Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mike tsaye duk har sai da ya zauna sannan suka zauna suma tare da gaishe sa, ya amsa ba yabo ba fallasa sannan ya kalli Amir yace "Amir ko?" Amir ya gyada kansa, haka kawai yaga daddyn yayi masa kwarjini. Shima daddy ya karanta labarinsa da duk abinda Sultan yayi masa. Ya jima yana kallon Sultan wanda ya sunkuyar da kansa yana jiran abinda zaice, can daddy ya bude baki yace "Sultan, zaka iya dawowa nan gidan ka zauna a gurina?"



Episode Fifty Six : What You Sow

Sultan ji yayi maganar wani iri, sam ba abinda yayi tsammani ba. Ya jima kansa a kasa kafin yace "daddy bansan me zance ba" daddy ya gyada kai yace "I understand. Kafin ince zan baka Moon ko ba zan baka ita ba, dole ina so inga how far you can change, dan haka nake son chanza maka environment zuwa gurina. Amma da akwai sharadi, indai har ka amince zaka dawo gidannan dole zaka bi sharuddan zaman gidan nan, na farko babu yawo, zaka iya fita iyakacin cikin gari amma in dai zaka bar gari sai na sani kuma sai na amince, a cikin garin ma duk inda kake in lokacin cin abinci yayi zaka dawo gida saboda tare muke cin abinci a gidannan breakfast lunch dinner duk tare muke ci, kuma duk inda kake 9pm tayi maka a gida, babu wayon dare. Sanna the most important thing, ba zanyi tolerating koda single drop of alcohol a gidan nan ba, kuma koda a waje kasha ba'a gidan nan ba zan sani kuma ni kadai nasan hukuncin da zan yanke maka. I also want a total change of friends daga gareka, Amir will still be your friend of cause amma shima in naga bashi da niyyar chanza hali dole zan raba ka dashi, ga Walid nan shine sabon friend dinka zan kuma gaya masa kar inji kuma kar in gani a tsakanin ku. Abu na gaba kuma gida na ba gidan 'yan dambe bane, ko da wasa kar inji ance ka daki wani a cikin 'yan aikin gidan nan, tsakanin ka dasu ya zama girmamawa da mutunta juna. Next thing is you will need a change of wardrobe, saboda kamar yadda nake yawo da Walid haka zan ke yawo da kai kuma ba zan ke shiga da kai cikin mutane da wannan shigar a jikin ka ba. Wadannan sune sharudai na, in kaga zaka iya yarda dasu then you are one step to getting Moon, in kuma kaga ba za ka iya ba shikenan sai ka chire ta a ranka Allah ya hada kowa da rabonsa" da sauri sultan ya dago yana kallon daddy wanda shi kuma ya dora kafa daya kan daya ya daiki jarida yana kokarin budewa, alamar ya gama magana kenan. Sultan wani iri yake jinsa, wani irin feeling mixed with kunya, tunda yake ba'a taba ce masa 'yi kaza ko kar kayi kaza ba' amma yau gashi daddy ya wanke shi tas kuma a matsayinsa na surukinsa to be. Da sauri Sultan yace "daddy na yarda, ni kam na yarda da duk sharudan" daddy ya ajiye jaridar yace "madallah da wannan hukunci, gobe da safe zanje fada da kaina zan nemi alfarmar dawowarka gidan nan a gurin mai martaba sarki" Sultan ya girgiza kai yace "ba zai ce komai ba, ba zai noticing ma bana gidan ba" daddy yace "whatever, hakkin sane a gaya masa, kuma ni da kaina zan gaya masa. Yadda muka yi dashi Walid zai kira ka ya gaya maka. You can go now" Sultan ya kasa tashi, shi maganar bata ishe shi ba, shi da za'ayi ta masa fada so yake yi, can ya dan taba Amir yayi masa rada "ask him ina Moon take" Amir ya dan yi gyaran murya yace "daddy ko zamu samu ganin Moon kuwa" ba tare da ya kallesu ba yace "you will see her when the time is right" still sultan bai tashi ba, he have one more question, ya matsa gaban daddy sosai yace a hankali "daddy, dan Allah a cikin informations din da kake dasu, I want to know, did my parents.... " sai kuma ya kasa karasa maganar, daddy ya ajiye takardar hannunsa sa yace "ina jinka" sultan ya hadiye yawu yace "did my parents marry before...... Did they marry kafin su haife ni?" Daddy ya jima yana kallonsa ya kasa magana, tausayin yake ji har cikin ransa, jin daddy bai yi magana ba yasa Sultan ya mike tare da cewa "thank you daddy, dama ina so ne kawai in sani, I always thought wannan shine dalilin da yasa babana baya sona" daga haka yayi hanyar fita, har ya kai bakin kofa daddy ya kira sunan sa, ya tsaya ba tare da ya juyo ba saboda wani irin zafi da yake ji a ransa, daddy yace "sultan iyayenka sunyi aure kafin su haife ka, you are a legitimate child, abinda ke tsakanin ka da babanka is totally different from haihuwarka" Hmmm

Kamar yadda daddy ya fada haka ya aikata, washegari yaje fada akayi masa iso gaban mai martaba sarki, bai yi tsammanin zai gane shi ba amma sai yaga ya tare shi sosai da fara'a da wasa da dariya yace "Muhammad baka da kirki, ace kana garin nan da iyalinka amma ba ka zuwa mu gaisa? Kasan ni nauyi yayi min yawa bazan iya ziyarar abokanai ba" daddy yayi murmushi yace "Allah ya taimake ka ai ni ma ba zaman garin nake sosai ba, kuma in dai nazo to abubuwa sukan yi min yawa har sai na koma. Amma ayi min afuwa, in sha Allah zan ke lekowa lokaci zuwa lokaci" Har palon da yake barkar manyan bakin sa ya saka aka shiga da daddy, nan suka zauna gaba dayan su akan carpet suka fara hirar yaushe gamo da labarin karatun su da friends dinsu wadanda yanzu kowa ya kama gabansa. Daddy yayi mamaki sosai yadda yaga takawa ya zage sosai yana hira da dariya, saboda shi ya dauka maganar da zasuyi formally zasu yi ta maybe a gaban mutane ma, ashe dai Sadiq din is still the same person da ya sani kawai dai nauyi ne ya hau kansa yanzu. Anan suka zauna har aka kawo musu lunch sam daddy bai lura da yadda lokaci ya tura haka ba, he totally can't believe cewa wannan elegant mutumin shi yayi raising Sultan. Da kansa mai martaba yayi serving dinsu a plate daya suka ci, suna cikin ci Abbas ya shigo a nutse yazo ya gaishe su sosai sannan ya fada wa babansa sako cikin girmamawa ya fita. Daddy yayi noticing wani abu, Abbas totally baya kama da Sultan, ba zaka taba cewa 'yan uwa ne ba. Sai da suka gama sannan daddy ya gyara zama yace "Allah ya taimaki sarki magana ce ta kawo ni. Akan dan mu Sultan" daddy ya fada yana kallon fuskar takawa, abinda yayi tsammani kuwa shi ya tarar, just mentioning sunan sultan ya goge dukkan fara'ar dake fuskar takawa, komawa yayi kamar bai taba dariya ba. Yace "Wani abun yayi?" Daddy yace "babu abinda yayi ran sarki ya dade, ina neman alfarma ne in da hali ina so ya koma gida na da zama" Takawa yace "saboda me?" Daddy yace "ba wani abu kawai mun hadu da shine sai naga kusan sa'an yaron wajena ne walid shine sai naga ina sha'awar in hada su a gurina for sometimes, in ka amince of cause" Takawa yayi shiru yana shan lemon hannunsa, har daddy ya fitar da ran cewa ba zai yi magana ba sai kuma yace "you can do with him as you wish. Kawai dai ka tabbatar duk abinda ya aikata maka kai ka jawo mu babu hannun mu a ciki, kuma ka tabbatar duk abinda yayi kar ka danganta shi da mu" daga haka ya ajiye cup din hannunsa ya mike tsaye yace "in ka kammala da akwai servants a waje zasu raka ka motar ka. Na gode da ziyara Allah ya bar zumunci"
I
