Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

loosing you, gani yake yi kamar kowa is against him" nace "amma Hafsat, upon all what we went through together, ya kamata ace by now ya yarda dani" tace "kin bashi reasons din da zai yarda da ke ne? Mun jima muna tattauna wa da Hafsat a waya, ban ankara ba kawai sai naji wayar ta mutu, ban kunna ta ba kwanta ina lissafa maganganun Hafsat a raina, is what happened my fault? Ban boye wa Sultan maganar cikin nan saboda komai ba sai don ina son inyi surprising dinsa, but I get more than what I bargain for. Naji an fara kiraye kirayen sallah dan haka nasan inna ce zan kwanta bacci zanyi missing din sallah asuba, dan haka na saka phone dina a charge nayo alwala nazo na bude al'qurani na na fara karatu, ina nan har akayi assalatu nayi sallah sannan na kwanta, kafin bacci ya dauke ni na yanke shawarar cewa first thing in the morning zan nuna wa Daddy picture din da Hafsat ta turo min, tunda ya san mahaifiyar sultan zai iya tabbatar min idan itace ko a'a, next thing zan kira Sultan inji halin da yake ciki, my heart can't take hurting him. Amma ga mamaki na ban farka ba sai after 11am, kuma nasan physical and mental exhaustion ne ya kawo min dogon baccin. Ina tashi na kunna wayata, ko wanka banyi ba na saka hijab dina na tafi neman Daddy, a palon sa na same shi shida Mommy, na karasa na gaishe su, Mommy tace "yanzu nake tunanin ko tashin ki za'ayi kichi abinci, sai Daddy n ki yace a barki ki tashi da kanki" na danyi murmushi ina searching picture din da Hafsat ta turo a waya ta, food is the last thing on my mind babu abinda nake so irin inga Sultan, maybe I am weaker than I thought in dai akan soyayyar Sultan ne. Ina samo picture din na karasa gaban Daddy na mika masa nace "Daddy kasan wannan?" Ya karbi wayar daga hannuna sannan ya mike zaune daga kashingiden da yake, ya kalleni sannan ya kuma kallon screen din yawar yace "a ina kika samu hoton khairat? An ganta ne?" Ji nayi wani excitement yana taso min tun daga kafafuwana har cikin kaina, nace "Daddy ita ce mahaifiyar Sultan?" Yace "of cause itace mana, baki ga kamar ba?" Da sauri Mommy ta matso tana kallon hoton tace "Allah mai iko, kamar tasu har ta baci" na tashi da sauri na rungume Mommy ina jin dadi, sai kuma naji kunyar ta na sake ta, Daddy ya tambayeni inda na samu hoton nayi masa bayani, nan suka kara wani mamakin, ikon Allah kenan, wai all this while a she sultan da Zayed 'yan uwa ne babu wanda ya sani. Mommy tace "to yanzu menene abinyi? Zaki gaya masa ne ko zaki bari Hafsat tayi bincikenta a can muji dalilin da yasa duk tsahon wannan shekarun bata nemi danta ba?" Na girgiza kaina , a raina nace "not again, na daina boyewa sultan komai insha Allahu" a fili nace "Mommy zan gaya masa, yana da right ya sani, shi zai yanke decision din me ya kamata yayi" Daddy ya amince, yace "amma ai naga jiya kin kore shi, yanzu kiransa zaki yi? Na dan sunkuyar da kaina ina murmushi, Mommy tace " kar dai kice min shikenan har kin gama horon nashi da zaki yi? Duk kurin zubar da ciki da waye har ya kare kenan, kar ki rako mata mana maimunatu" na rufe fuskata da hannayena, Daddy yace "in kin huce ma ni ban huce ba, sai yazo ya bada hakuri kuma yayi min alkawarin irin haka ba zata kuma faruwa ba. Shi kuma wancan har yanzu fa bai dawo haiyacinsa ba, dan haka nasa anyi wa family dinsa waya a can ibadan an gaya musu halin da yake ciki" bance komai ba saboda bazan iya yiwa Daddy musu ba amma ni kam da zai barni da yanzu zan tafi in kira sultan in bashi labarin mahaifiyarsa, maganar Ibrahim kuma naji babu dadi, it is a pity, naji tausayin mamansa da 'yarsa, a raina nayi masa addu'ar samun lafiya, Daddy yace "ko zaki je ki duba jikin nasa?" Nayi saurin girgiza kaina, there is nothing more between me and him, ni yanzu kawai mijina nake son gani.
