Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Abdulshakur. Zaman mu tare dasu Hafsat ya kara dankon zumunci sosai tsakanin zayed da sultan, dan zayed zama yayi tamkar brother din sultan tunda dama sultan bashi da brother. Ni kuma da Hafsat zumuncin mu ya kara karuwa muka koma tamkar twins. Duk da cewa gidajen mu daban ne amma komai a tare muke yi, Al'ameen ya saba dasu khairat sosai. Bamu dade da komawa England ba Ummee ta matsa mana lallai sai da na yaye Al'ameen aka mayar dashi Nigeria gurinta. Nan fa Sultan shima ya damu da rashin Al'ameen saboda ba karamar shakuwa suka yi ba, shima Al'ameen a can kullum sai rigimar neman Dad dinsa da Mom dinsa, amma Ummee taki dawo mana dashi a haka har ya saba da ita sai dai muyi waya dashi ko kuma idan munje gaishe su. Shekarun mu biyu muna karatu muka kammala, kuma Alhamdulillah mun samu sakamako mai kyau. Ranar passing out dinmu family din mu sunzo sosai, dan har Takawa sai da yazo taya ni murna. A lokacin da cikina wata bakwai, wanda aka tabbatar min twins ne a ciki. Wannan ya saka sultan yace ba zamu koma Nigeria ba sai na haihu, lokacin haihuwata yana gabatowa ummee ta dauko al'ameen suka taho gurin mu, a haka har na haihu, wannan lokacin kuma Alhamdulillah da kaina na haihu ba'ayi min aiki ba, amma fa nasha wahala ba karama ba, na haifi mace da namiji wadanda a take sultan yayi musu huduba da sunan ummee da na Takawa. Muna kiransu da Bassam da Basma. Gaba dayansu babu wanda yayi min kara, dan kamar Ummee da sultan suka dauko sak. Sultan harda yi min gwalo yana tsokana ta. Bayan haihuwar twins muka tattaro muka dawo Nigeria. Tunda muka dawo naga sultan yana ta kumbiya kumbiya, nasan akwai abinda yake boye min amma na kasa gane menene. Wani lokacin idan yana waya ina shigowa zai katse, da yawan fita da yake yi yanzu har weekends in ya fita tun safe wani lokacin sai magrib zai dawo kuma ya dawo min a gajiye, in na tambayeshi ina yaje kuma sai yace min yana gurin Takawa ko kuma yace gurin Daddy yaje, ni kuwa nasan daga Takawa har Daddy babu wanda zai gajiyar da shi. Tun ina dannewa har na fara damuwa, rannan yana shigowa ya kwanta yana ta juyi nazo na zauna na saka masa kuka, tashi yayi ya zauna yayi tagumi yana kallona ina ta rera kuka na, yace "wannan shagwabar ta mecece kuma?" Nace "ba kai bane kake fita kullum kuma kaki ka gaya min inda kake zuwa" ya matso kusa dani ya jawo ni jikinsa yace "My Love, na gaya miki ba wani gurin nake zuwa ba fa, most of the times ina gurin Takawa" nace "ni dai ban yarda ba, yanzu haka ma zance kake zuwa" dariya yayi sosai yace "zance kuma Moon? Where on earth do you get this Idea?" Nace "to bayan kullum in kana waya ma in ka ganni sai ka kashe?" Ya sake dariya yace "Love how many times zan gaya miki babu wata a gaba na bayan ke?" Nace "you are acting otherwise. Tun da muka dawo Nigeria kake boye min wani abu, kuma nayi nayi da kai ka samo min aiki kaki yarda, ya za'ayi ace ban samu aiki ba, ina ka taba ganin doctor ya rasa aiki, na gaji da zaman gida, I want to do something, it has always been in my dream in ga na zama doctor ina taimakawa mutane" ya saka hannu yana share min hawayena yace "wannan shi yasa kike zubar min da precious hawayen ki? To tashi ki saka hijab dinki ki bar su Bassam a gurin nanny din su ki zo muje in kaiki inda nake zuwa kullum, in ma budurwarce zaki gani" na tashi da sauri ina jin excitement na saka hijab dina muka fita. Hanyar office dinsa naga mun dauka, a raina nace 'so yake ya wayance ya nuna min office yake zuwa kullum har weekends'. Amma kuma sai naga mun wuce office din kadan sai muka tsaya a next building