Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

neman magana yake yi, naga ya chanza hanya na tambaye shi yace "Amir zamu dauko" da sauri Amira tace "What? Please ku sauke ni in hau taxi, I can't tolerate that man" duk dariya muke mata tace "am serious wallahi, he is so annoying" muna yin packing ya bude ya shiga baya, yana ganin Amira a ciki ya ja tsaki yace "damn it, wannan yarinyar me take yi a motar nan?" Dariya muka sake yi, ni drama dinsu dariya take bani. Daga nan naga mun kuma yin wata hanyar daban, this time banyi magana ba Sultan yace "I want to show you something" Bance komai ba har naga yayi packing a gaban wani katon building duk muka fito na daga kaina naga an rubuta a saman ginin 'MOON CONSTRUCTION AGENCY" na kalle shi da mamaki yace "to ba kin ki gayamin sunan da kike so ba, shi yasa na saka sunan da na fi so" muka shiga gurin suna nuna mana ko'ina suna kuma yi mana bayanin komai,gurin ya tsaru sosai, I trust sultan in dai ta gurin tsari ne, aikin architecture yayi suiting dinsa sosai. Daga nan muka tafi gidan su Amira, a can mukayi magrib sannan muka fito muka kai amir gida shima. Finally daga ni sai shi, nace masa "thank you for the name" yace "I only hope it will shine as bright as you" nayi murmushi. Yace "wai har yanzu Mommy ba ta ce miki komai ba?" Nace "akan me fa?" Ya nuna kansa sannan ya nuna ni yana mischievous smile dinsa. Na gane me yake nufi, na dan bata rai nace "ni ban san akan me kake magana ba" yace "common, how much longer do I have to wait ne wai. Ni aure na ke so seriously" na rufe baki ina dariya nace "kai Sultan, baka jin kunyata kake cemin aure kake so?" Yace "ke din zanji kunya? Ke fa zan aura kuma sai inji kunyarki? Please ki dan tambayi Mommy mana kiji me ake ciki" nace "kai ma wasa kake, me zan ce mata? Mommy yaushe za'ayi min aure?" Yace "exactly" na girgiza kai nace "sai dai kai kaje ka tambayi Daddy" yace "OK, wato ke kina nufin ba kya son auren kenan?" Nace "wai what has come over you ne yau?" A lokacin muka shigo gida, yayi packing amma be kashe motar ba yace "ai na riga ma gaya miki me yake damuna, aure nake so, ai nayi kokari, ya kamata a bani medal ma. Kinga yanxu abinda za'ayi, irin in kuna magana da Mommy sai kike gaya mata ga abinda kike so ayi da bikin ki, zata dauki haske ai sai tayi wa Daddy magana" nace "wai ni na ce maka ina son aure? Kai da kake son auren ba sai ka fada ba?" Ya juyo yana facing fina yace "look into my eyes kice ba kya son aure na" na ki kallonsa, yasa hannu zai juyo fuskata na kara matsawa, yace "kin gani ko? You want it too" na girgiza kaina nace "I don't want anything" yace cikin murya kasa kasa "then look into my eyes and tell me you don't want me" da sauri na bude kofar motar na fita, shima ya bude ya fito ya sha gabana "au guduwa zaki yi ko?" Nace "kafi karfina yau. Yau mood dinka is not for me" yace yana kallon cikin idona "I have always been in this mood, for you, only you. Kawai hakuri nake, please do something. Ni fa idan ba'ayi mana aure kwanan nan ba to akwai rigima." Dariya nake son yi amma shi fuskarsa so serious, can ya fara devilish smile dinsa sannan yace "laugh all you want, baby girl, my time will come, then I will do the laughing and you will do the crying" bansan sanda na daina dariyar ba, da sauri na nayi hanyar gida, ina jinsa yana kira na amma ko waiwayowa banyi ba.