Jin basu sake cemin komai ba na gane sun gama magana dani kenan, na tashi na tafi palo ina neman abinda zanci, na faki ido naga babu wanda yake kallona na dauko waya ta nayi dialing number din sultan, amma bansan me zance masa in ya dauka ba, tana ta ringing amma ba'a dauka ba, a raina nace yayi fushi shima, nafara duba messages wai ko ya turo min message ban sani ba, babu message din sultan sai na Amir, na buda na fara karantawa "your husband is sick, kuma ke yake nema" wayar ce ta zame daga hannuna ta fadi kasa, nima na bita na zauna dabas a kasa, for seconds kaina ya toshe, sannan kuma cikin karkarwar hannu na dauki wayar zuciyata tana wani irin bugawa na kira number din Amir, bugu biyu ya dauka yace "Moon ina kika shiga tun safe ina ta nemanki wayarki a rufe. Muna asibiti da Sultan fa bashi da lafiya" cikin muryar kuka nace "Amir me ya samu Sultan? Ya jikin nasa? Amir na shiga uku" yace "baki shiga uku ba Moon jikin Sultan da sauki, dazu dai babu yadda yake amma yanzu ya samu relief, please amma ki zo yanzu in ya ganki zai kuma jin dadi" na saki wayar na dora kuka na daga inda na tsaya, Sultan babu lafiya amma ni ina gidan mu bana tare dashi, kuma am 100% sure cewa ciwonsa dalilin maganganun dana gaya masa jiya da daddare ne, ni maimunatu na shiga uku, in wani abun ya sami sultan I will never forgive myself. My Darling Sultan. He calls me his love but I didn't act like love, bashi da kowa sai ni and I too pushed him away. What have I done? Amina ce ta sauko ta ganni ina ta rusar kuka ta karaso da sauri tana tabani tace "Moon lafiya? Jikin ne?" Ban bata amsa ba ta koma sama da sauri sai gasu tare da Mommy, Mommy hankalin ta a tashe tace "Moon lafiya" na share hawayena nace "sultan ne bashi da lafiya, yana asibiti" tace "kuma dai? Astagfirullah, Allah in laifi muka yi maka ka yafe mana".
Da kyar Mommy ta matsa min nasha tea kadan, shima ina gama sha nayo mata amansa, tunda na samu ciki ban taba amai ba sai ranar nan. Ni duk burina inga Sultan in san halin da yake ciki, duk wani abinci da maganar ciki ne dani su biyo baya, a gurina lafiyar sultan itace a sama. Ganin yadda na tashi hankali na ya saka Mommy tace mu tafi tare da Amina, in an jima ita sai su zo tare da Daddy, ai kam ban jira komai ba nayi gaba, Amina ma a mota ta same ni, muna zuwa asibitin Amina ta kira number din amir ta gaya masa munzo, ya fito yayiana jagora zuwa dakin da sultan yake.