after it. Ya fito ya zagayo ya bude min kofa nima na fito, muka jingina a jikin mota muna facing wani sabon gini wanda ko fenti ba'a yi masa ba, hawa biyu ne sama da kasa, kuma babba ne sosai. Sultan ya dora hannunsa a kafada ta yace "nan gurin nake zuwa kullum, bam sani ba ko anan budurwar tawa take?" Na dan ture shi nace "to amma ai kai ai architecture ne, menene hadin ka da field work kuma?" Yace "wannan ba aikin office bane ba, this is personal". Ya juyo dani ina facing dinsa yace " da banyi niyyar gaya miki ba har sai aikin ya kammala, amma tunda kin fara tunanin zance nake zuwa, gwara in gaya miki yanzu" ya cigaba "I am building a hospital for you. Shine wannan, tunda muka dawo nake aikinsa kuma almost na kusa gama wa. Takawa ya bayar da order za'a sayo miki duk machines din da ake bukata a asibiti. You will be the MD, sai ki dauki sauran ma'aikatan ki da kanki" na dan jima ina kallonsa kafin in fahimci da gaske yake bada wasa ba. Ai kuwa wani tsallen murna nayi na dafe jikinsa, shi kuma ya biye min ya ringa juyi dani a gurin in circles muna dariya, mutane har daga mota lekowa sukeyi suna kallon mu,, daga baya ya ajiye ni muka shige cikin building din da gudu kamar wasu yara. Da gudu muka rinka zagayawa room by room, sai na fahimci ma kamar gurin yafi girma daga ciki akan ta waje. I can't believe all this is mine. Muna gamawa na rungume sultan a jikina ina hawayen murna nace "bansan da wanne bakin zan gode maka ba. Na gode Allah ya kara maka budi, Allah ya raya mana zuri'ar mu" yace "Ameen my love, you deserve this and much more" daga nan ya saka babban dan yatsansa yana zagaya lips dina, ba sai na gaya muku abinda ya biyo baya ba. Lol.
Daddy na fara kira na gaya masa, yace min ai already ya sani, sultan ya gaya masa tun kafin ya fara aikin. Na kira Mahdi na gaya masa abinda ya faru, nace "I will appreciate it if you will help me in running the hospital" yace "it will be my pleasure" sannan yayi min murna sosai tare da fatan alkhairi.
Ranar har dare ina ta waya ina gaya wa mutane, kowa sai murna yake min da fatan alkhairi. Washegari da safe na shiga cikin gida nayi wa Takawa da Ummee godiya, Takawa yana ta yi min dariya wai sai washe baki nake yi, yace "haka zaki ke yiwa patients din naki?" Na sake washe bakin ina dariya. Ummee tace "yanzu menene plan dinki akan asibitin?" Nace "burina shine in rage kudin komai a asibitin, yadda mutane talakawa suma zasu ke samun best medical care a cikin kudi kalilan" Takawa ya gyada kai yace "Zakiyi mamakin kuwa yadda Allah zai saka miki albarka a cikin sa. In mutum ya fara business, ko wanne iri ne, idan ka saukaka kudin shine Allah yake saka maka albarka, idan kuma ka zafafa sai Allah ya barka da dabarar ka, wacce babu inda zata kaika. Sai kiga an fara business amma ko shekara ba za'ayi ba ra rushe saboda babu albarka a ciki" Allah yasa mu gane.
Watanni uku bayan nan aka gama komai, duk kayan da akayi order sun zo an sassaka, na shiga na duba komai sannan na sake rubuta wani list din na sauran kayan da nake bukata, Daddy ne ya karba yace shima yana son a saka shi a ladan, babu jimawa aka kawo kayan gaba daya. Yaya Walid ne ya shirya min opening party a cikin harabar asibitin, kusan duk 'yan'uwa sunzo, har Hafsat da Zayed sai da sula zo da 'ya'yansu guda uku kyawawa gasu kusan kansu daya, nan ma sultan ya saka ta a gaba da tsokanar wai duk saurin ta gashinan mun kamo ta, uku take dashi kuma muma uku muke dasu, ta harare shi tace "neman in kulaka kake yi muyi, ni kuma bani da lokacin ka, besides ni bana kula kannena". Itama yanzu ta samu aiki a hospital din da zayed yake aiki.
