Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ganin mu ko? Dadinta dai muma gidan zamu tafi muma mu huta" sai a sannan nayi magana nace "are u going home also" ya kalleni da seriousness yace "yes, i am going tomorrow, there is nothing for me to do here in kun tafi" na hadiye wani kululu da ya tsaya min a wuya na nace a hankali "ok". Mukayi shiru for sometimes sannan yace "i will see you guys tomorrow before you go" Amira ce kawai ta bashi amsa da ok
sir. Daganan muka tafi hostel. Duk jikina a sanyaye nake shirin tafiya, tamkar wacce ta tashi daga jinya haka nake ji na. Washegari tun a assembly ground nake ware ido ko zan ganshi amma babu shi babu alamarsa. Gashi wannan abun da ya tsaya min a makogwaro na har yanzu yaki wucewa. Wajen karfe goma aka bude get motoci suka fara shigowa. Hafsat sai ware ido take tana neman motar gidan mu ni kuwa adduah nake yi a raina kar suzo yanzu sai na ganshi. Muna cikin haka na hango motar mu tana shigowa, na lura Hafsat bata ganta ba sai nayi sauri nace mata "Hafsat zan danje toilet kafin azo daukan mu" batare data kalli inda nake ba tace "ok" na juya da sauri nayi hanyar classes ina ta waige waigen ko zan ganshi, har naje get din hostel ban banshi ba, kuma na tarar har an rufe get din dan haka na juyo, hawaye naji mai zafi yana tahowa daga kirjina amma naki na barshi ya karaso idona saboda kar a gani a tambayeni dalilinsa. Ina tafiya kaina a kasa naji an kama hannuna an jani da sauri cikin wani class, da sauri na kwace hannuna ina neman hanyar gudu sannan naji wannan mayataccen kamshin nasa ya ziyarci hancina, na juyo da sauri muka hada ido. Ya saka complete kaki na NYSC a jikin sa, p-cap din ya juya ta tana kallon bayansa, da wata katuwar school bag a goye a bayansa. Fuskarsa babu murmushi. Mun jima muna kallon juna sannan nace"i thought ka tafi" ya hadiye yawu adams apple dinsa ya motsa sannan yace "I am sorry, an kira mu meeting ne tun safe, i was really pissed na dauka bazan same ki ba" naji dadin maganarsa har cikin raina, take naji wannan kululun da ya tsaya min a wuya ya narke yana tafiya. Nayi murmushi nima nace "I was afraid ka tafi without saying goodbye" ya matso gaf dani yanda har muna iya jin lumfashin juna, sa saka hannayensa biyu ya ruko fuskata idonsa cikin nawa yace "I will never" a can kasan zuciya ta nake jin tana min warning cewa in kwace fuskata daga hannunsa in matsa daga kusa dashi amma jikina yaki yayi responding, na kasa koda dauke ido daga cikin nasa ballantana in matsa. A hankali ya sauke idonsa daga ido na zuwa kan lips dina sannan ya fara sauko da fuskarsa zuwa ta wa. I was screaming at myself from the inside, nasan what he was about to do, nasan kuma it is wrong but I failed to stop him. Kamar wanda akayi wa shocking sai kuma yayi baya da sauri sannan ya juwa min baya yana furta "A'uzubillahi minash shaidanir rajim" sannan