Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ranar kuma har yau ke kike controlling dinta" a lokacin aka fara serving din mu abinci, muka fara ci muna hira muna dariya, it's like mu kadai ne a duniyar, babu tunanin kowa babu tunanin komai a zukatan mu sai mu kadai. Yace "gwara fa ki samu kici abinci fa sosai, dan after today ba lallai bane ki samu damar cin decent meal ba kuma sai a gidan ki" nace "that goes also for you" yace "wa? Ni akwai wani abu da zai hanani cin abinci a kuwa? Amma nasan abinda zan ke yi miki in an fara bikin nan, kullum dura zan ke zuwa ina yi miki, kar azo a gama biki kuma ki kare da zuwa asibiti a bar ni da tagumi" na harare shi bance komai ba. Mun jima muna cin abinci sannan muka gama, ko bayan da muka gama ma aka gyara table din bamu tashi ba muka cigaba da hirar mu. Yana ta bani labarin friends dinsa da suka zo. A lokacin ne yake gaya min cewa 'yan gang bang duk sunzo, hotel daya duk suka kama suka sauka. Sai naji babu dadi, ni har na manta ma da zancen su, na dan bata rai, yace "what's wrong?" Nace "I thought ka rabu dasu, me suke yi kuma a bikin ka?" Yace "It's just biki kawai, kuma we have been friends shekara da shekaru, yanzu ba zai yiwu ace bikina yazo kawai sai dai suji labari ba" nace "why not? Ni dai sam bana son su wallahi, I don't want you with them" ya jawo kujerar sa kusa dani ya langwabar da kai yace "baby, I can't just send them away, babu dadi ai. Yaushe rabona dasu ma, yanzu fa duk mun girma kowa ya kama gabansa, in ba abu irin wannan ba bama haduwa. Yanzu kuma in aka gama bikin nan ba lallai ne mu kuma haduwa ba sai bikin wani kuma" na kalleshi cikin ido nace "ba zaka je bikin kowa ba" dariya yayi yace "yes ma'am, an gama. Please ki dan saki ranki mana" nayi murmushi yace "yauwa, ko ke fa" hannun da ya rike naji ya fara shafawa a hankali yana kallona, nayi sauri na kwace hannuna naja kujera ta baya, ina kallon fuskarsa yana so yayi dariya amma ya maze nace "wato tsokanata ma kake yi ko?" Ya dan bata fuska yace "ni din? Ni na isa in tsokane ki?" Nayi kwafa nace "as if I don't know you. Na san ka fa Sultan. Babu abinda ban sani naka ba" yace "really kin sanni?" Nace "yes, like the back of my hand. Na san ka ciki da bai" devilish smile dinsa ya fara, a take na fahimci so yake ya juya min magana ta, na bata rai, bai damu ba yace "yanzu da gaske kina nufin kinsan Sultan? Baby girl I let you know only what I want you to know. There is a part of me that you don't know, there is a part of me that even I don't know. Amma kar ki samu damuwa, we will soon explore that part very soon. But I think rannan mun dan buda page daya na wannan chapter din" ya sunkuyo saitin kunne na yace a hankali "In America" ji nayi tamkar kasar gurin ta tsage in shige ciki, wato abinda Hafsat ta fada gaskiya nr bai manta ba. Ina jinsa yana dariya kasa kasa ganin yadda fuskata tayi ja saboda kunya, ba tare da na kalle shi ba na saka hannu na dauki jaka ta na mike, yayi saurin rike hannuna na kwace na yi gaba da sauri kamar zan tashi sama. Da kyar na samu na dauko key din motar saboda yadda hannu na yake karkarwa. Ina bude motar yana karaso wa gurin "am sorry Love, ki tsaya in kaiki gida dare yayi" ban ko kalli inda yake ba na shiga motar zan rufe kofar ya rike yace "please ki bari in karki gida, I promise ko magana ba zan yi miki ba" har yanzu da akwai alamar dariya a muryar sa, ya zaiyi yayi wasa da wannan maganar? Amma kuma nasan ba iya tukin dare nayi ba kuma Mommy bata san ma na daukar mata mota ba dan duk a tunanin ta tare muka fita. Na fito na zagaya na shiga seat din baya na zauna, har yanzu dariya yake ya tayar da motar muka tafi. Har muka je gida ba wanda yayi magana. Muna packing na fito, ya fito shima ya sha gabana yace "thank you for today, I really had I great time" bai samu amsa ba na zagaye shi na shige gida. Seriously ni Sultan tsoro yake bani.