Da yamma Sultan yaji wayar Walid da sakon sarki ya masa maganar daddy, Sultan sam ya kasa tantance me yakeji a ransa, few things dinsa ya dauka ban da kayan sawa tunda daddy yace baya son irin su. To shi yanzu ina zai iya saka wata shadda ko yadi ne kam. Bashi ma da tailor. Yana zuwa gidan ya tarar da walid da Habeeb suna jiransa a compound, direct part dinsu suka wuce dashi fuskokinsu babu yabo babu fallasa dan sukam sam basa murna da wannan hukuncin na daddy. Four bedrooms ne dama a part din, sai palo mai hade da dining duk da dai ba mafani suke da dining din ba sai dai in bakon da ba za'a shiga dashi main palo ba. Walid ya bawa sultan key din daki daya da kuma spare key din palon. Sultan ya bude dakin ya shiga, ba laifi yana da girma, da gado da dan karamin closet sannan sai toilet. Yana gama duba dakin ya fita yana tambayar ina masu share share aka nuna masa su yace "dan Allah aron kayan cleaning nake so" da mamaki suke kallonsa, suka ce "ai mu zamu gyara maka" ya girgiza kai yace "thank you, zanyi, ba wani abu" Sultan sam bai yarda wani ya gyara masa dakin saba saboda gani yake ba za'a taba yi masa dai dai ba, tunda ya fara aiki bai gama ba har magrib, sannan ya shiga toilet yayi wanka ya chanza kaya ya fito da sauri, yana fitowa yaji dad yana cewa a kirashi su tafi masallaci, tare suka yi sallah suka dawo gida, suna zuwa suka zarce main palo, shi dai Sultan duk wani iri yake jin sa, yana zuwa masallaci wani lokacin amma bai taba zuwa tare da mahaifinsa ba ballantana ace wai harda siblings. A palon suka tarar an jera abinci a dining amma sam babu mommy, basu yi magana ba saboda kwana biyun nan haka take yi, kuma daddy ma baya son su hadu da Sultan har sai yayi mata magana da kansa. Suka zazzauna a dining din suna kallon kallo, can daddy yace "Sultan ai sai kayi representing Moon, kayi serving din mu" nan da nan sultan ya washe baki har kunne, ance yayi representing Moon, ya mike har da nade hannayen riga ya fara lafta musu abinci, walid yayi dariya yace "wannan uban abincin duk kana tunanin zamu cinye?" Sultan yace "why not?" Sai da kowa ya rage nasa abincin amma sultan ya chinye nasa tas. Daddy ne ya fara tashi ya koma palo, sultan ne na karshen gamawa, nan ya fara kokarin kwashe kaya, Habeeb yace masa "ka bar shi fa, za'a kwashe ai" shi Sultan ya saba da yiwa kansa komai, tunda aka kaishi america shi yake yiwa kansa komai, daya dawo Nigeria ma haka. Ya karaso palon, har zai zauna sai kuma yaji ajikinsa kamar zai shiga hurumin da ba nasa ba, sai ya mike zai fita, yana jin ba dadi a ransa, daddy ya kira shi ya dawo ya zauna yace "ina maganar kayan sawa da muka yi da kai?" Sultan ya dan bata rai yace "daddy ni ban taba dinki ba, ban masan inda ake saida yadikan ba ballantana wani tailor, amma in na samu zanyi" daddy ya kalli walid yace "gobe ka kai shi gurin tailor din mu ya auna shi, sai kuma ku shiga kasuwa kuyi siyayya" sai kuma ya juya gurin sultan yace "zaka iya ci gaba da saka kananan kayan ka a gida, amma duk sanda zamu fita ina so in ganka da manyan kaya da hula" sultan ya shafa kansa, lallai akwai rigima kenan, shi kam rabon da ya saka traditional hula tun kakansa yana da rai. Daddy ya juya kan su walid yace "ga Sultan nan, ina so ku rike shi tamkar shima dana ne da baya gurin mu amma yanzu yazo, kar inji kar in gani a tsakanin ku" duk suka amsa. Daddy ya sake cewa da Sultan "yi min bayani akan yadda kake gudanar da aikin ka" nan sultan yayi masa bayanin yadda yake yi, daddy yace "abinda za ayi yanzu shine, head office zaka bude, ka dauki ma'aikata sosai, ka saka wa gurin suna yadda zaka ke samun contract sosai. Na duba ayyukan ka naga suna da kyau sosai dan haka nima zan kara yi maka advertising dan kake samun contract a projects din government. Ina ganin hakan shi zai kara rage kama yawo, in ka samu abinyi zaka fi zama a guri daya" sosai sultan yaji dadi, babu wanda ya taba bashi shawara akan me zaiyi da rayuwarsa ko aikinsa. Ji yake yi wata soyayyar daddy tana shigarsa. Daga nan suka fara hirar su abin sha'awa, a tsokani wannan2, har mamaki sultan yake dama haka family yake? Dama haka uba yake a cikin 'ya'yansa?