ba tare da ya kalleni ba yace "go maimunatu, just go" sai a sannan naji jikina da dawo dai dai, da sauri na bude kofar class din na futa jikina yana ta rawa. Ina fita na hango Hafsat tana tahowa daga hanyar hostel, daga dukkan alama ni take nema, gurinta na tafi da sauri ina kiran ta. A tare muka karasa gurin motar mu Ya Walid yana ta fada wai na bata masa lokaci, ni kuwa hankali na har lokacin bai gama dawowa jikina ba. Muna shiga mota sai ga Amira da sauri tana tsayar damu. Muna tsayawa ta bani wani littafi wai inji Ibrahim. Wani novel dinsa ne Sands of time. Abin mamakin shine ni ban ce masa ina so ba, asali ma ni ba ma'abociyar karatun novel bace. Na karba na saka a hand bag dina muka yi sallama da amira muka tafi.
Kafin muje gida har na ware, Ya Walid yana gaya mana su Inna sun zo tare da Amina (wata cousin din mu sa'a ta a 'yalleman) dan haka muna zuwa gida da murnar mu muka tafi gurin mommy, daddy baya kasar a lokacin, muka tarar an shirya mana abinciccika iri iri, nan muka hadu gaba daya a falon su inna har daada muna cin abinci muna hirar yaushe gamo, Ya Walid yayi tayi mana hotuna saboda washegari zai tafi England hutun sa ya kare. Gaskiya ba abinda yafi Family dadi. Kowa yabar gida gida ya barshi. Har dare muna tare ana ta hira, ga mamakina Hafsat bata yi zancen Ibrahim ba. Sai mommy ce ma tace " Hafsat kina zuwa extra lessons din kuwa?" Hafsat tace "Eh, mommy ina zuwa" mommy tace "good, saboda bana son Moon take zama ita kadai tare da wannan malamin naku, kuma bana son in hana ta saboda naga tana benefitting" sai a sannan na gane manufar mommy ta hada mu da Hafsat, lallai ance abinda babba ya hango yaro ko ya hau dutsen dala ba zai hango ba.
Sai da dare yayi sannan muka koma part din mu. Na hada ruwan wanka na shiga tub sannan na fara lissafa abubuwan da suka faru. Tabbas maganar da Amira ta gayamin gaskiya ce. Shaidan yana iya shiga tsakanin 'yan uwa ciki daya ma ballan tana mu. Kuma tabbas I am attracted to Ibrahim kamar yadda ta fada, tunda gashi dazu ya kusa kissing dina kuma ban hana shi ba. I am weak. Zuciya ta is too soft. Ko zan cigaba da alaka da Ibrahim sai na dage sosai. Daganan na tuna da littafinsa a cikin hand bag dina. Bayan na fito daga wanka da shirya cikin riga da wando na bacci sai na dauko littafin na kwanta ina dubawa kawai sai naga takarda ta fado. Ina dauka naji kanshin turarensa a jiki, na bude naga rubutun sa kamar haka.
MAIMUNATU
I CAN NO LONGER STOP MYSELF FROM SAYING THIS, BELIEVE ME I TRIED. MAIMUNATU I LOVE YOU. I NEVER KNOW WHAT LOVE FEELS LIKE BUT I AM 100% SURE THAT THIS IS IT.
I AM NOT SURE IF YOU FEEL ABOUT ME AS I FEEL ABOUT YOU. PLEASE MAIMUNATU, IF MY ANSWER IS NO, CALL THE NUMBER AT THE END OF THIS LETTER JUST SAY NO, THEN I WILL ASK FOR TRANSFER BEFORE YOU RESUME. I CAN'T KEEP SEEING YOU KNOWING YOU WON'T BE MINE.
YOURS IN LOVE
IBRAHIM