Tuesday
Yaune kunshi da bridal shower. Tun sassafe akayi shimfidu a compound, madu kunshi suka zo, ni kam sam bacci bai ishe ni ba haka aka taso ni wai lallai ta kaina za'a fara kunshin. Jan lalle aka fara yi min, ana fara wa 'yammata suka zagaye ni aka fara wakar gada ana tafi. Hannu da kafa duk akayi min, ni kaina lallen yayi min kyau musamman saboda gyaran da fata ta tasha. Ana gamawa nace Amina ta daukar min shi a hoto ta turawa Sultan, tana ta dariya nace tayi shiru kar mutane suji. Tana tura masa ya turo min reply din kisses. A baki Hafsat ta zauna taba bani abinci ina ci har na koshi. Nan akayi ba'ki shima akan jan. Ai fa nan take na fito amarya ta sak. Tsofaffi sai guda, 'yammata sai waka. Ana gama wa dani aka koma kan sauran 'yammata. Mai kunshin ce ta dawo gurina tace "bara inyi miki wani abu as my wedding gift" nace "me fa?" Tace "wait and see" riga ta ta daga tana min wani abu a kasan kafada ta, ni dai dariya nake yi har ta gama, Amina nasa ta dauko min hoton gurin in gani, ina dubawa naga wani design tayi da bakin lalle mai kyau, a tsakiya ta rubuta S & M. Yayi kyau sosai, nayi mata godiya. Sai wajen la'asar aka gama kunshin dan har su daada dai da aka yiwa, wai suma sai sunyi gayu,lol. Ni dai ana cire min nawa na tafi daki nayi wanka na shirya cikin wata doguwar riga ta ta lace orange color, tayi bala'in yi min kyau dan kana gani na ba sai an gaya maka ba kasan nice amaryar. Dakina a cike yake da 'yammata ana ta shirye shiryen bridal Shower, su Hafsat kuwa ana waje ana making arrangements na gurin da za'a yi event din. A garden din gidan mu za'ayi, decorators already sun shirya gurin sai dan abinda ba'a rasa ba. Ana sallar magrib mai kwalliya tazo, Fauziyya tace "to ina kayan da amaryar zata saka ne wai?" Amina ta tabe baki tace "oho, sai ku tambaye ta, nima ban sani ba" na kira sultan nace ya aiko min da kayan yau, duk suka saki baki suna kallona, Hamidda tace "wai kina nufin kayan da zaki saka suna gurin angon?" Nace "yep" basu karasa mamaki ba sai da Maryam ta shigo da kayan a 'yar karamar jaka, suka buda duna kallo, doguwar riga ce fara tas, mai hannun vest, wuyanta ya shiga ciki sosai both gaba da baya, sai wani dogon siririn veil mai kamar jela irin wanda ake nannadawa a wuya ash color, takalmi da jaka ta ma duk ash ne, suna fito da kayan sai ga brazier da pant a kasa, a tare suka saka salati, ni kaina sai da nayi dariya, suka juyo suna kallona nace "wallahi ban san ya siyo da underwears ba" Hasiya tace "amma wannan angon shine number one a marasa kunyar Nigeria" Amina tace "Ai in da akwai number zero to Sultan ne" Sai da nayi sallah sannan ta fara yi min, a kawayena har da masu recording kwalliyar a video. Na saka kayana sannan muka fita ta kofar baya gurin event din, muna zuwa Hafsat ta dora min crown a kaina sannan ta rataya min tag da aka rubuta 'Bride' a jikinsa. Ni nayi shigar fari tas sauran duk mutanen da suke gurin kuma sunyi shigar baki, kowa a ganni a ranar sai ya sake kallo. An saka securities sun tare hanyar garden din babu namijin da zai shiga. Gaskiya tun a ranar nasan ina da kawaye masha Allah, dan har wadanda ban saka ran zasu zo ba sun zo. Ina jin waya ta tana ta kara a cikin jaka kuma nasan Sultan ne amma naki dauka na rabu dashi. Aka kawo min cake dina shima fari da kwalliyar baki, Hafsat ta taya ni muka yanka, akayi ta pictures daga nan kuma aka fara dancewa. Muna ta enjoying kan mu bamu san lokaci yaja ba sai da Mommy ta aiko tace ya kamata a tashi haka tunda da akwai masu nisa, sannan muka duba time muka ga after 11. Mommy ta saka drivers din gidan suka yi ta jigilar kai mutane gida.
A gajiye na shiga daki na fada kan gado duk jikina yana min ciwo. Gashi banyi sallar isha ba, wanka na fara yi sannan nayo alwala na fito nayi sallah sannan nayi shirin kwanciya. Sai da na kwanta sannan na dauko waya na kira sultan, yace "wato yau wannan matar kin manta dani ko?" Nace "ni na isa? Gurin da hayaniya in ma na dauka ba zaka jini ba" yace "to kuma shine ni ko a nuna min kwalliyar ko?" Nayi dariya nace "wannan kwalliyar ta yau tafi karfin idonka, ka bari zan ajiye maka pictures, randa duk ka kai matsayin gani sai in nuna maka" yayi ajjiyar zuciya yace "I can't wait" ban bashi amsa ba nace "good night Sultan" yace "fi amanillah"
Wednesday
Bacci nayi sosai da safe na huta, Sultan ne ya tashe ni da waya wai lallai yana son ganina kafin ya fita, da sauri sauri muka gaisa ya fita saboda mutane. Ranar anti Zaliha tazo, na gaisheta tace "Moon an samu abinda ake so ko? To baza muyi miki baki ba, Allah ya sanya alkhairi" sum sum na tashi na fice daga dakin. Rumfar motocin gidan aka gyara aka kwashe motocin gidan, anan za'ayi kamu. Ranar shigar atamfa nayi purple mai adon pink, sosai kalar atamfar ta kara haska fata ta, plain zani ne, na daura shi akan rigar, ana gama yi min kwalliya na shiga toilet na saka shower cap na rufe gashina tsaf da ita sannan aka daura min dankwali aka saka net aka rufe fuskata. Suna ta mamakin me yasa na saka shower cap a kaina ni kuwa nasan dalili. Nani ce tazo tare da mata da yawa daga fada. Dubu dari biyu suka ajiye da akwati guda na turaruka, sannan suka feshe ni da turare, daga nan aka bude fuskar amarya aka tayi min ruwan kudi, both dangin sultan da nawa. Sai da aka kusa gamawa sannan Hajja tazo tace sam kamu bai yi ba tunda ba'a zuba min nono ba, ai ni bafulatana ce dan haka da nono za'a kama ni. Kamar yadda tayi alkawarin sai tayi min wanka da nono haka tayi min, Mommy ta kule kamar zata yi kuka ni kuwa dariya ma nake yi abina, sai yanzu kawayena suka gane amfanin shower cap din dana saka. Ana gamawa direct toilet na shiga nayi wanka da special sabulu na, babu wani sauran karni daya rage a jikina. Bayan munyi sallar magrib kuma aka shirya tafiya walima. Doguwar riga na saka yellow mai adon golden stones, na saka jaka da takalmi suma golden, ina shiryawa na kira Sultan video call na nuna masa kwalliya ta, nan fa yace shi baiga dalilin da za'ace babu maza a walima ba, ai suma suna bukatar ayi musu wa'azin yadda zasu rike matan su, nace masa ai anayi amma suma du kadai banda mata, da kyar muka rabu wai bai gaji da ganina ba.
A abuja national mosque akayi walimar, anyi wa'azi sosai da nasihohi masu ratsa jiki kuma duk akan zaman aure, da kuma sirrika na rike miji bisa sunna. Naji wa'azin sosai dan jikina gaba daya dai da yayi sanyi. Muna dawowa gida na tarar Sultan yana jira na waishi lallai bai gama ganin kwaiya ta a waya ba sai ya gani a fili. A mota muka zauna ya fito mana da fura da nono mai sanyi da tsire, muna ci muna hira, ni har na manta ma bikin mu ake yi dai da amina ta kira ni tace "kinsan dai in baki yi bacci ba zaki tashi da kumburaren ido, kuma kwalliyar ki ba zata yi kyau ba" a raina nace 'oh Amina ko passion design kika karanta sai haka'


Episode Sixty Seven : The Wedding 2

Thursday
Tunda na tashi da assuba na koma na cigaba da baccina, cikin baccin naji kida na tashi kamar a tsakiyar kaina, na dauko pillow na dora a kaina na toshe kunnena amma a banza. Na mike a fusace ina mita "wai ba mother's eve aka ce ba? A bari sai evening din mana. Ni wallahi bacci bai ishe ni ba" Amina da ta fito daga wanka tana shiryawa tace "to ke da wa ya aike ki ki zauna hira da Sultan har karfe dayan dare? Dama ta yaya bacci zai ishe ki? Ai kawai hakura zaki yi ki tashi haka" na mike ina tsaki, na leka ta window na ga DJ ne ya baje kayan kidan sa a dai dai gaban tagar dakina. Na kara wani tsakin ina duba agogo, 11:30, kamar zan yi kuka nace "fi sabilillahi karfe goma sha daya za'a dasa min kida aka? Ni dai kam an shiga hakkina" Hafsat ta shigo cikin kwalliya tana kallona tace "wai yanxu kika tashi? Har Mommy tana cewa a kira ki ku gaisa da mutane?" Na kara bata rai na shige toilet. Ruwa na hada a tub na cire kayana na shiga na mayar da idona na rufe, take wani baccin ya sake dauke ni. Knocking kofar da akayi shiya farkar dani, ni ban ma san nayi baccin ba, muryar Mommy naji tana fada "uwar me kike yi a toilet din nan da har yanzu baki fito ba kin bar mutane suna ta jiranki?" Da sauri na tashi na kammala wankan ina mita a raina 'duk Sultan ne ya jawo min wallahi'. Ina fitowa na tarar mai kyalliyata tazo dan haka mai kawai na shafa na zauna muka fara, Hafsat ta shigo ta zauna tana feeding Khairat sai ga Mommy ta shigo itama, ta zauna akan bed side tana kallona tace "me ya hada ku da Amira?" Gaba nane ya fadi duk da dama nasan wannan tambayar tana nan zuwa, nayi shiru bance komai ba, ta sake cewa "fada kukayi ko?" Hafsat ce ta bata amsa tace "eh Mommy, fada suka yi" Mommy ta danyi shiru sannan tace "akan me?" Nan Hafsat ta zauna ta bawa Mommy labarin duk abinda ya faru, har ta gama Mommy bata ce komai ba. Sai da ta gama sannan Mommy tace "Maimoon3. Sau nawa na kira ki?" Murya can kasa nace "sai uku" tace "you are not to see that man again. Kinji ni ko baki ji ni ba?" Nace "Naji" ta kuma cewa "I am very serious in na sake jin maganar sa sai nayi mugun saba miki. Yanzu ace few days to daurin auren ki har kuma kina fada da best friend dinki a kan wani saurayi daban?" Nace "Mommy ni ba akan Ibrahim bane ba, akan tayi betraying dina ne, kuma ni ban hana ta zuwa gurin bikin nan ba, ita taga dama ta ki zuwa" Mommy tace "whatever, ni dai nace bana son sake jin maganar nan. Ok?" Nace "yes mother" tace "ita kuma Amira zata zo ta same ni ne, haka kawai akan wani saurayin da ko damuwa bai yi da ita ba zata watsar da rayuwarta kuma ta yi loosing best friend dinta" ta dauko wayarta tayi dialing ta fara magana "Hajiya salamatu lafiya kuwa? Jiya anyi kamu babu ke babu Amira yau ma kuma gashi har yanzu baku zo ba?" Ta danyi shiru tace "kani kuma? Me ya faru? Aa gaskiya ku dawo, please ko jirgi ku shigo ni zan biya ko baku samu mother's eve din ba ku sami dinner. Ok na gode sai kun zo din" ta kashe wayar ta fita.
