Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tsananin fushi, duk da cewa a buge yake, bana jin akwai wani abu nashi da ba zan iya facing ba"



Episode Seventy : The Wedding Night 3

Kafin mu dora a inda muka tsaya, bara mu dan taba magana akan abinda ya faru ranar kai amarya.

Abinda ya faru ba laifin Ibrahim bane gabaki daya, Moon tana da laifi haka zalika Sultan. Laifin Moon anan shine keeping secrets in a relationship. Wannan shine babban abinda yake wargatsa relationships, ko aure ko kafin aure. Idan kinsan ko kasan da akwai wani abu da kake ko kike boyewa partner dinki/ka to ku fito ku fada, ko da kuwa abinda zai bata masa/ta rai ne, gwara ya/ta sani daga gurin ki/ka akan suji daga wani guri, idan ke zaki fada kinsan da kalaman da zaki yi amfani, idan kuma wani ne zai fada zai iya ya kara har da gishiri da maggi kuma babu yadda zaka/ki yi ka/ki kare kanki. Wannan kuma shi zai kawo rashin yarda, ita kuma yarda da juna ita ce ginshikin ko wanne relationship.

Laifin Sultan kuma shine na yarda ayi organising party a cikin gidansa, wannan mistake ne babba. Ba tsohon saurayin matarka ba hatta su kansu abokanan ka basu da hurumin shigo maka gida irin haka. Ni a ra'ayina ina against siyan bakin amarya da abokanan ango suke zuwa yi. Kwanan baya anyi ta samun cases na raping amare, ni ina ganin wannan siyan bakin da kuma yawan kwashe2n abokanai zuwa ganin amarya yana daya daga cikin abinda yake kawo wadan nan cases din. Ballantana wanda yake da abokanai irin na Sultan.

Laifin Ibrahim kuma shine da yabar emotions dinsa sukayi controlling dinsa ya yanke hukunci ba tare da bincike ba. Babban mistake din da mutum zai yi shine ya yarda da maganganun mutane. Hear say. Wannan ya kara gishirinsa, wancan ya kara maggi wancan ya kara onga, before you know it gaba daya maganar zata chanza salo. Believe only what you see da idonka, ko kuma maganar da kaji direct daga mai ita, ba wai wani ya gaya maka yace wane yayi kaza ko kuma wane yace kaza ba.

Please guys, be a little softer on Ibrahim. He has gone through alot akan soyayyar Moon. He really deserves a break. Amma naga kowa dariya yake masa. Lol. Ni kam #teamIbrahim nake yi, na hana shi auren Moon ne kawai saboda a haka ne ma'anar labarin zata fi fitowa. Please, I am on my knees ku dan rangwanta masa mana.

Back to the story.
Mun jima muna tattaunawa akan abinda ya faru, anan ne Hafsat ta bawa Amina labarin alakata da Ibrahim, yadda Amira ta raba mu da kuma labarin rayuwar Sultan, Amina duk jikinta yayi sanyi ta kasa maganar kirki. Na durkusa a gabanta na rike hannunta nace "Amina, sam yanzu bana yiwa Ibrahim soyayyar aure, amma still ina jinsa a raina kamar dan'uwana haka nake jinsa. Na tausayawa rayuwar da yayi bayan rabuwar mu kuma ina tausayin halin da yake ciki a yanzu. He thinks he is doing a good thing. He thinks I am in trouble. He needs an explanation. He needs to know the whole truth. Dan Allah Amina ina son kiyi reaching out to him kiyi masa bayani yadda zai gane sosai cewa ni na zabi sultan duk da halayensa. Kiyi masa bayanin cewa sultan is not as bad as people think ge is. Ki bashi duk wannan labarin da muka baki yanzu ki gaya masa cewa na auri sultan saboda ina sonsa, saboda ina ganin soyayyata zata kawar da duk wani mugun hali nasa, kuma so far I have succeeded. Ki gaya masa kyaleshin da Sultan yayi yau alama ce ta cewa he is no longer who he was before" tunda na fara magana Amina take girgiza kanta alamar ba zata yi ba, ni kuma ban daina maganar ba har saida nazo karshe, tace "No, Moon, bazan iya ba, ba zai saurare ni ba, yaudara ta fa yayi ya saka na shigo dashi har cikin gidan ki" na kara rike hannunta nace "please Amina, you are my only hope akan sa, duk da yadda nake son in taimaka masa ba ni da yadda zanyi sai ta hanyarki kadai, please help me as your sister" da kyar na samu tace maybe zata yi in ta huce saboda taji haushin using dinta da yayi. Muna cikin haka Amir ya dawo yace amina tazo ta taya shi su kwashe abincin partyn da ba'ayi amfani dasu ba, wadanda ba zasu lalace ba suka shiga dasu suka adana, wadanda kuma zasu baci Amir ya aika dasu cikin gida. Ni da Hafsat kuma muka shiga ciki muka koma cikin bedroom dina muna cigaba da jajantawa, kafin su Amina su gama sai around 12:30, dan haka dole kwana ya kamasu a gidan. Hafsat ta kira zayed wanda tunda yazo bikin ya kama hotel, kullum da daddare yake lallabowa ya dauke matarsa sai da safe yake dawo da ita, ta gaya masa zata kwana a gida na saboda dare yayi. Sai da duk mu kayi wanka muka yi shirin kwanciya sannan naga sun tashi suna yi min sallama wai wani dakin zasu tafi su kwanta. Nace "saboda me?" Hafsat ta harare ni tace "oho miki, yau ne fa first night dinki, kawai kuma sai muzo muyi dare dare akan gado? In angon ya shigo kuma fa?"