Tun daga window na hango shi a kwance yana bacci. Nayi sauri na bude kofar na shiga. Shi kadai ne a dakin, babu riga a jikinsa amma an lulluba masa bargo har saman kirjinsa, gani nayi ya rame sosai, fuskarsa tayi fari tas. Duniya kenan, wai sultan ne ciwon kwana daya yayi masa wannan kayarwar. A hankali na karasa na dauki hannunsa na rike a nawa, muryata har ta dashe saboda kukan da nakeyi. Amina ta karaso ta dafa ni tana bani hakuri amma ko kallonta banyi ba. Ni kadai na san me nake ji a raina. Ba wai ciwon sultan din ne yake saka ni kuka ba, abinda yafi damuna shine kasancewar nice sanadiyyar ciwon nasa shine abinda yafi damuna. Ban san ma Amina ta fita ba sai dubawa nayi naga bata nan. Na fara yi masa magana a hankali "Sultan ka tashi dan Allah, menene hakan ne wai kai sai kace ba namiji ba zaka wani kwanta ka kama rashin lafiya. Kace ba zaka iya rayuwa babu ni ba, to ka sani nima bazan iya rayuwa babu kai ba, dan Allah sultan ka tashi kace ka yafe min, zuciya ta ba zata iya jurar ganinka a kwance ba Sultan zuciya ta bugawa zatayi in mutu, kaine rayuwata, kaini jinin jikina, kaine mijina kuma uban 'ya'yana. Sultan kayi hakuri, duk abinda na gaya maka wallahi ba da gaske nake ba. Dan Allah ka tashi, sickness doesn't suit you, ga babynmu kuma yana nemanka yana so ku gaisa." Na dora hannunsa akan mara ta na cigaba da cewa "ka ji shi ko? Kwanan nan zai fara motsi, he is going to grow up to be stronger than you, shi ba zai kwanta ciwo saboda sunyi fada da matarsa ba" na dawo da hannun sama na dora fuskata akai hawayena yana bin hannun nasa nace "my poor darling sultan, my sweetheart my honey, my angel my heartbeat, my life my happiness, my husband my babies Daddy" a hankali naga ya fara bude idanunsa, ya sauke su a kaina, they are the same most beautiful eyes I have ever seen, amma sun dan fada ciki kadan, murmushin gefen baki yayi min yace "indai wadannan kalaman za'a ke gaya min in bani da lafiya to kuwa kullum sai nayi ciwo" na saki hannun sa da sauri gaba daya na fada kansa na zagaye wuyan da hannayena ina sake wani sabon kukan yace "ouch, karki ballani mana baby girl, baki san kin zama 'yar lukuta ba yanzu?" Na dan dake shi kadan a kafada nace "kaine dai dan lukuti, mai kwanciya ya kama rashin lafiya kawai" ya saka hannu daya ya dago ni yana kallon fuskata yace "to ya isa haka kukan in ba so kike a baki gado a kusa da nawa ba" na tashi ina goge hawayena, har yanzu idonsa na kaina yace "you look terrible, da wasu jajayen kunburarrun idanuwanki" na dan harare shi nace "in kawo maka madubi ka kalli kanka kaga yadda ka zama?" yace "no, I don't want to see" ya daga bargon jikinsa, naga daga shi sai gajeran wando da singlet, yace "come here, zo in sammiki zazzabi na" ba musu naje na shige jikinsa na kwanta, ji nayi kamar wacce tayi tafiya nai nisa ta gaji sannan ta dawo gida, irin feeling din nan na finally I am home, na sauke ajjiyar zuciya na kara shigewa jikinsa ina jin zafin jikinsa yana ratsa ni, ya dora hannunsa akan marata yana shafawa a hankali, nace "am sorry sultan, for not telling you about the baby, I wanted to surprise you" murya can kasa yace "it is OK" a hankali yace "do you mean all what you just said. Da gaske abinda kika fada min a dakin ki ba da gaske kike ba?" Na girgiza kaina da sauri nace "wallahi ba da gaske nake ba. Am so sorry I said those words" yace "NO, I am sorry, ni nayi forcing dinki ai kika fada min hakan. Am sorry about what I did Nace "it is OK, ya wuce" mun jima a haka, na dauka ma ya koma bacci, sai naji yace "something weird happened da zu. Takawa yazo dubani" na daga kaina ina kallon fuskarsa da mamaki nace "what?" Yace "yes, i don't know me ya faru, amma ina tunanin Amir ne yaje ya gaya masa, sai dai bansan ya akayi yazo din ba, I just woke up and he was here, he held my hand and then he fainted" nace "fainted?" Yace "yes. Komai ya faru ne da sauri bansan menene ya faru ba, yazo nan, ya kama hannuna sai kuma ya suma, suka dauke shi suka fita dashi, sai doctor yazo ya saka na koma bacci, am just not sure whether da gaske abin ya faru ko kuma mafarki nayi" na mayar da kaina na kwantar a kirjinsa ina sauraron bugun zuciyarsa, na danyi tunani kadan akan abinda yace, we will have to ask Amir menene ya faru. Ba tare dana kalle shi ba nima na fara magana "something weird also happened jiya da daddare" nayi shiru kuma na kasa yadda zan fada masa, sai da yayi magana yace "what happened?" Sannan na cigaba da magana "Hafsat ta hadu da Ummeen ka a Riyadh" farko yi yayi kamar baiji me nace ba, sai kuma ya mike zaune da sauri, taking me with him, yana kallona fuskarsa babu alamar dariya yace "me kika ce?" Na jawo yawa ta na bude masa hoton mahaifiyarsa na mika masa, "Sultan wannan itace mahaifiyarka, you and zayed are cousins". A hankali ya karbi wayar yana kallon hoton, emotions fal a fuskarsa.