Bayan sun tashi daga hirar sunyi sallah isha daddy ya hau saman su, dakin mommy ya shiga ya tura kofa, tana zaune tana aiki a computer, taji shigowarsa sarai amma bata dago ta kalleshi ba, a ransa yace 'wai ita menene problem dinta ne?' A bakin kofar ya tsaya yace "Fatima, ina so in sanar miki cewa Sultan ya dawo gidan nan da zama" zumbur ta mike har tana ball da system din gabanta ta karaso kua dashi da sauri tace "Sultan fa kace?" Sai kuma hawaye "haba dear, ya zaka dauko yaro kamarsa ka hada shi da yaran mu, so kake suma ya bata mana su kamar yadda ya so ya bata Moon? Dan Allah kayi hakuri idan purnishing dina kake dan na daukr Moon, wallahi zan dawo da ita, please ka kore shi daga gidan nan" daddy ya girgiza kansa yace "bazan taba korarsa ba sai dai in shine da kansa yace zai tafi, wanda bana jin zai ce haka, kuma badan kinyi min laifi bane yasa na kawo shi nan ba, a'a nayi haka ne dan naga wani chance ne na samun lada Allah ya dora akan cinyata, shi da na kowa ne, baka san wane ne zai ji kanka ba wata rana, kuma ita rayuwa duk abinda ka shuka shine zaka girba, ina so in shuka alkhairi yadda ko bayan raina zuri'ata zasu girbi alkhairi na. Ban gaya miki ba har sai da ya dawo saboda ina son kini zafin da naji nima sanda baki gayamin kin dauke moon ba har sai da kika aikata din. Yanzu bazan matsa miki cewa ki dawo da ita ba har sai na tabbatar da changes din da nake so in gani agurin sultan tukunna" daga haka ya juya yayi tafiyarsa. Mommy ji tayi gaba daya duniya tayi mata zafi, lallai daddy is even softer and weaker than she thought. Amma babu komai, ta tabbatar cewa Sultan will teach him a lesson. Ita kuma ba zata dawo da Moon ba har sai daddy ya yi learning lesson a gurin sultan tukunna.

Cikin sati daya Sultan ya warware a gidan Ambassador MD. Ba laifi sun fara sabawa da su Walid, in da suke jinjina masa akan tsaftarsa dan gaba daya part dinsu ya chanza fasali kamar ba shi ba, har palon sai da yayi rearranging ya chanja labilaye da carpet. Daddy ya samo masa building din da zai bude head office dinsa, wanda ya fara dauka aiki shine Amir, tunda dama tare suke aikin su, nan da nan ya zama busy wajen gyaran gurin da interviewing maaikata, sai yanzu ya kuma gane abinda daddy yake nufi, dan in yana aiki sam mantawa yake yi da komai ballantana har yayi tunanin shan giya, ko a gida kuma har yanzu yana bin shawarar moon ta karatun Alqurani duk sanda ya ji yana son alcohol. Shi kansa yana jin chanji akansa, dan nutsuwarsa ta karu sosai. In dar har baya wajen aiki to suna tare da daddy, dan duk inda daddy zaije tare suke zuwa dashi da walid, har gurin manyan mutane, nan ya fara koyon saka manyan kaya da yadda ake gaishe da manyan mutane. Rannan har gurin president suka je, kuma he found it very interesting dan babu wanda yayi masa kallon wulakanci babu wani security daya hana shi shiga ballantana suyi rigima. Kuma wani abu da daddy yake yi shine, duk inda suka je sai ya gabatar da sultan a matsayin babban dan sarkin abuja, duk sai sultan yaji banbarakwai in yaga mutane suna bashi respect