Na kasa basu amsa har suka fice. A raina nace "wannan angon nawa ai Allah ka dai yasan inda yake" nayi tunanin in kira wayarsa inji ina yake amma kuma kar ya dauka wani abin nake nema. Na kwanta ina kallon dakina, karshen kyau yayi kyau, babba ne sosai dan duk girman gadon baifi quarter din dakin ba, babu ce kawai a kayan da ake bukata a daki Daddy da Mommy basu saka min a dakina ba. Komai yaji, komai da akwai except ango. Ina Sultan ya tafi? Na gyara nayi kwanciyata duk jikina yana yimin ciwon gajiya amma sam babu bacci a ido na, nafi 30 minutes a haka sai kuma na mike zaune na jawo wayata nayi dialing number dinsa, switched off, yayi fushi, nasan he has the right na yin fushi dani amma abinda yafi damuna shine abinda zai aikata a cikin fushin nasa, ya Ilahi give me the strength. Number din Amir na lalubo na kira, bugu daya ya dauka da alama bai kwanta ba, sai kuma na rasa mai zance masa, yace "Moon baku kwanta ba? Ko akwai abinda kuke bukata ne?" Nace "amm babu komai, dama ina son inji ko Sultan yana tare da kai ne?" Yace "No, ban ganshi ba, na dauka kuna tare ai" nace "a'a ai tunda ya fita bai dawo ba" na dan yi jim sai kuma yace "OK bara in duba shi" na zauna akan gado na harde kafata ina jiran tsammani, can Amir ya kira ni yace "naje har gate na tambaya sunce bai fita ba, kuma naga duk motocinsa da suke gidan nan suna nan, yana cikin gidan, kin duba part dinsa" na girgiza kai kamar yana kallona nace "a'a ban duba ba" yace "ok, ki duba can" nace "to na gode" sai kuma yace "Moon, he will be alright, Sultan is a tough guy, ya fuskanci abubuwan da suka fi wannan kuma yayi surviving. Idan kin duba baki ganshi ba just kiyi baccin ki, let him be, mostly in yayi zuciya yana rufe kansa a wani gurin ne ya zauna shi kadai har sai ya huce, you will be surprise in yazo zaki ga kamar ba'ayi komai ba" na ce "OK, thank you Amir, really thank you, for everything" yace "you are welcome". Banje part din Sultan neman sa ba, na dauki shawarar amir, I will let him come back on his own. Na koma na kwanta ina tunanin lamarin duniya, kana taka Allah na nasa, na tuna irin threats din da sultan yake min akan first night din mu, amma gashi ranar tazo, kuma anyi auren , kuma muna gida daya amma kuma zamu kwana a separate bedrooms. Na tuna baccin mu na jiya akan balcony da abinda ya gaya min sanda muka tashi, nayi murmushi ni kadai. I don't know a ina Sultan yake yanzu, but I know one thing for sure, he is not going to sleep tonight.

A hankali na bude ido na, ji nayi kamar yanzu na kwanta, amma kuma ina jin a jikina kamar gari ya waye, nayi sauri na kalli window naga haske yana shigowa. Na mike zaune da sauri na kalli agogo, 8:30, inna lillahi, ko sallar asuba banyi ba, na shiga uku, wannan wanne irin bacci ne kuma ko juyi banyi ba. Da sauri na shiga toilet nayo alwala nazo na gabatar da sallah sannan na tashi na gyara gadon dana kwanta na koma toilet nayi wanka na dawo daki, tun kafin in fara shiryawa na kira wayar sultan, still switched off, na shafa mai na shirya cikin lace coffee color, riga da skirt da suka kama jikina suka zauna sosai, na gyara kitso na, na bayan ya sauko har gadon bayana, na gaban ma na sake tufke shi yabi ta saman idona ya sauka a wuyana. Na fesa turare na na fito ina neman dakin dasu Hafsat suka kwana, dakin kusa da nawa basa ciki, na kalle shi naga kusan irin nawa ne amma nawa yafi shi girma. Na fita ta dan corridon da zai fita dani palo na, anan dakin ba'kina yake, na murda kofar na gansu sun ba rarraje suna kwasar bacci, nayi murmushi a raina nace 'sun gaji' na duba agogo naga kusan karfe goma, ni kam yunwa nake ji, na dan daki kafar Amina "ke ku tashi fa, kun ma yi sallah kuwa?" Hafsat ta sake jan bargo, nayi ajjiyar zuciya dan nasan ko nafi kuda naci Hafsat ba zata tashi ba, Amina na takurawa sai da ta tashi tana ta kunkuni wai ita bacci bai ishe ta ba an takura mata. Nan na barta tana kokarin shiga wanka na fita ina zagaya gida, a raina ina lissafin Sultan ne fa yayi min alkawarin zai zagaya dani, nasan lissafin yadda gidan yake a raina dan haka ban wani sha wahala wajen gano part din Sultan ba, na tura main kofar sa naji a bude take, na shiga palon sa, na jima a tsaye ina shakar kamshinsa, unique kamshin da yake sakani lumshe idona kullum na jishi, a hankali nake tafiya ina karewa palon kallo, kusan irin nawa ne sai dai ban bancin arrangement din kayan ciki, na shiga corridor dinsa, shima two bedrooms ne dashi irin nawa amma shi bashi da dakin bakin da nake dashi a palo, instead sai akayi part din baki maza daban wanda sai ka fita can main palo sannan za ka shiga gurin. Bedroom dinsa na farko bayanan, kamar ma ba'a taba shiga dakin ba, bedroom dinsa na biyu kuma ina shiga naga alamar anyi amfani dashi amma ba'a kwana a ciki ba, har da kayan sa da yaje daurin aure dasu akan gado, daga dukkan alama sauri yake ya shirya ya tashi gurin party kuma daga can bai dawo nan ba. Na juya jikina a sanyaye na fita. Ina sultan ya kwana? A main palo naga Amina ta fito suna zaune da Fa'iza suna ta zuba surutu, ina shigowa suka bini da kallo, fa'iza tace "wow, masha Allah, babbar yaya kinga yadda kikayi kyau kuwa? Kowa ya ganki yasan babu tantama amaryace" sai kuma ta leka bayana kamar mai jiran wani ya biyo bayana, sai kuma ta rage murya tace "ina angon? Ina fatan dai ba nan zai fito ba dan takura mana zai yi da harara da tsawa" nace mata "sha kurumin ki, baya nan, ya fita already" ta bini da kallon mamaki tace "ya fita kuma? Wanne irin ango ne haka zai fice da sassafe?" Nace "kinsan abokanan sa da suka zo bikin nan wadansu ma bada ga kasar nan suke ba, to duk yau zasu tafi shi yasa ya fita da sassafe dan suyi sallama" daga dukkan alamu ta yarda da bayani na, tayi ajjiyar zuciya tace "har naji dadi, na dauka har an fara gwadawa amaryar halin, kinsan fa sai kinyi hakuri wallahi, dan indai yaya Sultan ne sai ya saka miki ciwon zuciya, dan wani lokacin inya fice sai yayi kwana da kwanaki bama a san inda yake ba" dariya na mayar da maganar nace "really? Kice za'a samu chanji kenan yanzu. Kar ki damu daga yau duk sanda kike bukatar ganin yayanki kizo nan zaki ganshi, in kinga bayanan to office ya tafi" ta tabe baki tace "to Allah yasa" sai kuma tace "dama Hajiya naji tace azo a kawo muku breakfast shine nace bara in zo mu gaisa in kuma ga gidan sosai. Ga abincin can akan dining an ajiye" nace mata "mun gode, in kin koma ki mana godiya a gurin Hajiya" tace "laah chafdi, yaya Sultan fa duk gidan nan shine dan lelen Hajiya, kinga shi ba'ayi masa fada, ba'a saka shi ba'a hana shi, duk abinda yake so shi za'ayi masa, dan haka in kika ce zaki yiwa Hajiya godiya har sai baki kin ya gaji" muka kalli juna ni da Amina, Amina tace "ashe sultan dan gata ne mu bamu sani ba. To shi kuma daya brother din naku fa? Shi ba'ayi masa gatan?" Fa'iza tace "shi wannan ai sha wuya kenan. Shi fa ko time din kansa bashi dashi. Kullum yana tare da Takawa bacci ne kadai yake rabasu, komai nasa shi yake yi. Shi wannan ma banajin ko budurwa yana da ita. In kinga kuwa fadan da Hajiya take masa komai kankantar abu sai kinyi mamaki" Amina ta cigaba da bugar cikin ta "abin tausayi, kice ko karatu mai zurfi bai samu yayi ba kenan saboda bashi da lokacin kansa" tace "kamar kin sani kuwa, da kyar ya samu yayi diploma ya hakura, Hajiya tace masa menene amfanin karatun? Ai anayin karatu ne saboda a samu aiki ake samun kudi, shi kuwa he got all the money to last him a lifetime, aiki kuwa dama dashi aka haifeshi" Amina zara cigaba da yi mata tambayoyi na girgiza mata kai, na chanza topic din da cewa "ni fa duk wannan hirar da kuke yi ba jin ku nake yi ba, dan yunwa nake ji" daga nan muka tashi muka tafi cin abinci. Muna cikin ci Hafsat ta fito, taci kwalliya kamar ita ce amaryar, tayi joining din mu muka ci abincin tare. Dankali ne da kwai, sai farfesun kaji da farfesun ganda, sai kunun gyada mai dadi wanda ni shi nayi tasha, dan sam baki na babu taste, Sultan ne kawai a raina. Nace da Hafsat "kiyi waya mana a kawo khairat, kar tayi ta kuka" tace "ba zatayi rigima ba, nayi expressing breast milk da yawa na saka mata a freezer, da anyi warming an bata shi kenan".