An zo gurin, will Moon say yes knowing the consequences or will she say no knowing she will never see him again?


Episode seventeen: Reply

Na jima ina karanta takardar hannuna ina maimaitawa. Amma Ibrahim baka yi min adalci ba, yanzu me kake so ince maka? Yes or No? Ni dai nasan koda wasa bazan tunkari Hafsat da sunan neman shawara ba. Na saka karanta takardar kamar me saka ran ganin ganin chanji a rubutun. Tabbas handwriting dinsa ne, kuma kamshin turarensa ne. Na kai ido na kan number daya rubuta a kasan takardar lokaci daya na haddace ta. Na ninke takardar na mayar cikin littafin, a lokacin Hafsat ta shigo tana hamma, ta kalleni tace " kasa, a gidan ma sai kinyi baccin wuri" nayi dariya ban bata amsa ba saboda I am not in the mood. Ina kallonta tana shirin wanka na dauko littafin Ibrahim na fara karantawa saboda nasan sa idon Hafsa, tana shiga wanka na rufe littafin na saka a kasan filona na kwanta akai. Har ta fito ta shirya ta kwanta banyi bacci ba ina ta sakawa da warwarewa. What should I do? Ni nasan ina son Ibrahim har cikin rai na, wannan bani da tantama akai, amma nasan abu ne mai wahala kasancewar mu tare. Bani da problem da daddy sai mommy nake ji, kallo daya idan tayi min sai na gwammace ban taba ganin Ibrahim ba, Inna da baffa da kawunnai na na 'yalleman zasu iya haka rami su binne ni akan su barni in auri Ibrahim. Ina son family na fiye da komai dan haka maganar inbijire musu ma bata taso ba. A daya side din kuma inna cewa Ibrahim no nasan ba wasa yake yi ba akan maganar barin school din mu, kuma bazan sake ganin saba har abada sai dai wani ikon Allah. Anya zuciya ta zata iya daukan haka kuwa? Anya zan iya ci gaba da rayuwa ba tare da shi ba kuwa? What should I do? A haka bacci barawo ya dauke ni. Cikin bacci nayi mafarki wai gashi muna tafiya da family na a mota a nata hira ana dariya sai naga Ibrahim yana tafiya a kasa shi kadai, sai yayi mun murmushi nima nayi masa, mun wuce shi kenan sai ya fara bin mu da gudu yana kirana a haka har muka yi nisa na daina ganinsa. Na farka a firgice ina addu'ah. Na jima a zaune ina ta maimaitawa a raina cewa 'it is only a dream, you will see him again". Ina tashi na daga pillow na na dauko letter dinsa na je na bude locker din textbooks din mu na saka ta acikin wani biology textbook na mayar na rufe.

Hutun sam banji dadinsa ba, kona saki raina da na tuno da takardar da take cikin locker dina sai inji gaba na ya fadi. Rannan na fito daga wanka ina shirya wa kawai na kalli mudubi sai na fara wondering what happenned to me? Yaushe har nayi girman da zan fara tunanin soyayya? Yaushe daada ta daina goyani? Ni ba shekaru ba ni ba girman jiki ba amma na dora wa kaina wahala? Na tuno daddy da yadda zai zama disappointed in yaji labarin abinda yake faruwa. Da wannan tunanin na saka kayana direct na tafi part din daada, luckily na tarar tana bacci, banyi wata wata ba na dau wayarta na saka number din Ibrahim. Sai da ta kusa katsewa sannan ya dauka yace "hello" da muryar bacci. Dif duka nepar jikina ta dauke na tsaya sororo da waya a kunnena na kasa magana. Ya sake cewa "hello, who is there?" Still na kasa magana kuma na kasa kashe wayar. Ina jinsa yayi tsaki yana kunkuni kasa kasa ya kashe wayar. Na durkushe a kasa ina jin haushin kaina. What has Ibrahim done to me? I can't even say no to him.