Episode Eighty Four : Little Love

Ya dago ya kalle ni nayi masa murmushi ya sake kallon hoton sannan yace " then she is alive. All this time ina tunanin cewa bata raye shi yasa bata neme ni ba, amma tana raye ashe, kawai ta ajiye ni tayi tafiyarta, without a second thought" nace "please Sultan kar ka ce haka mana. Baka san uzurin ta ba. Ka bari idan ka samu lafiya sai mu tafi har Riyadh din mu same ta acan, ka gabatar mata da kanka, na tabbatar zata yi maka gamsashshen bayani a dangane da wacece ita" tun kafin in karasa maganar yake girgiza kansa, yace "I will not go, babu inda zanje, haka kawai muje ta wulakanta mu? Kamar yadda ta wulakanta ni ta ajiye ni ta tafi? If she wants to see me ai tasan a inda ta barni, in tana son ganina tazo inda nake" nayi sauri nace "sultan uwa ce fa, kar ka fadi mata maganar da Allah zaiyi fishi damu kuma" yace "ko menene nace mata Allah ba zai kama ni ba. I don't know much about love but naji ana cewa mother's love is the purest of love, hakan yana nufin ya kamata ace sonda take min yafi son da nake miki yawa, ni kuma nasan a yanzu yadda nake jinki a raina rabuwa dake will be the end of me. Ita wacce irin zuciya ce da ita?" Sosai naga ransa ya baci na tuna cewa bashi da lafiya, na karbi wayar daga hannunsa nace "sultan baka da lafiya, let's not talk about this now, in ka samu lafiya sai mu san abinda zamuyi akai" ya jawo ni jikinsa muka koma muka kwanta, ya jawo bargo zai rufe mu, temp dinsa naji da zafi na yaye bargon, ya rabu dani bai tanka min ba sai kara matse ni da yayi a jikin sa, yace "tell me something nice" banyi magana ba na dora hannunsa akan mara ta, yayi dariya kadan yace "yeah, that's a nice topic of discussion" ya danyi shiru sannan yace "mace nake so ki haifa, mai kama dake kuma mai halinki, kuma ina son itama take sona kamar yadda kike sona. Maimunatu zan saka mata" nayi sauri na kalle shi nace "maimunatu? Ai sai muyi maka yawa kuma" ya saka dan yatsansa yana zagaye lips dina dashi, abinda yake fara yi lokuta da dama in zai kissing dina, yace "kin taba ganin inda haske yayi wa mutum yawa a rayuwarsa? Gaba daya rayuwata a cikin duhu nake yinta sai da kika zo sannan kika fara haska min hanya, you brought so many blessings to me, uncountable, yanzu ga baby, to menene laifi dan na kira ta da moon itama, kogi ma ai baya kin dadi" naji dadin maganarsa amma nace "idan hasken yayi maka yawa kuma ai sai ya kashe maka ido ka kasa gani sosai" yace "sai in saka sunglasses" a tare muka yi dariya, abinda nayi tsammani shi ya biyo bayan dariyar tamu, hot kiss, wanda naji shi tun daga kafata har kaina, ganin yana neman zarcewa ya saka na ture shi nace "a asibiti fa muke baka da lafiya" ya shagwabe fuska "ni na warke ai" nace "to in ka warke ka bari a sallameka in munje gida koma menene za'ayi sai ayi, amma yanzu in wani ya shigo fa? Besides kai da baka da lafiya so kake ka karar da sauran karfinka ko?" Bai kula ni ba ya koma ya kwanta irin yaji haushin nan. Banyi aune ba kawai bacci ya dauke mu a haka, daga ni har shi.