Ranar tamkar wanda ake sake yin wani bikin a gidan, dan sosai gidan ya cika da mutane mostly 'yan uwan sultan masu son ganin amarya da kuma dakin amarya. Na gode wa Allah dasu Hafsat basu tafi sun barni ni kadai ba, dan su sukayi ta hidima dasu suna zagayawa dasu daki by daki, kowa kuwa sai ya yaba da tsarin gidan. Duk kuma wanda yazo sai Amina ta zuba musu kayan gara da snacks din partyn jiya da ba'ayi ba ta bashi. Ni kuma akwatin lefe na na kayan kyalliya guda daya na bude nake rabarwa. Har magriba muna abu daya. Hafsat tayi waya gida ta gaya musu sai dare zasu dawo saboda baki sun yi min yawa, nan da nan sai ga yammata biyu Mommy ta sake turo wa, suka taho da katan katan na drinks da chocolate saboda yara. Abinci kuwa daga cikin gida akayi ta aiko mana, dan haka ko tukunya bamu dora ba. Sai da mukayi sallar magrib sannan kafa ta fara daukewa. Har lokacin babu Sultan babu labarin sa. Na kira wayarsa har na gaji amma still switched off. Bayan munyi dinner muka hadu muka gyara gidan tas har fa'iza da yake bata tafi ba. Muna gamawa muka zauna muna hira, hafsat ta lura ina ta danna wayata ta sake tambayata a hankali "har yanzu bai kunna wayar ba?" Kai kawai na gyada mata, tace "ki kira Amir, shirun yayi yawa" na sake dialing number din Amir, ya dauka muka gaisa yace "ai nayi niyyar shigowa dazu kuma na hango gidan a cike na fasa" nace "wallahi kam yau gidan masha Allah" nayi shiru, yace "bai dawo ba?" Nace "eh, kuma wayar a rufe" yace "amma da mamaki, kusan 24 hours fa kenan" naji hankali na ya kuma tashi. Yace " I will know what to do, am sure yana cikin gidan nan tunda duk friends din mu da suka tafi a gaba na suka tafi kuma bai shiga motar kowa ba, sannan all his cars are here. Za muyi organizing search party mu nemo shi duk inda ya shiga" nace "to na gode, duk abinda ake ciki dai sai a sanar mana" ina kallon Fa'iza tana kallona tana son ta san maganar me nake yi. Tace "wai yaya sultan ba zai dawo bane har yanzu? Tun safe fa nake gidan nan amma baya nan" Hafsat tace mata "a cikin mutanen kike so ya shigo ya zauna?" Tace "a'a wai dai ko yaya ne ai a gaisa dashi. Gashi har dare yayi kar mu tafi mu barta ita kadai"

Bayan sallar isha Amir ya shigo, muka gaisa, nasan ganin fa'iza ne ya saka bai ce min komai ba, sai ya zauna kamar mai daddanna waya ya turo min text, 'couldn't find him, think we report to the police?" ina karantawa naji wani daci a bakina, amma kuma ina jin a raina cewa duk inda yake he is OK, dan da ace wani abun ya same shi da na tabbatar zanji a jikina. Na dago kai na kalli Amir naga baya kallona, nayi masa reply "bashi da wani secret hiding place a cikin palace dinnan? Kamar gurin da yake zama if he wants to be alone?" Ya amsa min "nan spot din dama shine gurin zamansa, cikin trees, yanzu kuma ya sare su yayi gida a gurin" ina tunanin abinda zance masa kawai naji wani feeling like someone is watching me, and that someone is Sultan, nayi sauri na dago kaina na kalli direction din da nake ji feeling din, bakin kofa, and there he is. Har yanzu kayan jiya da daddare ne a jikinsa, fuskarsa babu murmushi kuma babu bacin rai, idanuwansa tarwai a kaina. Nayi sauri na dauke idona na sunkuyar da kaina kasa, har lokacin babu wanda yasan ya shigo palon. A hankali ya fara magana, daga jin muryarsa kasan ya dan jima baiyi magana ba. Yace "waye ya baku izinin ku mayar mana da gida dandali?" Duk suka juya suka kalleshi da mamaki, ni kuwa har lokacin ban dagi kaina ba. Amir ya mike kamar zai ji tsalle yace "I think what you want to say is thank you for keeping my house alive and keeping my wife company" bai bawa Amir amsa ba ya juya yana kallon fa'iza yace "ke, tashi ki fita" jiki na rawa ta mike tace "to yaya babu driver a kusa" yace "Amir ya kaiki" ya karaso tsakiyar palon inda Hafsat take ta watsa masa harara, bai kula ta ba sai da fa'iza da Amir suka fita sannan yace "waye yace kuzo ku cika mana gida da surutu?" Ta yatsine fuska tace "gida? Ina gidan yake? Ai kasan tun kafin ayi daran akayi kwandi, tun kafin kusan zaku yi gida ni da mijina muke da gida, sau nawa kuke zuwa kuna zamar mana a gida bamu taba yi muku gori ba?" Yace "eh din, amma dai bamu je ranar da aka kaiki munyi bake bake mun hana Zayed zuwa gurinki ba" tace "to ai mu bamu muka hana ka zuwa ba. In baka sani ba ka sani, da Allah da annabi ta roke mu muka zauna ai, haka kawai ni an raba ni da mijina an zo an kawo ni cikin hayaniya an saka min ciwon kai" sun jima suna bugawa da Hafsat, daga karshe tayi zuciya ta tashi ta tafi daki. Ya juyo kan Amina da take ta dariya yace "ke kuma waye ya baki ikon saka kayan da ba naki ba?" Ta kalli kayan jikinta ta kalleshi tace "Allah yaso ma kayan 'yar'uwata ne ba kayan wani ba" yace "ni kuma kayan matata ne, sai ki gaya min waye yafi kusanci da ita" tace "to ai miji da mata suna iya rabuwa, dan'uwa kuwa har bada naka ne" yace "ba dai wannan miji da matar ba" tace "shi yasa naga ka tafi ka barta jiya, sai mu din dai 'yan'uwan nata mu muka zauna tare da ita" yace "sai kuma gashi na dawo yau kuma nace kowa yasan nayi, I need to be with my wife, alone" ta mike itama a fusace tace "in kaga na sake dawowa gidan nan sai kunje har gida kun bani hakuri" ina jinsa yana dariya kasa kasa, kafin ta karasa kofar shiga part dina sai ga hafsat nan ta fito musu da jakankunan su ta mikawa Amina tata tace "muje, gobe ma rana ce ai" har sunje bakin kofa Hafsat ta juyo tace "kuma ka sani, kamar a kunnen Zayed, sai na gaya masa ka koreni daga gidan ka" ya bita yana "haba babbar yaya matar babban yaya, ni na isa in kore ki" ya bisu kamar mai basu hakuri, suna fita ya jawo kofar yayi locking yana dariya kasa kasa.