Episode Sixty : The Prince

Sultan gaba daya ya rikice min, wai shi lallai sai na fada a gida cewa aure nake so, kaji mutum, kuma shi in nace masa ya fada sai yaki. Dole yanzu na fara rage doguwar hira dashi, a waya ma kuma sakin layi yake. Gaba daya ni yanzu lamarin sa tsoro yake bani, kuma gashi Daddy ko mentioning zancen mu baya yi, ballantana Mommy da ko maganar ma bata so ayi. Da yaga na fara gudunsa sai ya tsiyo da zancen driving lesson, Daddy ya gayawa, daddy kuma yace muke yi da yamma in ya taso daga office. Ni dai nasan ba wani abin arziki za'a koya min ba amma dai haka nake binsa muna fita, in muka je rabi lesson rabi hira. Rannan nace masa "to wai kai me yasa ba zaka je ka tambayi daddyn ba? Ai kun fi kusa dashi, ko kasa yaya Walid ya tambayar maka" yayi shiru yana kallona sannan yace "Daddy has done so much to me ne bana so inyi disappointing dinsa, bana so yaga gazawa ta ko kuma yayi tunanin dama abinda nake after kenan. Nafi so ace shi yayi min magana da kansa. Amma gaskiya na gaji da jira, I don't know how long zai taking kafin yayi min maganar" ya dan bata fuska yana kallona "ke ko ajikin ki ma wallahi, hankalinki kwance ke ko shekara za'ayi a haka babu ruwanki ko?" Nace "wa ya gaya maka haka?" Yace "to ai bakya nuna wa. At least kema ki dan ringa nuna min kina so mana, at least sai in san cewa the feeling is mutual ba wai ni kadai na ke abuna ba" nace "sultan komai fa da lokacin sa, musamman aure, in kaga anyi to lokaci ne yayi ba wai nuna ina so ko rashin nuna inaso bane zai sa ayi. Kai dai kayi ta addu'ah sai kaga komai yazo da sauki"

Sosai muke ta shirye shiryen haihuwar Hafsat, takanas Mommy ta dauko wata midwife suke kwana tare saboda in case ko haihuwar zata zo da daddare. Hafsat kam duk tayi laushi, bata da aiki sai cin abinci sai da yamma inna tafi driving lesson dina ita kuma ta tafi strolling. Kaya kam har dai da aka ware daki guda ake zubawa dan kullum sai an siyo wani abu na baby an ajiye, in dare yayi kuwa bata zaman palo, tana daki makale da zayed a waya har sai tayi bacci. Ni kuma kullum da daddare bayan an gama dinner zamu zauna hira da Sultan, Mommy ta hana hirar palo tace muke zama a compound in da mutane za suke ganin mu, ni ma banyi mata musu ba saboda wannan Sultan din ba na da bane ba, shimq dana gaya masa abinda Mommy tace sai cewa yayi "yauwa, ai gwara ma muke zama inda Daddy zai ke ganin mu yana tunawa da maganar mu"

Rannan ina gyaran kayana a daki kawai sai naga katin da musbahu ya bani a agadaz, shaf na manta dashi ma ni, dan adam kenan. Na dauka na saka number din nayi saving as 'musbahu ngr', sai bayan da nagama aikina kaf sai na dauko wayar na kira number dinsa, ya nayi masa sallama ya amsa yace "sai yau kika tina dani ko Moon?" Nace "lah ya akayi ka gane nice?" Yayi dariya yace "naga number din Nigeria kuma naji muryar mace, I have been expecting your call kuma shiru har na fitar da rai" nace "wallahi na rasa card dinne sai dazu na ganshi, ya su mustapha da sauran 'yan gidan?" Yace "lafiya lau. Ina Sultan?" Nace "au baka manta sunan sa ba?" Yace "It is kind of special ne shi yasa ban manta ba" muka dan taba hira na kashe na ajjiye wayar, ni sam ban kawo wani abu a raina ba sai da daddare muna tare da sultan ya karbi wayata yana kallon pictures din da mukayi dazu wajan koyon mota sai kawai naji an kira ni, na mika hannu ya ban wayata sai naga yanayin fuskarsa ya chanza, ya juyo min screen din na karanta 'musbahu ngr' wayar ta katse aka sake kira har ta sake katsewa bai bani ba kuma bai ce min komai ba. Can dai yace "why is he calling you?" A ina ma ya samu number dinki da zai kira ki" na bata rai nace "dazu na kira shi muka gaisa. Yace in nazo Nigeria in kira shi, tunda nazo kuma ban kira shi dinba saboda nama manta da maganar sa sai dazu" nan take naga yanayin fuskarsa ya chanza "ina ruwanki dashi to da zaki kira shi, yanzu gashi ya samu number dinki kuma har yana da guts din da zai kira ki yanzu da daddare" nace cikin lallashi "Sultan, gaisawa fa kadai muka yi, har tambayata kai sai da yayi, he means nothing, kuma ya taimakamin wallhi, badan shi ba maybe da har yanzu ina agadaz" Sultan yayi chuckling yace "he is fooling you, kuma zancen taimako ke fa kike gayamin kullum cewa komai yana da lokacinsa, dan haka tunda lokacin dawowar ki gida yayi dole sai kin dawo with or without his help" nayi shiru na rabu dashi tunda naga rigima yake ji da ita, jin nayi shiru sai ya cigaba " you called him yaji muryar ki, and now he is calling again saboda ya sake jin muryar ki. Ni da son raina ne in banda 'yan gidanku babu wanda zaki ke yiwa magana ballantana har wani kato yazo yace zai kula ki. Kamar yadda nake ban taba budurwa ba sai you and you are the last haka nake so kema tunda baki taba saurayi ba in zamanto the first and the last" gaba na ne ya fadi dana tuna cewa sultan fa har yanzu bai san labarin Ibrahim ba, nayi sauri na ture maganar daga raina nace there is no need for him to know, tunda dai what you don't know won't hurt you. Ya jefo min wayar kan chinyata yace "block him" na dauki wayar inajin zafin yadda ya dage yake fada akan abinda bai kai ya kawo ba, na mike tsaye nace "I won't block him, tinda ni ba butulu ba ce" da sauri ya mike tsaye shima, kamar zai ce wani abu kuma sai ya fasa, ya saka hannunsa a cikin gashinsa sai ya tafi kamar zaiyi hanyar gate kuma sai ya dawo sai da yazo daf dani ya tsaya, ke gezau banyi ba, ya kalleni cikin ido yace "in har naga kafarsa a gidan nan sai na babballashi wallahi" na hade rai nace " kai yanzu sai ka karya mutum dan ya kulani?" Yace "bazan san sanda zan karya shi ba ai, sai na ganshi a kasa sannan zan san me na aikata. So you better warn him" na juya ina kallonsa har ya fice a kafa daga gidan. Na sauke ajjiyar zuciya, lallai ina da aiki a gaba na, sultan zuciya, sultan kishi, dole sai yayi maganin wadannan abubuwan guda biyu sannan zamu zauna lafiya dashi. Na koma cikin gida, ban kira musbahu ba kuma banyi blocking dinsa ba, sai kuma naji babu dadi a raina, yau munyi fada da Sultan, amma nasan zai sauko na bashi nan da awa daya.

