada "why are you behaving like a teenager? Ke da za'a haifawa jika very soon?" Nan take ta maida hankalinta guri guda ta juyo tana fuskantar Sadiq da abokin tafiyarsa, sai yanzu ta kalli abokin Sadiq din sosai, he looks familiar, and he also looks like maimumatu and Hafsat, shi ya fara gaisheta, ta sunkuyar da kanta kasa ta gaishe shi itama, ya amsa, sai kuma suka yi shiru, ya mike tsaye yace da Takawa zai jira a waje, har yakai bakin kofa tace "You are Maimumatu's Father, right?" Ya juyo yana murmushi yace mata "that's right" tayi dariya tace "Ina Fatima? Ya baku taho tare ba?" Yana murmushi yace "zata zo itama, maybe daukan amarya zata zo, tunda ni nazo daurin aure" sai kuma taji kunya ta sunkuyar da kanta, shi kuma ya fita. Sun jima bayan ya fita babu wanda ya ce komai, sannan Takawa yace "so..., Fatima zata zo daukan amaryar a gaya mata ta shirya ko kuma ba zata zo ba a gaya mata tayi zamanta?" Ta dago suka hada ido, he looks just as she imagined he would, older, stronger and very confident, but then he is still the Sadiq she knows, the Sadiq she fall in love with, her husband, the father of her son, it feels like not a single day has passed. It feels like kamar dazu ne aka tashe su daga bacci aka ce su je ana kiransu a palon Takawa marigayi.
Sati daya chif bayan nan aka mayar da auren Sadiq Abdallah da Khairat Faisal Abdallah. Daurin auren ya samu halartar kafatanin 'yan'uwa da abokan arziki daga barin khairat, a bangaren Sadiq kuwa jirgi guda aka chika da manyan mutane daga Nigeria suka je suka halarci daurin auren. Abin ya kayatar sosai. A take mujallu da jaridu na duniya suka yi ta watsa labarin auren saboda ana ganin wani karin kulla zumunci ne a tsakanin kasashen musulmai. Wannan tamkar wani ci gaba ne ga musulunci da musulmai baki daya. Ana gama daurin aure ango ya dauki amaryarsa suka tafi umra dan nuna godiyar su ga ubangiji akan dawo musu da rayuwarsu da yayi, da kuma neman taimakonsa akan dukkan abubuwan da zasu saka a gaba. Sai da sukayi sati biyu sannan suka dawo Riyadh, daga nan kuma amarya ta fara shirye shiryen biyo angonta Nigeria amma shi kam ango yace ba zai jira wannan fi'ilin sai amarya ta tare ba dan haka shi kawai sai ya tare a gidan amaryar. Ajjiyar da aka yi masa ta three full decades ya zage yake ta karba. It is like nothing has changed, jin su suke kamar sanda suna America farkon auren

Please Login or Register in order to submit comment