Karar wayata ce ta tashe ni daga baccin nayi sairi na mike na sauko ina gyara kayana da sukayi squeezing, na dauka naga Amina ce, ni nama manta tare muka zo da ita. Na dauka da sallama tace "Moon dubiyar kenan? To albishirinki wallahi Mommy da Daddy har da Takawa sun shigo sun ganku" nace "na shiga uku Amina dan Allah da gaske kike?" Tace "wallahi Takawa dai ya shigo, su Daddy kuma yanzu suka zo suka turo ni, na ganku na koma, yanzu ni me zance musu" nace "gani nan fitowa, tunda basu ganmu ba da sauki, Takawa kuwa ba haduwa mukeyi ba ballantana in ji kunyarsa" na kalli sultan naga ya tashi yana kallona, nace "su Daddy sunzo suna waje, an ce Takawa ma ya zo amma ban sani ba ko yana nan ko ya koma" ya tashi zaune yace "then dazu ba mafarki nayi ba kenan" nace "yes Sultan, ba mafarki kayi ba". Na nemo rigarsa na saka masa, yana tayi min complain yunwa yake ji, Allah ya taimake ni su Mommy sunzo da abinci, dan haka suna shigowa na bude na fara zuba masa, dama Sultan ba kunyar Daddy yake ji ba, gwara ma Mommy, ya zauna ya fara cin abincinsa nima Mommy ta matsa min lallai saida na zuba naci. Muna nan tare dasu, Sultan ya ware suna ta hira da Daddy wanda shima naga ya dan sakarwa sultan din, Amir ya shigo, ya gaishe dasu Daddy, nan yake bamu labarin yadda yaje ya kira Takawa da abinda ya faru bayan zuwan Takawan, muka kalli juna ni da Sultan, Amir ya cigaba da cewa " kowa yayi mamakin me yasa yayi fainting, the doctor said he need rest wai stress ne, shine aka kaine daki aka kwantar kuma bayan an jima kawai sai gashi ya fito ko manyan kaya babu, ya karbi key din mota ya fice, babu wanda yasan inda yaje sai dazu ya dawo, yazo nan kuma ya koma can inda aka kwantar dashi, yanzu ya aiko akayi kirana yace inzo in yima sultan knocking ince ya tashi ya ci abinci yayi sallah" muka sake kallon juna ni da Sultan, Daddy yace da Amir ya koma ya gaya wa mai martaba sarki cewa sultan ya tashi har yana cin abinci ma, kuma ya gaya masa jikin sultan da sauki ya kwantar da hankalinsa. 'Yar karamar dariya sultan yayi sannan yace "he doesn't care, kawai drama yake playing" nan take Daddy yayi kansa da fada "ba drama ba koma menene yake playing he is your father, dole kayi respecting dinsa" dama Daddy da dan sauran fushin sa akan abinda sultan yayi, nan ya wanke sultan tas da soso da sabulu, Sultan bai sake magana ba. Bamu ankara ba sai ji mukayi anyi knocking kofa an shigo, Takawa ne da kansa a tsaye a bakin kofa, ya saka babbar riga yanzu, da hula a kansa babu rawani. Fuskarsa babu dariya, idonsa akan sultan. Wani kwarjini naga yayi min sosai, lallai sultan anan ya samu kwarjinin sa. Daddy ya fara kokarin gaishe shi amma sai muka ga ya mika wa Daddy hannu sunyi musabaha, ya karaso cikin dakin duk muka tashi muka fara gaishe shi banda sultan da yake kallon kasa, Amina ta kwashe kayan da muka gama cin abinci ta fita Mommy ma ta bita a baya, na tashi nima zan bisu amma Sultan ya rike hannuna ya dawo dani baya, Daddy ya kalle mu bai ce komai ba shima ya fita. Ya zama saura mu uku, na danyi dariya nervously na kuma kokarin fita amma sultan yaki ya saki hannuna kuma har yanzu kasa yake kallo. Takawa yayi gyaran murya yace "Maimunatu dan bamu guri zamuyi magana" Sultan yace "she is not going anywhere, duk abinda zaka fada min ka fada a gabanta" na kalleshi ina tunanin baiji fadan daddy ba kenan, nace "sultan? Takawa ne fa" yace "you are not going