Tun daga ranar ban sake gwada kiransaba kuma har hutun mu ya kare banyi making decision ba. Ranar da zamu koma haka kawai naji ni kamar marar lafiya, mommy duk ta dauka bana son komawa ne har tana yi min fada. Kamar tasan abinda yake raina tace "Moon zaku cigaba da lessons din da wannan copper din?" Na kalleta truthfully nace "I don't know mommy" tace "ok in zaku cigaba ki tabbatar kuna zuwa tare da Hafsat, I don't want you staying alone with him" na sunkuyar da kaina kasa nace "ok mommy". Da haka mukayi sallama muka tafi.
Motar mu tana packing na hangoshi a jikin staff room, ya jingina da jikin katanga ya rungume hannayensa a kirjinsa, idonsa akan inda motoci suke ajiye students. Muna fitowa Hafsat ta matso kusa dani tace "wow, he can't wait to see you Moon, can he?" Nayi banza na rabu da ita ina fito da bags din mu, na sake matsowa tace "au ba zaki bani answer ba? Ko saina fada da karfi ya Habeeb yaji? Maybe they can even be friends" na ajiye jakar hannuna nace mata "what exactly do you want to know?" Ta tsare ni da ido tace "is it going to be a Yes or a No?" Nan take naji daci a bakina, so Hafsat ta karanta letter din Ibrahim kenan, amma ban taba ganin mutum mai sa ido a rayuwata irin Hafsat ba. Na tsaya kawai ina kallonta ita kuma tana yi min murmushin mugunta. Ya Habeeb ya zagayo yace "Hey, zaku fara fadan tun kafin in tafi ko?" Hafsat tace "No, yaya Habeeb ba fada muke ba, we are just catching up akan harkar makaranta" Ya Habeeb ya kalleni yace "is she maltreating you, I know Hafsat can be bossy at times" na kalle shi kawai sai naji kwalla tazo min, na rungume shi sai kuka, nayi kuka na mai isata sannan na sake shi, sai a lokacin na lura ashe fada ya ke yiwa Hafsat ita kuma sai rantse rantse take yi cewa sharri nake yi mata babu abinda tayi min. Su duk basu san me yake damuna ba. Ina gama share hawayena na dauki handbag dina na wuce hostel. Ina zuwa hostel ko gado na ban gyara ba na dauko wani pink handkerchief dina mai ratsin purple, na duba locker dina da dauko permanent marker na zauna nayi rubutu a jikin handkerchief din na barshi ya bushe sannan na ninke na fita daga hostel din da sauri. Hanyar staff room na nufa ina tafiya ina share kwalla a ido na, a hanya muka hadu da Hafsat ta fara yi min bala'in na taho na barta da daukan kaya, ban kula ta ba na wuce na bini da kallo. Ina shiga staff room na ganshi yana arranging desk dinsa ya dago da sauri yana kallona, ya taho kamar zaiyi min magana na wuce shi na ajiye handkerchief din hannuna a kan desk dinsa na juya na fita. Ina kallonsa yayi sauri ya dauki handkerchief din sai naga murmushi ya baiyana a fuskarsa. Abinda na rubuta masa shine "I DON'T KNOW WHAT THE FUTURE HOLDS, BUT I WANT TO FIND OUT WITH YOU" na juya na koma hostel.
Washe gari muna shiga class naga students a tsaye a gaban board suna karanta wani abu, na buda su na shiga, rubutun Ibrahim ne akan board "THEN I WILL BE THE HAPPIEST MAN ON EARTH" na juya naje nayi zamana a seat dina. Ina zama sai ga Hafsat ta zo ta tsaya a gaba na tace "then it is a yes" na kalleta cikin ido nace "yes, it is"

Wow, then the battle has begun.


Episode eighteen: what's Next?

Hafsat ta tsaya saroro tana kallona. Sannan ta sunkuyo saitin fuskata tace "yanzu ke Moon kina ganin har kinyi girman da zaki fara soyayya? Har kina ganin kin isa ki yanke wa kanki hukunci? Har kina ganin kin san menene dai dai menene ba dai dai ba?" I was ready for her dan haka ko gezau banyi ba nace "7 years ago, sanda nace inna girma ina so in zama neorosurgeon murna kuka yi ta tayani kuna cewa nayi making right decision, ta yaya kuma yanzu zaki ce min ban isa in making decisions ba? I know what I am doing I just need u to support me please" Tayi min wani kallon wulakanci tace "lallai yau na tabbatar baki da hankali Moon" tayi tafiyar ta ta zauna. Nayi shiru ina tunani, lallai Hafsat bata gama sanina ba har yau.
Mutane da yawa suna cewa I am a genius, amma ni ban yarda ba, na san dai ina da brains kuma I am going to use it here. Tabbas nasan ina son Ibrahim amma hakan bazai sa in barshi yayi meddling with my life ba. Dole zanyi mana katanga tsakani na dashi. I said yes to him saboda bana son ya bar makarantar kamar yadda yayi threatening amma hakan ba yana nufin I will let him romance me ba. In dai har yana sona zai jira ni har in gama sec sch sannan we will see what will happen.