A gida kuma malami daddy ya dauko na karatun addini, bai ce saboda Sultan ya dauko ba sai yace yaga duk kowa a gidan ya watsar da islamiyya dan haka ga malami nan duk weekend zai ke zuwa za'ake karatu, har maaikatan gidan duk haduwa ake ana daukan karatu. Nan sultan yaga chance dinsa ya dauko alquranin sa ya fito, surorin daya manta nan duk suke bi suna tilawa tare da malam. A hankali karatunsa yake dawowa. In akayi dori ranar assabar ran lahadi kuma sai ayi tafsir, ko ayi karatin sauran littattafan addini, sai abin ya koma kamar discussion, kowa ya fadi abinda ya sani ayi masa gyara, in mutum yana da tambaya yayi. Sultan kam ya bude kunnuwansa sosai yana daukar karatu. Matsalar sultan yanzu daya ce, he terribly misses Moon. Kullum yana so ya tambayi daddy labarin ta amma baya so daddyn ya bata rai ko yaga gazawarsa. Kullum da daddare sai ya dauko bathrobe dinta daya dauka a toilet a america, da ita yake bacci yana jin kamshinta. Idan yana zaune shi kadai kuwa sai dai yayi ta kallon pictures dinsu da videos dinsu yana ta murmushi. She really is a Moon, her arrival in his life have brought light to his darkness.

Ina ma iyayen mu zasu zama kaman daddy? Allahumma Ameen.


Episode Fifty Seven : What You Sow 2

A 'yalleman kuwa tunda Munir yayi wa Hajja waya da sassafe ya hada mata karya da gaskiya ya gaya mata. Suna gama wayar ta fita daga part dinta ta tsaya a compound ta rafka wani uban salati "na shiga uku ni zuwaira yau wanne mugun labari zanji haka" a tare da baffa da inna suka fito daga part dinsa suna tambayarta "lfy? Me ya faru? Waye ya mutu?" Ita kuwa kuka take tana fyace majina da bakin zanin ta, "dama babu abinda ban fada ba aka ki daukan magana ta saboda bani na haifi muhammadu ba kuma shine dan gatan gidan nan, dama gata ai mugun abu ne, babu abinda yake haifarwa sai nadama. Wanda duk baiji bari ba ko ai zai ji oh'oh" inna tana jin zancen muhammadu ta ja da baya ta tsaya tana jiran taji alkaba'in da zai biyo baya. Baffa ma bari yayi sai da hajja ta gama sambatun ta sannan ya kuma tambayarta "me ya faru da muhammad din" Hajja ta duba taga duk yaran gida sun taru a compound suna sauraren abinda ake yi sannan tace "yaran nan babu yadda banyi ba akan ayi musu aure akaki, aka nuna min ban isa ba, to yanzu gashi nan abinda ake gudu ya faru. Manniru ne yayo min waya dazu hankalinsa a tashe, yace tunda yarinyar nan ta dawo kasar nan ta juya masa baya, in yaje gidan nasu sam ba'a barin shi ya ganta, in ya kira ta a waya bata dauka, to jiya da daddare wajan karfe daya ya fita neman abinci saboda yaje gidan sun hana shi abinci shi kuma yunwa ta dame shi, kawai yaga yarinyar nan a titin Allah tana yawo da dan skirt, ta sha giya tayi mankas ko tafiya bata iyayi sai wadansu maza ne suka rirriketa, shima kansa da kyar ya gane ta, kuma ya kira walid ya gaya masa, ashe sun riga sun san halin da yarinyar take ciki shi yasa basa barin ya ganta. Daya bisu gidan ya na tada maganar saboda ayi wa tubkar hanci sai walid da habibu suka taru suka yi masa dukan tsiya suka ce in dai ya sake ya fada wa mutane sai sun nakasa shi" wani irin jiri inna taji yana neman daukan ta, wannan wanne irin sharri ne munir ya shirya wa maimunatu? Palon ta ta koma ta zauna kanta yana bala'in sara mata, yaran gidan kuwa tunda suka gama jin abinda hajja tace suka fara fita daya bayan daya suna shiga makota kai rahoto, baffa kasa cewa komai yayi dan shima jirin ne yake dibansa, Ma'aruf dan autan hajja wanda kuma shi kadai ne ya rage a gidan ne yayi saurin dauko kujera ya zaunar da baffa. Sai da baffa ya mayar da numfashin sa sannan yace "hajja kin tabbatar munir ba karya yayi miki ba?" Hajja ta matso kusa dashi tace "yaya zaiyiwa yarinyar da yake so karya? Ita fa ya zaba ta zama uwar 'ya'yansa ta yaya zai yi mata sharri kuma? Ban taba ganin so na gaskiya irin wanda yaron nan yake yiwa yarinyar nan ba, duk da abinda ya gani da idanuwansa fa cewa yayi shi so yake ma a gaggauta auren ko Allah zai sa auren ya gyara ta" still zuciyar baffa taki yarda da maganganun hajja, yana kallon fuskar maimunatu a zuciyarsa, duk acikin jikokinsa yana son 'ya'yan muhammadu, kuma duk a 'ya'yan muhammadu maimunatu ta daban ce, ga tarbiyya, ga ladabi, ga fara'a, ga shiga ran mutane sannan uwa uba ga son 'yan'uwanta. Sam bata da girman kan wai babanta wani ne, duk sanda tazo sai ta zaga 'yan'uwa kai hatta 'yan aikin gidan nan kawayenta ne dan wani lokacin a cikin su zai ganta tana wasa. Hajja ta tankwashe kafar ta ta cigaba da zuba zance "ya gayamin ai ba laifin ta bane, wani yaro ta hadu dashi lalatacce shine ya bata ta, su kuma iyayen sun dauki son duniya sun dora mata shi yasa suka kasa raba su, dan ce musu tayi ko yanka ta za suyi ba zata rabu da yaron ba. Ni dai shawara ta shine, ka kira muhammadu ka gaya masa zama maza ya kawo mana yarinyar nan gurin mu, tana zuwa sai mu sata a lalle ayi auren nan kowa ya huta. Shi kuma wannan yaron da yace yaji ya gani zai aure ta a haka Allah yayi masa albarka" baffa da har yanzu kansa bai gama juya masa ba ya aika ma'aruf ya dauko masa wayarsa, amma maimakon ya kira muhammadu kamar yadda hajja tace, sai ya kira Aliyu, aliyu yana dauka ko gaisawa basu yi ba yace "Aliyu kaga abinda ka jawo mana ko? Taurin kanka ne ya hana ayi auren nan da yanzu duk wannan abin bai faru ba, to kasani ni babu ruwana, tunda kai ka jawo sai kasan yadda zakayi ka warware" yana kaiwa nan ya kashe wayar ya mike ya shige dakinsa, hajja ba haka taso ba dan tasan Aliyu sam ba zai taba goyon bayan munir ba, saboda kamar yadda take fada tace ya tsane shi saboda ba uwarsu daya da wanda ya haife shi ba. A bangaren inna kuwa tana shiga dakinta ta dauko wayarta ta kira mommy, sai da ta katse ta sake kira sannan mommy n ta dauka, itama ba tare da sun gaisa ba tace "Fatima me ya faru tsakanin manniru da maimunatu?" Cikin inda inda mommy tace "inna babu komai wani abu akace ya faru?" Inna ta bata rai sosai tace "Fatima dani fa kike magana ba da wani ba, cewa nayi me ya faru tsakanin munir da moon?" Mommy kuma sai kuka, sai da tayi me isarta sannan ta bawa inna labarin duk abinda ya faru a lokacin. Inna salati ta saka tace "amma fatima ya za'ayi ace yarinya tana tare da saurayi har tsahon shekara guda amma ke a matsayinki na mahaifiyarta baki sani ba?"Mommy tace "inna wallahi nasan tana tare da wani, amma bansan ko waye shi ba, da nasan yaron nan ne wallahi da tuni na raba su. Ita yarinyar nan kinsan halinta, har cikin zuciyarta gani take taimaka masa take yi" nan inna ta gaya mata duk abinda hajja take fada, mommy sai da ta sake wani kukan sannan tace "wallahi inna ba haka akai ba" kafin ta cigaba da magana inna ta katseta tace "na sani ai, ni nasan maimunatu, nasan abinda zata aikata da wanda ba zata yi ba. Yanzu dai zamu jira muji abinda baffa zai ce" Suna gama wayar uncle

Please Login or Register in order to submit comment