Nayi shirin kwanciya na kwanta, bacci ya fara dauka na kenan naji wayar sultan, har ya sauko, nima yanzu zanyi nawa fushin. Na rabu dashi yayi ta kira na naki dauka, message ya shigo, ina dauka naa emoticon na kuka, ya rubuta 'am sorry love' nayi murmushi a raina nace 'iyakacin zuciyar kenan?' Kafin ya kuma kira na kira shi, bugu daya ya dauka har da sauke ajjiyar zuciya nayi shiru bance masa komai ba, sai na kuma jan aji tukunna. Cikin muryar shagwaba yace "to wai ba nace am sorry bane ba? Dan kinsan ba zan iya bacci banji muryarki ba ko?" Na sake yin shiru yace "please please please haba love, this is so cruel wallahi. Am sorry nayi miki fada, i don't want you talking to any man. Ina kishin ki sosai. Please kar kiyi fushi dani akan haka" a hankali nace "ni ba akan kayi min fada nake fushi ba" yace "to akan menene, tell me, koma menene zan daina" nace "akan baka yadda dani ba" ya danyi shiru sannan yace "bangane ban yarda dake ba" nace "all this while ya kamata ace kasan how much I love You, ba musbahu ba koma waye mu kayi waya dashi ko kuma ka gan mu tare dashi bai kamata ka bata ranka ba, ban san menene a cikin zuciyar musbahu ba amma nasan menene a cikin tawa, and that should be your only concern. Sultan bana ganin wani namiji a gaba na ko a bayana sai kai, my heart is for you, only you, to menene naka na tsayawa kana bata ranka akan nayi magana da wani wanda ba lallai in sake ganin sa ba" jin yayi shiru ya saka na kwalli wayar na dauka duk wannan tsarin da nake yi kiran ya katse, naga seconds suna reading na mayar da phone din kunne na nace a hankali "sultan?" Can kasan makogwaronsa naji yace "I must do something, I really must do something" cikin confusion nace "ban gane ba?" Yace "seriously na gaji da fadar kalmar I love you na kuma gaji da jin kalmar i love you. I want to start giving some actions and receiving some actions. Kalmomin sun kare, I am out of words to show you my love for you. I want to start really showing you my love. I want you" nace "sultan zan kashe wayata" yace "go ahead ki kashe din, ai dai naji muryar ki. Tun ina yaro, if I want something, I go for it, yanzu ma haka, I want you and I will come for You" na katse wayar da sauri, na kashe ta gaba daya. Da sauri na tashi na rufe windows dina da kofar balcony na dawo na zauna akan gado, amma a raina nasan in dai Sultan yayi niyyar shigowa daki na to sai ya shigo, but I don't think he is coming, he is not going to throw away duk abinda ya samu ba.

Da safe yawa ta tana kashe dan haka bamu yi wayar da muka saba yi da safe ba kafin ya fita, bayan munyi breakfast na kira shi naji switched off, har aka zo lunch ban samu wayarsa ba, kuma bai zo cin abinci ba, daddy ya tambayi walid sai walid yace masa sunyi waya yace yau aiki yayi masa yawa ba zai zo ba. Muna gama cin abinci naje na hada masa basket guda na abinci na bawa driver nace ya kai masa office dinsa. Ga mamaki na sai ga drivern ya dawo yace wai ance yau baije office ba, suma nemansa suke yi. To ni maimunatu ina sultan ya tafi. Babu irin tunanin da banyi ba. Har akayi la'asar shiru. Ina kitchen ina zaune ina kallon su asma'u suna ta aiki, yau ko surutun ma bana musu, sai ga maryam ta shigo da sauri tace "kai kuxo ku gani yau baki akayi a gidan nan har da masu rawani da dogarai" da sauri na mike nabi bayansu muka leka ta tagar kitchen amma bama