Da yamma akayi mother's eve, ranar naga gatan iyaye da 'yan'uwa, gidan taf ya cika da mutane kuma wai kowa saboda ni yazo, su fa'iza ma sunzo tare dasu akayi komai. Har magrib sannan aka watse. Sallah kawai mukayi kuma muka fara shirin tafiya dinner. Na aika aka karbo min kayan dinner a gurin Sultan naxo na sake wanka na dan kwanta na huta zuwa isha sannan na tashi nayi sallar isha aka fara shiryani. Yadi ne cotton cream color doguwar riga data kamani daga sama sannan ta bude sosai daga kasa, daga baya kuma tana jan kasa sosai kuma anyi mata adon stones masu kyalli, ta gaba kuma anyi mata aiki kalar golden brown. Head dina, jaka ta da takalmina duk golden brown ne da adon stones cream. An gyara min gashina ya sauko har saman bayana an jera masa stones cream color sannan aka tubke shi da golden brown ribbon. Ni kaina dana kalli kaina a madubi sai da nayi mamakin irin kyan da nayi, a zuciyata nayi tasbihi ina godewa Allah. Around 8:00pm muka isa hall din taron, already kowa ya shiga ya zauna amarya da ango ake jira. Sultan da tawagarsa ne suka fara shiga, aka saka musu kidan su aka gama cheering, sannan akace mu shigo, na juya na kalli tawagar kawayena duk sun saka ankon su na jan lace da yellow head, ga Hafsat a kusa dani ita kuma da yellow kace da jan head a matsayinta na maid of honour. A hankali muka fara tafiya, flower girls dina na gabana su biyar da fararen kayansu suna tafiya suna watsa flowers, sai ni da Hafsat na rikr hannunta kamar zan balla shi, sai kuma sauran kawayen mu a baya. An saka mana namu kidan da ban na musamman, muna shiga kowa a gurin ya mike tsaye muka fara tafiya akan red carpet din da aka shimfida mana direct zuwa high table. Straight idona ya shiga cikin nasa, a hankali na saki hannun Hafsat dana rike. Irin yadin jikina shine a jikin sa shima amma nashi color golden brown ne da aikin cream, wato kayansa kalar aikin kayana ne kayana kuma kalar aikin nasa. Yayi kyau sosai, for the first time ya gyara gashinsa ya kwantar dashi baya ya dora hularsa da tasha adon stones. Murmushin fuskarsa from ear to ear. Nima murmushin na mayar masa. Sultan bai iya jira mun karaso gurin sa ba ya sauko daga stage din ya taho gurin mu, nan take gurin ya dauki ihu da tafi, yazo ya miko min hannunsa na kama muka karasa high table tare. Sai da muka zauna sannan kowa ya zauna. Aka fara gabatar da addu'ar sannan aka fara programs. Anyi abubuwa da yawa, jokes, speeches da sauran su. Amina da Amir ne suka ce suna da surprise for us, nan suka fara displaying pictures din mu ni da sultan tun muna yara, Sultan dan lukuti abin dariya, har da picture dina da Pampers fuskata duk chocolate, aka cigaba da nuno mu muna girma har zuwa yanzu, akayi ta saka pictures din mu tare, da wadanda muka yi a America da na England da na nan. Abin yayi kyau sosai. Sultan yayi introducing dina to most if his friends da suka zo gurin including the gang bang, ina ganin su na ga basu yi min ba sam amma da dake nayi musu murmushi muka gaisa suka tsokane ni suka wuce. MC ne yace zamuyi playing game wanda zai nuna how much do we know each other. Handkerchiefs aka saka aka rufe mana idanun mu, sannan aka chire mana takalman mu, aka bani daya nawa daya nasa a kowanne hannu, shima aka bashi. Daga nan mc ya fara yi mana tambayoyi yace min in amsar Sultan ne sai in daga takalmin sultan in kuma Moon ne sai in daga takalmina. Ya fada wa Sultan ma the same thing. Daga nan ya fara jero mana tambayoyi kamar; waye