Na gama tsara komai yadda nake so ya kasance. Abu na farko shine; ba zan ke bari muna kebewa ni da shi ba alone. Dan haka ana yin break na tashi a class nayi announcing cewa ina gayyatar duk wanda yake da ra'ayi zamu ke karatu tare. Kusan rabin class din suka ce suna so, nan muka zauna muka tsara timetable ta karatu, kullum da akwai subject din da zamukeyi, za muke fara wa 3pm mu gama 6pm. Nayi inviting duk class din ne saboda nasan kullum dole wani zai zo, baza mu kasance daga ni sai Ibrahim ba.
Abu na biyu da nayi shine na fito da duk textbooks dina na jefa akan desk dina yadda babu yadda za'ayi mutun ya zauna akai, no more sitting on the desk tactic. Iyakacin sa sai dai ya tsaya a gaban board ya gama abinsa ya fita. The next thing da nayi shine ana tashi a school na tafi gurin HOD na Islamic studies na kai masa complain cewa ina so a raba mana class din islamiyya ni da Hafsat, ina so a mayar dani B class. Da kyar na samu ya amince shima saboda muna mutunci dashi sosai tun jss1. Nasan in Ibrahim ya fahimci abinda nayi he will be mad but I am ready for him.

Ai kuwa sanda ya fahinci na chanja class a islamiyya he was furious. Muna zaune muna karatu a new class dina sai gashi ya shigo ya bawa yasaiyadin mu hannu suka gaisa sannan yace "I will like to see one of your students please" nasan ni yake nema amma sai naki dago kaina na dukufa ina karatu, ya sayyadin yace masa "kadan yi hakuri in ba emmergency bane yanzu muna karatu in mungama sai tazo" Ibrahim yayi masa godiya ya fita. Sai da naga saura less than ten minutes mu tashi kuma na riga na biya karatu na sai na tambayi yasayyadi nace zan je toilet, yace min ai it is almost time inna tafi inyi zamana kawai, dama haka nake so dan haka na dauki books dina sai hostel. Hafsat tana zuwa ta fara tuhumata akan menene yasa na chanja class nace mata its none of her business.
Ranar da Ibrahim yazo mana maths yaga na cika gaba na da texbooks, kawai ya tsaya yana kallona ni kuwa na dauke kaina kamar ban san yana yi ba. Duk yadda yaso in kula shi naki yarda har period dinsa ta fita, yazo ya tsaya a gabana yace "see me immediately after school" nace "yes sir" amma ko kadan banyi niyyar zuwa ba. Da yamma muka shirya wajan mu biyar muka fita karatu. Muna zuwa muka yi arranging chairs muka samo wani babban table muka saka, mun fara karatu kenan sai ga wasu ma sunzo, haka muka hadu wajan mu goma, muka shiga library muka karbo aron books da syllabus din term din muna tsara yadda zamu fara karatun sai ga Ibrahim. Tsayawa yayi yana kallon mu fuskarsa cike da mamaki. Yayi kwalliyarsa da sabuwar shadda sai, kamshi yake yi. Ya jingina da jikin library ya rungume hannayensa a kirjinsa ya zubo min ido, kallo daya nayi masa na dauke kai naci gaba da abinda nake yi. Amira ta taba ni tace "mutumin ki fa ke yake nema" nace mata "I know" na cigaba da karatu na, can ta sake cewa "duk wannan kwalliyar fa ke akayi wa" na sake ce wa "I know" taga dai bani da niyyar kulata ta rabu dani, ita Amira bata san zafin da nakeji a raina ba, I missed him alot amma still I want to be strong, na leka ta saman littafina ina kallon shi naga ya dauko wayar sa yana dannawa, nan na samu damar kare masa kallo. Sabuwar shaddar sa kalar ash mai haske ta sha dinkin tazarce da aiki kalar ash mai duhu, hular sa da takalmin sa duk ash mai duhu ne, fatar sa tayi tas. Ina kallonsa kawai sai tsintar ido na nayi acikin nasa, nayi sauri na dauke kaina. Sai kuma ya taso ya karaso inda muke, ina jinsa yana tsokanar Hafsat wai taje gida ta kara kiba, ga mamaki na sai naji ta kulashi tace shima yaje gida ya kara fari, ya dawo kusa da Amira yace mai ta kawo masa daga gida. Kusan saida yayi wa kowa magana a gurin amma banda ni, nima kuma bance masa komai ba.
Washegari muna cikin class sai gashi yazo yace da teacher din mu zai karbi sako a guri na. Ina jin haka nayi sauri nace "I gave Mr Victor to give to you" ya tsaya yana kallona, ni dashi duk munsan babu wani sako da zai karba a gurina, can yace "OK thanks" ya fita fuskarsa babu alamar annashuwa. Ranar da daddare muna zuwa islamiyya naga 'yan A class suna komawa hostel, na tambayi dalili sai suka ce yasayyadinsu yace baya jin dadi bazai samu damar zuwa ba.
Kusan 3 weeks muna haka da Ibrahim, he was so frustrated nima haka, har na fara tunanin anya zan iya kuwa? I am not as strong as I thought I was. San da mukayi wata daya daddy yazo mana visiting tare da yaya Walid, naji dadin visit dinsu saboda I was in need of little love, kuma na samu sosai a gurin daddy, mun dade muna hira kafin su tafi. A ranar da daddare bayan mun tashi daga islamiyya sai yasaiyadin mu tsayar dani akan maganar saukar mu, by the time da muka gama magana dashi almost kowa ya tafi, shima yana fitowa yayi tafiyarsa, nan naji tsoro ya kama ni, ina tafiya ina waige waige. Kamar daga sama naji an fincikeni an hada da jikin katanga, na takarkare iyakacin karfi na zan yi ihu aka toshe bakina da hannu. Duhu ne gurin dan haka na kasa ganin fuskar wanda ya rike ni, jikina sai karkarwa yake yi kamar mazari. A hankali na fara nutsuwa sai a lokacin naji kamshin sa. A bangare daya na zuciya ta naji dadi cewa ba barayon mutane bane ko dan yankan kai, a daya bangaren kuma wani tsoron ne ya shige ni, what is he going to do to me? Nan na fara kokarin kwace kaina daga hannunsa amma maimakon ya sake ni sai ya saka duk kannin jiki sa ya matse ni a jikin bango, na saka hannayena duka biyun na tattara karfina ina tura kirjinsa amma ko motsi baiyi ba, kawai sai na saka kuka, na kifa fuskata akan kirjinsa ina ta kuka na, a hankali a sunkuyo fuskarsa dai dai kunnena yace min "why do you say yes?, tunda kinsan ba kya sona mai yasa kika ce min you want to walk the path to the future with me? Why are you playing with me? Do you have any idea what you are doing to me?" Ya jera min tambayoyin da nasan ba zan iya amsa masa su ba, yasa hannu yana kokarin dago fuskata amma fir naki yarda, ya hakura ya rabu dani, ya sake cewa "ni kawai so nake in san me yasa kika amsa min bayan kinsan bakya sona, kina gaya min zan barki kiyi tafiyarki. You don't love me, right?" A hankali na girgiza kaina, ya saka hannayensa biyu ya dago kaina yana kallon cikin ido na yace "look into my eyes and tell me you love me" wasa ma kenan, na dauke ido na daga cikin nasa nace "I can't" "you can't what" "say it" "say what" "the L word" daga kirjinsa naji sound din dariya amma bata fito bakinsa ba. "Then why are you avoiding me" nan ma shiru babu amsa "are you ashamed to be seen with me?" Nayi sauri nace "No" "please just tell me why" sai da na dauki some seconds sannan na fara magana "I am just not ready for this, bana so in bata rayuwa ta, ina so in kara girma, at least in gama sec sch, am sorry ban gaya maka haka ba, i just don't want you to go" ya sake dago fuskata yace "look at me, I will never mess up your life, never. I love you and I will wait for you to be ready, no matter how long, kawai ina so in tabbatar cewa kina sona kema" sai kuma ya danyi dariya kadan "but tunda kin kasa fadar L word a gaba na dole in hakura da gyada kan" kunya ce ta kara kamani na cigaba da kokarin ture shi yana dariya, na hakura na barshi, sai da ya gama dariyarsa sannan ya sake rage murya yace "I missed you, please ki

Please Login or Register in order to submit comment