anywhere, in ba zaiyi magana a gaban ki ba ya fita" irin rikon da sultan yayi wa hannuna kamar zai balla ni da kuma yadda naga jikinsa yana rawa ya saka na fahimci ba wai ya hana ni fita ne saboda ya bata wa Takawa rai ba, a'a he is nervous, bai taba zama daga shi sai babansa sunyi magana ba, he needs my support. Na zauna akan kujerar gefensa ina kokarin mu hada ido amma yaki bari in kalli cikin idonsa. Takawa ya karaso gaban gadon sultan ya dan tsaya yana kallonsa, sai kuma naga ya zauna a bakin gadon wajan inda kafafuwan Sultan suke, ya saka hannu yadan bude bargon, ya fara shafa kafar sultan a hankali kamar mai matsa masa kafar, ya fara magana "my Little Love, you are just as strong and brave as I thought you will be. Bansan yadda zaka dauki maganganun da zan gaya maka ba amma ina son ka sani, duk abinda zan gaya maka shine gaskiyar abinda ya faru, kuma abinda zan gaya maka shi zai zamanto amsar tambayoyin da kake yiwa kanka kullum a kaina da mahaifiyarka" nan ya fara zayyano mana labarin da ya saka na saki bakina ina kallonsa, babu wanda yayi magana a cikin mu har ya gama maganar sa, tun daga haduwar su da khairat har dauketa daga gidansi da yayi da auren da sukayi a America, har labarin haihuwar sultan da kuma dawowarsu Nigeria, yadda rabuwarsu ta kasance da abinda Sarki Abdallah yayi bayan rabuwar tasu, aurensa da Hajiya da asalin labarin Abbas, yadda ya dawo hankalinsa yau da kuma sakin da yayi wa Hajiya dazu. Ya cigaba da cewa "ka sani Sultan, ba zan iya dawo da hannun agogo baya ba kuma bazan iya biyaka abinda kayi missing na kulawar iyaye ba, amma daga yau zan nuna maka me ake kira da soyayyar iyaye. Ina nema wa mahaifina gafara a gurinka a bisa abinda ya aikata, kuma ka sani, bayayi hakan bane dan son ransa ko dan ya cutar damu ba, a'a yayi hakan ne saboda yana ganin shine zabin da yafi dacewa a lokacin" ya mike tsaye kamar zai fita kuma sai ya tsaya ba tare daya juyo ba yace "you are no longer the little love I know, you are a grown up man now, kayi tunani akan duk abinda na gaya maka, sai ka yanke hukuncin da kaga ya dace" ni dai da ido nake binsa har yakai bakin kofa sai ya juyo muka hada ido, ga mamaki na sai naga yayi min murmushi sannan ya fita. Na dawo da hankali na kan sultan wanda har yanzu idanuwansa a kasa suke, I can't imagine me yake ji a ransa a yanzu, maganar is hard to digest, I only know that he needs a hug right now dan haka abinda na bashi kenan, a shoulder to cry on, na hau kan gadon na rungume shi idona yana fitar da kwalla, da sauri shima ya rungume ni kamar zai balla ni, sai jin saukar hawayensa nayi a bayana, nima kukan nake yi sosai. Rayuwar sultan kadai ta isa ta zama darasi ga dukkan mai tunani, komai yayi farko yana da karshe kuma ance mahakurci mawadaci ne watarana. Na fara rarrashinsa ina bubbuga bayansa a hankali, nace "shhhh it's over, komai ya wuce, everything is going to be alright".

Da daddare aka sallame mu, direct gida muka tafi. Ga mamakin mu har muka tafi Takawa yana asibitin, amma yana daya dakin sai dai ya turo amir ya ga me Sultan yake yi ya koma ya gaya masa. A motar Amir muka tafi gida, da escort a gaba, sai motar mu sai motar Takawa sannan sauran motocin. Yau sai ga Takawa a gidan mu, shine har cikin bedroom din Sultan, sai daya jaddada min lallai in tabbatar yaci abinci sannan ya rage masa AC n dakin ya tafi.

Please Login or Register in order to submit comment