yafi fara'a a cikin ku? Na daga takalmina, waye yafi tsafta? Na daga takalmin Sultan, who is the smartest? Na daga takalmina, who is the best cook? Na daga takalmin sultan, who love food the most, nan ma sultan na daga. Haka yayi ta mana tambayoyi ni dai ina amsawa amma bansan amsar da sultan yake bayarwa ba tunda idona a rufe yake. Ga mamaki na duk amsar dana bayar sai inji hall din ya dau ihu da tafi, anan na fahimci cewa the same answer muke bayarwa ni da sultan, it is like mind din mu tana working a tare, har mc ya gama tambayoyin daya rubuta ya koma karawa up head amma ba muyi missing ko answer daya ba. Gaba dayan mu dariya muke yi, we know our selves so much we are like two bodies with one soul. Finally, MC yace final questions, a cikin mu waye yafi son wani the most? Gaba daya gurin yayi shiru ana jiran amsar mu, muma kuma mukayi shiru din, sai daga baya a tare muka daga hannu, ni na daga takalmina ina nufin son da nake wa sultan yafi wanda yake min shi kuma ya daga nasa yana nufin son da yake min yafi wanda nake masa. Lol. Ai kuwa gaba daya hall din ya hargitse. MCn ma kasa magana yayi, sai daga baya yace "this means that the love is equal" daga baya aka bude mana idon mu. Bayan an nutsu aka kawo mana cake muka yanka. Akayi hotuna da family da friends Sai kuma aka ci abinci aka rufe taro da adduah.
Friday
A gajiye nake likis dan har saida nasha paracetamol sannan na danji dai dai, luncheon din da akayi is very brief and not as grand as dinner din jiya. Muna gurin luncheon din ne Amira tazo, ta zo guri na tace "hi" nima nace mata "hi" tace "kinyi kyau" nace "thank you" ina lura da sultan yana kallon mu ganin irin yadda muke magana casually amma bai ce komai ba, ta sauka ta tafi can wata corner ta zauna ita kadai saboda ba zata iya shiga cikin kawayen mu ba.
Babu kyau baccin bayan la'asar amma ranar sai da nayi, muna zuwa gida nayi sallah kawai na kwanta na rufe kofa nace kar wanda ya tashe ni, ban farka ba sai ana kiran magrib sannan na tashi na bude kofa nayi sallah na kira sultan muka dan taba hira sannan na sauka kasa. Ji nake yi duk jikina babu dadi saboda ina tunanin yau ce rana ta ta karshe a gidan mu, duk sanda zanzo sai dai inzo a matsayin bakuwa. A kasa muka zauna gaba dayan mu tun daga kan daddy har faruk, suma kamar masu yi min farewell, anan mukayi dinner tare suna ta tsokana ta, sai da suka ga na fara musu kuka sannan suka rabu dani. Daddy da Mommy suka tashi suka tafi suka bar mu. Muna ta hira har sallar isha, su yaya walid suka fita mosque suka dawo, can nace musu "wai ku ba za kuje bachelor's night din bane" yaya Habeeb yace "Allah ya kiyaye. Wannan night din ai yafi karfin mu" ban gane me yake nufi ba nace "saboda me?" Ya walid yace "kin san menene bachelor's night ma kuwa?" Nace "I thought kawai it is just a funny guys' thing. Just to have fun" yace "exactly" nace "to menene laifi? Don't you want to have fun?" Yace "ya danganta da irin fun din da za ai having" nayi shiru ina kallonsa yace "look parrot, wadanda suka shirya wa Sultan bachelor's night dinsa are not my kind of people, dan haka yana yi min magana nace ba zamu je ba"
Ban sake cewa komai ba nayi shiru ina tunani, su waye suka shirya masa? Take na samu amsata, the gang bang. Lokaci daya naji hankali na ya tashi. Tun da na dawo daga Niger ban kuma ganin sultan a buge ba, kuma bana jin ko a bayan idona yana sha duk da bamu taba maganar ba.

Please Login or Register in order to submit comment