Sai wajan sha biyun dare muka tashi, saboda hira da taki karewa. Muna zuwa gida na yiwa yara na wanka har Al'ameen da yake tare dashi muka je partyn kuma dare yayi dan haka bamu mayar dashi gurin Ummee ba. Na shirya su tsaf suka yi bacci saboda gajiya suma da suka yi. Na zauna a bakin gado ina kallonsu, kusan kamannin su daya dukkansu, ni dai a idona gani nake duk duniya babu kyawawan yara irin nawa, sai kuma wani tunani ya fado min a raina. Sultan ya shigo da sallama, na juya nayi masa alamar yayi a hankali kar ya tashe su, ya karaso ya zauna a kusa shima yana kallonsu, yace " Hmmm, they are beautiful, aren't they?" Nace "They are perfect" na tashi tsaye ina mammatsa masa kafadar shi da wuyansa, ya sauke ajjiyar zuciya yana kwanto da kansa a cikina, nace "wai Sweetheart yaran nan wanne tribe ne su?" Ya dan bata fuska yana kallonsu yace "oho, waya sani ne, menene ma'anar tribe din ma gaba daya? Menene kuma amfanin sa?" Nace "babu, bashi da wani amfani sai gurin rarraba kawunan al'ummar musulmi. Mutane sun kasa gane wani abu, we are atronger if we stand together, amma in muka rarrabu anan zamuyi falling easily. Yanzu kamar yaran nan, suna da jinin hausawa, larabara, fulani da buzaye, to wanne tribe ne su? A hakikanin gaskiya basu da tribe amma da mutum ya kallesu yasan they are perfect, ni a ganina mixed din su ne ya kawo perfection din su. Basu kadai bama, duk yaron da aka haifa a auratayya tsakanin two different tribes in mun lura zamuga yafi both tribes din kyau, wannan shi yasa duk duniya halfcast sunfi kowa kyau. Anya kuwa wannan ba wata hanya bace da ubangiji yake nuna mana cewa in muka hade kan mu a guri daya sai munfi samun kyakykyawar rayuwa akan in muka rarrabu?" Sultan ya jawo ni muka fada kan gadon yayi juyi ya mayar dani kasansa yace "maimaita abinda kika ce akan halfcast" nayi murmushi ina shafa fuskarsa nace "kunfi kowa kyau a duniya. Kafi kowa kyau a duk mazan dana taba gani a duniya, ba larabawa ba ba turawa ba, ba Africans ba koma wanne kabila ne banga wanda ya kamo kafar ka akyau ba" yana murmushi yace "ban yarda da wannan theory din ba miss psychologist. Saboda nasan ban kaiki kyau ba" nace "believe me Sultan ka fini kyau, ni macece kai kuma namiji ne. The most amazing thing is your skin, I love it" na fada ina saka hannuna cikin rigarsa ina shafa muscles din da suke rudani tun farkon gani na dashi. Ya juya fuskarsa yana kallon yaran da suke bacci a gefen mu, ya daga ni sannan ya dauke ni yace "let's go to my room sai ki maimaita abinda kika ce kiga yadda zan yi dake" muka fita muna dariya gaba daya.
Washegari ya dawo daga office ya tarar dani a palo ina feeding Basma, Bassam yana tsaye akusa dani yana wasa da toy car dinsu, yana jin muryarsa ya yar da motar hannunsa ya tafi da 'yar koyon tafiyar da suka fara yi zai tare shi, ya fadi ya sake mike wa, Sultan ya karaso da sauri ya daga shi yana juyi dashi a tsakiyar palon, Basma ta sake ni itama ta sauka daga jikina ta tafi, ita ma ya dauke ta yana tsalle dasu suna ta dariya, nace "to ni kuma fa?" Ya juyo yana kallona yace "naki special ne" sannan ya ajiye su a kasa ya durkusa a gabansu yace "albishirin ku, yaye ku za'ayi" na bata fuska nace "ai basu isa yaye ba, ka bari ko fifteen months suyi mana" ya karaso gaba na ya ajiye min wasu takardu, na dauka ina dubawa, naga takardun visa ne da kuma plight ticket zuwa Maldives, na mike da sauri na makalkale shi ina murna, ya daga ni sama nima irin yadda ya yiwa twins ya ringa juyi dani, yaran suka saki baki suna kallon mu, ya sauke ni yace "I promised I will take you back, didn't I? Gwara mu tafi yanzu tun kafin ki fara aiki ki zama busy. Amma ki sani, yanzu ba ki da ciki dan haka kiyi shiri na sosai" na harare shi nace "wancan zuwan ma da nake da cikin me aka fasa" yace "to wannan will ve double. You better get ready" na rungume shi kamar zan shige jikinsa nace "I can't wait, Darling. I love you so much Sultan" ya zagaye ni da hannayensa yace "I love you too, MyMoon".
The End
But remember, every ending is just another beginning.