hangowa sosai, na dai hango jama'ar gidan mu sunyi chirko2 a gefe, muna cikin leke Mommy ta shigo kitchen din da sauri tace min "zo ki fita ki tafi daki" da sauri na fice ina jinta tana bada order abinda za'ayi. Dakin hafsat na shiga na tarar tana sana'ar tata ta bacci, na daga labulen window dinta na leka waje, jibga jibgan motoci na gani har guda biyu sai kuma mota mai kalar kayan dogarai, yaya Walid na gani da sauri yaje gurin motar farko ya bude kofar ya durkusa ya gaishe da wanda yake ciki sannan ya matsa ya badu guri suka fito, manyan mutane ne sun sha kayan alfarma na sarauta, duk ban san suba, naga sun tafi palon da Daddy yake saukar manyan bakin sa. Aka matsar da motar gefe aka matso da dayar, matane suka fiyo su biyu, daga ganin su kaga manyan mata, dogarai suka zagaye su har suka shigo kofar palo. Nayi sauri na koma bakin kofa nayi kneeling ina leke ta keyhole, Mommy da mutanen ta suna ta kai kawo a gurin bakin amma bana hango su sosai kuma bana jin me suke cewa. Na zauna anan na jingina da jikin kofar, na kara kiran wayar sultan switched off. Dazan kama matar nan mai cewa switched off a waya da Allah kadai zai raba ni da ita. Ina nan zaune naji kiran Mommy ya shigo, na dauka tace "kina ina ne?" Nace "ina dakin Hafsat" sai a lokacin Hafsat ta tashi ta ganni nayi tsuru2 ta tambaye ni menene na daga mata kafada. Mommy ta shigo tana kallona sannan tace "ki zo ki gaishe su" da sauri na bude kayan Hafsat ina neman kayan sakawa, Mommy tace "NO, kayan ki are OK, kawai ki dan gyara fuskarki sai ki samu babban mayafi ki saka" na shiga toilet da sauri na wanke fuskata, jikina sai rawa yake, inna kama sultan ni kadai nasan me zan yi masa, in less than five minutes na shirya Hafsat ma ta dan gyara muka fita. Tunda muka fita kaina yana kasa amma inajin idonsu a kaina, muka zauna daga can nesa muka gaishe su suka amsa mana da fara'ar su. Daya ta fara magana "Sultan bai kyauta mana ba wallahi, sam bai gaya mana maganar nan ba sai yau. Yanzu gashi ya saka munji kunya bamu kawo mata wani abin kirki ba" wata kuma tace "marar kunyar ba, ni yaushe rabon da in saka shi a idona, kawai sai gashi da sassafe yaje min kamar an koro shi, ni na dauka ma baya kasar" sai kuma ta dawo kaina "Maimunatu kalle ni kinji, ni ba surukar ki bace ba, ni kakar ki ce, Nani sunana, wannan kuma Yaya" ta nuna ta kusa da ita, "wannan ita ce surukarki, matar galadima ce" na kara sunkuyar da kaina ina murmushi, yaya tace "mu kadai muka zo yanzu saboda bai bamu lokaci ba, yace lallai sai munzo yau, mu zuwa muka yi mu ganki mu saka miki albarka sauran kuma magana ta maza ce" Matar galadima ita ma tayi mana addu'ah aka ce mu tashi mu koma. Ina shiga daki na zube a kan gado, gaba ki daya jikina rawa yake yi. Hafsat tace "wai kina nufin bai gaya miki zasu zo ba?" Na girgiza mata kai. Muna nan zaune har suka tafi sannan muka fito palo, kaya muka tarar a gaban Mommy akwati biyu, kayan kwalliya ne kawai dana gyaran jiki. Ina ta jiran inji anyi min wata magana shiru babu wanda yace min komai, har muka yi dinner da Daddy shima bai yi min magana ba. Sultan bai zo ba kuma babu wanda yayi maganar sa. Na gaji da zama na tashi na ce musu sai da safe na hau sama. Na kwanta amma sai juyi nake yi na kasa bacci, me hakan yake nufi? Babu abinda zuciya ta bata ayyana min ba kuma duk marasa dadi. A haka har bacci barawo ya dauke ni.

Cikin bacci naji ana shafa fuskata a hankali, a tsorace na tashi ina rarraba ido, Sultan na gani a zaune a gaban gadona yana dariya, nayi sauri naja bargona lullube jikina duk da cewa dakin da akwai duhu. Nace "Sultan me kake yi anan ne? Na shiga uku, ka tashi ka fita, yanzu in Mommy ta shigo ta ganka fa?" Yana dariya ya saka hannu ya kunna bedside lamp, nayi sauri na kashe, nace "babu kaya fa a jikina dan Allah ka tashi ka fita" ya mike tsaye yace "OK, bara in juya bayana sai ki saka kayan sai in juyo muyi maganar" nace "kowacce magana ce ka bari mana sai da safe mayi, Sultan Mommy nake tsoro, in ta shigo ta ganka a dakina cikin dare me kake tunanin zata ce" ya zagaye gadon yaje bakin kofa yayi locking ya zare key din yace "problem solved" na sake cewa "me kake yi a dakina" yace "zuwa nayi inga amaryata" Hijab dina na nuna masa ya dauko min na saka sannan na fito daga bargon na zauna bakin gadon na kunna fitila. Gabana yazo ya zauna ya harde kafafuwansa yana kallona da murmushi, na bata rai, "shine ka kashe wayarka ko" yace "ramawa nayi, dan kiji yadda nake ji in kin kashe min waya" nace "amma dai at least ka gaya min plans dinka kafin ka aiwatar ko? We are suppose to be a team, kawai sai ganin baki mukayi bamu san da zuwan su ba" yace "I told you I must do something, kuma sanda na hada plan dina kin kashe wayar ki, da safe kuma na ai watar da plan dina. Tunda naga Daddy yaki cewa komai ni kuma bana so in tambayeshi shi yasa na je na gayawa galadima nace yazo ya nema min auren ki a gurin Daddy, munyi rigima dashi sosai kafin ya yarda yazo din, yace na daina zuwa gurinsa na zama dan kaina and all that, ni kuma abinda yasa na daina zuwa gurinsa saboda bana son cigaba da hada su rigima da Takawa, sanda nake zuwa gurinsa kullum sai Takawa yayi masa masifa akaina, so kawai sai na rabu dashi, ashe shi haushi na yake ji. Su kuma su yaya su suka gayyaci kansu, kawai galadima ne yace in je in gaya musu maganar shine sai suka ce lallai sai sunzo sungan ki, fitinannun tsofaffi kawai" ya mike tsaye yace "oh God yunwa nake ji wallahi" nace "to baka fada min ba kuma abinda akayi" ya daga gira daya yace "akayi me?" "Maganar da suka zo yi me akace?" Yace "yarinya tana so tana kaiwa kasuwa, bazan fada din ba sai kin bani abinci naci." Nace "dakai me kake yi ba kazo kaci abincin ba" yace "ina office wallahi ina zane" da mamaki nace "zanen me kuma cikin dare?" Yace "zanen gidan mu, I made all the plans, gobe za'a fara aiki" na saki baki ina kallonsa. Daga tsayen da yake straight ya fado kan gado, nayi sauri na mike nace "Sultan menene haka kuma, tashi min daga gado" yace "nace miki yunwa nake ji, ni bani da energy din tsayawa" nace "amma kana da energy din hawa katanga ka shigo wa mutane daki ta taga ba" ya tashi zaune "please ki samo min abinci inci, Allah yunwa nake ji" na tashi na dauki key na bude dakin, ina fiya na sake rufewa da key ta waje. Duk da saukowar da Mommy ta fara yi, na tabbatar in ta shiga dakina taga sultan a kwance a kan gado to koma menene aka shirya sai an warware shi, maganar aure ta tashi. Na duba kitchen naga duk an yi wanke wanke babu sauran abinci, a fridge na samo masa wata gasashshiyar kaza, na dumama ta a oven na hado masa da fresh milk na taho. Ina shiga daki naga agogo ya nuna 2:19. Ina shiga na kuma rufe kofar, yana kwance ya mike ya zauna ya harde kafa na ajiye masa a gabansa na shiga toilet na kuskure baki na na dawo, yana kallo na yace "menene na wani zuwa ki wanke baki?" Nace "tayaka ci zanyi" na hau gadon na zuba masa madarar na mika masa. Sai da ya fara ci sannan ya fara magana "Daddy yace 'yalleman za'a je, sunyi fixing jibi zamu je tare gurin baffa, shine zai ce ya bayar ko yace ya hana. Amma shi gurin Daddy yace ba matsala" nayi shiru bance komai ba, yace "hey, ya kamata ki bani tukwuici mana" nace "OK, me kake so in baka" yace "a hug will be very much appreciated" na harare shi nace "only in your dreams" yana murmushi yace "it happens only in my dreams now, it will happen in reality very soon" na sauko daga gadon nace "tashi ka fitar min daga daki" ya gyara zama yace "da ace zan yi miki wani abu baby girl, da tun sanda na shigo kina kwance kina ta sharar bacci a lokacin zan miki, so relax, i have waited for so long, saura kadan ya

Please Login or Register in order to submit comment