Har lokacin ban dago kaina ba, jinsa nayi shiru na dan gado kadan sai muka hada ido, nayi sauri na mayar da kaina kasa. Dariya yayi sosai sannan ya karaso inda nake zaune, ya zauna a kusa dani ya dan kwantar da kansa a kafada ta, gashin kansa yana gogar side din fuskata, ya kamo hannuna ya rike yana wasa da zobe na yace "Am sorry love, please forgive me, na bar zuciyata tayi controlling dina na daga miki murya a cikin mutane, sannan nazo na tafi na barki ke kadai a first night din mu. I don't know what came over me wai har ni ne na saka miki gun a hannunki. Wannan shi ya saka na kasa dawowa mu hada ido dake tun jiya, I am so ashame if myself. I don't know what to do with my temper" kasa ce masa komai nayi saboda ni basan ni ya kamat in bashi hakuri bashi ba, ni ce nayi masa laifi, duk abinda yayi yayi ne saboda ransa ya baci, kuma nice na bata masa ran. Jin bance komai ba sai ya sauko daga kan kujerar ya durkusa a gaba na ya dora fuskarsa akan cinyata yace "nayi kneel down, in still baki hakura ba kuma zan yi frog jump" nayi murmushi a raina nace "this is my sultan" na dora hannuna a hankali akan gashinsa kamar mai shirin taba wuta, a hankali na fara shafawa, it feels very soft, softer than I imaging. Ina jinsa ya sauke ajjiyar zuciya tare da kara pressing kansa a hannuna. Na fara magana nima a hankali "ni ba kayi min komai ba ballantana har ka nemi yafiya ta, nice nayi maka laifi, nice nayi keeping secret from you, duk da cewa kai baka taba boye min komai akan ka ba, u have the right to be angry at me, am sorry" ya dago kansa yana kallon fuskata yace "we are even then" ya mayar da kansa ya kwantar, na dan ture shi nace "it is not over though, ina kaje? A ina ka kwana ka wuni ka barni da tunanin halin da kake ciki, babu inda Amir bai duba ba a gidan nan baka nan" yana dariya yace "shi Amir din ne yace miki ya duba ko'ina? The fool. Ina part dinsa fa, ina guest room dinsa" nima dariyar nayi, sai da muka gama dariyar mu sannan nace "you really need a bath" ya langwabe kai "no, I need food first, then a bath and then you"

Maimoon is now on wattpad, follow me at @MamanMaimoon


Episode Seventy One : The Honeymoon

Hmmm let's talk about

Please Login or Register in order to submit comment