Alhamdulillah .
Na sadaukar da littafin Maimoon ga duk wanda ya karanta shi. Ina fatan duk wanda ya karanta yaji dadi ko kuma ya karu da wani abun to yayi min addu'ah, Allah ya bani dacewa a duniya da lahira.
Littafin Maimoon kyauta ne, duk wanda ya sayar min ta hanyar bugawa ko kuma a document ya sani Allah yana kallonsa kuma zai tambayeshi.
Da akwai lessons da na saka a littafin Maimoon, wanda nasan in dai har mutum yana biye to zai karu da one thing or another. Amma babban abinda nake so mutane su dauka shine to not judge a book by it's cover, things are not always what they seem, duk mutumin da ka hadu dashi a rayuwa to there is a story behind him, kowa da akwai labarin sa, kowa kuma da akwai dalilin da yasa yake yin abubuwan da aka ga yana yi. Akwai mutane da yawa a duniya kamar Sultan, suna nan a cikin unguwannin mu da lungunan mu, deep inside them mutanen kirki ne sosai amma yanayin rayuwa shi ya mayar dasu yadda suke, wadansu zaka gansu suna shaye shaye, wadansu sun zama 'yan daba, wadansu ma sata suke yi, amma da zamu zauna dasu mu tambayesu labarin rayuwarsu da sai mun zubar musu da hawaye, ba wai zabin sune ya saka suka zama haka ba, rayuwa ce ta mayar dasu hakan. Babban abinda zamuyi musu shine mu nuna musu soyayya, no matter how small, you have no idea how mu much a little love can change someone's life. Allah yasa mu dace.
Godiya mai yawa ga dukkanin masoya littafin Maimoon, ba zan taba mantawa da soyayyar ku gare ni ba. Ban taba tsammanin Maimoon zai samu karbuwa irin haka ba, musamman saboda kasancewarsa littafi na na farko, na fara da zero followers na gama da over ten thousand followers. Alhamdulillah. Ku sani duk ina sane daku, nasan sunayen most of you, kuma duk comments dinku ina karantawa kuma ina jin dadi.
Maman maama novels na WhatsApp na matan aure, you guys are always making my days, jazakumullahu bi khair. Maman Ahmad da jama'arta, Surayya ta hannun daman Sultan da Hannatu ta hannun daman Ibrahim, ina fatan kun gaisa kamar yadda sultan da Ibrahim suka gaisa. Nafisa Usman, R-sulym, ummu khulsum, Aishas (we have many), Fatimas, Ummis, Hadizas, Umaira, Saiham, Yagana, Nafeesa, dama sauran wadanda ban kira ba duk ina godiya.
Jinjina ga Umar Faruk (sadauki) wanda shi ya kirkira kuma ya tabbatar da kafuwar both WhatsApp and Facebook groups na maman maama novels, I will forever be greatful. Hayatuddeen, Aisha Tafida, Dr MB, Fadila, Haleema yuguda, Amina, Aysha, Rabiat, Abu Muhammad, da sauran wadanda ban kira sunan su ba, ina godiya for keeping the WhatsApp group lively. Ina jin dadin programs din ku na dare, kuma ina karuwa sosai, Allah ya bar zumunci.
Jinjina ta musamman ga constant Facebook followers of Moon, musamman
Abdul A A Rasheed wanda zan iya cewa shine first fan dina kuma ya cigaba da bin littafin maimoon har karshen sa. Ahmad, Salahuddeen Dama, Sadiya Usman Aliyu,
Yagana Babakura, Fadyla Ingawa , Ummi Ummusalma,Zeeta Aliyu , Aisha Aysha Muhammad Deejarh Muhammad , Bashir Muhammad Rahama , Maimuna, Nafisat Usman Tafida, Jamila Jibril , Nafisat Saleh , Muktar Ahmad, Hadiza UssainAdamu , Abdoulmaleeck Saleh, mata mutanenmu na amana, Ummu Kaltume Aminu , eve mohd, Abdulmajeed,
Zainab M Alhassan , Barkhe, It's B Y Ibrahim, da sauran wadanda karancin lokaci ba zai bar ni in fadi sunan su ba, ba wai dan ban san dasu bane. Allah ya bar zumunci, Ameen.
Maybe zan cigaba da rubutu, may be not, amma ko da zan cigaba din to ba nan kusa ba. Kamar yadda rana daya na tashi na fara rubuta Maimoon haka maybe wata rana zan iya tashi in fara rubuta wani.
Nagode
Alhamdulillah.

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment